da juna?”.
“Nabar komai a hannun UBANGIJI, shine mai sarrafa zuciyoyi a yanda yaso ai Zulfah, ina ji a raina zata canja”. RK ya bata amsa yana haɗiye damuwarsa. Aneesa ce tai ɗan murmushi, har cikin ranta tausayinsa take ji. Murya ta kwantar cike da son kwantar masa da hankali ta ce, “In sha ALLAHU kam tunda ka dogara da ALLAH zakaci riba. In dai Maanal matarka ce kuwa sai ka aura, itama nasan ba tana yin komai danta wulaƙantaka bane, akwai dai wani dalili, saboda duk wanda yasan Maanal sani na gaskiya yasan bata da wulaƙanci, na nesa da itane kawai ke mata kallon girman kai amma sam ba haka bane ba wlhy”.
“Nima shaida ne Aneesa, shiyyasa nake mata uziri”.
“Nagode sosai daka fahimci haka RK. Bari muje mu ƙarasa gida muma, mun gode sosai da ƙoƙarin ka, ALLAH yabar zuminci ya saka da alkairi. Mun tasoka tun daga Jos”.
Murmushi ya saki mai sanyi. Sai kuma ya girgiza kansa tare da shafa kwantaccen sajensa ya ce, “Babu damuwa. Dama Abuja zanzo ai. Ku ba nan anguwar kuke ba kenan?.”
“Eh anguwannin duk daban-dabanne”. Zeezah ta bashi amsa.
“Oh to ku muje na kaiku ai har gida kuma. Kunga idan na tashi dawowa saina tattaroku dan ƴar darun nan tawa al'amarin ta sai da ku a kusa”.
Dariya sukayi gaba ɗaya. Babu musu suka koma motar yaja suka bar anguwar. A gidan su Zezaah duk suka ce ya saukesu. Dan basu da nisa da Aneesa da ƙafa ma zata ƙarasa. Su Zeezah dai ba masu kuɗi bane ba. Amma akwai rufin asirin ALLAH. Da alama ƴar darun tasa ta fisu komai dai kam. Godiya suka masa da sake bashi haƙuri. Ya tabbatar musu babu komai sai ya dawo dubasu zuwa weekend. Zai kuma kirasu a waya in sha ALLAH. Daga haka yaja motarsa ya wuce...
★★★★★
A hankali ta jingina da jikin gate ɗin ƙwalla na cika mata ido. Dauriya kawai takeyi, amma tausayi RK ke bata matuƙa. Ta jima da fahimtar irin ɗunbin soyayyar da yake mata a cikin idanunsa. Sai dai tasan bazata iya bashi abinda yake buƙatar ba. Kota bashi ma zata cutar da shi ne kawai dan bazai taɓa samunta yanda yake huƙata ba. Dan zuciyarta ta jima da mutuwa. Mutuwa irin wadda mushenta ma baida daɗin kallo. A zahiri take Maanal, amma a zuciya tuni ta mutu, ta mutu babu ita a wannan rayuwar... RK na tuna mata abubuwa da yawa a rayuwarta da sam bata son tunawa, shiyyasa akoda yaushe take yakicesa a jikinta ta ƙarfin tsiya. Amma shi ya kasa fahimtar akwai wani ciwo ne a zuciyarta da ya jima da raunata ta ta yanda babu wani ɗa namiji da zai sake morarta.....
Raff-raff!! Sautin tafi da dariya ya sata dawowa hayyacinta. Hannu ta kai ta share guntun hawayenta kafin ta kai dubanta ga mai dariyar da basai an mata ƙarin bayani ba tasan Huznah ce. Ita ɗince kuwa. Ƙyaƙyƙyawar budurwa fara doguwa san kowa ƙin wanda bai samu ba. Zata girmeta a shekaru, girma ma bana wasa ba dan Huznah zata iya zama kusan sa'ar babbar yayarsu duk da dai ita yayar tasu zata iya girmarta....
“Agola kafi ɗan masu gida. Wato iskanci yayi lagwada har ba'a so dawowa gida ba kenan?”. Huznah ta faɗa tana watsa mata kallon wulaƙanci.
Idan gate ɗin da ke kusa da su ta motsa to Maanal ta tanka. Dan kuwa daga kallo ɗayan nan bata sake dubar ko sashen da Huznah take ba taja akwatinta tai gaba cikin tafiyarta mai sanyi da tarin nutsuwar da kowa ke ɗauka iyayi da yanga ce. Sai dai kuma hakan a gareta normal ne. Dan tun ma tana tashen rashin jinta tafiyarta mai sanyi ce.
Ba ƙaramin takaici rashin tankawar ya saka Huznah ba. Cikin haushi ta lailayo ashariya ta maka ma Maanal. Sai dai yanzun ma bata samu amsa ba, Maanal ɗin kuma bata waiwayo ta dubeta ba harta shige ɗaya daga cikin ɓangarorin gidan. Domin ɓangare har biyar ne a gidan ciff kasancewar matan mai gidan uku ne. Sai sashensa, sai kuma na samarin yaransa. Ƴammatan dai kowacce tana sashen uwarta ne....
Shigowarta sashen nasu da abinda ta taras ya wanke mata gaba ɗaya damuwarta. Dan kuwa taci karo da ƴan uwanta biyu da yaransu duka sunzo gidan domin dawowar tata kawai. Ai tuni ta watsar da damuwar RK data Huznah suka rungume juna. Sosai suke matuƙar ƙaunar junansu ta yanda idan ka gansu kai kanka sai sun matuƙar burgeka.
“Amma Didi kikace min ke bazaki wani zo tarbata ba”.
Dariya wadda ta kira da Didin tayi tana mai dungure mata kai da faɗin, “Naƙi zuwa babarki ta ƙulaceni Auta”.
A tare suka kwashe da dariya, dai-dai nan wata dattijuwar mata cikin kwalliya ta fito daga wani lungu mai nuni da hanyar kitchen ne dan hannunta riƙe yake da wani ɗan bowl. Tuni Maanal ta saki yayunta ta nufi matar da sauri ta wani daka tsalle ta rungumeta. Dariya yayunta da yaransu suka sanya. Yayinda matar ke faɗin, “Oh ya ALLAHU jama'a sai yaushe Maanal zata girma ne? Yanzu idan kika karyani fa?”.
Cike da shagwaɓa, tare da sake shigewa jikin matar ta ce, “Ni dai bazan taɓa girma ba Ammie. Nayi kewarki fiye da kowa da komai. I really miss you Ammie na”.
Ƙaramar dariya Ammien ta saki mai ƙayatarwa, tare da sake rungume ɗiyar tata a jikinta tana mai sumbatar kanta da faɗin, “Nima nayi kewarki sosai Maanal. Congratulations my Auta, yau dai finally an gama boko.”
“Kai Ammie dama ana gama boko?”. Ta faɗa cikin dariya mai ƙayatarwa da mutane da yawa basu san tana yi ba. Itama Ammien dai dariyar ta sake yi, sai kuma ta ɗagota tana mai ƙare mata kallo da ƙyau. “Auta duk kin sake rame min, kina lafiya kuwa?”.
Kanta ta kwantar a jikin hannun Ammien data riƙe, sai kuma ta amsa da, “Lafiya Lau nake Ammie. Kewarki ce kawai ta hanani sukuni”.
“Oh wai kin damu mutane da kewar Ammie kawai. Kina nufin mu bakiyi kewarmu ba ne Auta?”.
“To Sarkin kishi, ALLAH Ammie ban taɓa ganin mai kishinki sama da Didi Amal ba. Kijifa dan ALLAH, nayi kewarki itama dole sai nayi kewarta?”.
Jefota da filo Amal tayi, da sauri ta kauce tana murmushi. Yayinda Didi Shahidah da Ammie da yaransu ke musu dariya..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣4️⃣
______________
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
________________
.......Bayan an natsa da murnar dawowar tata da gaishe-gaishe Ammie tace ta wuce ta gaida mutanen gidan. Fuska ta ɓata kamar zatai kuka, sai kuma ta shiga roƙon Ammien akan dan ALLAH ta barta taje tai wanka ta canja kayanta tukunna. Ammie zata ƙi su Amal suka tayata roƙonta. Dole ta barta taje ta fara wankan sannan, yayinda su kuma suka cigaba da aikin shirya abinci dan dama girki suke sanda ta shigo.
Ɗakin da yake mallakinta ta shiga, an gyarashi tsaf ga ƙamshi mai daɗi na turaren da take matuƙar so na tashi a cikinsa. Sosai ɗakin ya haɗu, sai dai haɗuwar tasa baisa ta taɓa jin daɗin zaman gidan ba. Kawai dai tana zaune ne saboda mahaifiyarta na'a cikin gidan ne. Duk kuma inda Ammie take rayuwa koda a dokar daji ne itama zata zauna ta rayu saboda a duniya bata haɗa komai da soyayyar da takema mahaifiyarta ba. Ita ɗin dabance a zuciyarta. Idan tace daban tana nufin daban a cikin dukan daban. (ALLAH ka gafartama iyayenmu, wanda suke raye ka bamu ikon ƙyautata musu😭🙏).
Jacket ɗinta ta fara cirewa, tare da ƙurama rigar ido tana mai sakin murmushi. Finally yau ta gama sarvese, duk da Ammie tace boko ta ƙare, itafa a gareta yanzu ne aka saka ɗanba, sai dai Ammie tayi haƙuri amma sai taga ƙarshen biro in har ana ganinsa. Sanin yaran can zasu iya shigowa su fara addabarta yasa taƙarasa zame kayan nata da sauri-sauri ta ciri towol daga Waldrop ɗinta fari tas ta ɗaura. Bayin ta nufa dan tasan duk abinda zata iya buƙata Ammie ta saka mata shi kasancewar ta jima bata gida. Dan watanni biyar kenan bata zo ko weekend ba. Tunma data wuce sarvese sau ɗaya tazo gida, ɓacin ran data gumtsa a zuwan yasa tai alƙawarin ƙin sake zuwa har sai ta kammala. Alhamdullah kuma gashi sai da ta kammala ɗin.
Wanka tayi na gaske. Dan sai da ta tabbatar ko'ina na jikinta ya mata yanda take so sannan ta fito tana raɓar ruwa da ƙamshin shower gel ɗin ta mai shegen daɗi daya gauraya da na sabulunta da turaren wanka. Maanal tasan sirrin gyaran jiki da kula da jikin ma. Dan yarinya ce ƴar ƙwalisa akwai son gayu. Damma ba Maanal ɗin da bace data taso da shegen son kwalliya kamar ƴar aljanun. Tana tsaka da shafa mai Amal ta shigo. Cike da tsokana ta ƙaraso gareta tana faɗin, “Uhm kaga ƴar ƙwalisar gidanmu Autar Ammie. Irin wannan ƙamshi haka kamar zaki tashi gari”.
Murmushi mai sanyi Maanal ta saki da ɗan girgiza kanta tana ajiye man hannunta data matsa. Wanda ta matsa ɗin ta fara shafawa a fuska tana faɗin, “ALLAH Didi sai kisa a rataye mutum a tsakiyar kasuwa. Daddyn su Safnah na haƙuri dake gaskiya. Yanzu mine abin wani ƙwalisa anan daga shafa mai dai sai wanka. Ni ko fauda bazan shafaba ma”.
“A'a wlhy dole ki shafa. Zakije gaida waɗan can ƴan tsirkun ai sai kin cakare. Dama ga ɗan mutuminki yazo garin, dan muna shigowa da shi na fara cin karo a harabar gidan nan ɗazun”.
Cak Manaal ta dakata daga shafa man da take zuciyarta na wani irin motsawa da ƙarfi, a take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Sai kuma ta fara haɗiyar numfashi da sauri-sauri. Fahimtar hakan ya saka Amal wayancewa da faɗin, “Amma ban sani ba ko shirin komawa yake a lokacin dan da akwati na gansa ma fa. Fitinanniyar uwarsa a tare da shi ko rakkiya tai masa oho musu”.
A hankali Manaal ta saki numfashin data ɗan riƙe a maƙoshinta. Sai kuma ta cigaba da shafa manta da kauda zancen ta hanyar faɗin, “Ina dai fatan kin soyo min fara ta Didi?”.
“Harma da su Alewar madara Munaya ta matsa nai miki”.
“Oh my sweet daughter ɗina, Shiyasa nake son yarinyar nan. She is my bestie”.
“Uhm kudai kuka sani. Ni tashi ki shirya ke ake jira aci abinci. Kin san yau akwai hira duk an haɗu”.
Murmushi tayi cike da jin daɗi, dan tafi kowa son irin wannan haɗuwar tasu. Takanji kamar su dawwama a haka tare gaba ɗaya kamar yanda suke da can. A gurguje ta shirya cikin doguwar rigar Abaya milk color da ɗan kwalliyar coffee kaɗan a jiki. Ta saka turarrukanta masu sauƙin ƙarfi. Suna ƙoƙarin fitowa Shahidah ta shigo ɗakin, dariya suka sanya mata dan sun tuna baya. In dai kaga Shahidah tai irin wannan shigowar fuska a ƙwaɓe to abinci aka ajiye zasu fara ci sukuma suka maƙale a ɗaki hira, ita kuma sam bata da jimirin yunwa musamman idan ta dawo daga makaranta ta kwaso rana. Sai ta shigo cikin haushi tana faɗin (“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”).
Baki suka haɗa wajen furta (“ALLAH idan baku fitoba zanci nawa ne”). Ai ba shiri Shahidah ta sanya dariya da musu daƙƙuwa. Daga haka suka rankaya suka fito inda Ammie ke zaune a tsakkiyar falon da ƴan jikokinta zagaye da ita. Dan a anan aka shirya abincin yanda za'aji daɗin ci fiye da saman table.
Manaal na zama yaran duk suka matso kusa da ita kowa na faɗin tare da ita shi dai zai ci. Ganin abin zai zama rigima ta miƙe tana faɗin, “Kunga ku jira ku gani”. Kitchen ta shiga sai gata da babban faranti ta ɗakko, ganin haka Ammie tace, “To ai kawai zuba gaba ɗaya anan Auta sai muci duka baki ɗaya”..
Cike da farin ciki suka ci suka ƙoshi, damma Ammie ta hana surutu. Bayan sun kammala babbar yarinyar Didi Shahidah mai suna Barru ta gyara wajen tsaf sauran yaran na tayata. Maanal ya gyara zama da tunanin Ammie ta manta da batun zuwa gaida mutanen gida sai Ammien ta harareta da faɗin, “Oya tashi kije gaida mutane”.
Fuska Maanal ta ƙwaɓe sai dai babu yanda zatai dole ta miƙe. Hannun ƴar gaban goshinta Munaya ta kama suka wuce tare. ALLAH badan Ammie ba babu inda zataje. Da sashen Hajiya Yaya ta fara. Hajiya Yaya itace uwargida a wannan gida na Alhaji Usman Chalawa. Tanada yara bakwai tare dashi. Babban shine kaɗai namiji sauran duk mata ne. Macece mai son mulki da ƙyamar talaka. Dan mahaifinta kamar ma shine silar arziƙin mijin nasu shiyyasa take jin komai na gidan ta isa da shi kuma dole a bita har shi kansa mai gidan ma. Sai dai kasancewar shi ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa yasa wani abun bata da power a kansa, dan in ma ta nuna ƙarfa-ƙarfar yakan saurin taka mata birki. Kasancewar ta mace ta farko a gidan part ɗinta yafi na kowa girma da tsaruwa, sai dai hakan ba yana nufin na sauran matan ma bai haɗu bane. A'a a komai dai natan yana sama dana kowa kasancewar ita ta fara tarewa a cikinsa.
Sai da Maanal ta dana door bell har sau biyu kafin ta tura ƙofar falon da sallama duk da tasan ba sallai a jita ba kasancewarsa ƙaton gaske ne. Ilai kuwa babu wanda ya amsa mata sallamar duk da kuwa kusan duk yaran na falon harma da ita kanta Hajiya Yayan. Sai dai kasancewar ta danna door bell kafin shigowar yasa duk suka maido hankalinsu ga ƙofar dan son ganin mai shigowar. Suna yin tozali da Maanal wasu a cikinsu suka kauda kawunansu cikin jan tsaki. Yayinda Hajiya yaya ta zubama Manaal ɗin idanu tamkar zata cinyeta da su. Sai Autar Hajiya Yayan da zata iya zama sa'ar Manaal ɗin mai suna Amrah ce tai murmushi tare da miƙewa cike da farin ciki tana faɗin, “Oyoyo mutanen Jos sauka haka babu notis”.
Murmushi Manaal ɗin tai mata, yayinda ita kuma ta rungumeta. A dai-dai nan idon Manaal ɗin ya kai ga ƙaton dining table dake gefensu kaɗan. Sosai zuciyarta ta motsa sakamakon saukar ƙwayoyin idanunta akan wanda ke zaune a wajen shima ya zubo ma inda take idanunsa masu kaifi.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖0️⃣5️⃣
______________
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
________________
......Da sauri ta kauda idanun nata tamkar bata ganshi ba. Sai ma cikin wayancewa ta ɗago Amrah tana faɗin, “Wai haka kika ƙara lukucewa matar nan?”.
Dariya Amarhn tayi da kai mata mintsini a gefen hannunta itama tana faɗin, “Ke dai zauna nan kamar za'a hureki. Ni kin san bana wasa da cikina”.
Murmushi kawai Manaal ɗin tayi batare data bata amsa ba. Hakan yasa Amrah jan hannun Munaya tana mata wasa. Da wannan damar Maanal ta ƙarasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa ta kai duƙe duk da kallon wulaƙancin da Hajiya Yaya ke mata da sauran yaran ta shiga gaidata a mutunce. A yatsine ta amsa mata sau ɗaya ta ɗauke kanta. Hakan ya ƙona ran Maanal matuƙa amma sai ta daure, fuskarta da ɗan murmushi ta maida ga sauran yaran ta shiga gaishesu dan duk sun girmeta. Babu wanda ya amsa mata sai ma tsoki da wasu suka ja mata. Dai-dai nan saurayin nan dake zaune a dining ya miƙe zai fita a falon yana kai waya kunnensa alamar zaiyi magana.
“Ina kuma zakaje Yazeed?”.
Uwar ta ƙatse masa hanzari da ƴar tsawa-tsawa. Cikin dakiyarsa ya juyo da hannu yay mata nuni da waya zaiyi, batare da ya jira sake cewarta ba ya fice abinsa.
“Hummm! Wai shi mai wayo fa Mamma”.
Ɗaya daga cikin ƴammatan ta faɗa fuska a kumbure. Kafin wani ya bata amsa Maanal taja hannun Munaya suka fice suma. Duk rakata sukai da harara, sai kuma wadda tai maganar ta miƙe zumbur tana faɗin, “Ina zuwa bari na muku leƙen asiri. Dan nasan ko rantsuwa zanyi babu kaffara dan ita Yaya ya fita a falon nan babu wata waya da zai amsa”.
“ALLAH nima na fahimci haka Nanah, dan tunda ta shigo ya dakata da cin abincin ma sai wani binta da kallo yake. Kinga muje”.
A hasale Hajiya Yaya ta furta, “Aiko da naci ubansa a gidan nan yau. Tunda na rabashi da yarinyar nan na kuma haramta masa alaƙa da koda inuwarta ma balle ita. Amma kuje ku ganar min yana ina”.
Ai kafin ma uwar ta rufe baki sun fice da sauri har su uku. A dai-dai fitowar tasu kuma Manaal ke shigewa sashen Hajiya Basariyya. Hajiya Basariyya itace mace ta biyu a gidan. Itama dai ɗin ba kanwar lasa bace ba. Dan ba mutuncin ne da ita ba. Sai dai ita akwai banbanci tsakaninta da Hajiya Yaya. Dan a zahiri baka isa fahimtar ita ɗin wacece ba saboda macece mai fuska biyu. A zahiri akwai faran-faran da jama'a da son nuna ita ɗin ta ALLAH ce. Shiyyasa mutane da yawa sai ta gama musu illa suke farga da ita ɗin wacece. Macijin sari ka noƙe ce ita ta bugawa a jarida. Yaranta biyar itama a gidan kuma duk mata, dan ita bata da namiji ko ɗaya. Huznah da Maanal ta fara haɗuwa sanda ta dawo itace ƴarta ta farko. Itama ɗin dai family nata akwai kuɗi, dan Yayanta daya riƙeta hamshaƙin mai arziƙi ne. Kuma babban aminin Alhaji Usman Chalawa ne, suna huɗɗar kasuwanci sosai da har wasu ma ke ganin dukiyarsu a cuɗe take da juna. Shiyyasa itama bata yarda Hajiya Yaya ta ɗaga mata hanci ta ɓangaren dukiya dan kar ce tasan kar. Kowa najinsa a wani shege. Komawa su Nanah sukai nasu sashen cikin taɓe bakuna. Dan Manaal na ƙoƙarin shiga sashen Hajiya Basariyya shi kuma yayansu nama ficewa a gidan da motarsa.
Tun ma kafin su ƙaraso Hajiya Yaya data cika tai tab ta fara jeho musu tambaya cikin huci dan macece mai ƙiba sosai. Irin ƙibar nan bata wasa ba. Dan ko daga nesa ka hango ta kasan ALLAH yayi manyan mata a wajen nan. Zaune duk suka zube cikin takaicin rashin samo abinda za'aci mutuncin Maanal da uwarta yau a gidan. Nanah tace, “Mamma yama fita a mota. Ita kuma ta wuce sashen Momyn Suhana”.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 17