Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a Sultan Abdul Malik Royal Estate zasu shaida siffofin Gimbiyar mu mai jiran gado, ba mutanen Estate din nan kadai ba ɗaukacin Jama'ar dake rayuwa a ƙasar Egypt, ma'ana wanda suka samu halartar wannan taro da kuma wanda ke kallo a television zasu shaida hakan." Dan tsagaita wa yayi kadan kafin ya cigaba da magana kamar haka. "idan baku manta ba yau shekara 20 ciff rabon da Masarautar kasar Egypt tayi taro na aure, wanda da can an gabatar da irin wannan taron kafin aka ranstar da ko wace Sultana ko Malikat, Kun san ance wai waye admin tafiya, to bari mu wai waya baya don tunatar da jama'a wanda suka sani da wanda basu sani ba, Idan baku manta ba Malikat Nubia Allah ya kara mata tsawon rai mai albarka, an gabatar da irin wannan Shagali wanda yake al'adan wannan masarautar ce mai albarka, an ƙiyasta irin qualities din data ke dashi wanda akarshe Sheikh Muhammad Waseem ya bata suna kamar haka, wato 'UMM ALNUWR ma'ana THE MOTHER OF LIGHT." Dan dogon numfashi yaja kafin ya juya ya fuskanci Malikat Nubia ya mata gaisuwan ban girma tare da kirari cikin lafazin da tausassan murya. Bayan ya gama ne ya cigaba da magana kamar haka "bayan shekara 30 ciff aka kuma kara gabatar da irin wannan taron, wato lokacin auren Sultan Salahuddeen Allah ya kara masa girma da ɗaukaka, da Sultana Najda amincin Allah ya tabbata a gare ki, an gabatar da wannan taron sannan akarshe Sheikh Jabeer ya bata sunan da ya dace da ita da kuma salon Mulkinta, wato 'UMM ALNAJAH, ma'ana the mother of success. Kamar yadda ku ka sani ba haka kawai ake bawa ko wacce Gimbiya suna ba, sai anbi wassu hanyoyi da ka'idodi guda biyu, na farko shine Neman zabin ubangiji, na biyu kuma shine siffofi guda shida da ake bukatar ko wacce Gimbiya ta mallaki akalla guda uku daga ciki ko sama da haka, ko kuma duka. Ba tare da bata lokaci ba zamu gabatar da wa'yannan siffofin sannan mu ga wanne daga ciki Gimbiyar mu mai jiran gado keda shi, sannan karku manta zamu gabatar dakuma sanin haka ne ta hanyar alkalau guda uku, wanda suka kware wajen karantar halin dan Adam, Na farko shine Al SHARMEEM (shy), yana nufin kunya wato alkunya, a yanzu zamu dakata don mu bar alkalan wasa su tan tan ce kayan su," shiruu!!! Hall din ya ɗauka kowa yana jiran jin abinda alkalan wasa zasu fada, wasu har addu'a sukeyi Allah sa ta wuce wannan gwajin ga masu ƙaunar ta kenan, maƙiyanta ko babu abinda suke fata kamar suga gazawar ta, Daya daga cikin alkalan ne ya fara danna golden din maballin dake kan table din gabansa kafin duka biyun suma suka danna nasu wanda yake irin nashi golden colour, Cike da zumu di 😄Rayiys alhadath ke magana "Mashaallah 😍tabarakallah,🤩 tah niyyahn laki yah Zawjatul Ameer (congratulations to you Zawjatul Ameer), You have passed the first bridge, (Ina taya ki murna Zawjatul Ameer), kin wuce wannan gadan kin lashe, kin samu goldn crown 👑 (zaiban hulan girma) kin tsallake red ma'ana maballin gazawa wato na rashi , kika kuma wuce green wanda yake pass, wato kina tsaka stakiya ke baki fadi ba kuma baki zama tauraruwa ba." 😁farin ciki ya gagara boyu wa a fuskan masoyan ta kamar yadda bakin ciki ya bayyana ƙarara a fuskan maƙiya😡. "Ba tare da bata lokaci ba zamu zayya no quality na gaba wanda yake , uhmmm!!! Shine Al SHEZA (good religious girl) Yana nufin yarinya mai kirki da rikon addini, toh bari muga yadda abin zai ƙaya daga ɓangare alkalan wasa, amma nawa lissafin ko makaho ya laluma yasan Gimbiya mai jiran gado batayi kama da marar rike addini ba , sai de bari mu bar manya suyi aikin su," Kamar a farko gurin ya dauki shiru aka bar alkalan wasa suna nasu nazarin na fidda gwani. shiruuuu!!!! Kake ji kamar an jefa tsumma a randa, zaka ranste babu halittar ko ƙuda a hall din sai karar masu televising da masu aikin daukan hoto. Diiid diiid diiid!!!! Kake ji ƙarar maballin da alkalan wasan ke dannawa wanda sun danna lokaci daya duka su ukun, Zare ido 👀 kowa yayi dan ganin abinda suka danna baya Rayiys alhadath wanda yake jin kansa kamar ya fashe, "🤯 Jazakallahu Khairan, Mashaallah 😍 Zawjatul Ameer You have passed with golden crown 👑, kin wuce kin tsallake gada ta biyu, bari mu dan gana zuwa na uku, shine Al SHEENAZ (beauty) ma'ana kyau, ko wannan nasan ko mutanen dake cikin hall din nan zasu shaida hakan, don naga wata budurwa mai ji da kanta tana ganin Zawjatul Ameer tasa nikab 😅🤣😂, amma bari alkalan wasa su tan tan ce abun su ." Cike da tsarguwa yan matan da suka rena kansu ke ta faman cika suna bastewa, wacce tasan da ita ake kuwa kasan table ta shige ganin yadda kallo ya dawo kanta 👀😳👀. An dau lokaci mai tsayi ana muhawara tsakanin Alkalai, wanda sanda aka dan gana da fashion model, an dau akalla three minutes ana muhawara. Dan dan dan dan!!!! Cikin kowa ya dura ruwa ana jiran iran feedback, diiid diiid diiid!!!!! Kake ji karan maballi wanda state suka danna, Murmushi kawai Rayiys alhadath yayi don dama yasan za'a rina, "Mashaallah li annan laha Houwa ahsanul Khaaliqin 🤩, ko ban fada ba kunsan anan Zawjatul Ameer ta lashe, ta samu golden crown 👑, ta tsallake wannan gadan bari mu garzaya zuwa na huɗu, wato SUJA (calmness and quietness) ma'ana kamun kai da shiru shiru ko ince miskila, kunsan mafi akasari an fi son Sultana ko Malikat ta kasance miskila ko shiru shiru, ba wacce ina da hira ba ko ina da ita, kar in cika ku da surutu bari mu bar alkalan suyi aikin su," Shiruu kamar ba'a taba yin wani halitta ba'a cikin hall din, diiid diiid diiid!!! Kake ji karan maballi wanda alkalan wasan suka danna atare, "Allah Allah Mashaallah 😍 Zawjatul Ameer ta kara lashewa a karo na hudu, lalle ƙasar Egypt tayi Sa'an Gimbiya mai jiran gado, da alama za'a kafa tarihin da aka dade ba'a yi irin shi ba, Yan zu bari mu gangara izuwa kashi na biyar wato na biyun ƙarshe, yana daya daga cikin abu mai muhimmanci dan gane da zaben Gimbiya, shine AL SHELLA (truly Kind hearted and beautiful), ba tare da na Jamu da nisa ba bari na sada mu da alkalan wasa ," Dan jimmm suka yi suka hade kowa da abinda yake nazari cikin su, sun dau lokaci mai tsayi suna abu daya, Ta fannin Shazana Subaihat ji take tamkar ta hadiye rai ta fadi kasa macecciya tsabar takaici, na farko tayi asarar kudinta da lokacin ta wajen lalata wannan taro, tayi kokarin siyan alakalan da ƙudi mai dinbin yawa wanda sun ƙi karaba, wani mugun murmushin mugunta ta sake tunawa da tayi cewa ta musu barazana da rayuwar ƴayansu, kuma sun amince zasuyi abinda take so, duk da bata ga Alaman hakan ba sai de ta tuna cewa har yanzu akwai daman cin nasara tun da ba'a yi na biyun ƙarshe da na karshe ba wanda akansu akan iya fasa auren gaba daya, murmushin kafirci da zallan ƙeta da mugunta ta sake😏 . An kai akalla five minutes ana jiran su , har kowa ya cire rai da samun nasara, mahassada ko sun fara farin ciki, ba zato ba tsammani aka ji ƙarar maballin diiid diiid diiid!!! 👀😳👁️ Kowa ya zuba ido don jin abinda ke faruwa, cike da razana da rashin gaskata abin da idonsa ya gani ya kara ware idon na yan sakanni 🏢😳. With full of joy and jubilation ya ce "Subhanallah Subhanallah, I never thought Zawjatul Ameer will passed this bridge, Alhamdulillah she got golden crown 👑, " Sauke ajiyan zuciya Malikat Nubia tayi don har ta cire rai, ba ita kadai ba hatta Malik sanda ya sauke, Dukkanin su cikin zuciyoyinsu suka godewa Ubangiji, suka kuma zuba ido don jin ya za'a kaya a gaba. "Ba tare da bata lokaci ba zamu garzaya zuwa last step, wanda akanshi akan iya fasa auren muddin ba'a samu yadda ake so ba, wannan bridge tsallake shi da wahala, don sai anyi dogon bin cike shine AL SHAZFA (SUCCESS), ko wani ban gare na rayuwa muna da bukatan Sa'a, komai na rayuwa sai da Sa'a wanda in ka samu da kuma yardar Ubangijin ka komai naka zai tafi dai dai, anan ana bukatar dogon nazari da lissafi, za'a bincika aga wani irin Sa'a aka samu lokacin bayyanar Zawjatul Ameer, wani abun alkairi aka samu ta sanadin ta, bari na sada mu da alkalan wasa don suyi aikinsu," Yayi magana ne cikin sanyin jiki don har ga Allah anan bashi da ta cewa,hakan yasa jikin mutane da yawa yin sanyi, wanda suka san abinda suka taka kuwa hankalinsu kwance lubb irin su Shazana Subaihat, Wacce tasa hannu ta kama hannu diyarta Sabreena cike da hope na samun nasara , Sabreena ganin haka ne yasa ta saki zuciyar ta da ranta. Ana zaune har aka shafe tsawon mintina talatin alkalan wasa basu ce komai ba sai ma hade kansu da suka yi suna yan kus kus, kowa ya zuba ido👀 da kunne👂 yana sauraron abinda alkalan zasu ce, Tun ana sa ran zasu ce wani abu har kowa ya buge da yin harkar gaban sa, har an so manta abinda ya sa aka ka halarci wannan taro. Tsawon one hour Babu alamun zasu ce komai , shi kanshi Rayiys alhadath ya sare 😔 har ya samu guri ya zauna, Cike da karaya Sultana Najda ta Kama hannun Sultan Salahuddeen, kama hannunta yayi da kyau don ya fahimci ta sare 😔 murmushi ya sakar mata mai sanyaya zuciya. Ta fannin Ameer Mahbeer ya ci alwashin ko da Zawjatul Ameer bata da wannan feature shi zai zauna da abin shi a haka, ko da hakan yana nufin bazai mulki ƙasar Egypt ba, soft hand din ta ya kama gam cikin nashi yana jin wani sonta na kara Rasta jinin jikinsa, tabbas ya yadda so dashen ubangiji ne , bai taba yadda cewa akwai ranar da zata zo wanda zai so wata mace ba , musamman irin son da yake wa Shazana Mehnoor, A hankali tace " Zawjy am tired , Ina Jin yun wa, kuma i want to sleep my head is paining me," Cike da tausayi ya ce "don't worry Yan zu zamu tafi gida," Gyada Kai tayi ta kara je fa masa wani tambayan "Zawjy where is Pops and Ukhtie?," A hankali yace "shiiit keep quiet Hooriyya zasu zo yanzu," Dan cuno baki tayi gaba da kwabe fuska kaman mai shirin yin kuka, Murmushi yayi don stab yana iya hango yadda ta bata fuska cike da lallashi ya ce "don......," Ba tare da ya kammala furta maganan bakin ba yaji karan maballi diiid diiid diiid!!! Wanda yayi nasaran tattara hankalin ɗaukacin jama'ar dake hall din dama wanda ke kallo a television, Ba wanda yayi tsammanin hakan kowa ya zaro ido👀 😳👁️ , cike da rashin gasgata wa, Numfashin Sultana Najda har hadewa yakeyi tana kokarin yin magana ta kasa, yayin da hawaye sukayi nasarar riga kalaman bakinta fito wa, da sauri ta rungume Sultan Salahuddeen don baza ta iya jure hakan ba, Ni kaina Queen Mahirah nayi matuƙar mamaki ganin wannan al'amari, bani kadai ba hatta Rayiys alhadath kanshi har hayaki yakeyi 🤯, Tohh fahh readers ku biyo next page don jin yadda labarin zai kasance . Har ilah yau zaku iya tun tuba na ta wannan lambar a WhatsApp don na saki cikin WhatsApp group inda zaki samu cigaban page din nan. Ko kiyi following WhatsApp Channel anan zaki samu labarin tun daga page one har inda aka tsaya. Ban manta daku ba masu comment Wannan page din sadaukarwa ne a gare ku. Story and written by Queen Mahirah 👑🧕 The wordsmith 🖊️📖 Comment and Share fisabilillah😔 Karku manta book one free ne, book two ne na kudi game bukata ga WhatsApp number ta 09168962485. THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰) The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship, twin flame journey... Story and written by Queen Mahirah 👑🧕 Wordsmith 🖊️📖 Ban mamta daku ba masu comment 😁 ina godiya 🙏😍 Baya ku Oum Affan and bloody, na gode sosai da irin ƙaunar kuke nuna wa Novel Dina 🙏😁🤗, wannan page din sadaukarwa ne a gareku😏🤲. Ongoing Book 📚 📱 Typing FREE BOOK BOOK 1 🧚36🧚 KANO STATE (NIGERIA) MASARAUTAR SUHATAJ MUHD HABIBULLAH TURAKAR GIMBIYA ZUNNURA Kwance bisa shinfidadden Royal Bed dinta wanda aka lailayeshi da hadadden bed sheets. Tana sanye cikin kaya mara nauyi, kallo daya zaka mata ka hango zallan damuwa dake kwance lubb a fuskanta, gashi tayi wani fari da ita irin na matasa lafiya musamman masu ciwon damuwa. Cikin nustuwa da zallan Izza da sarauta dake yawo a jinin jikinsa, ya karasa ba tare da ya damu da rashin amsa sallamar nata ba, bai tsaya ako ina ba sai inda take kwance bisa shinfidadden Royal Bed dinta, dogon numfashi yaja da ganin yadda tarame cikin ƙan ƙanin lokaci, zama tsayi a kusa da ita ya kamo hannunta da nashi soft moist hand din, wani dogon numfashi yaja kafin ya fara magana cikin muryan sa na mutane masu hakuri, tausayi, yadda da kuma karfin imani, "Nur nadan kina jina, inason kisan duk abinda ya faru Muƙaddari ne daga Allah, kuma su yaran yanzu ka haife su ne baka haifi bakinsu ba, kidena sawa kan ki damuwa , ba laifinki bane, ƙaddara ce kuma tana kan kowa," Wasu hawaye masu zafi ke bin kunci ta wani irin kunyar hada ido takeyi dashi gani take duk laifin ta ne , da bata dauki Mubeen da niyar ya girma agunta ba da duk haka bazai faru ba, Hanu yasa ya tallafi face din ta hawaye ya sa hannu ya goge mata cikin nustuwa, "bude idon ki , " Ba musu ta bude idonta ta zuba su cikin nashi , Wanda suke narkakku masu daukan hankali da sanya nustuwa cikin zuciyar mai kallo su. "I told you is not your fault, stop shading your tears for no reason, ki dena fushi da Mubeen pls, ki masa addu'a shiriya, sannan kuma ki yafe masa koda zai samu rahamar Ubangiji, yanzu addu'ar ki yake bukata, inso kisan Allah shi ya bamu su mastayin ƴaƴa, haka ka zalika su amana ne a garemu, in ya karbi abinda bawai yana nufin baya ƙaunar mu bane ko baya ƙaunar su, sai dan yafi mu son su da sanin darajar su mastayin su na yan Adam, " Dakata wa yayi yayin da ya yana wani dogon numfashi cikin nustuwa kafin ya fesar, sannan ya cigaba da cewa "Mubeen ya rigamu gidan gaskiya, Allah ya karbi abun sa ," Cike da taahin hankali ta bude idonta atakaice Bara san lokacin da ta zauna ba, kallonsa take in disbelief, Kai kawai ya gyada mata , cike da karaya ta soma jijjiga kanta kafin ta fashe da kuka mai cin rai, kana gani kasan da iya gaskiyar ta take kukan , ma'ana daga zuciyar ta hawaye ke fitowa. Cike da karaya da tsananta tausayi yake kallon ta, yana daya daga cikin abin da yasa yake kara tausaya mata , wato rashin haihuwar da bata taba yi ba , yau shekara talatin da auren su amma ko haram wata bata taba yi ba, shiyasa data nuna tana son daukan ɗan ƴar uwar ta bai hana ta ba, ya dauke sa tamkar ɗansa babu ban ban ci tsakanin su, yau kuma da aka ce ya bar duniya bazai iya misalta irin radadin da ya je ji a zuciyar sa ba, duk da abubuwan d ya aikata a gare sa. Cike da tausaya wa ya rungume ta so tight ya fara petting back dinta cikin Muryar sa mai san yi da zallan nustuwa ya fara tattalin ta hade da yi mata nasiha mai Rasta jiki kamar de yadda ta kasance tana masa a duk lokacin da ya shiga wani hali na ƙunci. TURAKAR GIMBIYA NASHWA (FULANI) Zaune take cikin shiga na alfarma cikin kaya mara nauyi , sai de fari ne tas hannunta dauke da carbi, tana saye da hijabi shima fari tas, princess Mobina na kwance lubb bisa kafin Fulani sai jan ajiyar zuciya takeyi, da alama tayi kuka sosai, cike da nustuwa Fulani ke shafa kanta cikin salo na lallashi. Cikin muryan ta na sheshshekar kuka tace "yanzu kenan bazan ƙara ganin ya Mubeen ba Jaddatii ? Shikenan ya tafi ya barni da kewarsa sa ? Allah Jaddatii ya Mubeen ya nuna mun so, duk da a zuciyar sa ba haka bane, amma Ni abinda yake zahiri nake gani , ba komai tattare dashi wanda nake gani sai zallan ƙaunar da yake mun," Da hanzarin ta mike zaune ta haɗa hannunta guda biyu 🙏 cikin salo na neman gafara tace "Dan Allah ku yafe wa ya Mubeen, insao ya samu rahamar Ubangiji, wallahi ba laifin sa bane, nasan wani abun sa shi aka yi," Cike da tausayin ta Fulani ta kama both hand dinta tace "Sabr yah Hafidatiii, ki kwantar da hankalinki," Fashewa taI da wani mastanan cin kuka maiƙona rai da zuciya tace " Jaddatii baza ku yafe masa ba ? Dan bakwa ƙaunata ko?," Fulani ganin ta riki mata be yasa ta rasa mai zata yi guda ɗaya, don in akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce taga jikanunta cikin wani hali na tashin hankali ba , musamman ma Mobeena da take jinta tamkar ranta. Bata kai ga cewa komai ba sai ga Bana sarki ya shigo cikin keban ceccen farlon wanda ba'a yarje wa kowani bawa ya shigo ba, Cike da hanzarin da ya karasa inda suke ganin halin da Princess Mobina ke ciki, "Inna lillahi Mobina mai ya faru?," Tana ganin sa ta tashi ta gudu ta karasa inda yake ta rungumesa ta ce" Grandpa ya Mubeen ɗan Allah ku yafe masa kar Allah ya kama shi da laifin zunubin da ya aikata," "Shittt is okayy Maryama mun yafe masa duniya wa lahira, yanzu ba ban shigo nan ba sanda na tabbatar da sauran bayin sun yafe masa abinda ya musu, ko ba komai shi din ɗa ne a garemu kuma ya mana biyayya dai dai gwargwadon iya warsa, shi din ya zama jinin jikin mu, mun yafe masa Allah ya yafe masa shine abinda muke fata a yanzu," Fashewa ta karayi da wani kuka mai ƙona zuciya "shi ke nan yanzu ya tafi grandpa? Bazan ƙara kallon shi ba ? Bazai kara kira na a waya ba? Bazai ƙara kaini makaranta ba? 😭😭😭. Grandpa Dan Allah ku dawo mun dashi, wallahi na yadda zan aure shi a haka, na yadda koda shi baya sona, inason in saka mishi da irin kulawa da tattalin da ya yi gareni, ya nuna wa duniya babu yani, tur da irin halina duk Ni na jawo hakan daban tauna masa asiri ba da hakan bazai faru ba, duk da mugun nufinsa akaina na ƙwammace hakan ta faru da rasa kanshi da yayi yanzu , nadan Ni ce sa na di," ba tare da ta sani ba taji an soka mata allura, tana kokarin juyowa wani bacci mai nauyi ya dauke ta, da taimakon Dr Yusuf aka kwantar da ita bisa shinfidadden kujerar, mai taushin gaske, sauke ajiyan zuciya Fulani tayi ta ce "Allah ya kawo ka a dai dai Dr Yusuf, da naga ka shigo na zaci shine ma ," tayi maganan ne yayin da idonta ke cikin na Baba sarki, "hankali na ya gagara kwanciya ne shiyasa na ce bari nazo na duba ta," "Hmmm tun dazu ta rikice ga jikin ta yayi zafi sosai, sai sun batu take yi shiyasa nace bari kawai na kiransa ka turo mana Dr Yusuf," "Hmm kinyi kyan kai, mai yake damun ta ," Cike da girmamawa Dr Yusuf ya ce" damuwa ne da stress, sai zazzaɓi, amma yanzu na mata alluran bacci she will be alright inshaallah, and kar ana barinta ita kadai kuma ban da yawan tunani, I mean kar barta tayi stressing brain dinta," Gyada Kai kawai Bana Sarki yayi, yayin da yake shafa kanta cike da tausaya wa da zallan ƙauna. RUGAR HARDO BELLO (KANO STATE, NIGERIA) 8:00 pm Zaune muke a falo as always kowa da abinda ya keyi muna sanye cikin light wears wato kasa marassa nauyi, Sallamar da muka ji ne yasa hankalin mu karkata in da ake sallaman, wah zamu gani ??? Commodore Fareed ne da Captain Fudhal, suna sanye cikin fararen jallabiya, dan kifta ido nayi ina juya su kafin na amsa sallamar tasu, Bismillah shine abinda nace dasu yayin a Islam tun da ta amsa sallamar bata kara cewa komai ba, cike da fara'a ya samu guri ya zauna, shine Fudhal sai cika yake yana bastewa haka har ya zauna. Cike da fara'a ya ce "sannu ku da hutawa GENTLE ladies😁," Kai na dago na gansawa, sai kawai ya burge ni musamman yadda yake magana cike da fara'a, ko haka kadai ya nuna cewa mutum ne shi wanda ba shida damuwa. Murmushin ba mayar masa nace yauwa sannu ya kuke? "lafiyan mu kalau, ya ɗawainiya da mu?," Murmushi nayi na mai mai ta Kalmar ɗawainiya, "Ehh ai ba ƙaramin kokari kuke yi ba," Wani murmushin na kuma sakewa don nima gwana ce a wannan fannin musamman inna samu wanda na sake dashi. Ai ku bakin mu ne , bakon ka kuma annabin ka ne. Gyada Kai yayi ya ce "haka ne, if I guess right ke ce Mahnoor ko?," Yaff Ni ce, "Mashaallah, and this boss lady most be Khadijatul Islam," Murmushi nayi na ce You guess it right, she is the one. "You know am good at guessing," Humm kaji Dadi ni kam am not good at guessing, Dan karkata kai nayi na karewa Captain Fudhal kallo na yan sakanni kafin na ce, is he seek? Naga ya hade fuska kamar gumbar waina, cikin shi na ciwo ne? Murmushi Fareed yayi ya ce "he is not, haka yake bashi da fara'a," Dage gira daya nayi na ce Maama luya, so haka yake kullum da face dinshi kamar anyi gobarar attarubu? Wani mashiriritin dariya Fareed ya sake ya ce "You are so funny," Murmushi nayi na ce uhmm kaga ban ma san sunan ku ba? "Ohh my name is Fareed and this one is Fudhal," Ohh Masha'allah I guess I know you, but where? Ohh 😯 I remember you are Commodore Fareed, you are Air force , and this Mr Grumpy is Captain Fudhal, I think I guess it right, Wani murmushi Fareed ya sake ya ce"yapp haka ne, but a Ina kika san mu?," Ohh come on, Commodore saninku ai is not a big deal, Kuna cikin Top ten na the most famous and handsome rich guys a fadin Africa, Ni a gurin ƴan matan Class din mu ma na sanku. "Wow ki ce min yi wuta," Yayi magana yayin da yake dan daga kwalan jallabiyar sa, Dan ƙaramin dariya na sake yanda yayi ya ban dariya sosai, ina dayan kuma mai danne ƴayan mutane ajikin gini. Dan ware ido Fareed yayi ya ce "kai kuma acikin mu yake ," Zumburo baƙi nayi gaba na ce 😚 ehh mana kawai daga kai mishi abinci sai ya fara wa mutum mugunta, sanda fa ya gwalmadar mun da kashin kun kumi na😞. Zare ido 😳 Fareed yayi y ce"subahanallhi, uhmm am so sorry 😔 haka yake wallahi yana da zuciya sosai," Dan daga gira daya nayi nace, i guess ni bani dashi shi yasa ya mun haka, wai yana da zuciya, na fadi haka yayin da na kara turbune face nawa. "Sorry kin san yan uwan nawa sai ahankali a musu afuwa please 🙏," Kara cuno baki 😗 nayi gaba nace uhmm, ohh na manta ga can abincin ku a dining table, tun dazu Innani ta ajiye, muje nayi serving naku, Murmushi yayi yace "okay thanks 😊,," Yayi magana yayin da ya mike ya bi Bayan ta, shiko Fudhal sanda ya mula dan kanshi kafin ya mike, yayin da Islam tana kare mishi kallo azahiri ko zaka ranste waya take dannawa sai de idonta yana kanshi, tana karantar halayyar sa tsaff . END Of PAGE 36, FOLLOW FOR MORE 😢😁 Story and written by Queen Mahirah 👑🧕 The wordsmith 🖊️📖 THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰) The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship,Twin flame journey... Story and written by Queen Mahirah 👑🧕 Wordsmith 🖊️📖 FREE BOOK BOOK 1 🧚37🧚 Fudhal ko sanda ya mula dan kanshi kafin ya mike cike da izza ya je dining area, yayin da Mahnoor da Fareed sun shagala da hira zaka ranste sunyi Shekaru tare. Da

Chapter 22 of 25