Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shegen kyau wanda aaka shinfida masa wani hadadden carpet zaka ranste da zinare akayi stairs din stabar walwalin da yakeyi da daukan ido 👀. tafiya yake cikin nutsuwa wani daki ya nufa wanda da alama shine dakin Sultana Najda da mamakina ni Queen Mahirah yana zuwa kofan ta bude da kanta ya shiga yana shiga ta rufe kiriff. cikin hadadden dakin ya karasa wanda yasha Royal blue and golden furnitures, karasawa yayi gaban tafkeken gadon dake lullibe da labule ya kwaantar da ita, ya kai akalla 2min yana karewa cute face dinta kallo maganan da Mima ta fada mishi ne yake dawo mishi brain dinshi, har ya juya zai tafi ya tuno da abinda Mima tace sai ya fasa ya dawo, zama yayi akusa da ita ya kai akalla 50sec yana tunanin ta inda zai fara cire mata wannan uban kayan jikin nata ganin yadda tayi cuddling a guri daya kamar cat, dogon numfasahi yaja ya gyara zamansa akan gadon ya masto daf da ita yamika hannunshi ajikin ta yadan bude hannunta ya cire bottle din jacket 🧥 din wani dogon numfashin ya kara ja dan baisan ta inda zaai fara cire mata rigan ba mastowa ya karayi daff da itaa ya dago kanta ya kwantar ajikinsa atakaice da kyar ya cire wannnan rigan dan ba karamin yaki suka yiba sai cukuikuyeshi takeyi kamar zata koma caikinshi, yayi mamakin yadda bata tashi daga baccin ba kodai har da maganin bacci ake bata ne tunda yaji Mima tace anaso brain dinta ya huta, ajiye jacket 🧥 din yayi agefe ya fara tunanin yadda za'a cire sauran, veil din da aka mata rolling dashi ya fara cirewa gashinta da aka tufke ya ware wani sassanyar kamshi ke tashi daga ciki tsayawa yayi yana karewa tulin gashin nata kallo wanda yake baki wuluk dashi, hannunsa yasa ya shafa gashin nadan wani lokaci kafun ya maida hankalinshi ga alkebban jikinta bai shaa wiya gun cire alkebban ba, kyak'kyawan surarta ne ya bayyana wanda yasaa shi dauke wuta na wassu mintina, dakyar ya haadiye yawun wahala ya kauda kanshi gefe wani lallausa filo ya jawo ya dagota da niyan kwaantar da ita, anan ne kidan ya canja salo don chakumoshi tayi ya fado kanta rufff waani kukan wahala ta sake don ya mata nauyi aka, jiki ba karfi ya mike da kyar ya jingina kansahi ajikin gadon ya lumshe idonshi. a gaskiya an gama da rayuwarsa ayau kadai ji yake kamar kanshi yayi blowing, yanzu ahaka zai cigaba da zama da yarinyar nan yayi ta mata jegon jaka, gaskiya ba'a masa adalci ba ya kai 5min yana ta karanta wsikar jaki kafun ya yayi kokarin jan kanshi ya sauka daga kan gadon, ko juyowa baiyi ba bare ya yayi kuskuren ganinta ayanzu ma shi kadai yasan mai yakeji, yana zuwa bakin kofa sai ga Sultana Najda na shigowa cak ta staya ta kare mishi kallo ganin yadda ya hargiste idonshi yayi jaaa gaba daya ya canja kaman ninshi wani dummm zuciyanta ya bada da sauri tayi cikin dakin hango ta da tayi tana sharar baccinta tane yasa taji relief, shiko kafun ta juyo ya fece dan ya stargu da kallon da take mishi, murmushi tasaake ta jijjiga kai ta karasa bakin gadon da kamar anyi yaki ahankali tace "lalle ko gyara yayi kyau," saide tana mamakin yadda yarinyar take a gyare stafff don tun farkon zuwanta inka ganta zaka ranste amaryace don yadda fatanta ke glowing ta bangare da dama a gyare take hakan yasa tafara contemplating anya ma bata da aure, bata yadda ba sanda tasa gyne Dr ta duba ta tabbatar mata da she is still virgin kaafun hankalinta ya kwanta. NIGERIA {KANO STATE} Wata hadaddiyar shararriyar farlo ce mai stari irin na turawa black and white ne colour combination din farlon, ba wani babba bane dan dai dai ne mai cike da kayan alatu da more rayuwa , ba abinda ke tasahi sai wani sassanyar kamshi da sanyin A\C wanda ya kara kayata farlon, babu karan abinda yake tashi a farlon sai na A\c da kamshin dake tashi, wani halitta na hango zaune bisa daya daga cikin sofa na farlon ya jingene kanshi jikin sofa yana sanye da farar jallabiya, fari ne tas babu digon baki ko kadan ajikinshi kyak'kyawane na ajin farko wanda ko kyau ya ganshi sai ya sara mishi ban cire stammanin ya hada jini da Annabi yusuf ba, a iya tarihin rayuwata ban taba ganin halitta mai kyau irin wannan ba. fuskarsa yana shinfide da hadaddiyar man's pride dinsa baki wuluk mai stansti da daukan hankali, wanda ya kara fidda stanin kyansa da kwarjininsa, hancinsa tamkar kara aka staga yayi dai dai da face nasa sai kasancewarta ba katuwa ba siriri ne dan dai dai, idonsa dake aalumshe da zararan eyelashes dinsa da kuma well shaped eyebrow dainsa wacce tamkar shi ya saita abunsa, lip dinsa so cute dashi pink colour, hmmm abun sai wanda ya gani don ba'a cewa komai don Allah yayi halitta anan dana kare masa kallo na hango stanstan izza da kwarjini atattare dashi, kirar halittan sa da surar sa yafi karfin yaro a murde yake gashi yana da stayi kana kallonsa kasan ba karamin dakakken namiji bane, gashin kansa baki wuluk dashi mai tarin yawa da stansti. lips nashi na mosti ahankali wanda da alama tasbihi yakeyi, zarazaran finger dinsa na aikin bautawa mahaliccinsa wanda ya zauba masa kyak'kyawan halitta, karan takalmin dana ji ne yasa na maida hankali na kan mai tafiyan masha'Allah hakika babu abun bautawa da gasakiya sai Allah, godiya da yabo sun tabbata ga ubangijin da yayi wannan kyak'kyawan halittan. wani hadadden Giant handsome ne fari tass, yanaa sanye da unifoam na Navy wanda yake white colour ajikin rigar dagaa bangaren dama akwai inda aka rubuta CAPTAIN FUDHAL, unifoam din yayi matukar amsar sa ya kuma fidda murdadden surar sa mai firgitar da abokan adawansa, idonshi sanye da dark space cute lips dinsa sai kyalli yakeyi, pointed nose dinsa ya kara wa face dinsa kyau, face nashi kewaye da bakar sumarsa mai sheki, {wanda aka fi sani da saje} da daukan idon mai kallonta da mai karatu, ya karawa face din nashi kyau sosai, haka gasahin kansa yaa sha mayuka sai sheki yakeyi gashi dayawa ga stansti , hannunsa dauke da hulansa, ya cigaba da tafiyaa cike da isa da takama face nashi babu annurin fara'a ko kadan sai de hakan bai sa yayi muni ba sai wani kyau da kwarjini daya kara masa , tafiya yake tamkar zaki mai shirin baza taro har ya iso cikin farlon agefen wannan farin halittan ya zauna yaja dogon numfashi cikin husky voice nashi yace " how are you feeling" ahankali ya bude snake eyes dinsa ya zuba su a fuskan Captain Fudhal wanda shima alokacin ya cire dark space din sa ya zuba mishi lion eyes nashi, bai ce komai ba ya lumshe idonshi, daga fannin Captain bai damu da rashin amsan nashi ba don dama yasan ba lalle ne ya samu amsa ba, alama yayiwa house maid da hannu daya ajiye tire din abincin dake hannunsa akan wani glass centre table din dake farlon, cikin girmama wa ya ajiye tire din ya fara kokarin serving dinsu ahankali Captain Fudhal yace "no need you can go" cike da girmamawa yace "okay sir" ya dan sadda kanshi alaman ban girma kafun ya juya ya tafi, da kanshi ya mike ya dauki breakable plate ya zuba chips da soyayyan kwai sai pepper soup sai kuma hot choculate, janyo centre table din yayi dai dai da inda yake kafun yace "Tweeny sit well and eat, am very sure bakaci komai ba" bude lumsassun idonsa yayi ya zuba su a abincin nasa nadan lokaci kafun ya kauda kansa wani sarawa yaji kansa keyi rinste idonsa yayi da karfi ahankali yake ambaton sunan Allah, yana ji tamkar kan zai stage gida 2, lura dayayi da halin da yake ciki ne yasa shi tasowa da sauri ya zauna agefensa ya dafa shi yace "Fahreen are okay what is wrong with you" bai ce mishi komai ba sai kada kanshi da yakeyi ahankali ganin haka ne yasa shi fahintar cewa kansa ke ciwo, cikin wani yanayi ya kama kan ya fara tofa masa addu'a ya kai 30 second yana faman masa addu'a kafun can ya staya ganin ya dai na jijjiga kan nashi "sorry Tweeny Allah baka lafiya, anya baza mu fadawa su Ammi...," bai gama maganan nashi ba Fahreen yace "no no please don't tell them," cikin wani yanayi na storata da yanayin dan uwan nashi yace "okay i won't but please eat" hannu ya miko mishi idonshi akan abincin yana nufin ya bashi abincin, bai bata lokaci ba ya dauko plate din chips din ya bashi kare mata kallo yayi bawai dan bayaso ba ko baya jin yunwa ba a'a sai dan bashida appertite ne yasa bayason abincin rabonshi da abinci tun jiya da dare, ahankali ya kai abincin abakinshi kamar wanda aka sashi dole sai de bai fi 2 spoon yayi ba ya ajiye plate din , Fudhal ya mika masa bowl din pepper soup din ya dan ci kadan shima ya ajiye sai mug din hot choculate shine wanda ya shanye tas don dama yafi son abu mai ruwa da dumi, dogon numfashi yaja yace " "Alhamdulillah" ya koma ya jingine kanshi jikin sofaa ya kwanta, Captain Fudhal da kallon tausayi yake bin dan uwaan nashi, yau akalla 2 weeks kenan suke fama dashi sun rasaa abu daya dake damunshi duk ya rame ya lalace ya fita daga hayyacinsa, gashi ya ki yadda kowa yadda iyayesu susan abinda ke damunsa, karshe ma basusan inda yake ba su kansu ba'a san suna garin kano ba don kowa ya zaci suna gun aikinsu. sunyi maganin asibitin babu sauyi wani abokinsu Dr nema ya basu shawaran hadawa da islamic medicine sunyi kuma Alhamdulillah don ansamu ci gaba, sabanin da, da idan kanshi ya fara ciwo har bugawa yakeyi agini ya ringa abu kamar majnoon da kyar suke kama shi, amma yanzu da sauki ya dena buge buge sai de ciwon kan nanan, kuma koda wasa baya so ayi maganan gidansu ko kadan muddin akayi tohh zai rikice ya fara neman inda zai sa kanshi ya buya hmmm dogon numfashi yaja yace " ina Fareed ya staya ne nikam..," Daga nan waje wato balcony securities dake sanye da kakin sojoji ne suka wangale gate wani hadadden mota mai numfashi ne ta danno kanta cikin gidan tayi parking, daya daga cikin sojojin ne yayi hanzarin zuwa ya bude cab din motan ya kai akalla 2min kafun ya zaro santalelen kafansa wanda yake sanye cikin wani arnen white designer snickers after 3sec ya zaro dayan kafan kafun ya fitoo gabaa daya, ohhhh Allah ni Queen Mahirah sake baki 🤤 nayi har ban sanda alkalamin hanuna ya fadi ba, na sake baki ina bawa idona👀 hakkinsa. wani mashahurin hadadden stadadden gaye ne mai zubin sammudawa ya fito daga wannan arnen car din yana sanye cikin farar dakakkiyar shadda wacce ta amsa lafiyayyiyar surar sa, fari ne tas mai zubin larabawa, fuskarsa nada stayi tana kuma dauke da pointed nose dinsa hade da cute pink lips dinsa, sai eyes nashi wacce ta karawa halittansa kyau da man's pride dinsa baki wuluk dashi wacce da gani ba karamin naira aka kashe mata ba sai sheki yakeyi

Chapter 11 of 25