yaso, bata son hakan amma innani ta gagara gane wa, ba dama ta kwabe sa sai ta nuna bacin ranta,
ba abinda yakara bata haushi sai ganin yadda innani keta faman rarrashin sa da take yi,
itako har wani hawayen bakin ciki take yi, Abban tane ya kira ta ya nuna mata gefensa, wato tazo ta zauna ba musu taje ta zauna,
murmushi yayi yace "sabr ya Binti, dena zubar da kwalla akan danki, hakan ba kyau, ko bakya so yayi albarka ne,"
da wuri da jijjiga kanta ta goge hawayenta, murmushi ya kara yi yace
"Imam yaro ne,amma yana da fahimta, innani mahaifiyar ki ne kuma tana da fada, sannan tana kaunar Imam kuma bata son laifinsa ko kadan, ke kuma bakyason yanda yake yi mata wani abun ko,"
gyada mishi kai tayi yayi murmushi yace,
"tohh yanzu kinsan Imam nada fahimta, cikin nutsuwa zaki na daura shi akan hanya, ki nuna masa abinda yake ba dai bane, ba dole sai agaban innani zaki stawatar mishi ba aa daga baya sai ki kirashi ki mishi fada, akan abinda yake mata, sannan ki dena yin fushi dashi haka, dan zai iya jawo masa mastala arayuwar sa, in ya bata miki rai ki daure ki samasa albarka, ki kuma masa fatan shiriya, sannan kiyi kokarin daura sa akan hanya, ki kuma dena bata ran mahifiyarki akan Imam, in suna abu karki kula su ko ma kibar inda suke, inta bukaci kimasa fada to sai kiyi,"
"tohhh Abba inshallahu zan kiyaye",
" Allah miki Albarka, "
"amiiin Abba"
sallaman da akayi ne yasa hankalinsu ya koma kan wanda yayi sallaman tare da amsa masa,
wata yar matashiyar yarinya ne tashigo, hannunta dauke da basket wanda da alama na abinci ne sai wani jaka,
kallo daya zaka mata ka hango stananin kaman da suke da innani,
Faruq ne yaje da gudu ya mata oyoyo itama oyoyon tamishi kafin ya karbi jakan hannunta suka karaso har kasa ta stuguna,
cikin yaren fulatanci ta gaisar da Chief Imam ya amsa fuska dauke da faraa, ta juya bangaren innani ma ta gaishe ta, itama ta amsa sannan ta gyada ummin Imam, ta mata ya jiki, ta amasa mata gaisuwar duk cikin yaren fullanci,
Faruq yace" Umaima zo kiga triplet din mu"
murmushi tayi tace
"kaide little baa rabaka da shirme, triplet kuma a ina, ina muka samu yan uku,"
hannunta yaja yace
" zo kigani,"
haka yakaita har gaban gadon yaran dake kwance abin shaawa,
ware ido 👀tayi ta dafe kirji tace
" kai mai zan gani,"
ta juyo ta fuskanci su ummi tana neman karin bayani little yayi wufff yace
"mata stintar su muka yi nida jaddi na harda mamansu,"
waro ido tayi tace "
mun shiga uku stintarsu kuma, umma wai haka,"
tabe baki tayi tace
"bakiji abinda ya fada bane ko karya zai miki,"
"shine kuma aka wani hada su da islam kalen su shafa mata wani cutan waya sani ma ko aljanu, ne gaskiya bai dace ahadasu da islam ba,"
hannu tasa da niyan dauke islam innani ta daka mata wani stawa
"keeee karki kuskura baki da hankali ne waye sa'an ki anan, ke zaki nuna mana abinda ya dace muyi, wa kika fi,"
zumburo baki tayi gaba tace
"haba umma ni mai kuma nayi ai gaskiya na fada, kawai daga stinto yara sai ahada su da namu dube su fa kamar wassu yayan aljanu",
innani ne ta hau banbami da sababi shiko,
Chief Imam bai ce kala ba sai hasaso abubuwa da dama da yakeyi game da yartashi Zainab, wanda halinta ya ban ban ta dana yar uwarta,
kai kaf gidan ma ita halinta daban ne ita tana da bakin hali, bata son mutane bawai hayaniya ne bata so ba bare ace miskila ce aa ita nata bakin hali ne ayanda ya auna, tana kuma da hassada wanda har yar uwarta ma takanyiwa, tana kuma da girman kai da son ace tafi kowa, yana da labarin irin tabaran datakeyi arugarsu ko abota bada kowa takeyi ba sai mai kudi,
kuma yanzu ma yasan kyan yaran data gani ne yasa ta ce wa kamar aljanu,
haka koda aka haifi islam sanda tayi furucin daya girgiza shi, wai ita ma sai ta auri balarabe wanda yafi mijiin yayarta kyau ta haifi yayan da suka fi na yayarta kyau,
firgitt ya dawo normal sense nashi jin kukan jariran da alama sun tashi daga bacci,
kuka suke ba kakkautawa wanda suka ki yin shiru innani tace
"wannan bazaa akai su gun mahaifiyarsu ba kuwa, ko in sukaji dumin jikinta zasuyi shiru,"
ballawa Zainab harara tayi tace
"muna fuka mai bakin halin stiya sai ki dauki dayan muje ai,"
,Chief bai ce kala ba ya mike ya musu jagora har dakin da mtar ke kwance abun tausayi suka shiga,
wani dummm zuciyan Zainab yabayar ganin irin kyan matar wanda yasa ta mugun rena kanta,
tabbas duk inda zaa kwatanta kyau matar nan takai har tafi dan ko kyau da kanshi ya ganta sai ya bata guri,
stawan da innani ta mata ne ya dawo da ita hankalinta
"zaki bani yarinyar ne ko saina gaggaura miki mari,"
sum sum tamika mata dan duk rashin kunyar ta tana storon innani ta dake ta,
dan sai tayi kwanaki bata ware ba karban yar tayi ta kwantar da ita akirjin mahaifiyarta yanda tayi wa dayan,
kamar kibtawa da bismillah kuwa sukayi shiru basu kara cewa komai ba, suka yi shiru sai sauke ajiyan zuciya da sukeyi akai akai, cikin mintina kadan suka koma bacci balla mata harara innani tayi tace
"kije ki dauko mun jakan kayana da kayan sawan yaran, ki kuma kawo mun abinci,"
zumbura baki tayi tace nifa ban san inda kayansu yake ba, tana magan tana aunawa matar dake kwance harara wanda bata ma san tanayi ba,
innani ne tayi kanta tamkar zata gaggaura mata mari ko ince da niyan gaggaura mata mari ganin hakan yasa ta fita da gudu
tana fita ta hadu da Abban su wato Chief kallon daya bita dashi ne yasa ta hadiyan yawu tasan tabbas ransa ya baci matuka akan abinda tayi,
ita ta manta cewa yana dakin ma tayi wannan diban albarkan wani miyau mai zafi ta hadiya, dan tasan zataci stelen uwata dan Abba yamafi umman zafi sosai,
ai da sauri ta wuce kanta har wani hardewa yakeyi ta isa bakin kofan dakin saide abinda taji yar uwarta ta na fada ne yasa ta ja burki,
,wani murmushi tayi na nasara dan tabbas ta samu makamin da zata fatattki matarnan da yayanta daga gidansu, dan tasan muddin matar nan zata cigaba da zama agidansu tofa kashinta ya bushe,
yanzu ma tasan sai Abba yaci ubanta dole tasan yadda zatayi ta ingizasu wani murmushin ta karayi ta murda kofan dakin
QUEEN 👑 MAHIRAH 👸IDRISS
🧚THE TWO LIGHT ✨[RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰]🧚
Story & written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER 📖🖊️
BOOK 1
Follow this link to join my WhatsApp group shower 🚿 with comment and react 😁😍🤩
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
🧚3🧚
Murda handle din kofan tayi ta shiga cikin dakin inda ta hango ta tana zaune bisa sofa dake dakin da alama tayi zurfi cikin tunanin da take yi,
cike da kissa tayi wani murmushin munafurci 😏sannan ta karasa inda take tasa hannunta a shoulder dinta wanda yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula,
kara marairaice face nata tayi tace
"Adda Fati kema kina tunanin abinda nakeyi ko ?,"
cikin rashin fahimtan abinda take nufi tace
"mai kenan",
dan cuno😗 baki tayi gaba
"come on Adda don't pretend kidena acting as if like bakisan abinda nake nufi ba,
after all kin san komai",
dan hade fuska tayi
"nifa bana son shirme kiyi magana yadda zan gane kidena mun shiga da futa",
marairaice face nata tayi sai tazama abin tausayi,
"game da twins din nan nake magana nasan kema bawai kin yadda dasu bane musamman yadda inkika kula suke kama da little da ita kanta Islam din ma kamar yayi yawa ni dana gansu har na fara jin shakku,"
cike da zakuwa da son kin gasgata abinda yar uwar nata ke kokarin fada
" shakku akan mai,"
itako ganin yadda Addan nata ta dan rude ne ta kuma kafeta da ido, yasa tayi saurin sadda kanta kasa tana wani culprit din smile😏 a heart nata,
"yi hakuri Adda (yaya or anty) naga kaman ranki ya baci ni bari ma naje nayi abinda aka aiko ni,
dama Innani ne tace nazo na diba mata kayanta ita da sabin jikokin nata data samu daga gurin sirkinta,
ban san ma mai tagani ajikinsu ba wanda yasa sukafi Islam mutunci agunta ko dan ma ba abin mamaki bane yadda naga wannan mahaifiiyar tasu ba abin mamaki bane in hakan ta faru,"
tana maganan ne cike dason tunzura yar uwar tata bata yi kuskuren data bari suka hada ido ba,
sai de tana satan kallonta da kuma fahimtar irin yanayin data shiga wanda da alama hakan ta ya cinma ruwa,
ta cigaba dayin aikin daya kawo ta yayin da take cusa mata zancen da tasan tabbas zasuyi tasiri a zuciyar duk macen data cika mace mai kishin mijinta da aurenta,
wanda sai ka kai zuciyar ka nesa kafin ka kubutar da kanka daga halaka cikin stawa tace
"ya isa wai mai kike nufi ne",
murmushin nasara tayi a heart nata kafin ta karaso inda take hannunta dauke da basket da jakan kaya ta dire su agaban yar uwarta tace
"abu biyu nake nufi anan, na farko mahaifiyarki ta fifita wassu bare akanki wanda bata san asalinsu ba,
ta tafi ta barki alokacin da kike bukatanta,
haka danki ya kaurace miki ya tafi gun 'ya'yan da baa san daga ina suke ba,
abin dubawa anan shine mai zaisa little yin hakan??
aganina ba komai bane ke jansa sai jini, ina nufin jinin dasuka hada da yaran,"
ba shiri ta dago manyan idonta ta zubasu akan Zainab, da ta cigaba da zuba zance
"ehh abinda nake nufi kenan yaran jinin Faruq ne shiyasa jikinsa ke rawa akansu,
sanin kanki ne Faruq baya shiga harkan yayan mutane amma yaran nan ko ina aka kaisu yana bayansu sabida mahaifi daya garesu kuma shine mahifin Faruq k.......,"
hannu ta daga mata " ya isa Zainab bana son maganan banza, ni ba sa'ar ki bane da zakina fada mun duk zancen da kika ga dama hak mijina ba abokin wasan ki bane,
da umma ta tafi gunsu ai ba kina tayi ba su sun fini bukatar taimakon ayanzu shiyasa,
in Faruq yaso yaran to wannan ra'ayinsa ne", .
murmushi Zainab tayi tace" Adda kenan shiyasa kullum ake cutarki sabida kin fiye tausayi da yawa,
asibitin nan acike yake da masu aiki mai yasa ba'a umarcesu dasu kula dasu ba,
ita umman Dr ne,??
kuma shi mijin naki mai ya hanashi zuwa ya duba ki in yana da gaskiya,
ina tun kafin ayi suna dayazo bai kara zuwa ba,
kuma ai yasan baki da lafiya naga tun cikin ki yana wata 5 ya dawo dake nan rugar,
to shi waliyyi ne da zai zauna ba mace har na stawon wata hudu,
shi yasan abinda yakeyi kuma ba komai bane sai barikanci anan yasa mu yaran nan,"
tasssssssss kakeji Fatima ta wanke Zainab da marin da sanda taga taurari, sannan ta nuna ta da manuniyar ta
"this should be the last time da zaki kara fadin maganan banza akan mijina,
if not i will make sure i break every single bone from your body",
Zainab dataji marin tamkar saukar aradu ta ka ta gagara ko mastawa daga inda take,
.she is suprise cos Addan ta bata taba ko da zungurin taba arayuwarta duk dako irin azaban rashin kunyan datake mata, ko wani bata so taga yana tabata amma yau ita ta mareta da hannunta,
"Adda ni kika mara akan wassu kazaman bare da bakisan asalinsu ba,
stintattun mage ni Zainab Adda akan na fada miki gaskiya shine kika mun haka akan mutumin da bakisan asalinsa ba shida kwasassun mutanan can,"
tana magana tana pointing door da index finger dinta stawa ta daka mata tace
"get out Zainab ki bace mun daga gani na",
stugunawa Zainab tayi ta dauki basket da jakan ta kama hanyan fita sanda ta isa bakin door din ta juyo, tace
"wallahi zakiyi dana sanin hakan zakiyi mamakin abinda stintattun magen naki zasuyi,"
gafff tabude kofa ta fita zaman da ba shiri Fatima tayi dan tabbas zancen Zainab ya soki zuciyanta matuka,
taji zafin zancen nata sosai ta kuma kara dagula mata brain,
tabbas dabata kai heart nata nesa ba da tayi abinda tasan zatayi dana sani daga baya,
tasan bazai taba cutar da ita ba amma ai abinda Zainab ta fada yana kan gaskiya,
da wuri tayi kokarin kauda tunanin da ambaton sunan Allah wanda da haka ne ta yaki heart nata afari har ya hanata aikata abinda zatayi dana sani.
bata staya ko ina ba sai dakin patient din inda tabar Innani da ta cika tayi famm dan haushi,
tun dazun sai jiranta takeyi ga Faruq sun futa da chief bare ta aika shi ya kira ta,
tana bude kofa ta fara zazzaga mata bala'i kamar an kunna fanfo
" uban mai kika tsaya yi acan din 'kika barnin ina ta jira",
shiru tamata kamar bata jita ba hasala Innani ta karayi tace
"dan uban ki ba magana nake miki ba kinmun shiru",
zumburo baki 😙 gaba tayi tace "to ni mai kike so ince miki"
"eyyehhh lallale Zainab wuyanki yayi kauri ani kike zumbura baki, ki jira intashi sai naci ubanki dai dai gwargwado,
kuma ki wuce ki koma gida ki hada abincin Abbanku da furansa,
ki kuma hadawa Faruq kayansa ki bawa bashir driver ya kawo,
ki kuma tabbatar kinyi abincin dare da wuri wallahi kika barmu da yunwa irin na jiya zanci ubanki cikin buta,"
bata ce komai ba tayi ficewarta tabar dakin takama hanyan barin hospital din daniyan komawa gida don yin abinda Innani tasata tana tafiya tana kissima irin abinda zatayiwa wayannan stintattun magen da tun safe ake cimata mutunci akansu tun da safe yau take ta faman shan wiya akansu yau hartana murna Innani zata dawo ta karbi aikinta sai kawai akace sai gobe,
ashe duk mastiyatan nan ne suka hana su dawo wa kwafa tayi ta cigaba da tafiyanta har ta isa gida.
lokaci yacigaba da tafiya yabar zuciyoyi cike da waswasi Innani bata nuna gajiya warta wajen kula da wayannan yaran ba,
wanda ita tausayi ma suke bata haka har dare yayi kamar yadda Faruq ya nace haka ko akayi anan asibitin ya kwana.
washe gari Innani da kanta tayi wa jariren wanka suda islam,
akasa masu kaya sunyi matukarr kyau da daukan hankali,
ta kuma basu madaransu Dr ne ya shigo dakin da marar lafiyan take inda yasamu Innani, chief da fatima harda Faruq adakin,
bayan sallaman da yayi aka masa, iso akayi masa ya shigo suka gaisawa yamawa fatima ya jiki' tace
" Alhamdulillah yayi sauki gashi har na fito ma",
"little imam how are you?,
yace" am pretty fine,
Dr how about you ?,"
"am also fine ina Dad dinka, kunyi waya ne,"
"ehh munyi yace ma yana hanya ya kusa isowa rugar nan, zai zo yaga twins din mu ai nabashi labarin su,"
murmushi dr yayi ya shafa kan shi sannan ya karasa gaban gadon patient din ya dubata sannan ya juyo ya fuskan cesu with full of hope, Innani tace
" ya jikin nata",
yace "Alahamdulillah da sauki zata ma iya tashi nan da good 3 hours nan da wa uku kenan,
sai de zata iya tashi a firgice duba da irin yanayin data shiga a fari,"
"tohhh yayi kyau Allah tashi kafadunta,"
ameen kowa ya amsa dashi inji chief karasawa yayi gurin babies din yace
" mashaallah look at them they are so pretty just like egyptians,
kamar larabawa Allah de ya saka da alkairi gaskiya ba karamin kokari kuka yi ba chief da kuka cece su Allah saka muku da jannatul firdausi,"
murmushi chief yayi yace
"kuma ai kuna kokari sosai Dr, "
"ai bamu kai kuba kudin na daban ne, Allah de ya saka muku da alkairi,"
ameen suka amsa kafin ya fita ya je don duba sauran patient,
yabar kowa da abinda ke saka wa a heart nashi baya Fatima da abin duniya ya isheta,
. ba abinda ya kara daga mata hankali sai ganin matar datayi ganin irin zillan kyan da Allah ya mata, ga wani kwarjini na musamman da daukan ido da takeyi,
in tace bata storata ba tayi karya maganan zainab ne ya fara dawo mata karde ita ne dako ita ne data shiga uku,
tasan karshen zamanta da mijinta ne yazo muddin ya kasan ce abinda take storo ne,
tohh tagama aiki ajiyan zuciya tasauke, numfashinta har wani hardewa yakeyi,
jin an dafa kafadarta tane yasa tayi saurin daga idonta taga Abbanta dake gefenta fuskarshi dauke da smile, yace
"babu abinda zai faru sai alkairi,"
itama murmushin ta kakalo ta mishi bata ce komai ba.
.
wata hadadiyar car ce mai numfashi da keta hazo, ta keto cikin wannan rugar,
a back seat wani kyakkyawan halitta ne ke zaune yana sanye da Ralph Lauren brown suit da yayi masifar amsar jikinsa akalla zai kai 35years,
sai de sam shekarun basu nuna ajikinshi ba fari ne tas Mai daukan ido da hankali, kyakyawa ne Son kowa kin Wanda ya rasa,
Fuskansa zagaye yake da hadaddiyar man's pride dinshi Wanda da gani taji naira sai sheki take Tasha gyara haka sumar kanshi acike yake tamm dayawa baki wuluk dashi mai stansti,
Pointed nose nashi ya Kara kayatar halittansa Yana Nan zattt dashi ga small redish lips nashi masu ban shaawa, Eyes nashi are sexy kamar Mai Jin bacci haka suke ga zararan eyelashes nashi Daya Kara narkar da idon, eyebrows nashi tamkar shi yayi shaping kayanshi.
Yanayin kyansa da hasken sa yasani tan taman Anya bahaushe be kuwa ganin yanayin hasken fatar shi wanda azahiri yafi kama Dana larabawa.
Kai staye baza ka kira shi da balarabe ba sannan baza ka kirashi da bafulatani ba kai staye,
sai de kace dashi HALF CASS wato ruwa biyu,
kallo daya zaka masa ka hango zallan damuwan dake shinfide a kyakyawan face nashi ga wani stinkewa da heart nashi keyi,
duk da yasaba da hakan aduk lokcin da ya sako kafanshi a Nigeria hakan kuma nada nasaba da rayuwarsa na baya,
sai de yau stinkewan heart din na daban ne yarasa mai yakeji farin ciki ko aka sinsa,
sai de yana jin wani anna shuwa na daban yana jin tamkar zai hadu da wani abu mai mahimman ci to amma mai ye shi,???
shine amsan daya gagara bawa kanshi abu 3 ne masu muhimmanci a arayuwarsa,
daga inlaw dinsa sai wife nashi da children nasa Faruq da Islam,
sai kuma mai kankat wato FAMILY nashi,
tabbas yana farin ciki zai ga 'ya'yan sa da matarsa da inlaw dinsa,
saide akwai wani abu na musamman ayau to mai ne ne wannan???,
family dinsa yasan yayi ban kwana dasu badan baisan inda suke ba ko basa raye ba aa sai dan wani dalili mai karfin gaske,
dogon numfashi ya fesar 😤kafin cikin husky voice nashi yace
"bashir,"
da sauri ya amsa yace
"su ummin little sun koma gida ne ,"
"aa"
shine abinda bashir yace" okayy to kaini hosptal din ",
"tohh"
ya amsa masa dashi direct asibitn suka wuce basu wani dade suna tafiya ba suka iso,
parking yayi a harabar hospital din ya fito da wuri ya bude mishi cab din car din ya kai akalla 5 minute kafun ya zaro kafarsa ta dama bakinsa dauke da bismilla ya kara daukan lokaci kafin ya fito gaba daya,
wani irin bugu heart nashi yayi daya sa shi rinste idon shi da sauri,
ahankali ya fara taku cike da takama da mazantaka da izza, yana tafiya tamkar yana tausayin kasan kallo Daya zaka masa kanhango jinin SARAUTA dake yawo ajikinsa ga yanayin halittansa surarsa ya tabbatar mun da cewa ya hada da larabawa,
Yanayin halitta da girman gabansa ne yasa shi cikin jerin giant don a murde yake sanadin mosta jiki da yakeyi da Kuma yanayin halittansa,
bashir ya mishi jagora har dakin da su innani suke,
daga cikin dakin kuwa wannan baiwar Allah ta farka da salati abakinta kafin ta wani razana ta fara dube dube,
ganin mutane a zagaye da ita yasa ta kara rikicewa sosai ,ta fara ambaton sunan Allah,
Innani tayi kanta daniyan mata bayani amma ina ta dira daga kan gado tana yiin baya baya tana tambayansun abu daya cikin yare hudu,
na fari FULLANCI na biyu TURANCI na uku LARABCI sai na hudu HAUSA tambaya take ina
ya'yanta?,
suwaye su?,
kara yowa kanta Innani tayi kawai ta fasa ihuu tace
"don't touch me,"
ana cikin wannan hali sai wannan mutumin ya shigo dakin da sallama aba kinshi kanshi akasa,
jin wannan voice da ko daga bacci ta tashi baza ta taba mantawa bane yasa ta juya arazane sukayi 4 eyes 👀 dashi daga shi har ita suka staya cak kowa na nuna dan uwanshi baki dauke da zance da kyar yace
"ke! ya akayi kika san inda nake,"
itako da gudu taje ta yi hugging nashi so tight aka bar su Innani da sake baki😲🤤
END OF PAGE 3
MU HADU A PAGE 4
Queen Mahira Idriss
Follow this lin to join my WhatsApp group and shower 🚿 me with comment and react 😁😍🤩
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
Comment and share 😁
🧚THE TWO LIGHT✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰)
Monday, 01 january, 2024
04:48:07 PM.
Story and written by
Queen Mahirah
The adapted Expert Writer 🖊️📖
BOOK 1
🧚4🧚
Da gudu taje tayi hugging nashi so tight as if like her life defend on him ta fashe da wani mastiyacin kuka mai cike da maanoni da yawa,
kan kameshi takarayi sosai tana cewa
"am i dreaming pls in mafarki nake kar atashe ni,
i cant blieve this akace wai you were dead ina kashiga for all this long?
kabarmu cikin tashin hankali tunda ka tafi komai ya lalace komai ya baci ,"
dago da kanta tayi daga broad chest nashi tana kallon fuskanshi kallo daya zaka mishi ka tabbatar da ya shiga wani yanayi,
his eyes turn red as if like an wasta masa pepper gaba daya mood nashi ya canja
kana kallonsa kasan an taba masa inda yake masa kaikayi hannu tasa ta tallafo face nashi
tace "kayi shiru say something,"
daga can baya ne suka ji anyi gyaran murya Innani ne data gagara hakuri tayi gyaran murya dan gaba daya ta rasa mai zata fassara abinda ido da zuciyanta ke gani,
ba ita kadai ba kowa dake wannan room din hakan yake agunshi kai hatta little ma kanshi ya daure,
bare Fatima da gaba daya komai na dakin ke juya mata maganan zainab ne yake dawo mata cikin kwanyarta a halin data ke ciki kadan yarage heart nata baiyi blowing ba,
numfashinta har harde wa yakeyi Innani ne ta kara breaking silence din da cewa
"ko zaku samu ku mana bayanin abinda ke faruwa anan Hamma,"
[ haka innani ke kiransa dashikasancear sunan su Daya da yayanta ]
kokarin raba ta da jikinsa yayi dan sai yanzu ma ya tuna a ina suke,
wani ihu ta kara yi ta kan kameshi tana
"wayyo Allah na zasu kasheni kasheni zasuyi AKHIE, kataimake ni,"
ganin yadda ta riki ce ne yasa Innani dafe kirji tace
" mun shiga uku daga taimako sai abu ya zama bala'i,
mai zan gani haka baiwar Allah,
wai mai ma yake shirin faruwa ne??,
mai ne ne hakan wacece ke kin wani tukuikuye shi,"
itako kara kan kameshi tayi dan gani take kamar zaa raba su tamkar zata shige cikinshi,
Innani ta rafka uban salati tace
"mun shiga uku mai zan gani ni khadijatu matar sheiky keta hakki haka agaban magabata da ranar🌞 Allah,
kai Hamma kayi mana bayani mana ka cire mu aduhu🌚,
wannan wani irin abune agaban sirkanunka da danka uwa uba harda matarka,"
tana maganan ne cikin kukan neman magana irin nasu na stofi da gefen mayafinta take goge
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 25