Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nace k'alau, amma Kije taga zahir dai." Naji sanyin dad'I da momin'sa ta soma damuwa da al'amarina. Nace. "Yanzu dama nake tunanin naje na gaishesu, ita da Abba, to ban Sani bane, ko sun tashi daga bacci, ko basu tashi ba." Yace. "Ai mu nan gidan, in dai muka tashi da a suba mukayi salla, to bama komawa bacci. Idan ma a kwai mai komawa baccin, to nine, kuma ba kullum ba nima, Sai San'da bani da uzurori da yawa. Amma Kije Ku gaisa da momin, shi Abba ya fita yau da wuri, amma an jima zai dawo. Na dubeshi, cikin rausaya idanu. "Ancle, muje kayi min jagora, kaji?". Yace cikin bud'e min idanuwa. "Kina da larurar makan'ta?". Nace. "Ko d'aya". Then, why kike so na jagoranceki?". "Kunyar Momi, nake ji Allah." Ya gyad'a kai "Kina da aiki a gaban'ki Yarinya. amma fa bazamu jera ba gaskiya, Sai dai ki bari nayi gaba, ki biyoni a baya." Duk da bansan k'asadin'sa ba game da haka ba na hak'ura da hakan, saboda tuni na soma fahimtar'sa, Ancle Fa'iz, mutum ne shi da bashi karb'ar uzurin magiya ko roko, shi yasa ma ban soma ba. Sai da na bada sa'oi tukun na bi bayan'sa. A harabar tsakar gida na had'u da Muhibbat tana Shara, muka gaisa, amma dai banga sakin fuska sosai a wurinta ba. Ita kuwa Khairat, tana kichean tana had'in Karin kumallo, domin k'amshin soye soyen'ta ma ya kauraye gidan. Da yake, Ina d'an hangen'ta, duk da bata hangoni ba, na k"arasa bakin k'ofar kichean d'in muka gaisa, nayi mata sannu da aiki cike da fara'a saboda naga fuska a wurinta. Da fara'a sosai ta amsa tace. "Yauwa Anti." Yarinyar tashi d'aya ta shigemin zuciya. Da alamu zatafi Muhibbat kyakykyawar Mu'amala. Idan kuwa haka ne, Sai nace ta gama tako sa'a a matsayinta na 'ya mace. Domin kuwa ba k'aramar kyakykyawa bace Khairat. Kyau da hali, kuwa ai sai mai sa'a kan sa'a, d'ai d'ai Ku ke had'a duka. A zaune dirshan na samu Ancle Fa'iz a falon Momi, kuma a gaban momi, yana shan tea. Duk da jin shigowa ta, bai cira kai ya dubeni ba, face momin da ta zubamin idanu, Tana k'aremin kallo a hankali. Ban kuma yi Mamaki ba, saboda jiya da a ka kawoni wurinta da daddare fusKata a lullub'e take har muka baro wurinta. Yanzu ne kenan zata k"aremin kallo sosai. Bayan na zube na gaisheta tace . "Sumayya, yau kin wayi gari, a sabon wuri, yaya a kaji da kewa?". Kaina sunkuye cikin ladab nace . "Momi ai bani jin sauyin komai, tunda Ina tare daku, kamar Ina gida ne.Ku iyayena ne, su khairat kuma 'yan uwa nane". Na lura furucina ya faranta mata, a fuskarta na Karan'ta. Momi da Ancle Fa'iz suna kama sosai, har kalar fatar fara tas, mai sofanen jajaja, da kuma k'wayar idanun mai haske da yawa, da yalwar bakar gira mai duhu.Hasken cikin idanun suma da har yake bada launin shud'I shud'I iri gudane. Duk da shekaru, sun d'an hauta kasan ta zuba kyau na lokacin k'uruciya, domin kuwa har yanzun yana nan, sauyin kad'an ne, na turawar shekaru. Tabbas barewa bazata tab'ayin gudu ba, d'anta yayi rarrafe. Momi ta kalli Ancle Fa'iz da yake karyawa a nutse, tace. "Sumayya ga karin kumallonku can Khairat zata kai muku, kuma ga mijinki yazo ya dirarwa nawa, ai Sai ki matso Ku cinye Kawai tare, Khairat ta k'aro muku" . Kunya naji ta kamani, domin bazan iya wannan aiki ba gaban Momi. gashi kuma bazan iya bijirewa umarnin'ta ba. Ancle Fa'izu kub'utar dani yayi da yace da sauri. "A'a Momi, wannan ai yama k'are, ko bai k'are ba, gwara a kawo mata nata. Ni yau girkin ma na khairat, maleji nake yi da shi, duk ta cika magi. Can yana cikin ci yayi saurun furzar da wainar k'wai. "Magi, na tauna Momi, me ya samu Khairat haka?". Momi ta dubeni tayi 'yar dariya. "Sai kinyi kamar kina yi Sumayya, domin kin had'u da Miji mai tsirfa da k'orafi, ko yaya aka kuskure. Ni na faraci kafin shi amma banji wani magi ba. Gishiri ne ya fito d'an kad'an. Kuma baiyi yawan da za'a yi k'orafi ba ko kad'an." Nan ne naga ya d'aga idanu ya dubeni da sababben kallonsa mara manufar komai yace. "Sumayya, karfa Zancen Momi yafa kid'imaki, duk da gaskiya ta fad'I, amma nasan baza'ki iya dani ba kema. Shi yasa girki iya cikinki za'ki rink'ayi idan kin soma girki. Ya dubi Momi kuma "Momi, kwanon a bincina fa yana nan a wurinki kamar da, saboda Kinfi kowa sanin yarda nakeson d'and'anon a binci ko yaushe.Khairat ke kamanta irin girkinki, to naga Itama ta soma shiriricewar yin girki irin na Muhibbat, yau a bu yayi kad"an gobe yayi yawa, to Itama na yafe ta, randa duk ba kya gida baki samu damar yimin girki ba Momi, waje zanje na samu wanda yayi min na saya wallahi." Banga wani sauyi ba Sam, a fuskar Momi, game da furucin d'anta, duk da tace. "Kadai biyo hanyar da bazata b'illemaka ba Fa'iz. Kayi aure, amma baka da kwanon a binci? Kana dai da aiki a gabanka". Yace. "jama kuwa momi, kuma nasan zan iya ne". Nan nasan ko a jikinsa game da furucin momin sa, kuma hakan ya tabbatar min, suna hirar wasa da momi, kuma tana sake musu yarda basajin kunyar fadin abu a gabanta. Wani irin kallo da kulawa, naga momi tana yiwa Faiz na tsurar kauna irin ta uwa da danta. Nan tasan dan gaban goshin momi ne. Kaina yana sunkuye Momi da Ancle a na ta hira a nutse yayin da yake shan tea, abin gwanin shaawa. Can Ancle ya waiwayeni da nake can gefen Momi. "Sumayya kije ki karya rana tana yi, naga daren jiyan bakici komai ba, tun da banga kin bude kayan ma da na shigo da shi ba, daren jiya". Momi tace " Haka tayi bacci bata ci a binci ba, garin Yaya kai kuma ka barta, me yasa za kayi haka, bayan kasan amare basa iya cin abinci a ranar baki daya". Ya dan waro idanu ga Momi kadan. "Momi bafa laifina ba ne, sanda na dawo na tarar tayi bacci, da alamu ma bata samu bacci ba kwana biyu yarda na fahimta, domin baccin mai nauyi naga ta nayi, shi yasa na barta kar na tasheta ta samu ciwon kai, ko ta kasa komawa, wai ni tausayawa nayi ai". " Eh da gaskiyarka, bari na kira khairat ta kawo mata nan kawai". "Aa Momi bafa zata iya karyawa a falonki ba, nasan halinta, ta kai mata komai falonta dai". Ni dai ban tsinka ba, sai ya sake kallo na bayan ya dire cup din tea da ya gama sha. " Sumayya ko zaki karya nan din? ". Murmushi kawai nayi, don bazan iya cewa A'a ba, ko eh. Kiransa a kayi a waya kafin ya kuma magana, in da naga ya mike da nufin fita, bayan yace. " Momi ina zuwa Salima ke kirana". Jinayi ni dai kamar an daureni da da bai bayi, zuciya ta kuma ta soma wani dan kidan kalangu. Yayin da na fahimci momi jikinta yayi lakwas ita ma, ko na menene oho. _Taku_ Zainab ilyas mazawaje.. ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant inteligent_ Writer ....✍️ *Page 12* Bayan na sauko daga saman Momi na kuwa tarar tuni khairat ta kawo min karin kumallona, tea a fulas na shayi da madara da bornvita da kwalin cube na suger a gefe sai soyayyan kwai da dankali ga kuma bread a gefe dai. Sai da na waiwaya gefe na kula da wata poly bag mai kyau da Ancle Faiz ya shigo da ita daren jiya. Na bude in da na tarar da gasassun kaji biyu manya lullube cikin rolling silk paper, anyi musu gashi na kwararru sosai da ko kwana biyu suka yi baza suyi komai ba, sun sha cabbage fried onion da tomatoes da kayan kamshi mai tsinkar da yawu. Tuni kuwa yawun nawa ya tsinke, naji cikina ya soma kugin yunwa, domin gaskiyar Momi jiyan yini guda ban iya cin komai ba, saboda fargabar sabuwar rayuwar da zan fada. Amma nasan Ancle tun da bai taba ba har yanzu, wata kil nasa dabam ya dauka, na dauke robar babbar yagort da har lokacin da ragowar sanyin sa, cikin wata karamar poly bag shima, na a jiye gefe, dole sai anjima na dada dumama kazar, tun da ta kwana. Na zauna ina karyawa zuciyata tana ta sake saken yarda al'a mura zasu kasancemin a gidan, gashi na shiga tsakanin tsofaffun masoya biyu masu masifar son junansu, wato Ancle da Salima, kaddarar aure ta cillo ni auren gun wanda zuciyar sa ta na ga wata har gobe, tare burin ya mallaketa, amma kaddara ta riga fata, nice kaddararriyar matarsa ta farko da Allah ya hukunta tun fil azal. A gurin Ancle auren wata manufa yayi, amma ni a zuciyata sam ba na halarto hakan yanzu tunda igiyar aure ta sarkemu. A haka dai kamar bazan fuskanci wata matsala ba a gidan ga yarda na lura, harshi kanshi Ancle Faiz banga ya nunamin wata halayya mara dadi ba, sauyi ma na gani a kan kafin muyi aure. To fatana tafiyar ta ci gaba a haka ko bazai rinka shiga cikin sabgogina ba yarda na ke so, zan dai samu nutsuwar da zan soma janyo raayinsa a hankali, daga alkiblar da yake fuskanta, duk da gashi ya soma da cewa ma Momi ce zata ci gaba da yi masa girki duk da yayi aure. Ire iren wadan nan basu soma damuna ba saboda nasan manufar auren da mukayi da shi a zuciyarsa . Amma ni a Zuciyata, aure ne nake ji munyi mai manufa kyakykyawa, irin wanda a keso. Shi yasa ni a binda zan maida hankali a kai, shine ta yaya zan janyo ra'ayin'sa gareni kawai na kuma fahimtar da shi kuskuren da yake kokarin aikatawa, wanda nake ganin zai yi wuya ya fahimce ni, ko ya ma saurare ni a yarda nasan waye Ancle Faiz tun tuni. Bayan na karya na hau sama na gaishe da Abban su Ancle da naji shigowarsa, mutum mai halin karimci da kirki da ka ganshi, yayi ta samin albarka, tare da adduoi cikin auren mu, duk a gaban momi, domin suna tare. Zuciyata naji ta washe da samun nutsuwa da farin ciki da halin karimci da adduoi da Abban yayi min. A hanyar saukowa daga bene mukayi kicib'is da Khalifa, in da ya dakatamin yaja baya, domin na wuce. Shine farkon ganina da shi, Shima haka. Ta yiyu wannan dalili naga yana yimin wani mayataccen kallo Sama da k'asa nasha mur, saboda duk namiji mai wannan hali na kallon k'urilla, haushi yake bani.Amma duk da haka, bai sauya da k'uramin idanu ba, sai fara'a da ya sake sakima yana washe hak'ora, a haka muka gaisa, ya haye saman Momi. Ni kuma na sauko, na nufi d'akina, in da naga Muhibbat tana wanke wuri da tsintsiya. Nayi mata sannu da aiki, ta amsa cikin wani salo na i sa. Araina nace, wannan miskilanci ta d'orawa kan'ta, ko kuwa haka yanayinta yake?. Bani da mai bani amsa, shi yasa dole sai munyi nisan zama da ita zan canki amsa. A kan kujerar da Ancle Fa'uzu ya tashi ta falona na kula da wata tsadaddiyar wayar sa a kife. Mantawa yayi, ko a jiyewa yayi yana sane bansani ba domin dazu ai Salimar ta kirashi a waya a saman Momi ya sauko, kenan a falona ya zauna. Halin nawa nayi, na d'auka, domin a ganina yanzu ina da hurumin tab'a abin Ancle Fa'izu, tun da Mijina ne. Numfashina Sai da ya tsaya cak! na wucin gadi, ganin wacce ke kan fuskar wayar Ancle. Duk da ban tab'a ganin ta ba, nasan ita ce. SALIMA. Kyawunta da a ka kod'a to zarta ma da na ganta, a hoto gaskiya. Wani irin kishi naji ya ziyarci zuciyata mai rad'ad'i. Shine shaidar farko da yake nunamin na tsundima tsindim a kogin son Ancle Fa'izu wanda da nake yaudarar kaina da da cewa bana son'sa. Duk da nasan Salima yake so, ni auransa kawai na rabauta da shi, babu zuciyarsa kuma sanadin dai salimar. Hakan baisa na daina jin ciwon kishin sa ba. Salima tafi kama da irin larabawan Lebanon d'in nan, da basu cika haske ba da yawa, Sai tsagwaron kyau. Bata kai hasken fatar Ancle ba ko kusa, illa dai cikar halitta ta koina. English wear's tasa, wacce ta matsemata jiki, surar halittar ta ta d'iya mace, ta bayyana a sarari, domin rigar daga sama kamar 'yar shimi bata da hannu a jiki, gata mai nuna surar jiki daga ciki, domin shef din unders dinta har launin kalar a na hangowa, rigar banzar mai shara shara bata boye komai nata daga ciki ba, don da ita rigar saman da baasa ba, ni banga bam bamci ba, kanta kuma babu d'an kwali ta Saki yalolon gashinta ya zubo gadon baya,wani kad'an ta gefe ya zararo kan k'irjinta. Ni dai nasan tana sane kawai tayi wannan shigar ta iskanci, bawai rashin wayo ko rashin sanin kuskuren haka ba, duk wanda yaga hoton dole ya karar kai tsaye akwai manufarta. sai dai meye manufarta ga hakan, ubangiji masani. Na sake kallon ta a hoton na zumburi baki, na jin haushi. Sam shigar zub da darajar da tayi ta bawa namiji har ya zame masa mudubin dubawa a waya kullum ya sik"eni, bawai iya Kishi bane. Saboda kayan da gani masu tsadar gaskene, sai dai sun tashi a banza, tun da masu nuna tsiraicine gaskiya. Shi kuma Ancle soyayyace ta rufe masa idanu ya biye mata ya iya ajiye hoton a fuskar wayar sama, bansani ba, ko ita ta bashi damar a jiyewar, a fuskar waya ya biyewa soyayya ya ajiye din, duk zai iya yiyuwa. Sau tari wasu matan, suna ganin tallata surar jiki ga namiji wayewa ce, da k'arin janyo soyayya. To wallahi karyane. Na karya ta ni Sumayya. Bayan janyowa kai zunubi, ragewa kai daraja da k'ima ne matuk'ar babu aure gibi kuma sukewa kan'su sosai. Ko namiji bai nuna ba, ko bai hango aibi ba a lokacin to a gaba kuwa za'a karb'i raddi wallahi. To ni Ancle Fa'izu ya fita laifi a wurina, da ya kasa hango kuskuren ballantana yayi mata gyara, kuma wai nan aurenta yake so yayi, sai gashi har ya a jiye hoton ya zauna a fuskar wayarsa, ko yaushe kenan da shi zai fara tozali, idan ya d'auki waya. Tabbas giyar soyayya ta bugeshi yayi yana sane, bawai a ce bai hango illar hakan ba. Irin haka ne, idan namiji soyayyar banza yake yiwa mace, to ya samu kofa, tun da kalar tarko ne a ka da na na kama mutum da shi, ko da ba ma namiji bashi da mummunar manufa kan lace hadari ne, tunda akwai shaidan zuga zugi a gefe. To al'amarin soyayyar Ancle da Salima, bazan iya sharhi ba, tun da bansan ciki da wajenta ba, amma a zato da kallon da nake yiwa Ancle Faiz, ba mutumin banza ba ne, amma sanin mutum na badini, sai ubangijin dai da ya halicce shi. Sai dai nasan ko meye a keyi a boye na rashin gaskiya, wataran zai bayyana. Bansan sanda nayi Jifa da wayar ba jikin bango saboda kishi da haushi. Jikake tus! na d'auka naga glass d'in ya fashe. Na d'ora jikin TV stand. nasan masifa ce kawai zan sha. Iya ka kenan. Duk da Khairat ta kawomin break fast , ban karya ba, Sai da nayi wanka na shirya cikin kwalliya da ado sosai. Na zauna na karya. Har lokacin Ancle Fa'iz banjiyo motsinsa ba, ko yana dakinsa ne, domin da na baro saman momi yanzu bayanan. A shiryen sa ya shigo min, Shima yayi wanka yasa shadda ruwan goro, hartin d'in gajera ce iya gwiwa, gaban rigar anyi masa aiki na kwala mai kyau. Sunfi yi masa fiye da wacce ya cire. Duk da sirrin kyawun ba'a kaya yake ba,a halittar ne, sai baza wani sassanyan kamshi yake yi mai tashi a hankali, da shiga ruhi. Yana shigowa na dake, saboda laifin da nayi masa, amma jikina na soma jin ya soma rawa rawa kadan na tsoro kuma, saboda nasan waye Ancle idan ransa ya baci. Wayar tasa kuwa ya Shiga nema . "Ba nan na bar wayata bane?". Mik'ewa nayi tsam naje na d'auko inda na a jiye. Har na mik'a masa naga yanayi min wani salon kallo, da alamu na tuhuma ne, kafin daga bisani ya d'ora idanu a kan wayar yayi tozali da ta'asar da nayi. Ya sake dubana. "Garin yaya kika fasa min waya?". Na sunkuyar da kai nace. Garin tsautsayi ne kayi hak'uri Ancle." Na koma na zauna a bina. Ransa b'ace yace. "Garin ganganci dai kika fasa min waya Sumayya. Me ya kaiki d'aukar wayar da take a jiye? Lek'en a Siri ko meye?". Naji shigar furucin'sa amma na dake, saboda nina jawa kaina. Kawu Sulaiman ya Sha yi min nasiha na daina tab'a a binda banawa ba, musamman na sirri, nace sai na gani, gudun fad'awa rigima, saboda binciken da nake yi masa a d'aki. Na k'ara bashi hak'uri. "Ancle kayi hakuri nayi laifi, amma bazan kuma ba please". Nayi masa tayi da tea da na Sha saboda ko rabi na kasa sha, bansan dalili ba, ga kuma yunwar ban cike gurbinta ba, duk da nasan yasha tea saman momi, duk domin kau da zancen ya wuce. Kuma babu dad'i, daga auren mu a ce mun soma samun Sab'ani. Ancle ya iso gareni, ya zauna gabana, kamar tea d'in zai sha, amma Sai naji yace a hankali cikin wata galabaitacciyar murya. "Sumayya, me yasa kike kishi a kaina?". K'warai gaskiya ya fad'i, kishin yafi kaini ga hakan, amma bazan so ya yarda ba, duk da ya d'ago, shi yasa nace. "Wajibine mace tayi kishin mijinta". Ya sake jefomin tambayar da ta hargitsani. "To, Kina so na ne?". Nayi kokarin sarrafa kaina. "Ai ko da so ko babu so, mace zatayi kishi a kan mijinta". Da sauri yace. "That's not true. Sai da da so ake yin kishi. Nayi mamaki da a d'an tsukin nan da zuciyarki ta iya So na. ke kinga na can canta kuwa?". Na kasa iya cewa komai, saboda sani a gaba da yayi, ya tsareni da idanun nan nasa masu sace zuciya farat d'aya. "Idan za kiyi shawara dani tabbas zance kiyiwa zuciyarki shamaki da soyayyata, domin bata da amfani a gareki Sumayya Sam ,Sam, kuma ko a gaba bazata amfane ki ba, kece mace ta farko da bazan so, ki kamu da soyayyata ba. Kamar yarda nake kallon su Khairat, haka nake kallonki Sumayya. Zan iya bugar k'irji nace miki k'anwata, zan iya ce miki kuma my Daughter duk dalilin Sulaiman. Really, ke matata ce, amma a furuci ne kawai, misalin auren mu kamar shirin wasan kwaikwayone da mutane su ke gani, su rinka zaton gaskiya ne, idan suna gani, amma a badini ai duk shiri ne, sabanin tunanin su. To a wurina, haka ne. Shi yasa bazan yarda na d'ora miki wani nauyi nawa ba. Kema nasan bazaki so ba, ko zaki so, ni bazan so ba. Shi yasa tun farko ban b'oye miki komai ba, ballantana ki Shiga duhuwa, idan kika ga ba yarda kika zataba. Ko da yake Ancle sulaiman yace WAI NI DA KE MUN DACE. To ni ban kai hangen dacewar da yake nufi ba. Ko matakin benen soyayya bamu hau ba, yace MUN DACE? Bazan yi miki k'arya ba, nace Ina sonki, saboda kiji dad'i, kuma bayan k'aryar ma kuma ai da yaudara. Shawara ta, ki daure ki rink'a kallona a matsayin Kawu Sulaiman ba miji ba, hakan zai kawar miki da damuwar da zaki iya samun kan ki a ciki, ko takura. Zai sa ki Samun sakewa da farin ciki a zaman mu, idan kika da sawa zuciyarki hakan. Ki jarraba Sumayya, zaki tarar da a binda na fad'a miki,zaki gasgatani." Ni dai har ya fice, kamar gawa, na gaza yin motsi. Nasan shi ko a jikinsa, game da furucin da ya furta min, saboda babu d'igon kunya ko kawaici a tare dashi, wurin fad'in a bu, ko yin abun da yasa kan'sa. Tun da gashi bai b'oyemin komai ba, tun farko. Amma a bu da nafi jinjinawa. Farko yace na rink'a kallon'sa a matsayin kawuna Sulaiman. Wurina kamar haramta halas ne. Shi Mijina ne, to don me zaice na rink'a kallonsa a matsayin Kawu na,da aure ya haramta a tsakanina da shi. Sannan ya dubi cikin idanuna yace yana k'yamatar wai na soshi. Kuma wai aure na dashi iya furuci ne, ban da a aikace. Banyi zaton za'ta kai mu da nisa haka ba, domin zatona duk wata d'awainiyar aure zai bani damar nayi masa, iyakaci ya k'aurace min, tun da baya Sona. Komai kenan bazan yi ba, hoto zan zama. Gaskiya da sake. Na dad'e a daren ranar ban iya samun bacci ba, ina tsara salo salon yarda zan fitowa Yariman kawu na, mai wuyar Sha'ani da tsadadden samuwa. Idan yasan wata ai baisan wata ba. Nayi wayewar sanin komai, da iya komai. Zan fito masa duk ta inda bai zata ba. Kuma cewar da yayi na rink'a kallon'sa a matsayin Kawu Sulaiman zan kuwa fitine shi, duk shagwab'a da tab'arar da nake yiwa Kawu Sulaiman tun ina yarinya, har girmana zai shata salo salo, bashi da k'orafi ko sababi, idan yayi zance ai shi yace na rinka kallonsa a matsayin kawu na, zan ce shi yaja, tun da shi ya ban damar hakan, sai duk a binda zai faru ya faru. Da ace ban riga na aure shi ba, ya furta min kalaman nan, to tabbas zan yi zuciya na barshi. Amma tun da yayi saken da igiyar aure ta sark'emu, to wallahi bazan hak'ura da shi ba, Sai inda k'arfina ya gaza. Bani ba, ko wacece ma a binda zatayi kenan, in dai ta samu nasarar mallakar miji irin Ancle Fa'iz. Baza ta yarda ta canza shi da wani ba sai dai tayi k'ok'arin canza shi zuwa ga yarda takeso, idan zata iya, Ko taci layar hak'uri ta zauna da shi da halinsa. A ranar dai nayi ta bak'i amma yawanci k'awayena na jami'a saboda su na gayyata a yinin biki na, saboda bana son tsofaffin k'awayena na secondry su san na auri malam Fa'izu, terere za'ayi tayi, ana kwazawa. Daren ranar Ancle Fa'izu ya shigo falona, amma ba muyi hira ba doguwa. Duk yarda naso ya saki jiki ya jima yak'i, ya kawomin uzurin wai a gajiye yake, na kuma karb'a. Ko minti biyar bai yi ba, yayi min sai da safe ya wuce d'akin sa. Da safe na a jiye bak'unci gefe d'aya, tun da nayi sallar a suba ban koma ba. Ancle Fa'iz nema ya tasheni sallar a suba bai san nima gwanar tashi bace k'arshen dare nayi nafilfili har zuwa a suba, to Sai yazo ya tarar dani zaune Ina lazumi, Sai ya juya. Tare muka Shiga hada hadar girkin safe da su Khairat, duk da Khairat tayi tayi na bar aikin sayi nak'i. Ta hak'ure, Sai gashi muna aikin tare cikin armashi, har 'yar hira mu keyi. Ita kuwa Muhibbat baya ga gaisuwa bata sake cemin komai ba. Bayan miskilanci, ma da naga tana fama dashi da jin kai ainun, ko irin yanayin yayan tane da ita ban Sani ba. Amma shi Ancle sanadin aure ya d'an sauya,tun da har yana 'yar hira dani. Ta yiyu ita ma ta sauya idan an Kwan biyu, amma fa a zatona. Muhibbat dai tafiyar ta tayi ta barmu da aikin, kuma na lura sanadin zuwa na ne. Khalifa ne ya lek'o kichean d'in ya soma yiwa Khairat Maganar ta dafa masa ruwan wanka idan ta gama.Sai kuma yayi Jim, da ya ganni, in da ya sake bina da mayataccen kallo, Sannan ya miko gaisuwarsa gareni. Na amsa da sauri na kau da

Chapter 7 of 13