fuska kadan.
Karo na farko kenan da na tab'aji ya nuna jin dad'i a a binda a kayi masa a sanina.
Gudun kar na kuma laifi, nayi saurin cika cup da lemon maltina mai sanyi na mik'a masa.
Kafin ya karb'a yace.
"Lady Kinyi karatun ta nutsu Kenan!. Ban tanka ba.
Ya Mik'a hannu ya karb'a, Amma bai shaba, ya Shiga juya d'aya kwalbar lemon da ban bud'e ba.
"Yaya a kayi, kika San Ina son lemon malt?.
aikin Sulaiman ne dai na sani".
Idanun'sa na kan lemon yake surutan.
Ya shanye, ya sake cika cup ya shanye. Ya bud'e d'aya kwalbar ya cika cup ya Sha, ya a jiye ragowar a gefe.
"Da k'ishirwa na iso, Sai kika samu ladana kika yi a binda ya dace. Ina son maltina sosai a rayuwata. Na kansha kwalba uku ko hudu wurin training ko gasar boll."
Nace.
"Lallai kana son"ta da yawa."
"Ke baki son'ta?" .
Yace.
Nace.
"Kadai d'arsa min son'ta, ga yarda ka damu da ita."
Yace cikin wani lumshe idanu kan kwalbar lemon.
"Look, ki fad'i opinion d'inki Kawai, ba ruwan'ki da zab'ina ok? ".
Naji rashin jin dad'in gwaliyar da yayi min,
amma Sai na danne.
"Domin na tayaka son a binda kake so laifine.?"
Yace.
"Kuskure ne dai, saboda ra a yina da bam naki dabam, banga dalilin da zai sa ki tayani son wani a bu ba, don ni bazan tayaki ba anan zance na fisabilillah, iya nawa zan tsaya, kinga kuwa bai kyautu kiyi min kara ba, gaskiya ni kullum ba na boyanta bayyana ta nake, ko da kuwa kowa zai tsane ni, i don't care".
Kafin na wartsake daga wannan ya jefomin wani.
"Sumayya wai addu'a kika yi min ne?".
Na waro idanu waje.
"Wace addu'a zan yi maka ni kuwa Ancle Fa'iz?".
Yayi harr da idanu ya sake kafeni da irin kallon d'azu, jin furucina
"Wallahi da da na tafi, naci alwashin bazaki sake gani na ba, saboda gidadancin da kika nunamin. Amma bayan few days, Kawai Sai samun kaina naji Ina son waiwayarki kuma, kuma zuciyata ta nuna min fin karfin sani sai da nazo ba domin na niyyaci zuwan ba, naga kin canza yau, kina d'an tab'uka abu. Kenan komai da kika yimin rannan kina sane Kenan.?".
Bani da amsa, idan ma a Kwai bazai jiba. shi yasa na zab'i yin shiru.
"Kin a mince zaki jure irin Zaman aure N'a? ".
Samun kaina nayi da juya idanu na rausayar
"Zan jure man, tun da na iya jure zafafan bulalanka goma, masu ratsa k'ashi da tsoka."
Sai ya d'an d'aga idanun'sa Sama, mai nuna a lamun ya tuno komai. Sai yayi dan murmushi da banyi zato ba.
"A shefa kin tab'a fad'owa tarko na ko? amma wannan shafar mai ne, idan kika yi saken da kika sake fad'owa tarko na. Kinsan yanzu matsayi uku zan had'a a wurinki da an shafa fatiha.
Malaminki nake, Sannan Ancle,Sai na gaba mijinki.".
Da hannun'sa yake nuni, ta hanyar lank'wasasu.
"Haka ne?".
'Yar dariya na saka.
Yace.
"Zakiyi ta gasken ne"
Ya tattaro, Nutsuwar'sa.
"Ina so ki fad'amin nawa zaki buk'ata na shirin auren'mu na biki, domin na tanadeki , banason auren nan ya wuce Wata guda fa. "
Da hanzari, na dubeshi. Duk nasan saboda manufar sa ne,da yake so ya cimma. Wani zafi, naji a k'irjina.
Eh, ga 'yar tsana ka samu, dole ka gaggauta.
A raina na fadi, saboda nasan ban isa na fadi a fili ba mu kwashe lafiya.
"Barshi, na yafe. Ni babu shagalin da zan'yi."
Ya jefa min kallon hadarin kaji.
"Kija Mani zargi ko? to bazai yiyu ba. Bazaki tozarta min aure ba, ko ba kya Sona , kuma ko banason'ki za'ayi shagali irin Wanda ya dace. Kije kiyi nazarin adadin kud'in da zakiyi amfani da shi. Idan na dawo naji. Dole ne , kima saddak'ar."
Shiru nayi, jin zai soma hawa dokin zuciyar'sa da nake tsoro.
Bayan sa'oi kamar mai wani tunani sai kuma ya dago kai gareni da nayi shiru cikin kafeni da idanun'nan nasa masu narkar da zuciya.
"Kiyi min magana ko?"
Nace.
"Zan fad'awa Kawu Sulaiman, idan na lissafa."
Ya kwaikwayi salon yarda na furta.
"Zan fad'awa Kawu Sulaiman idan na lissafa. To Wai meyasa zaki nuna bam bamci tsakanin ni dashi? Nima ba kawun bane?".
Da nayi shiru, ya tafa hannun'sa a hankali, ya kuma dunk'ule.
Shikenan 'yar gidan Kawu Sulaiman, Sai naji daga gareki."
Ya ci gaba da lissafomin irin shirin da ya soma na auren. Lefema da Sadaki, da kud'in aure yace rana guda zai kawo. Kenan Ranar d'aurin aure Kawai za'asa . Yarda yake nuna a fuwa da komai, Sai a zaci, wani auren soyayya za muyi da shi, na an matsu da juna. Bayan nan bana gaban'sa na Sani, ko na sakan na a gogo. Manufar'sa ya d'anawa k'ahon zuk'a.
Fargaba d'aya nidai ta ragemin, shine kar a zal ta fad'amin Ancle Fa'iz ya samu damar yi min cuta ta k'arshe. Shine burin'sa Yana cika ya sakenj, nazo na bud'e faifan Zaman zawarci. A binda nafi tsana Kenan a rayuwata, zawarci..
Jinake yi, har gabana na yankewa ya fad'i idan na tuno.
Nina shirya had'uwata da Nuriyya domin taji labarin da zai kid'imata. Wato na aure na da Ancle Fa'izu. Mutumin da ta k'wallafarai a kan'sa kamar ta zautu, wai yau shi yake shirin aure na. Inda a ke neman'sa yayi b'atan dabo..
Ko da yake batasan waye Ancle Faiz ba dangane da halayya, da ko daura mata a kayi sai ta kwance, duk son da take masa ba za ta iya da halayen sa ba, saboda ita ba ta da hakuri, ga tsiwa. Ai a guje za ta raina kanta, ta ce ba da ni ba.
_Taku a kullum_
_Zainab ilyas mawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
_Zainab mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_...... 🖋️
*Page 10*
Nuriyya kuwa ta girgiza da jin komai. Nasan baza taji dad'iba, tun da ta nunamin irin son da take yi masa a baya. Sai dai bani da zab'i face dole na fad'a mata, tun da babbar a miniyata ce dole taji. Ban sanar da ita sirrin komai ba, na dai ce Kawu Sulaiman ya had'a auran, amma ni a fargaba nake.idanunta naga yayi rau rau.
Tace"Sumayya al'amarin ubangiji ya shallake tunanin bayi. Tsakanina dake a wannan lamari addu'a Kawai, to yaya zanyi? bani da yarda zanyi Sumayya."
To nima d'in dabara ta kubce, bani da yarda zanyin da na barmata, toma idan zan iya barmatan uban gayyar karba zai yi?
Dani da itan da take azabar son sa
duk rukuni guda muke. Babu Wacce ta rabauta da Soyayyar'sa, Sai ni da k'addarar auran'sa ta sauka a kaina.
"Ni haushi kike bani da kike Kiran wai kina zullumin auren'sa.
Kamar wannan zuk'ek'en saurayin za'a nok'ewa auran'sa?
Wallahi da motsi a cikin kan'ki, ba kalau kike ba koma ba na gari bane, ke dai ko baki tashi da ribar komai ba, kika tashi da ribar kyawawan fararen yara, ai kin gama da shi. Kasuwa ta tashima ai d'an koli yaci riba".
Ni kam haushi furucin'ta ya bani. Ana ga yak'i tana ga k'ura.
"Inaji ganin jarabarki ta son kyau da fari, Sai kin auri maye, nasan ko kinsan mayen nema auren'sa za ki yi ".
Tayi 'Yar dariya.
"Tabbas!. Ko zai rink'a lasar kurwata kullum Ina suma na farfad'o zan aureshi in dai irin Ancle Fa'izu ne."
Na jinjina furutanta.
"Al'amarinki Sai dai neman sauk'i Nuriyya, amma ba waraka ba."
"Bani buk'atar warakar Dama".
Tace, ni kuwa binta nayi da kallon mamaki kawai.
Akwatu Shida set da kit d'aya Ancle Fa'iz ya had'o min na lefe. Ya zuba abubuwa kuma gaskiya masu tsada fiye da zaton kowa.
A tamfofi Holand manya guda goma ne. Bayan masu matsakaitan kud'i goma. Lesuna masu daraja guda goma ne. Shaddodi da material ma sunyi . Hakanan Takalma da jakunkuna babu masu rangwamen kud'i. Sai a jakar Kayan sarkoki' za'a sha kallo. Duk da babu gold, Sai da aka zab'a a ka darje wurin zab'o k'ayatattun sark'oki na cinyewa, launi launi. Tilas a ce isashshiyar mace da tasan kan sirrin iya ado da kwalliya ta zab'o.
Ni dai Abin yayi matuk'ar d'auremin kai, na yarda ya narkar da kud'i irin haka a auren da yafi kowa sanin manufar'sa da makomar'sa a gaba.
Hajiya Mariya tafi kowa, murnar zuwan aure na, inda tayi ta kod"a lefen tana labartawa ga wad'anda basu gani ba, tamkar kaina farau, kuma k'arau. Haka ma 'yan uwan uwa da ubana kowa Sai Sam barka da Fatan alkhairi.
Sati hud'u a kasa d'aurin auren. An tasheni tsaye an kuma tashi Kawu Sulaiman tsaye da kakana. Domin duk basu shirya ba suma, saboda basu zaci zuwan aurena a tsukin ba. Amma Kawu Sulaiman naga ko a jikin'sa. Murna yake sosai da zumud'in zuwan auren . Kuma dama komai Ancle Fa'izu yace ga yarda yake so a yi a kan aurena da shi, to ta zauna. Shi yayi ta nacin kar a d'aga bikin ma kamar yarda kakana yaso, saboda yasan Yariman nasa, bazai so ba Sam!. Ashe kawu Sulaiman yayi tanadin'sa na aure na. Duk da yace min, suna Samun kud'I, shi da Ancle Fa'izu yanzu sosai a kan da a harkar boll, musamman ma Ancle Fa'izu da ya zama shine champion d'in su, duk yafi su Samun kud'i Amma na jinjina komai sosai da yayi min.
Hidimar Kayan d'aki da komai shine mai kaso saba'in cikin d'ari a cikin 'yan uwa. Cikin hukuncin Allah komai anyi min na fita kunya. Ko saboda maraicina ne hagu da dama yasa kowa ya k'ure kan'sa wurin hidimtamin?.
Bayan d'aurin aure na da Ancle Fa'izu da safe naji komai ya fice a raina.
Jikina yayi sanyi, domin na tabbatar na Shiga hannu, Sai yadda ta kaya dani kuma.
A cikin wannan yanayin, Ina cikin k'awayena uku, da 'yan uwa Ancle Sulaiman ya turo yana kirana. Na Shiga d'akin'sa da sallama, yana zaune gefen katifa, ya nunamin kusa da shi daga gefe yace.
"Zauna, Sumayya, magana nake so muyi."
Na zauna, na juyar da kaina gefen k'ofa da mutane suke wucewa 'yan uwa, Jifa Jifa, daga
zuwa cikin gidan, ko daga ciki zuwa waje, saboda k'ofar d'akin bud'e take, ana hangen Mu.
"Yaya naga baki da walwala ne? Kina da Wata damuwa ne, Sumayya.?".
Nace muryata tana rawa.
"Allah Ancle banason nayi nesa da kai. Wallahi auren ya ficemin daga rai. Bazan iya jurar na wayi garin Allah banganka ba, kawuna. Don Allah ka taimaka a sahalcemin auren nan."
Yayi murmushi, ba tare da ya nuna damuwa da furutaina na sokonci, da kuskure gami da wawtaba.
"Sumayya, hak'uri zakiyi. Ko ba jima ko ba dad'e dole Mu rabu Sumayya. Babu yarda za'ayi Mu dawwama tare.Aure shine cikar darajar mace, shi yasa nafi kowa farin ciki da auren'ki. A yau zan cika alk'awari na fad'a Miki dalilan da yasa na aura Miki Ancle Fa'izu, ko kya rage damun kan'ki, kafin kiga zahir kema da idanun ki ki tabbatar..
Yarima Mutum ne mai gaskiya kuma kaifi d'aya ne a magana, bashi da fargaba ko
tsoro wurin tsage gaskiya, ko kad'an.
Kinga mai irin wannan hali, za'ki sameshi da rik'on a Mana. Babu mai rik'on a Mana kuma Sai Mutumin kirki.
Babbar d'abi'arsa da tafi burgeni, shine bashi da ZARA.! Wato kule kulen 'yammata, daga wannan a koma wannan, yarda yawancin a bokan'sa naga wasu suna da irin wannan hali.
Zan iya rantse Miki, Sai kyawawan mata guda goma su wuce ta gabansa bai kulaba, saboda ba mai ra'ayin kule kulen 'yammatan bane. Macen da yake so, shi ita kad'aice a gaban'sa.
Duk namiji mai zara, za'ki sameshi da d'auka da a jiyewa. Kome kike Tak'ama da shi, da yaga Wacce ta fiki, tauraruwarki zata dushe, yayi k'ok'arin barinki ya kai mata hari. Kuma namiji mai zara, kullum cikin hange hange zai kasance, ko aure yayi matarsa ba za ta tab'a gama gamsar da shi ba.Kenan daga nan, k'ofar matsaloli sun bud'e. A yi hattara mata.
Namiji mara zara kuwa zaki sameshi da tsayawa ka'in da na'in a kan guda d'ayan nan da ya keso, Wata ba za ta yi ta d'auke masa hankali ba. Kuma ko k'addarar aure ya ratsa zai yi, to bazai rink'a auri Saki ba. Yau ayi gobe a Saki. Kuma namiji Mara zara, zaki sameshi da son matar'sa da kulawa da ita sosai da kishin'ta. Ki Sani suffofin Yarima fa nake wassafamiki, cikin rukunin namiji mara Zara.
Mutane da yawa fassara d'aya suke yiwa Yarima, shi yasa har Sukan manta da wasu d'abiun'sa kyawawa masu wuyar samu a zamanin nan. Kuma nafi kowa sanin Yarima da fahimtar'sa cikin a bokan Mu. Shi yasa muka shak'u tamu tazo d'aya.
Tuni na fahimci cikin halittarsa ne wannan d'agawar da jin kan da za'kiga yanayi. Amma a zuciyar'sa babu wani nufin yanayin hakan ne da nunin d'agawa na yafi kowa wani a bu haka nan d'abi'arsa take.
Amma idan kika fahimceshi sosai, kika fuskanceshi, kika samu kan'sa Kuna Mu'amala ta d'asawa, to za'kisan Yarima a wasu juyin Mutum ne a bin so. Yana da kirki Sumayya, amma fa Sai Kinsan makamar iya zama da shi za'kisan hakan, har ki yarda.
Nasan ke damuwar ki babba, babu soyayya tsakanin Ku. To ki Sani, anayin aure babu soyayya kuma a sameta daga baya. Kuma a na yin aure da soyayya daga baya ta gushe. Kinsan in'da matsalar take?".
Na girgiza kai a hankali.
"A cikin d'abi'a matsalar take Sumayya."
Nace "Ancle Yaya a bin yake ban fahimta ba."
Da sauri yace
"Yauwa 'yar albarka, wato kowan ne da Wanda ya dace dashi ya aura wurin d'abi'a, shi ake kira da Sab'awar halaye. Kinga kamar a kan'ki keda Yarima. Babban a binda yasa nake ta jaddawa ma Kenan a raina na cewa KE DA SHI KUN DACE.
Farko Kinga Yarima yana da zuciya sosai. Ke kuma kina da hak'uri. Ba komai ne ma yake b'ata Miki rai ba ke.
Yarima yana da d'an rik'o da rashin saurin yafiya.
Ke kuma kina da saurin yafiya, da mai da komai ba komai ba. Kafin ma a nemi a fuwa kin yafe, tun da take kin ma manta an b'ata miki ma.
Yarima yana da d'an zafi, a wasu Mu'amalolin. Ke kuma kina da sanyi sosai. Sau tari Yarima bashi da son magana, Sai ki bashi sunan miskili ma kai tsaye. Amma a wani tsukin Sai kiga kamar bashi ba, har hira Sai kusha. Amma dai rashin son hayaniyarsa yafi yawa. Na fuskanci ke kuma kin iya zama da mai irin wannan halin. Kin iya da halayen mutane wurin zama. Kuma nasan za'ki iya da wannan halin nasa mai kama da miskilanci Shi yasa nace. KUN DACE.
Wannan shine Sab'awar halayen da ake so tsakanin ma'aurata, domin Muddin Mutum ya had'u da mai irin d'abiar sa a komai, to alamarin ba zai yi kyau ba, ko kad'an, tamkar BOM a ka dasa, dake buk'atar lokacin tashin'sa yayi, yayi bindiga.
Kema ki auna a bu d'aya rak!.ace mai zuciya, ya had'u da mai zuciya, Yaya kike zaton makomar?".
Nace
"Ai Sai a binda aka gani Kawai na rigima my Ancle."
Yace k'arshen furutan'sa.
"Ai Sumayya, wurin Sab'awar d'abi'u a ke sanin an dace, amma ba'a wurin Samun mai mai kudi irin kaba, komai kyau irinka ba, ko ilimi da sauran a bubuwa da akayi tarayya a cikin'sa.
Wata soyayyar ma a waje iskace wani lokacin, Sai anzo an zauna, 'yar manuniya ta nuna na halayya da za'ayiwa juna dai dai, Sannan soyayya ta gaskiya zata maye gurbi. Shine an dace da juna, da kuma Soyayyar. Me yasa kike ganin, anyi shaharar riyar soyayya da anzo zaman auren Sai yak'i dad'i kuma?"
Kawu Sulaiman yayi gaskiya. Na fahimci komai Kam, daki daki. Ya kamata kuwa ma'aurata kafin suyi aure, su fahimci irin d'abi'un wanda za'su aura, koda da bin cike ne, domin a San an dace da juna kar Sai an Shiga a fad'a cikin matsaloli.
Dole naso Kawu Sulaiman, sosai ya hanamin kuka lokacin da zan yi. Ya kuma sharemin hawaye lokacin zubar'su. Na fad'i hakan ne, saboda dangin babana da su ya dace Sufi tsayamin a aure, cogewa suka yi, kuma babu a binda suka yi min, Sai k'afafuwa suka kawo a kayi biki da su, maza kuma d'aurin aure. Ko ganin k'asa ta rufewa Mahaifina idanu ne, suka watsar dani? tun da ko nemana ba sayi. Da babu Kawu Sulaiman a Sha'anin aurena, da bansan irin tozartar da zanyi ba. Har sark'ar gold Kawu ya bani a ranar k'irar dubai yari da sarkarta karama bayan shine jigo na yimin kayan daki. Ko bai tatike aljihunsa ba a kaina, nasan 'yan sulalla suka rage masa.
Da daren da za a mikani na rinka kuka kamar wacce za a kai gidan yankan kai, har sai da murya ta ta dashe. Kawu Sulaiman da kyar ya lallasheni sai na koma kukan na zuci na bar na fili saboda farin cikin sa, domin na lura ya shiga damuwar rabuwar mu sosai shima domin kamar kwalla ma naga ya na gogewa a sace.
Karfe tara dai dai motocin da Yarima ya turo a dauke ni suka iso, dama an gama shiryani da komai da zaa yi min, ni suke jira da 'yan rakiyar a marya na tsaya kuka. Cikin mintina a shirin an gama duruwa cikin motocin harda ta kai amarya, in da aminin Yarima Hashim shine ya dauke ni a atasa motar da kawayena uku.
*Alkalamin zee taku*🖋️
Muje zuwa.Yanzu ne za a soma labarin.... ✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
_Zainab mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer......🖋️
_Page 11_
A cikin motar kai amarya Hashim yana ta hirar barkwanci da kawayena, yaso ya tsomani a hirar, amma ya fahimci bazan tanka musu ba, a raina baisan harshi kanshi haushinsa nake ji ba, domin nasan shima yasan kullin da suka shirya game da auran, tun da babban aminin Ancle Fa'iz ne, na hannun da ma.
_TUSHEN KOMAI_
Unguwar magajiya cikin garin zariya, cikin wannan unguwa gidan'su Ancle Fa'izu yake. Nan kuma zan zauna cikin gidan'su, tun da ginin'sa bai hattama ba, da saura sosai, saboda babban gini ya kamfatowa kan'sa da zai jima bai kammala ba, tun da bashi da samu na sosai da sosai da zai kammala da wuri.
Gidan na su, babban gidane sosai, amma irin fasalin ginin dane dashi, kamar shekara talatin baya. Fentin da a kayiwa kafatanin gidan yayi kyau, duk da ba k'erarren bane. Babbar k'ofa d'aya ce ta bak'in k'arfe ta Shiga gidan.
Khalifa, shi yake bima Ancle Fa'izu, d'akin'sa za'a fara tararwa da an shigo harabar makeken cikin gidan. Muhibbat, ita ke bima
khalifa, d'akin ta na can gaba da nasa.A kwai kuma wani falo madaidaici da ya shiga tsakanin'su a rufe yake amma ruf, da alamun babu kowa. Khairat, ita ke bima Muhibbat, d'akin'ta yana jikin na 'yar uwarta.
Wanda ke gaba da na khairat, falona ne babba mai d'akuna biyu. Kuma da usuli, anan khairat da Muhibbat suke a tare, sanadin zuwa na ne suka barmin wurin, saboda yafi yalwa, shi zai dace da a marya Irina. A kwai kuma wani fallen d'akin gaba da nawa, nan Ancle Fa'izu yake, amma da usuli Shima d'akin'sa kusa da na Khalifa yake. Duk daga baya suka canza tsarin komai, saboda auran.
Bangaren hannun daman hagun d'akunan dake zagaye da farfajiyar gidan benene gajere da zai kai ka b'angaren iyayen Fa"izu, nan suke gaba d'aya.
Gaba da benen kichean ne babba na Momi. Gaba dashi store ne madai daici, shi ya zama kichean d'ina, bai ma cinye komai ba, tun da Deep freezer ta bata samu Shiga ba, Sai Friedge da yake shi k'aramine. Daga bayan benen band'aki ne, gaba dashi ma wani ban d'akin ne.
Gaskiya, komai nasu ya birgeni duk da ba masu arzik'in bane, amma na lura a Kwai
soyayya da rayuwa mai ban Sha'awa a wurin iyalan gidan, kamar yarda sukan su iyalan gidan suke kyawawan gaske. Duk mahaifiyar"su suka d'auko, Amma Khalifa shi ya baud'e.
Bayan sun wawashe kyan na gado sun barshi da kad'an, Sai ya fito kuma bak'i. Amma daga baya da naga Mahaifin"su, Sai naga a she shi ya biyo sak"! Kamar ni kenan.'Yan uwan mahaifiyata sun cemin wai Mahaifina na biyo, Wai da na biyo mamata khadija, da sai nafi haka kyau, domin kyakykyawa ce sosai kamar kawu Sulaiman, domin ta fishi ma a kace. Toni godiya na kewa mahaliccin halittar, domin nasan nafi wasu. Kuma babu mai dubana yace min mummuna. Ina nan a tsakiya. Idan ba'a yaba ba, to kuwa baza'a kushe ba.
Idan Mutum yana duban na k'asa da shi, to bazai yi butulci ba ga mahaliccin sa, domin duniya kafi, a fika ne. Idan Mutum kullum kallon na Sama dashi zai rink'a dubawa, to ba zai zama mai godiya da tawakkali ga ubangiji ba. Kuma ni ban yarda a Kwai mummuna ba. Sai mace taso zata zama mummuna, in dai tana la'akari da wasu da suka fita tana sarewa, tana k'ask'anta kan"ta, to baya zatayi tayi.
idan mace ta yarda ita mai kyauce Itama, to kullum k'ara kyawun zatayi, domin zata kasance ne ko yaushe
cikin yin a binda zai k'ara mata kyau.
Ra'ayin Sumayya ne.
Ni dai, tun da aka kawoni d'akina a ka watse, banyi tunanin komai ba Sai bacci. Kukan da na Sha, yasa b'arin kaina ya matsamin da ciwo, nasan babban maganin'sa irin na Kwan'ta nayi bacci. Sam banyi tunanin wai na jira Ancle Fa'iz ba, ban sa rai da zan saka shi a idona ba ma a ranar.
Bani da bashin salla, har shafa'i da wuturi na sauke kayana. Tun da na Kwan'ta ban tashi farkawa ba, hudu da rabi na dare . Da Saura sallar a suba. Na jero addu'oi na fito rik'e da torch light mai haske, domin na kasa bacci kamar kullum. Fargaba da rashin sabo na sabuwar rayuwa. Kona koma bazan iya ba sosai saboda kar na makara a sallah. Na fito domin duba a gogon falo.Falon babu kowa wayam. Amma naga an rufe k'ofar falon da na sayo kad'an, an rufe sosai.
Wannan shi ya bani tabbacin Ancle Fa'izu ya shigo, bayan nayi bacci.
Daga kishingida sai bayan sallar a suba na farka, gari ya soma haske. Na mike na fito domin sallar sallah , wato naje nayi alwala
Sararo nayi, saboda ganin kuma Ancle Fa'iz kwance kan kujerata kamar mai bacci a falo. Singlet ce a jikin'sa, ya rataye rigar kayan' jikin hannun' kujerar. Na tabbatar bayan na koma na dan kwanta ne ya shigo.
Hannun'sa da yasa ya rufe fuskar'sa shi yasa na kasa tantance bacci yayi, ko idanun'sa biyu. Sai dai da nazo zan wuce na fita, Sai Jinayi yace "Ina zaki?" Idanun' nasa , dai a rufe yake da na juyo na kalleshi.
"Alwala zanje nayi"
Nace.
Shiru yayi.
Bayan naje nayi alwala na dawo, na tarar kuma bayanan. Al'amarin' nasa Kam da d'aure kai.
Ya sake shigowa bayan gari, yayi haske sosai. Yana saye da rigar wandon shaddar da yasa d'azu, milk colour.
Dama Ina zaune a falon nayi zugum. Tunani kala kala sun lullub'eni.
Yace dani
"Ranki ya dad'e".
Da ya shigo mukayi arba. Ban tab'a ganin'sa cikin nishad'i ba da walwala irin na ranar ba.
Nayi murmushi nace.
"Ancle ai Sai ku wannan."
Daga nan na rusuna na gaisheshi a ladabce.
Ya d'an nade rigar'sa ya zauna a kujerar dake gefen tawa, ya juyo yana kallona yace.
"Sumayya aike kika kika can,can'ta da a baki kambun sarauta guda. Irin wannan harkar hutu haka? Tun jiya kika yi kwanciyarki da wuri, har na shigo baki Sani ba. Da a suba ma na shigo na k'wank'wasa jikin gadon'ki domin kiyi sallah, bakisan a nayi ba. Ni kuwa Ina na samu wannan hutun jin dad'in?".
"Kai d'in dai kai ka dace da rik'e kambun sarauta Ancle. Ko a sunan da a ke kiranka da shi, ai an yarda anbi. Yarima fa kake".
Murmushi yayi, da ya k'ara masa wani
sihirtaccen kyau, ya saki zancen, domin yaga nayi baki, har na fishi hujja.
"Kije Ku gaisa da Momi, domin muna gaisawa take tambayata ke, Wai yaya kika kwana,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 13