Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fidda ma gwani. Tausayin Usman shi yayi rinjaye a raina, bawai son'sa ko son auren'sa ba. Saboda nacin sa da magiya na a mince amma nace ya bani kwana ki biyu nayi magana da Kawu na. Yayi ta murna kuwa. Ranar da mukayi zan fad'awa Kawu Sulaiman, Usman zai zo yaji inda a ka kwana, ranar Kawu na ya tashi da gyare gyaren d'akin'sa, saboda ranar lahadice baya fita Sai yamma, ni kuma bani da lacture. Na shiga taya shi, saboda gyaran da yawa. Kusan yayi d'ai d'ai da komai na cikin d'akin. gyare gyare da goge gogen da yawa. Na kafe Sai ya barmin nayi ni kad'ai. Ya saduda ya tafi ya barmin. Da yake Ina da saurin aiki, sai gashi na gama, ina mai da komai muhallin'sa naci karo da wata farar ambulan 'yar babba. Ko Ancle Sulaiman ya sanni da lafiyar bincIke. kamar nawa na Shiga k'ok'arin bud'ewa, domin naga menene a ciki. Amma a tsorace nake kar ya shigo ya ganni, yace mai hali kin soma ko? Domin na saba da wannan kalma tun Ina yarinya. Tuni na fahimci hotuna ne, da sauri na shiga zaro su, duk zatona hotunan budurwar sace da ban tab'aji da gani ba. A bin takaici a gareni, hotunan maza na gani, saye da kayan 'yan boll har dashi. Wani Mutum uku wani mutum biyu wani shida. A Kwai kuma wanda suka had'u su duka suka sa boll d'in a tsakiya shida 'yan club d'in nasu. Amma menene yaja hankalina na kasa a jiye hotunan kamar yarda naso da fari, da naga ba hoton mace bane? Mutumin da na yanke zaton zan sake gani a rayuwata, Mutumin da nasan babu wani dalili na sake had'uwata da shi, shine a cikin hotunan 'yan club d'in su Kawu Sulaiman.wanene? Faiz Bukar. Na sake kai ganina ga hoton, amma bisa ga wanda ya d'au hankalina da ganin'sa wato Fa'iz. Gaba d'aya ya haske hotunan. Kowanne da ka kalla, shi zai fara janye kallonka. Muryar Kawu Sulaiman naji a tsakar kaina. "Me hali baya fasa hali dai. Bincike kike min ko gyara sumayya?" . Nace. "Yi hak'uri my Ancle. Wani malamin mu na secondry na gani shi yasa na tsaya dubawa ma, dama kasan shi kawu?". Na nuna masa shi. Ya duba yace. "Au, Yarima kike nufi?". Na sake nuna masa shi, ga zatona bai kulaba. "Ka ganshi fa, wannan farin na cikin ku, malam Fa'izu fa." Yace. "Shi d'in nima nake nufi ai , sunan'sa Fa'izu, amma mu a bokan'sa Yarima muke ce masa. Mu kance masa kuma Gimba, wato d'an sarki, a hausance kenan. Amma mun fi Kiran'sa, da Yarima, a yaren barbarci ne, saboda usulin mahaifin'sa babarbare ne, mahaifiyarsa kuma k'abilar shuwa a rab ce. Na dubi Kawu saroro. "Me yasa kuke ce masa Yarima Ancle.?". Murmushi yayi ya karb'i hoton."Abokai suka sa masa kuma ya bishi. Baki ga takunsa yayi kama da na masu wannan sunan ba kema?". Nayi gajeriyar dariya. "Tabbas na harbo jirgin Kam, sunan ya dace da shi sosai, kun iya sa sunan a muhallin'sa. Ai ya yiwa dalibai horo sosai a school d'in mu. Bana zaton a kwai d'alibar da zata mance dashi. Sunayen ma da za'a kirashi da shi suna da yawa. Dama d'an club d'inku ne Ancle?". "Sosai, a harkar boll kuma muka had'u muka saba. Shekara shida Kenan da ya shigo club d'in mu na Kaduna united. Ya iya boll fiye da zaton mai zato, da shi muke ji a club. Ko jiya na had"u da shi da yamma a club, mun Sha hira a kan gasar wata boll da muka je. A Kwai mutunci tsakani na dashi, duk da babu wata a bota dai sosai tsakanin mu, Sai mutunci sanadin club tare da buga k'wallo. Hirar ta datse ne saboda baba Talatu da ta kirani. Usman dan fodiyo da yazo hak'uri na bashi, nace ya k'ara min kwana biyu dai. Mantawa nayi ban yi Maganar da kawuna bama. Kwana biyu tsakani da yamma Lis, ina zaune tsakar gida, Kawu sulaiman ya shigo, nayi masa sannu da zuwa, haka ma baba Talatu. Yayi mata sannu da gida. Ya dubeni yace. "Sumayya yau ina tare da Yarima, yace a gaisheki." Nace"Ina amsawa." Ya wuce yana yin wani murmushi da bansan musabbabin'sa ba. Ni dai nasan babu yarda za'ayi wallahi Fa'izu yace a gaisheni. Mutumin dake bala'in jida kan,sa. Ta ina ma ya tuna da sumayya, a rayuwa? Shekaru biyu fa Kenan rabona da gama makaranta. Kawai bazan iya k'aryata kawuna bane. Washe garima da Kawu zai fita sai yace min. "Sumayya yau ma zamu had'u da Yarima da k'arfe uku na rana a club, me zance wa Yarima?". Nace"Bani da a binda zance masa Kawu." Yace. "Kikayi haka baki kyauta ba, amma shi yace a gaisheki? amma zan ari bakinki na cimiki albasa kawai. Ni dai ban tofa ba. A yar tambaya ce ta soma tsayamin a rai name kawuna yake nufi da son had'a a lak'ata da malam Fa'izu? anya babu wani b'oyayyan al'amari a zuciyar'sa? . Ture komai gefe kawai nayi na shiga dakon jiran'sa ma na ya dawo nayi masa zancen d'an fodiyo, domin ya matsamin da sai ya turo iyayen'sa Usman yazo zance wurina, gaisawa Kawai mu kayi, kafin ma muyi nisa da magana, Sai ga Kawu Sulaiman ya dawo. Yana shigowa farfajiyar gidan, Usman ya rusuna ya gaisheshi, cikin tsantsar ladabi. Ni kuma nayi masa sannu da zuwa. Yace. "Sumayya zo na ganki na 'yan mintina". Nace"To, gami da Mik'ewa. Ya kuma waiwayi Usman yace. "Usman, kad'anyi hak'uri na katse muku hira, yanzu zata dawo." Ya nuna har a fuska babu komai. Hanyar fita waje yayi, na bishi. Kafin mu isa ga k'ofar fita yace."Sumayya, Yarima na kawo miki Ku gaisa. Daga meeting muke na wasan k'wallo da zamu buga da k'ungiyar 'yan boll ta Dolfin, very soon. Shi ya kawoni gida ma a babur dinsa, kinsan nawa ya samu matsala. Sai nace to why not bazaku gaisa ba, ko kuwa?" Murmushi nayi nace "To, Ancle." Kawai Samun kaina nayi da fargabar had'uwata da Fa'izu. Gabana ya rink'a fad'uwa ma, Yayin da na tuno d'abiun'sa na cin zarafi da fushi ko yaya aka kuskuroshi. Ban manta komai ba. Shi yasa nake ganin komai ma kamar lokacin da yana koyar damu, kamar zan yi masa kuskure yaci zarafina. A k'ofar gidan Mak'ocin mu Alhaji Bilyanu muka sameshi ya jingina jikin sabon Jan babur daya kasance nasa. Hasken fitilar k'erarren gidan mai haske komai ya haskemin shi sosai. Saye yake da Kayan 'yan boll koraye, Amma wandon dogone mai taushi. Ban tab'a ganin Mutumin da kayan 'yan boll suka yi masifar yi masa kyau ba, irin Fa'izu. Domin sun k'ara haskaka shi ma. Wani kyau naga ya k'ara da haske da 'yar k'iba ma kad'an, da ta k'ara yi masa kyau fiye da da. Ko har yanzu yana koyarwar?. Kaina na tambaya. Na yarda lallai ya samu dan cigaba na rayuwa, don ada bashi da babur sanda yake koyar da mu a makaranta. Na rusuna na gaisheshi. Ya k'ara d'aga idanu ya dubeni sosai bayan ya janye daga jingina jikin'sa da yayi jikin babur. ya dubi kuma Kawu sulaiman. Kawu Sulaiman kuwa tsare mu yayi da kallo ni da fa'izu ya kalleni ya kalleshi hak'oran sa waje cike da nishad'i da bansan dalili ba. Fa'iz ya dubi Kawu na. "Kasan Sai yanzu na ganeta Sulaiman? ai da ban fahimci wacce kake ta kwatantamin ba, saboda d'aliban da yawa ,ko na santa, ko sunan'ta iyanzu mantawa zan yi, an fa jima da yawa. Na manta sunan ta dai, amma na ganeta a ido. Sanin monita nayi mata na Class 6 B ko?.fitinan nun school ai dole na rike wannan class, duk da na gyara musu tsari". Tabbas baka da mantuwa Malam Fa'izu. Zuciya ta ta kimsamin. Na gyad'a kai, Sannan na kai dubana ga Kawu Sulaiman, na kuma dire kan Yariman nasa . Carab Sai muka had'a idanu kuwa. Sai yayi dan murmushi kafin ya maida kallon'sa ga Kawu Sulaiman ganin mun hada idanu. Zan iya cewa shine farko da nata b'a ganin murmushin Fa'izu gareni, a iya sanin da nayi masa. Cikin tausasa murya yace. "Sumayya, ai ban tab'a sanin ke Jinin Sulaiman bace. Da nasan hakan, Atleast ai da kinsamu kulawa irin wacce ta dace. A Kwai a minci da girmamawa tsakanina da kawun naki, he mean so much to me. Ina ganin k'imar'sa da shi kan'sa baisan iya ganin kimarsa ba da nake ji game ni. Nima yanzu Ancle d'inki ne Sumayya kinji ko?". Na sunne kai k'as cikin murmushi nace"To". Ya maida hankalin'sa kan Kawu Sulaiman kuma. "My man, Ina cikin mamaki fa yarda k'addara take ta had'ani da wannan Daughter taka, bayan mun rabu. Sau uku Kenan fa. Three times Sulaiman. Ya nuna yatsun'sa uku yana nuni da shi. Ni Kam sak'e sak'ena nake, Ina ganin kamar a majigi komai ke faruwa. Malam Fa'iz ke tausasa harshe yana fad'amin wad'annan kalaman? Dama ya iya tausasan kalamai a she? Kawu Sulaiman ya duba yana mai cewa. "Farko ta yarda wayar'ta na tsinta, ta kira layin mu kayi magana ta kwatan'ta min gidan nan na kawo mata. Kasan ban tab'a zuwa gidan nan ba Sai yau ai da tun a ranar na d'au haske, domin Sai yanzu komai ya dawo min,nan gidan nazo na kawo mata waya. Bayan watanni mun sake had'uwa da Sumayya a makaranta nayi teaching d'inta, Kenan a malamin ta nazo. Yanzu kuma Bayan shekaru biyu mun sake had'uwa da ita ta dalilin ka. Me hakan ke nufi Sulaiman, da sanadi ke ta had'ani da 'yarka?". Murmushi Ancle d'ina yayi yace. "Da walakin goro a miya. Kuma ruwa baya tsami banza. Idan kaji gudu kuma to da magana. Fa'izu baice wa kawuna komai ba, game da furucin da yayi, don wasa ma naga ya dau zancen. Ya sake dubana cikin dan jin kan nan nasa kamar bazaice komai ba ya dan juyar da kai sannan ya dawo da shi kaina yace. " Karatu kike yi ne Sumayya?". Nace"Eh". "Da kyau, kin birgeni. Ki daure ki zurfafa karatu, kici moriyar sa tun da kIna da k'wak'walwar fahimta. Ina yi miki fatan alkhairi da nasara." "Na gode Ancle." Na fad'a cikin wani nishad'i da naji ya bak'unci zuciya tashi guda. Gani nake tamkar ba Fa'izun da na Sani bane. Wannan yafi wancan kyawun Siffa ma da ake ta kwaroroto, da dan jiki kadan da ya kara, duk sanadin dan hutu da na fahimci ya samu, kuma sai naga yafi kyau a hakan, kuma halinsa ya canza wurin sanyi da sauk'in kai, amma nasan da dalili. Amma dai tabbas shine, tun da gashi mun tuna baya ma. Sai dai nasan komai yanayine sanadin kawu Sulaiman ne wanda ya nuna yana da muhimmanci a gareshi. _Ku biyo ni dai labari ba a soma ba ma tukun_. _Taku Zainab mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* *Zainab Mazawaje* _Best brilliant interlligent writer_........🖋️ *Page 5* Nasan albarkacin kawu sulaiman naci na daga fuskar da na samu wurin malam Faiz. Zuciyata ce ta fad'amin. Fa'izu ya dubi kawu yace da Kawu na. "Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa." Cikin 'yar dariya Kawu na yace. " Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka." "Kaji ka da wani zance. ni kad'ai ne zanji da komai? wato dani kuka dogara a nasarar ku ko?to kuwa wallahi zan kayar daku Ina sane." "Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa". Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya sha mur serious babu kafar zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne. Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman. "Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri." Nace. Yace. "Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba." Nace"Karka damu, yace nan da Jibi zai yi magana da kakanni na zai yi maka magana" . Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane. Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan. Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu. Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu a bisa tsautsayi , yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan. Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali. Ga yarda a bin ya faru a tak'aice. Gidan k'anwar kakata naje wata Hajiya mariya, Wacce ita ta fara rainona bayan mutuwar mahaifiyata, kafin baba na ya rasu Shima. Bansan na yarda wayata bama, Sai da nazo gida, Ina kici kicin zaro canjin kud'ina zan yi aike, ga yaron aiken kuwa tsaye a gabana. To babu kud'I kuma babu wayar a babban zip d'in jakar, da bansan lokacin da suka zube bama. Dama jakar ta d'an farke Sai gani nayi ta yage ma sosai a she ban Sani ba. Nan nasan na rasa wayata a karo na biyu, domin ko wata biyu batayi da saye ba da kawuna ya sayamun Sabuwa bayan an sace waccan. Kuma mai tsada ce a kan waccan. Damuwa ta tayi nisa, a raina a ranar, saboda kar Kawu Sulaiman yace Ina da sakaci da rashin kulawa a kan abinda yasa k'ud'i ya saimin. Waccan an sace, wannan kuma nayar? ai bazai ji mutuwar sarki a bakina ba kuma. Ba kina naja na tsuke. Amma fa kullum a farga ba nake, kar ya ne mini a waya ya fahimci komai. Kwanaki hud'u tsakani Sai ga wata a miniyata mai suna Nuriyya.Muna hira nake fad'a mata b'atan wayata. Ta jajanta min. Nace. "Bani a ron wayarki ma na kira layin, duk da ban saka rai bama. Duniyar yanzu ba gaskiya. Masu tsoron cin haram ko rik'e haram, sun yi K'aranci. Da kud'i a wayar taki?". Tace. "Kinfi kowa sanin waya ta kullum cikin credit take, bata zama fanko, saboda Ina da masu yi mata hidima." Na warce wayar Ina cewa. "Allah ya shiryeki Nuriyya. Kullum baki da aiki Sai tatse samari, kuma ba auran su zakiyi ba, Wallahi kiyi hattara". "Na nawa kuma, wai ance da kuturu ka gama lafiya. Namiji ai yaso yaudarata, amma na nuna masa ni 'yar zamanice ai ni naci dubu Sai ceto, nafi gaban a washeni, domin murucin ni kan dutse ce ban fito ba Sai dana shirya. Ke dai ki jarraba Kiran ko kya dace, idan kina da rabo. A kwai na kirki a duniya." A ringin na uku, a ka d'auki wayar kuwa, bayan na k'agu da a d'aga. Muryar namiji a hankali naji tayi min sallama. Muryar bata da d'agawa irin ta maza. "Dawa nake magana?". Nace. "Sunana Sumayya..... Bai bari na k'arasa ba yace. "Ko zaki taimakeni Sumayya ki had'ani da mai layin wannan wayar da kika kira? Tsintar ta nayi a hanya zan wuce kwana ki hudu da suka wuce. Naji sanyin dad'i a raina nace"Wayar tawa ce wallahi yanzu ma kira nayi ko zan dace. Yace "Kin kuwa dace 'yammata. Zaman wayar ma a hannu na duk ya dameni, so nake na mik'ata ga mai ita Kawai. Don da na tsinta caji ma babu, Sai da na Sai mata caza Sabuwa na caza ko mai ita zai bugo, sai yau a kayi dace a ka bugo. Yaya za'ayi ki karb'a?". Nace. "Fad'amin in da zan sameka Sai nazo na amsa." Yace" Ba haka za'ayi ba, ke zaki kwatanta min in da kike nazo na kawo miki, dama fita zan yi. A wace unguwa kike?". Nace" Ina unguwar Doka". Yace. "Anya na tab'a Shiga unguwar nan?". "Kai ba d'an garin zariya bane?". Nace da shi. "Haifaffe ma kuwa. Yace da hanzari. Domin kana d'an gari ai baza'ace ko'ina kaje ba. Amma dai zan zo, idan na shigo unguwar Sai na tab'aki a layin da kika kira kiyi min jagora, kar na manta. Tare da a bokina suhail zamu zo, tun da shi idon gari ne. Amma ki tanadi ladan tsuntuwafa. Kinsan yanzu ba'ayin aikin da babu in come". "Ga zatona da gaske yake. Nace"Babu damuwa, zan bada idan babu yawa." Yace"Babu yawa ai. 'yar dubu goma ce kawai'. Fa'izu yace da Kawu na."Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa." Cikin 'yar dariya Kawu na yace" Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka." "Kaji ka da wani zance. Ni kad'ai ne zanji da komai? Wato dani kuka dogara a nasarar Ku ko?to kuwa Wallahi zan kayar daku Ina sane." "Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa. Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya Sha mur serious babu kafar Zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne. Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman. "Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri." Nace Yace"Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba." Nace"Karka damu, yace nan zai yi magana da kakanni na a sa lokacin da zaka turo, sai na fada maka. Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane. Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan. Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda Kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu. Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu, yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan. Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali. Unguwa naje na yarda wayata bansani ba, a she kasan jakar ya yage. Na kasa fadawa kowa musamman kawuna da ya sai min kuma bata dade ba, nasan bazai ji dadi ba. Rannan kamar wasa Nuriyya kawata tazo nake fada mata, sai tace na kira a wayarta ko za a dace, tun da tana da lambata. Na kira babu musu amma bansa ka rai ba gaskiya, domin takai sati biyu da yarwa. A kira na farko a ka daga. Nayi sallama muryar namiji ce ta daga kiran, muryar ba ta da dagawa irin ta maza, ga dadin saurare. "Sunana Sumayya, .... Da sauri ya katseni. Ko zaki taimakeni Sumayya ki hadani da mai wayar nan, ta jima a wurina tsinta nayi z hanya". Nace " Ai tawa ce wayar, bugowa nayi ma ko zan dace na samu". Yace "Kin kuwa dace 'yammata, yaya zaayi ki karba". Nace " Ka kwatanta min in da kake sai nazo na karba". Yace "Ba haka ya dace ba, ni ya kamata nazo na kawo miki, a wace unguwa kike". Nace " Unguwar Doka". Yace "Anya na taba shiga unguwar nan". " kai ba dan garin zariya ba ne". Yace da sauri. "Haifaffe ma kuwa, domin kana dan gari ai ba dole bane a ce koina ka shiga, amma zanzo tare da abokina Suhail, dama zamu unguwa a babur din sa, shi idon garine nasan yasan unguwar, idan na shigo sai na kiraki a layin da kika kirani ki kwatanta min gidan, amma ki tanadi ladan tsuntuwa, domin ba a aikin da babu income yanzu". Nace"idan babu yawa baifi karfina ba zan bayar". "Ba yawa dubu goma sha biyarce kacal". Da sauri cikin mamaki nace " Dubu sha biyar? to daga nan na bar maka wayar mana, tunda ko sai da ita zaayi ba zatafi haka ba yanzu, tun da anyi amfani da ita". Ya sake yin wata 'yar gajeriyar dariya da ta k'ayatar da ni, banganshi ba, amma dai zuciyata sai haskomin hoton sa take, saboda tsadaddiyar muryace mai wani irin amon sanyi da dadi, da take kamancece niya da irin cikar surar mai ita. Kawai Ina jin a lokacin a cikin salo na raha yake sosai, domin barkwanci da raha basa cikin halayyar Fa'izu a sanina. "Bari nazo dai sai mu kashe maganar".Abinda yace kenan ya datse kiran kafin ma nayi. Nuriyya da tayi sararo tana jin mu ni da fa'izu, saboda hand's free nasa . Bayan na kashe wayar tace. " Kiji mu da Mutum. da har ina yabon'sa a zuci, ina kaga na Allah mutanen arziki, ta fad'a hannun Mutumin kirki,a she duk gayyar tsiyar ce . A bashi dubu goma kamar tasa ce zai bamu mu Saya?". Nace. "Ke dai rabu da shi, yazo tukun, muga gudun ruwan'sa. Nace a hankali domin tausarta. Cikin a binda baiga gaza a wa guda ba, Sai gasu sun kafe babur a kusa da k'ofar gidan mu da taimakon kwatancen da nayi musu a waya da suka shigo unguwar. Muna tsaye dama a k'ofar gida ni da Nuriyya. Samarin d'aya fari ne sosai, d'aya bak'i. Bak'in yafi sakin fuska da fara'a a garemu shima black beauty ne gaskiya. Bayan musayar gaisuwa, farin saurayin ya zura hannu cikin aljihu ya zaro waya gami da sabuwar caza ya mik'o mana. Ni na karb"a cike da godiya. Yace. "Sai ki kula, karki sake yarwa, domin ba lallaine ta dawo ba." Nayi mamakin canzawar sa kamar ba shine mai barkwanci a waya ba. Nuriyya tace da sauri. "Gaskiyane kam, domin ba domin mun yi dace da mutanen kirki irin ku ba, ai da tarasa kenan. Kuna da kirki da karimci gaskiya, don Allah yaya Sunayen Ku?" . Ni Kam naga Zak'ewarta, shi yasa nayi kasak'e ina kallon'ta. Wannan saurayin bak'in ,shi ya bata amsa. "Sunana Suhail labaran. Shi kuma sunan sa Fa'izu Bukar". "Kai Amma Sunayenku suna da dad'i, kamar na larabawa? a wace unguwa kuke ne? ". Nan naga mai suna Fa'iz d'in ya jefeta da wani irin kallo a sakarce, dake nunin ta isheshi da Surutu. Ni kuwa dama tuni ta k'ular dani na irin wannan shishshigi. Su ya dace su nememu da hakan, ba suyi ba, Sai mu mata? domin kawai ta zubar mana da daraja?. Tuni dama na fuskanci wannan Fa'izun d'an ji da kaine da fad'in rai. Tun daga Maganar farko bai sake cewa komai ba. Ko kallon mu bai sake yi ba, Sai da Nuriyya ta Shiga k'wak'ulen tambaya ga a bokin'sa ya waigeta sau d'aya, kallo ma na raini. "Zo nu tafi Suhail, kasan sauri muke yi, kuma ba jiran mu zasu yi ba". Inji Fa'izun. Inda ya ce masa "To" . Amma bai motsaba, saboda Nuriyya da ya soma yiwa kwatancen in da suke dalla, dalla. Bai yi nisan ma da zata gane sosai ba Fa'izun ya sake cewa. "Idan ba zaka zo mu tafi ba, ni kaga tafiyata. Bazan jiraka ba wallahi idan ka tsaya, ka taho daga baya." Faiz Ya dubeni yace. "Sai anjima." Nace. "Na gode, Allah ya saka da khairan." "Amin.". Yace bayan ya soma tafiya. Ganin haka Shima Suhail d'in yayi gaggawar binsa saboda ya fuskanci tafiya zai yi ya barshi, bayan babur guda suka zo kuma. Bai k'arasa yiwa Nuriyya kwatance ba dai ya tafi. "Gayun nan sunyi a rayuwa. Musamman ma farin, Fa"iz.Sai dai naga d'an girman kaine da nuna isa , d'an hana ruwa kuma gudu, abokin'sa ya fishi kirki. Yanason a k'ulla zumunci ya hana.Ya bani haushi fa!". Nace".Naji

Chapter 3 of 13