Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani lokaci muna tare muna kallo na sake tsirar tsifa. Ina cikin yi nace. "Wash!. Ya waiwaye ni. "Me ya faru?" . Nace"Wani ciwo ne a yatsana da naji, garin tsifa gashi ya yanki wurin". Yace"Garin Yaya kika ji ciwo?". Nace "Jiya ne ina yanka nama". Yace" Sannu, cikin dan tausayawa, zaton sa gaskiyane, yace "Ya kamata ki rink'a kula." Na faki idon'sa nayi murmushi. Nace "Ancle don Allah ka tayani, kaga gobe mai kitsona zata zo, kuma ciwon hannu na bazai barni na Karasa tsifar ba. Please za'ka tayani my Ancle?". Ga mamakina mai makon ya fara da fusata yarda ya bayi min, sai naji ya ce. "Sai dai nayi miki aski, ni shi na iya Kawai." "Haba dai aski. Yaya zan yi aski ina mace dani." Naci gaba da marairaicewa. Yace"Sumayya wai ni bawan kine kome?". Na fik'e murya irin ta d'a,a nace" Haba! Haba!!. ai ko a shirin wasan kwaikwayo, dole a ce da mijin iya Baba. Darajojinka sun girmi haka tuni, mijina, ba domin na isa ba, sai don larurar nan, kuma nasan kai mai tausayine fa". Ya sassauto, domin naga ma ya d'an Saki fuska. "To, nawa za'ki bani na Lada?". Na marairaice. "Haba, my Ancle. Ina Daughter guda sukutum Sai na biya" Yace "Idan baza'ki biya ba, to kisa hak'uri kuwa." Na Shiga magiya da naci da shagwab'a duk dai, babu shirI ya fizgi kibiyar dake nake mik'a masa cikin fusata. "Wannan Yarinyar wallahi da ace kina da maita, kika kama kurwa ba zaki saki ba, daya zan miki, daga shi babu k'ari". Banyi fushi ko kusa face 'yar dariya ma. "Na yarda wallahi, mai shirin zuwa sama ko takarda ya taka ai ya rage". " inji wa babu in da yaje, kawai zance ne". Yace cikin bani amsa cikin kosawa, don har da 'yar harara ma, ya fizgi kibiyar daga hannu na cikin fusata ya soma. Yana kan kujera ina gabansa a kasa. Daga d'aya Sai da a ka tafi uku, kuwa, saboda naci na. Amma yanayi yana dunguremin kai. A raina fad'i nake, aje a hakan, naci nasara, tun da ka samu, kazo hannu, hakan yake kuwa tayani tsifar ya zame masa k'ara'i, ko ba yawa, ina shan dai sababi, amma Sai na jure. Wani lokacin littattafan makaranta na na kan kwaso nace ya koyamin wasu a bubuwan. Zai koyamin na gane, amma Sai nace bangane ba, domin mu ja lokaci. Sai Nasha fad'a kafin ya sake. Duk Ina yin haka ne domin na Shiga jikinsa, da rayuwar sa, mu k'ara shak'uwa. Kuma bana yarda na zauna nesa da shi, ko tazara kad'an bana bari, jikin sa dab nake rakab'uwa kamar 'yar kyanwa kullum in dai ya zauna. Farko randa na soma yi masa hakan, matsawa yayi. A wayance muna hira na kuma matsowa jikin sa. Ya sake dan matsawa, a na uku Sai yace min. "Wai duk wadatar wurin nan Sai kin matsamin Sumayya?" . Murmushi nayi, nayi masa Farr da ido nace"To, ya kake so nayi? bani da kowa yanzu da yafi kusanci dani Sama da kai. Idan ban rab'u da kai ba, Ina kake so naje?". Bai tsinkamin ba, ya maida kallon sa ga mutuniyar tasa, wato boll. Wannan damar tasa na sake shigar da wata. Sai muna zaunen, Sai na rink'ayin layin baccin k'arya, Sai nayi luuu! na zubo jikin, sa, har sau uku Ina yi, yana d'an tureni. Nan ma da fari yayi k'orafi yace. "Wai menene haka ne Sumayya?" Nayi firgigit Ina mitstsike idanu. "Me ya faru? Menene Ancle.?" . Kamar bansan komai ba nayi. Mik'ewa yayi yace "Na lura kora da hali kikemin. Bari na tarkata na barmiki wurinki kafin kiyi min kora da kara." Dariya ta cikamin ciki fal! amma ina bari ta fito zai d'ago komai, shi yasa na gintse a bata. Nan ma tun yana mita har ya zame masa jiki, ya rabu dani, ko nayin baya tankamin, kuma baya janye jikinsa, Sai ya mai da idon sa kan kallo Kawai, domin kallon ke sawa ya jima sosai ma a falona. Domin ni nake samo irin film d'in da yake so, har na boll masu tashe. Duk domin na ja hankalin sa ya rink'a jimawa sosai. Shi yasa har k'arfe d'ayan dare yana kaiwa. Wani lokacin ma bacci zan yi, shi zai tasheni idan ya gama kallon. Wani zubin shi zai yi bacci, ni zan tashe shi. randa ya gaji kenan idan ya buga boll. Kuma duk dare, Sai ya koma d'akin sa, bai tab'a kwana a wurina ba. Tun daga ranar da nayi wa Ancle Fa'iz gyaran d'aki ya zame min jiki. Kullum Sai na Shiga nayi masa gyara,domin bai karb'i mukullin d'akin ba da na cira, yana wurina. A bu d'aya yafi damuna, nake gwagwagwar juriya. Shine na yarda Ancle yake yawan yin waya da Salima, kuma a gabana. Sautari ita ke bugo masa, kuma ya amsa ya biye mata a falona suyi ta hira. Ko Ancle baisan ina son,sa ba, bai kamata yayi min haka ba a zatona, tun da yasan aure mu kayi, dole zanji babu dad'i. A binda Zuciyata ta bani kawai, Ancle Fa'uz bai d'auki auren mu a bakin komai ba, face aure ne kawai na wata manufa, mai wa'adin k'arewa. Sai dai na lura, Salima tana cikin damuwa ainun na aure na da Ancle Fa'izu. Domin Kusan kullum idan suna waya, a lallashi da ban hakuri yake k'arewa. Sababbun kalmomin da yake fad'a mata har na haddace sune. "Kinfi kowa sanin matsayinki a zuciya ta Salima. Wallahi sonki da k'aunarki babu a binda ya gutsiresu, suna nan. Kiyi hakuri lokacin zai zo, kamar yanzu ne. Aure na dake babu fashi, za'ayi in Sha'Allah. Ki soma kiran kanki ma matar Fa'iz." Idan hirar tayi tsayi tashi yake ya fice da wayar suna hirar soyayya, bazan sake ganin sa ba, Sai safiya. Kishi sosai nake ji, amma danne zuciya ta nake yi, kar nayi wa kaina gurun gund'uma. Domin sautari, nuna matsanancin Kishi, kan sa mace, tayi a sarar wanda take kishi a kan'sa. Ina ga ni kuma da har yau ban mallaki zuciyar sa ba?. Ancle Fa'iz, har yau bai je Kiran da maman Salima ke aiko masa ba da sak'on yaje ba. Na lura kuma bashi da niyyar zuwan ma a kusa Sam. Tayi aike har ta gaji. Nasan kuma ko da kanta tazo bazai saurare ta ba. Kuma ko kunya bai ji ba, ga 'yarta suna tare kullum a na shek'a soyayya a waya. Ancle Fa'iz da bam yake. Na gama shirina tsab na makaranta. Na rufo k'ofa, na nufi d'akin Ancle Fa'iz a karo na uku yana ciki tun da na aure shi. Da safen da na Shiga d'akin Ancle Fa'iz, haka kwance yake kamar mai bacci, amma da nayi sallama Sai naji ya amsa. Na zauna kan wardrobe gajera dake jikin gadon, na, fara da gaisheshi. Nace kuma."Ancle, zan tafi makaranta." Ya bud'e idanu a hankali, ya mik'e ya tashi. Ya nufi sib,ya bud'e ya k'irgo kud'i jikin kyauro sabbi fil, ya zara ciki ya mik'omin. "Ga kud'in mota dana kashewa." Nace"Wallahi, kabarshi Ina da kud'i da yawa." Zan masa gaddama, a karo na farko, ya lalubi tafin hannu na, ya mannamin kud'in ciki, ya dunk'ule. Yace. "Ungo nan malama, hak'k'inki wuyana yake, I don't care, a bout, you have money or not." "Na gode, Ancle. " Na fad'a a ladafce. Lokacin na kula da irin iskar da ya sakarwa kan'sa. Ga fankar tsaye, kusa da kan'sa ga fankar Sama, Sai kad'awa take. Kuma ya saki k'arfin'ta. Nace"Ancle Fa'iz iskar nan fa tayi maka yawa." Bayan ya koma kwance ya bani amsa da cewa. "Tayi min kad'an ma." Nayi dariya a hankali nace. "Shikenan,Kawai Sai a huda bango a k'ara Maka da A C." Ya rungume fulon da yake kwance sosai kafin yace. "Wannan a bune sassauk'a tun da Ina da Hajiya kamarki, Sai kisa a yimin a kusurwoyi hud'u ko?." Murmushi nayi, cike da jin dad'in zolayar da yayi min, ban taga ba kuma saboda sauri nace. "Na tafi Ancle." Yace. "A dawo lafiya." Momi kuwa da nayi mata sallamar zan tafi makaranta bayan gaisheta, bata cemin ko cikan ki ba. khairat ce tayi min a dawo lafiya, a tsakar gida. Muhibbat tsarabar harara na samu. Khalifa baya nan shi. Abban su Fa'iz ma a waje na sameshi na gaisheshi har k'as nace na tafi makaranta Abba. Addu'a mai kyau yayi min.Mutum ne mai kirki da kyautatawa na lura. Ga shi da sanyin zuciya sam ban tab'ajin ya d'aga hak'ark'ari ga kowa ba, Sai dai na jiyo muryar Momi. Ina yawan jin hargowar fad'anta ga Muhibbat. Ita ma Kenan. Komawata makaranta, na samu sauk'in damuwa. K'awayena suka yi ta murna dayi min shak'iyanci kuma. Abubuwan da suka wuceni tuni na mai dasu, saboda a minai, gashi ni kuma akwai himma da fikira wacce baiwace daga ubangiji. _Tabbas Sumayya ta soma samo bakin zaren sakarta, amma bamu sani ba, zai tsinke ko zai tafi dodar ga irin sakar da take so tayi_ *Taku* _Zainab mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe. *NI DA GIDANA* *Zainab ilyas mazawaje* __Best brilliant interlligent writer_ ........ ✍️ *Page 17* Ranar litinin sai yamma Lis ni da gida. Sai naji na sarara a raina a kanda. Sanda na dawo daga makaranta, Kichean nake shiga na dafa a binda ya samu, nayi shigewata d'aki, idan ba alwala ba bana sake fitowa. Amma duk a binda na dafa, ina kaiwa Momi. Bata tsinkamin, amma sai na a jiye gefe. Bansan yaya take da shi ba. A lokacin babbar damuwata na samu kulawa koyaya daga Mijina, kar abin yayi min yawa wai shege da hauka. Cikin nasara na soma samun kuwa. Domin Ancle yana d'an zama a falo na fiye da da, muyi 'yar hira kad'an, da sai dai mu zauna kawai muyi jugum jugum, ko shi naga yana ta chat a waya, kuma nasan da Salima ne, sai yayi kamar ma ya manta da ni a wurin. Da abin yana da muna daga baya sai na dai na sawa kaina damuwar, domin naga ba mafita bace. Ancle baya jimawa dai sosai ma a falona idan ba wani kallo na kunna da yake so ba. Kuma bai fiya yi min hira ba, Sai dai ni. idan kuma na cika jan shi da hira, Sai yayi min shiru, nayi ta zuba kamar kun nan niyar rediyo baya tagamin. Idan hirar ma tayi tsayi, Sai kawai naga ya tashi ya fice. Hakan na nufin na dameshi da Surutu kenan. Da na fuskanceshi, sai nake binsa da salon halinsa. Da naga yayi shiru ya daina tayani, ko bani amsa, Sai nima nayi shiru. A hankali a hankali na soma sanin Ancle Fa'iz. Me yake so, menene bayaso. Kuma hakuri da kwantar da kai yasa na soma fahimtar. Ancle yana da wani irin hali da raayoyi da ya bam bamta da na wasu mazan, baison turare mai tashi, sai mai sanyi can kasa, baison turaren wuta na daki sam, ko za asa sai dan kadan sosai da baaji sai sama sama, haka ma air freshner nunawa yayi baiso ta yi yawa sai kadan. Sannan baya son k'unshin zamani da ake yayi, yanzun. Bansani ba, Sai bayan nasa an zo har gida an rangad'amin.hannu da k'afa, marun da bak'i na fulawoyi, yayi kyau ya zanu. Amma yana arba dashi yace. "Wannan ai b'ata jiki ne,menene a bin Sha'awa game da wannan shirmen." Nace"Kwalliya cefa ta mata Ancle." Yace"b'ata kwalliya dai, Ina a bin burgewa a ciki?". To kwalliyar fuska ma ta mata, baya so Ancle Fa'iz. Ranar wata lahadi banje makaranta ba, bayan kwalliya ta situru nasha make up.powder eye liner, da eye shadow ,lipstic da white lips da jagira tsararriya, da tasha shape. Wallahi kuma nayi kyau har ga Allah. Amma Ancle yana shigowa da ya kalli fuskata ai sai naga ya kwashe da dariya. Dariya sosai da ban tab'a ganin yayi ba. Zatona daga can wurin su Momi ya taho da a bar'sa, ai sai na ta yashi, ina yi ina tambayar ba'asi. Abin gwanin bandariya wai yaro ya tsinci hak'ori. Yace"Kema dariyar kikewa yi wa kan ki?". Nayi harr da ido, Nace. "Kamar yayafa?'". Ya sake duban fuskata, ya tintsire da dariya. "Kinga fuskarki kuwa? Sai kace wata sabuwar aljana?". Tabbas furucin'sa ya sosa min rai, amma na daure zuciya ban nuna ba, ko furtawa ba. Cikin salo ma na kamar shagwab'a nace. "Kai Ancle, me fuskata tayi?". Yace"Kin cikata da shafe shafe da yawa. Ga na fuska, gana ido gana leb'e gana gira, gana zagayen ido. Is too much, Sumayya. Don Allah karki sake yi." Tun daga lokacin kuwa ban sake yi ba. Iya kacina powder kad'an, kwalli. Sai white lips idan tayi hali. Domin ragowar basa burgeshi, baya so. A bubuwa da yawa basa burge Ancle Fa'iz. Lokacin da ka Tak'ark'are Sai kayi masa bajinta, to lokacin zai kushe. Shi yasa daga baya na sanyawa Zuciyata salama, bana fushi sam idan nayi abu ya kushe bana fushi, sai dai nayi k'ok'arin gyarawa irin yadda ya nuna yana so, ko bana so kuwa. A cikin 'yar hira dana ke Samun albarkacin ta a tsukin, nake bincikar sa irin ra'ayoyin sa da a binda yake so da wanda baya so. Ya kan fad'a min, wani zubin. Wani lokacin kuma ya bijire yace wai menene dalilin da nake damunsa da tambayoyi da bincike?. Nan saduda na rabu jdashi, na tara gaba kuma. Har lokacin babu ka lamun somi somin Sona dana fuskanta daga gareshi. Har lokacin girkin Momi kawai yake cI. Cikin hikima nake yi masa magiya nace ya rink'a ragomin, nima ina Sha'awar girkin Momi. To wani zubin ma nan falona yakan zo da shi yaci, saboda naci na. Nima daga nan Sai na turo masa nawa da magiya nace yasa albarka. To dai nawan ma kushewa yake a gabana. Ya kance gishiri ya zarta. Ko kuma magi. Ya dai ficewa na cika attaruhu. To Sai na rage sa attaruhu, na rage magin ma da gishiri, nayi iya iya wata wurin kyautata komai. To amma me.? ya daina k'orafin, amma ba yabo. Na lura girkin Momi kawai ya fiso. Kuma naci, na yaba Kam. Yabon gwani tilas. Momi ta iya girki sosai kuwa. nafi zaton fannin girki ma ta karanta. Na dai zamewa Ancle Faiz dan kadafi, na manne na nace, cikin shiga al'a muransa, duk furucin da zai jefamin mara dadi ba na yin fushi ko zuciya, zuciyar tuni ta horu da haka har ta bushe. Ni keyin zaraf cikin al'amuran sa, kafin ya buk'aci a bu nayi. Sam. baya so na yi masa d'awainiyar komai. Rufe dakin sa yake yi da mukulli idan zai fita. Idan yana ciki, kuma bayaso nace zan Shiga ballantana nayi masa gyara ko Shara kamar yarda na k'wallafa rai, Sai ya hanani fir!. Baisani ba rannan na zari d'aya daga cikin 'ya'yan mukullin sa da yake jikin key holder na b'oye. Da yamma Lis, na taso daga makaranta da wuri saboda lacture ta ranar gajeriya ce na bud'e d'akin nasa. Gaban su Muhibbat da Khairat suna hira, suka bini da kallo. Gyara nayi masa sosai. Dakin a share yake tas, amma a kwai 'yar k'ura jikin sib da wardrobe. Na k'alk'ale komai . Na cire zanin gadon nasa masa sabo gau, nawa duk da nasan ma baiyi wani datti ba, saboda ba laifi Ancle yana da tsafta. Haka ma labule na cire nasa masa nawa sabbi masu kyau, domin biyu aka yi min. Nasan ma mai kyau ne, amma nawa sabone ful, domin kala biyu ne dani masu tsada. Zanin gado kuma kala uku. Na tsara masa Kayan cikin kwabar sa, na jera, saboda yana yawan hautsinawa ya barsu garin binciken kaya. Nayi masa gyaran da bazai rinka hautsina komai ba, komai dalla dalla. Na ware under's d'insa da singlet da gajerun wanduna, har da Kayan boll da babu wanki na kai d'akina na a jiye da niyyar gobe na wanke. Na fesa masa air freshner Sama Sama, kar yayi min k'orafin turare ya hau masa kai. Shi yasa ma ban k'ara da turaren wuta ba. Dakin nasa yayi kyau sosai kamar ba shi ba. Da yake falon ma babu tarkace, kujera guda ce sai TV dake jikin bango da risiba. Wata laptop d'in Ancle na gani madaidaiciya ta d'au hankalina na bud'e. Tabbas da nasan me zan yi tozali da shi, da ban bud'e ba. Hoton Salima ne da Ancle Fa'iz ya cika fuskar laptop d'in. Suna jikin juna, Salima ta kwanto a jikinsa ya tallafota da hannayensa ya mannata gam a jikinsa. Tamkar mata da Miji. Abin ya d'aure min kai, dama Ancle Fa'iz zai iya haka? Ko kuwa soyayyarce duk ta zautar da shi, ya biyewa hud'ubar shaid'an?. Sai da na daure zuciya na sake kallon hoton. Su duka murmushi suke yi a hoton. Sai da nayi tasbihi ga mahaliccin surorin'su. Ita da shi d'in babu kanwar lasa wurin kyau. Sun dace da juna Kam in dai wurin duba ne.idan kuwa suka tashi haihuwa,wad'anne irin kyawawan yara za'su haifa. Za'a Sha kallo. Ko shakka Ancle Fa'iz yana son Salima sosai. Kusan duk wani abu nasa mai muhimmanci hotonta ne a kai. Wayoyin sa biyu ne banason gani ma, Saboda duk hoton Salima ne. Da dai da key holder dinsa na d'aki hoton Salima ne, k'arami a ciki anyi masa siffar zuciya. Lallai Ina da gagarimin aiki a gabana, tun da ko makami na yak'i daya ban mallakaba, na satar zuciyar mijin da muka kusa tarayya da Salima. Ko ince ni zaman wucin gadi nake yi a wurin Ancle, waadi nake jira. Tayi min fintin kau Salima na k'wace Miji tuni. Tun da familyn sa ma duk mayak'anta ne na fagen daga. Gashi kullum kuma k'ara zarmewa nake cikin Soyayyar Ancle Fa'iz. Shi yasa kullum kishin sa ma k'aruwa yake a raina, duk da bai a jiyeni a rukunin mata ba ma. Ba domin na tabbatar Sai mun d'ebi 'yan kallo da shi ba, da Sai na rotsa laptop d'in nan. To laifi kan laifi ma zanyi. Na shigo masa muhalli bai Sani ba, kuma nayi masa tsadadden ta'adi. Nan ma cewa zai yi lek'en a Siri ya kaini. Wannan hoton, ko ba'ace ba, nasan yana ji dashi. Da na fito daga d'akin Ina rufe komai, Momi da Muhibbat na gani daga saman bene sun kafa min idanu, nayi kamar bangan su ba. Nasan Muhibbat ta kai mata tsurku. Fuskar'sa d'auke da alamomin Mamaki ya shigomin. Hannun sa ya dafe kujera yana daga tsaye ya ce. "Wa ki ka ga ya shigar min d'akina?" Kamar da gaske na dake "Anya an Shiga d'akinka kuwa yau Ancle? Wani a bune ya faru?". Yaja dogon numfashi. "Tabbas an Shiga an jima, domin komai na d'akin ya canza. An canzamin tsarin komai na wurin. Wanene mai wannan aiki, ko nace wacece?". Na kanne cikin b'oye dariyar dake son k'wacemin. "Ta'adi a kayi maka Ancle?". Yace. "Gyara a kayi, tun da wurin ya k'ara haskaka yayi kyau". Naji dad'i sosai na yabon da yayi. Ancle Fa'iz kafin ya yaba abu a ya'ra. Saboda Jan zare, na zolayeshi da cewa. "Ancle, Ina Jifa aljanun cikin d'akinka ke sonka, suka yi maka gyara." Yayi min k'uri da idanu, har Sai da naji wani abu mai hargitsa yanayi kafin ya nisa tukun yace. "In dai haka ne, to kece shugabar aljanun, ke kika jagorance su." Dariya nasa ta burgewa. Wato ya fahimci ni nayi masa dai gyaran. "Ina kika samu mukullin d'akina? Yace. Nace. "Jikin mukullayenka na cira." Nayi zaton zai min fad'a, amma Sai naji yayi shiru.Na fahimci yaji dad'in gyaran da nayi masa a fuska. Duk da kullum nunawa yake yi baya so nayi. Tamkar kaska haka na Mak'alewa Ancle Fa'iz, saboda ya rage kyarata da yawan yi min fada,a kan da. Domin takai ko bai shigo d'akina ba, ni zan bishi nasa d'akin, bana kuma shayi, ko fargabar mutanen gidan. Tuni na soma yin sabo da shan zagi, harara, habaici da zund'e. Shi yasa idan ma anyi min, bana d'aukar'su a bak'on al'amari da zai yi ta damuna. Wannan yasa zuciya ta ma ta kangare ta bushe, domin idanuna sun rufe da Soyayyar Ancle da bin hanyoyin da zan janyo ra'ayin'sa gareni. Duk da Shima Ancle Fa'iz d'in ina shan wuyar sarrafashi wurin shishshige masan da nake yi. Yakan nunamin ma k'arara cewa na ta kuramasa, wani lokacin, amma Sai na shanye. Bayan Ancle Fa'iz ya sauko daga saman Momi, ya sameni zaune a d'akin'sa Ina dakon'sa. Ya samu wuri ya zauna, ya fara da cire hular kan'sa. Nayi zaraf na d'auka, nasa a kaina na dubeshi nace. "Ancle tayi min kyau?". Ya jefeni da kallo d'aya na gefen ido yace. "Ke namiji ce da hula za'ta yi miki kyau?". Sai na cire daga kaina nasa masa a kan'sa. Ya cire ya ajiye. Na sake d'auka na rik'e nace. "Wallahi hula ba k'aramin kyau take yi Maka ba, my Ancle." Yace. "Ko?". Na sake saka masa a kan'sa, ya kuwa cire da sauri yace. "Wai yaya haka ne, ina cirewa kina samin?". Nace. "To, ni nafi son ganin ka da hular, kafi kyau Allah". Wannan Karon wani murmushi naga yayi Maimakon hasala da nafi zato, yace. "Sumayya, kina fa takuramin, kina fa sani surutun da ban shirya ba, Allah kina ma cin darajar maraicinki ne nake sassauta miki, domin ina tausayinki wani lokacin, amma a kiyayi dai zuwa rafi kullum, wataran sai an fasa tulu". "Nayi murmushi. "In dai bukatar da a kaje na debo ruwan ya samu to ai ba damuwa, Ancle kasan ranar biyan bukata rai ma ba a bakin komai yake ba". Ya dan daga min bakar girar sa gami da dan fito da ido. "I see". Iya a binda yace kenan, da alamu ya dan shiga duhu da furucina, ko kuma ya fahimta ya maze, saboda na fahimci yana da saurin karantar mutum sosai, amma sai ya waske yayi kamar baisan me kake ciki ba, ni kuwa da gayya na furta. Kwana biyu na sake samun Ancle a daki ya na bubbude sababbin wasu unders da ya sayo daga leda ya na dubawa, bai dago kai ba gareni duk da ya amsa sallama ta. Na zauna gefen sa kan kafet din dakin, shi kuma yana gefen gado. "Sannu da aiki my Ancle". Nace ina murmushi. Yace " Yauwa sannunki". Na mika hannu zan amshi singilet din dake hannun sa, ya janye. "Ancle gani fa zanyi". Yace "Ahaka ba kina gani ba, look karfa kizo ki matsamin, bana son takura". Na sake yin murmushi. "Ni ba takura maka zanyi ba Ancle, kawo to na ninnin ke nasa maka a ward robe". " Barshi nayi". Nace "Kai my Ancle bai kyau tu ba ina zaune kayi aiki ba gaskiya kawo please". Yace " Hmmm!! " Kawai. Kamar bazai bani ba sai ya miko min kayan duka ya mike yana mai fadin. Yarinyar nan duk kin bi, kin hanani sakat? nasan idan ban baki ba baza ki barni ba, bansan wa kika gada ba wurin kafiya a dangi". Nayi 'yar dariya nace. "A dai laluba za a samu, domin ruwa baya tsami banza" "Bulala kawai Allah zan a jiye kusa dani. Surutun da ki ke Sani banyi niyya ba, yayi yawa fa". Nace "Barewa fa a dawa ance da d'anta take wasa Ancle Fa'iz. Kaman ta bani da kowa Sai kai? Kaine uwa, kaine uba, kaine Kawu, kaine Yayana kaine....." Ya da katar dani da hannu. "Ya isa !. Ke kin fiye Surutu, Sai kace aku kuturu." In da sabo na saba da irin wad'an nan lafazai nasa. Kuma a hakan muke ci gaba da hirar bana fushi kamar kullum. Ranar dai na ganshi cikin walwala dai, Bansan dalilin ba. Ya nutsu ya soma cemin. "Ki ta yani murna, na samu shigowar wasu kud'ad'e masu yawa na wasu wasanni da muka yi a state uku, Sai jiya aka turomin nawa cikin a count. Ban tab'a Samun kud'i masu yawa a wasa ba irin wannan. Nayi kasafin su ma. Na wari wanda zan ba Momi da Baba, na wari Wanda zan Sai mota, da wanda zan sake jefawa a harkar ginina da yake taci min kudi, da na samu da ya handame". Naji dad'i sosai da na samu matsayin da ya fad'amin sirrin ci gaban'sa. Na kuma yi ta surfamasa godiya da addu'a na kyautar kud'in da zai ba iyayen'sa, Sai a zaci nawa iyayen zai

Chapter 10 of 13