ko?".
Kafin na samu amsar bashi ya zarce.
"Sumayya Yarima ya amince da auren'ki. Abinda bani da tabbas d'in yiyuwar'sa, Yarima ya tabbatar min."
Gabana ne nidai ya bada ras! addu'ar da nayi bata Shiga ba kenan? Sai na soma istigfari a zuci, saboda addu'a ai bata fad'uwa k'asa banza, nasan sai dai in kaddara tace ta dole tasai na auri ya tozarta ni ba yarda zan yi, sai dai daga baya Allah ya kawo min sassauci da mafita kawai.
Cikin uku kuma na abinda mutum ya roka a addua za'a rabauta da abu d'aya dole cikin ni'imomin Uban giji. Tayi yu ni Allah ta wani gefen ya bani. Jikina sanyaye na dubi kawuna da bakin'sa yak'i rufo saboda farin ciki. A karo na farko naji farin cikin daya nuna ya sosa min ma rai. Sai kace Wacce zata auri wani Mutum na musamman da ya zama abin wasoso wurin kirki? amma basarwa nayi, na d'an kau da kai nuna alamun kunya, kar ya fahimci halin da nake ciki.
K'arshe yace "Yarima yana Kano, ma a waya mu kayi magana. Ya tafi buga boll da club d'in heart land da suka gayyace shi. Amma nan da kwana uku zai dawo.zai zo wurin'ki ku tattauna".
Har ya Fice ban iya cewa da shi komai ba.
Tun daga ranar na soma yiwa kaina jaje, tun da babu mai min. Tawa ta sameni. Auren Ancle Fa'izu ni wurina jarraba ce mai Zaman kan'ta.
'Yan mata da yawan gaske nasan za'su so auran Yariman kawuna, ko da kuwa a shirin wasa ne. Amma ni koda wasan ba na fata. Ban tab'a zaton zai a mince da aure na ba, duk da auren son zuciya zai yi. Wato babu niyya har zuci, Sai domin ya cimma wata manufa. Ko shakka, Ancle Fa'iz a minin Kawu na bashi da tabbas.
Nasa rai kacokam da bazai yarda da aure na ba,Sai gashi ya a mince babu musu.kuma yarda nayi imani zan mutu haka nayi imanin babu ko digon sona a zuciyarsa, kawai domin ya cimma manufarsa ne.
Suna tare da kawu Sulaiman a d'akin sa da daddare, ranar da ya soma zuwa zance wurina ban Sani ba, Sai da Kawu Sulaiman ya
shigo gida yace na kimtsa nazo ga Yarima yazo yana d'akin'sa. Ba
wani wahalallen shiri
nayi ba, kadaran kadahan, saboda nasan kome nayi ba burgeshi zan yi ba. Na Shiga d'akin Kawu Sulaiman da yake bude da
sallama, Ancle Fa'iz ya amsa, gami da cire kai sau guda ya dubeni, ya sunkuyar. Na ajiye tire dake d'auke da drink's mai sanyi da snack's da Kawu yace na kai masa.
Na gaisheshi a mutunce, da girmamawa, na nemi kujerar dake fuskantar tasa na zauna.
K'amshin turaren'sa mai sanya zuciya shauk'I, Sai tashi yake sannu sannu, shi yasa banajin nawa ma. Kallo guda nayi masa nima na kasa k'ara na biyu. Baki d'aya Sai na raina kaina. Shadda yasa pink colour mai duhu, da tayi masa kyau iyaka. Abinka da fari. Ancle Fa'izu mai nak'altar iya kwatance yayi tsararo ya iya misaltamaka cikar surar kyawun'sa cikin sauk'i, ko yayin to sai ya rage. Sai ka ganshi zaka tabbatar da hakan.
"Sumayya, kinji komai daga bakin Sulaiman ko?".
Da sauri ya furta .
Nace "Eh!".
Ya zarce"Sulaiman ba komai ya fad'a Miki ba, saboda ba komai na fad'a masa ba. Dalili, ni dake komai ya shafa da za muyi auren. Yace min, ya nemi yardar ki, kin amince zaki aure ni,shi yasa nima na amince nan da nan..
Bazan b'oye miki komai ba Sumayya. Ni ban iya boye boye ba, ko rufa rufa ko b'oye gaskiyar a binda ke zuciya ta. Ina so gaskiya da a Mana suyi Mana jagora sumayya. Nasan kuma kinyi niyyar taimakamin, tun da Kinsan me ya tursasani yin auren gaggawa irin wannan.
Sumayya! Yace cikin kafeni da idanun nasa ma'abota kyau da fari masu launin shud'i shud'i. Kasa iya had'a idanu nayi dashi,sai amsawa.
"Kiyi hak'uri da jin a binda zai fito daga bakina. Dole na tsage miki Gaskiya. Aure na dake na wucin gadi ne. Kinga ne ai".
yace cikin d'aga bak'ar girar sa.
A razane na dubeshi, batare da na niyyata ba.
Auren wucin gadi, na nufin aure na zai yi na wani d'an lokaci ya rabu dani. Zuciyata ta tunasar min.
Na jinjina kai a hankali, cikin jinjina kalaman'sa. Duk da na zargi auren da zai yi da auren manufa, ban kawo wannan niyyata sa ba. Amma ta yaya ma zan jefa kaina cikin wannsn rigimar da Zai iya janyo min zargin mutane, domin biyan bukatar kan sa shi kadai?
Sam bazai yiyu ba, da sake.
Ya d'aga kai yana mai kallon idanu na, da nak'i yarda mu had'a ido tun da nazo. Ko kallon'sa zan yi a sace ne.
"Salima, ita kad'aice d'iya macen, da na tab'aso a rayuwa ta. Kuma har gobe, ita nakeso. Kuma a k'ok'arina na na sameta ne, ta hanyar rama a binda a kayi min na shirya wannan auren bakatatan. Ta yiyu kema kina da wanda kike so ko?".
Ya zama lazim, nace masa Ina da wanda nake so, kar ya d'aukeni, wata kara zube, tun da gashi Shima Sai zuzuta son wata yake a gabana, tamkar gabansa take, saboda cin fuska, ni haka na fassarashi.
Nace.
"Ina da wan'da nake so".
Sam banga wani sauyi a tare da shiba, Sai ma d'an murmushi, da yayi yace.
"Shi Kenan, Kinga Sai ki fad'a masa irin auren da zaki yi ba d'orarre ba ne, face na wani lokaci, da zai k'are, na taimakona domin cimma manufata. Idan da fahimta da k'auna ta gaskiya zai fahimceki, ya jira . Yarda na d'aukeki sumul, haka zan dawo masa dake, ko k'warzane, bazaki yi ba. Zan kula masa dake. jin abin nayi wani bam bara kwai wai namiji da suna hajara, wani wawan namiji zai yarda muyi yarjejeniyar auren wucin gadi na dawo masa ya aure ni? gaskiya Ancle Faiz son zuciyarka ya zarme yarda ka manta da damuwar wani ko mafitarsa face taka. Zuciyata ce ta shaidamin.
Ya gyara zama, cikin hard'e k'afafun'sa.
"Hak'ik'a naga a lamomin hankali, da nutsuwa da addini a tare dake Sumayya. Shi yasa Sulaiman, yana cemin ke ya zab'amin na a mince, musamman da naji yace ma kin yarda da aure na. Amma dai Ina jimamin, yin auren wucin gadi, da d'iyar wanda nake ganin k'imar'sa da darajarsa a idanuna. Amma na kasa juya baya. I think, some thing is wrong with me."
Nace.
"Kaji da shi." A zuciya ta.
"Amma fa wannan magana da mukayi, ina so ta zama sirrin mu, bana so taje kunnen kowa, saboda mu ta shafa."
Nan kuma cewa nayi, a cikin zuciya ta.
"Ka makaro".
Yace.
"Idan kina da a binda za'kice kema, kina iya fad'amin."
Abinda na iya cewa Kawai shine.
"UM!. Saboda naga al'amarin nasa, ya gagari cewa ta. Ya daga kai a hankali cikin kasalallen kallo ya dubeni da yaji shirun yayi yawa, ya dan tabe baki irin na jin haushi, ya maida kansa kan waya, naga yana ta danne danne, ashe flashing yake tayiwa kawuna, kuma shigowar da kawu yayi shi ya tabbatar min shi ya kira.
"Lafiya dai Yarima?".inji kawu na.
Yarima ya ce " Tafiya zan yi Sulaiman, shine na kira muyi sallama".
"Haba dai, daga zuwa, ko minti goma ba kayi ba?".
Yace a dan fusace. "Idan na zauna, ciwon zuciya sai ya karni ai, wannan bagidajiyar 'yar taka taki cewa da ni komai, sai kauyanci take ta dokamin, ina zan iya, gwara na ware kawai".
Kafin kawu yayi magana, na dan dago kai muka hada idanu bazata, sai kuwa ya jefomin wani kallo da jefamin wata irin harara, da sauri na sunkuyar da kai.
*lallai abin na yi ne inji mai tsoron wanka*.
_mu dai je zuwa_
Alkalamin*....... 🖋️
_Zainab ilyas mazawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
_NI DA GIDANA_
_Zainab Mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️
*Page 8*
Kawu Sulaiman, banga ya nuna komai ba illa yace.
"Karkayi saurin rik'on'ta Yarima, had'uwar kuce fa ta farko".
Yayi saurin d'aga masa hannu.
"Kaga, kar ka bata wata kariya saboda tana 'yarka. Tana sane. Yanzu da cikin k'awayen'ta ne, da tuni ka soma jiyo shewarta, wai sunan ita 'yar jami'a ce, kyau a maidota primary, kuma ma a ji d'aya."
Raina kam, naji ya sosu da furutan Ancle Fa'izu nacin fuska a gareni. Tabbas, halin'sa yana nan nacin zarafi, bai ragu ba ma, Sai k'aruwa ni a ganina. A gaban fa Kawu Sulaiman, Wanda zai nemi aure na a wurin'sa yake min irin wannan wulak'ancin. Gaskiya Ancle Fa'iz baisan wata aba wai ka ra ba, ko kawaici, ballantana kunya.
Kawu Sulaiman ya dubi komai da aka kawo masa bai tab'a ba, yace.
"Yaya baka Sha ko d'an lemon bama. Me yasa?".
Yace.
"Ta banine? a jiyewa fa Kawai tayi. Wai look at her, batasan ma yaya zata tarbi bak'o ba? to Sai yaushe? Wannan 'yar taka Sulaiman da gyararraki, ba gyara ba. Ya juyoyo gareni ya sake watso min wani kallo mai kama da harara.
"Kinzo kinyi min wani dimkim dake. Sai a bin ya bashi 'yar dariya ya dara kad'an. Sunan fa wani ganye wai Shima dinkim. Sai ya sake sakin 'yar dariya da ban tab'a ganin yayi irinta ba.
"Ya kuma fa isheka haka haka, Yarima. Kai wani irin siriki ne wai, gaba na sai aibatamin d'iya kake.Ko mutuwa ance tana alkunyar idanun iyaye.Wai kai bakasan Kawai ci ba, ko kunya?".
Bud'ar bakin'sa yace.
"San'da a kayi rabon su bana nan, ko zaka sammin taka?".
Ancle Sulaiman ya bishi da kallo kawai, kamar bazai taga ba, sai yace.
"Ank'i a sammakan, kasan darajar su ne."
Murmushi Ancle Fa'iz yayi.
"To, rik'e Kayan'ka, ka kuma mai da wuk'ar. Ka Sani, ko nace Sumayya tayi zuciya ta daina gidadanci kawai, shine zai sa na sarara mata Wallahi, ba Sai ka tada komad'a bama."
Ni dai daganan, Sulalewa nayi na barsu, suna sa insa basu sani ba. Nace, sun fi kusa. Ga duk kan alamu suna irin wannan karawar, mai kama da wasa, a zahiri idan ka gansu.
Wannan nasan somin tab'ine a kan matsalolin da zan fuskan'ta idan nayi saken auren Ancle Fa'izu. Duk yarda zanyi kuwa zanyi, domin yakice auren.Sam! ban shiryawa cin fuska ba, da tozarci da wulak'ancin Ancle Fa'izu. wato Yariman kawuna.
Bazan yarda burina ya rushe ba. Tuni zuciya ta ta tsaramin, yarda nake son rayuwar aure na ta kasance. Rayuwa nake so, sosai ta soyayya da nishad'i da walwala, da farin ciki, da fahimta. Na tabbatar na auri Ancle Fa'izu duk sun rushe. Ballantana ma Wai auren wucin gadi, yake so nayi,wanda zai k'are kusa ne, nesa ne ban Sani ba, shi ya Sani. Abinda na sani, ni zai cuta kawai. Domin na tabbatar ko wani abu bai ratsa tsakanina na aure da shi ba, tilas ya sakeni kallon bazawara za'ayi min. Ban isa na goge tambarin zawarci a goshi na ba a idon mutane. Ga zato mummuna da za'ayi min a ce bani da hali ne. Dad'i ma samarina na baya suyi min dariya, da Allah ya k'ara, tun da ga zaton'su ni mayaudariya ce. Mak'iya na su sami hakoran yi mini dariya.
Bani da abokin fad'a Sam. Amma duk Mutum nasan baya rasa masoya da mak'iya.
Nasan kuma Kawu Sulaiman bashi da masaniyar nufin Yariman'sa. Nasan ko giyar wake yasha, bazai so nayi irin wannan auren ba. Dad'i ma naji daga baya, da yake bani da hak'k'in Yarima, gashi ya fad'a min k'udirin'sa kafin aure. Kenan na sake Samun hujjar ya kice auren cikin ruwan sanyi. Sai dai idan
Kawu Sulaiman bai ji ba. Dole kuwa yajin.
A d'akin Kawu Sulaiman, Ina rakab'e bakin k'ofa, shi ya fara magana kafin na fara,kamar yarda naso.
"Abinda kika yi, dole ya b'ataran Yarima, saboda shifa wayayye ne sosai, mai son harka ta wayewa. Ballan,tana shi da ya sabayin hira da wayayya gogaggiya mai babban a ji irin Salima, dole ki sik'eshi.Bai kamata ki rikid'e masa ga siffar da nima nasan ba taki bace Sumayya .wani daliline a ranki, kika yi masa haka ko? Sannan domin k'arin kwab'a kika yi tafiyar'ki baku ko yi sallama ba. Menene damuwarki Sumayya?".
Wannan damar nake jira.
Kawu, ni wallahi halin'sa bazan iya da shi ba. Ko a makaran'ta tsoron karo da shi nake. Abu k'arami, Sai ya tozarta Mutum. Ka gani ma da idanun ka Kawu, gaban'ka ya rink'a yab'amin maganganu, ko nauyin'ka bai jiba."
Ya katseni da hannu.
"Da Kinsan Yarima sosai, da fahimtar'sa baza ki yi wannan k'orafi ba."
Na fahimci kamar kariya kawuna Sulaiman yake bashi ma, shi yasa na fito masa da da Zancen da idan yaji, Sai ya zargeshi.
"Ancle Fa'izu fa cewa yayi aure na zai yi na wani lokaci ya sakeni Kawu, saboda cikar burin'sa. Wallahi ya fad"a kaji na rantse."
Ga mamakina wai Kawu nan ma bai damu da furucin Yariman'sa ba, da manufar'sa.
"Karki damu da abinda ya fad'a. Ikon komai da tabbatar komai yana hannun ubangiji. Zukatan bayi, suna hannun ubangiji, shi yake sarrafasu yarda yaso. Saboda haka karki damu da komai. Ke ki nufi auren ku, da kyakykyawan zato,da niyya mai kyau, da kuma kyakykywar addu'a zaki dace.za kuma ki amintu
daga a binda kike fargaba Sumayya. Ba kya gani, ko Mutum ne, ya nufeka da mugun nufi, kai kuma ka nufeshi da zuciyar alkhairi, sharrin'sa bayayin tasiri a gareka? Karki turje, kan wasu a bubuwa marasa tabbas d'in d'orewa, ki yasar da a binda yafi alkhairi a gareki, baki Sani ba. Ki dubama yarda k'addara take ta had'aki da Yarima, Ku had'u ku rabu, Ku sake had'uwa.Sannan ni da nafi kowa son'ki a yanzu, ubangiji ya jarrabi Zuciyata da son ki auri Yarima. Kuma Sam, bana k'aunar a binda zai kawo cikas a auren. Gani nake, Yarima shine kad'ai ni ya dace da rayuwarki a duniya kaf Sumayya. Shine kuma Wanda nake jin zai rik'emin a manarki ko bayan raina.
Jikina ke fad'amin haka Sumayya. Sai auren ya gabato, zan fad'amiki dalilan da yasa na nace da aurenki da Yarima.
Ban kuma damu da yana son'ki ko baya son'ki ba. Ke da kan'ki baki Sha Mamaki da ya amince da auren'ki ba? Aikin k'addara Kenan.Hakan na nufin fa, ke k'addarar cikin rayuwarsa ce ko yana so ko baya so. Wannan bai i sheki ishara ba? In da na barki, kema auren rashin soyayya zaki yi da d'aya daga cikin masu son aurenki, domin na tabbatar su suke sonki ke ba kyason su tun da kika tsaya ruwan ido.
Tun da haka ne, ki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya mana. Ki auri Yarima domin dalilai da zan fad'a miki su a gaba. Kuma ki yarda shi k'addarar rayuwarki ne, da bakisan me Allah ya shirya muku ba, ki aure shi saboda wannan. Ni dai ya fiyemin tarkacen samarin ki sau d'ari.
Domin nasan komai a kan'sa, usuli da halayan'sa. Na gani, kuma naji a majiya ta gaskiya.Amma nasan ba lallai ki yarda da shi ba har zuci yanzu, saboda kallon wasu halaye na zahiri da kike yi masa. Amma a Kwai na bad'ini da bakisan da su ba. Shi yasa kike gani baza ki iya da shi ba. Tabbas zaki iya zama da Yarima, matuk'ar kika fahimceshi, kuma kika kiyaye a binda ya keso da wan"da baya so.
Nasan ko baki gwanance ba, zaki iya koyawa zuciyarki, ki jure kiyi, Saboda kina da hak'uri da biyayya.
Kuma ki sani, idan ma kink'i auren'sa ba damuwa zai yi ba, ba kuma hak'ura zai yi ba da auren cimma wata manufa ba. Wata zai samu ya aura. To ita Watan kina zaton irinki ce mai kyawun zuciya da zata ceto shi daga yin kuskuren da yake son aikatawa, nayin auren wucin gadi? Ke kuwa nasan ko baki taimakeshi da komai ba, zaki taimakeshi, da nasiha da addu'a. Sanin kan'kine yin aure da niyyar Saki daga baya saboda wata manufa, haramun ne. Kika yi kandagarkin hana afkuwar hakan bakiyi babban aikin Lada ba Sumayya? .
Naji jikina yayi sanyi Lis, da furutan Kawu.
Tabbas Gaskiya ya fad'i , a binda nake shakkar
yiyuwar, na yarda Ancle Fa'izu zai karb'i nasiha daga gareni, ko shawara. A yarda yake ji da kan'sa, ni kuma yake ganina a raine.
Kawu yace.
"Kuma ki rink'a nuna kulawarki wurin mahaifiyar'sa, domin yana tsananin son'ta. Zan iya ce miki nan ne sirrin farin cikin'sa. Ki soma d'ana tarkon'ki tanan. Ki kula.
_Nan farin cikin sa yake_
ni na sake jaddada wannan a raina, har sau uku ma.
Da wad'an nan kalamai Kawu Sulaiman ya sake farauto Zuciyata ta a minta da auren Ancle Fa'izu. Amma fa ban daina farga ba ba, da zullumin auren. Tabbas ba domin na yarda da irin K'aunar da kawuna kemin ba, cewa zanyi farin cikin rayuwata ne baya so, shi yasa yace na auri Ancle Fa'izu.
Amma duk da haka ni fatana ke dai kar ya dawo, fushin da tafi da shi na nayi masa kaiyanci ya hanashi dawowa. Amma idan kaddara ta sa ya dawo bazan bujire ba, ba dai haka na so ba.
Babbar fargaba ta kar na kamu da son sa ma, nafi shan wahalarsa, saboda siradi ne mai wuyar gaske mace mai sunan mace ta dora idanu a kansa ta dauke ba tare da ya zabaro zuciyarta ta kamu da soyayyarsa ba. Shi yasa ban fiye son na hada idanu da shi ba, domin a kwai sakonnin da kallon ke aikewa zuciya ta da ni kadai na sani, in da shi kuma yake jin haushin hakan, ya kuma daukeshi a matsayin kauyanci na ko kallonsa ba na iyawa.
Allah gani gareka, baiwarka marainiya, ka kawo mata dauki.
Na fadi a hakan a zuciya ta ni kadai ina zaune cikin tagumi.
_Taku har kullum_
_Zainab mazawaje_
Alkalami yafi takobi... 🖋️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
*NA*
_Zainab mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer...... 🖋️
*Page* *9*
Nayi sauri na fito daga d'aki, na karb'e tsintsiyar da Baba talatu, ta soma Shara da ita. Bata Musa ba, ta sakar min. Sai da na share ko Ina na cikin gidan tas!. Na had'o Kayan wanke wanke zan'yi Sannan tace.
"Ke dai Sumayya bakison kiga nayi komai, in dai kina gidan nan."
Nace.
"To, Baba Talatu, kina da kamata kiyi aiki? aiko tsari babu. Kiyi kwanciyarki, nayi aiki nayi kuma girki, Sai dai Kawai na kawo miki kici. In dai ina gidan nan baza kiyi aiki ba."
Tace
"Koda a Kwai d'iya irin'ki mai kyawun hali, gaskiya k'alline. Kina da kyawun d'abi,a Sumayya, ga biyayya, ga tausayi. Ta Yaya kuwa bakina zai gajiya da sa miki albarka? da Fata na gari. In Sha'Allah Sai kin haifi masu binki, kuma Sai kin gwangwaje Miji na alfahari. Saboda kowa ya bud'i baki a kan'ki fata na gari ne. Addu'ar iyaye da 'yan uwa kullum bibiyarki za tayi tayi."
Tuni na saba da lafazan Baba Talatu da d'ad'a, kullum ne bata gajiya.
Tsawon kwana tara, ban sake ganin ko inuwar Ancle Fa'izu ba, ga wawtata farin ciki na Shiga sosai, a zatona ai ba zai iya dani d'in ba ne, kamar yarda yace, shi yasa ya janye.
A tsukin aka sake gayyatar k'ungiyar su Kawu sulaiman Kaduna united zuwa ga buga boll, cikin k'asar Enugu, za'su kara da club din
Ranger's.
Nan ma su Kawu na ne suka cinye. Ya bugo min waya, cike da farin ciki yana mai shaidamin, dama sau biyu muna waya da shi, bayan tafiyar'su. Nasan da Ancle Fa'izu suka tafi, amma ko zancen'sa bai yi ba, nima banyi ba.
Na fiddaran hakan, Sai ji nayi Ancle d'ina yace.o
"Ga Ancle Fa'izu zan kai masa ku gaisa, kuma kiyi masa murna, domin shi yaci mana k'wallon nasarar guda biyu. Yana dakin hutu amma na barshi yana shan mutuniyar tasa multina, bari na kai masa.
Da sauri nace.
"Don Allah Kawu ka rabu da shi, basai munyi magana ba, kace Ina yi masa murna Kawai".
Yace.
"Zai fi kyau ki kira wayar'sa ki fad'i masa. Idan baki da ita zan turo miki. Nayi d'an Jim, daga bisani nace.
"Ina jin nauyin hakan, Ancle. Naga shi ya kamata a ce yama nemi sanin lambata, ya kirani, amma bai yi ba. Shi yasa nake ganin kamar zan karyar da kaina idan na fara. Amma idan kace na kirashi, zan kirashin".
Yace.
"A'a. Rabu da shi kawai, na fad'a masa. Kinsan dai komai a kan'sa. Kinga kuwa komai ba zai shige miki duhun menene dalili ba. Kinsan dole zaki rink'a had'uwa da irin haka, amma kiyi hak'uri wataran Sai labari kinji shalelen. Ni da shi mukayi 'yar dariya.
"Gaskiya Ina son Kawu Sulaiman, har bansan adadi ba, ko misali.
Kwanan'su d'aya tal da dawowa kawuna yace min.
"Sumayya, yau Yarima zai zo. Don Allah, ki kula a komai, kar ki bani kunya kuma. Ki canza".
Nace.
"To, Kawu zan yi bakin iyawa ta"
yaji dadi.
Na samu kaina da tsala kwalliya da ado fiye da farkon zuwan'sa sosai. Less nasa kalar marun mai adon duwatsu da filawoyi ,mai kyau, da nasan sunai mini kyau, saboda kawaye na ma ko dani suke idan nayi ado dashi. Mayafi da takalmi to mach, daurin nan ya kafu a kaina kamar nike koyar da dauri ga 'yammata, bansa sarka ba tun da ba gani zai yi ba, sai fasion da bangles. Sai turare mai sanyin kamshi da humra da nasa. Nasan dai duk a banza wai talaka ya girmi sarki a wurinsa, nayi ne kawai domin jin hakan ya dace, kamar yarda na cewa kawuna zan yi a binda ya dace da duk zan iya.
Har bakin k'ofar waje da yake tsaye na isa na tarboshi, saboda Kawu Sulaiman Baba ya aikeshi ya tafi, kafin fitowata wurin Yarima.
Saboda haka kujeru na roba na Kawu na fito dasu harabar cikin wajen gidan kusa da dakin Kawu dake kusa da k'ofar fita waje, da yake a katange yake ba'a hangen na ciki.
Kamar had'in baki, Yarima Shima Man less yasa na maza, kalar pink mai cizawa. Sun yi masa wani irin kyau Kam.
Duk da naje har bakin k'ofa na tarboshi cikin sakin fuska sosai, da sakin jiki da girmamawa, Sam banga ya sakarmin fuska ba. Ya dai dubeni, a dak'ile ya kau da kai.
Abin a hali ne. Nace a hankali cikin dan tabe baki, duk da nasan ba sona yake ba, amma na dan ji ciwon kallon saurin da yayi min yayi saurin dauke kai kamar yaga abin kazanta.
Tare muka jeru zuwa mazaunin Zaman, hannun'sa cikin aljihu, yana tafiyar nan tasa ta isa da jin kai. Naga Sai wani shan k'amshi ma yake, kamar wanda aka tilasta Sai yazo wurina.
Kujerun da zamu zauna, suna fuskantar juna, kuma ni na a jiyesu ina sane a hakan. Zuciyata ce naji ta soma k'ek'ashewa, daga fargabar da nake ciki ma na auran Ancle Fa'izu, saboda na hanga gabas da kudu da arewa, ban hango matsera ba, na tserewa auran. Shi yasa Kawai na mik'a wuya, tare da nemo hanyoyin da zanbi, na k'ubuta daga tozarcin'sa da ya zama lazim.
Nasan idan na ci gaba da nuna d'ari d'ari da shi, da Jan jiki, da alkunyar nan, to kullum gumamin takaici zai ci gaba da yi, shi ko a jikin'sa, ni zai bari da ciwon zuciya.
Tare ma muka zauna. Bayan na gaishe shi nace.
"Yaya momi, da fatan tana lafiya "
Sai da ya fara da yi min wani irin salon kallo da Idanuwan nan nasa masu farauce zuciya. Amma na tabbata, babu manufar komai cikin'su.
Baki d'aya Sai naji yanayin komai nawa ya canza tashi guda. Wani irin feeling naji, da bantab'aji ba kan wani namiji ba. Gashi na jawa kaina, muna fuskantar juna bare na kub'uce, gaskiya macen da za ta iya kubuta daga tarkon shauki ko kaunar Ancle faiz ba ace babu ba, amma zai wahalar, sai dai wacce ba a halitta da shaawar son da namiji ba.
"She is doing fine. Yace cikin dan sakin fuska.
Na barota lafiya Lau. Amma yaya kikasan Momi?".
Nace.
"Tun da nasan'ka ai dole na San'ta"
Yace"A'a ni kad'ai kika sani. Ita dai kinji sunan'ta wurin Sulaiman. Any way, naji dadi da kulawar ki a gareta." Sai naga ya dan kara sakin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13