Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bawa. "Wallahi ka kyauta Ancle Fa'iz, musamman alkhairi na kyautatawa ga iyaye yafi kowanne. Allah ya saka da alkhairi, ya k'ara bud'i" Ya gyara zama daga kishin gid'ar da yayi gefena da nake ninke masa kaya. "Kema za'a baki Lada na ganin ido, kamar 'yar dubu goma, tayi?". Nayi masa murmushi "Wanda za'a ba kyauta har yana da zab'i? aiko naira goma ka bani godiya zan yi tayi, ballantana har dubu goma Ancle?". Ya kanne ido guda cikin dubana yace. "Na lura, kina da Yakanah! Saboda haka bari a k'ara miki dubu goma su zama twenty thausand. Godiya nayi ta surfawa da addu'a." Yace. "Ya isa haka Sumayya, Sai kace kyautar rai na baki?". "Ancle wai kuwa wacece Anti Husna da naji su Khairat suna yawan fad'e?". Yace"k'Anwar Momi ce, ita ce autar su. "To, Ancle Jamil fa?". Yace. "Yayan Momi ne" Na sake cewa "Maman fahad fa?" Cikin nuna 'yar k'osawa yace. "K'anwar Babar Momi ce, Kenan uwa take a wurin Momi. Na gaji Sumayya, tashi Kije ki kwanta, bacci zanyi karfe goma na dare ta gota, ina son yin sammako". Nace"Abin har da kora my Ancle?". Yace"Wanzami dama ba yason jarfa, ni me yasa jiya kika koroni daga d'akinki?". Cikin 'yar dariya nace. "Au, daga kayi bacci na tasheka nace kaje ka Mik'e a gado?". Yayi doguwar hamma kafin yace. "Wannan a bu duk mai sauki ne, idan baki son tafiya, nan d'akin yayi miki, Sai na kawo miki guzurin filo, ba Shike nan ba?" Na kuwa ce "Kawo min". Sai kuwa naga ya tashi, ya na kokarin jawo filon, nan nasan da gaske yake. Kafin ya dauko kuwa na mike da sauri na fice, in da nace masa " Sai da safe Ancle". A tsukin cikin wata hudu da aure na da Ancle Fa'iz, a bubuwa sun soma zuwa min yarda nake so. A lokacin ne kuma na sake shiga tsangwama da takura da fitintunu a cikin gidan, saboda sun fuskanci muna d'an d'asawa da Mijina, yana nunamin kulawa fiye da da. Kwana ne kawai Ancle bayayi a d'akina, amma har a binci tare muke ci, idan ya shigo d'akina. Kuma ni na gadar masa da hakan, domin ko shi kad'ai ya soma ci, Sai na zo na sashi a gaba,nima na soma ci, muci gaba da ci tare. Ko a bincin Momi ne kuwa, domin naci na yasa kullum Sai yaci nawa. Shi yasa baya cika cikin'sa ma da a bincin Momi, saboda yasan nawa d'an k'a'ida yana jiran'sa. Wulak'anci da cin mutunci muraran a ka Shiga yi min a gidan, da kare ma ba zai ci ba. Duk wani laifi idan a kayi a gidan, Momi ni take cewa. Babban a bin takaici har Sata a ka kallafamin. A zatona babu wani abu da ake sacewa, domin a d'oramin laifin sata ne kawai. sai Momi yau tace an sace mata a bu kaza, gobe ma haka, kuma tace nice ware, nice lallai zan d'auka, domin cikin 'ya'yan ta babu b'arawo. Momi ta kirani cikin 'ya,'yan ta, ban da Ancle, taci min mutunci a matsayin ni b'arauniya nayi mata Sata. Khalifa ma da Muhibbat su zageni son ran'su. Khairat ce Kawai bata tofawa, zanga ta b'ata rai sosai. Na lura bayan kirkinta, hak'uri ne da ita ainun. Muhibbat ta matsamin lamba sosai a tsukin. Idan nayi wanki, nayi shanya ta zubar a k'as. Da yake Ina wanke ma na Ancle marasa nauyi, amma bata zubar da na yayan'ta. Kunji son zuciya. Ni ke sharar gidan, amma randa Muhibbat ta so tsiya, Sai ta fizge tsintsiyar daga hannu na, ta share ko'Ina. Sharar idan ta kwashe Sai ta watso falona. Na rink'a dauriya, Saboda Kawai bana so K'orafi ya fara b'ulla daga bakina wurin Ancle ko wani nawa. Sannan Zuciyata tayi nisa a son Ancle Fa'iz, banason a binda zai haifar da sa'in sa tsakanina da kowa nasa . Zaman aure na mutu ka raba na k'uduri yi da shi, iya yina. Komai nawa na Kayan kichean, ni da Muhibbat muke amfana, musamman idan tayi bak'in k'awayen'ta, komai na kichean d'ina za'tayi facaka da shi. Filet filet da kofuna na k'arau ta yi amfani da su, ta zubemin a waje babu wankewa, ta kuma fasa na fasawa da gayya, duk dai Sai an cuzgunamin nayi magana, an zagi ubana. To, ni kuma Sai nayi lub, kamar banji ciwo ba. Kayan kichean d'ina duk ta farfashe k'arau d'in, ban dai tanka ba, na k'yale. Sun Sani a kwana sosai Muhibbat da Khalifa. Wulak'anci salo salo, zagi da Habaici. Hannune kawai basa sawa su dakeni. Sau d'aya nayi wa muhibbat magana da ta fasamun fulas d'in shayi, da shi kad'ai ya ragemin, ta kuma kwashemin drink's na Friedge da nake tanada saboda Ancle.da tayi bak'i. A binda ya fito daga bakin'ta shine. "Ai naga, ba' daga gidan uba, akazo da drink's ba, yayan mu ya saya, aikin banza shishshigi babu kwarjini, diyar matsiyata ke har wani kaya ne ma dake na kichean da zakiyi fariya a kai, kuma komai na ci ko sha ai yayan mu ke sayowa ba daga gidan tsoho a ka kawo ba". Raina ya sosu, tamkar na fallamata mari, amma na daure zuciya, saboda ubana da baya raye da ta tsomo a ciki". Tabbas yayanta na sayo komai, amma wanda duk ta kwashe ni na Saya. Kawu Sulaiman yana aiko min da kud'i a kai a kai, kuma yawanci, wurin yiwa Yayan su d'awainiyar sa kai na, suke tafiya. Sauk'inta bana yini a gidan,saboda makaranta, ba domin haka ba, a bin yawa zai min, wai shege da hauka. Ranar a sabar bani da lacture, banje school ba. A kayi dace nayi bak'i kuma.'yan uwan ummata da suke uba d'aya, baba Maryam, da baba Hasana. Tare na had'a mana a binci mukaci, Sai yaran su, dana ware musu a faranti guda. Ancle Fa'iz ne ya shigo da a zahar da ba sabon'sa ba. Ina hangen sa ta taga, saman Momi ya haye rik'e da poly bag k'arama, irin ta take a way. Muna hira da bak'ina ya shigo falon da sallama, baisan da bak'in ba, Sai da ya shigo. Bayan sun gaisa, na gabatar masa da su suka gaisa a mutunce kuwa. Sai yace nazo yana son ganina dama tsintsiya ce a hannuna, zan share a bincin da yaran suka watsar, sai baba Maryam tace naje Kiran mijina ta share. Nabi bayan Ancle Yana tsaye a d'akin nasa ya rungume hannu a k'irji, ya jingina da bango, kamar wani a bu yana damunsa na fuskanta. Nace "Ancle yau ka dawo da wuri Amma " Fuskar'sa babu walwala yace "Eh!" Yayi shiru. Sai daga baya Yaci gaba. "Momi ta dawo dani,saboda waya tayi min wai na taho mata da take a way yunwa take ji. Nace mata yanzu Momi a binci Sai ya gagareki a gidan bayan da a kwai komai? Saboda bana son dawowa, Ina kan wani a bu mai muhimmanci, amma Sai da na barshi, saboda tace min su Khairat dama ke dafa binci su bata, kuma duk sun tafi unguwa tun safe . Kuma gashi likita yace lallai Sai taci a binci sosai kafin tasha magungunan ta, na larurar rashin lafiyar da take ciki." Nan na dubeshi nace, Dama Momi bata da lafiya?". Ya dubeni galala. "Wace irin tambaya kike min? Waye baisan MomI bata da lafiya ba, kwana biyu? duk da tace kikan jima bakije kin gaisheta bama, amma ai za'kiga ta fad'a kwana biyu". Wannan abu ya Sosa min rai, shi yasa kika ga na kasa juriyar a jiyewa zuwa wani lokaci. Domin da nace Momi tayi miki magana ki bata a binci, tun da kina gida, Sai tace bata buk'atar a bincin ki, tun da baki damu da ita ba. Tunda ta kwanta jiyya baki tab'a yi mata sannu da jiki ba, ba kya gaishe ta ma. Kuma da kina bata a binci, kika daina, Sai dai kiba almajiri. A binda ciwo a ce Momina ta rasa a binci a gidan nan Sai da na dawo, amma ga bak'inan su sunci, har sun zubar". Tun da nazo gidan raina baitab'a b'aci ba irin ranar. Duk a binda suke yi min, ni banyi k'orafi ba Sai Sai su? Kuma gashi ya Shiga cikin su, ya yarda tun da yake tuhumata. Na had'iyi yawu da k'yar . "Nifa ban fahimci zargin nan da ake so a lik'amin ba. Sam ni bansan Momi bata da lafiya ba. Waya fad'amin? Kuma Ina gaisheta, ni banga alamun wani rashin lafiya ba. A binci Ina bata ta dai naci tace bataso, to yaya zan yi. Na sake daukar zafi saboda na fuskanci Ancle yana bayan su, yarda ya daure fuska yana yimin wani kallo a sangarce. Kuma a binci ma ai cewa a kayi nayi iya cikina, nifa a ka ware. Kuma ai ba'a bani umarnin ma bawa Momi a binci ba, iya kaina a kace na dinga dafawa, ina dalilin da zaa dawo a na zargina kuma. Ni fa nasa kaina nake bawa Momi a binci". Take naga ya fusata ga rashin zato na. "Har wani alfahari kike na wai ke kika sa kanki kika ga damar bawa Momi a binci? Sai da kika ga dama? to kiga kuma hagu. Kar ki sake bawa Momina a binci, umarni na baki Shima. Ki dafa iya cikin ki na sake fad'a. Ki Sani, ko zan iya hak'uri a kan wani a bu, banda a tab'amin uwa. ko wanene bai isa ba wallahi." Take zuciya tazo min iya wuya. A fusace nace. "Girkin ma ai ba dole bane. Domin iya cikina zan wahala? nama daina dafa komai, kome na samu ya fad'o bakina ya wadatar. Kuma Allah shine Sha'hidi a kan kome nene gaskiya. K'arya ta shekara k'arya. Gaskiya na makwafinta". Ina fad'in haka na mik'e nayi ficewata. Na fusatashi sosai na gani kan fuskar sa, amma Sai naga ya gaza cemin komai, face bina da kallon Mamaki, har na fice.Tun daga ranar na rufe kichean ruf, ko ruwan tea bana dafawa. Sam bana karyawa da safe, ko ina gida. Abinci Sai a bu mai ruwa ruwa,Sai ciye ciye Sama Sama. Amma banacin gaskiya a bincin kirki a cikina. Ga damuwa da na d'orawa zuciyata. Kuma na d'au fushi da Ancle Fa'iz ko falonsa bana zuwa. Da safe yana shigowa wurina Bayan sallar a suba. Bayan na gaisheshi, bana sake ko kallon sa ballantana na tsinka masa. Shima ganin babu fuska, Sai ya ajiyemin kud'in da yake bani, batare da sake kulani ba. To dai banga ya d'au fushi kamar ni ba, yarda na fuskanta. Komai ya sayo zai kawomin nawa d'aki ya a jiye. baya cewa komai, Sai ya fita. Ni kaina banyi zaton Ina da zuciya ba, Sai da aka kaini bango. Dama wasu sunce, mai hak'uri bai iya fushi ba. Ba iya Ancle Fa'iz ba na d'au fushi da shi ba, duk gidan ne. Ji nayi an kai ni gargarar da bazan kuma d'aukar raini da wulak'anci ba. Momi Kawai zan iya d'agawa k'afa, albarkacin Ancle Fa'iz da kuma darajar haihuwa, tun da ta haifeni. Amma ita kan'ta Momi taga canji a wurina. Kullum zan je na gaisheta, Amma fuskata babu walwala, da rawar jiki na biyayya da nake yi mata. Domin da kullum naje gaishe ta, Sai na tambayi ko da wani aiki da zan yi mata. Bayan fa Kusan aikin gidan gaba d'aya da na kallafawa kaina, kamar mai aikatau. Momi ta ban Mamaki da tace wai bana zuwa gaishe ta, da bata a binci, da dubiyar rashin lafiyar da ban San da ita ba. Gaba d'aya zuciya ta ta karkata wurin yarda da cewa Momi yak'i take yiwa Salima bayan idonta. Domin Khairat ce ta sameni rannan da babu kowa a gidan bayan sallar magariba, tazo d'akina tace min. "Matar Yaya, wallahI ki k'ara rik'e mijinki da kyau, domin Kusan kullum Sai Salima ta yiwa Momi waya. Rannan hands free Momi ta manta tasa, naji Salima tana yiwa Momi magiya kamar zata yi kuka, Wai tana bala'in Son Yayan mu, shi yasa baza ta iya zama da kishiya ba, Wai Momi ta taimaka mata. Saboda Salimar ta cewa Yaya, ya sakeki tun da saboda ya sameta ya aureki, kuma tun da Momin ta ta sauko ma tace ko yaushe yazo a yi aure. Amma Sai Yaya yace mata babu ruwanta da zancen auren sa dake, tayi gefe da shi. Kawai tasa himma a kan tsara musu zaman farin ciki da Soyayyar da za'su shimfid'a, kafin isowar auren. Ita burin Salima fa Kawai Yaya ya sakeki kafin auren ta da shi. Shi kuma yak'i bata amsar yiyuwar hakan. Momi hak'uri ta bata dai, tace tabar komai a hannun'ta zatasan yarda za'ta b'ullowa komai, saboda yanzu binsa take yi a sannu, saboda har yau bai gama hucewa ba, da a binda maman'ta tayi masa. Kuma Khairat ta ce min, taji Momi tana fad'awa Ancle Fa'iz wai ya d'auki matakin plannig, wato tsarin iyali a auren ku, saboda batason ya haihu da ke kafin zuwan Salima. In so samu ne ma ya sallameki yanzu, tun da kwalliya ta biya kud'in sabulu. Amma Sai cewa Momi yayi. Momi nasan a binda nake yi nima name ya kamata nayi a lokacin kuma da ya dace, kusamin ido". Momi bataja musu da shi ba, duk da bata fahimce shi sosai ba. Haka za'lika nima ban fahimta ba. Amma fatana kar burin su ya cika a kanki Anti Sumayya. Wallahi ni nafisonki da Anti Salima." Wani irin k'aunar Khairat ya k'ara mamayeni. Rungumeta Kawai nayi, nace ."Khairat Ina k'aunarki, fiye da kowa a gidan nan. Allah ya ganar da su gaskiya, su san ni ba a bokiyar hamayya bace, face masoyiya ga Ancle, mai son sa da son ci gaban'sa, da su baki d'aya. Ta kuwa ce. "Amin". Murmushi nayi, da a ke gudun, na samu ciki na haihu da Ancle, to duk Ina tunanin su ya tafi? Ko jituwar da suka ga munayi da shi a tsukun, suna zaton komai yana tafiya na aure tsakanina da shi? da sun San komai nasan Momi bazata yi a sarar yawun bakin'ta ba. Tun da Khairat ta fad'amin maganganun nan, suke tayi min yawo a rai. Tabbas k'wace goriba hannun kuturu bazai yi wuya ba. Za'su iya iya rabani da Ancle Fa'iz nan da nan, tun da ko tubalin ginin dasa sabo da k'auna da shak'uwar da nake fad'i tashin yi kullum, bai yi nisa ba, ballantana yayi k'warin da Sai anyi gwagwagwa da shi, kafin a rushe. Shi yasa wata zuciyar ke min shelar cewa, Kawai na shafawa kaina lafiya da Ancle, na saddak'ar, nasa rai da isowar cikar wa'adin auren mu, na rungumi k'addarar shiryawa zaman zawarci, da tunkarar sabon wani auren da bazan tab'a so ba, Sai dai nayi a larura. Saboda manyan matsaloli ne masu wuyar warwaruwa ke ta tunkaro ni cikin aurena da Ancle Fa'iz. Ko ga na Momi Kawai ya isa na sare. Saboda naga k'iyayyar mai zafi ce, tunda har ba'ason had'a jini dani. Lallai Khairat, tana k'aunata sosai, tun da ta iya fad'amin sirrin mahaifiyarta. Na tara bokiti bakin fanfo zan debi ruwa zan Shiga band'aki nayi wanka, saboda wani zafi da ake surfawa, Muhibbat ta taho da sauri da nufin angijeni tayi saurin shigewa saboda neman fitina, bayan ta baro wani band'akin a bayanta. Batasan a yarda nake ji da tsiya ba, kowa ya tunkaroni a lokacin karawa za' muyi. Shi yasa banyi jinkirin angijeta ba,iya k'arfina, Sai gata a k'asa wanwar . Ta kuwa Mik'e da masifa za'ta soma aunamin zagi, yarda ta saba. Nace cikin d'aga murya. "Ahir. yarinya. Karki d'auki kawaicina a matsayin gazawa. Kuma karki d'auki hak'uri na a matsayin tsoro. Idan har ke kin cika d'iya ta halas, to ki kai ga jikina, domin fad'a na baki na matsorata ne." Sautin murya ta da yayi Sama, a she Momi taji yo, Sai ta fito, haka Khairat, suka zubo Mana idanu daga saman bene. Muhibbat tayi min wani matsiyacin kallo, cike da mamakin yarda na rikide tashi guda, don duk iskancin da take min sunkuyar da kai nake yi na wuce. Tace cikin tafa hannu. "Samun wuri, Wai d'an wake a hotel. ke bora, kuma 'yar tsaron k'ofa, har kina da bakin magana? har da fiffik'a? to ba za ta kaimu da nisa ba, zakisan matsayin ki idan kin manta. Bari yaya ya dawo." Na sake hada idanu da Momi sai kuwa na sake daga murya a fusace. "Yazo din, me ya isa yayi min, datse min numfashi, ko duka na zai yi, don bazan daku ba wallahi, iko daya ne dai cal zai iyayi kololuwa, shine ya sakeni, kuma na shirya tsab, tun da ba autan maza ba ne. Gari da yawa ai maye baya cin kansa". _wasa farin girki, har yanzu ba a shiga farfajiya na rigin gimu da manufofi da soyayya da dadin wannan littafi ba, duk maison ya kashe kwarkwatar idanun sa, to ya turo_500 kacal 👌🏻 Ta wannan a count no👇 8025527956, Opay. Zainab ilyas _Shaidar biya ta wannan number ta whattap_. O9096409711 _Zainab ilyas mazwaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab ilyas mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_.... 🖋️ *Page 18* Furutaina na fahimci sun tunzura Momi, saboda gabanta nake tijarar, kuma tasan na ganta. Kuma tasan idan 'yarta tayi sake muka dambata, Sai na lallasata sosai, saboda na fita siffar k'arfi ma a ido. Ita 'yar kyalan kyalan take. Bata da cikowar komai a jiki na cikar surar mace. Kyan iya fuska yake, Sai farar fatar abin alfahari, irin na 'yan uwanta, idan aka cire Khalifa. Momi tace cikin daga murya da fusata. "Karki kulata Muhibbat. Ai Kare baya yi Maka haushi ka rama, Sai Ku zama d'aya. Ko a usuli da nasaba kun bambamta, ba kya daka ta tata ba. Kinsan kuma harbi ga d'an kunama gado ne." Na d'aga kai na kalli Momi a zuciye, na kau da kai, Kenan ta ramawa 'yar ta. Darajar haihuwa taci, da tazarar shekarun da ta bani, gashi na samu tarbiyyar girmama manya, da ta gane ita ma shayi ruwa ne. Domin sun kaini k'urewar bango. "Momi, ni Mamaki take bani fa! wai bora kuma 'yar jiran k'ofa keda a bin cewa. A cewar Muhibbat. Na Doka mata kallon k'ask'anci. " Ke shashasha, ragowar yunwa, A littafin maganganun dake bakina wallahi , shafin farko ma ban bud'e ba. Zan kuma karance miki shi, in dai kika ci gaba da ja dani. Matsoraciyar Kawai, Wacce a fad'an baki tafi kauri". " Ina kai nan, Sai muka had'a idanu da Khairat. Murmushi tayi, dake nunin taji dad'in 'yancina da na karb'a.Dole idan ba'a kiyaye ni ba, za'a sassauta kuwa. Nan na wuce band'aki na bar Momi da Muhibbat suna ta yada maganganu. Na fahimci na had'a musu zafi, bayan mamakin da na basu. Basu tab'a zaton zan iya haka ba. A na Kiran sallar Isha'I na jiyo sallamar Ancle Fa'iz ya shigo. Nasan Kiran'sa a Kayi a waya, domin baya dawowa dai dai wannan lokaci. Nan ma saman Momi ya wuce kai tsaye. Ina zaune rik'e da kofin flastic, Ina shan corn flake's, domin shine ire iren kalar a bincin da na komawa, mai ruwa ruwa. Sati biyu kenan da k'untatawa kai na da nayi na k'in yin girki. Saboda b'acin ran da nake ciki, bayan rashin a bincin kirki, duk na soma rama, k'asusuwan kwarin wuya na sun soma yi min mirjani. Ga bak'i da na soma yi. Ancle ya shigo min da sallama a sanyaye jikin sa naga. Saye yake da rigar kakin jin's riga mai gajeran hannu da wandonta na jin's. Gaban rigar manyan mab'allaye ne, ya b'alle biyu na saman a na hango k'irjin sa kad'an.Kayan jajaye ne masu duhu, shi yasa sun k'ara haskaka kyawunsa da hasken fatarsa. Kyawun da suka yi masa bazai misaltuba. Tamkar d'an bak'on balarabe a k'asar Hausa. Bantab'a ganin yasa kayan ba. Ta yiyu, sababbine ko a jiyayyu. Ranar ko sannu da zuwa na kasa yi masa,saboda nauyin damuwa da ya rik'emin Mak'oshi. Tun da muka samu Sab'ani da shi, dama gaisuwa Kawai ke had'ani da shi, ko sannu da zuwa, idan ya dawo ya shigo ya a jiyemin nawa a binda ya sayo na mak'ulashe. Ancle Mutum ne mai sakin hannu sosai na sayo wannan sayo wancan na wasa baki, in dai yana da shi. In yayi kud'i za'aci dad'i kam ba kad'an ba. Ya zauna kusa dani kan kujera. Na basar na ci gaba da shan corn flakes d'ina kamar ban San da tsirar sa ba. K'iris Kawai nake jira, a yi b'atacciya. Yace "Sumayya!. Na amsa da k'yar. "Wai maye yake damunki ne? gaba d'a ya kin canza, kan d'an a binda bai kai ya kawo ba. Ban San ki Sam da halayyar fishi ba, ko rigima, ballantana fad'a. Ina kika a ro wad'an nan d'abi'u? " Duk a sanyaye naji yana furutan ma. Na fusata nace. "Ba'arowa nayi ba ma, Karb'owa nayi kyauta, domin na ceci kaina Ancle." Yayi d'an jinkirin magaba, domin jinjina furutaina. "O k, naji. Yanzu fad'amin a binda ya faru a yau". "Au, ba'a fad'a Maka ba?" Yace. "Ko an fad'amin a dalcine naji kuma daga b'angarenki ko?". Nayi yak'e na takaici. "Duk a binda akace Maka nayi gaskiya ne Ancle. Bani da kirki. Duk d'abiar da kasani ta banza, toni gwanace. Matsalolin duk da suke faruwa a gidan nan, nice sila, tuntuni fad'a Maka ne ba'ayi. Saboda haka babu wani bincike da zaka kumayi, na kuna kuma yanzu babu wani kauri ko hayaki da zai tsoratani, kazartar min da hukunci Kawai, shine magana". Kuka ne ya nunamin fin k'arfi, na aibata kaina da nayi, domin na yarda k'wallon mangwaro na huta da k'uda kawai. Nayi k'ok'arin Mik'ewa na shige d'aki, Sai Ancle ya rik'e hannu na, domin dakatar dani. Iya k'arfina da bansan ina da shi ba, nasa kuwa na fizge, saboda a tunzure nake sosai nace. "Ni ka rabu dani, Ancle ka zartar min kawai da hukunci, shi ya rage kawai". Na fad'a d'akin ina sheshshekar kuka. Baki bud'e na bar Ancle Fa'iz, domin furutaina sun girgiza shi ainun. Ina Shiga d'aki Sai gashi ya biyo ni. Na hau kan gado, Shima ya hawo. Ina ja da baya, yana biyoni. "Wai ka rabu da ni Mana. Bana fad'a Maka gaskiya ba? Ka k'yale ni Ancle" Cikin kuka nake fadi. Nama rasa a binda ya hanashi yin zuciya a lokacin ya rabu dani, domin mai zuciyar ne. Sai da na kai k'arshen gado, na hak'ure, saboda ya kureni yarda bazan iya zullewa ba kuma. Ga Mamaki na, sai yayi dan murmushi ya d'ago fuskata, da hannayen'sa ya shiga sharemin hawayen fuskata da wani tisue da ya fito dashi daga aljihunsa. A hankali kamar mai rada ya soma cemin. "Ban yarda ke mutuniyar banza bace, mai kuma mummunan halaye, banyarda ba Wallahi, duk da kinyi ik'irari da bakinki. Duk in da kika je kika b'ata kanki, zanje na k'arya taki nace karya kike yi. Zan baki Kariya sosai, na kuma wankeki, nace Sumayya yarinyace me ladabi, mai kirki, mai hak'uri, mai addini, tayi zarra wurin yakanah da kamun kai.". Furutan sa sun zo min a ba zata. Ban tab'a sanin shi d'in ya tsaya nazarin sanin halayena ba, har ya karance su tsab, a tsawon watanni Kusan biyar da auren mu. Jikina yayi sanyi, kuma yayi laushi lub'us. Har lokacin hannun sa yana rik'e da hab'ata fuskata na fuskantar tasa dab yace. "Bansan me ya hargitsaki ba, ya kuma tunzuraki, har kike k'agar halayyar banza kike danganta su, da kanki. Me zai sa kiyi haka? haba my Sumy." Baki d'aya lakar jikina ta mace. Sunan da ya k'irk'iran min lokaci d'aya, yayi matuk'ar karb'uwar jin dad'in sa da tasiri a Zuciyata, wurin hab'aka k'aunar Ancle a zuciya ta, da da nake k'oK'arin ya kicewa da k'arfi, saboda wuya, da fitintinu, wani irin yanayi na samu kaina a ciki da bazai misaltu ba, game da irin yanayin da muke ciki a lokacin da Ancle, domin numfashinsa ma inajin saukarsa kamar ni nakeyi, bai kuma saki hannuna ba, da habata da ka kaita dab da fuskarsa ba yana magana. Cikin sauk'i Ancle Fa'iz yajanyo ra'ayina na fad'a masa a binda ya faru, Amma banda na can baya. Ko sunan Momi ban kamaba,domin matsayinta gareshi, bazan iya cewa tayi min wani a bu ba. Fushi sosai na gani kan fuskarsa, yace. "Banyi Mamaki ba, Muhibbat zata iya fiye da haka. Dadai Khairat ce, shine zanyi ko kwanto, domin shigen halayyarku d'aya. Muhibbat

Chapter 11 of 13