dad'in a binda yayi Miki, haka Kawai daga had'uwar k'addara Sai ki Zak'alk'ale? Wannan halin zub da ajine Nuriyya. Nayi mata tatas, tayi lub. Amma fa an d'auki lokaci in dai mun had'u Sai tatada Zancen wai taji ciwon rabuwar mu da su babu a direshi.
Rannan kuma muna hira tacemin.
"Kinsan me Zuciyata ta ayyanomin yanzu?"
"Ta ina zan Sani,baki fad'iba.".
Nace da ita.
Tace"Zuciyata ke sak'amin, Ina ma ina cikin tafiya, na had'u da miskilin gayen nan, ai ko bai kulani ba naci riba."
Nace.
"Kin Shiga uku Nuriyya."
Tace"A wani dalilin zaki kiramin musifa".
Nace "Ai kuwa kin shiga cikin ta yanzu, tayaya za ki kwallafa rai da mutumin da ko kallo baki ishe shiba? dama daya hand some din guy bakin kike so, sai ince dan dama dama, don zai iya sauraronki ko baya sonki, saboda naga yana da saukin kai shi gaskiya. Ke ruwa ma ba saan kwando bane gaskiya daga yanayin ganin samarin nan kinsan ma ba saan nin yi ki ba ne, sun kuma kama dahir, kawai kisa hakuri".
Ta harareni kawai taja tsaki. Nayi zaton za ta kuma tankawa na kare mata tanadi, sai tayi shiru. Domin gaskiya haushin yarda take zubar da aji nake, gashi sun nuna mata a aikace na ba ma gabansu, amma ta rufe ido ta kulle tunani, wai bata dau haske ba, saboda son zuciya kawai.
Kunji wannan.
Daga bakin alkalamin....🖋️ Zainab mazawaje muje zuwa
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
*By*
_Zainab mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️
*page 6*
Tun daga lokacin na fahimci Nuriyya kamar tayi fushi da furucin da nayi, don naga bata kuma dauko min zancen ba, a raina nace ya dai fiye miki hakan, kisan ciwon kan ki da mutuncin kan ki gaskiya.
Daga lokacin, na samu lafiya ta dai na yi min Zancen, amma bansan cikin Zuciyarta ba ko tana sak'awa.
A daren ranar dai Alhaji Rabi'u yazo ya matsamin lamba na sai na bashi dama ya turo iyayen'sa Yasan matsayin'sa. Sayayya fal yayi min kuma. Yace ya kuma gaji, ko yin ko bari yana son sani. Nace ya bari, zanyi magana da kawuna.
Kafin ma na fad'awa Kawu Sulaiman, da Nuriyya k'awata tazo, ta rikirkita min lissafi.
"Wallahi ni nafi miki Sha'awar Alhaji Rabi'u domin yafi Usman kud'i . Alhaji Rabi'u yafi Usman shekaru da gwagwarmayar sanin wahalar aure da juriya da sanin darajar iyali. Kefa kika ce zaune yake da matarsa lafiya, gashi kince yana yabon matar Sama. Mai wannan ai Sai namiji na gari. Shi kuwa Usman baki da misali a kansa da zaki samu tabbas, Sai kin Shiga zaki gani. Kuma kin tab'a cemin kin tsani kiyi aure ki fito a rayuwarki, ba kyason zawarci ko aure sau biyu. Tun da haka ne, dole kiyi taka tsantsan wurin aure, kar Kibi son zuciya. Tun da su duka sun yarda da karatunki da aiki da zakiyi to kar kibar Alhaji Rabi'u, shi ya dace dake. Kinsan maza irin su manya suka auri budurwa, ba k'aramin tarairayarta suke ba da nuna mata soyayya."
Na Shiga rud"ani, domin cikin maganganun'ta a Kwai a bin dubawa ko ba du ba. Bata gushe da yi min hud'uba ba, Sai da ta cusamin auren Alhaji Rabi'u, naji shid'in kawai zan aura. Shi yasa banji fargabar sake tunkarar Kawu Sulaiman da Zancen ba, duk da nafa kai masa zancen Usman yace na saurare shi. Idona ya rufe.
dubana yayi cikin 'yar fusata.
"Wai ke Sumayya me kike nufine? Maza biyu za ki aura, ko menene k'udurin'ki?"
Na duk'ar da kai zan soma magana ya katse.
"Fad'amin wakike so da Gaskiya,Alhaji Rabi'u ko Usmanu?".
"Alhaji Rabi'u." Nace.
Jinayi gaba d'aya ya k'aryatani.
"K'arya kike yi, Shima ba son'sa kike yi ba."
Ni kuwa nace me zanyi, idan ba kallon'sa ba.
"Tun da kika tsaya ruwan idanu tsakanin Alhaji Rabi'u da usman, ya nuna su duka ba wani so na hak'ika kike musu ba. So guda d'aya ne tak! Kuma ba'a yin ruwan ido a cikin'sa. Da kina son Usman, ba zaki dawo daga baya kice Alhaji Rabi'u kike so ba. Kuma da Alhaji Rabi'u kike so, tun farko shi zaki zab'a. Nafi zargin cusa miki ra'ayin'sa a kayi.
Ya sauke numfashi a hankali, ya dubeni.
"Bazaki auri d'aya daga cikin'suba, domin duk basu dace dake ba. Wanda ya dace dake a dabi'ance zai zo nan kurkusa in Sha'Allah. Zaizo, kuma kafin yazo zaki ga alama ta sanarwa ko nuni na hannunka mai sanda kam idanu na zuba masa kawai.
Cike da Mamaki na dubi Kawu, amma kaina ya d'aure ban fassaro komai ba, a fuskarsa ko a kalamun'sa.
"Zan sallami Usman da Alhaji Rabi'u da kaina. Babu ke babu su, ko a hanya, kinji na fad'a Miki. Na sake jadda da Miki, ko ki yarda ko karki yarda basu dace dake ba. Bayan ba son'su kike ba, kuma bani da garanti a kan'su. A ido kawai nake ganin'su, tunda babu wata huld'a da take Shiga tsakanina da su. Ina so ki darje Miji Sumayya ko domin maraicinki kinji."
Sam banji dad'in hukuncin da Kawu ya zartar ba, don dai yafi gaban nayi jayayya da shine, matsayin sa ya wuci nan nesa. Amma na k'alubalanci tunanin'sa. Usman da Alhaji Rabi'u duk babu na yadawa wurin yabo. Sun Sha d'awainiya dani da Zaman jirana na shekaru, amma tashi d'aya a koresu? da wani ido zan kallesu? Wani zargi zasu yi min? ta ina zan maida irin'su? Wani lokaci kuma zan d'auka Zaman jiran wanda zai dace dani a d'abiance, bayan shi hali ba'a goshi yake ba da za'a gani a tabbatar. Abin a lullub'e yake. Addu'a ce kawai na tabbatar za tayi jagora
Ta ina zan lalubo wanda ya dace dani, amma ba hasashe, ko zato ba.
Na Shiga damuwa har wayewar gari, amma ban bari kawu ya fahimta ba, saboda ina jin nauyi da kunyar yasan hakan. Domin bani da kamar sa a duniya. Bana iya had'a kaunar'sa da ta kowa. Abinda yayi min a rayuwa, cikin family d'ina kaf babu Wanda yayi min rabi rabin'sa. Ya cancanta da nayi masa biyayya a komai da bai wuce k'a'ida ba, wato haramun. Da wannan dalili nayi ta jinyar damuwar Zuciyata a b'oye Ina had'awa da addu'a har komai ya sassauta a raina. Ban sake fita zance wurin Usman ko Alhaji Rabi'u ba. Sun dai daina zuwa, bayan d'ayansu kowan ne da yazo sau d'aya Kawuna Sulaiman yaje ya gana dashi. Bansan yaya suka k'arke ba. Ni dai nasan, duk Sanda tsautsayi ya had'oni da su a hanya, zan sha kunya, kamar na nutse. Bana fatan zuwan wannan rana ni Sumayya.
Bayan watanni har biyar da korar Usman da Alhaji Rabi'u, hak'urina ya soma gazawa saboda Wata uku da suka wuce a ka soma gwab'amin da Zancen aure. Wai naki aure, duk sa'oina suna d'aki da yara d'aya ko biyu . Wai na fake da karatu. a Kawu na a ke jefa k'orafin, Wai shi ya huremin kunne na tsiri karatu domin kar nayi aure nayi nisa da shi. Saboda kowa ya lura da irin k'aunar da yake nunamin. Kuma a binda ya jawo matsalar, duk cikin dangin iyayena na kusa babu mai karatun jami'a mace. Kakana ma Sai da ya gwab'amin magana cikin hirar wasa yace, Wai na kusayin kwantai, saboda na tsaya ruwan ido da buri. Kakata Hajiya Mariya ita kullum naje k'orafin Kenan na aure. Itama kan Kawu Sulaiman ta d'ora laifin. Wani lokacin Hajiya Mariya fushi take yi sosai har takance. "To ya jik'aki ya shanye mana, tun da bayason kiyi aure. Na kan sake kunnata nace" Tsohuwar nan kin fiye rigima. Kinci zamani irin naki, ki barmu muma muci irin namu Mana, kai fa ya waye yanzu, karatu a ke fara zurfafawa kafin aure. To nan fa Sai ta balbaleni da fad'a har korata ma take yi tace kar na k'ara zuwa mata gida.
Amma Sai na koma. Baza'a rabu ba Sai mun kuma yin fad'an. Sai dai idan bata matsamin da zancen aure ba. To ban san me zasu ce ba ko zasu yi kuma, idan suka San ya kori masu zuwa neman aure na. Duk da hukuncin nasa Sam bai min dad'i ba nima, bazan iya suka ko tona komai na Kawuna saboda bana so aga laifinsa.
. Ina tsananin k'aunar sa, bazan iya b'ata masa ba Ina sane.
Maganganun sun dameni lokacin da Usman ya aikomin da wasik'a a ciki yace wai naci a manar sa Ina sane, nasan wani za'a bani amma nayi masa alk'awarin aure. Ban ko bashi amsa ba na rabu da shi, saboda nasan kome zan fad'a masa bazai yarda ba. Alhaji Rabi'u kuwa, ban sake jin d'uriyar'sa ba shi.
Rannan Ina zaune a tsakar gida, Baba Talatu ta tafi unguwa. Ranar bani da karatu, a hutu muke. Komai ni nake yi dama in dai Ina gida, kuma ni nake sa kaina, bawai Baba Talatu ke cewa nayi ba. In dai ta ita ne wanke wanke Kawai zanyi da sharar tsakar gida. Na gama komai, Ina zaune, Kawu Sulaiman ya shigo, ya sameni zaune nayi shiru .
Ya jawo kujerar k'arfe da Baban'sa yake zama, ya zauna gabana d'an daura dani.
"Sumayya a Kwai wani a bu da zakiyi yanzu?"
Nace"Babu Ancle. Sai girkin dare, kuma Sai yamma sosai zan d'ora,tun da mai sauk'ine.Wannan damar nake jira da baki komai, kuma babu kowa Mu tattauna Wata magana dake. Kisa Nutsuwar nan taki da nasan ki da ita ki saurareni, ki kuma fahimceni 'yata".
Kafin nan zan baki wani d'an labari da zai zama shine sharar fage,na a binda zamu tattauna."
"Kinsan ai Yarima ko? .
Na dubeshi da hanzari, Sai ya zarce da cewa. Ko daya ke, Kinfi ganeshi da Fa'izu. Zan baki labarin'sa a tak'aice, bazan b'oye Miki komai ba, saboda gaskiya da gaskiya ce za'suyi aiki.
Yarima haifaffen garin nan ne, amma a salin'su 'yan maiduguri ne.
Mahaifiyarsa sunan'ta Suwaida. Kuma k'abilar shuwa Arab ce . Baban'sa kuma babarbare ne, sunan'sa Alhaji Bukar, amma asalin'sa bafulatani ne na sokoto.
K'annen Fa'izu uku, biyu mata Sai namiji dake bi masa Khalifa. Tsiran'sa da Khalifa,shekaru uku yace min. Bad'an masu kud'i bane Yarima, ba kuma talakawa bane can. Sai sa Sai sa. Amma dai yawancin d'awainiyar gidan Yarima keyi, musamman na kannensa mata
Yarima d'an boll ne sosai, domin kuwa makarantar school a cadamic yayi dake cikin k'asar Ghana kuma cikin birnin Ghana ACCRA.
Suna koyar da boll ne da karatu. Tun tashin Fa'izu da son buga k'wallo ya taso, tun yana k'arami, har girman'sa. Ya kuma samu sa'a a cikin harkar, ko nace yana kan samu. Iya boll d'insa yasa wani a gent dake hayowa 'Yan club a turai k'wararrun 'yan boll, yace zai kai shi spen wurin 'yan club d'in bacelona, ko real Madrid dake k'asar turan ta spen su sayeshi. Saboda ya iya boll sosai Sumayya. Duk fita Sai yaci mana cup. Lamba sha d'aya yake bugawa, Kinsan sune 'yan gaba, amfi ji dasu. Da yawa ma club Sukan gayyaceshi ya buga musu boll idan za'su gasa. To sai yasa kan'sa dai yake zuwa, Kinsan halin Mutumin.
Yayi harkar teaching na wani lokaci da yasa kan'sa. Amma fa ya watsar yanzu, saboda harkar boll tasha masa kai, kullum Samun ci gaba yake yi a cikin'ta.
Burin Fa'izu tafiya spen kawai, amma har hanzu egent d'in dai bai nemeshi ba."
Ni kuwa na kada baki nace.
Ancle, mai yasa sai yaje wata k'asa?".
Yayi a garin'su mana."
Yayi 'Yar dariya.
"Sumayya ai fitar sa k'asar turai shine ribar wahalar buga boll d'insa. Domin kuwa can ne ake Samun kud'i na fitar hankali. Kinsan idan ya taki wannan sa'a ya tsallake tudun mun tsira kuwa? Ko kinsan a kwai d'an boll d'in da yake d'aukar miliyan talatin duk Sati a k'asar turai?"
Nace cikin rik'e baki a rud'e.
"Duk Sati Ancle?".
"Sosai kuwa. A Kwai mai d'aukar Sama da haka Sumayya. Nan ma a na Samun k'ud'in musamman idan club ya shahara, amma ko kusa baza'a had'a shi da k'asar turai ba Kinsan yawancin kud'in ma daga wurin 'yan kallo a ke Samun yawan kud'in, to can turai, Mutum d'aya kika ji kud'in da zai biya ya Shiga kallon gasar k'wallo Sai ki rik'e baki. To Mutum miliyan nawa, ko Mutum d'ari nawa zasu Shiga kallon gasar boll na wata wata na kasa kasa, na cub club ke karawa da juna. Bari dai mubar Maganar boll, muyi
wacce a kanta za muyi magana.
Yarima yana da Wata budurwa da suke matuk'ar son juna mai suna Salima. Tana da kyau wai ainun, a fad'in a bokin Yarima na hannun dama mai suna Hashim. Ni dai ban tab"a ganin'ta ba, Sai jin labari.
Mak'otan mune, suna zaune a Kaduna, cikin unguwar sarki.
Mahaifiyar Salima attajira ce, domin business take na saro furnitures daga k'asashen waje. Sun rabu da Mahaifin Salima, ta sake wani auren wani attajiri a unguwar malali. Amma Salima tana gaban'ta. Ita kad'aice 'yarta a duniya, tana son'ta kamar rai.
Salima tana da tarin masoya da yawa 'ya'yan attajiran gaske, amma Yarima take so kadai, kuma tasan wanene shi.Sun had'u da fa'izu a heal's and Bally da sallah. Shekarar su biyar Kenan suna soyayya.Wannan Shekarar Salima ta soma bautar k'asa. Maganar auren'ta ta taso, tace bata son kowa Sai Yarima. Mahaifiyar'ta ta nemi ganawa da Yarima.
Bayan gaisuwa tace masa me yayi tanadi, game da auren 'yarta tun da yasan 'yarta ba gama garin 'yammata ba ce. Bai b'oye mata komai ba na matsayin'sa da kuma a binda yake yi, amma yace yana da wani buri da yake so ya cimma. Kuma in dai ya cimmasa to komai da take so zai yiyu, amma yanzu haka bashi da wani shiri irin Wanda take nufi. Yace yana da dai dai arzik'insa Wanda zai iya rik'e mace. Sannan gini yake yi ma yanzu ko rabi bai kaiba.
Nan Sai ce masa tayi.
"Haba Fa'izu! yaushe zamu saka rai da a binda bashi da tabbas? Wayasan San'da wannan buri naka ma zai cika. K'arshe Salima tayi aure har tayi haife haife burin bai cika ba. Nama tabbatar Sai ta rigaka aure. Kai da kan'ka kasan Salima ba matar talaka bace, ko a talaucin ta taso, ballan'ta na ta taso, gidan iko.
K'warya ai 'yar uwarta take bi, domin idan tabi a kushi kunya zata sha."
Yarima baya barin ta kwana, da anyi masa zai mai da raddi.
Yace
"Mama, ai ita k'waryar tasan da 'yar uwarta, amma Sai ta zab'i bin a kushi. Kenan ita taso taji kunyar. Salima ita ta fara nuna muradin'ta a kaina, duk da tasan wanene ni, me nake dashi. Daga k'ulla a bota da mutunci farkon had'uwa ta mai dashi soyayya. Bazan b'oye ba, wallahI, tun da na had'u da 'yarki mama ta Shiga raina sosai. Amma banyi a zarbabin nuna mata ba, Sai da ta fara. Kinga kuwa 'yarki ta rakito miki ni. Kuma burin mutum, ubangiji ke cika masa a Sanda duk yaso. Babu kusa kuma babu nesa. Saboda haka a kowani lokaci, ban fitar da ran cikar burina ba. Kuma bana gaggawa, na barwa mahalicci na ikon'sa a kaina. Salima kuma Ina mai tabbatar miki bazata rigani aure ba, saboda nasan duk runtsi bazata iya auren Wanda ba ta so ba. Duk tsayin shekaru nasan Sai ta jirani, da ta auri wanda bata so. Kinfi ni iko da 'yarki, amma nafiki kusanci da sirrikan dake zuciyarta. Babu a binda take b'oyemin. Ba kuma zan iya jiran Salima ba, saboda burin da aka ci mata. Zan yi aure a kurkusa, saboda addini mata hud''u ya halattamin. Zan auro dai dai dani a arzik'I. Ban kuma bar Salima ba,zan aure ta idan damar hakan ta samu a gareni duk jimawa. Bata da laifi, kuma nasan tana Sona. Wannan shine uzurin da yasa zan aure ta. Ba domin haka ba, to Wallahi da na barta Kenan har a bada. Domin bana waiwaye idan nayi gaba in
dai aka nunamin iyaka ta, a kan komeye."
Daga haka sallama yayi mata yayi gaba. Bai jira ma me zata ce ba. Amma ya lura maganganun'sa sun kad'ata."
Kawu Sulaiman bai dad'a ba, bai raga ba, Sai ga kakana ya shigo, wato Mahaifin'sa. Da sauri Kawu Sulaiman ya karb'i jakar da take hannun'sa, ni kuma na karb'a daga hannun Ancle.
Ya dubemu yace.
"Hira kuke kai da 'yar taka?".
Yace"Eh! Baba. Wata magana muke tattaunawa".
Yace.
"Zan kuwa katse muku hanzari kwa k'arasa daga baya.
Wata unguwa nake so ka kaini Sulaiman ta gaida mara lafiya. Dan babban a Minina a ka kwantar a asibiti saurayi babu yarda yake. Ai baburin'ka lafiya yake ko?"
Kawu yace. "Ai na gyarashi Baba. Dama matsalar kafireto ne".
Yace" To, Muje ka ka kaini. Nan hirar tamu ta datse. Ni kuwa na k'agu naji yarda al'amarin ya Kaya. Da kuma Maganar da Kawu Sulaiman yace za muyi ta musamman.
Kwana biyu ne rak tsakani , muka sake Samun sakewar ci gaba da hirar Yarima, wato Fa'izu Bukar. Baba Talatu tana d'akin Baba, wato kakana bayan kai masa bincin dare suna tasu hirar suma.
Kawu Sulaiman Yaci gaba da cemin.
"Sumayya Yarima yana buk'atar aure a kurkusa, domin yace Sai ya d'au fansa. Sai ya maida martani. Yaci alwashin, Sai maman Salima tazo tana rok'on'sa ya auri Salima, kuma Sai ya garata sosai. Yace Sai ta aza kwandon dana Sani a kan'ta tayi yawo dashi ta gaji."
"Idan na fahimci dai dai, auren huce takaici Ancle Fa'iz yake so yayi?". Injini
"Haka ne, Sumayya".
Na sake cewa.
"Ancle har Yaushe zai samu Wacce yake so cikin gaggawa yayi auren."
"Kawu yace"Maganar a ce Sai ya samu wacce yake so bata taso ba Sumayya . Karki manta fa Yarima wato Fa'izu a cikin soyayya yake
bai fita ba. Bai daina son Salima bafa, suna tare har yanzu. Amma bai fad'a mata a binda maman'ta tayi masa ba. Yasan kuma bata Sani ba. Yace ko Salimar bazata San zai yi aure ba, Sai ya basu katin gayyata".
Nace.
"Amma dai zai tashi hankalin Salima Gaskiya.Zai kid'imata ainun. Daga Sama fa zataji komai, bayan yasan suna son juna."
Kawu na yayi murmushi.
"Ai hakan shine muradin'sa. Mahaifiyar Salima tana mugun son'ta kamar rai. Idan kuwa hankalin Salima ya tashi, ta Shiga tashin hankalin da bata tab'a zato ba, to fa neman a gaji maman nata zata tafi na ceton 'yarta. Kuma dole Sai wurin Yarima".
Kawu Sulaiman yasa Wata siririyar dariya.
"Yarima yasan takan tsiya".
Ni kuwa jagale nayi Ina kallon'sa.
Yaci gaba da cewa.
"Satin da ya wuce, na sameshi wurin training. Bayan ya gama nace masa me a ke cikine yanzu.yace min har yau bai nutsu wurin Samun wacce zai aura ba. Yace yanason yarinya mai hak'uri da hankali da addini ba Ballagaza ba. Domin Sai da mai irin wannan kyawun halin zai cimma manufar'sa ta a binda ya himmata cikin nasara.
Amma wai a bokan'sa suna ta kawo masa tayin mata da suke ganin sun isa a sosu, bai je ya gan'su ba. Kuma ana ta kawo masa hotunan 'yammata kyawawa a cewar'su. Hotunan yace baisan a dadi ba, tun da ko bud'awa ma bai yi ya gaggan'suba.
Na tambaye shi me yasa.
Yace shi ganin hoton mace bazai gamsar da shi da komai ba. Ya ganta a zahiri, yayi kuma hira da ita, tanan zai san ta can can'ta.
Nace masa, yanzu idan aka kawo maka ita kaga tayi zaka aura? Yace min.
Maganar wai a ce tayi min ma, baya cikin tsarina, kuma bana kwad'ayin hakan, saboda nasan ba za ta tab'a yi min d'in ba ne. Sai dai Kawai na aureta saboda wad'ancan halayya idan na tabbatar tana da su.
Kawu Sulaiman ya dubeni sosai yace.
"Sumayya kin yarda dani?" .
N'a gyad'a kai, cike da mamakin furutan'sa. "Na yarda da kai fiye da kowa Ancle."
"Akwai Abinda zan umarceki kika sayi min Sumayya?"
Nace"Sai Sab'on mahalicci dai?".
Yace"To, Sumayya Ina so ki auri Fa'izu, wato Yarima."
Na kad'u k'warai da jin furutan'sa, na kuma gaza cewa komai Sai sunkuyar da kai.
"Yarima ya bani zab'in na samo masa irin Wacce yake nema in dai Ina da iko. Ni kuma ke Zuciyata ta halarto min, kina da irin wad'annan d'abi'u, kuma ke kad'aice a bar iko na a du,cniyar nan. Kina da irin wad'an nan d'abi'u da Yarima ya zayyano, har ma da k'arin wasu kyawawan da bai Sani ba. Ke kika dace da auren Irina Yarima, Amma ke da shi baku Sani ba. Kuma nasan ko kun Sani, bazaku yarda cewa kun dace da juna ba a d'abian'ce tun da kowa a bai bai yake kallon d'an uwan'sa. Kiyimin alfarma Sumayya ki a mince da auren Yarima. A Kwai dalilai da yawa da fa'idodin hakan, amma sai kin fara amincewa za kiji su daga baya".
_Tofa_!
Muje dai zuwa...
*Daga alkalamin*...... 🖋️
Zainab mazawaje
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
_Zainab Mazawaje_
_Best brilliaant interlligent write_..... 🖋️
*page 7*
Jikina yayi sanyi, na lalubo k'arfin hali nace.
"Ancle bani da Uban
da ya fika yanzu. Zaka iya zartar ma da hukunci a kaina a duk san'da kaso, ko bansa ni ba. Amma idan kafiso kaji daga bakina ne, to na amince".
Sai da na daure iya dauriya domin farantawa wanda ya fikowa so'na da son farin ciki na, amma ba domin raina na yana son auren Yarima ba. Auren da na tabbatar bazan tsinci ribar komai a cikin'sa ba, face k'ask'anci, bayan rashin rabauta da soyayya irin wacce nake buri a aure, nasan Fa'izu da murd'ad'd'en halin'sa,mai iyawa da shi bazance babu ba, amma sai wacce taci hak'uri ta tada kai dashi, har tayi guzuri. Ma'ana mai hak'urin gaske.
Kawu ya cika da farin ciki mara misaltuwa game da a mincewa ta. Albarka kuwa nashata kwando kwando.
Na kasa danne amma tambayoyin da suke tayi min zallo a zuciya ta nace.
"Kawu, Ancle Fa'iz fa ya sanni tsayin zamani, bai nuna yana da muradin irina bafa".
Yace"Na fiki sanin haka."
Ganin bai d'ora ba kan haka na sake cewa.
"Na Sani, kuma kai ma ka Sani Ancle Fa'izu baya sona, kuma nasan bazai tab'a Sona ba."
A cewar Ancle.
"Na yarda yanzu kam baya son'ki.Saboda bashi ya nuna ma muradi a kan'ki ba. Bai kuma halarto kima cikin macen da zai yi auren huce takaici ba. Amma hakan bashi yake nunin bazai tab'a sonki ba. Ko bai soki yanzu ba , zai iya son'ki nan gaba. Idan kuma bai so kin'ba to bazai wulak'antaki ba Sumayya. Saboda kina da d'abi'u irin na mata na gari. Kuma irin'su basa tozar'ta a gidan aure.
Yaja dogon numfashi.
Ki kwantar hankalinki. auren'ki da shi ba lallai bane. Jarraba sa'a ta zanyi na k'oK'arin had'a auren ki da shi, saboda Sha'awar hakan, da ganin dacewar hakan. Yarima kaifi d'aya ne. bashi da shayi, ko jin nauyi na b'oye a binda ke cikin zuciyar'sa. zai iya cewa ya amince da aurenki, zai kuma iya cewa Sam bai a mince ba. Saboda haka ki tsaya a k'ila wa k'ala."
Jin haka na d'an samu nutsuwa. Dabara ta fad'omin. Daren Ranar ko bacci ban samu ba ko na awa d'aya. Addu'oi nayi tayi da nafilfili kan aure na da Ancle Fa'izu kar yayiyu. Rashin yiyuwar dai yace baya ra'ayin Sumayya a aure. Da wannsn niyyar nayi ta addu'a.
Nasan cewa Anle Fa'izu yafi gaban a ce ba'a son'sa. Amma Ina! nasan ko kusa ba zamu dai dai ta bane. Saboda irin sanin halin'sa da nayi lokacin da yana koyar damu, ko yana son mace ba za ta iya da baudadden halin sa ba, ballantana ba ya sonta.
Ni burina nayi auren soyayya mai dad'i da kwanciyar hankali, kuma d'orarre. Ta ya ya kuwa zuciyata zata so irin wannan aure? ai daraja kan daraja irin ta Kawu Sulaiman Kawai zan yarda na aureshi, duk da nasan makomar bazata yi min kyau ba. Amma duk da haka bazan iya bad'awa kawuna k'asa a idanu ba. Bazan iya ba.
Na had'a Kayan miya ina sauri zan markad'a a blender, saboda kar su d'auke wutar. Kawu Sulaiman na gani ya shigo kichean, da ba sabon'sa ba ne.shi yasa na cika da mamaki na sararo ina kallonsa kafin nace. "Sannu da zuwa my Ancle."
Cike da wani farin ciki da bansan musabbabin'sa ba yace. "Sannunki da aiki shalelen Ancle. Kin ganni har tsakar kichean
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13