Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke ko? Kuma a Ina kika zama senior? Kan ki fanko ne fa babu komi Sai tarin rubish. Simple topic irin wannan kika sa understanding? Ballagaza dak'ik'iya irin ki Zaman gida, shi yafi dacewa dake. Mai makon dai kizo a yi biyu babu. Ki wahalar da malami, ki kuma wahalar da kan ki, tun da k'wak'walwarki ta kifi ce ,ba fahimta za kiyi ba ma." Intisar Kam ta muzanta a lokacin, Wai ita aka tozarta gaban wad'an da take ganin ta fisu. Za'ace ba'a tab'a ci mata mutunci ba a rayuwarta ma Sai ranar. Kuma namijin da take takawa. Kasa cewa komai tayi, saboda yarda ta karanci zafin sa, idan ta sake tagawa, Sai a binda ta gani kuma. To bata tsaya nan ba, babban a binda ba'a tab'a yi mata ba, ranar an yi mata. Zafafan bulalai yayi mata da tafi ta kowa. A hannu yake bulalar sa, da tak'i tsayawa ne, ya k'arashe mata a jiki. Tasha kuka, Sai gata magiyar Hak'uri take bashi. Bai kuma saurara ba. Na yarda Fa'izu baisan kalmar hak'uri ba.Kowa bulala Sai da ya fito ya karb'a Kam. Amma biyar biyar, Sai dai ko Wacce d'aya Sai ka fad'awa mutan garin Ku. Yarda yake da zafi, haka ma bulalar'sa. Ni Amma na tsira, Sai d ai na k'ara tsorata da lamarin malam Fa'izu. Ai tun daga ranar kowa ya Shiga taitayin'sa da shi. Karatu babu wasa. Nutsuwar fahimta, kowa Sai da ya lalubo, idan ma baka da shi, to Sai ka aro. Tuni ya gyarawa marasa kunya zama da kuma dak'ik'ai , da yayi tambaya kuwa rige rigen bashi amsa ake yi. 'Yan a jin mu da malamai ke masifar ji damu, to fa'izu yafi tsanar mu shi. Yafi kuma takura mana ma. Amma yana da hujja gareshi. A Kwai ranar da yace. "Na fahimci kun d'auki kan Ku Wata tsiya, shi yasa kuka d'auki girman kai kuka d'orawa kan Ku. To zan saukar muku da shi kuwa." Gaba d'aya makaran ta ta d'auka da Fa'izu Bukar,ko'Ina ka zaga Zancen sa. Makaranta tuni ta soma gyaruwa, saboda matsayin displine master a ka bashi, saboda jajircewar sa wurin kawo gyara a makarantar. Ya gyara makaranta Kam, ko ga tsafta da tarwatsa Zaman da malamai suke na hira a k'i Shiga a ji koyarwa. Meeting na dole yasa a kayi harda prince pal aka kawo sauye sauye. Ko a makararru ma an samu sauk'i sosai. Domin Sai a jima ma ba'asamu wad'anda za'a tare ba da sunan makara. Saboda malam Fa'iz ke hukuntawa. Kuma babu sauk'i ko a fuwa a lamarin sa, ko wacece ke zaneki zai yi tas kuwa. Kuma idan zaki d'ige kina bashi hak'uri bazai hak'ure ba. Bada Hak'urin ma shi fusata shi yake yi naga. Tofa!. watan'sa na biyar nima na fad'a komar sa. Dama yayi min baki. Garin tsautsayi rannan Sai gani cikin makararru guda biyar. Zance tsautsayi, tun da ban tab'a makara ba. Abinka da matsoraciya. Jiki har rawa yake Ina bashi hak'uri da yazo kaina ya rik'e baki. "Cab' , monita kina shugabar d'alibai amma kika makara? Muk'amin ki bashi da wani amfani, tun da ke shugaba mai gyara kin gaza wazai gyaru kuma?" "Wallahi sir ban tab'a makara ba, yau ma akasi a kasamu na tuba, bazan k'araba." Yace"Kome zaki ce ba zaki tsira ba Wallahi. Kuma bulalarki Sai ta ninka tun da shugabanci aka baki ga 'yan baya, dole muna so ki ki yaye. Zafafan bulalai goma yayi min da naji kamar na shid'e domin zafi. hak'uri da nake bashi naga kamar tunzurashi ma nake, shi yasa na hak'ure. Hannaye na har tara jini suka yi bayan kumbura. Na yarda Fa'iz mugu ne na k'arshe. Da gayya ma nasan yayi min irin wannan bulalar mai ratsa k'ashi. Tabbas Sai a lokacin na yarda da zafin bulalar sa da d'alibai ke fad'a suna tsoro. Tun daga ranar naji na tsaneshi. Tun da uwata ta kawoni Duniya Kam ba'a tab'ayi min bulala ba nima ballantana mai zafi irin wannan. K'udirewa nayi a raina na daina yi masa magana ko a aji.Amma daga baya dole na saddak'ar, saboda malam Fa'zu yafi gaban nan. Tambaya ma baka amsa masa ba, hukunci ne mai zafi. Domin kuwa ko zagin'sa na tsamar nama yayi maka ma bainan nasi, ya cuceka. Ga dai intisar nan duk tayi laushi ta horu. Duk rashin kunyar nan da felek'e ta dire. Muddin ya shigo class wata nutsuwa ma take yi. Amma a jita jita naji wai son sa take kuma. Bama ita ba ya kwashi Jama'a masoya mata jingim, amma na b'oye. Tun da dai kota Ina babu Wata alama da ta nuna Fa'zu Bukar Zai karb'I tayin k'ok'on barar Soyayyar wata mace a makarantar, face ma Sai dai yayi fatali da k'ok'on barar. Ni Kam duk Wacce zata so ma Fa'iz wahalalliya na d'auketa, Wacce kuma aka yankawa kazar wahala a kace Sai ta fige.wahala bata ishe suba ne da wulak'anci suke neman k'ari. Haka nake cewa duk Wacce aka cemin ta Mato a kan son Fa'iz. Ban kuma yarda ta had'oni da malam Fa'izu ba, gudun inda zan ganshi ma nake yi idan ba 'ajin mu ya shigo ba. Duk domin kar ya kamani da laifin da zai ci zalina, saboda na daku, jikina bai manta ba. Kuma kumburin hannu n'a bai gama Sab'ewa ba. Amma duk guduna da shi, Sai da rannan ta sake had'oni da shi. Rannan na Shiga staff room Kiran malam labahani saboda period d'in sa ta shiga bai zoba. Ina Shiga staff room bisa tsautsayi idanu na da malam Fa'izu suka fara kicib'is. Suna zaune shida malam Abba da na fuskanci tasu tafi zuwa d'aya suna cin gyad'a. Malam Abba yana kan desk d'in da suka zube gad'ar, shi kuma malam Fa'izu yana kan kujera, suna hira har suna 'yar dariya ma. A raina nace. Dama malam Fa'izu yana dariya? Zatona ko murmushi bai iya ba. Da wuya ma naje staff room na ganshi Sai Jifa Jifa idan bashi da class, saboda a Kwai himma a wurin sa wurin kula da karantar da d'alibai. Muna had'a idanu da shi kuwa, ya wani d'aure fuska, ya kuma sakar min wani uban muzurai. "Zonan ke monita" Jiki ya na rawa na isa garesu. "Gidan'ku ba'a koyar da tarbiyya ne?" Yace , bayan ya jefa gyad'ar da ya murje bakin sa. Na Shiga dawurwura saboda bansan laifin da nayi ba, Sai da malam Abba yace min. "Tsuguna Mana Sumayya. Ya kiraki kuma kin zo kin tsaya Mana a ka. "Nan na fahimci Laifina, amma ni shi duk ya gigitani. Ganin Fa'izu Kawai tsorata nake yi. Malam Fa'izu batare da ya ko kalleni ba yace. "Sintirin me kike damun Mu da shi a staff room? Kullum kina kan hanyar zuwa nan? Uban me yake kawoki matattarar malamai?" Na sunkuyar da kai sannan nace. "Malami nake kira idan period d'in sa ta Shiga bai shigo ba". Ya tsaya da cin gyad'ar cikin d'aga murya da fusata yace. "Wayace Miki aikin ki na monita yana cikin haka? Hak'k'in ki ne Kiran malami, ko Hak'k'in malami ne yazo teaching da kan'sa?" Ba suna da time table ba ma?" Nayi tsuru tsuru da ni nak'i magana, gudun nayi laifin da zai casani. Tuni duk kallon malaman dake staff room yayi yo kan Mu, saboda yawancin malaman suna hallare. Da k'arfi Fa'izu yake magana, kuma nasan domin sujine, domin babu Wanda yake shakka, Sai ma su da suke shakkarsa, har ma da prince pal, da vice prince pal.saboda bayan zafin sa,ya tab'a cewa a kunne na da suna hira da malam Abba bayan staff room da zan wuce ta window, cewa yaja kunne a meeting domin kowa yayi hattara, na yana da hanyar da zai kai k'ara ma'aikatar ilimi ga shugaban kula da matafiyar ilimi na k'asa, in dai shugaba da malamai suka ci gaba da cin albashi a b'agas babu kula da hak'k'okin aikin su. Malam Fa'izu ya dubeni cikin fushi. "Kar ki sake na k'ara ganin k'afarki a staff room da niyyar Kiran wani malami. Wallahi na sake ganin ki? zaki fuskanci hukunci na ban Mamaki. Ihope you get it?". Na jinjina kai. "Kin fahimta nace? Talk to me." Na gyad'a kai da sauri. "Na fahimta, sorry sir." Yaci gaba da kallo ga malamai da suka kafa Mana idanu. "Albashi a na biyan kowa duk month mai nauyi kowa ya lamushe cikin jin dad'i amma ace wai Mutum baisan time d'in aikin sa bama Sai an kirashi? Why? Is not fair gaskiya. Menene amfanin time table da agogo Kenan? zamu sake zama da prince pal da teachers dole a yi gyara." Babu wanda ya iya cewa kanzil kuwa, saboda gaskiya ya fad'i da ba kowa zai iya bugar k'irji ba ya fad'I, Sai irin sa Mara tsoro mai dakakkiyar zuciya kuma. "Tashi Kije".Yace dani da nayi sunk'ui da kai. Tun daga ranar, ban sake yarda naje staff room ba, saboda gargad'in malam Fa'iz. Domin nasan makomata ma idan ya kamani. Ba'ajima ba kuwa na fahimci anyi gyara. Domin da lokaci ya Shiga malami Zai shigo da kan'sa. Ba kuma Zai fita ba, Sai lokacin'sa ya fita. Kuma karatu ya k'ara zafi. Malamai sun daina shigo da hira da wasanni cikin karatu, Wanda nafi kyauta ta zaton malam Fa'izu ya fahimci duk matsalolin dake cikin harkar koyarwa yasa aka kawo gyararraki. Ko Mak'iyin malam Fa'izu tabbas ya yarda sanadin zuwan sa, makaranta ta gyaru. Sauye sauyen ci gaba da ya kawo da yawa na ci gaba. K'orafin da a ke yi da shine bai kau ba wato na tsanani da cin zarafin studen't fiye da k'ima idan sun yi laifi. To ni fahimtata da hakan , Kawai na fahimci Fa'iz Mutum ne mai fushi da zafin zuciya. Shi yasa ma Sam baya d'aukar raini. A binda ya shige min duhu da shi, na yarda baya karb'an uzuri. Kuma baisan kalmar Hak'uri ba. Watanni uku suka rage muyi jarrabawar kammala makaranta. Saboda haka rannan Bayan malam Abba ya gama yi Mana subject d'in sa na mathematic, ya zauna yana bamu shawarwari domin mu kara zage damtse da karatu mu samu sakamakon jarrabawa mai kyau. *Zainab mazawaje* [6/20, 7:58 AM] Zainab Mazawaje: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* Zainab mazawaje _Best brilliant intrlligent writer_..... 🖋️ *page 3* Malam Abba, ya gyara tsayuwa, ya fuskanto mu yace. "Ko da yake yanzu kuna birgeni, naga ma ai duk kun canza kunyi laushi. Da idan an shigo a jin nan kamar kasuwar trade fair, amma yanzu kamar gidan makoki. Ko babu malami zanga Kowacce ta d'auko littafi tana bitar karatu. Wai yaya a bin yakene.? Ko walwalar ku ma bana gani." Ya karashe furucin cikin wani murmushi mai nunin da wata manufa a cikin maganganun sa. Fati d'alha tace "Sir, gaskiya ya kamata kayiwa aminin ka nasiha, ya fiye tsanani. laifi da k'arami da babba duk hukunci d'aya. Zagin da yake mana, ko iyayenmu basa yi mana. Wallahi matar'sa ta Shiga uku." Intisar tace. "Addu'a zaku yi masa kawai, domin ya gyara halin sa, amma mutum ko aljani ba za su iya sauya malam fa'izu ba wallahi". Kowa Sai da ya dubeta na Mamaki. Shi kuwa malam Abba murmushi yayi. "Yauwa 'yar gari, Kunji in da ake kalamai na nutsatstsu. Kuma idan b'era da Sata ai daddawa ma da wari. Kuma k'iriniyarku tayi yawa, dole Sai irin malam Fa'izu ne zai yi dai dai daku. Malam Fa'izu idan ba'ace Sam barka ba, baza'a kushe ba. Gyaran da ya kawo cikin makarantar nan ai ya yawaita. Ko prince pal da vice sun Sara masa. Ai addu'a ya dace Kuyi masa ta alkhairi. Ya dan yi shiru kafin ya numfasa yace. Bayan tarbiyyar da ya kimsa muku ya gyara muku harkar karatu sosai. Kuma ku zakuci amfanin sa a gaba. Shi ba ma mazauni bane jiddin. A Kwai a binda yasa a gaba, da ya samu zai bar harkar koyarwa, Kawai ya Shiga harkar da ba itace burin'sa ba, sabod kishin kasarsa. Zan iya rantse muku albashi ma shi baya gaban'sa. Burin sa a samu sauyi da ci gaba. Saboda haka kuskure ne d'alibi ya zauna yana aibata malami ko da dalili, tun da kullum cikin cin amfanin sa yake. Kuma ba'a iya biyan malami kun sani sai ubangiji ne kawai zai iya biyansa". Jikin kowa yayi sanyi. A ka rasa me iya cewa komai. Ni kuwa dama nasan kuka suka kawo gidan mutuwa. Malam Abba na hannun Daman malam Fa'izu ne, bazai tab'a yarda a ai bata shi ba ya k'yale, duk da dai gaskiya ya fad'I. Alkhairan da malam Fa'izu ya kawo, a makaranta, bai kamata a aibatashi ba, koda yayi laifin. Kowa ma yaji ba domin kud'i yake koyarwa ba, Sai domin kishin k'asar'sa. Wannan kad'ai ya isa yasa ya karb'i lambar yabo. Tunani na kenan da na wasu d'alibai da muka zanta daga baya. Daga baya ga mamakin mu, malam Fa'iz ya sassauta tsananin nan da tsaurara hukunci garemu. Kuma na lura canzawar da yaga munyi ne, Shima yayi d'an laushi. Sannan ya fito da wata hanya ta taimakon mu, don mu haye a jarrabawar mu ta gama makaranta ta gaba to. Lesson ya tsara duk yamma cikin makaranta ga duk wacce ke ra'ayi amma. Shi ya d'auki nauyin komai.hud'u da rabi an Shiga a tashi k'arfe shida na yamma. Duk d'alibai kuwa a ka yi ta tururuwar zuwa, saboda kowa so take taci jarrabawa. Ba kuma iya darasin turanci yake koyawa ba, har ma da sauran darussa. Kuma yawancin a binda yake koya mana wanda yake tunanin zai fito mana ne a jarrabawa. Baki d'aya muka ga ya canza ma. Ya rage zagi da fad'an nan da tsare gida. Amma duk da haka fa babu fuskar da za'a kawo masa raini ko wasa. Har hira ma yake damu amma fa a kan karatu, da bamu shawarwari masu kyau, duk a kan harkar karatu, saboda jarrabawar dake dosomu. Da jarrabawar tazo kuwa mun taki babbar sa'a. Domin kuwa yawancin a bubuwan da malam Fa'iz ya koyar damu shi ya fito. Har zargi ma muka rink'ayi anya bai samu tambayoyin jarrabawar ba a boye, domin komai ya fito da ya koyar damu. Ai sai yayi kuma farin jini wurin mu. Domin yayi mana k'ok'arin da babu malamin da yayi mana irin sa. Mun kammala jarrabawar cikin sa'a da kyauta ta zato, domin duk wacce ta sare, sai dakikiyar da kwakwalwarta ba ta aiki. Ranar da muka kammala jarrabawa da yamma, aka sha hotuna, har da malamai a kayi hotuna. Amma fa banda malam Fa'izu. Kuma anfi kwad'ayin ayi hoton da shi, saboda tarihi. Kuma abin alfaharine ga d'alibai, amma mirsisi yak'i. Ko da yake tsoron tun karar'sa ma a ke yi, malam Abba a ka tura. Ya dawo yace. "Kuyi hak'uri fa. Abokina yak'i yace yana da mata, kuma zatayi kishin haka. Duk d'alibai sun yarda, nice dai kunne na bai karb'a ba. Lambobin waya ma na malamai da ake karb'a malam Fa'izu hanawa yayi. A ka koma takan malam Abba ya bada lambar wayar malam fa'iz yace shi bashi da ita. Ta yiyu shi ya hana shi ya bayar, nafi kyautata zaton hakan. Intisar tafi kowa damuwa da lambar Fa'iz, saboda son da take yi masa ma ya fito fili. Amma ko giyar wake tasha bazata iya tambayar sa ba. Tun daga Sanda tayi masa rashin kunyar nan suke takun sak'a da shi. Ta gasu a hannun'sa. Tsakanin sa da ita hararace. Duk Sanda ya shigo class Sai ya tasheta yayi mata tambayoyin abinda ya koyar. Ta fad'i wanda ta d'an fahimta, tana yi yana jefa mata kallon wulakanci, da ta kakare kuwa zai ta gasa mata maganganun tozarci da gwara dukan ma dasu gaban dalili bai, to ya fuskanci tafi jin ciwon bakaken kalmomi, shi yasa baya dukanta ma sai dai ya tozarta ta gaban jamaa, ta hanyar cin zarafi da furuci. Gaskiya Ancle Fa'iz yasan takan iya tsiya, da ka fada tarkon sa, gwara a jefa ka gidan yari iya na waadin laifin ka. A cewar zuciyata . Tsawon wata guda, tun da na gama secondry, babu in da nake zuwa bayan islamiyya. Sam kuma fitar bata dameni ba ma saboda ni dama ba ma'abociyar son yawo bace. Sannan soyayya da tarairayar da nake sha wurin kawuna sulaiman ta isar min daga damuwa da wani a bu a rayuwa da zai sa na rinka yin tunane tunane. Kulawa gata, sangarta so da k'auna duk Kawu sulaiman ya tattare su a kaina. Haka ma kakana Laminu mai turare. Sai 'yar korar su mai taya su, matar kakana Baba Talatu da ya auro bayan rasuwar Inna Hajara kakata. Duk da baza'a had'ata da kakata ba inna Hajara, amma tana kamantawa sosai. Ni d'in marainiyace ta sosai, tun da ban bud'i idanu da iyaye na ba duk sun rasu Ina yarinya sosai. Bayan nan kuma nazo na rasa kakata Hajara ita ma data rungumi maraicina da kyau, take nunamin k'auna muraran. Sai da ta shekara da rasuwa kakana yayi aure, kuma saboda ni. Saboda babu yarda za'ayi ya zauna dani babu mace. Naga mutuwa a rayuwa ta Kam. Amma Sai a tara masu iyaye Sama da d'ari ba'a samu mai Samun kulawa da tattalin k'auna iri naba. Shi yasa bayan rasuwar kakata Soyayyar ta dawo kaina. Haka ma kawuna Sulaiman Soyayyar dake tsakanin sa da yayarsa mamana Khadija da bazata fad'uba, kaina ya tattarota bayan rasuwarta. Su biyu ne tal wurin iyayen su, kuma a Kwai k'auna da fahimta mai zurfi tsakanin su. Wannan dalili yasa Kawu yake mugun Sona da tausayina. Motsi kad'an yana bibiyar me nake ciki. Kome ya samu ni zai kawowa. Tun da ya gama digree babu aiki ya Shiga buge bugen aikin Samun k'ud'i na k'arfi, daga wannan zuwa wannan, duk saboda ni. Ma'abocin son K'wallon k'afa ne sosai. Suna da Club babba ma na matasa irin sa. Suna buga mach kurfa kurfa na state state bayan na garin su idan an gayyace su. Yama fi Samun kud'i tanan babu laifi. Amma lokacin daya ke bawa boll dabam, lokacin buge bugen sana'oin sa ma na kafi zuru da bam. Yayi rini, yayi Aikin gini, yayi aikin electric, har aikin fenti ya iya, idan an kirashi zai b'adda bami yasa Kayan aikin yaje yayi ya karb'i kud'in'sa. Mai k'wazon neman na kaine Kawu Sulaiman, bashi da girman kai Sam. Kuma duk sana'ar da yaji ana Samun kud'i zai koya, ba tare da raina taba. Shi yasa baya rabo da'yan kud'ad'e. Bamu da shi sai dai na rufin a sirin rayuwa, kakana ma a zaune yake ba kullum yake fita ba, da harkar Sai da turare ta karye masa. Da kanti ne da shi guda na saida turarurruka, yanayin rayuwa komai yaja baya. Kawu sulaiman ne ke k'ok'arin a bubuwa da yawa. kuma rayuwar mu babu fallasa, komai a Siri a rufe ruf.'Yan kayan k'walam na motsa baki ma Kawu na kan sayo lokaci lokaci. Ban rasa kuma 'yan Kayan ado irin na 'yammata ba, Kawu sulaiman yana fito dani kunya, ko ban furta ba zai sayo dai dai ikon sa. Ya kuma ban k'ud'i ko zan buk'aci wani a bu. Wani lokaci zaice na samo takarda da biro na rubuta duk abinda nake bukata na 'yan mata, nakan rubuta na bashi, shi kuma duk sanda ya samu iko ya kan sayo su a hankali a hankali. Kuma da an dauki lokaci zai sake cewa na rubuta abinda nake bukata, sannan ya kan bani 'yan kudi na kashewa ma jifa jifa, kuma ya danganta da nauyin aljihunsa na daga a binda zai bani. Ya wanke min duk wani hawayen maraici, saboda ubana talaka ne sosai, bai barmin komai na gado bama. Ko gidan da suke zaune da mahaifiyata ma na hayane, kuma biya masa ake yi. Tun mahaifiyata tana raye Kawu na yake nunamin Wata irin kulawa da soyayya, da Ina yarinya naji daga kakata, bawai sai data rasu ba. Domin da ta rasun ninkawa kuma yayi. Ya kusa zautuwa ma kawu da mamana ta rasu saboda kusancin sa da ita da k'auna. Kakana ma da matar sa kulawa da k'auna suna bani iyayin'su, saboda maraici hawan hawa da na samu kaina a ciki. Ina da ra'ayin son ci gaba da karatu, shi yasa ma aure baya gabana, ko kula kula da shaannin samari ba nayi, kuma kawu ya goyamin baya. Ina da samari, tun kafin na kammala secondry. Duk da haka dai i na da samari biyu da nake sauraren su sama sama. A Kwai Alhaji Rabi'u magidanci mai mata da yara. Yana da sukunin sa kuma yanayi min 'yan hidindimu. Yana da mota da yake zuwa wurina ma. Sai usman shi kuma saurayi ne, tela ne na aikin surfani. Hankalina ya d'an fi kwanciya da Usman saboda shi saurayi ne dai dai dani. Ina tsoron fad'awa tsakiyar ma'aurata. A nawa ra'ayin gwara tazo ta sameni. Amma shi Alhaji Rabi'u kullum zancen'sa na bashi dama ya fito, amma bana bashi had'in kai. Shima Usman ya damu da azo a yi wani a bu, Shima d'in ma ni nake bashi matsala. Ina son na samu ilimi sosai nayi aiki na rink'a tallafawa Kawu da kakannina. Wannan shine burin sumayya a b'oye. Kwanci tashi jarrabawar mu ta fito na samu sakamako mai kyau k'warai. Shi yasa direct jami'a,suka amsheni. Kawu yayi ta samin albarka. Sosai yayi farin ciki, har kyauta yace zai min. K'awaye nama duk sunci da kan mu yake a had'e. Saboda halayyar mu guda ce ta son karatu. Amma nafi su kyawun sakamako dai. Kawu sulaiman yayi min nasiha sosai da shawarwari, wurin tafiyar da rayuwata ta jami'a. Yaja kunne na sosai a kan kar nayi mu' a mala da k'awayen banza da samari. K'arshe yace. "Na baki dama, don Allah kar ki bani kunya Sumayya, kija mutuncin ki, kiyi a binda ya kai ki Kawai, wato karatu." Nace" Kar kaji komai, Ancle, zan kiyaye, ka ta yani da addu'a." To ban bashi kunyar ba kuwa. A shekarata ta biyu a jami'a ya dad'a sakin ransa sosai saboda yarda yaga komai nawa yana tafiya dai dai, Sai ma k'arin ci gaba. Na k'ara nutsuwa wurin kula da tattalin kaina. Na k'ara sanin darajar kaina sanadin k'yamatar wasu a bubuwa da nake gani. Na k'ara kyau na gogewa da wayewa kuma, amma wayewa ta sanin mutuncin kai da darajar kai, da iya muamala da mutane, da kiyaye abinda zai rusamin rayuwa. Ba fara bace ni, amma za'a iya sani a layin farare idan sunyi k'aranci. Saboda kulawa da kaina da nake sosai, fatata Sai ta k'ara gogewa ta haskaka sanadin gyara. Kawu lokacin Samun'sa ya k'aru, ya kuma Saki Samun'sa sosai a kaina ma a lokacin. Burin sa Kawai Sumayya ta zama a bar kwatance da alfahari. Alkalamin...... 🖋️ Zainab mazawaje [6/20, 8:19 AM] Zainab Mazawaje: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️ *page 4* A tsukin kuma wanda nake kira da dan fodiyo wato (usman), ya matsa lamba. Sai ya nuna ala tilas sai na barshi ya turo manyan sa shi ya gaji da jirana. Ga a binda yace da nak'i yarda. "Sumayya, don Allah ki rufamin a siri nasan Matsayina. A farga ba nake tsindim na zaki iya kub'cemin. A komai kin canza kin samu haskakar da za'a k'yalla idanu a kan'ki a kawo miki hari. Babban a binda nafi kwad'ayi a kan'ki shine kamun kan'ki da nutsuwa da tarbiyya. A ina kike tunanin zan lalubo irin'ki idan na rasa ki? Tabbas zan shiga tasku idan na rasa ki. Ina sonki Sumayya fiye da tunaninki, don Allah kar kiyi min wasa da hankali. Ni dai na fito a San dani nasa rai ma. Aure zan jiraki zuwa lokacin da kika shirya." Sam aure baya raina a lokacin, ko

Chapter 2 of 13