Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fallasa ya karba, yanzun nan ta ba musaddik naira dubu dari hudu. Amma shi da kullum yake wahala akan lamarinta. Ta kirgo dubu talatin ta ba shi, ba tare da godiya ba ya ce "Mun barki lafiya' Tare suka jera da Musaddik suka fice, yayin da Hajiya Hudah ta bi su da kallo har suka bace ma ganinta. A zahiri ta ji dadin haduwa da Musaddik,domin ya yi mata matukar Kyau kuma bai yi kama da irin iskancin da Alhaji Hamza yake kira masa ba, domin bata dauka zata same shi da sauran nutsuwa ba. Sosai taji zuciyar ta ta aminta da yin hulda da shi ba tare da wata fargaba ba Alhaji Hamza kuwa suna fara tafiya, ya a mota ya waiwayo ya dubi musaddik Yace “Gaskiya ban san irin sa'arka ba Mazaje” Ya dan dube shi ya ce "Na me fa?" Ya ce "Na yadda Hajiya Hudah ta ba ka Wadannan makudan kudin ba tare da ta ga jama 'ar da za ka raba ma ba, ta yarda da kai cikin kankanin lokaci.wanda ba dabi’ar ta bace yin sabo ko damka ma wani amanarta nan da nan,don ko ni da na yi shekara da shekaru tare da ita, idan maganar kudi ta zo to fa sai ta ga komai da idonta, duk da tana haukar son wannan kujerar, za ta iya yin komai, domin hawa kujerar. Page 139 To fa duk da haka, ba ta kwasar kudinta irin haka tana bayarwa. Sai ta ji, ta kuma gani. Shi ya sa yadda ta ba ka wannan kudin abin ya yi matukar ba ni mamaki, Don mace ce me son abin duniya”. Musaddik ya yi murmushi ya ce “To ai komai ya zo gaf ne Kila ta yi tunanin idan ba ta bada kudin ba, za su yi boren ne, kamar yadda na gaya mata,tunda kuma tana son kujerar ai babu abinda ba zata yi ba gudun kada a sami matsala,kuma kaga ba mu taba haduwa da ita ba sai yau”. Alhaji Hamza ya nunfasa ya ce. "Allah shi ya san dalilinta na yin hakan, sai kuma ita kanta, ka na ji?" Ya juyo ya kalle shi ya ce. "Ina jin ka ya akayi Alhajin Allah “ Alh Hamza yace 'Dan yago min wani abu, don wannan dan kudin da ta ba ni, ba abinda za su yi min, ina da dumbin matsaloli amma ta hadani da dubu talatin, saboda tsabar rashin adalci”. Ba tare da yace komai ba Musaddik ya bude ledar, ya dauko dubu dari biyu cikin kudin da ta ba shi, ya mika masa. A gaggauce Alhaji Hamza ya ce "Dubu dari biyu ne fa mazaje”. Ya gyada kai ya ce. "Ina sane, Wadannan sun isa mu raba ko dubu biyar-biyar ne, ba damuwa, sauran dubu dari biyun nawa zan karama mutanena akan nasu duk sai mu raba saboda nasan kai ba za ka kashesu ta hanyar da za mu kashe ba, za ka yi amfani da su a inda ya dace ne, tunda kai ka ji dadi ka mori rayuwarka, babu shashanci a ciki. Idan na tafi da kudin nan, ni a banza zan kashesu akan abinda ba zai taba amfanar rayuwata ba”. Cike da tausayinsa. Alhaji Hamza ya ce “Mazaje iyalinka fa?"ya girgiza kai Yace "Ko na kai mata, sai ta tuhume ni ina na samo su, bata son wannan bangar siyasar da nake yi, kai mata kudin ba zai faranta ranta ba, sai dai ya bakanta ranta, ni kuma a duniya babu abinda na tsana sama da bacin ranta. Inda ina da iko da kaina da duk abinda nake yi yake bata mata rai na daina, to na zama tamkar wanda ake sawa yin abu dole idan banyi ba bana jindadi, kuma ko ma na kai mata kudin ta amsa to ni ne zan koma na kara karbesu na kashesu a banza, a duk sanda kuma na je amsa, ranta sai ya baci, domin ta Page 140 san abinda zan yi da su, amma ba za ta taba nuna min bacin ranta ba, za ta dauka ta ba ni, to kaga gara ma kada na kai mata." Alhaji Hamza a sanyaye ya karbi kudin hakika halin Musaddik, ba irin halin da Yake kallonsa da shi ba ne da kuma wanda yake aikatawa ba , kwarai yana da kyan zuciya, tausayi da kuma imaninsa, wannan halin da yake ciki hakika ba nasa bane, bai kuma dace da shi ba, ga kwarjini da dadin mu'amala. Karo na farko kenan da Alh Hamza ya fara yi masa addu' ar shiriya. Ya kirga dubu ashirin ya mika masa yace. "Ga shi ka kai ma matarka, na tabbatar kafin ka waiwayesu, sun kare, tunda babu yawa, kuma ba zata tuhumeka da inda ka samo su ba sabida basu da yawa kamar yadda na fada,don Allah ka kai mata”. Ba tare da musu ba, ya karba, ya tura a'aljihunsa har suka kai inda ya aje shi. Alhaji Hamza fatan shiriya yake masa, tare da yi masa addu'a, ya kuma sa a ransa ba zai taba mantawa da abinda Musaddik ya yi masa ba a rayuwa, tare kuma da alkawarin sa shi a cikin addu'arsa, a duk sallolinsa na farilla. A daran ranar da wuri Musaddik ya koma gida, hakan ya faranta ran Afrah, ta kawo masa abinci ya ci ya koshi. Tabbas yana jin dadin abincin matarsa, ba tun yau ba, domin ta iya girki.Afrah Ta kai, ta dawo yana kallonta, haka nan yake jin kunyarta, a duk lokacin da take hidima da shi Lokaci daya kuma tausayin ta yana kara kama shi. Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 141 Cikin wata irin daskararriyar murya musaddik yace “Zo nan ki zauna” ya fada yana nuna gefensa da hannunsa. Afrah ta koma a hankali ta zauna, tana kallonsa ya ce, yana cigaba da kallonta "Zauna haka nan ki huta ma kanki, nagode Kwarai da gaske, yadda kike kulawa da ni idan ina tare da ke har gani nake ban kai ki ba ni irin wannan cancantar ba, sai na dinga jin ta ko wane bangare na gaza a kanki” Ta dan yi murmushi,tana kara gyara zamanta ta ce “Haba yaya Musaddik, wai sai ka dinga yi min godiya akan abinda ya kamata na yi maka?bayan hakkinka ne nayi maka komai, batun cancanta kuma Allah ne ya baka wannan cancantar a matsayin ka na shugaba a gare ni” ido ya dora mata sosai yana jin tana kara burge shi yana jin wani irin shauki a kanta. Yana da kima da martaba a cikin gidansa Afrah bata taba kyamatarsa ba, yana jin zai iya yi ma Afrah komai domin ta jidadi ta kuma samu kwanciyar hankali,to amma me yasa ya kasa daina abinda yake yi wanda acikin abinda zai iya yi mata din wannan shine karami, amma me yasa ya kasa.ya sauke numfashi a hankali Yace "Na sani, duk da haka dai na gode, domin ni kadai nasan irin kokarin da kike yi a kaina, Allah ya kara yin albarka a cikin rayuwarki kanwata”. Ta jidadin furucinsa tayi murmushi tace “Amin” a ranta kuma addu’a take masa Allah ya kawo karshen al’amarin sa. Musaddik ya ciro dubu ashirin a aljihunsa, ya mika mata, ta sa hannu ta karba cike da mamaki tana kallonsa.tace “Na meye wannan kudin?” Yace “Na ki ne, wani abokin harkar siyasata ne ya ba ni, ya ce in kawo miki" ta yi dan murmushi tace “Amma nagode Allah ya saka masa da alheri,to amma sai ka dauka duka ka ba ni, ka diba mana”, Ya girgiza kai ya ce "A'a na ki ne, ba zan dauki ko sisi ba” Za ta yi magana kenan, ya mike yana gyara kwalar rigarsa yace “Ni zan fita" Nan da nan Afrah ta gintse fara'ar fuskarta gami da marairaice murya tace “Ina kuma za ka tafi?"ya dan dakata yana kallon yanayinta, yana jin wani abu wanda ada baya ji a game da Afrah, domin a yanzu ko yaya ta canja fuska ko ta nuna damuwarta akan wani abu da zai aikata yakan ji tamkar an dora masa dala da gauron dutse a kansa. Yanzu ma hakance ta kasance da shi. A hankali ya koma ya zauna daf da ita yadda suna jin bugun zuciyar juna, nan dan Afrah ta ji wata kasala ta rufeta, ta yi saurin yin kasa da idanunta. Ya mika hannunsa ya janyo hannunta ya fara nurzasu shi kansa jinsa ya yi yana neman fadawa wani hali, wanda baisa ya saki hannun nata ba, a sanyaye ya kira sunanta “Afrah”, bata iya amsawa ba illa idonta data dora masa. Ya cigaba da cewa “ki yi hakuri, a wannan gabar dole sai kin kara hakuri akan wanda ki ke yi da, zabe ya zo na kuma riga nasa kaina a cikin wannan aikin, dole ina bukatar hadin kanki, kamar yadda ki ke bani a ko wane lokaci”. Afrah ta lumshe idanunta ta bude ta kara dorasu akan fuskar nijinta, tayi dan murmushi tace “Ba ni da ikon shiryar da wanda Allah ya batar sabida haka nasan bani da ikon da zan dorawa kaina damuwar abinda yafi karfina, shi yasa nake yi maka addu’a a kullum, ina kuma da tabbacin wata rana Allah zai share min kukana,sai dai ba zan gaji da rokonka ba, don Allah Yaya, don girmansa da kuma darajarsa, ka yi ma kanka fada, ka natsu, ka san rayuwar da ka ke yi, ba ta dace da kai ba. Ka yi ma kanka fada, tun kafin ka fara haihuwa, a fara goranta ma yayanka” Musaddik ya kankame hannunta ya dora su duka akan fuskarsa, yace “ina rokon Allah kada ya dauki raina ba tare da burinki ya cika a kaina ba”. Ta kasa jurewa gaba daya kawai saita rungume musaddik tsam a kirjinta shi ma tamkar ya na jira ne don haka shima sosai ya rungumeta ya na shinshinar kamshin jikinta, lokaci daya kuma dukansu suka yi ta kuka me motsa zuciyar duk wani mai saurare. Basu san iya lokacin da suka dauka suna kuka ba, sai daga bisani Musaddik ya janye jikinsa daker tashi kawai ya yi ya kalleta, ba tare da Yace komai ba, ya fice, daga dakin, a hankali ta gyara zamanta a kan kujerar. Page 142 hawaye na cigaba da malala mata, alokacin da ko wane magidanci yake dawowa gidansa, shi a lokacin yake fita shin yaushe musaddik zai fahimci masifar da yake ciki, yaushe kuma zai gane girma a kullum zuwa masa yake .hankali ta daga hannunta sama tana addu'ar neman shiriya ga mijinta A ranar sai tsakar dare Musaddik ya dawo gidan, tana sallar nafila ya dawo cikin maye,don haka ko ta kanta bai bi ba, ya wuce ya yi kwanciyarsa da takalmi a kafarsa. Sai da ta idar da addu'o' inta ta zo kwanciya, sannan ta cire masa takalman. Amma irin warin da Musaddik yake yi, ya hanata kwanciya kusa da shi,duk da tun dazu take jinta cikin matukar sha’awar mijinta. sai falo ta dawo ta kwanta akan kujera, tana zubar da hawaye, Bakinta na fadin lahaula wala kuwwata illa billah, domin sanin wannan addu’ar tana da matukar tasiri wajen korar dukkan damuwa. Kullum Musaddik bata mata rai yake yi da dabi'o' insa, amma har yanzu zuciyarta ta kasa tsanarsa, maimakon haka ma tausayinsa ya fara haifar mata da kaunarsa, don yadda take jin Musaddik yanzu a ranta tasan tana sonsa domin tabbas ba don wannan halin ba. Musaddik mutum ne. kuma miji ne da ko wace mace zata so samunsa a matsayin miji. Tun safiyar ranar da za'a gudanar da zaben, Afrah ta sami kanta da matukar faduwar gaba da kuma damuwa, domin gaba daya ba ta gamsu da yanayin da mijinta ya fita ba, don haka bakinta ya kasance cikin addu’a, Page 143 Ta bangaren Musaddik kuwa, yana can tare da mukarrabansa suna bin mazaba-mazaba suna aikata abinda aka umarcesu da aikatawa, inda suka ga Hajiya Hudah za ta ci. Su kan daga ma wajan kafa, inda ko ba za ta ci ba, da sun ga alamar haka, to su kan tada fitina a wajen. Ta hanyar dukan mutane da kuma kone - kone, a yayin da duk bayan mintuna Alhaji Hamza da Hajiya Hudah suna buga masa waya, domin jin halin da ake ciki. Abu ya kai makura fitina ta yi kamari , domin har an fara rasa rayuka . Jama"a sai gudu suke yi. Domin tsira da rayukansu. Nan da nan Kafin ka ce meye wannan? "Yan sanda sun cika duk wajen da akwai matsala. Haka nan suka shiga kama jama'ar wajen a Kokarin su na kawo karshen fitinar, cikin wadanda aka kama kuwa har da Musaddik da kuma wasu tsirarun abokan aikinsa. Wannan kamun ko a kwalar rigar Musaddik, domin dai ya san yana da wadanda za su fito da shi, don ya san Alhaji Hamza ba zai taba barinsa a hannun Yan sanda ba, don an yi hakan ya fi a kirga. Tunda ya dade yana aiki da Alh Hamza ko ba’a kan siyasa ba. Tunda Afrah ta fahimci fada ake yi, domin yadda garin ya yi shiru, sai warin tayoyin da ake konawa; ka na daga cikin gida ka na hango inda wuta ke tashi, tana rimi, tuni hankalin Afrah ya yi mummunan tashi, fatanta daya. Allah ya sa fitinar ba ta rutsa da Musaddik ba. Ta kasa zaune, ta kasa tsaye damuwa ta kusa kaita kasa. Page 144 A yayin da ta kira wayarsa ya fi sau a kirga amma wayar na kashe, tun daga lokacin hankalinta ya kara tashi, har dare ba Musaddik, ba alamarsa , duk da a lokacin gaba daya abubuwa duk sun lafa, da taimakon Jami’an tsaro komai ya dawo dai-dai. Tana ganin zuwa lokacin ya kamata ace Musaddik ya dawo gida. Amma har gari ya waye, bai dawo gida ba.Zuwa yamma damuwar Afrah ta Kara fadada, ta kasa ci ko sha. a daddafe gari ya Kara wayewa, kwana biyu kenan babu duriyar mijinta, tasan yakan kwana baya gida amma wannan karon tana ji a jikinta ba lafiya ba.hakurinta da dauriyarta sun kare don haka ta fito daga bangarenta zuwa bangaren Haj kilishi. kai tsaye falon Hajiya Kilishi ta nufa. Ta tadda ita tare da Hajiya Rakiya suna zaune suna hirar hatsaniyar da ta faru shekaranjiya. Yadda Afrah ta fado falon a gigice, ya sa Hajiya Kilishi ta waigo ta dubeta a firgice, tana ganin itace ta canja fuska tace “ke lafiya zaki fado ma mutane falo haka, menene?” Afrah ta dakata tana kokarin mallakar nutsuwarta, zuciyar ta kuma tana tunatar da ita alwashin da ta ci na cewa ba zata nemi taimakon haj kilishi akan komai ba, sai dai kuma wata zuciyar tana gaya masa ba bu abinda ba zata yi ba saboda musaddik, don haka tace cikin sanyin murya, "Ki yi hakuri Hajiya. Ina cikin matsala ne, na san kuma za ki iya taimakawa, shi yasa na zo gare ki” Haj Kilishi ta dubi Hajiya Rakiya da take yatsina fuska ta ce “Me yafaru?” Afrah ta dan gyara tsayuwarta, sannan tace "Hajiya, tun shekaranjiya da Yaya Musaddik ya fita wajen zabe bai dawo gida ba, shine na ke cikin fargabar ko hargitsin daya faru ya rutsa da shi ne, saboda wayarsa tana kulle bata shiga” ''To shi ne ki ka zo guna na yi maki me?"Cewar Hajiya Kilishi. Cikin isa da gadara. Duk da naganar ba ta ma Afrah dadi ba, bai hanata kara Page 145 marairaice murya ba tace "Shine na zo ki taimaka min,kisa hannu tunda hannu daya baya iya daukar jinka, ki tayani binciken inda yake, tunda nasan kina da hanyoyin da zaki iya sanin inda yake”. Cikin fusatar da Afrah ta rasa dalili Haj kilishi tace, "Tunda ni gidan Rediyo ce ko? Ko gidan jarida , Ina ruwana da rashin dawowarsa gida, kuma ke akan lamarin Musaddik, ai kin wuce hannu daya, hannu miliyan ce, meye na karaya Kuma yau ba kin ce kin ji, kin gani ba. Kuma banda ma iya yi da neman magana irin naki, da kuma kokarin dora min wahala yau Musaddik ya fara fita ya je ya kwana bai dawo gida ba? Dan iska har wani damuwa za ayi da halin da yake ci, bayan kowa yasan yana can wajen iskancinsa hankali kwance”, Hajiya Rakiya ta yi tsaki ta ce "Ni ba Karamin firgita ni ta yi ba, meye wani Musaddik da za ki tashi hankalinki, don kawai bai dawo gida ba, sai kace yau ya saba. Don Allah ki sassautawa kanki wannan wahalar tun kafin ki kai ga faduwa”. Haj kilishi tace “To ai ni ban ma gane hausar wai na taya ki binciko inda yake ba, to ni ina da abin yi, ba zaman banza na ke yi ba, balle ki ce kin ga ina zaman banza ne, ki ka ba ni aikin yi. Musaddik Allah ya dawo miki da shi lafiya, amma ni babu abinda zan iya yi miki." Afrah da take tsaye, zafin maganganun su Hajiya Kilishi ya tilasta ma idanunta fitar da wasu zafafan hawaye. Zuciyarta tuni ta cika da badama da danasanin kawo kanta wajen Haj kilishi don ba don ta kawo kanta ba babu yadda za’ayi su kara mata bakinciki a kan wanda take ciki.Hajiya Kilishi ta juya gun Hajiya Rakiya suka ci-gaba da maganganunsu, suka bar ta nan tsaye, tamkar babu wata halitta a cikin falon bayan su. Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 146 Ahankali Afrah tana goge hawayenta, ta fito daga falon, wanda lokaci daya Hajiya Kilishi da Hajiya Rakiya suka barke da dariya, me cike da wulakanci.Hakan ko ba karamin Kara Kona ran Afrah ya yi ba.A daddafe Tana shiga daki ta fada kan kujera ta cigaba da kuka me motsa zuciya, daga bisani, ta tabbatar kukan bazai amfaneta da komai ba , don haka ta tashi ta wanke fuskarta, ta dakko hijabinta ta zura, ta daura nikaf dinta, ta fito dai-dai kofar get ta hadu da Baba Maigadi.Ganin yanayinta. Ya tilasta masa yi mata magana, domin Baba Mai-gadi ya damu da lamarin Musaddik kwarai da gaske,domin tun kafin a haifi Musaddik yake gadi a gidan har zuwa yanzu da tsufa ya kama shi, duk irin rayuwar da Musaddik ya shiga, ya sani, yana daya daga cikin masu masa addu'a, masu kuma damuwa da lamarinsa. "Lafiya dai ko Afrah, za ki fita cikin ranar nan?" Afrah ta dan daidaita muryarta tana kokarin boye damuwarta tace “Baba fitar ni ma ta dole ce, ba ka lura ba yau kwanan Yaya Musaddik biyu, bai dawo gida ba, kuma wayarsa tana kashe”,Ya jinjina kai cikin damuwa sosai yace "Na sani Afrah, domin har wayarsa na Kira ni ma domin naji inda yake, amma ni ma a kashe nake jinta a duk likacin da na kira, na shiga damuwar ko hatsaniyar da aka danyi na siyasar nan shekaranjiya ta rutsa da shi be”.Afrah tace “Dama ni ma fargabata daya ce irin taka , kada ace ya fada cikin hayaniyar, hankalina ya tashi matuka domin bansan a wane hali yake ciki ba” Ya ce "Dole ki damu, to yanzu menene mafita? Ya zamuyi mu san yana wane hali ne”, Afrah ta rausayar da kai tace “Eh to na bukaci Haj ta taimaka tasa hannu tunda tana da hanyoyi amma ta nuna ba zata iya taimaka min ba Page 147 don haka yanzu na fito zan je na dudduba (Police Station) mafi kusa ko zan dace da sanin halinda yake ciki” Tausayi da sha'awar halayenta suka kama Baba maigadi ya gyara tsaiwarsa yace “Allah ya yi miki albarka, amma ke ma ai kin san Hajiya ba za ta taimaka miki da komai ba akan Musaddik. Allah dai ya takaita wahala yasa baya cikin wata masifar , ni ba don kada na sami matsala da haj ba, ai da na tafì tare da ke mun neme shi ko Allah zaisa mu dace” Ta girgiza kai tace “A'a Baba kada na ja maka matsala, ka zauna kawai abin ka, zanje ni kadai, na gode da kulawarka”. tana gama fadan haka Ta juya ta fice da sauri A yayin da ya bita da kallon tausayi, tunda yake bai taba ganin muguwar mata irin Haj Kilishi ba, ta maida dan kishiya marayan Allah, ya zama abokin gabanta, ta sa shi a ranta, me yasa mata suke maida dan kishiya abokin gabansu ne?bayan shi da na kowa ne, domin baka san wa zai more shi ba, babu ruwan yaya da kishin da ke tsakanin iyayensu.batun yau ba zuciyarsa bata yi masa dadi akan yadda Haj kilishi ke tafiyar da rayuwar musaddik, kamar yadda dabi’unsa na yanzu suke tayar masa da hankali. Domin har yanzu ya kasa yarda da cewa gata ne ya maida Musaddik haka. Akalla fitar Afrah ta je (Police Station) kusan hudu, tana cigiyar Musaddik, amma ba ta same shi ba ba ta kuma sami labari a kansa ba. Ko kadan bata son tayar ma da mahaifinta hankali kamar yadda nata ya tashi shi yasa bata son ta gaya masa halinda ake ciki, amma dole yasa ta ga sai ya sani domin tasan duk duniya bata da wani mataimaki bayan mahaifinta.Ana kiran sallar magariba ta isa gidansu. A kofar gida ta tadda Malam Mahmud yana alwala, ta tsaya har ya idar da alwalar. A cikin damuwa ya dubeta, domin jikinsa ya gama gaya masa ba lafiya, ya dubeta a sanyaye yace “shiga cikin gidan, ki yi sallah, zan je masallaci, idan na fito zan same ki”, Cikin dishewar murya Afrah tace Page 148 "To, a dawo lafiya." Sannan ta shiga gidan.Mama Hauwa na kwasar tuwo. Na'ima na zaune kan tabarma a kofar dakin Mama Hauwa Tana shigowa. Mama Hauwa ta katse fara' ar fuskarta, ta yi kicin-kicin da rai daker take amsa gaisuwarta, ganin hakan ya sa ta koma kan kujera 'yar tsugunno a kofar dakin mahaifinta ta zauna cike da damuwa, ba daman ta yi sallah, tunda yau ta tashi da fashin sallah.sai dai bakinta baya rabo da ambaton Allah wato zikiri. Bakin Mama bai bude ta tambayeta dalilin zuwanta gida a wanna lokacin da ba ta saba zuwa ba, wanda da yar da ta haifa ce da tuni tabar duk abinda take yi ta dawo gareta domin ta ji dalilin zuwanta. kamar yadda Na'ima ko magana ba ta yi mata ba. Ka'idar Malam Mahmud sai ya yi sallar Issha'i, sannan yake dawowa gida, amma yau ana idar da sallar magariba ko addu'a bai tsaya yi ba, saboda ya matsu ya ji damuwar *yarsa, ya dawo gida Ya bukaci a shimfida masa tabarma. Mama Hauwa ta dube shi tace "Hmmm Ka dawo da wuri ko a kawo tuwon yanzu?" Ya dubi Afrah ya ce "Eh, na dawo ne, saboda Afrah, bar abincin sai anjima" Mama Hauwa ta tabe baki, ba tare da tace uffan ba. Ya Kara kallon Afrah, sannan ya ce “Afrah kin ci abinci ne?" Ta girgiza, kai alamar ba ta ci ba. Agaggauce ya kwala ma Mama Hauwa kira, wacce tuni tabar wajen, ta amsa gami da tahowa, ya dubeta ya ce "Ki ba Afrah abinci ta ci”. Ta yi mata wani irin kallo ta ce "Oh cewa ki ka yi ban ba ki abinci ba?" Ta yi saurin girgiza kai ta ce. "A'a ban ce masa komai ba, tambayata kawai ya yi na bashi amsa”, ta fadi maganar cikin nuna alamun rashin son yin hayaniya, mama Hauwa Ta saki tsaki ta ce Page 149 “Idan ma kin gaya masa ban baki abinci ba , wannan matsalar ki ce, tuwo na ban sa da ke ba, san da ki ka shigo kuma na riga na gama kwasa, tunda ban san za ki zo ba, to nawa ki ke so na dauka na baki, hamshakiya “ Malam Mahmud ya ce a fusace "Ki ba ta nawa ta ci”, Afrah ta gurgiza kai da sauri tace “A’a Baba ni bana jin yunwa a koshe na ke". Mama Hauwa tayi saurin cewa “To ka ji, a koshe take” .Ya yi mata wani mummunan kallo yace "Na ce ki dauko min abincina ko” Ganin fusatar dake kan fuskarsa yasa Ta juya itama a fusace tana fadin "Kai ka sani, ina ruwana cikinka nefa, ba nawa ba. Ke Na’ima dauko abincinsa ki kai masa” Tana gama fadin haka, ta shige dakinta, Yayin da Na’ima ta dauki abincin ta je ta kai masa, ita ma tana ajewa ta shige daki. A hankali Afrah ta goge hawayen da ke fita mata a ido. Rana zafi, inuwa kuna. Malam Mahmud ya tabbatar mata ba Zai saurareta ba, har sai ta ci abinci ta koshi, hakan shi ya tilasata mata cin tuwon, tana ci, amma tamkar tana cin guba ne, domin babu abin da ke mata dadi a bakinta. Sai bayan da ta kammala, sannan ya bukaci jin abinda ya kawota gida a cikin wannan daren, duk da zuciyarsa ta gama gaya masa matsalar musaddik ce A hankali Afrah ta gaya masa komai. Ta kara da cewa “bayan fitowa ta gida na je (Police Station) har guda hudu, amma ban same shi ba, shine na ga ya dace na zo na gaya maka tunda ban da wanda zai taimaka min sai kai” Page 150 Damuwar Malam Mahmud ta Kara yawa Ya gyara zama yana lissafin ta inda zai fara lokaci daya yana cewa “Daman Haj kilishi ai ba za ta iya taimakawa akan

Chapter 9 of 15