Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MUSABBABI. NA HAJ. HABIBA ABUBAKAR IMAM https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=H7yQptZbm29jaY6x Page 1 Fateema Mahmud wacce aka fi sani da Afrah, a sakamakon sunan kakarta ta wajen uba da ta ci, nagartacciyar yarinya ce, kyakyawa haifaffiyar garin Minna. Mai cikar kamala, hakuri, juriya, sune manyan halayenta na-gari abin koyi, sai kuma tsantsar ilimin Islama da Allah ya wadata ta da shi, domin tun tasowarta take kokarin koyon addininta, har zuwa yanzu da ta mallaki hankalin kanta. Ta zama cikakkiyar mace, domin tuni ta kammala karatunta na sakandire, tana zaman jiran sakamako ne a yanzu. Idan akwai abinda ya ragi Afrah a rayuwarta. To ba zai wuce maraicin rashin uwa ba, domin ta dandani dacin maraici tun tana 'yar shekara biyu, kuma ita ce kadai 'yar da mahaifiyarta ta haifa tare da mahaifinta Malam Mahmud. Bayan rasuwar mahaifiyarta ne, rikonta ya koma hannun matar Babanta. Mama Hauwa, wacce a matsayinta na uwargidan Malam Mahmud, tana da yayyi guda biyar biyu maza, Mansur wanda shi Page 2 ne na farko, a yanzu ma'aikaci ne a hukumar wutar lantarki, wato (NEPA). Yana rife da babban mukami, ya yi aure har da 'Yarsa daya, sai Kabir, shi kuma ma'aikacin banki ne, shi bai wuce watanni uku da aure ba, sai Naja"atu da Sakina, su ma duk sun yi aure. Na'ima ce ta rage, wacce take tsarar Afrah, duk tare suka kammala makaranta. Sai dai abu daya da Afrah ta rasa a gidan mahaifinta, shine kulawa da kowace "Ya take samu na uwa, domin irin rikon da Mama Hauwa ke mata, ba irin riko bane na amana. Wanda maraya ya kamata ya samu ba'a kowane mataki. Mama Hauwa na nuna bambanci kiri-Kiri tsakanin Afrah da 'ya' yan ta, Ko kadan ba ta kyautata mata, rayuwa take a gidan tamkar ba "yar gidan ba, duk da Malam Mahmud yana iya kokarin sa domin ganin marainiyar 'Yarsa ta samu riko me kyau daga Mama Hauwa. Amma hakan ya kasa tabbata, domin Mama Hauwa ta zama tamkar tauraruwa me wutsiya, domin shi kansa Malam Mahmud din ta fi karfinsa, ta kan yi duk abinda ta ga dama ko a gaban idonsa ko a bayan idonsa. Inna Halima wacce ita kadai ce kanwar Malam Mahmud. kuma ita kadai ce take iya Page 3 takama Mama Hauwa birki akan irin mugun rikon da take ma Afrah Hakanne ma ya sa, kusan rabin rayuwar Afrah take yi a gidan Inna Halima, domin duka ranar juma'a. Can take tafiya, sai ranar lahadi take dawowa gida, wannan dalilin ya sa Mama Hauwa da Inna Halima ba sa shiri ko kadan. Makarantar Islamiyyar da Afrah take yi, anan kuma take koyar da kananan yara, saboda hazakarta. Ya Sayyadinsu Habib ya maida ita Malama, a ajin haddar Kur' ani ta kananan yara, tana daukarsu gun koyon Kur ani da Tauhid. Malam Habib shine mutum na farko da Afrah ta fara tsayawa da shi a matsayin masoyi, ta kuma amshi tayin soyayyarsa, domin yarda da ta yi da irin son da yake mata na tsakani da Allah da kuma hanyar Ubangiji da yake doreta akai. Hakan ya sa take da tabbacin cewa daga gare shi za ta sami kyakkyawar rayuwa, ko ba kudì da jin dadi, to idan har akwai Allah a cikin rayuwarsu, to ya ishesu daga dukkan komai, don haka ta tsayar da zuciyarta gun mutum daya, wato Ya Sayyadinta Habibu. Page 3 Yau asabar ne Afrah tana gidan Inna Halima, yau gyara take mata na gidan gaba daya. Inna Halima tana gefe a zaune, duk inda Afrah ta yi, tana bin ta da kallo, tana matukar sha'awar yarinyar da halayenta, domin duk inda ake neman yarinya me hankali wacce ta rike maraicinta, aka sami Afrah, to an wuce wajen. Tana matukar jindadin kasancewa da Afrah, a duk sanda ta zo gidanta, ta daina aikin komai, duk abinda za ta yi Afrah, ta kan dauke mata, hatta girki ba ta yi, ta kan dauke mata komai. Inna Halima. na tsaka da yin wannan tunani aka bugo kofa da Karfi. Musaddik ya fado cikin gidan, tamkar wanda aka jefo ba tare da sallama ba, Inna Halima ta mike tana kallonsa 'Musaddik". Ta Ambaci sunansa da karfi, a yayin da Afrah ta yi saurin ja da baya, domin kar ya bugeta. Musaddik nagartacce,kuma kyakkyawan matashi. wanda ya hada komai da za ka iya kiransa da jarumin matashi, sai dai kallo daya za ka yi masa. Ka san ya rasa wani ginshiki na rayuwarsa, wanda ya hana shi damar da za'a kira shi da mutumin kirki, ba shi da natsuwa, da ganinsa ka ga wanda ya yi nisa a shaye-shaye, ko a yanzu ba'a cikin hayyacinsa ya ke ba. Page 4 "Inna abinci na ke so,yunwa nake ji” ya fada da wata irin budaddiyar murya Inna Halima ta yi ajiyar zuciya, sannan ta kalli Afrah ta ce "'Afrah aje tsintsiyar nan, ki zubo ma yayanki abinci.” A hankali ta yi kasa da tsintsiyar, sannan a sanyaye ta wuce kicin. Inna Halima ta maida kallonta ga Musaddik, wanda yake tsaye ya nannade kafafun wando tace "Zo ka zauna" Ta nuna masa tabarmar da ke shimfide, ya wuce da takalmi da komai ya zauna akan tabarmar, ba ta damu ba, domin ba yau ya saba yin hakan ba, ta ja kujerar da ta tashi akai, ta koma ta zauna tana kallonsa. Tana saka abubuwa da dama a ranta. •Har zuwa lokacin da Afrah ta dawo dauke da faranti cike da shinkafa da miya da ta dafa,a hankali ta aje a gabansa, sannan ta juya ta wuce Zuciyarta cike da tsananin tausayin Musaddik da halin da yake ciki. Musaddik yace "Inna na kan so na zo cin abinci gidanki duk ranar sati, saboda na san Afrah tana gidan nan, ina jindadin abincinta, komai rashin gyaransa” Maganar Musaddik ta katse mata tunani da take yi ta juyo da idonta tana kallon sa, a yayin da Inna Halima ta jinjina kai tace Page 5 "Ba kai kadai ke jin dadin girkin Afrah ba, kowa yana yabawa, tun daga kan yara har zuwa maigidan kansa.” Ya yi dan murmushi, a yayin .da yake cin abincin, ya dan waiwayi inda Afrah take wacce Ke cigaba da karasa shara ya ce, "Haka ne Inna, shi ya sa ni ma na kan kwaso yunwata zuwa gidanki. Don na san idan na ce kwadayin girkinta zai dinga kai ni gidansu kullum, za mu sami matsala da Mama Hauwa, don na san farantina ba zai dinga cika ba kamar yadda yake cika a gidanki." Gaba daya suka yi murmushi, a yayin da ya maida hankali kan cin abincinsa. Inna Halima kuma tana zube masa da ido, tana matukar tausayin Musaddik da kuma rayuwarsa wacce bata taba tsammanin zai koma haka ba. Duk tsananin Kamun kansa ilimi da cikar kamalarsa. Amma rana tsaka rayuwarsa ta koma haka. a lokacin da ya kamata ace rayuwarsa ta inganta, babu wanda zai ga Musaddik ya yarda ya kuma amince Musaddik din da ne, lamarin yana da matukar daure kai. Inna Halima ta yi kasa da murya à hankali, ta fara yi masa magana "Musaddik, anya ka na ganin wannan rayuwar da ka dora ma kanka za ta kai ka ga hanya madaidaiciya, wannan wace irin rayuwa ce? Da mutuncinka da darajarka, rana tsaka duk ka kore wannan, ka koma ka na Kaskantarciyar Ku dakace ni YAR GIDAN IMAM bazan yarda da rashin yin comments ba don wallahi ina iya barin yin posting din idan bakwa comments. MUSABBABI NA HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=8hYIJhGWi10v_gOI Page 6 rayuwa mara dadin ji ko gani, shin meye dadin wannan rayuwar? A hankali Musaddik ya cire cokali a cikin abincin, fuskarsa gaba daya duk ta canza ya shiga cikin damuwa, ya ce a sanyaye, "Inna babu wani dadi ga rayuwar da na ke ciki, hakia inda ina da ikon canja hanyar da na biyo, da na yi gaggawa na canja, domin ko kadan ban jin dadin rayuwar. Amma na rasa dalilin da ya sa na kasa yaki da zuciyata na daina, duk da ina kyamar abinda na Ke aikatawa ni ma,” Inna Halima ta jinjina kai fuska cike da tausayinsa tace "Ka yi yaki da zuciyarka ne, ka dage ka kori shaidan, domin hakika shine yake yi maka huduba, ka tuna irin gata da arziki da ka taso a ciki Musaddik kayi tunanin irin girma da kamalarka da dubban jama' a suke gani a da, sannan ka tuna irin ilimi da hangen nesa da ka ke da shi wanda a yanzu duk sun tattara sun gudu, a sanadiyyar tsarin rayuwarka da ka canja, ka duba ka ga yadda ka maida kanka, hakika lamarinka na damun mu, yana kuma daure mana kai kwarai da gaske Afrah da ke tsaye gaba daya sai ta juyo ta dora ma Musaddik idanunta wadanda suka cika da hawaye, zahiri tana daya daga cikin wadanda lamarin yayanta Musaddik ke damu, ta kan shiga Page 7 dimbin damuwa da tunani idan ta tuna halin da yake ciki, Sannan ta kan rasa inda zata sa kanta, idan ta kasa gane dalilin canjawar Musaddik, mutumin da ya taso da nagarta, kamala, natsuwa, ilimi da matukar hangen nesa, tana daya daga cikin wadanda rayuwar Musaddik ke matukar burgewa. Yana matukar ba ta sha'awa, rayuwarsa da yadda yake tafiyar da lamuransa, abin a tsaya a kalla ne a kuma yi koyi da su.amma meya kawo wannan canjin?. "Inna kada ku gaji, ku yi ta tayani da addu'a don Allah". Furucinsa ya Kara dasa tausayinsa a zuciyar Afrah. Inna Halima ta ce "Addu'a muna nan muna yi Musaddik. Allah ya shiryeka, ya dawo da kai hanya madaidaiciya, ba za mu gaji da yi maka addu'a ba." Ya gyada kai ya ce "Na gode Inna, bari na tafi” inna Halima tace "Ka karasa cin abincin mana” Ya girgiza kai lokaci daya yana mikewa. "Na koshi Inna, na gode.” Ya juya ya dubi Afrah Yace "Na gode da girki,." Yana gama fadin haka, ya juya da sauri ya fice. Inna Halima ta numfasa cike da damuwa tace "Allah ka yi mana maganin abinda ya fi karfinmu." Afrah ta amsa da "Amin."Sannan ta juya ta ci-gaba da aikinta,amma zuciyarta na cike da tunanin Musaddik da tausayinsa, domin ta san hakika yana bukatar taimakon addau'a, ta kuma kara shan alwashin Page 8 za ta ninka akan addu'ar da take yi masa Haka ta kasance cikin tunaninsa da tausayinsa a wannan ranar kamar yadda ta saba a duk lokacin da suka hadu da juna. Washegarin lahadi. Inna Halima sai dare, sannan ta sa Afrah a gaba zuwa gida, domin tana son ganin Dan’uwanta Malam Mahmud, hira suke yi a hanya har suka isa gida. Dawowar Mallam Mahmud kenan daga masallaci sallar Issha"i, fuskarsa ta fadada da fara' a yana kallon "Yar-uwarsa, ya ce. "'Halima, ai na dauka "yar ta ki sai gobe za ta dawo, da na ga dare ya rufa? “ Ta yi murmushi, tace “a’a yaya. Na ce ta jirani ne mu taho tare, saboda ina son ganinka, na san kuma iyanzu ne zan sameka a gida a tsanake” Ta karasa maganar tana zama a kan tabarmar da yake zaune akai. A yayin da Afrah ta durkusa ta gaishe shi, Cike da so da Kauna ya amsa mata, sannan ta wuce dakin Mama Hauwa, domin ta gaida ta, amma haka nan ta amsa ba yabo ba fallasa fuska a hade, Na'ima ko tana kwance akan gado ko kallonta ba ta yi ba harta fice ta shige dakinta. Mallam Muhmud ya dawo da kallonsa ga Inna Halima bayan sun gama gaisawa, sannan ya ce “Halima ina fatan dai lafiya ki ke son ganina, da daddaren nan?"' Inna Halima ta gyara zamanta Page 9 Tace “Yaya ba wani abu bane dama magana ce na ke son mu yi akan Musaddik". Mallam Mahmud ya jinjina kai ya ce "Ya kara dakko wata maganar ne?” Ta girgiza kai Ta ce "*A'a, babu abinda ya yi, kawai dai wani tunani na yi akan halin da yake ciki, wanda yaya ka fi kowa sanin duk duniyar nan. Mu ke nan mu uku iyayen mu suka haifa, daga kai sai marigayiya Harirah mahaifiyar musaddik sai kuma ni, yadda ba za mu so mu ga 'ya ' yan da muka haifa cikin wata fitina ba. Haka shi ma. Musaddik ba shi da kowa duk duniyar nan sai mu, kuma mu kadai ne ba za mu juri ganinsa cikin wani hali ba, don ina da tabbacin da mahaifiyar sa ce take a matsayinmu. Ita ma sai inda karfinta ya kare akan 'ya yan mu, shi kadai ta haifa a duniya kuma shine sanyin idaniyarta, don haka duk yadda za mu yi, ya zama dole a kanmu mu yi kokarin daidaita rayuwarsa. Malam Mahmud ya numfasa, damuwarsa ta Kara fitowa fili. Ya ce "Halima kin fi kowa sanin duk duniya ba ni da wata damuwa da ta wuce -damuwar Musaddik.ina cikin tsananin tashin hankali akan rayuwar da yake yi, ina kuma takaicin yadda na kasa taimakonsa akan ya natsu, babu kuma abinda ba zan yi masa ba,matukar zai shiryu domin ba ni da wani burin da ya wuce haka, duk addu’ata akan musaddik take karewa Halima”. Ku dakace ni YAR GIDAN IMAM Bazan yarda da rashin comments ba don wallahi zan iya daina posting din idan bakwa yin comments. MUSABBABI Na HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=z2twfJh8yZkWrt_r Page10 Inna Halima ta numfasa gami da gyara zamanta ta ce "Ni Yaya akwai hanyar da na ke ganin wata Kila zai iya zama sanadiyar shiryuwarsa". Mallam Mahmud yana kallonta yace “Wace hanya ce wannan?” Ta dan muskuta tana kallonsa sosai sannan tace “Aure, yi ma Musaddik aure ina ganin zai iya zama wata hanya ta samun nutsuwarsa, domin duk rashin jin namiji , idan ya yi aure ko yaya ne akan samu sauki, ko bai daina abinda yake yi duka ba, zai rage". Mallam Mahmud ya ce. "Haka me, aure hanya ce ta samun natsuwa, zai kuma iya canja wa rayuwarsa tsari, amma ba anan gizo ke sakar ba, wacece za ta aure shi, kada ki manta a dalilin halinsa ya rabu da matarsa, sannan tun daga lokacin babu wata da ta karav sauraronsa, saboda ba shi da natsuwa, to yanzu ina zai samo mata shi da ko lokacin kansa baida shi balle lokacin wata, wace ce za ta yarda da shi har ta aure shi a haka?" Inna Halima Ta ce. "Tabbas! Abinda kamar wuya, samun me auransa, domin kowace mace burinta ta sami kintsattsen namiji. Domin ta samu kwanciyar hankali a gidan auranta, don haka yaya ya zamar mana dole mu yi sadaukarwa saboda zumunci.?” Malam Mahmud ya dubeta cikin rashin fahimta Yace “Sadaukarwa? ban fahimce ki ba”Inna Halima ta ce "Ina nufin dole a cikin 'ya' yan mu mu sadaukar da daya ga Musaddik ya aura, mu yi aikin zumunci”, Ta gyara zamanta fuskarta ta canja alamun damuwa ta ce. Page 11 "Ban taba jin ciwon ba ni da ya mace ba irin yau, amma ko'ina da 'ya macen ma, yaya ka san, babu aure tsakaninta da Musaddik tunda Musaddik ya riga ya sha nono na, amma yaya me ka gani akan shawarata?" Mallam Mahmud ya dubeta ya ce "Shawararki ta yi, abar kuma dubawa ce, kuma kada ki kara tunanin ba ki da 'ya mace, domin 'yayana naki ne haka zalika hada Musaddik aure da yar’uwar shi kadai ya kamata, domin 'yar-uwarsa ita kadai ce zata rufa masa asiri, za kuma ta yi hakurin zama da shi”. Inna Halima Ta ce "'Haka ne". Ya ce "Saboda haka, zan hada shi da Na'ima, tunda ita ce gaba da Afrah, Inna Halima ta yi murmushi sosai. tace “Allah ya saka da alheri ya kara dankon zumunci, yasa sanadiyyar shiryuwarsa ce” Yace "Haba Halima wannan duk yi ma kai ne, na kuma gode da wannan tunanin naki, wanda ni ban yi irinsa ba, na kuma ba ki damar ki yi magana da Musaddik ki gaya masa hukuncin da muka yanke" Ta ce “In sha Allahu zan yi magana da shi." Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa na dan wani lokaci kafin su yi sallama ta tafi, ba tare da sun gaisa da Mama Hauwa ba, yadda ba ta fito sun gaisa ba, haka nan ita ma ba ta bita daki sun gaisa ba, dama sun saba yin hakan. Page 12 Washegari bayan sallar azahar, Afrah na zaune tana wanke-wanke. Na'ima kuwa dawowarta kenan daga gidan kitso, tann zaune akan kujera Yar tsuguno tana latse-latsen waya. Mallam Mahmud ya yi sallama ya shigo. ya dawo daga masallaci, cike da tausayawa ya dubi A frah ya ce. "Sannu da kokari, har yanzu ba ki samu hutawa ba, kin yi sallah dai ko?" Ta amsa “Na yi sallah Baba” ya jinjina kai zai wuce “Sannu da zuwa” Cewar Ni'ima, ya dubeta fuska tamke ya ce. "Yauwa, ke ba kya aikin komai ne?" Kafin ta yi magana Mama Hauwa ta cafke a lokacin da ta Ke fitowa daga daki "Ta gama nata, ko shi ma aikin sai ansa ido a kansa?” Bai Kara magana ba har ya isa kofar dakinsa, sannan ya Kwala ma Mama Hauwa kira, kai tsaye ta nufo inda yake ba tare da ta amsa ba. "Ga-ni” ya dubeta gami da girgiza kai sannan ya ce. "Ba ni abin zama, magana za muyi me muhimmanci” Nan ma ba ta amsa ba, ta shige ta dauko. tabarma ta shimfida masa ya zauna, ita kuma ta jingine jikin katanga tana kallonsa. "Wace magana za mu yi?" Ya ce a yayin da yake kallonta "Ina bukatar natsuwarki, domin magana za mu yi kamar yadda na gaya miki kuma me muhimmanci ce maganar” tace "To ai ina jinka." Yace “Dama maganar Na'ima ne, ina ganin lokaci ya yi daya kamata Page 13 ace ta yi aure, don haka na yanke shawarar ni da Halima akan zan hada ta aure da Musaddik”, Haka nan Afrah ta ji gabanta ya fadì, wanda ta rasa dalilin hakan, sai dai ta ji ta sami kanta da matukar tausayin "yar-uwarta, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma ya zama dole ta tausaya mata, domin ta san auren miji irin Musaddik hakika rashin dace ne ga ko wace ya mace. Mama Hauwa ta zaro idanu waje, tamkar za su fado kasa, bakinta na tsuma ta ce "Wane Musaddik din?” Yana kallonta yace "Musaddik din har nawa garemu? Musaddik dai nawa mana” Mama Hauwa ta saki salati tana tafa hannu, Tace “Eh, sai yau na kara tabbatar da cewa Malam baka son yayana,sannan Halima ba zata taba barina na zauna lafiya ba, yau ko maza sun kare kaf a duniya. Me Na'ima za ta yi da Musaddik? Sakaran yaro mara natsuwa, babu wanda bai san halin da yake ciki ba na barbada, da can sanda yake na kwarai me ya, sa ba ka yi tunanin hada shi auran da "yarka ba, sai yanzu daya zama lalatacce. Sanda yake da kumbar susa yake shiga mota yana fita, ai ba ka ce za ka ba shi 'yarka ba, duk da a lokacin har tayin Sakina na yi maka, akan ya aureta Ka ce ya riga ya sami mata, ba kuma zaka tursasa masa ba, yanzu ina matar, halinsa ya koreta, ya zama shakulatin bangaro, Page 14 sai da ya zama mara amfani shine za ka ce Na'ima ta aure shi, to ba ka isa ba." Malam Mahmud ya nuna kansa ya ce "Ban isa ba a matsayina na ubanta?" Ta turo baki. "Eh, in dai akan wannan maganar ne ba ka isa ba, kada ma ka kara furtawa. Na'ima ta fi karfin Musaddik, ko shi ne autan maza ba za ta aure shi ba." Mallam Mahmud ya fusata ya ce. "To zan ga wanda ke da iko da ita tsakanin ni da ke, domin na riga na gama magana, na ba Musaddik Na'ima.” Mama Hauwa ita ma ta fusata, bakinta na kumfar masifa tace "To za mu ji, za mu gani, wai an binne tsohuwa da rai, domin in dai ina raye Na'ima ba zata auri wannan tambadaddan yaron ba, aniyarku duk zata bi ku kai da Haliman” Ta juya fuuu! Ta tafi. Malam Mahmud ya tashi ya bude dakinsa ya shiga cike da matukar bacin rai. A yayin da Na'ima ta saki tsaki ta mike tana turo baki, tana kallon Mama Hauwa "Allah Ya yi min tsari da wannan mutumin, lallai babu kauna tsakanina da Baba”, Mama Hauwa ta yi tsaki ita ma ta ce "In dai kauna ce, ai baya kaunarmu gaba daya. Musaddik din me. Allah ya tsari gatari da saran Shuka, wuce ki shiga daki” Na"ima ta shige daki tana surutai na rashin tarbiyya da ilimi. Haka Mama Hauwa ta wuni a cikin gidan tana sababi, wanda duk akan Afrah ya kare. Ku dakace ni YAR GIDAN IMAM Bayan yarda da rashin comments ba, wallahi ina iya daina posting din idan ba zaku dinga yin comments ba. MUSABBABI NA HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=6OcF1jmDVM1SQHTK Page 15 harara da hantara da sa aiki duk Afrah ta sha su a ranar, don dai Mallam Mahmud ya tanka, ta kara juye kwandon masifarta a kansa, duk dalilin haushin hukuncin daya yanke akan Na'ima, A yayin da Inna Halima a ranar dai ta nemo Musaddik ta zauna da shi, ta yi masa bayanin duk hukuncin da suka yanke a kansa. Musaddik ya mumfasa gami da kallon Inna Halima. Sannan ya ce "Anya Inna ki na ganin Mama Hauwa za ta amince da wannan maganar, idan akayi la'akari da abinda ya faru a baya a game da sakina kuma ki na ganin ita kanta Na'ima za ta yarda ta aureni, a halin da na ke ciki a yanzu?" Inna Halima ta gyara zama cike da damuwa tace "Wannan duk ba damuwarka bace, kawai kai ma na gaya maka ne saboda ka sani, ba don mu zauna muna tattaunawa ba, abinda muka yanke kenan saboda wannan halin da kake yi ya na neman ya tagayyara duk kan tunanin mu, muna tunanin kuma wannan hanyar itace kadai zata iya taimakon mu dawo da kai hanya madaidaiciya, don haka babu ruwanka da abinda Hauwa zata yi, tunda Na’ima ba yarta bace ita kadai ba”. Ya gyada kai fuska cike da jimamin wai yau shine ake nema masa matar aure sabida babu wacce zata iya da shi, idan ya tuna yadda mata ke turo kansu a da wajensa, yakan ji komai ya tsaya masa a rai. A hankali Yace “Shi kenan Inna. Allah ya yi mana zabin abinda ya fi zama alheri, nagode da kokarinku a gare ni” Ta jinjina kai, cike da karin tausayinsa ta ce “Amin Allah kuma ya sa sanadiyya ce ta shiryuwarka, Allah ya rabaka da wannan 'mummunan halin, ya dawo maka da matsayinka na da “ Ya amsa a sanyaye, “Amin” sannan ta kara dubansa tace, "Zuwa yau da daddare ko gobe ina son ka bulla gidan Kawun naka, domin ka yi magana da Na'ima ka kuma samu Kawun naka, ka yi masa godiya tare da nuna masa amincewarka akan hukuncin mu” Yace “To zan yi kokarin yin hakan."ta zuba masa ido sosai tace “Musaddik yaushe rabonka da wanka? Ka ga kayan jikinka , me yasa kake kokarin maida kanka mahaukaci ne” shuru ya yi ya maida kansa kasa , ta aje numfashi tace

Chapter 1 of 15