Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abinda ya shafi Musaddik ba, kema da gangan ki ka bukaci taimakonta amma kada ki damu, ki kwantar da hankalinki, da ikon Allah babu abinda zai same shi, zai Kuma dawo gida cikin Koshin lafiya” Karo na farko kenan da ta ji ta sami saukin damuwa domin duk addu’ar da mahaifinta zaiyi mata tasan karbabbiya ce a wajen Allah.Ta ce "Allah ya tabbatar da hakan Baba, yace "Yanzu dare ya yi babu inda zan fita nemansa amma Ni da kaina gobe zan fita nemansa, za' a kuma dace in sha Allah domin banji a raina wani mummunan abu ya same shi ba, kema kuma ki sassauta ma kanki damuwa” Ya Kara kallonta cikin matukar so da tausayi , ya ce "Tashi na maida ke dakin mijinki" tace “Toh". Daga nan ta mike, za ta je dakin Mama Hauwa, domin ta yi mata sallama, Malam mahmud ya dakatar da ita ya ce. "Ba sai kin mata sallama ba, wuce mu tafi”. Ba tare da musu ba, ta juyo suka tafi baki dayansu cikin damuwa. Yar gidan Imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️ Page 151 Ta bangaren su Hajiyn Hudah kuwa, tunda aka sanar da sakamakon zabe, suke cikin matukar farinciki mara misaltuwa, a dalilin lashe kujerar ta da ta yi, duk burinta ya gama cika.sun kasa zaune sun kasa tsaye, saboda tsananin murna sai karbar waya suke daga ko'ina, domin taya su murna. Amma duk da haka hankalin Hajiya Hudah yana wajen Musaddik, ta kasa sukuni tana matukar son ta san halin da yake ciki.Daga bisani ta samu kebewa da Alhaji Hamza, domin su tattauna, "Alhaji Hamza har yanzu ba wani labari a game da (Police Station) din da aka kai Musaddik ne?" Alh Hamza ya dan jinjina kai ya ce. “Kokarin da na ke ta yi kenan, amma har yanzu ba'a gano min Police Station) din ba, amma mutane hudu nasa su bincika min Kuma duk suna da himma nasan zasu iya nemo mana inda yake, na san za' a dace" Hajiya Hudah ta numfasa cike da damuwa tace “Ban san dalilin daya sa farin-ciki na yake raguwa ba, a duk lokacin da na tuna ba mu san halin da Musaddik Yake ciki ba, don Allah Alhaji Hamza ka yi iya okarinka, domin gano halin da yake ciki, yau Kwanaki biyu kenan fa ba wani labari. Alhaji Hamza cike da mamakin yadda ya ga ta damu akan Musaddik, matar da ya san halinta na rashin nuna damuwa akan rayuwar kowa, sai ta ta rayuwar, amma yau ji yadda duk ta gigice ta fita hayyacinta duk murnar da take ciki bata taka rawa ba wajen dakushe damuwar da take ciki ba a game da Musaddik, shin wane irin matsayi Musaddik yake da shi a wajen uwar dakinsa. Alh Hamza ya hadiye mamakinsa gami da kallonta yace “zanyi iya kokarina in sha Allah mu gano inda yake mu kuma fito da shi, tunda mun sami tabbacin yana daya daga cikin wadannan jami’an tsaro suka kama”. Haj Hudah ta numfasa tace “ Amma dai kana ganin ba zai bude baki ya fadi sunan mu bq a gaban yansanda”. Ya yi saurin girgiza kai yace “ wa musaddik ai ban taba ganin me amanarsa ba a cikin irin masu halin sa, ai da ya fadi sunan mu a gare shi gara an kashe shi,” ta lumshe manyan idanunta ta bude zuciyarta ta kara cika da sha’awar musaddik ta kara ji a ranta lalle wannan abokin tafiya ne. Page 152 Don haka ta kara gyara zamanta tace “Alhamdulillah to don Allah kayi iya yinka, domin , ba na son tun Yanzu ya fara tunanin ba shi da amfani a gurin mu ya dauka bamu damu da nemansa ba” Alh Hamza yace “ Babu damuwa, komai zai tafi yadda yakamata” Ta gyada kai ta ce "To godiya na ke sarkin yaki, ko nawa aka nema idan an ganshi zan bayar domin a fito da shi” Alh Hamza ya yi dan murmushi yace “Na sani tabbas zaki iya ba da ko nawa ne domin hakan ya tabbata “, bata ce komai ba, ya kara gyara zamansa yace “Ya shirye-shiryen party da za ki gudanar zai kasance?" Ta girgiza kai ta ce. "Batun Musaddik da gano inda yake, ya fi komai muhimmanci a yanzu ni a guna, saboda haka ba maganar Party har sai an san halin da yake ciki." Nan ma zuciyar Alhaji Hamza ta cika da mamaki irin wannan karbuwa daya samu cikin kankanin lokaci daga uwar dakinsa, abinda har yanzu ya kasa gasgatawa , ya gyada kai yace "Hakan yana da kyau. Allah ya nuna mana shi, ya takaita masa wahala” Ta amsa da "Amin". Dai-dai lokacin wayar Alhaji Hamza ta dauki kara da karfi, da sauri ya dauka, ganin daya daga cikin yaran daya sa su nemo masa Musaddik ne. Watau Isah. Daga daya bangaren Isah ya amsa “Alhaji mun gano (Police Station) din da aka kai musaddik(Police Station) din Kan Tudu ne, amma abinda me kulawa da su ya fada, shi ne zuwa gobe za’a' a wuce da su Abuja" Alhaji Hamza ya zaro ido”Abin har yayi Kamari haka ,Abuja kuma?" Ya amsa “Kwarai da gaske”Ya ce "To na gode, sai mun hadu." Page 153 Yana aje wayar ya juya ya dubi Hajiya, Hudah wacce ta tsare shi da ido duk ta kosa ya gama wayar ta ji abinda ake ciki tace “Me yake gaya maka ne?”Alhaji Hamza yace “Yana (Police Station) din Kan Tudu, kuma gobe za'a wuce da su Abuja don haka sai mu san abin yi, na san dai za mu kashe kudi masu yawa kafin fitowarsa”Haj Hudah tace "Ko nawa ne, na gaya maka zan iya Kashewa domin ya fito, tunda koma wane hali ya shiga ai akan aikin mu ne, kuma mu ne dalili, saboda haka ya kamata ka zo ka tafi asan abin yi".Alhaji Hamza ya dubi agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa, karfe goma sha daya saura kwata ne na dare Yace “Eh dole yanzu ya kamata na tafi tunda goben ne suke tunanin kai su Abujan”. Hajiya Hudah ta wuce zuwa cikin dakinta ta dakko kudi har nera dubu dubu dari uku , ta mika ma Alhaji Hamza ta ce. "Ka rike wannan, ka je ka ji yadda za’ayi da yansandan, duk yadda za’ayi ayi domin ganin an cire sunansa a cikin ko wace takarda dake police station din”. Da sauri Alh Hamza ya karbi kudin, Lokaci daya ya fice a hanzarce. Zuwan Alhaji Hamza (Police Station) din a kalla sai da ya sami ganawa da 'Yan sanda guda shida, sannan ya samu nasarar samun Insifektan da Matsalar ke hannunsa, lamarin ya zama na sirri,domin matsalar ta su Musaddik me girma ce.suna tsare ne a matsayin yan ta’adda wadanda ake amfani da su a lokacin zabe domin a tada hankulan jama’a, da kuma ana tuhumar su da laifin lalata akwatin zabe da kuma sacewa, sai dai har yanzu sun ki fadar wanda su ke ma aiki. Page 154 A dalilin kuma sun ki fadan wanda suke ma aikin, ya sa matsalar tasu ta kara girmama, shi ne dalilin ma da za’a maida su Abuja. Wata Kila a can idan su su ka ga ba Sarki sai Allah sa yi bayani.domin acan din ana iya batar da su har abada . To zuwan Alhaji Hamza dai, shine ya Ceci Musaddik da sauran yaransa, domin da kyar Insifektan ya yi alkawarin goge matsalar tare da bada belinsu, amma sai da suka yi ciniki. Yi cinki saboda tsabar cin hanci da rashawa ya yi ma kasar mu illa.Domin shi ma ya ce sai ya sallami yaransa ya rufe masu baki, don kada ta tashi a wajen manyansu. Don haka Naira dubu dari shida Insifektan ya nema. Haka aka yi ta ciniki har kudin suka koma dubu dari biyar . Don haka Alhaji Hamza ya ba- shi dubu dari biyu da rokon zai dawo gobe ya cikasa masa dubu dari uku, Amma Insfektan bai yarda ba, har sai da ya hada shi da Hajiya Hüdah a waya, suka yi magana, ya tabbatar ita ce, sannan ya amince. amma ba su yi maganar nawa za’a ciko ba dama dai don ya ji muryarta ne ya tabbatar itace ta turo.Daga nan aka fito da Musaddik da yaransa gaba daya. duk sun fita hayyacinsu, saboda duka da yunwa, sun yi bakinkirin kamar sun shekara a kulle. Bayan an fito da su, aka ba su kayan su da wayoyinsu, daga nan suka fito, anan ne Alhaji Hamza ya dubi musaddik yace "'Motata Musaddi& kawai za ta dauka, don ta yi maku kadan, ga wannan” .Ya dauko dubu biyar ya mika masu. "Duk da dare ya yi, sai ku san yadda za ku yi ku tafi gidajenku”. Suka karba suna Page 155 godiya. Musaddik da Alhaji Hamza suka shiga mota, suka tafi,musaddik a jigace yake. Sun yi "'yar tafiya kadan, sannan Musaddik yadan dubi Alhaji Hamza Yace “Ashe ku na da alkawari, ai na dauka kuma duk kanwar ja ce?" Alhaji Hamza ya girgiza kai ya ce "*Hajiya Hudah ta shiga matukar damuwa a game da-halin da ka shiga, yau kwana biyu kenan muna billayin neman inda ka ke, sai Yanzu cikin daren nan, aka san inda ku ke. Ta kasa sukuni kwata-kwata. Naira dubu dari shida ta biya kudin belinku,” ya fadi kudin ne saboda yana son ya ci wani abu a ciki dubu dari biyu yasa ran zai ci. Musaddik ya yi dan murmushi ya ce “Ta burgeni, don ina son mutum me cika alkawari, darajarta da kimarta' sun karu matuka a idona, ya labarin zabe?" Alhaji Hamza ya yi dariya ya ce “Komai ya yi dai-dai, domin Hajiya Hudah ta kara komawa kujerarta ta lashe zabenta a karo na biyu”. Ya yi murmushi cikin jindadi da farinciki ya ce. "To Alhamdulillahi." Alhaji Hamza ya dube shi ya ce. “Mu wuce can gidan Hajiyar ne, tunda dare ya yi, gobe ka karasa gida ko kuwa me ka gani?" Musaddik Ya dube shi ya ce “karfe nawa ne yanzu?”. Alh Hamza ya duba agogonsa yace “ karfe uku saura minti biyu “ ya gyada kai yace “Mu wuce gidan Hajiyar, duk da ba yau na saba yin dare na koma gida ba, kawai dai bana son na shigar ma matata gida a wannan lokacin da nasan tana cikin damuwa gara na shiga gida da safe ido na ganin ido” . Kafin Alhaji Hamza ya yi magana Haj Hudah ta kira wayarsa, da sauri ya dauka, tace “Kun taho ne?" Ya amsa "Eh, muna hanya Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 156 bamu dade da fitowa ba” ta dan yi murmushin farinciki tace “Ka gaya masa, idan babu damuwa ka wuto da shi gidana ya kwana, tunda dare ya yi, idan yaso gobe sai ya karasa gidansa”.Alh Hamza ya yi dan murmushi Yace “Na san za ki fi bukatar hakan, don haka na yi masa maganar hakan, ya kuma amince, zai taho yanzu haka muna kan hanyar gidan ki” ta kara murmusawa tace “Allah ya kawoku lafiya". Daga nan ta aje wayar. Har suka isa katon get din gidan Hajiya Hudah. Alhaji Hamza mamakin lamarin Hajiya Hudah yake yi. Wane irin gamon jini ne ya shiga tsakaninta da Musaddik. Me ya sa ta damu da lamarinsa? Suna isa. Mai-gadi ya bude masu get. A zahiri gidan Hajiya Hudah ya ba Musaddik mamaki, saboda kyansa, bama zaka fara hada shi da gidan ganawa da bakinta da musaddik ya taba zuwa ba, wannan gidan shine karshen zance. A gaskiya Hajiya Hudah ta aje. kudi. A hankali ya dubi Alhaji Hamza, bayan sun zauna a katon falon ta na kasa . "Yanzu wannan ma gidan Hajiya Hudah ne?” Ya gyada kai ya ce "Eh, wannan gidanta ne da take kwana a ciki, wancan da ka hadu da ita a ciki,ai kasan gidan ganawa da bakinta ne”. Musaddik ya jinjina kai yana kara kallon falon yace “Amma matar nan ta tara kudi ba kadan ba, siyasa ta karbeta, ta shekara hudu kan kujerar ta, ga shi ta kara komawa”. Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce. "'Hmmm! Ai Hajiya Hudah ba ta dogara kadai da Page 157 siyasa ba, domin tun kafin ta shiga siyasa tana da matukar kudi……..? Bai karasa maganarsa ba, sallamar daya daga cikin masu yin hidimar gidan ta katse shi. Ta shigo cikin falon tana kallonsa.Tace "Sannunku da isowa, dama ku na ke jiran isowarku, domin na nuna maku inda za ku kwanta, ita Haj ta ce na gaya maku ta kwanta, sai gobe zaku hadu” Musaddik ya dubi Alhaji Hamza. A yayin da lokaci daya suka mike, sannan a hankali suka bi hadimar a baya. Har zuwa wani katon falo mai dauke da dakuna uku a ciki, kowannensu ta bude masa dakin da zai kwanta tare da ba su tabbacin za su sami duk abinda suke bukata a cikin dakin. Sai da suka shiga dakunan nasu sannan ta tafi. Shigar Musaddik dakin ya dade, yana kallon kayatuwar dakin, komai nq dakin na alfarma ne. Sai daya dumama cikinsa da ruwan Tea hade da wani daddadan Cake. Sannan ya shiga bandaki, wanka ya yi sosai, saboda tsananin tsamin da jikinsa ya yi, ga wari da yake yi Saboda datti jikinsa, har wani danko- danko yake yi, ba karamin dadi ya ji a jikinsa ba. Ya yi mamakin ganin riga da wando Kananan Kaya masu matukar tsada a jiye a cikin dakin, amma daya tuna abinda hadimar da ta kawo su dakin ta fada Page 158 Sai ya daina mamaki, tunda ta ce duk abinda za su bukata, yana cikin dakin. Don haka ya aje nasa Kayan da suke surma uban wari, ya sanya wadanda ya gani a dakin ba tare da tunanin komai ba Sai Karfe hudu saura ya samu ya Kwanta .Asubar fari Musaddik, ya tashi ya yi alwala ya yi sallah, wanda rabonsa da yin hakan har ya manta.yana idarwa bai jira komai ba, ya fice zuwa falon Kasa a kofar farko, nan ya hadu da hadimar gidan, ta Yi masa kallon mamakin irin samamakon tashin da ya yi tace "Har ka fito haka da wuri?" Ya dubeta Ya gyada kai ya ce. "Eh, zan tafi ne, taimaka ki bude min kofa*. Ta wuce zuwa wajen kofar tana fadin "Me zance wa ranki ya dade, idan ta tashi? Ta bukaci zata ganku bayan ta tashi” ya yi mata kallon tsaf,yace "Ki gaya mata na tafi gida wajen iyalina domin suna bukatar sanin halin da nake ciki suma”, Ta jinjina kanta, lokaci daya ta bude masa kofar ba tare da tace uffan ba, yana rike da kayan da ya cire jiya a hannunsa. ya fice da gaggawa, duk da ba shi da ko Kwandala a aljihunsa. Haka ya. yi ta tafiyar sa a kasa tamkar wanda baya cikin hayyacinsa. Page 159 Sai da gari ya gama wayewa tangaran! sannan MusaddiK ya isa gida, a zahiri Baba Mai-gadi ya yi matukar murnar dawowarsa. Afrah na zaune akan kujera Kuka take sosai, tun idar da sallar asubah dinta tana zaune kan sallayarta tana rokon Allah ya tsare musaddik a duk in da yake ,lokaci daya kuma takan dakata tayi kuka saboda fitar hawayen shine kesa ta ji abinda ya tokare kahon zuciyarta ya sauka.turo kofar da aka yi, ya sa ta yi saurin kallon kofar dakin. Musaddik ne ya shigo cikin sallama, ganinsa kamar daga sama ya sa Afrah ta mike zumbur ta na kallonsa daga sama har kasa,tana kallon yanayinsa na natsuwa babu alamar ya sha wani abu ga kayan da ke jikinsa, babu alamar musaddik ya na cikin wata masifa, a sanyaye ta kira sunansa “yaya musaddik”,ya amsa yana kokarin zaunawa akan kujera, zuciyarsa ta cika da tausayinta,domin kallo daya ya yi mata ya hango tsananin tashin hankali da damuwar da take ciki,wanda yasan shi ne sila. Sannan yana jin bazai iya jure irin kallon da take yi masa ba me cike da jin zafi da tuhuma. Ya mika hannunsa ya janyo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi yana cugaba da zuba mata tsararrun idanunsa masu kama da mayen karfe domin ji take yi a duk lokacin da ya tsareta da idanun tamkar ana fisgo kaunarsa ana sanyawa a cikin zuciyarta.bata raba daya biyu da gaske ne zuciyarta ta afka soyayyar musaddik soyayya kuma me karfi yadda yanzu take jin damuwarsa fiye da da. Itace ta fara kauda idanunta a cikin nasa gami da yin kasa da kanta,tace a sanyaye,cikin wata fuska me kunshe da damuwa tace “yaya Musaddik ina ka shiga, in dai lafiya kalau kaje ka yi zamanka ba tare da ka dawo gida ba, to ka dauki alhakkina idan har kasan lafiyarka kalau, don me ba za ka fahimtar da ni hakan ba, sai ka bar ni, ina wahala a kanka. Alhalin ka na cikin koshin lafiya. Na rantse da Allah ba ka kyauta min ba, ba ka kyauta ba...?” Ta barke da kuka, cikin damuwa da tashin hankali ya sanya hannu ya janyota zuwa kirjinsa ya rungumeta yana bubbuga bayanta da daya hannunsa alamar lallashi, ya dora bakinsa a kunnanta yana rada mata “kiyi hakuri bata miki rai shine abin da na fi tsana akan komai a rayuwata, kiyi hakuri “ kalamansa da irin rungumar da ya yi mata ya haddasama jikinta mutuwa, ji tayi tana bukatar kirjin da zata yi kuka don haka ta kara lafewa a jikinsa hawaye na cigaba da fita mata. Page 160 Ya kara rungumeta shi ma yana jin irin abinda Afrah ke ji a ranta. Lokaci daya kuma ya na yi mata bayanin dalilin rashin dawowarsa gida, ya kara da cewa “Abinda ki ke zato ba haka bane, na san na kan kwana ba na gida wani lokacin amma ai muna magana ta waya, muna sanin halin da junan mu ke ciki, amma wannan karon tunda ki ka ji irin wannan shirun, ba ni ba waya, tabbas kin san ba lafiya ba, tunda ko ina nake ki yarda da ni Afrah ki na cikin raina da tunani na” Ta dago da jajayen idanunta tana kallonsa ta ce. tana kara kallon , amma sai yasa hannu ya kara kwantar da kanta akan faffadan kirjinsa, ta aje numfashi tace “Ba lafiya, ba amma jikin ka ai bai nuna haka ba, ga ka nan fes! Da sababbin kaya a jikinka” Ahankali ya cire hannunsa a bayanta, ya dagota sannan ya mike tsaye ya cire rigar jikinsa, ya juyo mata bayansa yace “Ki kalli bayana,ki gani” Afrah ta dago ta dora idanunta akan, bayansa ,duk a farfashe, wani wurin ma ya kumbura, ta mike a gaggauce tana fadin “Subahanallahi! Waye ya yi maka wannan aikin, wane mara imanin ne?"tana magana tana dora hannunta akan ciwon tana ji tamkar ta cire ta dawo da shi cikin jikinta. Ya juyo yana kallonta ya rike hannayenta ya maidota jikinsa ya kara rungumeta duka kan kujerar suka kara zaunawa yana rungumeta da ita cikin sanyin murya ya gama sanar da ita komai. Ya dubi kayan jikinsa yace “'Hatta wannan kayan a gidanta na samu nasa Ita ce ta taimakeni ta fitar da ni daga wannan Kangin, ba don haka ba, yau din nan za"a kai mu Abuja, Idan ko aka kai mu wannan garin , sai yadda hali ya yi, domin ko miliyoyi ba zasu iya fitar da mu ba, kuma duk sai sun illata rayuwata kafin na fito , don haka Allah zamu yi ma godiya, sannan mu yi ma Haj Huda godiya ,domin ta bambanta da sauran yan siyasar da na sani da alama ita zata yi tausayi da amana. Yar gidan Imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 161 Cikin hawaye Afrah ta sauke numfashi tace “Allah ya saka mata da alheri. ta taimake mu sosai” ta kara lafewa sosai a jikinsa, tana jin abubuwan da bata saba ji ba suna yawo a cikin jikinta,zuciyarta ta kara cika da kaunarsa,domin bata kara tabbatar ma da kanta ta fara son Musaddik ba so kuma na hakika sai da baya gidan. Ta yunkura tana son tashi,amma sai ya kara sa hannu ya janyota, yana tsareta da ido yace “ina zaki,bayan kinsan babu abinda na fi bukata sama da jin dumin jikin ki”, ta dago da idanunta ta dora a cikin nasa idanun, tana kokarin son gane ko shi ma ya fada irin tarkon da ta fada ne na soyayya, zuciyarta ta cika da fatan Allah yasa shi ma ya fara sonta ne. Ta dan dauke idonta a kansa tace “Ina son na je na samo maka ruwan zafi ne domin ka gasa jikinka,sannan kuma na samar maka abinda zaka ci”. Ya matseta sosai yace “zan fi bukatar samun kulawarki ta musamman fiye da duk wannan abinda ki ka lissafa, sosai nake sha’awar ki Afrah”.ta ji kunya sosai ta sadda kanta kasa. Ya yi murmushi gami da mikewa tsaye ya tada ita tsaye, da kansa ya rufe kofar dakin sannan ya ja ta zuwa cikin uwardaki, bata yi musu ba, domin itama tana son abinda yake son yi din, musamman idan ta tuna rabon da ya kusanceta cikin kyakkyawan yanayi irin wannan harta manta. Sai da suka kammala komai, hakanan Afrah ta rushe da kuka sosai, nan da nan musaddik ya gigice ya birkitota yana kallon yadda hawaye ke fita mata yace “me nayi miki?me yasa ki ke kuka kuma”. Ta lumshe idanunta ta bude tace “Nayi sha’awar ace kullum haka ka ke zuwa min cikin nutsuwa, tunda mu kayi aure ban taba jindadin kusantarka irin yau ba, baka cikin maye baka wari, yau cikin nagartarka ka fito min, na yarda kai jarumi ne yaya Musaddik don Allah ka taimake ni ka dawo cikin nutsuwarka”, shuru ya yi ko wace kalma da ta fito daga bakin Afrah tana gasa zuciyarsa, ya kasa cewa komai hakan yasa Afrah ta cigaba da magana cikin muryar tausayi. “Me ye amfanin wanna rayuwar, don Allah Yaya, don darajar Annabin rahama ka natsu, kai fa ba karamin yaro bane, ka dubi irin shekarun da ka ke da su, ka sani da kyar ne idan za ka Kara shekarun da ka yi a baya, ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da, rayuwa me dadi da tsafta irin wacce ka yi a baya Ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da,Ka yi yaki da shaidan. Ka rabu da abokanka na banza, ka koma ma abokanka na da, na-gari, ka yi tsaftatacciyar rayuwa, Ko ka dawo da kima da darajarka da ka rasa,wannan ba irin rayuwarka bace, ba ta kuma dace da kai ba ko kadan. Shin ya za ka yi da Yayanka idan ka fara haihuwa?" Ta kara nisawa tace “ina son yin rayuwa da kai har abada, a kalla ni ma yakamata na samu farinciki a gareka ko yaya ne, yanzu da kayi kwanaki a kulle ba ka sha komai ba ka mutu ne, me ka ragu da shi”. Kamar daga sama kawai ta ji Musaddik ya saki ajiyar zuciya yace “Na sha, ko da nake kulle Afrah na sha domin ba zaki gane halin da nake ciki ba ko nace bazan sha ba ji nake kamar za’a cire raina idan ban sha ba”. Jikin Afrah ya yi sanyi kalau, ta dago ta na kallonsa sosai tace “kana rufe ta yaya ka samu kayan maye ka sha?”. Ya runtse idonsa da karfi ya bude yace “A cikin ma’aikatan yansandan muke samun me sayo mana duk dare, mu kan sha kuma lafiya lau ba tare da wata matsala ba, domin ko da safe ba’a ganewa saboda muna kiyayewa”. Tirkashi lalle al’amarin kasata ya kazanta abinda Afrah ke fada a ranta kenan wajen hora masu laifi anan ake ba mutum kayan lefi ya yi amfani da shi, to ta ina za’a iya samun gyara. Musaddik ya tashi ya nufi bandaki yana cewa “Addu’a kawai nake bukata Afrah domin duk duniya babu wanda ya kaini son shiryuwa, ki kara hakuri mu jira lokaci kawai, domin na fiki kosawa na sami shiriya”. Ya tsaya a bakin bandakin ya na juye da bayansa ya cigaba da cewa Page 162 "Ko Ki na tunanin wannan abin baya damuna ne? To duk duniya na rantse miki banda wata damuwa sama da wannan, ina cikin matsananciyar damuwa, domin tun bayan aurena da ke Burina bai wuce na kintsu ba, saboda na san abinda ki ka yi min na aurena a l Lokacin da babu wata mace me hankali irinki da za ta iya aurena.a salima ban taba jin zan iya yin komai domin na shiryu ba sai bayan da na aure ki Amma abin mamaki na kasa barin koda abu daya, wannan lamari yana matukar damuna gami da daure min kai”. Ya karasa magana cike da damuwa sannan ya dan waiwayo ya dubeta yace “ki yi hakuri ki yi min afuwa”. Afrah ta ce ta na me cike da jin tausayin sa, “Tunda har kana son ka daina, to ina son ka sa ma ranka zaka iya bari, ka yaki shaudan sannan kuma ka jajirce, ka sani duk abinda

Chapter 10 of 15