Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yake ciki, ko kadan ba na son a sami wani canji a game da rayuwarsa a dalilin auransa". Ya yi dariya yace "Wannan ai babu canji, ko na yi aiki akai ko ban yi aiki akai ba, ba za'a samu wani canji ba. Page 67 Zai ci-gaba da zama a halin da yake ciki, auransa ba zai canja shi da komai ba” Hajiya Kilishi ta ce "Godiya na ke" ta balle jaka ta fito da kudì ta mika masa, ya amsa yana godiya gami da kara karfafa mata guiwa akan lamarin Musaddik, daga nan suka yi masa sallama suka fito. Har sai da Hajiya Kilishi ta fara tuka mota, sannan Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce “Amma yarinyar da za ta auri Musaddik mahaukaciya ce ko?" Hajiya Kilishi ta ce "Ko daya da hankalinta ras, tasan abinda take yi” ''To idan ba mahaukaciya ba, me za ta ci da Musaddik, wane jindadì za ta samu daga gare shi mutumin da ina ganin ko wanka ba ya yi, Kullum yana wurin *yan daba yana shaye-shaye, yana kuma yawon bangar siyasa, ko dai suna tunanin za su sami kudi ne a hannunsa?" Ta girgiza kai ta ce "Ubanta ya fi kowa sanin Musaddik baida ragowar sisin kwabo, ni dai ban 'san dalilin da mahaifinta yake son hada wannan auran ba da zai zama masifa da fitina ga yarsa dama shi mutum ne me kafiyar tsiya, amma 'tabbas ba na son Musaddik ya auri *Yarsa Afrah" Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce “To ki na ganin za mu gwada sa'ar wani wajen ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Hajiya. A gaskiya na yarda da aikin Mai Rakwacam, kin fi kowa sanin cewa Page 68 duk shekarun nan, shine yake taimaka min, bai taba yi min aiki na ga rashin sa' ar aikin ba. Idan kuma abu ba zai yiwu ba, zai gaya min, ba zai cin min kudi a banza ba, na kuma sha gwada wani wajen, idan ya ce ba zai yiwu ba. Haka nan za'a ci min kudi kuma babu biyan bukata, shi ya sa yanzu idan ya gaya min abu ba Zai yiwu ba, na kan hakura gaba daya na rungumi kaddara, kamar yanzu da na saduda na hakura akan maganar auran nasu” Ta nisa gami da hadiye yawu kafin ta ci-gaba da magana. Hajiya Rakiya ta ce “ kina da gaskiya, tunda kin yarda da shi, gara ki aje hankalinki waje daya, domin tabbas ya iya aiki”, Haj kilishi cikin fuska me cike da bakinciki tace “Hakane, amma nayi alkawarin bazan taba barin Afrah ta samu kwanciyar hankali ba,dole zansa auran ya fita a ranta da kanta zata nemi wajen gudu in dai nice”, Haj Rakiya ta yi dariya tace “ kin ji ki da wata magana za ki bata ma kanki lokaci, dai kawai domin rashin kwanciyar hankali, har ya wuce wanda mijinta Zai sakata a ciki? Halinsa kadai ya isa ya sa ta gudu ta bar shi, wa zai iya da Musaddik” Hajiya Kilishi ta yi dariya ta ce "Kai Hajiya Rakiya sai a barki, kuma fa hakane” Gaba daya suka kwashe da dariya . Sai dai fa ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, domin har cikin zuciyarta auran nan yana daya daga cikin binda ta tsana a duniya, amma babu yadda za ta yi, tunda haka kaddara ta riga fata, sosai take jin tsanar Afrah a cikin zuciyarta da mallam mahmud. Page 69 Ta Bangaren gidan Malam Mahmud kuwa shirye- shiryen bikin Afrah da Musaddik ya kankama, ita kuwa Na’ima tunda ta dawo gidan, take ma Allah godiya daya gajarce mata wahalar auran. Musaddik . Inna Halima da kanta ta sai ma Afrah gado da katifa da sauran tarkacen kayan kicin. Kudin kuma da su Kabir suka ba mahaifinsu a matsayin gudunmuwa, su ne ya ba Inna Halima ta sayo kujeru kayan kallo da firij har da keken dinki da sauran duk kayan da ake bukata. Duk da haka sai da kudin suka ragu, su ne ya yi amfani da su ya sayi kayan abinci. Mama Hauwa kuwa tunda ta fahimci Mansur da Kabir ne suka bada makudan kudin sayayyar Afrah, ta ji bakinciki kamar ya kasheta, don sai da ta Kirasu ta yi masu kaca-kaca. Ta nuna masu matukar bacin ranta. Shirye-shirye sun yi nisa, sun kankama, amma ga Afrah, al'amarin ya fara ba ta tsoro , saboda tun daga ranar da Musaddik ya zo gidansu suka Yi magana, bai kara dawowa ba. Ba shi, ba labarinsa, dan ko, ta je gidan Inna Halima ranar juma'a har ta gama kwanakinta ta dawo gida, ba zai zo ba. A zahiri abin yana damunta, tana matukar son ta san halin da yake ciki Ga shi ba ta san inda za ta same shi ba, balle ta neme shi ta ji lafiyarsa. Haka zalika bata nuna damuwar komai a gaban kowa Page 70 Musamman mahaifinta da Inna Halima, haka Zalika ko yaushe tana samun karfin guiwa daga Ya Sayyadi Habib tare da addu'o'"i, wadanda a yanzu su Afrah ta rike suka zamar mata garkuwa. Idan ma akwai abinda ke damunta, to bai wuce habaici da maganganu marasa dadi da Mama Hauwa ke mata ba, tare kuma da nuna mata tana cikin jin dadi, don ganin rayuwarta za ta lalace, a dalilin auran Musaddik, amma da yake ba ta son damuwar mahaifinta, haka ta dage tana hadiye duk abinda Mama Hauwa ta yi mata ba tare da ta nuna damuwarta ba, don bata son mahaifinta ya dauka tana damuwa ne akan zata auri musaddik wanda ita zuwa wannan lokacin ta riga ta sa ma kanta auran musaddik bata jin wata damuwa a yanzu. Har yau daya rage saura kwana shida daurin auran Musaddik da Afrah, da yamma Afrah na cikin wankin ragowar kayanta, gefe mallam Mahmud ne zaune tun dazu, da alama wani yake jiran zuwansa, dai-dai lokacin Musaddik ya yi sallama ya shigo.Afrah ta yi saurin dago da kanta tana kallonsa, ko don ta dade ne ba ta gan shi ba? Sai ta ga yayi baki, ya rame duk bakinsa ya bushe kamar wanda ya shekara bai sha ruwa ba, tausayinsa ya Kara kamata, amma shi kallo daya ya yi mata, ya dauke kansa ya wuce wajen Kawunsa, ya tsuguna a gabansa, da kayansa duk sun yi datti ya gaishe shi Malam Mahmud ya dade yana Kure masa da ido cike da tausayawa, babu abinda bai saka a zuciyarsa ba, musaddik kyakkyawa me farar fata yau dubi yadda ya koma idan ba kyakkyawan sani kayi masa ba tabbas ba zaka iya gane shi ba a yanayinsa na yanzu. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam ✍️ MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 71 Mallam Mahmud ya numfasa yace “ina ka shiga kwana biyu,duk inda yakamata na nemeka na nemeka amma baka nan, haka kuma wayarka itama bata samuwa, lafiya kake ko?” Musaddik Ya dan numfasa, sannan ya ce "Kawu kasan idan zabe ya gabato bama samun zama, na dan kwana biyu ma bana garin, wayata kuma ta samu matsala sai da na gyarata Mallam Mahmud ya girgiza kai yace "Yanzu Musaddik don Allah ba za ka yi ma kanka fada ka fita daga harkar nan ba, bangar siyasa ba ta dace da kai ba, kana sane da irin wahala da zubar da mutunci da ku ke yi akan mutanen da su kansu ba su san darajar kansu ba balle darajarar ku, ya kamata ace ka natsu ka san inda duniya ta sa gaba." Musaddik ya dan sosa keyarsa ya ce “Sai hakuri Kawu, ayi ta mana addu'a dai har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana agaji, a kara hakuri da mu don Allah “ya gyada kansa Cike da damuwar data riga ta zamar masa jiki yace “Allah ya kyauta ya kuma shiryaka” Ya gyara tsugunnansa ya ce yana fadin "Amin” Malam Mahmud ya dube shi ya ce “Kana Kirge da kwanakin da suka rage na auranku ko ?”ya gyada kai alamar eh, sannan ya ci-gaba da magana '"To shine dalilin nemanka, akan maganar wajen da za ku zauna, ka na da wajen da za ku zauna dunne ko kuwa babu ?" Musaddik ya zame ya zauna sosai a kasa ba tare da ya damu da kurar dake kasan ba, yace “ Eh kawu,nayi magana da Haj shekaranjiya, ko zata taimaka min da aron gidan da zan zauna, ko da nawa ne na da da na zauna da Hannatu Page 72 sai ta nuna min ai ba ta da iko da gidan, tunda na Hannatu ne, ba nata ba” Ya dan yi shiru. Sannan ya dora da cewa “Shine ta ce sai dai ta taimaka min da daki anan cikin gidan namu, na kuma amince da hakan, tunda banda sauran wani zabi, sai dai ban sani ba ko Afrah ba zata so zama tare da ita ba” Malam Mahmud ya yi shiru na dan wani lokaci, sannan ya dago da idonsa ya kalli Afrah da take ta wankinta tamkar ba ta jin abinda suke fada a hankali ya dawo da kallonsa ga Musaddik, sannan yace "To shi kenan, Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri. Allah kuma ya daidaita zaman da ita, domin nasan Afrah bata da wani jayayya akan hakan” musaddik ya kara risinawa ya na cigaba da yi ma kawunsa godiya har sai da ya dakatar da shi. Daga nan Mallam Mahmud ya tashi ya shiga cikin dakinsa, a nan ne Musaddik ya juya yana kallon Afrah, ita ma ta juyo ta kalle shi, fuskarta dauke da murmushi, cikin jin nauyinta ya dauke idonsa a kanta. Zuciyarsa cike da mamakin irin zuciyar Afrah, ya kamata ace ta yi fushi da shi, a dalilin rashin kara waiwayarta da bai yi ba, amma babu alamar damuwar hakan ko tsanarsa akan hakan. Dai-dai lokacin da Malam Mahmud ya fito rike da kayan sawa. Mama Hauwa ta fito daga daki ta tsaya ta kama kugu ta rike tana kallonsu. Mallam Mahmud ya zauna, Sannan ya mika ma Musaddik kayan, shaddoji ne da yadiddika masu kyau, akalla zasu kai kala bakwai yace “ Nasan babu abinda ka tanada na game da komai na hidimar bikin Page 73 don haka ga kayan sawa nan, sannan ga wannan”Ya mika masa Naira dubu goma yace “Bance kaje ka kashesu a banza ba, ko kaje ka sha wani abun da su ba, na umarceka da ka aje su ka yi amfani da su a bikin ko wata harkar ta alheri”. Ya karba cike da godiya da yabo, ya yi ta godiya Malam Mahmud yana fadin. "Ka daina yi min godiya, don ban ga dalilin yi min godiya ba, kai fa dana ne don na yi maka wani abu, babu bukatar ka yi min godiya." Musaddik ya ce "Kawu karamcinka a gareni, ya kai duk inda ya kai, godiya ba za ta isa ba. Sai dai na ce Allah ya kara girma."Mallam Mahmud zaiyi magana kenan Mama Hauwa ta amshe. "Ai dole ka ce godiya ba za ta isa ba, gata mugun abu, aka ce inji wanda bai samu ba, Yanzu wanda zai kawo kayan lefe, shi ake ba Kayan sawa, wannan aure shine gallafiri, tunda na ke ban taba ganin irin wannan auran gatan ba.ta juya ta kalli Afrah tace “ lalle Afrah ba zaki taba yin daraja a wajen musaddik ba, don baisan darajarki ba, balle tsadarki, daga sama kawai ya sameki”, Malam Mahmud ya daga mata hannu, ransa a bace yace “Na gaya miki, na Kara gaya miki, ki fita daga cikin duk abinda ya shafi auran Afrah, babu ruwanki, ki shiga taitayinki, na rantse idan kika kaini bango za’ayi auran nan bakya cikin gidan nan” , a hankali ta saki tsaki Page 74 tace, a yayin da take shigewa dakinta "Kanku ake ji, ni meye nawa, iyakar mu ido” ta karasa shigewa daki harda turo kofa tana cigaba da maganganunta a hankali. Malam Mahmud ya dawo da kallonsa ga Musaddik, wanda fuskarsa ta nuna matukar damuwa da maganganun da Mama Hauwa ta fada, yace “Kada ka damu Musaddik Hauwa ce fa haka take, ba za ta taba canjawa ba, don haka babu dalilin da mutum zai damu da dabi'unta, kai ma ina umartarka da ka manta da duk zantukanta”, ya jinjina kai yace “ Hakane kawu, babu komai, nagode” Daga nan Musaddik ya hada kayansa a cikin leda, wanda zuwa lokacin Afrah ta gama abinda take yi ta shige dakinta, ranta da hankalinta a tashe da maganganun da Mama Hauwa tayi. Wanda hakika ta san gaskiya ne. Duk abinda ta fada, ba ta da wata daraja a wajen Musaddik Ko ba'a kan rashin tsinana komai akan bikin ba, Ko a cikin zuciyarsa, ta san ba ta da daraja, domin daga dukkan alamu. Musaddik baya sonta dole zai aureta, don Kawunsa, kamar yadda dole za ta aure don mahaifinta. Malam Mahmud ya riga Musaddik fita daga gidan, don a tunaninsa zai tsaya su tattauna da Afrah, ita ma Afrah ta yi tunanin zai nemeta su yi magana, musamman akan auran nasu, duk da ta san ba wani shirye-shiryen da za su yi akan auran amma ga mamakin Afrah, mahaifinta yana fita. Page 75 MusaddiK ya tattara kayansa shi ma ya fice, ba tare da ya nemeta ba, ko ya shigo dakinta sunyi magana ba.Shin wane irin aure za ta yi? Me Musaddik ya dauketa?”, wadannan tambayoyin Afrah tana matukar bukatar amsar su., amma ba ta san inda za ta samo amsarsu ba. Saura kwana uku daurin auran. Afrah ta nemi hutu a Islamiyyarsu, a ranar Ya Sayyadi ya nuna matuKar damuwarsa na rabuwa da yarinyar da zuciyarsa take muradi. Iya yadda ya so ya boye damuwarsa a yau, hakan ya faskara, yadda idanun Afrah suke fitar da hawaye, haka idanunsa suka yi ta tsiyayar hawaye shi ma masu matukar dumi da kyar ya samu ya lallashi kansa Sannan ya ci-gaba da yi mata nasiha gami da shawarwari a game da zaman auranta da za ta fara da Musaddik, wanda ta ji dadin nasihohinsa, domin tasan tabbas za su taimaketa. Daga bisani ya ba ta wata takarda a matsayin gudunmuwarsa. Ta karba ta yi godiya kwarai, wanda sai da ta isa gida ta zauna, sannan ta san abinda Ya Sayyadi Habib ya ba ta a matsayin gudunmuwarsa, kudi ne kimanin Naira dubu talatin . Ta kara tausaya ma Ya Sayyadi, ta kuma kara tausaya ma kanta da wannan auran Kaddarar daya gitto rayuwarta. Hakika ba za ta taba mantawa da Ya Sayyadi ba, kuma ba za ta taba daina yi masa addu' ar samun mace wacce ta fita komai ba. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR lMAM Page 76 mace ta-gari ba, wacce ta fi ta komai. Ta dade tana tunanin yadda za ta yi da kudin, domin dai ba zata iya kai ma mahaifinta kudin ba, don ba ta son ya san cewa akwai wani da namiji da take so a cikin rayuwarta Don ba ta son ta sa masa damuwa na tunanin ya hanata abinda take so. Ya hada ta da abinda zuciyarta ba ta taba so ba, don haka ta adana, Kudin ta Boyesu da kyau da tunanin bayan bikinta za ta san abinda za ta yi da su. Washegari daya kama sauran kwana biyu daurin auran. Inna Halima da yayyin Afrah, Naja' atu da Sakina da 'yan-uwan mahaifiyar Afrah su biyu su ne za su je su yi ma Afrah danki, amma kafin su tafi, sai da Malam Mahmud ya ja kunnan Inna Halima akan duk abinda Hajiya Kilishi ta yi masu, kada su biye mata, ko su tanka Su yi abinda ya kai su kawai, su dawo, domin ya san Hajiya Kilishi, ya san halinta. Inna Halima ta yi masa alkawarin babu abinda zai faru, daga nan suka dunguma tare da motar kayan zuwa gidansu Musaddik. Amma ga mamakin Inna Halima, sai ta ga Hajiya Kilishi ta yi masu kyakyawar tarba har da lafiyayyen girki, wanda ya ji nama, ga lemo kala- kala, ga sakin fuska da suka samu. Wannan lamari ya ba Inna Halima mamaki,domin bata taba zaton haka ba, hakanan kuma ta ji bata samu nutsuwa da hakan ba. (Boys Quarters), Page 77 Haj Kilishi ta ba Musaddik mai dauke da dakuna biyu da bandaki, sai kicin, an yi ma Afrah dankinta, dai dai karfinsu daki ya yi kyau matuka, Domin ita kanta Hajiya Kilishi ta yi mamakin irin kayan da ta ga an malala ma Afrah. Babu makusa. Hakika Malam Mahmud ya yi matukar kokari, wai ma ina ya sami kudin daya fitar da Afrah kunya? Domin dai ta san bai aje ba, bai ba wani ajiya ba. Bayan komawarsu gida, cike da jin dadì da farin-ciki Inna Halima ta ba Malam Mahmud labarin irin karamcin da Hajiya Kilishi ta yi masu. Wanda shi ma ya yi mamaki, ya kuma ji dadi tare da addu'ar Allah ya sa har cikin zuciyarta ta gyaru, ta kuma amshi auran Afrah da Musaddik da zuciya daya. Ita ko Mama Hauwa a lokacin da Naja'atu ta gaya mata irin kyakyawar tarbar da suka samu a gidansu Musaddik, gaba daya sai ta ji bakin-ciki da 6acin rai ya cika zuciyarta, ko kadan ba ta so hakan ba, domin bata faran Afrah ta samu sassauci ko dadin aure ko yaya ne, tayi zaton Haj kilishi ta zabi zama da su Afrah waje daya ne ai sabida ta kuntata mata, amma kuwa yadda tasan bakin halin Haj kilishi anya dagaske take ta amince da Afrah?.ko kuwa dai wani tuggun ne. Sai washegari wanda ya rage saura kwana daya daurin auran, sannan Musaddik ya zo ganin Afrah, shi da wasu abokansa guda hudu marasa kyan gani, don da ganinsu ka san shaye- shaye ya gama da su, banda wari ba abinda suke yi, hakan yasa Afrah ba ta dade a wajensu ba, ta yi karyar za Page 78 ta koma ta karasa aiki. Haka suka tafi babu wani abin arziki Afrah na komawa gida, ta shige daki ta kulle kofa ta shiga rusar kuka tamkar ranta zai fita, ba ta taba ganin irin wannan auran ba, wanda miji da mata duk ba sa dokin sa, auran da Ko kawarta daya ba ta gayyata ba, auran da ko dan-kwali miji bai kawo gidansu a matsayin lefen ta ba. Anya kuwa ta yi ma kanta adalci? Na karbar auran Musaddik? Sai dai ta Bangaran zuciyarta daya tana kara karfafa ma kanta guiwa akan auran don ba don farin-cikinta za ta yi ba, don Farincikin mahaifinta* za ta yi, kuma biyayya ce tasa ta sadaukar da farin-cikinta ga mahaifinta, don haka tana addu'ar Allah ya ba ta ikon cinye wannan jarabawar, ta kuma sa a ranta zata jure komai har zuwa lokacin da burin mahaifinta zai cika akan musaddik, tausayin musaddik kuma zaisa ta kara jurewa da halayensa ko da bata sonsa. Ta tashi ta goge hawayenta, ta bude kofa ta fita, ta je ta dauro alwala ta shiga gabatar da sallolin nafila , domin samun natsuwar zuciya da Kuma yayewar bakin-ciki. Dai-dai agogo ya nuna karfe daya da kwata na dare. Afrah na kishingide kan darduma, tun bayan da ta gama nafilolinta, barci ya kwasheta. Malam Mahmud ya tura kofar ya shigo a hankali, gami da sallama, ya dan jima tsaye a kanta yana kallonta, kafin ya kira sunanta. A gaggauce Afrah ta tashi ta zauna tana kallon mahaifinta. Page 79 "Ki natsu Afrah, magana zan yi da ke". Ya fada a lokacin da yake zaunawa a gefen , katifarta ita ma ta gyara zamanta sosai , tana kallonsa. tace “To baba” - Malam Mahmud ya numfasa cike da tsantsar damuwa, ya zuba mata ido, sannan ya . fara magana”Na kwanta, amma barci ya kasa kwashe ni, iya yadda na ke boyewa tare da danne darnuwata a 'wannan daren, na kasa, domin damuwata tafi ta kullum kasancewar gobe ita ce ranar da zan rabu da ke, itace ranar da za ki kafa sabuwar rayuwa a wata duniyar, da baki sababa” Ya kara nisawa, sannan ya dora da cewa "Ina matukar kaunarki fiye da duk yayan da na haifa a dalilin ke ma kin fi su kaunata, na kuma fi samun kulawa da mutuntawa daga gareki. Afrah ina son ki sani, har ga Allah ba irin auran da na ke kwadayin ki yi kenan ba, Kamar yadda ba mijin da na ke miki mafarkin ki aura ba kenan, amma babu yadda za mu yi da Kaddara da kuma abinda Allah ya hukunta a kan mu Afrah ina son ki sa ma ranki cewa auranki da Musaddik jihadi ne, ki kuma sa a ranki cewa kin yi domin Allah ne, domin kuma taimakon rayuwar dan-uwanki.sannan ibada zaki je yi gidansa” Hawayen idanun Afrah suka balle ta shiga zubar da hawaye, tamkar an bude famfo. Malam Page 80 Mahmud ya muskuta, damuwarsa ta kara yawa a hankali ya ci-gaba da magana cikin rawar murya “Afrah na rokeki don girman Allah ki yi hakuri da dukkan hali da dabi 'un Musaddik, na san ba mutumin kwarai bane a yanzu, sabanin da amma muna da tabbacin da ikon Allah halinsa na da zai dawo gare shi, ki yi hakuri, ki yi juriya, sannan daga Karshe ina rokonki da ki yafe min Afrah ki yafe min” da sauri Afrah cikin kuka mai karfi tace, “Haba Baba me ya sa'ka ke neman gafarata? Babu komai, na riga na daukar ma kaina yi maka biyayya akan duk abinda ka ke so, na kuma yi imanin cewa Allah zai taimakeni, na cinye wannan jarabawar. Kuma can a allon kaddara ta , babu sunan kowa a matsayin mijina, sai Yaya Musaddik, saboda haka na karbi wannan kaddarar da hannu biyu”. Malam Mahmud cikin sanyin jiki ya kara duban Afrah, yace “Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira,Allah kuma ya tabbatar da alheri a cikin rayuwarki da ta aurenki, Allah yasa wannan auran ya zama sanadiyyar dawowar musaddik hanya madaidaiciya”. Wannan addu’o’in sa mahaifinta ke mata yana daya daga cikin abinda ke karfafa mata guiwa tare da jin tana samun nutsuwa a zuciyarta. ta dube shi cike da kauna ta ce "Amen Baba, na gode sosai”, daganan ya yi mata sallama, ya tashi ya tafi, jikinsa a matukar sanyaye, yana fita ta kara rushewa da kuka tayi ta kuka har ta ba uku lada. Hakika dole ta sa ma kanta hakuri da dangana, domin ba za ta taba ba mahaifinta kunya ba, zata yi iya yinta domin cika masa burinsa, a wannan daren gaba daya ta aje dukkan burikanta a gefe. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 81 tasan babu so ko kaunar musaddik a cikin zuciyarta ,amma tayi alkawarin za ta ba shi dukkan kulawa da Kariya a gare shi, za kuma ta yi zama na so da kauna tunda babu wanda ke da ikon ganin zuciyarta balle asan bata son sa, sannan kuma za tayi zama na mutuntawa da Musaddik, za kuma ta dauke shi shugabanta, kamar yadda addini musulunci ya tanadar, don baida nutsuwa bazai bata lasisin wulakanta shi ba tare da muzanta shi ba. Washegari kuwa Karfe biyu da rabi alkawarin Allah ya cika akan Musaddik da Afrah, domin Kuwa an daura auransu a kofar gidan Malam Mahmud akan sadaki Naira dubu arba’in kacal! Wanda shi ma ba tare da sanin kowa ba shi ya biya kudin sadakin. Bayan daura auran. Afrah ta ci kuka har ta gaji, musamman da Inna Halima ta shigo dakin nata, ta sa ta gaba da nasihohi da shawarwarin yadda za ta zauna da Musaddik. Har zuwa lokacin da za°a kai ta dakinta, wanda abin takaici hatta motar da za'a kai ta dakin mijin nata, da motar yayan ta Mansur aka , kaita Inna Halima da su Naja'atu da matar Mansur Sai dangin mahaifiyarta su uku su ne suka kai Afiah dakin mijinta, nan ma Hajiya Kilishi ta yi kokarin wadata su da abinci har suka bar gidan ba su yi kuka da komai ba. Inna Halima kuma addu’a take yi Allah yasa Haj kilishi ta dore akan wannan sabon canjin da ta samu rana tsaka. Sun tafi sun bar Afrah ita kadai. Da kanta ta tashi ta zazzaga dakin nata, hakika ta yaba ma mahaifinta, domin dai dakinta ya kawatu, kamar na kowace *yar gata, tabbas an fitar da ita kunya Page 82 Bayan ta gama ganin ko'ina ne, ta dawo ta zauna tana tsammanin shigowar angon nata. Amma shiru, har zuwa lokacin da agogon bangon ta ya buga karfe daya na dare ba Musaddik, babu alamarsa, ta tashi cikin matukar damuwa ta kulle kofar dakin, sannan ta wuce bandaki, ta dauro alwala, ta kyautata niyyarta ta shiga yin sallar nafila, zuciyarta cike da tsantsar danuwa Afrah ba ta gushe tana sallah ba, har sai da aka fara kiran sallar farko na asubah, dai-dai lokacin Afrah ta ji ana bugun kofa da Karfin gaske, tamkar za’a balle Kofar, ta mike a gigice zuwa bakin kofar tana kokarin sanin ko waye. "Afrah ki bude kofar” muryar musaddik ta daki dodon kunnenta, da sauri ba tare da tunanin komai ba ta bude kofar, tana budewa, ya fado dakin a buge yake, koda Afrah bata san warin giya ba, to tabbas Musaddik tsami da warin giya yake, da sauri ta matsa, ya fada kan doguwar kujera yana sambatun surutai.wanda bata gane ko kalma daya da yake fada ba. A sanyaye ta maida kofar ta rufe, ta dawo ta tsaya a gabansa tana kallonsa, hawaye na malala daga idanunta, ya dago da idanunsa jajir! wadanda ba su iya buduwa duka, ya ce "Kin tsaya a kaina, ki matsa ki bani waje” • Da sauri Afrah ta koma kan daya kujerar ta zauna, tana goge hawayenta Da kyar ta samu ta tashi ta yi sallar asubahi, wanda kafin ta idar musaddik ya gama wanke Page 83 Kasan dakinta da aman giya, me

Chapter 5 of 15