Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ka ga mutum bai daina ba to baisa kansa ba ne, zaka iya yaya musaddik,kuma Allah zai taimake ka, a kullum ka tuna kai maraya ne a yanzu iyayenka na bukatar addu’ar ka amma nasan ko lokacin addu’ar ma ba ka da shi, yakamata ka taimaki kanka Ka dawo cikin tunaninka Dukiyar da mahaifinka ya bar maka, ba ka kirkinta ba, rashin natsuwarka ya sa an rabaka da komai, saboda an san babu abinda za ka iya yi, don ba ka amfani kanka ba ma, balle ka amfani dukiyarka wannan babu inda zai kai ka. Shekara da shekaru ka na cikin wannan mugun hali, ba ka ko tunanin gaba” Maganganunta sun yi tasiri a zuciyarsa, ya ji yana neman ya tsani kansa ya numfasa ya sa hannu ya bude kofar bandakin har zai shiga sai ya kara tsayawa, sai kuma ya juyo ya dawo gefen gadon ya zauna. “Duk maganganunki hakane, kuma ke ma ba zaki gane halinda nake ciki ba Page 163 Shi ya sa ban so a kashe rayuwarki ta hanyar aurena ba, na san ba ki dace da ni ba, ba ni ya kamata ki zauna ki yima biyayya gami da bauta ba a matsayin mijinki, ban so ace nine me cutar da ke ba, ki na da wani matsayi a guna na musamman da duk bata miki da nake yi nakan ji abin har cikin jinina na kan ji damuwar da tafi taki, bansan dalili ba, amma dai nasan ke ta musamman ce, kin yi hakuri Domin na san a iya tsawon lokacin da ki ka dauka tare da ni. Ba ki taba samun wani farin-ciki daga gareni ba, ban taba faranta miki ba, don haka bai kamata na ci-gaba da tauye r rayuwarki ba, Hakan ya sa zan kawo wata shawara tsakanin mu." Afrah ta kara goge hawayen da ya fara fita mata, saboda tausayin musaddik, ta tattaro ta tashi ta zauna sosai tana kallon yadda babu wasa a fuskar Musaddik alamar maganar da yake son su yi babbace, kila kuma mai muhimmanci ce, a hankali ta ce "Wace irin shawara ce?” Ya dan gyara zamamsa gami da hadiye wani zazzafan yawu, alamar shi kansa abinda yake son ya furtan, ba me dadi bane a gare shi, kuma da alama ba don kansa zai kawo maganar ba, kila don sadaukarwa irin ta yadda ya fassara yadda Afrah take a gare shi. ya dade yana kure mata da ido sannan tamkar yana jin shakkar furta abinda yake son furtawa, sannan yace "Ba wata shawara bace Afrah face Shawarar rabuwa da junan mu”, Gaban Afrah ya yi mummunan faduwa domin jin maganar da bata taba zaton jinta daga bakinsa ba, Ta yi gaggawar kallonsa gami da bude baki, tana maimaita kalmar rabuwa. Ya gyada kai yace “Eh saboda bai kamata ki lalata rayuwarki don ki gyara rayuwata ba, kamar yadda ki ke son ki ganni cikin farinciki na rantse miki haka nake so na ganki cikin farinciki, yadda ki ke son rayuwata ta yi kyau haka nake son taki rayuwar ta yi kyau, duk yadda ki ke jin kin damu da ni haka ni ma nake jin na damu da ke “. Ya kara kallonta damuwa da tashin hankalin da ya gani shimfide kan fuskarta yasa ya ji zuciyarsa ta yi duhu sai dai duk da haka bai fasa cigaba da jaddada maganarsa ba “amma zan ba ki kwana biyu, ki yi tunani Domin babu abinda zan iya zartarwa sai da amincewarki amma ina son idan za ki yi tunanin, ki cire tausayina ki aje shi a gefe, domin na san shi kadai ne a ranki, ba so na ba Ki sa a ranki hukuncin da za ki yanke me kyau, shine zai ba ki damar auran wanda ki ke so, kuma yà dace da rayuwarki, ki haifi 'ya'ya daga Page 164 tsatson uba na-gari. Don Allah kada ki yi tunanin tausayina da taimako na a cikin tunanninki, ni kuma duk abinda ki ka yanke, da shi zan yi amfani." Ya kara kallonta, ya ci-gaba da cewa “Haka zalika kada ki damu da maganar kawu,ni zan fahimtar da shi komai, ba kuma zai taba ganin laifinki ba, a cikin wannan tunanin da nake son ki yi Tunanin makomar rayuwarki kawai za ki yi." Bai damu da kallon kaduwa da mamakin da take yi masa ba, ya tashi kai tsaye ya shige bandaki domin ya yi wanka. Ta dawo da kallonta ga cikin dakin da ta ga gaba daya ya na juya mata.ya aje wayarsa. Idanunta suka kara cika da hawaye. Ta yaya za'ayi Musaddik ya fara tunanin rabuwa da ita, har wane tunanin za ta yi wanda ba ta yi shi ba kafin auransu? Tabbas a da tausayinsa ne kawai a cikin zuciyarta, amma yanzu sonsa ya riga ya cika dukkan zuciyarta, ba ta jin akwai wani abu da zaisa ta rabu da shi, idan tunaninsa tausayinsa ne kawai a ranta to ya yi kuskure, domin duk da bakin halinsa shi zuciyarta ke so yanzu matukar so. Page 165 Ita ko Hajiya Hudah bayan tashinta, babu wanda ta tadda cikin musaddik da Alh Hamza, domin shi ma Alh Hamzan bayan tashinsa da ya fahimci Musaddik din ya tafi , shi ma sai ya tattara ya nufi gidansa, sosai ran Haj Hudah ya baci, domin ita kanta ba ta san dalilin daya sa take kwadayin Kara son ganin Musaddik ba a rayuwarta. Ta kira wayarsa, ya fi a kirga, amma wayarsa tana kashe. Daga bisani dai da hakurinta ya gaza dole ta kira Alhaji Hamza sosai ta nuna masa bacin ranta na rashin jiranta, da su kayi ta fito.sannan ta umarce shi daya gayyato Musaddik Party din da za su gudanar a gobe, tunda dama dawowar Musaddik din kadai take jira su yi party domin nuna murnarsu na cin zabensu. Alh Hamza Ya ba ta hakuri tare da yi mata alkawarin gayyato Musaddik kamar yadda ta bukata.wanda zuwa wannan lokacin Alh Hamza ya daina mamakin irin damuwar da Haj Hudah ke yi da musaddik ya sama ransa Allah ne dai ya dora Musaddik din a kanta kawai. Malam Mahmud kuwa tun da sassafe ya fita ya je (Police Station) da yawa, amma bai dace da samun Musaddik ba ga shi ya kwana wayarsa babu caji hakan yasa duk irin kiran da Afrah ta yi masa domin ta sanar da shi dawowar Musaddik bata yi nasarar samunsa ba.sai azahar ya yanke shawarar dawowa gida, domin ya ci abinci ya kuma dan huta sannan ya kara fita. Zuwa lokacin kuwa Inna Halima itama tana can cikin muguwar damuwa domin tun safen kafin ya wuce sai da ya shiga gidanta ya sanar da ita abinda ke faruwa, itama kuma duk motsi saita kira wayarsa domin ta ji halinda ake ciki amma wayarsa na kashe. Yayi sa’a ya tadda akwai wuta hakan yasa yana shigowa gidan ya sanya caji. Mama Hauwa kuwa sai kaiwa take tana komowa cikin rashin nuna danuwarta akan duk abinda yake faruwa, domin har cikin ranta tana ganin mallam Mahmud ya so ba kanshi wahala ne kawai don babu wani amfanin fita neman musaddik mutumin da ya saba yawon tambadarsa. Sai dai bata furta komai ba domin yadda ta ga fuskar mijin nata idan ta sake tayi masa maganar da bata gamsar da shi ba zai iya ci mata mutunci. Mallam Mahmud ya na idar da sallar azahar ya kunna wayarsa, kamar ana jira ya kunna ,Kiran Afrah ya shigo cikin Wayar, da sauri ya dauka, bayan sun gaisa ne, cikin natsuwa ta gaya masa tana ta neman wayarsa ta sanar da shi dawowar Musaddik da kuma abinda ya faru, amma wayar tana kashe Malam Mahmud ya numfasa cikin yi ma Allah godiya. Yar gidan Imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 166 Mallam Mahmud ya gyara zamansa, ya tsinci damuwa a cikin muryarta sosai, don haka yace, “ki yi hakuri Afrah ko wane bawa akwai irin kalar tasa kaddarar, don haka ina son ki sa a ranki wannan itace irin taki kaddarar,kuma kada ki yanke tsammanin samun shiriyar musaddik ki sa a ranki shi komai lokaci ne. Don haka idan Allah ya kawo iyakar lamarin,Shi kenan, sai ki ga kamar ma ba'a taba yi ba. shiriya da batarwa duk suna hannun Allah, kuma duk wanda Allah ya batar. Idan duk duniya za ta taru ba su isa su shiryar da shi ba, wanda kuma ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi, komai yana hannun Allah Shi ya sa ya ce mu yi imani da kaddara me kyau ko mara kyau. Saboda haka ki sa Musaddik da lamarinsa a matsayin kaddarar rayuwarki, ki yi hakuri, ki yi komai domin Allah, sai ki ga Allah ya taimakeki. Ki ci-gaba da yi masa nasiha gami da addu'a tare da biyayya a matsayinsa na mijinki, Wanda duk lalacewarsa Aljarnarki tana Karkashin kafarsa ne”. Cikin hawaye gami da sanyin jiki Afrah ta ce. "Na ji, nagode Baba kuma za ka sameni me biyayya tare da tsare dokokin aurena". 'A hankali yace “Allah ya yi miki albarka, ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira”, cikin jindadin addu’ar tace “Amin Baba”.sannan suka aje wayar lokaci daya. Mama Hauwa da take tsaye tun bayan daya fara wayar, ta yamutsa fuska ta wuce dakinta ba tare da tace uffan ba. Page 167 Domin tun daga ranar da Malam Mahmud ya yi mata takarar kada ta Kara shiga harkar Afrah da auranta, ta daukar ma kanta alkawarin ba za ta kara sa bakinta , a komai ba.Ko da ko me zai faru,. Hakan ya sa duk da ta san meke faruwa, ba ta yi magana ba, domin tasan ko da tayi maganar ma duk fushinsa a kanta zai juye.shi yasa ko jajantawa ba ta yi ba.Babu abinda ya dameta. Afrah kuwa tun bayan wayar da tayi da mahaifinta sai ta ji ta kara samun kwarin guiwa akan aurenta da Musaddik, damuwar da take ciki na maganar rabuwa da Musaddik ya yi sai ta ji ta ragu a zuciyarta, domin bata jin a yanzu akwai wani dalilin da zaisa ta iya rabuwa da Musaddik domin da zata iya rabuwa da shi da tun farko ma bata aure shi ba. Haka zalika ta yi mamakin yadda Musaddik ya ki fita ko'ina, tun bayan dawowarsa, bayan da ya yi wanka barci Kawai yake yi, ko wayarsa bai bude ba. Hakan ya sa bai san irin neman wayarsa da Alhaji Hamza yake yi ba, har sai wajen karfe goma na dare daya bude wayarsa, yana budewa, wayar Alhaji Hamza tana shigowa.Bayan ya dauka, tambaya Alhaji Hamza ya jefo masa, “Meye dalilin kashe wayarka? bayan ka tafi ba tare da ka yi sallama da kowa ba?" Ya dan runtse idanunsa yace "Na gaji ne, barci na yi, shi ya sa ban bude wayar ba, ya aka yi ne Alhajin Allah?' Daga nan Alhaji Hamza ya gaya masa bukatar Haj Hudah na amsa gayyatar Party din murnar cin zabenta, da za’a gudanar a gobe,Musaddik ya jinjina kai Yace "Karfe nawa ne goben?”, Yace "Karfe bakwai na dare wannan gayyatar ta musamman ce, da fatan za ka amsa"Ya gyada kai ya ce. "Babu damuwa Allah ya kaimu goben”. Daga nan suka yi sallama. Hakika yana son mutum me cika alkawari, daga dukkan alamu kuma Page 168 Hajiya Hudah mace ce me cika alkawari, da alamar wannan gwarnatin za ta amfane shi. Washegari kuwa tun karfe bakwai da rabi, Musaddik ya isa tankasheshen (Hall) din da ake gabatar da liyafar, haka zalika duk da dimbin jama'ar da ke wajen, sai da Musaddik ya samu tarba ta musamman daga Hajiya Hudah. Wacce ta ci kwalliya da kaya masu matukar daukar hankali. Daga wuyanta zuwa kunnenta da yatsun hannayenta duk zinare ne, sai daukar ido suke, ta sha kyau har ta gaji. Cike da farin-ciki da annashuwa ta dubi mutumin da ke gefenta, wanda shi ma yake cikin shiga ta alfarma, ya tsare gida, ta nuna Musaddik ta ce, cikin murmushi "Yallabai ga mutumin da na ke ba ka labarinsa da irin taimakon da ya yi min tun a waya Musaddik”. Mutumin ya dubi Musaddik ya yi masa kallo daga sama har Kasa,fuskarsa ta canja wani yanayi irin yanayi me wuyar fassara, sannan ya ce "Sannu Musaddik mun gode da kokarinka, duk da komai an yi shi ba na nan, to na sami labarin duk kokarin da ka yi da kuma hatsarin da ka tsallake, sannu da kokari", ya karasa magana yana kara Kafe idanunsa akan kyakkyawar fuskar Musaddik, wanda ya yi dan murmushi, domin ya jidadin yadda a yau aka maida shi mutum mai daraja, wanda rabonsa da ganin hakan har ya manta, ya dubi mutumin ya ce "'Haba ai babu komai, ni ma nagode, da irin taimakon da Haj tayi min”. Hajiya Hudah ta dubi Musaddik, tana kokarin gyara zamanta ta ce “Musaddik wannan shine mijina Alhaji Yusuf sanda” Page 169 Musaddik ya yi gaggawar Kara bude idanunsa sosai cike da matsanancin mamaki, ya Kara duban Alhaji yusuf sanda yace “Mijinki?" Ta amsa masa da "Eh, shine mijina”, ya kara kallonsa yace "Sannu Mai-gida, da fatan kana lafiya? “, Alhaji Yusuf Sanda ya kara kura masa ido tamkar yana wani tunani, sannan ya ce "Lafiya kalau Musaddik." Daga nan musaddik ya wuce a hankali zuwa kujerar da zai zauna, a yayin da Alhaji Yusuf Sanda ya bi shi da wani irin kallo da shi kadai yasan dalilin yi masa irin kallon. Har aka yi liyafar nan aka tashi Musaddik yana cikin matukar mamakin Kasancewar Haj Hudah matar aure, domin koda wasa bai taba kawowa a ransa cewa Hajiya Hudah Matar aure bace, domin babu alamar hakan. Kwarai musaddik ya so kebewa da Alhaji Hamza, don kuwa haka nan ya ji har cikin ransa yana son sanin wasu abubuwa game da Haj Hudah Amma hakan bai samu ba har sai da ya yi sallama da Hajiya Hudah, da nufin tafiya gida ta kuma gaya masa ta na son ganinsa gobe karfe sha biyu na rana, kafin ta wuce zuwa Abuja. Musaddik Ya kan rasa irin kallon da Alhaji Yusuf Sanda yake tsare shi da shi, da ya rasa dalili, domin ko ya ya ya juyo idon sa kawai ya ke gani a kansa.Sai da zai tafi ne, sannan Àlhaji Hamza ya dauke shi domin ya kai shi gida kamar yadda Haj Hudah ta bashi umarni. Page 170 A lokacin kuwa karfe biyu saura kwata ne na dare, sun dan yi nisa da fara tafiya, sannan hakurin Musaddik ya gaza, inda ya dubi Alh Hamza yace "Alhajin Allah, dama Hajiya Hudah matar aure ce?”. Alhaji Hamza ya dan saki numfashi, gami da ƙara riƙe sitiyarin motar sosai sannan yace "Matar aure ce mana, kai ba ka san hakan ba ne sai yau” Musaddik Ya girgiza kai ya ce. "Ban san hakan ba, ban kuma taba tsammanin hakan ba, domin kai kasan ban dade da fara yin hulda da ita ba, kuma kai na sani akan harkokinta Tunda kai ne ka nemeni akan aikin nata, Sannan kuma yanayinta da yadda take gawurtacciyar yar siyasa da yadda take gogaggiyar mace, gaskiya ban taba tsammanin mace irinta za ta iya zaman aure a karkashin wani ba, musamman ma yadda take da masu gidan rana a hannunta." Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce "'Haka ne maganganunka, amma lalle ka na bukatar ka san wace ce Hajiya Hudah, domin ka kore ma kanka shakka akan rayuwarta, amma dare ba zai ba mu damar na tsaya na gaya maka wacece ita ba.Sai dai abu daya zan gaya maka, tabbas duk da dukiyar da Allah ya ba ta, to fa Allah ya jarabceta da son yin aure, domin cikar kamalarta da take kokarin nunawa duniya ita me kirki ce, duk kuma da kasancewarta yar siyasa to tana son aure, kuma wannan siffa da ta fito da ita ta taimaka wajen kara mata yawan masoya a harkar siyasarta,kuma tabbas Alhaji Yusuf Sanda a yanzu shi ne mijinta”. Musaddik ya dubi Alh Hamza cike da gamsuwa akan maganar sa sannan yace “To amma a matsayinsa na mijinta, me ya sa ba'a san shi ba, Yar gidan imam ✍️ MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 171 musamman akan lamuranta na siyasa, me yasa kuma har muka sami damar kwana a cikin gidansa, ba tare da mun gan shi ba, sannan duk harkokin siyasarta, me ya sa babu shi a ciki?" Shi kansa musaddik baisan dalilin irin wannan tambayoyi ba da ya ke zubama Alh Hamza ba. Cikin rashin damuwa da tambayoyin na sa Alh Hamza ya amsa masa da cewa, “mun kwana a cikin gidansa ne, a dalilin a ranar baya ma kasar, yau din nan da rana ya sauka, yana Paris, duk wannan badakalar siyasar da ake yi bayanan, nasan kuma da yana nan da komai da shi za’a yi”.Musaddik ya dan dube shi yace “Me yake yi a Paris? Da ya fi masa muhimmanci fiye da shiga harkar matarsa, a lokacin da take da bukatarsa?" Zuwa lokacin Alh Hamza ya fara jin wani iri akan irin tambayoyin da Musaddik ke yi masa, a kan Haj Hudah, da mijinta. Duk da haka ya yi kokarin amsa masa yace “Saboda can din ma aikinta yake yi, domin kusan shi yake rike mata da kasuwancinta da take gudanarwa a kasashen waje, don haka bai cika zama ba a Najeriya, Kusan duk sabgoginsa ya fi yin su a kashashen waje”. Musaddik ya jinjina kai, ya yi shiru ne Kawai ba don wai tambayoyinsa sun kare a kan Hajiya Hudah ba, a'a sai don bai ga dalilin da zai zauna yana tambaya akan matar da baida wata dangantaka da ita ba, don haka ya ja bakinsa ya tsuke har suka kai Kofar gidansa Sannan ya sauke shi ya yi ma Alh Hamza godiya, gami da sallama sannan ya shiga buga get din, yana son a bude masa.Baba Mai-gadi ya taso da sauri domin sanin babu wanda zai buga gida a wannan lokacin sai musaddik, ya na bude masa kofar ya tsaya yana kallonsa,lokacin da yake shigowa abu daya ya yi ma Baba Mai-gadi dadi, shi kuma ya hana ya yi Masa fada kamar yadda ya saba kullum, wato ganinsa cikin hayyacinsa, babu alamar ya sha wani abu balle ya bugu, sai dai abinda bai sani ba ya sha abubuwansa sai dai ba da yawa ba, hakan yasa bai fita hayyacinsa ba. Page 172 ◦ Cikin nutsuwarsa ya yi ma Baba maigadi saida safe, sannan ya wuto cikin bangarensa. Lokaci daya Haj kilishi ta saki labulen windon da ta yaye tana kallon musaddik zuciyarta a dagule, tun bayan dawowarsa gida bata san komai dangane da abinda ya faru ba, domin Afrah bata kara shiga wajenta ba tun daga ranar da ta shiga neman taimakonta.taso ta ji inda ya shiga na tsawon wadannan kwanakin,duk da tafi yarda da yawon iskancinsa da ya saba ya tafi. Sai dai kuma ta na jin damuwar yadda tun bayan dawowar tasa ya rabu da shigowa gida a buge, domin tsawon lokacin da Musaddik zai dawo tana nan makale jikin windo tana jiran dawowarsa a buge, ko yau gashi nan fes da shi, ba cikin kazanta ba, har wata kwalliya taga ya sha, don ganinsa haka sai da gabanta ya fadi domin sosai ya yi mata kama da Musaddik din da, shin meke faruwa? Me yasa abubuwa suke yin baya maimakon su yi gaba su kuma kara tsananta. Afrah, Haj kilishi ta ambaci sunan ta cikin tsana, ta gyada kai kamar tsohuwar kadangaruwa, tabbas shigowar Afrah rayuwar musaddik bata raba daya biyu shine dalilin koma bayan al’amarin ta, dama batun yau take jin wannan fargabar ba, addinin Afrah da maida lamuranta da Allah kadai tasan sun isa su rushe mugun nufinta. Sai dai kuma bata jin zata cigaba da zurawa Afrah ido, zata yi maganinta. Shigar Musaddik cikin falon Afrah da ya samu turowa kawai tayi bata rufe ba, yasa yana shiga ya maida kofar ya rufe da makulli, zaune ya tadda ta kan sallaya ta idar da nafila hannunta na sama tana jero addu’ar ta, gefenta ya samu ya zauna ya zuba mata ido shi ma ya daga na sa hannayen, ta dade tana addu’a daga bisani duk tare suka shafa, a cikin sanyin murya yace “Allah ya amsa”, tayi dan murmushi tana zube masa da ido, ganinsa babu alamar maye ya sata farinciki, kamar yasan irin tunanin da take yi ya yi dan murmushi har gefen kuncinsa daya ya lotsa, sannan yace “Babu abinda na sha, a hayyacina na ke”, ta fadada fara’arta tace “Na gani, yaya musaddik Allah yasa ka dore a hakan”,. Ya yunkura ya tashi yana cewa “Amin, ki taso ki kwanta hakanan ki huta”, ta tashi tana cire hijabin kanta. Tace “Da so na ke na hada maka ruwan wanka kayi wanka kafin kayi bacci domin zaka fi jindadin bacci”baya son ya na yi mata musu don haka ya kyaleta ta hada masa ruwan wankan. Bayan fitowarsa kuma ta hada masa ruwan lipton me zafi ya sha ya gasa cikinsa, sosai yake jindadin jikinsa, daga bisani ya kwanta domin bacci yake ji sosai, Afrah ma tayi shirin kwanciya ta haye gefen mijinta ta dora fuskarta akan gadon bayansa, jin zuciyarta take tana mata dadi har wani sunsunar jikinsa tana jin irin kamshin da yake yi, fatanta daya Allah ya sa ya dore Washegari kuwa musaddik bai boyewa Afrah komai ba a game da kiran da Haj Hudah ke yi masa,ta kuma yi masa addu’ar Allah yasa alheri ne, da wuri yabar gida, ya biya wajen harkoknsa daga bisani Karfe goma sha biyu dai-dai na rana Musaddik ne ke zaune a falon Hajiya Hudah, a cikin gidanta. kan daya kujerar me zaman mutum biyu kuwa Hajiya Hudah ce zaune gefenta cikin Kayatacciyar shiga Mai- gidanta ne Alhaji Yusuf Sanda. Tun shigowarsa falon masu aiki ke shigowa da kayan ciye ciye, idanun Alh yusuf sanda na dore akan abincin da ake ajewa lokaci daya kuma yana dawo da kallonsa kan musaddik kamar wanda ke ganin matsayin Musaddik din bai kai a dinga yi masa wannan bajintar ba. Irin kallon da yake ma Musaddik har ya fara tunanin ko dai cikin dabi’arsa kallo yake, domin dai maganar gaskiya ya fara gajiya dan haka ya kosa ta gaya masa dalilin neman nasa ko ya samu ya fita ya bar gidan . Tamkar Hajiya Hudah ta karanci abinda ke cikin zuciyarsa ta dan muskuta ta gyara zamanta, sannan ta fara magana, “kamar yadda na yi maka alkawarin cewa bazan taba mantawa da kai a cikin tafiyata ba, hakan yasa nayi shawara da mijina ya kuma ba ni goyon baya asalima shi da kansa ya kawo shawarar irin aikin da ya kamata na baka,domin a yadda Alh Hamza ya yi min bayaninka yace baka da wani aikin yi da ya wuce zaman banza da kuma irin aikin da muka dakkoka kayi mana”. Musaddik ya gyada kai alamar hakane, a yayinda Alh yusuf sanda ya kara wani narkewa akan kujera yana cigaba da nazartar yanayin musaddik. Haj Hudah ta cigaba da magana “kayi Kokarin da bazan taba mantawa ba, don haka zan baka wannan aikin”. Alh yusuf sanda ya amshe maganar yace “Hakanan na ji zuciyata ta sami nutsuwa da kai , tun a ganina da kai na farko a jiya, naji a raina matata zata samu kariya daga gareka, shi yasa na zabi ta baka irin wannan aikin, domin shi ne nasan ko yaushe zaka iya kasancewa tare da ita, yadda bana zama nasan zan samu nutsuwa a duk lokacin da na tuna kana tare da ita domin tsare lafiyarta”. Page 173 Ya dan rankwafo yana watsa masa irin kallon da Musaddik ya fara tsana, sannan ya cigaba da cewa “ wannan dalilin ne yasa na ce ta daukeka aiki a matsayin me kare lafiyarta na musamman, wanda duk inda zata dole ka kasance tare da ita”, A gaggauce musaddik ya dago ya na kallonsa, ya rasa dalilin murmushin da ya ga Alh yusuf sanda yana yi, idanunsa kuma suna bayyanar da wani irin yanayi sa musaddik bai fahimci komai ba. “Me kare lafiyarta?” Musaddik ya kara tambaya, Alh yusuf sanda ya kara murmusawa yace “Eh, domin a yanayin halittarka nasan zaka iya, don haka ina son ka karbi wannan aikin domin idan ka karba aiki ne wanda ba zaka taba mantawa da shi ba a rayuwarka”, ya karasa magana wannan karon dariya yake sosai ba murmushi. Haj Hudah ta aje numfashi a hankali, sannan tace “Kada ka damu da albashi, domin zan yanka maka albashi mai tsoka, wanda zai isheka daukar dawainiyar kanka da iyalinka, tunda dama Alh Hamza ya gaya min matarka daya ba ka da da kuma, don haka abu ne mai sauki, albashinka zai

Chapter 11 of 15