Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dakin Mallam Mahmud. Mama Hauwa na zaune akan kujera yar tsugunno tana jin maganar da Mallam Mahmud yake yi “Duk kokarina na hada Na'ima da Musaddik aure, abin ya ci tura, saboda rashin samun goyon bayan mahaifiyarku. Karshe ma Hauwa ta dauketa ta boyeta ba tare da na san inda ta kai ta ba, don haka na, Kiraku domin na gaya maku Afrah ta share min, hawayena ta amince za ta auri Dan-uwanta, shi ya sa na kiraku domin na shaida maku, na ba Musaddik Afrah, na kuma sanya ranar bikinsu uku ga sabon wata me kamawa”, Mama Hauwa ta yi karaf! Ta amshe cike da farin-ciki “ Alhamdulillah, wai hankalina har ya kwanta. Allah ya ba su zaman lafiya, yanzu ka yi magana, dama Na'ima ai ba ta yi dai-dai da shi ba ita ma Afrah ta gama kinibibinta matsalarku, ni dai tunda Allah ya kubutar da 'yata komai ya yi dai-dai “ Mansur ya kalli Kabir sannan ya dubi Malam Mahmud ya ce”Amma baba anya kana ganin wannan lamarin me yuwuwa ne kuwa?” Ya gyada kai yace “kwarai kuwa mansur me ka gani Mansur. ya gyara zamansa yace “Baba gani nayi kamar ba’ayi mata adalci ba ba hadata aure da Page 50 da mutum irin Musaddik. Baba ko yanzu da zan taho nan na hadu da shi yana rangaji alamar a buge yake, gaskiya ina ganin bai kamata a hada su aure ba, domin babu ta inda suka dace, halayen Musaddik a gaskiya sun kazanta ." Kabir ya amshe naganar “Kwarai kuwa Baba, idan aka aura ma Afrah Musaddik, gaskiya ba'ayi mata adalci ba, ba za ta iya zaman rayuwa da shi ba. Baba kai ma ka san ko waye Musaddik, gaba daya aure ma bai dace da shi ba, domin babu Macen da zai iya rikewa, don Allah ka janye wannan maganar baba”. Malam Mahmud ya numfasa ya ce “Na ji dadin yadda ku ka damu da rayuwar kanwarku, sai dai ku sani, ina da manufar hada auran Afrah da musaddik Tunda kuma ta yarda ta ba ni goyon baya, babu abinda zai canja, uku ga wata zan daura auransu, idan lallai kun damu da ita, to ku tayata addu'ar Allah ya ba ta ikon cinye jarabawar daya dorata akai" mansur yace “Amma ….bai karasa ba Mama Hauwa ta katse shi "Kai ya isheku, ba "Yarsa bace, yana da damar da zai yi duk abinda ya ga damar yi da ita, ina ruwanku" Mallam Mahmud ya yi mata wani irin kallo me cike da tsana ya ce "Ni ban sa maganar nan da ke ba, ban gayyatoki cikinta ba, don haka zai fi sauki ki rufe bakinki tunda ba maganar yarki Na’ima ake yi ba, kamar yadda kika fada ne ya ta ce yar kuma da nake alfahari da ita”. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam Kuyi comments domin karfafa guiwa MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 51 Mama Hauwa ta saki tsaki ta cc "Dama ai ban ce ya shafe ni ba, ka ga wanda ya shafenin ai na hana, na kuma dauke "yata, goben nan kuma za ta dawo gidan ubanta. Allah ya kawo mata miji nagari, ba tambadadde irin Musaddik ba.” Ta mike ta shige dakinta, a yayin da Mallam Mahmud ya dubi su Mansur cikin Bacin ran maganganun Mama Hauwa ya ce “Ita kenan maganar, ku na iya tafiya, Allah ya ba mu alheri” Yana gama fadin haka ya tashi ya shige dakinsn, ya bar su nan zaune suna kallon juna, daga bisani su ma suka tashi suka shiga dakin mahaifiyarsu . Suna shiga Mama Hauwa ta hau fada “Ina ruwanku da za ku hana shi hada auran Afrah da mahaukacin dansa, can su suka sani, meye naku Shi ya fi kowa sanin waye Musaddik, Kuma ita kanta wacce ku ke kokarin kwato mata "yancin, na Yancin na yi imanin kunya za ta ba ku, don Yadda na san wannan kinibabbiyar yarinyar. To ba za ta taba kauce ma umarnin Mallam ba, matukar dai ya bude baki ya nemi ta auri Musaddik, to tabbas duk duniya babu wanda zai hana hakan faruwa, sai dai Allah, don haka ban ga amfanin sanya bakinku cikin wannan maganar ba Page 52 Mansur ya kalleta ya ce “ mama rayuwar Musaddik kullum kara lalacewa take yi, babu wani abun burgewa ko kadan a rayuwarsa. Ko wacce ba ni wacce ba ni da dangantaka da ita, ba zan so ta aure shi ba domin na san rayuwarta ta gama lakacewa Balle jinina kanwata Mama, amma tunda ba’a bukatar gudunmuwar shawararmu, to Allah sanya alheri, fitinar da ke ciki. Allah ya Kare Afrah kuma Allah ya kawo mata mafita." Ta yi masa wani sakaran kallo ta ce “To Shehin Malami, addu'ar taka ta yi, Allah ya karba akaramakallahu” Kabir ya ce "Ai Kabir ya dubeta yace “Ai duk maganganunsa gaskiya ne. Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri" Gaba dayansu suka tashi ba su damu da hararar da take banka masu ba, suka yi mata sai da sale, suka kama hanyar gida. Ita ko Mama Hauwa zuciyarta cika ta yi da tsananin farin-ciki, dama ba ta taba yi ma Afrah fatan samun miji na-gari ba, burinta ya cika Afrah za ta yi auran wahala, •ta yi wani bushasshen murmushi, domin dukkan mafarkinta akan Afrah ya kusa tabbata. Ta lalubo wayanta da ke kasan filo, ta kira lambar Na'ima, tana dauka, bayan sun gaisa ta tace “ Na'ima ki shirya gobe ki dawo gida. Cike da son karin bayani Na’ima tace "Na dawo gida Mama? Babu sauran matsala kenan”. Page 53 Mama Hauwa cike da fara’a tace "Eh, ki dawo gida, saboda komai ya wuce maganar auranki da Musaddik an maida shi Kan Afrah Na'ima ta ce "Mama kan Afrah, ta Kuma yarda ta amince?" Mama Hauwa ta yi dariya sosai tace “Tana da za6i ne? Ai in dai akan mhaifinta ne, ba ta da zabi, duk abinda yake so shi take so, ko da ba ta so, ko kin manta halinta ne kinibabbiya ce mai kokarin maida kanta mara "'yanci, saboda farin-cikin mahaifinta, don haka ta yarda, duk kuma abinda zai biyo baya, wannan ruwansu, su ta shafa" Na'ima ta ce "Amma lallai Afrah ta shiga tara ma ba uku ba". Mama Hauwa ta ce "Idan ana Shiga dari ma, to ta shiga, auran mashayi sakarai wanda bai san darajarsa ba balle ya san darajar wani" Na'ima ta ce "Lallai kam!" "Saboda haka ki tattaro ki dawo, dama kadaicin rashinki duk ya ishe ni”, cike da murna Na’ima tace “zan dawo goben nan kamar yadda ki ka ce mama “, daganan su kayi sallama, kowa cike da farincikin kawo karshen matsalar su. Page 54 Gida ne katon gaske mai kyakkyawan fasali, Kallo daya za ka yi masa, ka tabbatar da cewa gida ne na masu hannu da shuni, gidan marigayi Alh Mansur maifata kenan. Hajiya Kilishi na zaune akan daya daga cikin kujerun da suka mamaye katon falon nata, idonta dore akan akwatin Talabijin. Sallamar Musaddik ya sa ta kalli kofar falon ba tare da ta amsa sallamar ba. Shi ma bai jira ta amsa ba, ya shigo lokaci daya, ya zauna yana kokarin gaisheta, ta amsa kamar kullum ranta a bace, fuska ba walwala, "Daga ina ka ke yau kwana biyu kenan rabon ka da gidan nan “ ya kaskantar da kansa yace “Haj ayi hakuri aiki ne kawai ya yi min yawa” tayi masa wani irin kallon banza tace “Aiki ?har wane auki ka ke da shi, kana dai can yawon gantalinka da ka saba, ai ba hanaka zanyi ba Allah ya bada sa’a”. Musaddik ya numfasa, duk da baya jin dadin yadda Hajiya Kilishi take bi da shi, to fa bai hana shi yi mata biyayya tare da tsoron bacin ranta ba bai kuma taba kallonta a matsayin mai kinsa ba asalima tana daya daga cikin Mutanen da Yake tsananin ganin girmansu tare da. ganin mutuncinsu . Ya dago yana kallonta, a yayin da ta maida kallonta kan akwatin Talabijin dinta, tana fadin Page 55 "*Idan yunwa ce ta kawoka, ka shiga kicin ka debi abinci, don Lami ta fita balle ta kawo maka Ya girgiza kai ya ce “A’a Haj a koshe nake magana dai na zo muyi da ke” ba tare da ta kalle shi ba tace “wace irin magana ce?” Ya dan muskuta ya gyara zamansa, sannan ya ce "Magana ce mai muhimmanci akan aurena da da ya gabato”, A gaggauce Hajiya Kilishi ta juyo ta kalle shi, hankalinta a tashe, kamar wacce aka gaya ma sakon ranar mutuwar ta "Auranka?" Ta maimaita a tambayance, ya daga kansa ya ce "Eh, Kawu Mahmud shi ne ya ba ni auran Yarsa Afrah, ya kuma sanya ranar daurin auren uku ga watan da zai kama, shine ya ba ni damar na zo na sanar da ke.....?" Ta katse shi a matukar fusace ta ce "'Ka zo ka gaya min a matsayina na wa, me na isa, sannan meye amfanin gaya min, tunda har sai da ku ka gama kulla komai sannan aka turoka ka gaya min To meye amfanin gaya min? Musaddik ya rude, a dalilin ganin 6acin ranta ya ce "Don Allah ki yi hakuri Hajiya. Kada ki sa damuwa akan wannan maganar, ni kaina a Kurarren lokaci aka gaya min, sannan babu wani bata lokaci ya sanya ranar “ Ta sakar masa harara cikin hadewar fuska da wani bakinciki ta ce” a kurarren lokaci ai komai kurewar lokaci, don me ba za ka iya zuwa ka gaya min ba? Page 56 tabbas akwai wani abun da Mallam Mahmud ya hanga yasa yake son hada auranka da Afrah , domin tabbas! Aure a yanzu bai dace da kai ba, illa iyaka wata manufa da yake da ita, to bari kaji idan yana tunanin dan abinda ya rage maka na daga gadonka ne yake son ya hada auranka da 'Yarsa, don su kwashi rabonsu. Ai ya kamata ka yi masa bayanin cewa ba ka da sauran komai, domin abinda ya ragen ka dade da cinyewa, wasu ka sayar , ka yi shayc-shaye da kudin, babu abinda yarsa zata aura sai musaddik tsurarsa da wahalarsa “. Hankalin musaddik ya tashi ko kadan baya jin dadin maganar da Hajiya Kilishi take yi ta cin fuska da wulakanci, ga kawunsa. ya yi Kasa da kansa, ransa na kuna, a yayin da ta cigaba da magana “Ni wannan yarinyar ko kadan ba ta burge ni, ba ta taba ba ni sha'awa ba , don haka bana murna ko maraba da auranka da ita". Ya dago ya kalleta sosai sannan yace "Hajiya ke ce mutum na farko a duk duniya da na taba jin kin ce Afrah ba ta burge ki, domin Afrah tana burge kowa, ko ba don kyawun fuskarta ba, don kyawun halayenta da natsuwarta, dole ta burge kowa”, Hajiya Kilishi ta ce tana yi masa wani mugun kallo “ Wato ka na son auranta kaima ko Musaddik, ba shirin Kawunka bane kadai, kai ma ka na so” Musaddik ya hadiye bacin ransa ya ce Page 57 “Aure baya gabana ba na kuma yi ma kaina sha’awar zama shugaban kowace mace. Domin na san ba zan iya yi mata adalci ba, amma zuciyata na sameta cike da dokin auran Afrah, don haka ke ma ki amince da ita, domin alfarma za ta yi min na aurena.” Yana gama fadin haka ya tashi ba tare da ya saurari komai ba daga gareta , ya fice ransa da hankalinsa a tashe Bakin-ciki da tsananin damuwa suka Kara cika zuciyar Hajiya Kilishi. Ta tashi ta shiga kai gauro ta kai mari a tsakiyar falon, ko kadan ba ta bukatar Musaddik ya Kara yin aure, domin tana da tabbacin idan ya yi aure ranta na bata Dole ya rage wani abu daga cikin ta'asar da yake yi, wanda ba za ta taba son hakan ba, kuma auran nasa zai zama sanadiyyar da zai samu shi ma ya kafa tasa zuri'ar, sannan ko yaya ne za 'a dinga ganin mutuncinsa, abinda bata so kenan amma tunda yana da iyali, ko ya ya ne sai an samu me dan ganin mutuncinsa . hakika auran Musaddik fitina ne a gareta, don ranta baya so. Kuma abu ya zo gaba daya cikin kurarren lokaci, amma gaskiya dole ta yi wani hobbasa akan kokarin watsa auran tun kafin ayi, gara Musaddik ya zauna ya ci-gaba da gurbatacciyar rayuwarsa ta yi imanin kuma babu macen da za ta tattagoma kanta auran shashasha irinsa, In dai ba irin wannan auran zumuncin ba na sadaukarwa Babu ta inda za'ayi Musaddik samu auran wata mace a irin lalacewar rayuwar da ya ke ciki. Page 58 shin ya aka yi Malam Mahmud ya yi tunanin yi ma musaddik aure da yarsa kuma meye manufarsa?”. Domin dai ta fi kowa sanin cewa Mallam Mahmud ya san Musaddik bai aje ba, bai ba Wani ajiya ba balle ta yi tunanin don abin duniya Yake son ya hada auran nasu, kamar yadda ta fadawa musaddik hakika wannan abu bai yi mata dadi ba kwata-kwata. Hakan ya sa gari na yin sanyi, karfe biyar da rabi dai-dai motarta ta tsaya a kifar gidan Mallam Mahmud, ga sa'arta kuma Malam Mahmud din yana gida bai dade da dawowa-gidan ba,mama Hauwa ce ta tareta “Hajiya Kilishi ce da yamman nan? “ Cewar Mama Hauwa, tana kokarin aje tsintsiyar hannunta, da take kokarin tattara gudan da ita Hajiya Kilishi ta ce fuska tamke “Nice Hauwa” Mama Hauwa tace “ shigo mana daga cikin daki Ta girgiza kai ta ce "A'a ba zama na zo yi ba, sauri na ke na koma gida, wajen Mai gidan na zo, ina fatan yana nan" Mama Hauwa ta yi murmushi dimin ta fahimci Hajiya Kilishi bada arziki ta zo ba, ta san kuma dama ba wata jituwa ce tsakaninta da Malam Mahmud ba, don haka tace “yana nan” Kafin ta yi magana. Malam Mahmud ya fito daga dakinsa yana kallon Hajiya Kilishi yace "Sannu da zuwa" da sauri ta juyo ta kalle shi ta amsa "Yawwa, ina gajiya?" "Lafiya Kalau, hala dan naki ya gaya miki sakona ne?" Page 59 Tace cukin kara hade rai “eh ya zo ya sanar da ni dazu shine dalilin zuwana ma yanzu”Yace “Toh” .Hajiya Kilishi ta gyara tsayuwarta, sannan ta fara nagana “Yanzu tsakani da Allah wannan abin an yi dai-dai kenan?" Ya ce *Kamar yaya?" Ta ce “Kamar na yadda za'a gaya mana magana daga sama, ni dai a'iya sanina Musaddik da Afrah ba sa soyayya, haka zalika bai taba yin min maganar yana son ya Kara yin aure ba, tun bayan rabuwarsa da Hannatu, don haka na yi mamakin jin lamarin. Kuma wane abu ne ya sa ka tunanin kulla wannan auran? Bayan kana sane da halin da yake ciki, auran ma ba zai iya rikewa ba. Don haka ina ganin maganar auran nan a bar ta kawai har zuwa lokacin da zai sami natsuwa, ya nemo 'yar da yake so da kansa” Malam Mahmud ya jinjina kai cikin wani irin Yanayi yace “wace irin magana ce wannan ki ke yi, shin meye amfanin sanya ma Musaddik ido ya Ki yin aure, don kawai ana kallonsa a matsayin dan iska Wanda ke kin sani , ni na sani jama'ar ma da suke yi masa kallon hakan sun san cewa da ba haka yake ba, kaddarar rayuwa ta maida shi haka. To don me ba za mu taimake shi ba, ni zumunci na ke ma, domin Musaddik ba shi da bambanci da dan da na haifa, tunda "Yar-uwata ce ta haife shi, don haka ko ta wane hali, dole na taimaka ma rayuwarsa, zan kuma aura masa Afrah Page 60 ne , domin ya samu mai kulawa da shi da kuma rayuwarsa. Don haka maganar a janye wannan auran ba za ta yiwu ba, domin mun riga mun gana yanke magana.” Hajiya Kilishi ta yi tsaki ta ce "Ka na wani daga murya sai ka ce wanda aka zo yin fada da shi ni ba fada ya kawoni ba, rayuwar "yarka da na ga kana so ka lalata, shine na ke son na fahimtar da kai kuskuran hakan, idan kuma da manufarka ta daban ne to ka yi ganganci. Domin ka fi kowa sanin Musaddik baida ragowar komai na gadonsa, ina tsammanin wurin zama ma, sai dai idan na ga dama na ara masa, daki haka idan ka na tunanin abin duniya ne, ya sa ka ke Kokarin cuso "'yarka, to ka yi kuskure..... Ya dakatar da ita rai a matukar bace ya ce “Kada ki Kara yi min wannan maganar, wane arziki zaki gaya min, ke ce ke hadamar arzikin Musaddik tunda kuma kun gama cinyewa ke da Yar’uwar ki Hannatu, ba shi kenan ba, ku je ya yi Maku arzikn duniya da lahira, yadda kuma Hannatu ta bar shi shine ku ke tunanin ba wacce za ta iya auransa, to kunyi kuskure Auran Afrah da Musaddik ko bayan raina ne, sai anyi shi, kuma za ta zauna da shi ko da shi ya fi kowa talauci da lalacewa, domin na isa da 'Ya ta, za kuma ta share min hawayena tun kafin ya zuba”. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️ Page 61 Haj kilishi ta kara fusata tace "Eh, Hannatu ta bar shi, don bai dace da ita ba, dukiya kuma da ka ke magana da kansa ya bayar, don haka ba dalilin maimaita maka, 'yarka ko ka yi ta aura masa, ina kuma taya yarka murnar auran musaddik, ina mata barka da fadowa rayuwa mai cike da nadama da danasani ". Daga nan bata jira komai ba ta juya a fusace za ta tafi. Dai-dai zaure suka ci karo da Afrah, ta tsaya ta yi mata wani mummunan kallo, Sannan ta fice ba tare da tace mata uffan ba Jikin Afrah a sanyaye ta shigo cikin gidan, ganin fuskar mahaifinta a dagule ya tabbatar mata da cewa ba abin arziki ya kawo Hajiya Kilishi gidansu ba, ta kalli Mama Hauwa ta ga sai Fara’a take, tana harkarta. Afrah ta dawo da Kallonta ga mahaifinta ta ce a sanyaye "Baba make faruwa ne, naga Hajiya Kilishi a fusace ta fita?"mallam mahmud ya yi gaggawar boye damuwarsa, yace “A’a Afrah lafiya kalau, na kirata mun yi magana ne a kan auranki da yayanki”, Mama Hauwa ta yi karaf! Ta ce "Me ya sa ba za ka gaya mata gaskiyar cewa Hajiya Kilishi ba ta son auranta da Musaddik ba, kuma ta yi maka maganganu na wulakanci da batanci wanda ta saba” A kidime Afrah ta dubi mahaifinta ta ce "Wulakanci da Batanci akan me? Wace ce ita da har take da dama da garantin tsayawa a gaban mahaifina ta yi masa wulakanci?” Mallam Mahmud Page 62 ya dubi Mama Hauwa ransa a bace zai yi magana kenan, ta riga shi. "A'a ai ba ta da laifi, don kawai ta zo ta tunatar da shi cewa Musaddik baida sauran ko Kwandala a gadonsa, don haka idan don Kwadayin dukiyar ya sa zai aura masa ke, to ya fa tuna baida komai, kuma ni ban ga laifinta ba. Don ta yi tunanin hakan, don kowa ma hakan zai dauka, don idan ba hakan ba, ba dalilin aura ma Musaddik ke a irin muguwar rayuwar da ya dora kansa a kai ………? Cikin fusata Malam Mahmud ya daga ma Mama Hauwa hannu ya ce "'Idan ki ka Kara yin magana akan batun da ya shafi Afrah da Musaddik ko auransu ko akan abinda ya danganci Hajiya kilishi Ki rubuta ki aje, zan yi matukar ba ki mamaki, domin zan yi miki abinda mafarkinki bai taba nuna miki zan yi miki ba, zan aje duk wata alaka da ke tsakaninmu, na ci miki mutunci" Mama Hauwa ta bude baki za ta yi magana, ya kara dakatar da ita “kada ki yi min wata magana, ki wuce ki tafi, ki ba ni waje.” Tabbas Mama Hauwa ta ga bacin rai a fuskar mijinta me tsanani, don haka jikinta ya yi sanyi, a hankali ta juya ta shige dakinta, a yayin da Mallam Mahmud ya dawo da kallonsa ga Afrah wacce take take tsaye kamar an dasata. Page 63 '"Baba abinda Mama Hauwa ta fada gaskiya ne? don zan dauki komai, amma banda wulakanta min kai, don ka fi karfin komai a gare ni,” Mallam Mahmud ya yi dan murmushi cike da kaunar yarsa yace “Hakane Afrah, amma bana son ki sa wannan a ranki balle ya dame ki tunda mu munsan duk abinda muke yi domin Allah mu ke yi kuma dama ai bai kamata Hajiya Kilishi ta so duk wani ci-gaba da Musaddik zai samu ba. Tunda ba ta sonsa ba ta kaunar sa, ba kuma ta kaunar duk wani ci-gabansa, shi kadai ne bai gane hakan ba, yake daukarta a matsayin mai, kaunarsa don haka ko kadan kada ki sa damuwa akan lanarinta”.Afrah ta numfasa tace "Haka ne Baba, amma ci maka mutunci shine abinda zuciyata ba za ta dauka ba". Ya ce "Ki yi hakuri ya ta ki sabar ma kanki kauda kai akan duk wani da zai yi batanci a gareni, musamman haj kilishi wacce zakiyi rayuwa da ita idan kuma ta gane taba ni shine karayar ki shikenan ta samu hanyar kuntata miki Ki sa ma kanki hakuri, kada kuma ki nuna ma kowa, taba ni shine nakasunki, don idan makiyi Ya gano inda lagonki yake, to za ki sha wahala, don ya sami hanyar 6ata miki rai kenan." Afrah ta dan samu natsuwa sannan ta ce “ Na yarda da maganarka Baba, nagode kuma da fahimtar da ni da ka yi". Ya yi murmushi ya ce “Badamuwa. Ki je ki yi sallah, ni ma masallaci zan tafi, Page 64 ga shi can ana shirin tayar ma da sallar." Ta gyada kai, lokaci daya ta wuce zuwa dakinta, domin ta aje jakarta ta makaranta,. Zuciyarta cike da tsanar Hajiya Kilishi. Domin duk wanda zai taba mata mahaifi, to ba ta da makiyin da ya fi shi. Karfe daya da rabi na rana Hajiya Kilishi ta tsayar da motarta a kofar gidan Hajiya Rakiya, lokaci daya ta janyo wayarta da ke dore a saman motar, ta dannan ta kira wayar Hajiya Rakiya. Bugu daya ta dauka kamar ta na jira "Hajiyar Allah.”, ta fada cike da zumudi, Haj kilishi ta amsa "Ga-ni a kofar gidanki, ki yi sauri ki fito don Allah da sauri tace “Toh, ga-ni nan fitowa yanzun nan" Mintina uku tsakani Hajiya Rakiya ta fito a gaggauce, ta bude gaban motar da sauri ta shiga, bata jira komai ba ta harba titi, Sun yi tafiya me nisa, sun fito daga cikin garin Minna har zuwa wata yar karamar rugar fulani, kafin su karasa rugar. Hajiya Kilishi ta tsayar da motar, suka fito da Kafa suka Karasa rugar. A dai-dai gaban wata Yar Karamar bukka suka tsaya, gaba dayansu. Hajiya Kilishi ta ce “ Ahuwonka”daga cikin bukkar aka amsa “lale, shigo daga ciki”, nan da nan suka cusa kai cikin bukkar, wani bafullatani ne mara kyan gani a zaune akan wani buzu, Gabansa duk tarkace ne na kayan tsubbu, yana ganin Hajiya Kilishi, ya washe baki, ya hau fara'a, ya ce. Page 65 "'Ashe Hajiya ce?" Ita ma ta yi dariya ta ce "Nice Mai Rakwacam!” Bayan sun zaunane, Mai Rakwacam ya bukaci jin abinda ke tafe da Hajiya Kilishi, ta gyara zamanta tana kallonsa sosai ido cikin ido, Sannan tace “Na zo hankalina a tashe ne Mai, Rakwacam Akan maganar MusaddiK ne, aure zai Yi,ni kuma ko kadan ba na bukatar ya yi auren, domin auransa zai iya zama hanya ce ta arziki, kuma hanya ce da za ta iya kai shi ga samun canjin rayuwa. Ni kuwa ka fi kowa sanin duk wani ci-gaba na Musaddik ba na maraba da shi, kuma Yarinyar Yar-uwarsa ce ta can dangin mahaifiyarsa, auransu ina da tabbacin zai Kara kusanta shi da dangin Mahaifiyarsa wanda kasan bana son hakan tun farko,”Mai Rakwacam ya dubeta ya ce "Yanzu me kike bukatar ayi Haj “ Ta muskuta ta kara lankwashe kafafunta Ta ce "Kamar yadda ka saba taimaka min kuma na ke ganin haske, shine na zo gareka, abinda na ke bukata, shine a lalata Maganar auran, kada ya yiwu, a bata komai da Komai a bar shi a yadda yake, ya ci-gaba da gararambarsa ta lalacewa kowa ya daina ganinsa da wata daraja” Mai Rakwacam ya janyo wani katon tulu ya shiga surkullansa, ya dauki tsawon lokaci yana aikin tsubbunsa, sannan ya dago ya kalleta, Yana girgiza kai, muninsa ya kara fitowa,sannan ya ce. Page 66 "A gaskiya Hajiya kin san tsakanina da ke babu cuta babu cutarwa, ba na kuma boye maki duk wani abu da na gani na dadì ko na rashin dadi don haka maganar auran Musaddik babu abinda zai hana shi yiwuwa, sai dai mutuwar daya daga cukinsu”, Hajiya Kilishi ta dafe Kirjinta, hankalinta ya tashi matuka ta ce "Yanzu babu wata hanya da Za’a bi a dakile lamarin, dole sai hakan ta faru?" Ya jinjina kai yace “Kwarai kuwa Haj . Dole sai wannan auran ya kasance, babu wata mafita, idan kuma ba ki yarda ba, to ki je duk inda za ki je, amma ki sani, kudinki za su ci a banza babu biyan bukata” Hajiya Kilishi ta kalli Hajiya Rakiya, duk jikinsu a sanyaye, sannan Hajiya Kilishi ta dawo da kallonta ga Mai Rakwacam ta ce "Na yarda da maganarka, ban kuma kasance me jayayya akan duk abinda ka fada ba, domin ina ganin gaskiya a cikin aikinka, sai dai abu daya" Ya dubeta yace “Menene shi?"' Ta ce "Na saduda akan auran, tunda banda wata mafita amma ina son Musaddik ya dawwama akan halin

Chapter 4 of 15