Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
“Baka da sabulun wanka da wankin ne”, ya gyada kai alamar eh ba tare da ya yi magana ba tace “Amma ba ni nace ka dinga zuwa kana yin wanki ba,har cewa nayi ka dinga dakko wankin kana kawowa gidana ni zan dinga yi maka, irinku ba a wofintar da ku ajiiki ya kamata a dinga janku , na gaya maka duk damuwarka ka dinga zuwa kana gaya min” idanunsa cike da hawaye ya mike tsaye ya juya baya saboda baya son ta ga hawayensa , Yace cikin muryar kuka yana magana yana tafiya, “zan zo nayi wankin gobe inna”daga nan ya yi sallama da ita ya fice daga gidan. Page 16 Zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka gama tattaunawa da Innarsa.washegari da yamma dawowar Afrah kenan daga makarantar Islamiyya, tare suka jero da Sayyadi Habibu, hira suke cike da annashuwa da kaunar juna har zuwa kofar gidansu. Anan suka tsaya, domin su yi sallama, dai-dai lokacin Musaddik ya tsaya shi da dan acaba, daga shi har wanda ya goyo shi, babu mai kyan gani idanu jajir! "Ka jira ni yanzu zan fito" Musaddik ya gaya ma abokin tafiyar ta sa, sannan kai tsaye ya nufi cikin gidan, murya a sanyaye Afrah ta gaida shi, ya amsa yana kallonta "Afrah ya gidan?" Ta ce "lafiya lau". Mallam Habibu ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya shige cikin gidan, a yayinda Mallam Habib ya dawo da kallonsa ga Afrah, wacce duk fuskarta ta canja ta shiga wani irin yanayi na damuwa, ya ce "Afrah me ya faru ki ka canja fuska haka?” Ta yi dan yake ta ce "Ba komai Ya Sayyadi." ya gurgiza kai cike da kulawa yace “Hmmm! Da komai mana, Afrah duk abinda ki ka ga ya faru da bawa, to rubutacce ne akan allon kaddararsa, ko kadan Kada ki sa damuwa akan lamarin Dan-uwanki, bai kamata ba, domin addu' a kawai ita ce magani, ita ce kuma zata taimake shi Page 17 Domin duk wanda Allah ya Batar, babu wanda ya isa ya shiryar da shi, haka zalika duk wanda ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi. Idan ki na tuna haka, ba za ki taba samun damuwa ba. Da ai ba haka yake ba, don haka a yanzu ma wata kaddarar ce ta hau kansa, wacce sai an dage kwarai da addu’a”. Afrah ta gyada kai cike da jindadin nasihar malaminta, wanda hakan yana daya daga cikin dalilan da ya sa take matukar sonsa, ta ce, “Naji ya Sayyadi, nagode kwarai da nasiharka, na kuma yarda da duk abinda ka fada, sai dai ina rokon kai ma ka dinga sa Dan-uwana cikin addu"arka da bakinka me cike da ambaton Allah” Ya yi murmushi ya ce "Zan sa shi a cikin dukkan addu'oi ta Afrah. Allah ya shiryemu gaba daya." Ta amsa "Amin, nagode", Hayaniyar da Afrah ta jiyo tana tashi daga cikin gidan, ya tilasta mata yin sallama da Mallam Habib, domin ba ta son ya fahimci akwai matsala a cikin gidan, bayan sun yi sallama. Da sauri Afrah ta shige cikin gidan hankalinta a tashe , muryar Mallam Mahmud cike da fusata yake cewa, “Na gaya miki ki yi shiru ko, Na’ima dai ya ta ce, ina da damar da zan aura mata duk wanda na ga dama ko da dan kashin kasuwa ne, karewar lalacewa, ke wace ce da za ki dakatar da ni?" Cewar Malam Mahmud da yake tsaye ransa a matukar bace. Musaddik na tsugunne a gabansa. Page 18 Mama Hauwa na dogare a jikin katanga, ta yi zufa ta yi kasharban saboda tsabar masifa. Afrah na shigowa ta jingina da jikin kofar dakinta, idanunta sun cika da hawaye. Don ta tsani damuwar da take gani a idanun mahaifinta, kamar yadda ta tsani muzantar da ta ga Musaddik ya yi a tsugunne. Mama Hauwa ta ta ja tsaki tace “Duk abinda za ka fada, sai dai Ka fada amma ba zan taba nade hannu na zauna nasa maku ido kuna kokarin nakasa rayuwar 'yata ba, don haka Musaddik ka tattara ka tafi. Duk abinda Kawunka ya fada, ka watsar da shi, don ba mai yiwuwa bane, zan kuma yi mummunan saba maka matukar ka matsa sai ka auri "yata, babu ruwan biri da gada, don haka ina mai gargadin ka da ka dauki maganar da na ke gaya maka, don ita ce hanya me bullewa a gareka. Ka koma can gun tsohuwar matarka da ta talautaka ta kuma gudu ta bar ka, bayan ka zama abinda ka zama. Wacce ta sa ka zabeta, ka bar Sakina, iya rashin kunya yau ina ganinta, to ba dai Na'ima ba, ka kara gaba”. Idanun Musaddik jawur! Ya dago ya dubi Malam Mahmud ya ce "Kawu na gode kwarai da niyyar da kayi na kuma kara tabbatar da cewa ba ni da wanda ya fi ku kai da Inna Halima, domin wannan abinda kake son yi babu me yi min shi sai wanda ya ke matukar kaunata, don duk macen da zata iya aurena yanzu da kuma mahaifin da zai iya ba ni yarsa na aura to sai nasu karfin imani” Ya maida bakincikin da yake yunkuro masa ya cigaba da cewa “ Duk abinda mama Hauwa ta fada gaskiya ne ban cancanci Na’ma ta aure ni ba , haka kuma ba ni da wata cancantar daya kamata ace na sami mata me cikar kamala, Page 19 bayan ni ba ni da wannan cikar kamalar, gaskiya ne ko wace uwa tana bufatar farin-cikin 'yarta, don haka Mama Hauwa ba ta da laifi don ta hangi rashin farin-ciki ga "yarta bayan ta aureni". Ya Kara kallonsa, bayan ya ajiye numfashi. sannan ya ci-gaba da cewa, "Saboda haka abar wannan maganar, ni aure ma baya gaba na, kuma bazan boye maka ba bani da wani sha'awar yin aure a yanzu, domin babu yarinyar da na ke bukatar na cutar da rayuwarta Zamana ba wani a karkashina ya fi min kwanciyar hankali, don haka Kawu abar maganar nan kawai don Allah “ Kalamansa sun yi matukar ba Afrah tausayi, nan da na hawayen da take kokarin mayarwa suka suka balle a kumatun ta. Mama Hauwa ta dubi Mallam Mahmud daya sandare a tsaye, komai ya tsaya masa cak! Don bakin-ciki da damuwa. Mama Hauwa Ta watso ma musaddik harara sannan ta dawo da kallonta ga Mallam Mahmud tace “To ka ji yaro, ashe akwai sauran tunani a kansa, abin mamaki ma sai na ga yana neman Yafi Kawun nasa zurfin tunani, domin duk abinda ya fada gaskiya ne. Don haka ya rage naka, kai ma ka'aje makaman yakin naka, kai da kanwar taka da take zuga ka”. Tana gama fadan hakan, daga nan ta juya a fusace ta shige dakinta dai- dai an fara kiran sallar magariba. Page 20 Mallam Mahmud ya a saki ajiyar zuciya sannan shi ma ya durkusa a gaban Musaddik yana kallonsa, ya dagoshi gaba daya suka tashi tsaye, yana kallonsa ido cikin ido. Musaddik ya ce "Kada ka sa ma kanka damuwa Kawu, ka bar maganan nan, komai lalacewata, ina da tabbacin ba zan rasa wacce za ta iya sona domin Allah ba” Malam Mahmud ya girgiza kai ya ce. Cikin matukar fusata, “Ina nan fa akan bakata, na riga na yi alkawarin sai na aura maka ya ta ,a cikin wannan halin da ka ke ciki kana bukatar kulawa ba daga bare ba, daga Yar’uwa, don haka kada ka yi tunanin zan tashi akan maganata, yanzu ka wuce ka yi alwala, mu tafi masallaci mu yi sallar magariba, sannan ka tafi gida, zan nemeka da kaina idan na gama daidaita komai” Da sauri Afrah ta goge hawayenta ta wuce da sauri ta dauko buta guda biyu ta cikosu da ruwa tazo ta aje, daya a gaban mahaifinta, daya a gaban yayanta. Malam Mahmud ya dago ya zuba mata ido a hankali ya ce "Sannu Afrah. Shi ma Musaddik din kallonta kawai yake ba tare da ya ce mata komai ba, ya ja butar ya fara alawala.duk da yasan akwai bashin salloli a kansa ba, amma baya son kawunsa ya fahimci hakan.’ Ita ma Afrah ta wuce a hankali zuwa dakinta, kasancewar tana fashin sallah, hankalinta a tashe yake tana matukar jin tsoron rayuwar, duniya musamman idan ta tuna yadda Musaddik yake ada da yadda ya koma a yanzu. Ku dakace ni Yar gidan imam Rashin yin comments tabbas zai iya sawa na bar yin wannan posting din. MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️ https://youtu.be/UxoBM6ImosM?si=SA_azT97toNTQa7P Page 21 da yadda kuma mata ke kokuwar kawo kansu gare shi, amma yau saboda canjin yanayi , mace daya da za ta so shi ta zauna da shi, ya rasa. Shi kansa Musaddik bai taba Bata lokaci ya tsaya ya yi tunanin rayuwarsa da makomarta ba. irin daran wannan rana, ya dade yana nemar ma kansa amsar dalilin canjawar rayuwarsa, amma har yanzu ya rasa amsa, da ba haka yake ba. Babu kuma dalilin da zai sa ya koma haka a yanzu, shin wace irin rubutacciyar kaddara ce Allah ya rubuta masa? Sai dai duk da haka yana addu’ar Allah ya ba shi ikon cinye wannan jarabawa. Washegari tun hantsi Mama Hauwa ta kwashi jiki zuwa gidan Inna Halima da kashedin ta fita harkar ta da ita da 'yarta, anan ma Inna Halima da Mama Hauwa sun kwashi 'yan kallo, don babu wanda ya raga ma wani a tsakaninsu, kaca-kaca su ka yi cikin diban albarka. Mama Hauwa ta bar gidan Inna Halima, tana komawa gida ta shirya Na'ima ta ba ta kudin mota ta ce ta tafi can garinsu, wato Suleja, gidan kakanninta ta zauna can, sai ta gama da lamarin Malam Mahmud. Sai ta tabbatar ya sauko daga maganganunsa, sannan ta dawo, ai ko nan da nan Na'ima ta shirya ta tafi abin ta, ba tare da Malam Mahmu* ya sani ba. Page 22 Har sai bayan ya dawo daga sallar Issha'i Inna Halima ta zo ta gaya masa duk wulakanci da diban albarkar da Mama Hauwa ta je ta yi mata har gida. Kwarai da gaske ran Malam Mahmud idan ya yi dubu ya baci, a fusace ya kira Mama Hauwa ta fito, tana yamutse-yamutse ta dogare a tsaye ta ce "Ga-ni menene?" Malam Mahmud ya dubeta rai bace ya ce "Wai ke Hauwa me ki ke nufi da ni ne, meye matsalarki, shin Na'ima "yar ki ce ke kadai, don me za ki tayar mana da hankali, kin hanamu sakat! dan kawai nayi nufin kulla alheri” Ta yi karaf, ta katse shi ta ce "Ka yi niyyar Kulla sharri dai, kuma ba dai da 'Yata ba, banda mugunta, ai ba Na'ima bace kadai 'yarka da ba ta yi aure ba Don me ba za ka canja ba, sai ita, don ba ka Kaunarta." Ya jinjina kai ya ce "Na ji, to meye ya kai ki gidan Halima ki ka yi mata wulakanci? Wannan abin ai tsakanina da ke ne, don me za ki sa yar-uwata a ciki?" Ta ce cike da fusata "Saboda na san duk kulle -kullenta ne wannan saboda ba ta kaunata, shi ya sa take bakin- ciki da kwanciyar hankali na, don haka ka gargadeta ta fita harkata da 'ya'yana". Inna Halima ta dubeta tace. "'Kin ci sa'a a gaban yaya muke, duk abinda za ki fada, ba zan iya maida miki a gabansa ba, Page 23 don yana da daraja da kima a guna." Ta tabe bak; "Wannan ke ki ka sani kuma” Malam Mahmud ya daka mata tsawa ya ce "Ke Hauwa ba ruwanki da Halima kuma idan ki Ka Kara taka gidanta, ki ka yi mata abinda bai kamata ba, sai kin yi mamaki na, don ki sani, ba tsoranki nake ji ba, kin kusa kai ni bango, ki fita a cikin lamarina, kafin na yi miki abinda zakiyi mamaki” shiru ta yi ta na cigaba da kumbure kumbure, Ya bude baki ya kwala ma Na'ima kira. Mama Hauwa ta dube shi ta ce "Wace Na'imar? na riga na turata inda ya kamata, ba kuma za ta dawo ba har sai ka janye wannan mummunar maganar, daka tsiro da ita ana zaune lafiya” 'Malam Mahmud ya fiddo da idanu waje ya ce "Ina ki ka turata ba tare da sanina ko izinina ba?" Ta ce ' ta kara tamke fuska tace “Ba dole bane ka sani, izininka kuwa dama ban nema ba, don na san ba zan samu ba, shi ya sa nayi gaban kaina”, Mallam Mahmud cike da fushi yace “To shikenan ina son ki sani na ba ki daga wannan daran zuwa gobe, ki tabbatar Na'ima ta dawo gidan nan, ko kuma ki tattara ki bi ta , domin bana bukatar ganinki a gidana matukar zansa doka ki ki bi banga amfanin kasancewarki mata ta ba”. Inna Halima tace "A’a yaya kada ayi haka, ka fita harkar Hauwa, don na lura tana jin dadin ci ma mutane mutunci, ka bar ta, duniya ma ai makaranta ce, idan har wani abu zai samu dan wani na assha baki tausaya ba a matsayinki na uwa ba to ba na zaton akwai imani a tare da ke, musaddik kuma da ki ke kyamata ki sani shi ma ba shi ya tsarawa rayuwarsa haka ba, kin kuma fi kiwa sanin cewa da ba haka yake ba, idan baki tausaya masa ba bai kamata ki dinga nuna masa irin wannan tsanar ba” Mama Hauwa ta ce "Kada ma ya bar ni, ba kuma za ta dawo ba, ni ma ba inda zan je, zama daram! Idan kuma neman kwanciyar hankali ku Ke yi to ku janye batun auren nan, shine kawai maslaha, kuma naganar kyamata na kyamace shin meye abin so a gun sa” Page 24 Daga nan ta juya fuuu! Ta shige dakinta gami da rufe kofa. Inna Halima ta juyo tana kallonsa ta ce "Yaya ina ganin maganar Na'ima a bar ta, saboda abinda muke kwadayi, ba za mu samu ba, hakuri da juriyar zama da Musaddik ba za ta iya ba, ko mun tursasa an yi, to ba za mu samu hadin kanta ba balle ta ba mu gudunmuwar dawo da rayuwarsa kan hanya, tunda ba ta so, mahaifiyarta ma ba ta so. Domin tashin hankalin Hauwa ma kadai, ya isa ya hana su zaman .lafiya da kwanciyar hankali, koda ita ma Na'imar tana so. Balle bisa dukkan alamu ya nuna tana tare da mahaifiyarta, tunda har suka iya shirya ta gudu. Allah ya ga tunanin mu, ya kuma ga niyyar mu. Allah ya ba mu ladan niyya, shi kuma Musaddik Allah ya kawo sanadiyyar shiryuwarsa, ko da ba ta dalilin auren ba, domin ko anyi auren sai dai ya kara jefa musaddik cikin wani kangin”. Malam Mahmud ya saki ajiyar zuciya ya ce "Kai babu wata jarabta ga da namiji irin rashin sa'ar mata ta-gari, shi ya sa ba zan taba mantawa da marigayiya ba, wacce ta so-ni, ta yi min biyayya har me rabawa ta rabamu, na yi kwadayin ace ita ce ta cika min gida na da 'ya*ya kafin rasuwarta, amma duk da haka na san tà bar min daya tamkar da dubu wato Afrah" Inna Halima ta gyada kai ta ce "Haka ne, Allah dai ya jikanta, yasa ta huta, tabbas kayi rashin mata” ta karasa magana fuskarta cike da jimami, tana tuna irin zaman arzikin da sukayi da mahaifiyar Afrah. .Mallam Mahmud Ya ture hularsa keya ya ce Page 25 "Amin, kuma ina nan akan bakana na hada Musaddik da 'yata aure” Inna Halima ta dube shi sosai tace “Amma ta yaya, ina za mu iya da tashin hankalin Hauwa, bayan faruwar komai ba ni gaba daya al’amarin ya fita kaina, domin na hango fitina acikin auren nan har garama kada ayi “Mallam Mahmud ya jinjina kai yace “ Na fahimci duk abinda kike nufi na kuma gamsu amma babu komai, akwai wata mafitar da na fara hangowa, bayan maganganun da Hauwa tayi yanzu na hango wata mafitar, ki tashi ki tafi gida dare ya yi sosai, zuwa jibi idan na gama tunani zan neme ki” Ta jinjina kai, ta ce "To Allah ya kai mu, ya kuma kara maka hakuri da juriya akan zama da Hauwa". Ya ce "Amin Halima” Daga nan ta tashi ta yi masa sallama ta leka dakin Afrah wacce duk abinda ke faruwa tana zaune akan katifarta tana jinsu, nan ma sallama ta yi da Afrah. Sannan ta wuce zuwa gida, zuciyarta cike da tsanar Mama Hauwa da jin haushinta. Page 26 Yau alhamis ba makarantar Islamiyya, tun safe Afrah ta kwashe wankin mahaifinta ta wankesu tsaf? Ta shanya; sannan ta shiga dakinsa ta gyara Kamar yadda ta saba duk ranar alhamis, haka zalika duk wani aikin gida, babu wanda Mama Hauwa ba ta, ba ta ba, duk kuma ta yi ta gama har zuwa yanzu da ta hada wutar guga ta goge kayan mahaifinta Ta kammala kenan, ta kwasa za ta kai masa daki, ya dawo, ya shigo yana kallonta dauke da kaya ya ce "Afrah, yanzu bayan wanki har guga Ki ka sami damar yi min, bayan aikin da na fita na bar ki da shi a gaba?" Ta yi murmushi ta ce "Eh Baba, ai har ma na gama, sannu da zuwa" cike da kauna yace “ Yauwa Allah miki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah ya baki kema masu jin kan ki, masu taimakon ki yadda ki ke taimako na”. Cike da jindadin addu’ar tace “Amun Baba” Daga can nesa inda Mama Hauwa ke zaune ta saki tsaki ta ce “ Ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta”, wani irin mugun kallo ya sakar mata sannan ya wuce dakinsa ba tare da ya tanka mata ba, don maganar gaskiya haushi take ba shi ba ta ko son kallonta. "Ayi dai mu gani." Ya yi mata wani irin Ita ma Afrah ta bi bayansa dauke da kayan a hannunta. Tana shiga dakin ta tarar da Malam Mahmud zaune akan kujerar da ita kadai ce a dakin, ya yi tagumi hannu biyu fuskarsa dauke da matsananciyar damuwa, bayan ta aje kayan ne,inda ta saba ajewa ta shiryasu, sannan ta Page 27 juyo ta dora masa ido, zuciyarta ta dagule ta shiga damuwa, domin gain mahaifinta cikin damuwa. Tana matukar so ta zauna su tattauna damuwarsa, amma ba ta da yadda za ta yi, domin bai nemi hakan daga gareta ba, ta juya a hankali zata fita, har ta kai kofar dakin, zuciyarta cike da addu’ar Allah yasa ya kirata domin su tattauna damuwarsa, ta ji muryar mahaifinta ta dakatar da ita daga fita, ta hanyar kiran sunanta, ta amsa da sauri, lokaci daya ta dawo ta durkusa a gabansa ta ce "Ga-ni Baba” Malam Mahmud ya dawo da kallonsa gareta, ya fara magana. "Afrah ina cikin wani hali na tsaka mai wuya, na daukar ma kaina alkawarin da na ke neman na gaza a kansa, na shiga wani hali da banda wani zabi da ya wuce na roke ki a matsayinki na wacce na ke tunanin tana da maganin matsalata." Ya dan numfasa, sannan ya ci-gaba da cewa "Musaddik Dan-uwanki ne, idan rayuwarsa ta gyaru, na yi imanin za ki zama daya daga cikin masu jin dadì, ko kadan ba ni da nufin kara ma rayuwarki damuwa, saboda maraicin ki da kuma irin hannun rikon da ki ka taso. Hakan ya sa na ke miki kwadayin samun miji na-gari wanda zai taimakeki, wanda zai rikeki da mutunci, wanda kuma za ki sami dukkan gata daga gare shi Shi ya sa ban yi tunanin hadaki aure da Musaddik ba, don na san duk abinda na lissafa, Page 28 ba za ki taba samu daga Musaddik ba, shi ya sa na yi tunanin hada shi da "Yar-uwarki Na'ima.” Ya numfasa gami da gyara zamansa, ya kurama fuskar Afrah ido wacce take tsugunne, banda faduwar gaba ba abinda take yi, ya ci-gaba da cewa “Ba sai na gaya miki matsalar da na ke fuskanta daga Hauwa ba Tunda na furta maganar hada auran nasu, domin na san kin ji, kin kuma ga irin cin mutuncin da Hauwa ke min, karshe ma ta dauke Na'ima ta boyeta, ban san inda ta kai ta ba. Don haka Afrah ina rokonki da hannaye na biyu, ki taimakeni ki share min hawaye, ki sadaukar da farin-cikinki saboda farin-ciki na, ki yi min biyayya kamar yadda ki ka saba, ki amince ki auri Musaddik don Allah... Da sauri Afrah ta dakatar da shi "Don Allah Baba ka daina rokona, wace ce ni da har sai ka rokeni, don na yi maka biyayya, duk irin so da kauna da ka nuna min ace sai ka rokeni don kawai za ka aura min Dan-uwana. Har kullum ina fatan Allah ya kawo ranar da za ka nemi wani abu daga gareni, domin ba ni da abinda zan saka maka ko na biyaka daga irin rikon da ka yi min “ Ta yi kokarin maida hawayen daya cika mata ido, sannan ta ci-gaba da cewa "Saboda haka zan sadaukar da farin-ciki na, kamar yadda ka Page 29 bukata, zan auri Yaya Musaddik, zan kula da shi tare da kokarin sanya shi a hanya madaidaiciya Allah kuma ya shirya shi." Son Afrah tare da tausayinta ya kara kama Malam Mahmud, a yayin da farin-ciki ya cika zuciyarsa, amma daya kalli cikin idanun Afrah, sai ya ji wani bakin-ciki ya kama shi, domin duk yadda Afrah ta so ta Boye damuwarta, to ba za 6oye ma Malam Mahmud ba, hakika bai hango son Musaddik ko son auransa a kwayar idanunta ba. Abinda ya hango daya ne, shi ne tsantsar biyayya da kaunar faranta ransa, ya nisa gami jinjina kansa sannan ya ce. "Ki yi hakuri Afrah, ba haka na so rayuwar ta tafi ba. Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki 'ya"ya masu jinkanki, Allah kuma ya albarkaci abinda zai shigo rayuwarki. Allah ya juya wannan al'amari ya kasance alheri a gareki, da mu ba ki daya, domin Allah ya ga kyakkyawar niyyar mu akan wannan auran, na gode, na gode" Afrah ta dan yi murmushi ta ce “ Baba kana sa ni jin nauyi, idan ka na min godiya, don Allah Ka daina min godiya". Ya gyada kai cike da kauna yace “Allah ya yi miki albarka Afrah tashi ki tafi.”. ' A hankali ta mike ta fita, gabanta na cigaba da matsanancin faduwa. Tana shiga dakinta ta fada kan katifarta,kuka take riris Komai ya kwance mata, meke shirin faruwa da ita? Ko a mafarki ba ta taba kwatanta Page 30 Musaddik a matsayin mijin aurenta ba, shin me kaddara ta tanadar mata? Zama da mutum irin Musaddik wanda bai ma san inda rayuwarsa tasa gaba ba. Wanda bai san yadda zai tarbiyantar da ita ba sai dai ita ta tarbiyyar da shi, ko kadan ba irin Musaddik bane mijin da take kwadayin zama a karkashinsa. Ya Sayyadi Habib shine wanda ta horar ma da zuciyarta kaunarsa, take kuma kwadaita ma kanta auransa. Domin tana da tabbacin shine wanda zai yi mata jagora har gidan aljanna, sai dai kash! Ba ta so yadda labarin ya tsaya ba, ba ta so karshen labarin ya zama haka ba. Domin kuwa ko ta ki ko ta so soyayyarta da Ya Sayyadi ta zama tarihi daga lokacin da mahaifinta ya umarceta da auran Musaddik, tabbas! Za ta yi ma mahaifinta biyayya, koda hakan zai zama sanadiyyar fadawarta mummunar rayuwa, domin duk duniya ba ta da kamar mahaifinta. Ba ta tunanin akwai abinda zai bukata ta yi masa, matukar tana da halin yi masa ta kasa yi, don haka za ta iya sadaukar da komai nata, domin samun farin-cikin mahaifinta, tunda Allah ya taimaketa ta samu ta yi rayuwa da shi, dole ta lallaba ta samu albarkansa, tunda Allah bai kaddari za ta yi rayuwa da mahaifiyarta ba. Ta sa hannu ta goge hawayen da ke malala a saman kumatunta, ko kadan babu soyayyar Yaya Musaddik a cikin zuciyarta. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam ✍️ Kuyi comments da ra’ayiyun ku rashin yin comments zai iya sa wa na daina posting MUSABBI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 31 sai dai acan karkashin zuciyarta akwai tsantsar tausayinsa, gefe daya kuma tana tausayin kanta da Ya Sayyadinta na yadda za su rabu da junansu, domin Allah bai rubuta shi ne mijinta ba a allon kaddarar su, ta kara goge hawayenta. Sannan ta yunkura ta tashi ta tura kofar dakinta, domin ta ji dadin yin kukanta, sannan ta dawo ta kure karshen katifa ta ci-gaba da rasgar kuka,; domin tana ganin hakan ne kawai zai sassauta mata radadin da take ji a cikin zuciyarta. Haka Afrah ta kasance cikin rashin sukuni a wannan ranar, har zuwa idar da sallar Issha'i, tun bayan idar da sallar, tana zaune akan sallaya da casbaha a hannu tana lazimi, lokaci daya ta kan yi kokarin goge hawayen da ke fita mata da daya hannun. Tana jin dawowar mahaifinta daga masallaci, bai dade da shigowa ba, kuma ta ji sallamar Inna Halima, haka nan Afrah ta tsinci kanta cikin matsananciyar faduwar gaba. An dau tsawon lokaci kafin ta ji muryar Malam Mahmud, ya kwala mata kira. A daburce ta amsa da sauri, ta tashi ta aje carbin, sannan ta fice kai tsaye dakin mahaifinta ta nufa. •Mama Hauwa da ke zaune a kofar dakinta ta rakata da kallo har ta shige dakin, sannan ta saki tsaki ta tashi ta dauki kujerarta 'yar tsugunne ta Page 32 shige daki tana fadin "Halima uwar kinibibi, sai dai ya Kare a kanku ba dai 'yata ba”, a fili take fadan maganar cike da zafin rai. Cikin sallama Afrah ta shiga dakin, ta yi Kokarin boye dukkan damuwarta, ta nufi inda Inna Halima ke zaune, ta zauna kusa da ita. "Inna sannu da zuwa” Ta amsa tana yi mata wani kallo me cike da Kauna da tausayi, ta fara magana "Afrah ban Yarda da hukuncin da mahaifinki ya yanke ba a Kan aurar dake ga Musaddik. Afrah ke marainiya ce ina matukar tausayin rayuwarki, miji irin Musaddik bai kamace ki ba, gara kawai an hakura mu ci-gaba da yi masa addu'a." Afrah ta yi

Chapter 2 of 15