Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
matukar wari, tana idarwa, ko addu' a ba ta gama yi ba, ta tashi ta shiga aikin goge aman, tana kuka me dauke da sautin ban tausayi. Bayan ta gama gyara wajen ne,ta taimaka masa ta janye shi daga falon zuwa uwardaka. Ya bata wandonsa da fitsari, ya bata rigarsa da amai duk da tana cike da jin nauyinsa, haka ta taumaka masa wajen cire kayansa, ta sa masa wasu , sannan ya koma kan gado da kansa, ya kwanta, cikin rashin cikin rashin dawowa hayyacinsa . Bayan ya kwanta ne. Afrah ta fice ta koma falonta, ta zauna ta dasa wani sabon kukan, gaba daya har jikinta ya yi dumi, shin wace irin mummunar rayuwa ta shigo a daranta na farko a gidan mijinta? Ba ta fara da komai ba, sai da aikin kwasar aman dan giya da aikin gyara wajen fitsarinsa, shin haka rayuwarta za ta kasance tare da Musaddik? Idan ko har haka ne rayuwarta ta riga ta kare babu sauran wani abu na farin-ciki ko na jin dadì da ya rage à gareta. Kaiconta, kaicon wannan mummunan rayuwar, hakika ta yi sadaukarwa me girma, a yanzu ne kuma ta fahimci ba karamin aiki bane a gabanta, duk yadda take tunanin abin ya wuce nan,lalle dole ta karfafama kanta guiwa, Karfe takwas Afrah ta yi wanka, ta gyara kanta, sai dai kallo daya za ka yi mata ka san tana cikin tashin hankali da matsananciyar damuwa, domin kuwa har ta rame idanunta sun zurma ciki, fuskarta ta yi fauu! Idanunta ma'abota girma da Page 84 haske, duk sun kankance, a sakamakon kukan da ta yi, har zuwa lokacin Musaddik barci yake yi ko motsi ba ya yi, ta leka shi yafi a kirga amma kwance yake tamkar matacce. A dalilin hakan Afrah ta janyo hijabinta ta sa ta fito zuwa cikin gidan, domin ta gaida Hajiya Kilishi. A katon falonta ta tadda ita zaune da me aikinta Amimi, tana ta kaiwa da komowa wajen shirya abincin karyawa akan tebur, cikin sallama Afrah ta shiga falon Hajiya Kilishi. Ta dago ta kalleta gami da amsa sallamar can cikinta. Har kasa Afrah ta zube tana gaida ta cike da girmamawa da mutuntawa. Hajiya Kilishi ta amsa ba yabo, ba fallasa, rai a bace kamar wacce aka yi ma wani laifi, hakan ko ya ba Afrah mamaki, Domin sanda aka kawota gidan a jiya, ba haka ta karbeta ba, ta karbeta cikin kyautatawa da kauna, to mènene yanzu? Me ya yi zafi? Za ta ga irin wannan canji nan da nan, ko daman Hajiya Kilishi tana da dalilinta na yin duk abinda ta yi a baya ne? "Ya kwanan amarci?" Tambayar Hajiya Kilishi ta katse Afrah daga tunanin da take yi, ta dan kalleta kadan, ba tare da ta ba ta amsa ba. Hajiya Kilishi ta ci-gaba da cewa "Na san kin yi kwanan amarci me dadì, domin ina da tabbacin angon naki ya ba ki kyakkyawar kulawa da dawowa akan lokaci dai-dai sallar asubah, na san kuma ya zo maki da kyakkyawan sakamakon kaiwa asubah a waje, kinsan abinda yasa yakai wannan kokacin a waje , nasan kuma kin fahimci cewa mace bata gaban musaddik, abinda ke gabansa kenan wanda idanunki suka ganar miki”. PAGE 85 Cike da mamakin maganganunta. Afrah ta dubeta idanunta sun kada sun yi jajir! Hajiya Kilishi ta gyara zamanta gami da yi mata wani sakaran kallo, sannan ta ce “Afrah na yi mamakin da ki ka amince da auranki da Musaddik a matsayinki na yarinya mai natsuwa, mai kuma ilimi, na yi zaton za ki yi kokarin girmama kanki, ki samu rayuwa ta-gari, wacce za ta amfaneki ta kuma amfani yayanki, wadanda zasu so samun uba nagari, sai ga shi kin buge da watsa ma kanki rayuwa da kanki. Meye riba ko amfanin auranki da mutumin da bai san inda rayuwarsa tasa gaba ba, me zaki tsinta?” Ta kara kura mata ido ta ci-gaba da cewa. "Shi mahaifin naki daya hada auran ku, ya san cewa Musaddik bai dace da ke ba, idan kuma don abin duniya ya aura miki shi. Ya san cewa Musaddik baida ragowar komai na gadonsa, asalima inda ku ke zaune yanzu, a matsayin alfarma ce, taimaka maku na yi, alfarma nai maku, na ba shi aron wajen da ya aje ki. Idan na so sai na ce ya je ya nemi wajen zama, amma na taimaka masa, domin Allah." Anan ne Afrah ta dago da idanunta, da tuni suka fara zubar da hawaye ta ce "Mahaifina bai taba tunanin ya aura ma Yaya Musaddik ni sabida tunanin fanshewa daga wani abin duniya daga gare shi ba………….. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan Imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 86 ya aura ma sa ni ne, saboda Allah ya riga ya rubutani a cikin matan da Yaya Musaddik zai aura Ita kuma Kaddarar Ubangiji babu wanda ya isa ya kauce mata, don haka a shirye na ke da na karbi Kaddarar, zan kuma rike Yaya Musaddik da daraja fiye da tunanin me tunani, zan zamar masa majingina “ Hajiya Kilishi ta saki tsaki ta ce "A hakan har wace daraja Musaddik yake da ita? Ke kam! Ki na da babban aiki a gabanki, na zama da dan iska, dan giya a matsayin miji" Afrah ta yi dan murmushi ta ce "Ba komai. Allah ya ba ni ikon ci-gaba da zama da shi a hakan domin ta nan zan sami aljannata”. Tana gama fadin hakan, ta mike, ta ce "Dama na zo na gaisheki ne, bari na koma, kada ya tashi barci ba na nan” Tana gama fadin haka ba ta saurari komai ba, ta fice, a yayin da Hajiya Kilishi ta bi ta da wani mugun kallo, zuciyarta a zafafe, lallai yarinyar nan zuciyarta a dake take, yanzu duk abinda musaddik ya yi mata a jiya ba ta gani ba? Mai-gadi ya tabbatar mata da cewa sai asubah ya dawo gida, kuma ya dawo a buge da giya, ace ango ya yi ma amaryarsa haka a daren farkonsu ai ya isa dalilin da za ta nemi kashe auran ma, amma kalleta ko a jikinta. Hmm! Rashin sani, ya fi dare duhu, domin Hajiya Kilishi ba ta san dalilin auran Page 87 Afrah da Musaddik ba kenan, don ya sami me taimaka masa, tare da tallafa masa da kuma Kokarin maido da shi hanya madaidaiciya, don haka duk halayensa ba baki bane agun Afrah, ta sani, asalima halayen nasa su ne suka sa ta aure shi . Afrah na shiga daki, ta tadda Musaddik zaune a bakin gado, ya yi tagumi hannu biyu, tana ganinsa a haka, ta yi saurin korar damuwar da ke fuskarta cike da fara' a, ta karasa inda yake, ta ce “ ka tashi kenan”, ya dago fuska cike da damuwa mara misaltuwa, ya kalleta a hankali cikin matsananciyar kunya, ya dauke kallonsa daga gareta, sannan ya ce. "Afrah don Allah ki yi hakuri, ki yi min afuwa “ - Ta dan yi murmushi ta ce "'Me ka yi da ka ke ncman afuwata?" Ya numfasa ya ce "Kin fi kowa sanin abinda na yi, domin ko ni da na yi, sai dai na kintaci abinda na yi, na tuna, dan abinda zan iya tunawa amma sanin komai, sai ke da na yi a gabanki, don haka ki yi hakuri, koma me na yi a daran jiya, ina neman yafiyarki, don Allah"ta jinjina kai tace "Ya wuce, babu komai, amma kasan wani abu?” Ya so ya kalli cikin kwayar idonta amma sai yaji bazai iya hada ido da ita ba, ya girgiza kai yace “A’a” Afrah ta dan gyara tsayuwarta tace "Ina yi maka kallon me ilimi wanda ya san abinda Allah ya fada akan giya da kuma me shanta, ban taba tunanin zan Page 88 tadda kai a cikin shaukin shan giya ba, bayan ka san giya ita ce uwar kaba’irai Komai za ka iya aikatawa, idan ka sha giya, to me zai sa ka sha, me zai sa ba za ta zama abar tsana a gunka ba, sai dai abar kauna, sannan ka rasa lokacin da za ka sha, sai a daren auranka yaya Musaddik? Me ya sa za ka yi min haka?, ko ya ya ne ba zaka iya hakuri ba ko da a wannan daren ne, da nake bakuwa a gareka”. Musaddik ya runtse idanunsa, ya bude, sannan ya ce "Ba za ki taba ganewa ba Afrah, ba za ki gane ba, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa na ke tsoron aurenki, ba zaki gane komai ba a yanzu, ni nasan yadda nake ji” Yana gama fadin haka, ya mike yana kokarin shiga bandaki. Ya na kauda kansa a dalilin baya son taga hawayen da yake kokarin boye mata. Afrah ta yi kokarin maida hawayenta, jikinta ya yi sanyi tayi saurin cewa “yakamata ka fara yin wanka ne kafin kayi sallah, bari na kaima ruwan wankan” A hankali musaddik ya dawo da baya, ya koma ya zauna a bakin gadon, ya sadda kansa kasa,a yayin da Afrah ta yi gaggawar fita, ta hada rishonta, ta dura Kananzir wanda harda shi a cikin kayan da aka kawota da su.ta kunna ta dora masa ruwan wanka, cikin kankanin lokaci ruwan ya yi zafi, ta juye ta kai masa. Ya yi wankan, ya yi kuma alwala , bayan ya fito ne ya kintsa ya yi sallar asubah. Dai-dai Karfe tara da rabi zuwa lokacin ta gama abin karyawa. Domin Malam Mahmud ya yi kokarin hado Afrah da garar abinci, hatta garin tuwo, sai da ya hadota da shi. Musaddik yana gama karyawa bai saurari komai ba ya fice duk da abincin ma kadan ya ci. Ko kadan babu dokin auran a ransa, balle har ya yi tunanin ya zauna a gida na dan lokaci tare da matarsa. Haka ya tafi ya bar ta cikin matsananciyar Page 89 damuwa. Domin duk yadda ta dauki abinda sauki Ta ga ba haka bane, hakika akwai katon aiki a gabanta, ta ko wane bangare. WAIWAYE, ADON TAFIYA....... Alhaji Mansur Musaddik Mai Fata shahararre ne, kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya mallaki manya- manyan kamfanoni na sarrafa fatu, sannan bayan hakan yana safarar fatun zuwa kasashe makwaftan Nigeria. Hakan ya sa kasuwancinsa ya kara fadada, ya kuma sami karbuwa sosai, mutum ne me saukin kai, me addini tare da son kyauta ma 'yan’uwansa, duk da ya taso cikin matsananciyar tsana ta Yan uba a dalilin maraicin uwa da uba da ya yi gaba daya, amma duk da haka bai hana shi taimaka musu ba, bayan da Allah ya zabe shi a cikinsu ya azurta shi. Haj kilishi itace matarsa ta farko,auren saurayi da budurwa. Haj kilishi macece me ji da kanta, fadin rai da daukar kanta wani abu, tana da karfin izza, gata da matsanancin kishi, wanda hakan yasa take ganin Alhaji Mansur ba zai iya yi mata kishiya ba, musamman idan ta yi la'akari da irin son da yake mata, da kuma bai taba nuna mata yana da sha’awar wata ya mace ba bayan ita, ko sha’awar ya kara aure ba, shi yasa ta mike kafa take shimfida iko da mulki.ta haifa masa 'ya' ya har uku duk mata Hassana da Hussaina, sai Amina. Bakincikinta daya a rayuwarta, shine yadda bata da da namiji, ga haihuwar ta tsaya mata, ta tashi hankalinta wajen ganin likita da son ta cigaba da haihuwa amma likita ya tabbatar mata lafiyarta kalau haihuwar ce dai kawai Allah bai kawo ba. Wannan al’amari ya kara tada hankalin haj kilishi domin tana da Page 90 gamshahshen sanin cewa babu abinda mijinta yake so yake kuma nema ido rufe irin magaji da namiji, saboda yana kwadayin ya samu mataimaki a lokacin da karfinsa ya kare, jikin Haj kilishi ya fara sanyi, damuwa ta fara mata yawa, tunaninta na mijinta va zai iya mata kishiya ba ya fara canjawa.don haka kullum addu'oi 'nta. Allah ya ba ta haihuwar da namiji, amma ba ciki ba dalilinsa, Hakan ya sa a lokacin da Alhaji Mansur ya furta mata maganar Karin auransa da Harirah hankalinta ya yi masifar tashi, hauka ne kawai ba tayi ba, haka zalika ta yi Kokarin lalata auran ta hanyoyi da dama. Domin ta yi ta asarar kudinta a wajen Malamai da Bokaye, don dakatar da auran. amma da yake Kaddararran al'amari ne. Allah ya riga ya Kaddara Harirah sai ta kasance uwar dan Alh Mansur, sai da Allah ya tabbatar da auransu. Sai dai Harirah ta zauna cikin kunsar bakin- cikin Hajiya Kilishi, domin kuwa ta kankane komai a gidan. Harirah ba ta da wani karfi a matsayinta na matar gida, komai sai Hajiya Kilishi ta amince, ta kuma sa baki sannan yake yiwuwa. Koda ta bangaren Mai-gidan ne, domin Hajiya Kilishi ta riga ta gama mallake shi ta hanyoyin sihirinta. Hakan ya sa Harirah ta ci-gaba da zama a wulakance a kaskance a gidan mijinta. Har zuwa lokacin da Allah ya yanke mata wahala, ya dubi hakurin da ta yi a dalilin cikin da ya bata, tunda ta sami cikin, kadarin Hajiya Kilishi ya Karye, domin yadda Alhaji Mansur ya dauki son duniya ya dora akan cikin, tamkar ba’a taba yin ciki a gidansa ba sai akan Harirah. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI BISMILLAHIR RAHMA NIRRAHIM Page 91 ga kuma kyakkyawar kulawa da take samu daga gare shi, wannan lamari ya fi komai tayar ma da Hajiya Kilishi hankali. Musammam da ta fuskanci da gaske Harirah ciki, gareta don haka ta ci-gaba da asarar Kudinta a wajen Malamai, domin a lalata cikin Harirah Amma ina. Alkawarin Allah baya tashi. Komai tayi a banza, cikin Harirah ya ci-gaba da girma da kuma samun kulawa. Haj kilishi ta cigaba da zama cikin dar dar da fargabar kada Harirah ta haifi da namiji. Har zuwa lokacin da cikin ya isa haihuwa. Da yake Allah ya riga ya rubuta Harirah ba za ta rayu da danta ba, ya sa tana haihuwar dan, Allah yana daukar ranta, ga koshi, ga kwanan yunwa kenan! Alhaji Mansur na murnar samun abinda ya dade yana addu'ar samu, ga tashin hankalin rashin matarsa, uwar dansa daya tilo daya fara samu. Wacce yake sa ran za ta kula masa da dansa har zuwa girmansa. Ya shiga tsananin tashin hankali, irin rashin kyautatawar da ya ke yi ma Harirah a da ya yi ta dawo masa yana ta da masa hankali, ya so Harirah ta rayu ko don ya jiyar da ita dadin da bai jiyar da ita ba a baya. Ta Bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ba Harirah ta so ta rasu ba, dan da ta haifa ta so ya rasu, domin tana ganin duk duniya ba ta da wani bala'i sama da shi.don haka don Harirah ta rasu, ai ta barta da masifa tamkar an kashe maciji ne , ba a sare kan ba Rasuwarta ba wata fa'ida a gareta, gaba daya tsanar dan da Harirah ta haifa ya gama ratsa Jinin jikin Hajiya Kilishi, ko kadan ba ta kaunarsa. Hankalin yan’uwan Harirah yafi na kowa tashi adalilin rashin yar’uwa da su kayi da kuma tunanin yadda dan Harirah zai rayu ba tare da mahaifiyarsa ba. Page 92 Tunaninsu kuma ya kara karkata akan waye zai dauki Musaddik ya rike shi, ya raine shi kamar yadda uwa zata raini danta.Inna Halima wacce ita ke bin Harirah a haihuwa, da yake kuma shekarunsu ba wani tazara bane sosai, ya sa tare aka yi masu aure. 'Inna Halima kuma ta rigata haihuwa da makwanni hudu, danta ita ma namiji ne, mai suna Abdullahi, don haka ta roki Alhaji Mansur da ya bata Musaddik ta hada da Abdullahi ta shayar da su. Alhaji Mansur ya yi farin-ciki matuka, ya kuma sami dimbim natsuwa ya kuma kalli Inna Halima a matsayin maganin matsalarsa, kuma mai taimaka masa akan gudan jininsa Musaddik dan da yake jin kamar ba shi da kowa duk duniya Sai shi. Dan da yake jinsa har cikin jinin jikinsa, wannan shine dalilin da ya sa Inna Halima ta dauki Musaddik ta hada shi da danta da ta haifa. Wanda ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, ta so Musaddik a bar shi ya tagayyara ne, da rashin nonon uwa, har' shi ma ya bi uwar ta sa, amma sai ga shi ya sami wata uwar wacce take da tabbacin zata bashi kulawa kamar yadda mahaifiyarsa zata ba shi ko ma fiye da haka, domin yan’uwan Harirah suna daya daga cikin yan’uwan da bata taba ganin zurfin zumunci irin na su ba, ga shi dai basu da yawa sai shegiyar zuciya da hadin kai kamar kashin awaki. Page 93 Bayan "yan watanni, lamarin ya fara kwanta ma Hajiya Kilishi, musamman da yake ba ganin Musaddik take ba, ta kuma mallaki hankalin Mijinta waje daya, domin baya sha'awar ya kara wani auran. Amma abu daya ya ci-gaba da nukurkusar zuciyar Hajiya Kilishi tare da hanata samun, sukuni shine ganin irin yadda Alhaji Mansur yake matukar kulawa da Musaddik. Domin hatta gadon da zai kwanta, sai da ya saya masa, kaya kuwa na sawa na alafarma yake saya masa, duk wani abu da ake ma da dan gata, to fa shi yake ma Musaddik, kuma kullum kwanan duniya, in dai yana kasar , to duk aikin da ke gabansa, sai ya ture ya je ya ga Musaddik sau uku safe rana da daddare, hakan ya sanya shakuwa tsakaninsa da dansa. Su kansu su Inna Halima rikon Musaddik ya amfanesu sosai, tunda mijinta ba shi da wani, Karfi don haka Alhaji Mansur ya dauke shi ya ba shi aiki a daya daga cikin kamfanoninsa, wanda ake yin takalma, sannan kuma shine ya rushe gidansa, ya Kara gina masa sabo dai-dai da rayuwar dansa. Wannan lamari ya tayar ma da Hajiya Kilishi hankali, dalilin da ya sa kuma kenan ta tsani Inna Halima, domin ta sha nikar gari ta je har gidan ta ci mata mutunci ta kuma kirata da makwadaiciya , tun tana shanyewa har ta gaji, ta gaya ma Alhaji Mansur. Page 94 Wanda hakan ya yi sanadiyyar da suka sami sabani da Hajiya Kilishi. Ya yi mata kaca-kaca, ya kuma gargadeta da kada ta kara taka gidan Inna Halima da sunan cin mutunci, idan kuma ta Kara to ta shaida a bakin auranta. Hakan ya sa dole Hajiya Kilishi ta hakura da zuwa gidan Inna Halima, ba don ta so ba, ko don ta daina jin zafinta ba, sai don tana son igiyar auranta da take tunkaho da ita, sai dai ta cigaba da bin bokaye da malamai domin a raba soyayyar da ke tsakanin Musaddik da mahaifinsa, ta kashe kudi ba iyaka, amma bata dace ba, ko ya yi kamar ya kama sai kuma ya karye. Ta rasa yadda zata bulloma al’amarin. Shekarun Musaddik biyar , ya fara makaranta wacce ta masa sunanta, a lokacin ne kuma Haj Kilishi ta fara sa kahon zuka tare da tusa ma Alh Mansur son ya amshi Musaddik ya dawo hannunsu Amma Alhaji Mansur ya ki daukar hudubarta, domin ya fi kowa sanin halinta, yana da tabbacin Musaddik ba zai taba jin dadin zama da ita ba. A haka a daddafe har Musaddik ya kammala firamare, cikin kyakkyawan yabo da sakamako, ga kyakyawar tarbiyyar daya samu daga uwar rikonsa ,halinsa na hakuri da son mutane ya kara taimaka masa wajen cikar kamalar rayuwarsa. Musaddik tun yana yaronsa, kyakyawa ne sosai me cikar kamala, kwarjini ga farin-jini. Burin Hajiya Kilishi bai cika ba na raba Inna Halima da Musaddik har sai da Musaddik ya kai aji hudu na sakandire, sannan Alhaji Mansur da kansa ya zauna da Inna Halima da mijinta Malam Saminu da kuma Malam Mahmud mahaifin Afrah, ya Page 95 bukaci zai maida rikon dansa hannunsa, ya Kuma yi masu godiya a bisa rikon da suka yi ma marayan dansa. À ranar Inna Halima ta yi kuka har hawayenta suka Kare , domin ta shaku da Musaddlik tana kuma Kuma Kaunarsa fiye da ya' yanta da ta haifa, babu wanda bai tausaya mata ba a cikin wadanda aka yi zaman da su. Alhaji Mansur ya ba Inna Halima da mijinta da Malam Mahmud kyautar kujerun makka, tare da kudi masu tsoka, domin ya yi ikirarin ba shi da wanda suka fi masa 'yan-uwan Harirah, Domin su ne suka taimake shi akan dansa a lokacin da yake bukatar taimako, kuma ba zai taba mantawa da 'Yar-uwarsu Harirah ba, wacce ta ba shi abinda zuciyarsa ke shaukin samu, ta kuma rasa ranta a dalilin hakan. Wannan karamci da Alhaji Mansur ya yi masu, ya ba su sha'awa sun kuma yi masa godiya sosai, sai dai kamar yadda Inna Halima ta shiga damuwa akan rabuwa da Musaddik, haka shi ma Musaddik din ya shiga matsananciyar damuwar rabo da Mamansa, ya yi kewarta, ya yi kuka mai tsanani, amma ba shi da yadda zai yi, domin haka Allah ya Kaddara ma rayuwarsa. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 96 Komawa da rayuwarsa gidan mahaifinsa ya fuskanci bambanci matuka na kulawar uwa abinda ya saba Inna Halima na yi masa, na nuna Kauna tausayi da soyayya, sam ba haka ya riska a gidan mahaifinsa ba. Daga matar ubansa, domin babu abinda yake fuskanta sai tsana da tsangwama daga Hajiya Kilishi. Amma a bayan idon mahafinsa, domin a gaban idonsa, duk duniya babu me kima da mutuncin musaddik a gun Haj kilishi.domin takan nuna duk duniya babu wani abin da take so sama da shi. Hakan ya sa Alhaji Mansur ya sami natsuwa, domin a tunaninsa Hajiya Kilishi ta canja halinta, tana zaune da dansa domin Allah akan mutuntawa. Shi kam Musaddik masifar tsoron Hajiya Kilishi yake yi, don haka ko a cikin tunaninsa. Bai taba tunanin ya gaya ma mahaifinsa halin da yake ciki da Hajiya Kilishi ba, sai dai idan abin ya dame shi, ya kwaso jiki zuwa gidan Inna Halima da kukansa ya na gaya mata. Amma ko ta yi kokarin ta je ta gaya ma Alhaji Mansur, sai Musaddik ya hanata, a Cewarsa baya bukatar duk wani abu da zai tayar da hankalin mahaifinsa, don haka idan tana son farin-cikinsa, to kada ta gaya masa komai, har kullum Inna Halima tana sha' awar halin Musaddik na damuwa da farincikin wasu fiye da farin-cikinsa. bata da yadda zatayi tunda tana bukatar kwanciyar hankalin musaddik, sannan kuma bata son ta shiga lamarin gidan Alh mansur, a kokarin ta na tsira da mutuncinta a wajen Alh mansur din. Haka lamarin ya ci-gaba har zuwa lokacin da Musaddik ya kammala makarantar sakandire, Page 9 inda Alhaji Mansur ya yanke shawarar kai Musaddik kasar waje, domin ya samu Digree dinsa a can,Tashin hankali! Hajiya Kilishi ta samu matukar damuwa akan hakan, shin wace irin kulawa ce Musaddik yake samu fiye da "ya 'yanta, wadanda tuni suna ma'aura, ko wacce na gidan mijinta. ita shi kenan ba ta da wani abu da za'a kyautata masu, kamar yadda Alhaji Mansur yake kyautata ma musaddik Me ya sa ya fi son Musaddik akan kowa? Ko don shine Magajinsa? Ita shi kenan haka za ta tashi a tutar babu? A gaskiya Musaddik ya zamar mata fitina, yanzu har kasar waje zai je ya yi karatu domin idonsa ya Kara budewa.yasan "yancinsa, ya gagareta ya kuma buwayi rayuwarta. Duk hanyar da za ta bi, don ta kawo cikas akan kai Musaddik kasar waje, ta bi, amma ba ta sami nasara ba.don tuni Alh mansur ya samo masa gurbin karatu a oxford university dake london.Haka zalika ba a dauki wani dogon lokaci ba, aka gama komai. Alhaji Mansur da kansa ya dauki Musaddik zuwa London, bai dawo ba sai da komai ya yi dai-dai. Watau ya tabbatar da Musaddik ya fara shiga aji,sannan ta dawo Nigeria kan kasuwancinsa a yanzu ji yake ya mallaki komai na duniya, tunda yana da babban da namiji kamar Page 98 Musaddik,wanda zai iya daukar nauyin kasuwancinsa, zai iya kula masa da dukiyarsa, shi ya sa yake kokarin ba shi ingantaccen ilimi da zai amfane shi. Ya kuma amfani rayuwarsa. baida fargabar komai a yanzu, koda mutuwa ya yi. A yayin da Hajiya Kilishi kullum take kwana take tashi da tunanin, yadda za ta yi da, Musaddik domin ta dauke shi a matsayin shine matsalar rayuwarta. Musaddik ya dage wajen mutunta rayuwarsa a London, ya rike mutuncinsa, duk wata harka, idan ba ta arziki bace, ba za ka taba ganinsa a ciki ba, ya rike addini da al'adarsa, abinda ya kai shi, shi yake yi, ya maida hankalinsa sosai wajen karatunsa domin ya riga ya fuskanci abinda mahaifinsa ya fi bukata kenan a duniya Don haka ba zai taba ba shi kunya ba, zai tsaya ya yi abinda ya kamata. Dalilin hakan Musaddik sai da ya zama (Best Student), saboda tsananin hazakarsa .cikin haka har ya kammala Digree dinsa, ya kuma dora Masters dinsa, sau uku kawai ya taba dawowa Najeriya. Sai dai Alhaji Mansur da yake kokarin ziyartarsa akai-akai, har ya kammala Masters dinsa ya tattaro ya dawo gida Najeriya, ya zama nagartaccen matashi me kwarjini da cikar kamala, ga kyakkyawan hali abin koyi ga kowa. Page 99 Dawowar Musaddik Najeriya bayan kammala karatunsa. Alhaji Mansur ya sami cikar burinsa, gaba daya ya ji ya gama mallakar duk wata ni’ima ta duniya, mako uku da dawowarsa. Aka yi gagarumin bikin ba shi kamfanin yin siminti na Alhaji Mansur daya mallaka masa, ya kuma mallaka masa katafaren gida, da mota. amma wannan. karon sai da Hajiya Kilishi ta yi bore akan ba za ta taba yarda da wannan hukuncin ba. Domin ita ma 'ya' yanta da ta haifa ai 'ya' ya ne, ganin yadda ta tada hankalinta, ya sa akan dole ya sai ma 'ya'yanta motocin hawa, duk da suna gidan mazajensu, sannan ya mallaka musu makudan kudade domin su tsaya da kafafunsa.hakan ne kawai ya sassauta mata damuwar da take ciki. Sai dai tana ganin lokaci ya yi da za ta dauki Kwakkwaran mataki akan Musaddik. A lokacin ne kuma Alhaji Mansur ya bukaci Musaddik ya fito da mata, ya yi masa aure. Domin cikar kammalarsa, domin duk a rayuwarsa abinda ya rage ya yi masa kenan, ya cikasa rayuwar dansa, shi kam! Musaddik ba

Chapter 6 of 15