Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi da wata mace da yake so, asalima shi bai taba tsayawa ya yi soyayya da ko wace mace ba. Ko da ya je gidan Inna Halima ya gaya mata abinda mahaifinsa ya umarce shi da yi, shawara kawai ta ba shi akan ya tsaya ya nemo ma 'yayansa uwa ta-gari, don haka ya yi taka-tsantsan! wajen nemo matar aure. Page 100 Domin zai iya yiwuwa macen ta so shi domin abinda ya mallaka ko don gidan daya fito ko don kyau da cikar kamalarsa. Tabbas! Maganar Inna Halima gaskiya ce. Ya zamar masa dole ya tsaya ya nemi abokiyar rayuwa ta-gari. A yayin da gefe daya Mama Hauwa ta fara yi ma kawun musaddik Malam Mahmud maganar mai zai hana Musaddik ya zo ya nemi 'yarsu Sakina, ayi tuwona maina.tunda tana ganin ya isa da Musaddik din yana cewa ya ba shi sakina shikenan, domin tana kwadayin yarta ta samu gidan hutu gidan arziki irin gidan Alh mansur. Nan da nan Malam Mahmud ya gargadeta akan kada ta fito da maitarta a fili, idan Musaddik yana son Sakina, da kansa zai furta. Tunda ai gidan ba bakonsa bane, yana zuwa yana kuma. ganinta, Don haka idan yana sonta, ba sai an yi masa magana ba, da kansa zai furta, hakan yasa dole Mama Hauwa ta yi shiru da maganar. sai dai ta dora Sakina a hanyar ta dinga nuna ma Musaddik so da kulawa a duk sanda ya zo gidan, har ya 'Fahimci inda ta dosa, Amma abinda Mama Hauwa ba ta sani ba, shi ne tuni Hajiya Kilishi ta gama shirinta tsaf akan kokarinta na farko na ganin ta tarwatsa rayuwar Musaddik.Domin zuwa wannan lokacin gaba daya ta gama tsara yadda zata kawo karshen kyakkyawar rayuwar da Musaddik yake shimfidawa.Don haka Ta yi tunanin hada auran Musaddik da 'yar kanwarta Hannatu da suke zama a birnin tarayya Abuja, ta bukaci ta dawo nan Minna gunta da zama tunda ta; gama makaranta zaman banza kawai take yi. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 101 Amma kafin Hannatun ta dawo , sai da Haj kilishi tayi magana da Kanwarta Hajiya Kubra, wacce kusan halinsu daya, don haka koda ta gaya mata kudurinta na hada Musaddik da Hannatu aure da dalilinta, ba ta ji darr! Ba, ta amince, domin tana ganin duk Karuwarsu ce. Hannatu za ta zama musabbabin kusanta su da arziki, ta umarci Hannatu da ta tafi minna,don haka Hannatu ta tarkata kayanta ta yi minna. Gargadì na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi mata, shine kada ta sake ta dora ma Kanta son Musaddik, domin ta sa a ranta aure ne za su yi na wucin gadi, na dan lokaci, sai ga shi Kuma anyi sa'a Musaddik din burge Hannatu kawai yake yi, amma babu sonsa ko kwayar zarra a zuciyarta. Sai dai ta ci-gaba da shishige masa tare da nuna masa kauna da kuma kokarin nuna masa ita yarinya ce ta-gari, kamar yadda Haj kilishi ta nuna mata, sai dai ko kadan Musaddik bai taba sa ma ransa wai zai so Hannatu ba Ko kurna tana yin abinda take yi masa, don ya so ta ne. Tsawon lokaci Hannatu ta share a gidan, amma Musaddik baya ko bi ta kanta, hidimarsa kawai yake yi. Hakan kuwa ya fara tayar ma da Hajiya Kilishi hankali, ta rasa mafita, don haka ta nemi aminiyarta Hajiya Rakiya, domin neman shawarar yadda za'a bullo ma lamarin, ba tare da wani dogon tunani ba. Page 102 Hajiya Rakiya ta bada shawarar a hada Lamarin da Malamai, domin a hada soyayyar Musaddik da Hannatu ta karfi da yaji, wannan shawara ta yi dai-dai da tunanin Hajiya Kilishi don haka ta bukaci rakiyar Hajiya Rakiya zuwa wajen amintaccen bokanta Wato Mai Rakwacam, suna isa tun kafin su fadi abinda ya kawosu. Mai Rakwacam ya gaya masu dalilin zuwansu, ya kuma tabbatar masu da cewa auran Musaddik da Hannatu tamkar an yi, an gama ne. Ya yi ta surkullen ayyukansa, daga bisani ya ba ta kwallin da Hannatu za ta sanya a idanunta,wanda suna hada ido do Musaddik Shi kenan, sai turare da za ta shafa a jikinta,wanda so ake kawai ya ji kamshin, sai kuma wani garin magani da za ta zuba masa a cikin abincinsa da zaran ya ci abincin shikenan bukata ta gama biya. Bayan dawowarsu daga wajen Mai Rakwacam ne. Hajiya Kilishi ta ba Hannatu duk abubuwan da za ta yi amfani da su. Na sawa a abinci kuwa da kanta take sanya masa, kuma sai ta tabbatar ya ci, sannan take barin wajen, kwanaki uku kacal! Tsakani. Musaddik ya haukace akan soyayyar Hannatu. Bai sami sukuni ba, sai da ya gaya mata, ta kuma amince. Da kansa ya sami Alhaji Mansur ya gaya masa ya sami matar aure, wato Hannatu. Alhaji Mansur ya karbi maganar babu yabo, ba fallasa, don dai a so samunsa ne, ya sami wata wacce ba ta da alaka Page 103 da Hajiya Kilishi. Domin baisan dalilin da yasa ya ji kwata kwata bai samu wata natsuwa ba da jin zabin musaddik duk da baida wani buri da ya wuce na musaddik din ya fito da matar aure ya yi masa .Amma tunda abinda dansa yake so, shi yake so, ya sa ya amshi zabin na sa hannu biyu ba tare daya bari ya gane zabin na sa bai yi masa ba. Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ta sami jindadi, farin-ciki da kuma natsuwa, domin hakanta ya kusa cimma ruwa, nan da nan aka shiga shirye-shiryen biki kasancewar Hannatu marainiya ce mahaifinta ya rasu, kuma zuwa wannan lokacin ba su da komai sai gidan da suke ciki a Abuja shine kadai rufin asirinsu bayan haka basu da wani abin da zasu yi tunkaho da shi. Hakan ne ya sa Alhaji Mansur ya dauki nauyin komai na dakinta da abinda za’ayi mata. Haj kilishi kuwa marairaicewa ta yi ta na yi masa godiya, tana kuma nuna masa tamkar bata damu da auren ba tamkar bata so, don ta nuna don dai kawai musaddik din ya matsa ya na sonta ne ba don haka ba ai Musaddik ya fi karfin Hannatu. Sabida tsabar makirci. A ranar da Musaddik ya je ya gaya ma Inna Halima, Hannatu ya zaba a matsayin matarsa ta yi masa fatan alheri tare da sanya ma lamarin albarka.duk da acan kasan zuciyarta itama tana jin tamkar danta musaddik bai dace da Hannatu ba, amma alokacin da ya kawo mata ita har gida ta gaisheta sai ta ji ta yaba da hankalinta da nutsuwarta saboda nuna mata tayi duk duniya babu wanda ya kaita ladabi da biyayya da kuma son Musaddik din. Hakan yasa inna Halima ta watsar da wancan tunanin nata, ta yarda da Hannatu. Daga bisani musaddik ya je gidan kawunsa Malam Mahmud domin shi ma ya sanar da shi maganar auren nasa da Hannatu., a ranar ya tarar da Afrah tana wanke-wanke cike da mutuntawa ta gaishe shi. Ya amsa cikin nuna yabawa da lamuranta. Domin dai duk cikin *ya yan Kawunsa, babu yarinyar da haka nan yake ganin girmanta tare da kaunar dabi ‘unta irin Afrah, yarinyar gaba daya rayuwarta daban ce, ba ta da hayaniya. Bayan ya gaisa da Kawunsa da Mama Hauwa yake sanar da Malam Mahmud maganar Hannatu Malam Mahmud ya yi murna, ya kuma sa albarka sabanin Mama Hauwa da ta hade girar sama da ta kasa, idan ranta ya yi dubu, to ya baci, ta dubi Musaddik tace “Amma Musaddik ca na ke soyayya ka ke da Sakina?” Page 104 Ji Musaddik ya yi saurin kallonta ya ce Cike da mamaki yace”Soyayya, kamar yaya?" Ta ce "Irin yadda na ga taku ta zo daya, sai na ke zaton ko soyayya ku ke yi, ka ga shikenan tuwona, maina, sai ayi hadin zumunta kawai" Musaddik ya girgiza kai ya ce “Mama Hauwa kin fahimta a bai-bai, domin gaskiya ba soyayya muke yi ba. Asalima ni ban taba dasa ma kaina tunanin zan so-ta ba, daya wuce ina sonta amma soyayya ta 'yan-uwantaka. Hannatu dai ita ce na ke son na aura, ita nake kwadayin ta zama abokiyar rayuwata”. Mama Hauwa ta yi turus! Tana kallonsa Cike da takaici, a yayin da Mallam Mahmud ya ce "Kyaleta ka ji, neman zance ne da ita kawai. Musaddik Allah ya sanya alheri, ya sa Hannatu abokiyar arzikinka ce, ya kawo zaman lafiya a tsakaninku” Cike da girmamawa Ya amsa da "Amin" Daga nan ya zaro kudi ya aje masa, Mallam Mahmud ya yi godiya, kamar yadda ya saba.sannan ya tashi zai tafi, dai-dai inda Afrah take, ya tsaya ya dakko kudi masu yawa ya ba ta, ganin irin kallon wulakancin da Mama Hauwa ke yi masa, ya sa ya fice ba tare da ya bata ko sisi ba. Kamar mama Hauwa na jiran musaddik ya fita kawai ta kafama mallam mahmud gwanjon bala'i, wai yana da damar da zai sa Musaddik ya auri Sakina, amma ya ki sa baki, illa ma goya masa bayan auran Hannatu da yake yi. Daya gaji da sababi da bala'inta ne ya kakkabe rigarsa ya tattara ya bar gidan. Page 105 Bayan auran Hannatu da Musaddik, a Katafaren gidan da Alhaji Mansur ya ba shi ya tare, babu Wanda baya sha'awar rayuwar Musaddik. Allah ya rufa masa asiri, amma baya wulakanci. Baya kyamatar talaka, ga taimako da son shiga duk abinda zai daukaki addini, ba Alhaji Mansur kadai yake yaba da halayen dansa ba, har sauran jama"a suna matukar ganinsa da kima da daraja, domin dai Allah ya tabbatar da natsuwa a cikin rayuwarsa. Musaddik Mansur musaddik kenan. Wadannan halayen nasa da jefa shi a cikin sahun mutanen kirki da kowa yake yi, da kuma alfahari da mahaifinsa yake yi da shi, ya na matukar bakanta ran Haj kilishi ji take kamar ana fisgar ranta. Duniya ba matabbata ba. Watanni biyu kacal Da auran Musaddik. Allah ya dauki ran jigo kuma gatan Musaddik, wato Alh. Mansur, ya yi rasuwar farat daya a dalilin hadarin mota a hanyarsa ta zuwa Kano daga Abuja, domin halartar wani taron yan kasuwa da suka gayyace shi. Sai gawarsa ce ta dawo Minna, inda a nan ne aka yi masa suttura aka rufe shi. Fadin tashin hankali da kuncin da Musaddik ya shiga, bata lokaci ne. Nan da nan ya rame, ya fige, ya fita hayyacinsa. Rasuwar mahaifinsa ta yi Mummunan taba shi, hatta abinci baya iya ci. Duk wani me imani, dole ya tausaya masa, domin ya fada mawuyacin hali. Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM Page 106 Haka Inna Halima da Malam Mahmud su ka yi ta Kokarin dawo da shi musaddik hayyacinsa tare da yi masa addu'ar samun dangana. Ita kam Hajiya Kilishi duk da rasuwar mijin nata ya taba mata zuciya, to fa maganar abinda ya mutu ya bari, ya fi damunta, bakin-cikinta daya ne na kaso mafi tsoka da Musaddik zai samu, domin dai ta san kason 'ya' yanta mata biyu. MusaddiR zai ci shi kadai. Idan da akawi abinda za ta fi shi da shi, bai wuce tumunin takabarta ba da kason 'yarta daya, ta san kuma babu abu daya da 'ya'yanta zasu bari a hannunta, tunda sun riga sun mallaki hankalinsu. Suna kuma tare da mazajensu, don haka ta san da kasonta kadai za ta tashi, shin ya za ta yi? Ta san dai ba ta da damar hana Musaddik gadonsa, domin ya san yancinsa. Yasan abinda musulunci ya tanadar masa. Abinda ko take gudun ne ya faru, domin bayan fitarta takaba, aka yi rabon gado, ba gidan Musaddik ba motarsa ba kuma kamfaninsa na siminti a cikin rabon Domin Alhaji Mansur ya rubuta a rubuce cewar duk wadannan abubuwan ya ba shi su kyauta ne. Hakan ko ya tada hankalin Hajiya Kilishi, domin zahiri wannan karon Alh mansur ya yi son rai don kamata ya yi yadda ya ba musaddik wannan tarin dukiyar ace su ma su Hassana ya basu domin su ma yayansa ne, amma soyayyar musaddik ya makantar da shi daga ganin illar wannan bambancin da yake nunawa a tsakanin yayansa, wanda kusan shine dalilin da ya jefa rayuwar gudan jininsa cikin gararin rayuwa bayan rasuwar tasa, domin dai Haj kilishi ta kara haukacewa da tsanar musaddik fiye da kullum, domin duk akasafin rayuwarta babu abinda take hangowa sai gado, duk da babu wanda yasan gawar fari, To ga dai abu a rubuce, balle ta ce karya ne ta kuma danne , babu wannan damar Sannan da aka yi rabon gadon Musaddik ya tashi da kaddarori da Kudade makudai amma duk ba su a gabansa, ba su kuma burge shi ba, ya fi Page 107 bukatar mahaifinsa fiye da komai a duniya, ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa gaba daya tunaninta ya tafi ne akan dukiyar Musaddik da tunanin yadda dukiyar za ta zama nata, watau ta mallake ita daya. Abu na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi, shi ne kokarin mallake Musaddik, da taimakon Bokanta Mai Rakwacam, ta kashe makudan kudi Kafin bukatarta ta biya, domin kuwa ta sami mallake Musaddik, komai zai aikata ko zai zartar akan duk abinda ya shafi rayuwarsa sai da saninta, sai da kuma amuncewarta Yana matukar jin tsoronta tare da tsoron bata mata rai, sai daya zamana duk duniya Musaddik gani yake baida kowa sai Hajiya Kilishi, hatta dangantakarsa da su Inna Halima duk ta ja baya, domin ko kafin ya je gidanta ma aiki ne. Kwata kwata ya dauke kafarsa basa ganinsa wanda hakan ba karamin ta da hankalin su ya yi ba.A yayin da Hannatu take tsiro da halayen wulakanci da musgunawa ga musaddik sam ba ta ganin mutunci ko darajarsa mutuncin ko darajarsa.abu kadan tun bayan rasuwar Alh mansur zata hau cin mutuncinsa. Gaba daya duk ta canja. yayin da shi kuma musaddik din ya dora ma kansa tsoronta da shakkarta, gaba daya lamuran Musaddik suka dagule, rayuwarsa ta shiga cikin gigita da dimauta. Wannan shine tushen fara lalacewar rayuwar musaddik. Domin dai baida tunani nasa na kansa, sai wanda Hajiya Kilishi da Hannatu suka tusa masa, haka zalika baida ta cewa, sai cewarsu, Page 108 A hankali Hajiya Kilishi da Hannatu suka fara karar da dukiyar Musaddik,ya zama wanda da sun ce,ya yi kaza bai samun sukuni, sai ya aikata masu, Haka Hajiya Kilishi ta yi ta sa Musaddik yana sa hannu akan Kadarorinsa me tabbatar da cewa ya mallaka mata, wasu kuma ya mallaka ma Hannatu. Daga Inna Halima har Malam Mahmud babu wanda ya san wainar da ake toyawa, balle su taimaka masa su yi ma tufkar hanci tun nesa sa kofa .Hatta kamfanin ya daina zuwa kullum yana gida, hakan ko ya fi komai yi ma Hajiya Kilishi dadì, inda ta fara tura Hannatu kamfanin tana shiga ofis dinsa hakan ko ya janyo cece ku ce a kamfanin a tsakanin ma'aikatan, daga bisani Hajiya Kilishi tasa Musaddik ya yi ma ma'aikatansa bayanin cewa Hannatu ce za ta ci-gaba da daukar nauyin kamfanin, domin shi ayyuka sun yi masa yawa Sannu a hankali cikin dabara da kauce hanyar Allah ta bin Bokaye da Hajiya Kilishi ta saba ta sami nasarar kwace kamfanin daga hannun Musaddik, inda ya sa hannu aka kuma kafa shaidu akan cewa ya bar ma natarsa kamfanin halas-malak. Wanna lamari ya daga hankalin abokin Masaddik kuma (Cashier) na kamfanin Murtala domin zuwa wannan lokacin ya fara zargin tamkar Musaddik baya cikin hankalinsa, domin abubuwan da suke faruwa abubuwa ne masu matukar daure kai matuka. Akwai alamar tambaya domin hatta mu’amalar Musaddik da mutane duk ta canja. Yana yin abubuwa tamkar bai san abinda yake yi ba. Page 109 Da kansa ya sami Musaddik ya tunantar da shi muhimmancin kamfanin a gare shi, ya kuma tambaye shi meye dalilinsa na barin ma matar da bai taba koda haihuwa da ita ba irin wannan dukiya? Anya kuwa yana cikin hayyacinsa. Musaddik ya numfasa yana kallon Murtala, sannan yace cikin wata irin fuska “Ni fa babu abinda ke gabana, ko Yake min dadì gaba daya rayuwar ma ni ta fita kaina, don haka duk wata dukiya, ni ba ta gabana. Kuma Hannatu matata ce, ko ta haihu ko ba ta haihu da ni ba, zan iya yi mata kyauta, saboda haka don Allah ka tsaya a matsayinka na aboki na, ka daina kokarin shiga abinda bai dameka ba,” Haka Murtala ya bar Musaddik cike da mamakin irin maganganun daya gaya masa, domin dai ya san ba haka Musaddik yake ba a da don haka bai ji haushi ba. Ya yi alkawarin zai ci-gaba da fahimtar da shi illar abinda yake aikatawa, har ya fahimta, ko ya nemi wani shakikin Dan-uwansa ya sanar da shi abinda ke faruwa ko za su iya taimakawa. Sai daya zamana Hajiya Kilishi ta gama zare komai, domin hatta gidan da yake ciki, ya mallaka shi ga Hannatu, sannan har zuwa wannan lokacin babu abinda bangaren dangin Musaddik na wajen uwa suka sani.a lokacin ne Hajiya Kilishi ta ga ya kamata ta dauki mataki na karshe na karasa lalata rayuwar Musaddik. Page 110 Domin ba ta kaunar duk wani sanadi da Zai sa Musaddik ya farga ya dawo hayyacinsa, ya fahimci irin mummunar barnar da ta yi ma rayuwarsa, ko kuma hankulan mutane da na dangin mahaifiyarsa su ankara da halin da ta jefa Musaddik. Don haka ta fara neman shawarar aminiyarta Hajiya Rakiya yadda za su yi da Musaddik. Hajiya Rakiya ta yi shiru tana nazarin lamarin, a nan ne Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce "Ni fa Hajiya Zuciyata a bushe take akan Musaddik ko kadan ba na kaunar yaron nan, musamman idan na tuna ni fa ba ni da da namiji, sannan ga irin fifikon da ya samu sama da nawa yayan, sannan wannan daraja da natsuwa da yake da shi da kowa ke sha’awar sa ya na matukar bata min rai,sai na ji tamkar na raba Musaddik da doron Kasa" Ta dan hadiye yawu gami da kallon Haj Rakiya da take sauraron ta, sannan ta ci-gaba da cewa cikin wata muguwar Fuska, da gaba daya ta canja yanayin ta, ta koma tamkar ba ita ba. "Kamar yadda a yanzu na gama tunanin lokaci ya yi da zan raba Musaddik da duniya gaba daya, domin duk wani amfani da zai yi min, ya riga ya gama yi min, kuma ina ganin mutuwarsa ita ce kadai hanyar da asirina zai rufu akan dukiyarsa, domin babu wanda zai tuhumeni..” Hajiya Rakiya ta yi gaggawar dakatar da ita tana yi mata kallon ko kin haukace ne? Ta ce "Haba Hajiya. Shin rashin imaninki har ya kai ki fara tunanin daukar rai, bayan duk irin ta'asar da ki ka yi masa na raba shi da arzikinsa mallakarsa, da raba shi da yancin zama miji me cikakken iko a gidansa.duk wannan bai isa ba, sai kin kashe shi? Ku dakace ni Daga taskar Yar gidan imam MUSABBABI NA HABIBA ABUBAKAR IMAM page 111 abin ya yi yawa gaskiya, kuma ni ban goyi bayan wannan shawarar ta ki ba na a kashe shi, saboda babu komai a cikin shawarar taki sai gagarumin hatsari Shin ba kya ma tunanin ko Musaddik ya rasu yan-uwan mahaifiyarsa za su iya bin kadin dukiyar musaddik din daya mallaka miki, ba gara kin bar shi araye, shi ya gaya ma duniya da kowa ma cewa shi ne ya mallaka maku dukiyar ba. Idan ko mai kaya ya ce ya bayar, to waye ya isa ya ce bai bayar ba? Idan kuma ki na tunanin shi zai iya yi miki bore wata rana ne, ai akwai wata hanyar da ta fi wacce ki ke son bi saukin bi."Haj kilishi cike da gamsuwa da maganganun Hajiya Rakiya ta ce "Wace. hanyar ce?" Hajiya Rakiya ta ce "Ba sai a lalata rayuwarsa ba, a raba shi da kyakkyawan tunani, a hana shi shiga cikin mutanen kirki, balle har shawarwarinsu su yi tasiri wata ran a rayuwarsa. Me zai hana a kwace kwarjini da kamalar da jama"a suke ganinsa da ita, ina nufin a hada shi da shaye-shaye, domin shaye-shaye shine tushen lalacewar rayuwar, duk wani matashi. Shine kuma zai zama abin kyama a wajen mutanen kirki “ Ta gyara zama tana kallon aminiyarta cike da jindadin maganarta da jin shawarar ta ta itace abar dauka ta ce “ ina jinki Haj” Hajiya Rakiya ta ci-gaba da cewa, "Kin ga kuma mutane ba za su taba zarginki ba, za su dauka don dukiyar da aka bar masa ne ya sa ya canja halinsa da kuma bakin-cikin rashin mahaifinsa, Page 112 wasu ma cewa za su yi ya sayar da kaddarorinsa ne,ya yi iskancinsa, babu wanda zaiyi zargin kece kika kwashe dukiyarsa,” Hajiya Kilishi ta yi dariya sosai ta ce “Amma haj ban taba tunanin ki na da kaifin basira haka ba, idan ka kashe makiyin ka ma, ai ka taimaka masa ne, gara ka'aje shi ka yi ta kallon sa yana wahala a rayuwarsa, don haka shawararki ta yi, na kuma dauketa, ki na kuma da tukuici na musamman' Hajiya Rakiya ta ce "To godiya na ke babbar giwa, musaddik din me da zai dinga tayar miki da hankali” Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce "Amma ina fatan za ki ci-gaba da rike min sirrina kamar yadda ki ka saba, kada wanda ya ji ko ya gani, mu haka mu binne, kamar yadda muka saba” Haj Rakiya ta yi dan murmushi ta ce "Haba, haba, ai ba ki da wata matsala in dai nice, ki sha kuruminki, babu me ji ai tsakanin mu ya wuce haka” Haj kilishi ta sauke ajiyar zuciya ta na jin tamkar ta gama mallakar komai na daga cikar burinta a duniya. daga nan suka ci-gaba da tattaunawa akan yadda komai zaibtafi yadda suke so ba tare da wata matsala ba. Page 113 Washegari kuwa da taimakon rakiyar haj Rakiya suka tafi rugar Mai Rakwacam dauke da bukatunsu, da fatan samun dacewa. Mai Rakwacam ya dauk tsawon lokaci yana bincikensa, kafin ya dubi Hajiya Kilishi ya ce, '"Aiki zai yiwu, bukata kuma za ta biya, ki aje Naira dubu dari biyu da hamsin, za' a sayi kayan aiki." Nan da nan Hajiya Kilishi ta Balle jakarta ta aje masa kudin, ya kara kallonta ya ce "To ku tashi ku tafi, jibi goshin magariba ki dawo” Haj Kilishi ta yi godiya, suka tafi Kwanaki biyu tsakani goshin magariba kamar yadda me Rakwacam ya bukata. Hajiya Kilishi da Hajiya Rakiya suka isa rugar, sun tadda Mai Rakwacam ya kammala duk mugun aikin da zaiyi akan bukatar su.don haka Ya dauko wata bakar laya da ta ji surkulle, ya dubeta yace ta sami kasan jijiyar bishiyar kuka ta binne hade da wani dan karamin kasko daya ji daure-dauren bakin zare, duk jikinta an zaneta da Sunan Musaddik, ya ce ta hada da layar ta binne, da zarar ta binne aiki ya kammala. Babu wanda zai raba Musaddik da Shaye-shaye da lalacewa, sai ranar da aka tono wannan layar da kaskon. Don haka ta san yadda za ta binne da kuma inda za ta binne.domin ana son dadaddiyar kuka da ta dade. Ya kara da cewa, ba zai karbi ko sisi ba, sai aiki ya ci. Daga nan za ta dawo ta cake masa Naira dubu dari uku cif! Hajiya Kilishi ta karbi komai ta Page 114 yi godiya tare da alkawarin dawowa ta ba shi hakkinsa da zarar bukata ta biya, daga nan suka dauki hanyar gida Suna cikin tafiya ne. Hajiya Kilishi ta dubi Hajiya Rakiya ta dan rage gudu fuska cike da farinciki ta ce "Yanzu ina za mu samu bishiyar kuka, inda za'mu binne wannan asirin?" Hajiya Rakiya ta yi murmushi ta ce. "Dadina da ke mantuwa, ai ni tunda ya ambaci bishiyar kuka, na ji na sami kwanciyar hankali , kin manta rikakkiyar bishiyar kukan da ke bayan gida na, abubuwa nawa muka binne a kasanta, tun marigayi megidanki na raye,” Hajiya Kilishi ta fashe da dariya ta ce "Godiya “ Anyi haka, godiya na ke da samun aminiya, mai share hawayen kuka na, yanzu kawai mu wuce gidan naki mu aiwatar da aikin kafin na wuce gida” Haj Rakiya ta yi dariya tace “Angama kawata”. Sun isa dare ya yi, gari kuma ya yi duhu, Hajiya Rakiya ita' ce me haska ma Haj kilishi bakin bishiyar da hasken wayarta. Hajiya Kilishi kuma na aikin haka, sai da ta haka rami me zurfi. Sannan ta binne kaskon da layar. Babu Wanda ya gan su har suka gama, suka tafi.hankali kwance kamar wadanda su ka aikata abinda ya dace, Allah kasa mu fi karfin zuciyar mu, yasa duk runtsi mu tsira da imanin mu. Kwanaki biyu tsakani, sai ga Hannatu hajaran majaran tana gaya ma Hajiya Kilishi ba za ta koma. gidan Musaddi& ba, domin jiya kwana ya yi yana shaye-shaye, ta ce dama ya iya shayc-shaye ne? Mutumin da ko taba ba ta taba ganin ya sha ba, Page 115 amma rana amma abin tsoro da mamaki sai gashi rana tsaka ta gan shi cikin wannan mummunan halin. Hajiya Kilishi ta fashe da dariya, ta mike tayi rawa, ta yi juyi, ta daga hannu tana yi ma Allah godiya tare da yi ma kanta kirari na sharri. Hannatu ta yi galala tana kallonta cike da mamaki Hannatu tace “ Ya na ga ki na murna Inna, wannan fa magana ce ta canja sabon babi magana ce ta lalacewar rayuwar Musaddik da ni kaina” Hajiya Kilishi ta koma ta zauna, tana Fadin “ waye yace miki haka Lalacewar rayuwarsa dai, ina ruwan ki, ko kin manta tun farko na gaya miki wannan aure ne na dan lokaci; aure ne kuma na samun arziki, ko kin yi kuskuren fara sonsa ne?" Hannatu ta girgiza kai ta ce "Ban fara sonsa ba gaskiya amna a zahiri na fara tausayinsa, saboda in dai rayuwar da ya fara a yanzu akanta zai cigaba da tafiya to babu abu daya na alheri da zai zo gabansa a duniya “ .Haj kilishi ta saki tsaki tace

Chapter 7 of 15