Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe in Allah ya yarda zan juya." Tace "Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a." Suka amsa da "Amin." BAYAN KWANA BIYAR. Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan baccinta riga da wando kalar dark pink, tana shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran sunanta. "Meenah..." Ta kalle ta gami da yin murmushi tace "Na'am Zarah." Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take kwance tace "Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da gaske." Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da Zarah. "Wane mutumi kenan?" A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya had'u da ita a Instagram! "Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi." "Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..." Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana k'ok'arin karantawa. Zarah tayi ajiyar zuciya tace "Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki sauarare shi." Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah tace "Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke, ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan." Zarah ta kalle ta da mamaki tace "Me kike gudu?" Meenah tace "Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara, ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina, sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..." "Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da gaske..." "Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya yin soyayya yanzu ba..." Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta ranta idan yayi dubu to ya 6ace. "Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka? Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba! Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..." Ta d'aga mata hannu "Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance, shikenan?" Zarah tayi murmushi "Shikenan, kiyi karatunki sai da safe." Tayi murmushi "Allah ya kaimu lafiya." Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta wayarta. Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki. Dubawa tayi. "Hello." "Hey." "No answer?" "How are you dear?" "Hmm." "Are you sleeping?" "Please talk to me mana." Da k'yar tace "Hi." Yana kwance yana latse latse a laptop nasa message nata ya shigo, ya ware manyan idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya rubuta mata. "Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i thought na maki wani laifi ne?" "A'a bakomai..." "So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?" "Hmm." "Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i ko?" "A'ah..." "To ki bani mana, idan ba rowa ba." Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta tura masa number d'in. Minti biyu tsakani... Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri, bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu ta d'auka.... AUREN FANSA 19 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹19 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Tun kafin ta kai ga d'auka haka kawai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, ta kira sunan Allah don neman nutsuwa cikin zuciyarta. Cikin ikon Rabbi kuwa ta samu nutsuwa sai dai kafin ta d'auka tuni wayar ta katse. Ajiyar zuciya tayi, sai dai tana katsewa wani kiran na shigowa. "AssalamuAlaiki yake ma'abociyar kyau, kwarjini da kuma nutsuwa." Abinka da rashin sabon waya da maza, tuni ta rasa nutsuwarta, da k'yar ta amsa masa "Wa'alakumsalam." "Yau dai na taki sa'a tunda har aka d'auki wayata sannan aka d'aga lokacki d'aya, lallai ni mai babban sa'a ne. Ko ba haka ba 'yan mata?" Ta k'ara kiran sunan Allah a karo na biyu, saboda rashin sabo da kuma muryar mutumin da bata san ko waye ba, sai dai me? Jin muryar takeyi kamar ana busa sarewa, bata ta6a jin murya mai dad'i ba irin ta wannan mutumin ba... "Ya kikayi shiru Princess?" Gabanta ya yanke ya fad'i, wai wannan mutumin kamar aljani? Da yayi mata magana sai gabanta ya fad'i. "Nidai muryar nan taki ko dai zan biya ne don na lura tana tsada..." "Ina wuni?" Yayi murmushi, har tana jiyo sautin yana bugun dodon kunnenta, sannan a take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr! "Kina lafiya?" "Lafiya lau." "To masha Allah, zan d'an baki dan gajeren labarina, bana so ki zo kina ce min bakisan ko da wa kike waya ba... ko ba haka ba?" Tace "Uhm." Yace "Yauwa, da farko sunana Faruk Adam, shekarata 26 kacal a duniya, iyayena sun rasu gaba d'aya tun ina k'arami, yanzu daga ni sai k'anwata muka rage, ina zaune gidan wani uncle d'ina a garin Abuja. Mahafiyata shuwa ce while babana fulani ne. Yanzu dai na kammala karatuna ina aiki. To kinji kad'an daga cikin tarihin rayuwata, ko zan iya jin naki?" Tace "uhm, Allah ya jik'ansu." Yace "Amin, ina jinki fa." Da k'yar ta iya tattaro nutsuwarta wuri d'aya ta soma magana mai cike da nutsuwa. "Sunana Amina Hamza, mahaifina d'an garin Katsina ne amma yanzu aiki ya kai shi Abuja, na kammala karatuna na fita daga secondary ina jiran admission zan tafi university. Mu biyu ne kad'ai a gidanmu daga ni sai k'anwata mai suna Fatima." Yayi murmushi "Allah sarki Allah ya taimaka, to baki fad'a min shekarunki ba?" Tace "16." Yace "Wow, lallai ashe dai da sauranki yarinya." Tayi murmushi mai cike da kunya. Haka suka 6ata wannan daren Faruk na janta da fira, tun tana d'ari d'ari har ta d'an saki jikinta tana bashi amsa, idan akayi labarin dariya suyi dariya, daga k'arshe ganin har uku na dare ya sashi yayi mata sallama akan zai kirata da safe. Koda ta kwanta kasa bacci tayi, muryarsa kawai takeji cikin dodon kunnenta kamar yanzu yake mata magana. Daman bata sallah sheyasa ma bata tashi da asuba ba. Bacci takeyi har kusan goma da rabi na safe. Juyi d'aya tayi akan gado tayi tozali da wayarta kamar had'in baki sai kuma ta fara ruri. Ganin number d'in jiya ya sata sakin murmushi ba shiri. A kasalance ta d'auka gami da yin sallama. "Good morning! Rise and shine, raina ya bani yanzun nan kika farka daga bacci, ko da yake laifi nane dana hana ki bacci da wuri tun jiya ko? To ayi min afuwa. Bazan sake ba." Cikin ranta tace "Wannan sai kace aku ko gajiya baiyi da magana?" "Ina kwana?" Yayi murmushi "Lafiya lau da fatan princess d'in tawa ta tashi lafiya?" Ta langa6ar da kanta gami da lumshe idanu tace. "Alhamdulillah, thanks." Yace "Yauwa, to yanzu abinda ya kamata kije kiyi wanka sai kici abinci." "To." Kawai tace gami da yi masa sallama ta kashe wayar. Ganin Zarah tsaye bakin k'ofa ya sa gaban Meenah ya yanke ya fad'i. Zarah ta k'araso tana dariya "Love in the air, yanzu don Allah bakiji dad'i ba? Amma ace mutum ya takura ma kansa da rayuwar kad'aici haba!" Murmushi tayi ta sauka daga kan gadon tace "Bari nayi wanka." Tana jin Zarah na d'aga murya tana fad'in "Wai don dai kar ayi maganar zaki wani shige wanka." Murmushi kawai tayi. Wunin ranar zungur a d'aki tayi shi, har dare bata fito ba, ba abinda ke tashinta daga gado sai shiga toilet. Washe gari kuma haka ta tashi sukuku. Zarah ta rasa gane kan yayar tata. Haka dai komai ya cigaba da gudana a tsakanin Meenah ta Faruk, wuni sukeyi mak'ale a waya, zuciyarta ta aminta da shi lokaci guda, ta yarda ta amince shi d'in takeso. Tun da ya turo mata hotunan sa taji yayi mata, lokaci guda ya sace zuciyarta ya kuma tafi da imaninta gaba d'aya, har ta soma cewa cikin ranta "Anya ba surk'ullensu na fulani yayi mani ba?" Wata rana da daddare yana ta kiranta ya sanar mata gobe zaizo wurinta, daman sunyi zaizo Katsina, idan yazo zai shigo su gaisa. A lokacin da yake ta kiranta tana bacci kuma wayar a silent take. Washe gari da safe sai ta iske message d'insa ya turo mata. "Just to say good night! With you in my mind... ?" Sai tayi murmushi ta tura "In both the soul and mind...." A lokacin da ta tura masa sak'on bai gani ba saboda yana cikin jirgi don tahowa Katsina! AUREN FANSA 20 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to each and every reader, you always support me, and i am grateful for that! Thanks alot!❤️ 🌹20 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina, yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala. Banda su snacks da aka tanada. Goggo da k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta lek'o tana fad'in. "Kai lafiya me kuke dafawa?" Zarah tayi dariya tace "Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su Meenah ake ta shiri haka." Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Goggo tayi dariya tace "Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan." Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i zaizo. Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya ta tura masa da message akan yasa a shigo da shi bakin k'ofa (main entrance). Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri. Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a hoto... Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i ma suka zauna masa had'e da hutu, ga kuma uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya. Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta. Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta ce "Ya hanya? Ya kuma gajiya?" Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya yace "Alhamdulillah, ya gida ya hutu?" Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace "Komai alhmdulillah, yasu Anisah?" Yace "Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?" Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a mutunce, yace "Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki. Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about you, gaskiya sister nan taki tana ji take." Zarah tayi dariya "Haka ne, nima ina ji da ita ay." Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice. Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa 6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta. Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba, Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba, gaba d'aya ta fad'a tarkon so. Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan ta kar6a tana godiya sosai. Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki, basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma kullum yana kan hanyar zuwa wurinta. Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya, sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta. Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya, ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar kuku ba! Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa na har k'arshen rayuwarta ba. AUREN FANSA 21 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹21 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan kwana biyu da safe sai ga Baba ya diro garin wai da niyyar d'aukar su Meenah, hanakalin Meenah ya tashi don tasan da k'yar idan Mami zata barta tayi soyayya ba, tasan dai Baba baida matsala, amma Mami take ji. Aikuwa tana sanar da Faruk cewar gobe zasu koma Abuja yace shima zai tattara ya koma daman ya gama abinda ya kawo shi, sai ya koma zai cigaba da kawo mata ziyara. Washe gari kuwa suka tattaro suka dawo gida. Duk da hankalinta a tashe yake hakan baisa taji ko d'ar a zuciyarta game da son da takeyi wa Faruk Adam ba. A ganinta shi d'in yasan menene so, yasan darajar abinda yakeson, ya kuma iya tafiyar da shi ta hanyoyi daban daban, ya iya tarairaiyar mace da bata kulawa yadda ya kamata. Sheyasa son da take masa shi yake k'ara bata k'warin gwiwar fuskantar Mami. Suna dawowa kuwa kusan kullum sai yazo, har dai ya zama d'an gida, yadda taga Baba ya amshi Faruk hannu bibbiyu ya sanya dole taja bakinta tayi tsit, kuma kullum yazo Zarah ke raka Meenah fira, hakan yasa ita kanta Mamin ta rasa gane wurin wa yake zuwa, amma tana fatan wurin Zarah yake zuwa, don a yadda take gani mutum ne mai kud'i sosai. * K'arfe takwas na dare kamar kullum Faruk ya isa gidansu Meenah, kasancewar ya zama d'an gida tsakanin Baba da Mami. Bayan sun gaisa da Baba, a lokacin Baba yana da niyyar fita, haka ma Mami tana sama tana fama da lissafin kud'in kasuwancinta. Yana nan zaune yana jiran Meenah. Aikuwa sai gata ta fito tayi kyau kamar kullum cikin material mai taushi silver da ratsin bak'i a jikinshi, d'inkin doguwar riga, d'inkin bai kama jikinta ba. Tun daga nesa suke sakarma da junansu murmushi mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange, pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa gami da rausayar da kai yace. "Barka da hutu!". Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi maganar, tace "Alhamdulillah, muna ta sha kam." Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace. "Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?" Ita dariya ma ya bata tace "Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan." Ya langa6ar da kai yace "Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar aurenki zanyi..." Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e mata zuciyarta, tace "Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu had'in Allah ce, i respect you and your values.. Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi, bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin mijin aurena na har abada..." Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba kamar pampo, amma daga baya sai take ganin kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa "Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan kulawa." Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan marmarin yana sha. *** Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman k'arin bayani takeyi tasan Zarah bazata ta6a fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji. Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun kuma manta komai. Don haka taga babu mafita illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda take zargi. K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci. "Mami....?" Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace "Amina....!" Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho mata tambaya "Meke tsakaninki da Faruk?" Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba, sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita k'wala. "Bada ke nake magana ba?!" Cikin sark'ewar murya tace "Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina, kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar sanar daku muna son junanmu... mun yanke shawarar yin au..." Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin wawan marin da har sai data ga giftawar wuta, ta nemi ji da ganinta ta rasa! AUREN FANSA 22 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa, Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️😍 🌹22 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bilki ta soma magana cikin fushi. "Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa Meenah."! Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana. "Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba, ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai kuma ta juya mata baya gami da had'e hannayenta wuri d'aya tace "A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta, amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!" Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a Meenah na fad'a. "Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike neman ki fad'a min magana Meenah." Ta fad'a tana nuna kanta. "Bafa saurayi na bane Mami." Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace "Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida tabbas a kanta? Mami! Ki sani Meenah 'yar uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin saurayina ne?" Tayi murmushi tace "To ba haka bane, ni kawai mun saba ne sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani na bin wani, tasa hannu ta share mata tace "Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki ne ke kad'ai kinji?" Suka rungume juna suna kuka. Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta fice daga d'akin cike da kunya! A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda taga rana haka taga dare. Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta, itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha jiya sai gabanta ya fad'i. * K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune parlor tana chanza channel, tun daga jin sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa. Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin magana a cikinsu. Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin basarwa yace "Munyi ma Mami laifi ko?" Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu tace. "Tun jiya take haka, mun rasa gane mata." Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace "K'ila bata amince dani ba..." Tayi saurin cewa "Bakomai zata huce ne." Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa. Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa. Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da girmama juna, can Baba yace "Umar Faruk." Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace "Na'am Baba." "Meke tsakaninka da Amina?" Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya sadda kansa k'asa. AUREN FANSA 23 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹23 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Baba yayi murmushi yana dubansa yace. "Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar da nayi maka." Ya daure yace "Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace min batada wanda ta tsada, to amma... amma mun daidaita kanmu." Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na 'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan Faruk. "Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida, hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kafin na amince maka da auren Meenah, ina so kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta, shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka. Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara." Yace "Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a kaina insha Allah babu matsala." Baba yayi murmushin jin dad'i yace "Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo magabatan naka." Faruk yayi murmushi. Yace "To Baba babu damuwa insha Allah." Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye. Yace "Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya amsa da "Amin." Baba ya yi gaba, Faruk yabi bayansa yana jinjina al'amarin. *** Abu k'arami na neman zama babba, tun tana ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba. Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame masa zuciya farat d'aya, duk wani observation nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar ke zaune a kai ta dafa ta. "Yaya Jidda..." Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole. Anisah tayi murmushi. Meyake damunki?" Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace "Babu komai." Anisah ta girgiza kanta. "Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce kin zama wata iri? Har Mama ta soma tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi miki..." Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana kallon wayarta. Yusra ce ta lek'o tace "Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri kiran nada mahimmanci." Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace. "Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta girma ta iya soyayya ko?" Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu sakata gaba da zolaya. Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar tunani. "Ya Najeeb." Yayi sassanyar murmushi yace. "Anisah kina lafiya?" Tace "Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?" Yace "Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni ba?" Tace "Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa na fito." Yayi murmushi yace "Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun karatunku ina kukayi applying?" Tace "Nayi applying first choice d'ina a Base nida Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile. Sai last mukasa BUK." Yace "Ok yayi Allah ya taimaka." Tace "Amin." Yace "To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma yau ba inda zaki sai kin fad'a min." Cike da kunya tace "Wace magana ya Najeeb?" Yace "Kin fini sani." Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace "Ke nake

Chapter 9 of 11