Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
satinsa d'aya da tafiya, amma insha Allah ya kusa dawowa." Najeeb yace "Ok... hakane munyi waya yake fad'a min batun tafiyar tasa Allah ya dawo dashi lafiya." Aka amsa da "Amin" Daga haka kowa yayi hanyar d'akinsa. Faruk d'akinsa ya burgeshi yadda yayi tsab sai k'amshi da sanyin ac ke ratsa dukkanin illahirin jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya fad'a toilet. Yana gamawa ya saka k'aramar riga da dogon wando. A dinning aka hallara kowa yayi serving kansa jollof d'in shinkafa, da pepper soup, sai kaza gasassa sai salad. Sun fara cin abincin ne Mama tace. "Alhamdulillah, Allah na gode maka daka nuna man wannan ranar, ranar da 'ya'yana suka kammala karatunsu lafiya, fatana Allah ya albarkaci karatunku, Allah ubangiji ya baku sa'a." Gaba d'aya sukace "Amin amin." Ta cigaba "Yanzu dai ga Likita Najeeb, ga Detective Faruk, ga kuma Banker Nabeel, kai masha Allah! Allah yayi albarka." Suka ce "Amin Mama mun gode Allah ya saka da alkhairi." Tace "Amin, yanzu dai ya kamata kuyi settling kowane ya nemi mata yayi aure, shine kad'ai abinda ya rage." Duk kansu k'asa basu ce komai ba, itama Mama murmushi tayi a haka suka cigaba da cin abinsu. *** Bayan Wata D'aya...! Zaune yake kan kujerar office d'insa yana faman dube dube a computer d'insa, aka shigo da sallama, a hankali ya d'aga ido ya kalli k'ofa yayi murmushi. "Ah Usman! Shigo mana ya zaka tsaya a bakin k'ofa?" Ya k'araso yana gaishe shi "Ina wuni sir?" "Lafiya lau zauna magana zamuyi." Bayan ya zauna, Faruk ya soma magana. "Wani aiki zan saka, don Allah ina so duk abinda nake nema ka yi k'ok'ari wajen ganin ka samo min duk wani abu zan buk'ata." Usman yace "Insha Allah, ay ba yau ka fara sani aiki ba, kuma duk lokacin da kake sani abu ina k'ok'ari waje ganin na gano maka koma me kake nema." Faruk yace "Haka ne, to yau ma ina tafe da wani aikin mai matuk'ar mahimmanci a wurina." Ya fad'a yana fiddo wani abu a cikin drawer d'in table d'insa. "Karanta kaga." Da ladabi ya kar6a ya soma karantawa. Bayan ya gama yace "Yalla6ai amma suna ne kawai nake gani." Faruk yayi wani d'an guntun murmushi yana juya kujerar da yake zaune akai. Sai da ya d'auki tsawon mintina biyu zuwa uku sannan ya soma magana. "Eh sunaye ne na mutum biyu, bincike nake buk'ata akansu." "Toh yalla6ai." "Yawwa, i want every bit of information regarding them. Ina buk'atar komai idan nace komai i mean everything. Wane gari suke? Wace unguwa? Sunada 'ya'ya? Guda nawa ne? Suna da miji? Meye sunansa? Wane aiki yake? Ina da ina suka fi zuwa? Wace makaranta yaransu suke? Don't left out anything, including their photos." Usman ya gyara zamansa yana fuskantarsa. "Angama amma yalla6ai meyasa kake neman information d'innan haka? Sannan ta ina zan samo hotunan su?" Faruk ya mik'e tsaye tare da dawowa gaban Usman gami da zama saman table a kusa da shi yace "Usman bana son shishigi, aiki na saka shi zakayi min, kawai kaje ka kawo min abinda na saka please banda wasa, sannan hotunansu wannan kai zaka nemo." Usman yace "Hakane insha Allah zanyi k'ok'ari." "Yauwa kana iya tafiya." Daga haka ya fice, inda Faruk yayi murmushi yace. "This is my first step towards my goal, waiting for the next step." Yayi murmushi yana kad'a kai. AUREN FANSA 16 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹16 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Tsaye take a gaban wardrobe tana gyara zaman skirt d'inta, duk da kayan dake jikinta sun mata kad'an hakan bai hana ta yin kyau ba, ji tayi an rungume ta ta baya, tasan baya wuce aikin Zarah. "Auch! Haba mana Zarah so kike ki k'arasa ni ne?" Zarah tasa dariya, tace "To sarkin fad'a, yanzu dai maida wuk'ar albishir nazo miki dashi." Meenah ta juyo da murmushi saman fuskarta tace "Ina jinki." Zarah tace "Fari ko ja?" Meenah tace "Fari k'al ma kuwa." "Baba yace nayi WAEC d'ina yanzu idan naci mu tafi university tare!" Zarah tace cike da murna. Meenah farin ciki ta rasa ina zata sa ranta, dama ta dad'e tana addu'ar su tafi university tare da Zarah, sai dai tasan Baba ne ya hana yace bazatayi ba sai ta kai SS3, amma yanzu ko ya akayi ya yarda? Meenah tace "Amma ya akayi ya yarda?" Zarah tace "Wallahi ikon Allah, kuma fa ba tambayar sa nayi ba, shi da kansa ya kirani yace na shirya yin exam tare da ke." Meenah cike da murna tace "Lallai ikon Allah, Allah yasa kici." Zarah ta rungume Meenah tana murna tace "Amin sisi." "Kai meye kun cika ma mutane kunne da hayaniya?" Cewar Bilki daga bakin k'ofar d'akin tana tsaye, fuskarta ba yabo ba fallasa. Sukayi tsit, ta kuma daka musu tsawa "Ba da ku nake ba?" Zarah tace "Da... dama, Baba ne yace za... zan iya tafiya university tare da Meenah..." Take ta washe baki kamar ba ita ba, tace "Allah d'iyar Baba? Yaushe ya yarda?" Tace "D'azu kafin ya tafi wurin aiki." Bilki tace "Alhamdulillah, yayi daidai Allah ya bada sa'a sai ki dage, tun kafin ace bakida k'ok'ari, ko kuma ace wasu sun fiki." Ta k'arasa tana ma Meenah wani irin mugun kallo. Duk sun san abinda take nufi kuma hakan ya sosa ransu. "Ke! Meenah zo ki matsa man k'afa ta." "Mami zan taya ta." Wani kallo ta watso mata na irin kika k'ara magana sai na kakkarya ki sannan ta fice. Meenah ta dafa ta tana fad'in. "Don Allah Zarah daga yau ki daina cewa zaki taya ni idan tasa ni aiki, wallahi fad'a kike ja man duk sadda kika fad'i haka." "Uhm." Kawai Zarah tace, daga haka Meenah ta juya da sauri zuwa sashen Mami. Da sallama ta shiga, zaune take kan wata kujerar hutawa ta baje k'afafuwanta ma'ana ta mik'ar dasu saman kujerar, tana faman danne danne a wayarta k'irar iPhone 7plus, tana zuwa ta durk'usa har k'asa tace "Gani Mami." Sai data samu tsarabar harara sannan tace "Meya tsaida ki tun d'azu nake zaman jiranki?" Bata ce komai ba kanta na k'asa dai. "Sai anyi magana kiyi sum sum da kai kamar mutuniyar arzik'i..." "Kiyi hak'uri Mami, wallahi ban tsaya yin komai ba nan na taho." Tayi tsaki gami da mik'o mata k'afa. "Ni matsa man k'afata, kuma saura kiyi mani mugunta irin na rannan wllh sai na yi maganinki, don yau sai dai a kaiki asibiti don sai nayi miki lis!" A hankali take matsa mata cikin lalla6awa, sai kuma ta sakar mata k'wanya a kai. "Ke bakida hankali ne? Ya zaki dinga mani abu kamar susar k'adangare?" Sai ta hau yi da d'an k'arfi, nan ma ta kai mata wanda yafi na d'azu zafi. "Yau ga muguwa! Zaki 6alla min k'afa ne?" Ta rasa yadda zatayi, mistake kad'an sai taji k'wanya mai shegen zafi a kanta. Da daddare tana kwance ita dai abin duniya yabi ya dame ta, zuwa yanzu ta yarda ta amince ba Mami ta haife ta ba, ta yarda Baba ne babanta amma sam ta kasa yarda Mami ce ta haifeta. To ina mahaiyarta? Ta rasu ne ko tana raye? Ko kishiyar Mami ce? Kullum ire-iren wad'annan tambayoyin sune suke mata yawo a cikin kai, kuma har yanzu ta rasa amsa. Daga k'arshe ta yarda ta amice mahaifiyarta ta rasu kuma kishiyar Mami ce kawai. Wasu zafafan k'walla suka zubo mata, ita kam batasan dad'in uwa ba, bata san ya ake ji ba idan mutum na tare da mahaifiyarsa. Sama sama tayi bacci gudun makara saboda ga aikin gida ga kuma shirin makaranta. Da asuba ta mik'e bayan ta gabatar da sallar asuba tayi wanka, ta yi aikin gidan kamar kullum, ta had'a kalaci, d'aki ta wuce ta sanya uniform d'inta da basu samu guga ba, bayan ta gama shirinta tsab ta fito don ta karya, tana bud'e kular abinci sai ta ganta wayam! Nan ta hau dube dube amma kaf ba komai a ciki. Mami ce ta sauko cikin kayan bacci da d'aurin gaba tana zuwa tabi Meenah da mugun kallo, ta wuce kitchen. A ranar haka nan ta hak'ura da kalacin daman sun makara, sauk'inta ma Baba ya basu kud'in makaranta da batasan ya zatayi ba. *** BAYAN KWANA BIYU Da sallama ya shigo office d'in, yana zaune yana fama da aiki kamar kullum, d'ago da fuskarsa yayi yace "Shigo mana Usman." Sai da ya kammala abinda yakeyi sannan ya maida dubansa ga Usman dake zaune d'auke da wata babbar brown envelope. "Yalla6ai daman akan aikin da kasani ne, to Alhamdulillah na kammala maka komai shine na kawo maka ka gani." Da sauri ya d'ago yana duban Usman yace "Da gaske ka kawo duk abinda nake buk'ata?" Usman yana murmushi sosai yace "K'warai kuwa gasu." Ya sa hannu ya zazzaro wasu hotuna guda biyar ya dire a gabansa, sannan ya fiddo wani dogon paper mai rubuce rubuce a samanta.... AUREN FANSA 17 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the support you are special to me! Love you guys❤️ 🌹17 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon Usman yace. "Nagode, sai kayi min bayaninsu." Usman ya gyara zama yace "Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta komai amma duk da haka zan maka bayani da baki. "Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran bincike akansu kafin nazo nan." Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa. "Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata. Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar. Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana Kaduna da zama da mijinta mai suna Alhaji Sambo, sai d'iyarta k'wara d'aya mai suna Yasmeen." Gwauron numfashi Faruk ya sauke a lokaci guda kuma ya d'auko hotunan yaran nasu da akayi masa nuni dasu yana ta kallonsu yana juya hotunan. Aje hotunan kuma yayi yana kallon Usman tare da d'ora hannayensa saman table d'in yace. "Good job, so anything else?" Usman ya cigaba "Yes, makaranta d'aya suke zuwa mai suna Turkish, ita babbar tana k'ok'arin kammala karatun nata ne while ita k'aramar wato Zarah tana SS2 a yanzu. Duk weekend suna zuwa Katsina wurin mahaifiyar Hamzan mai suna Hajiya Fatima. Idan suka je kamar misali ranar Juma'a zasu dawo ranar Lahadi, amma yanzu bincike ya nuna mani cewar sunyi akalla sati biyu basuje ba, sakamakon jarabawa da d'iyar Alhaji Hamza take shirin zanawa ta fita daga secondary. Alhaji Hamza yakan d'auki yaranshi su fita yawon shak'awatawa duk ranar Alhamis da daddare." Ajiyar zuciyar ya sauke yana kallon Usman ya kuma cewa "Anything else? "Yawwa, ka tambaya ina da ina suke zuwa, to a zahirin gaskiya yaran Alhaji Hamza basa fita yawo, daga makaranta sai islamiyya, amma daga nan basu cika zuwa ko ina ba. Amma kayi hak'uri a 6angaren Hajiya Layla sai na k'ara bincike don bansamu wani information sosai ba, na dai gano cewar tana yawan fita Dubai saro kaya." Faruk yace "Nagode, ka manta ka sanar dani aikin da sukeyi fa." Usman yace "Sorry sir, Alhaji Hamza ma'aikacin banki ne, amma matarsa bata aiki tana harkar kasuwanci, wanda naji ance tana da gidajen mai, shaguna, mall, tana da k'aton shagon saida saide, da sauransu. Haka zalika Alhaji Sambo shi d'an kasuwa ne kuma yana aikin gwamnati." Ya saki ajiyar zuciya yace "Nagode da taimakon da kayi min duk da akan aikinka ne amma ni ka taimake ni ba kad'an ba, so nagode Allah saka da alkhairi." Usman yayi dariya "Haba yalla6ai menene na godiya? Ni keda godiya ay." Faruk yace "Bakomai Usman zaka iya tafiya." Daga haka ya amsa da "To." Sannan yayi masa sallama ya fita. Yana fita ya saki murmushin da shi kad'ai yasan mana'arsa. Murd'a k'ofar akayi aka shigo, Najeeb ne, da murmushi Faruk yace "Ka shigo mana." Bayan ya zauna ne Najeeb ya soma magana "Ka bani mamaki Faruk, ban ta6a tunanin haka daga gareka ba..." Gaban Faruk yayi mummunan fad'uwa, yace "Me akayi?" Najeeb yace "Yanzu daman abinda kake shiryawa kenan baka sanar dani ba? Inda banji me kuke cewa ba da bazaka ta6a fad'a min ba ko?" Faruk yace "Ko kad'an ba haka bane, naso ace sai na gama duk abinda ya kamata sai na sanar maka..." Najeeb yace "To tunda yanzu naji sai ka fad'a min komai." Faruk yayi dariya yace "Akan dai maganar nan ce ta kwanakin baya." Najeeb yace "Maganar iyayenka ko?" Faruk yace "Eh ita, so wani d'an bincike nasa aka yo mani akan mutanen kuma an kawo." Ya k'arasa yana mik'a masa hotunan. Najeeb ya duba bayan ya gama yace. "Ok to menene next move naka?" Faruk yayi murmushin nasa da ya saba yi masu ma'ana daban daban yace "Zan sanar da kai komai, yanzu muje muyi sallah mu dawo." Najeeb yace "Ok muje." A tare suka mik'e suka fice daga office d'in. *** Yana shiga d'akin nasa ya jiyo k'amshin turaren wuta mai dad'i, ga sanyin ac gaurewa da d'akin. Yasan baya wuce aikin Jidda, don ya lura tunda suka dawo take faman d'wainiya dashi, bakin gado ya zauna ya shiga cire takalminsa da safa, bai kai ga gamawa ba ta shigo d'akin nasa, hannunta d'auke da tray d'in ruwa da lemon kwali 5alive, a d'an k'aramin table ta ajiye ta d'ago tana kallonsa cike da kunya, tace "Sannu da zuwa yaya." Yace "Yawwa sannu da aiki." Tace "Yawwa, kana buk'atar wani abu?" Ya d'an karkato gami da kallonta yace "A'a nagode." Daga haka ta fice daga d'akin a yayinda shi kuma ya fad'a toilet don watsa ruwa. AUREN FANSA 18 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹18 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su Meenah sun gama zana exams d'in k'arshe. Ranar da suka gama Baba yayi musu kyauta mai tsoka sannan ya musu alk'awarin tafiya Katsina hutu. Murna a wurin Meenah ba'a magana, daman tafison can saboda can tafi sakewa tayi abinda takeso, babu mai takura mata. Haushi Bilki kamar zata fashe, daman duk sadda zasu je Katsina hutu sai hankalin Bilki ya tashi a cewar ta mai mata ayyukan gidan bata nan. Akan dole takeyi har sai sun dawo. A tsarin hutun sati biyu zasuyi inji Baba, don haka tun ranar Meenah ta fara shirin tafiya. Ta wanke kayanta ta goge. Ranar da zasu tafi tunda asuba ta tashi, bayan tayi wanka ta d'auko cikin sabbin kayanta na wata sallah ta saka, blue atamfa d'inkin riga da skirt, tayi kyau sosai. A lokacin data sakko k'asa ta iske Baba da Zarah suna karyawa, yana ganinta yace. "Maza zo kici abinci mu kama hanya." Da saurinta kuwa ta taho tana murmushi. Bayan sun kammala, Hassan mai gadinsu ya shigo ya fara fitar musu da kayansu yana sakawa boot. Bilki ce ta sauko tana yak'e, tace "Badai tafiyar bace?" Baba yayi dariya yace "Itace yanzu zamu kama hanya ma." Ta had'iye 6acin ranta tace "Wai tun yanzu Alhaji?" Sai da yayi murmushi yace "To idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe zamu tafi? Katsina fa ba nan ba." Tace "Hakane kam, to Allah ya tsare ya kaiku lafiya." Yayi murmushin jin dad'i yace "Amin." Bayan gama ban kwana, Alhaji ya d'auki hanya zuwa Katsinan Dikko. Sai can yamma suka isa, da gudu su Meenah sukayi ciki suna zuwa suka haye 'yar tsohuwar dake zaune tana hutawa a parlor. "Kai kai zaku 6alla ni ne?" Sai kuma tayi murmushin jin dad'i "Ahh Aminatu da Fatsima ne? Saukar yaushe?" Meenah tace "Yanzun nan muka iso, ina wuni Goggo?" Tace "Lafiya lau, ina Baban naku." Meenah tace "Yana waje yanzu zai shigo." Bata rufe baki ba ya shigo. "Lale maraba da Hamza." Yayi dariya tare da zama k'asa yana kai gaisuwa zuwa ga mahaifiyar tasa. "Mun same ku lafiya? Tace "Alhamdulillahi, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, ya k'arfin jiki?" Tace "Sai godiyar Allah." Yace "Allah k'ara lafiya, daman yaran suka kammala makaranta shine na kawo suyi maki sati biyu, naga sun kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe in Allah ya yarda zan juya." Tace "Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a." Suka amsa da "Amin." BAYAN KWANA BIYAR. Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan baccinta riga da wando kalar dark pink, tana shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran sunanta. "Meenah..." Ta kalle ta gami da yin murmushi tace "Na'am Zarah." Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take kwance tace "Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da gaske." Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da Zarah. "Wane mutumi kenan?" A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya had'u da ita a Instagram! "Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi." "Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..." Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana k'ok'arin karantawa. Zarah tayi ajiyar zuciya tace "Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki sauarare shi." Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah tace "Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke, ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan." Zarah ta kalle ta da mamaki tace "Me kike gudu?" Meenah tace "Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara, ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina, sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..." "Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da gaske..." "Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya yin soyayya yanzu ba..." Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta ranta idan yayi dubu to ya 6ace. "Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka? Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba! Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..." Ta d'aga mata hannu "Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance, shikenan?" Zarah tayi murmushi "Shikenan, kiyi karatunki sai da safe." Tayi murmushi "Allah ya kaimu lafiya." Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta wayarta. Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki. Dubawa tayi. "Hello." "Hey." "No answer?" "How are you dear?" "Hmm." "Are you sleeping?" "Please talk to me mana." Da k'yar tace "Hi." Yana kwance yana latse latse a laptop nasa message nata ya shigo, ya ware manyan idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya rubuta mata. "Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i thought na maki wani laifi ne?" "A'a bakomai..." "So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?" "Hmm." "Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i ko?" "A'ah..." "To ki bani mana, idan ba rowa ba." Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta tura masa number d'in. Minti biyu tsakani... Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri, bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu ta d'auka.... AUREN FANSA 19 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹19 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Tun kafin ta kai ga d'auka haka kawai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, ta kira sunan Allah don neman nutsuwa cikin zuciyarta. Cikin ikon Rabbi kuwa ta samu nutsuwa sai dai kafin ta d'auka tuni wayar ta katse. Ajiyar zuciya tayi, sai dai tana katsewa wani kiran na shigowa. "AssalamuAlaiki yake ma'abociyar kyau, kwarjini da kuma nutsuwa." Abinka da rashin sabon waya da maza, tuni ta rasa nutsuwarta, da k'yar ta amsa masa "Wa'alakumsalam." "Yau dai na taki sa'a tunda har aka d'auki wayata sannan aka d'aga lokacki d'aya, lallai ni mai babban sa'a ne. Ko ba haka ba 'yan mata?" Ta k'ara kiran sunan Allah a karo na biyu, saboda rashin sabo da kuma muryar mutumin da bata san ko waye ba, sai dai me? Jin muryar takeyi kamar ana busa sarewa, bata ta6a jin murya mai dad'i ba irin ta wannan mutumin ba... "Ya kikayi shiru Princess?" Gabanta ya yanke ya fad'i, wai wannan mutumin kamar aljani? Da yayi mata magana sai gabanta ya fad'i. "Nidai muryar nan taki ko dai zan biya ne don na lura tana tsada..." "Ina wuni?" Yayi murmushi, har tana jiyo sautin yana bugun dodon kunnenta, sannan a take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr! "Kina lafiya?" "Lafiya lau." "To masha Allah, zan d'an baki dan gajeren labarina, bana so ki zo kina ce min bakisan ko da wa kike waya ba... ko ba haka ba?" Tace "Uhm." Yace "Yauwa, da farko sunana Faruk Adam, shekarata 26 kacal a duniya, iyayena sun rasu gaba d'aya tun ina k'arami, yanzu daga ni sai k'anwata muka rage, ina zaune gidan wani uncle d'ina a garin Abuja. Mahafiyata shuwa ce while babana fulani ne. Yanzu dai na kammala karatuna ina aiki. To kinji kad'an daga cikin tarihin rayuwata, ko zan iya jin naki?" Tace "uhm, Allah ya jik'ansu." Yace "Amin, ina jinki fa." Da k'yar ta iya tattaro nutsuwarta wuri d'aya ta soma magana mai cike da nutsuwa. "Sunana Amina Hamza, mahaifina d'an garin Katsina ne amma yanzu aiki ya kai shi Abuja, na kammala karatuna na fita daga secondary ina jiran admission zan tafi university. Mu biyu ne kad'ai a gidanmu daga ni sai k'anwata mai suna Fatima." Yayi murmushi "Allah sarki Allah ya taimaka, to baki fad'a min shekarunki ba?" Tace "16." Yace "Wow, lallai ashe dai da sauranki yarinya." Tayi murmushi mai cike da kunya. Haka suka 6ata wannan daren Faruk na janta da fira, tun tana d'ari d'ari har ta d'an saki jikinta tana bashi amsa, idan akayi labarin dariya suyi dariya, daga k'arshe ganin har uku na dare ya sashi yayi mata sallama akan zai kirata da safe. Koda ta kwanta kasa bacci tayi, muryarsa kawai takeji cikin dodon kunnenta kamar yanzu yake mata magana. Daman bata sallah sheyasa ma bata tashi da asuba ba. Bacci takeyi har kusan goma da rabi na safe. Juyi d'aya tayi akan gado tayi tozali da wayarta kamar had'in baki sai kuma ta fara ruri. Ganin number d'in jiya ya sata sakin murmushi ba shiri. A kasalance ta d'auka gami da yin sallama. "Good morning! Rise and shine, raina ya bani yanzun nan kika farka daga bacci, ko da yake laifi nane dana hana ki bacci da wuri tun jiya ko? To ayi min afuwa. Bazan sake ba." Cikin ranta tace "Wannan sai kace aku ko gajiya baiyi da magana?" "Ina kwana?" Yayi murmushi "Lafiya lau da fatan princess d'in tawa ta tashi lafiya?" Ta langa6ar da kanta gami da lumshe idanu tace. "Alhamdulillah, thanks." Yace "Yauwa, to yanzu abinda ya kamata kije kiyi wanka sai kici abinci." "To." Kawai tace gami da yi masa sallama ta kashe wayar. Ganin Zarah tsaye bakin k'ofa ya sa gaban Meenah ya yanke ya fad'i. Zarah ta k'araso tana dariya "Love in the air, yanzu don Allah bakiji dad'i ba? Amma ace mutum ya takura ma kansa da rayuwar kad'aici haba!" Murmushi tayi ta sauka daga kan gadon tace "Bari nayi wanka." Tana jin Zarah na d'aga murya tana fad'in "Wai don dai kar ayi maganar zaki wani shige wanka." Murmushi kawai tayi. Wunin ranar zungur a d'aki tayi shi, har dare bata fito ba, ba abinda ke tashinta daga gado sai shiga toilet. Washe gari kuma haka ta tashi sukuku. Zarah ta rasa gane kan yayar tata. Haka dai komai ya cigaba da gudana a tsakanin Meenah ta Faruk, wuni sukeyi mak'ale a waya, zuciyarta ta aminta da shi lokaci guda, ta yarda ta amince shi d'in takeso. Tun da ya turo mata hotunan sa taji yayi mata, lokaci guda ya sace zuciyarta ya kuma tafi da imaninta gaba d'aya, har ta soma cewa cikin ranta "Anya ba surk'ullensu na fulani yayi mani ba?" Wata rana da daddare yana ta kiranta ya sanar mata gobe zaizo wurinta, daman sunyi zaizo Katsina, idan yazo zai shigo su gaisa. A lokacin da yake ta kiranta tana bacci kuma wayar a silent take. Washe gari da safe sai ta iske message d'insa ya turo mata. "Just to say good night! With you in my mind... ?" Sai tayi murmushi ta tura "In both the soul and mind...." A lokacin da ta tura masa sak'on bai gani ba saboda yana cikin jirgi don tahowa Katsina! AUREN FANSA 20 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to each and every reader, you always support me, and i am grateful for that! Thanks alot!❤️ 🌹20 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina, yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala. Banda su snacks da aka tanada. Goggo da k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta lek'o tana fad'in. "Kai lafiya me kuke dafawa?" Zarah tayi dariya tace "Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su Meenah ake ta shiri haka." Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Goggo tayi dariya tace "Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan." Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i zaizo. Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fitou Alaikum..." Bilki ta d'ago tana k'are mata kallo. "Wa'alaikumusalam." Daga sama har k'asa na k'are mata kallo, Meenah ce ta girma haka? Tayi tsawo ta k'ara kyau, wannan ita ake kira black beauty, ga gashin kanta duk d'ankwalin da ke kanta hakan bai hana shi fitowa ba... "Mami na gama wanke kayan." Bilki ta ta6e baki. "Kin gyara min kitchen?" Tace "Eh na gyara." "Kinyi shara da wanke wanke?" Meenah tace "Eh nayi..." "Kin wanke toilets?" "Eh na wanke naki..." "Na d'akin Zarah fa? Shifa wa zai wanke?" Ta d'an bata rai. "Mami home work kawai zanyi sai na wanke, an bamu home work har biyar gashi ko d'aya ban ta6a ba." Ta doka mata harara, "Sannu 'yar boko, toh bari kiji bazakiyi ba sai kin gama min aikina tsab a gidannan sannan zaki yi wani home work." Tayi narai narai da fararen idanunta wadda suke kamar an d'iga madara a ciki. "Ke! Bansan iskanci ya ina miki magana kin tsaya kina wani kallon mutane zaki wuce ko sai na mauje ki!" A zahirin gaskiya bawani assignment d'in da zatayi, don ta riga tayi shi da asuba, daman gudun aiki yayi mata yawa sheyasa data gama sallah take home work ko karatu, kawai ta gaji ne tun safe take aiki bata huta ba, daga wannan sai wannan ko kalaci batayi ba... "Mami zan taya ta." Bilki ta 6ata rai "Kiyi ki gani yadda zanyi da ke a gidannan, maza kije kuma kar tayi nata home work d'in sai ta gama maki naki!" Sum sum Zarah ta fice zuciyarta cike da tausayin Meenah... AUREN FANSA 13 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹13 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Duk'e take tana faman wanke toilet Zarah ta lek'o, cikin muryar rad'a rad'a tace. "Meenah bari na taya ki." Meenah ta d'ago tana duban Zarah tace "A'a ki rufa man asiri Zarah, yanzu da Mami tazo zata dake ni." Zarah tayi murmushi "Ay dana ji ta taho zan bari..." "Nidai gaskiya ina tsoro ki bari kawai..." Da sauri Bilki ta shigo d'akin, tana zuwa ta jawo Meenah. "Ke maza kije kiyi wanka ga babanku nan dawowa, bar wankin toilet d'in zan k'arasa..." Halin maman tasu na basu mamaki, sun rasa meyasa da babansu ya kusa dawowa sai

Chapter 7 of 11