Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
saurare fa." Tace "Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?" Yayi dariya "Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da suke so, matan kuma su gabatar masa da wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na maina. Ko ba haka ba?" Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai. Tace "To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Yaji dad'in kalamantanta sosai yace "To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji daga bakinki." Tayi murmushi. Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma su tashi su shige ciki. MSB💖 AUREN FANSA 24 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹24 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Baba na zaune a parlonshi ya kira Bilki yace ta turo masa Meenah. Tana d'akin Zarah a bakin gado tayi tagumi, Zarah kuma na jera kayanta cikin wardrobe da aka kawo daga wurin wanki da guga da safe. Bilki ta shigo d'akin, da sauri Meenah ta d'ago fararen idanunta ta kalle ta, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin damuwa mai tsanani, take Bilki ta 6alla mata harara tace "Taso muje." Ta mik'e a sanyaye tabi bayan Bilkin har parlon Baba, jikinta yayi matuk'ar yin sanyi. Baba na duba newspaper da idanunsa mak'ale cikin farin gilashi a lokacin da suka shigo. Ya ajiye takardun gefe ya kuma cire gilashin yabi Meenah da kallo a lokacin da take zama kan carpet, sai ya saki murmushi yace "Aminatu jiya wannan yaron Faruk yake sanar dani cewar yana sonki, kuma yana so in bashi izini don ya turo da magabatansa, k'warai na yaba da hankalin yaron da kuma nutsuwarsa, amma kinsan bazanyi saurin yanke hukunci kai tsaye ba, ina so inji ta bakinki tukunna. Shin Amina kin amince Faruk ya turo da iyayensa ayi magana, ko kuma baki amince ba?" Farin ciki marar misaltuwa taji ya lullu6e ta har ta gaza 6oye hakan, take kuma ta sadda kanta k'asa fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi. Ta kai dubanta ga Bilki taga yadda ta had'e rai tayi murtuk. "Amina." Ta d'ago ta kalli Baban tace "Na'am Baba." Yace "Ke nake sauraro, shin kin amince Faruk ya turo magabatansa ko baki amince ba?" Da k'yar ta bud'e baki saboda matsananciyar kunyar da takeji tace "Haka ne Baba, kuma na amince." Yayi murmushin jin dad'i yace. "Alhamdulillah, idan yazo kice ya turo magabatansa, Allah yayi muku albarka." Kanta na k'asa tace "Amin Baba." Yace "Tashi ki tafi." Tashi tayi ta fita. Tana fita Bilki tace "Alhaji!" Ya dube ta yaga tayi kicin kicin da fuska yace "Lafiya dai Bilkisu?" Dama kamar jira take tace "Haba Alhaji don me zaka biye wa yarinya daga tace tana son mutum sai ka d'auke ta ka bashi, sannan baka ganin yarinyar nan k'aramar yarinya ce duka duka nawa take da zakayi mata aure yanzu? Ko university fa bata shiga ba, gaskiya ni ban amince ba sam." Sai ya kalle ta yayi murmushi yace "A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina k'in auren Meenah ne saboda k'aramar yarinya ce? To ni banga k'ank'anta a tattare da ita ba, shekaru goma sha bakwai gareta idan baki manta ba wata mai zuwa shekararta goma sha takwas, a hakan ne kike ganin yarinya ce?" Tayi shiru tana ciccin magani. Ya cigaba "Babu wani abu da iyaye zasuyi alfahari dashi face suga sun aurar da 'ya'yansu, shine kad'ai kwanciyar hankalinsu saboda idan zaki auna karatu baifi aure ba, haka zalika zata iya cigaba da karatunta d'akin mijinta. Saboda haka nake gargad'inki da kiyi gaggawar kawar da wannan gur6ataccen tunaninki ki koma hanya madaidaiciya." Jiki a sanyaye tace "Kayi hak'uri Alhaji, a had'o shayin ne ko sai anjima?" Yace "Bari sai anjima." A ranar duk wanda ya kalli Meenah yasan tana cikin matanancin farin ciki. Cike da farin ciki ta lalubo wayarta ta kira Faruk, bugu biyu ya d'auka. "My baby." Ya fad'a yana murmushi. Tayi murmushin jin dad'i. Tace "My soul." Sunan ta dake kiransa kenan. "Albishirinka!" Yace "Goro." "Fari ko ja?" Yayi dariya "In banda abinki ya ina ganin farin goro zan d'auki ja? Ay farin zan d'auka." Tayi murmushi "Haka ne, to Baba ya baka izini ka turo iyayenka my soul." Yace "Wow alhamdulillah! Gaskya nayi farin ciki insha Allah zan sanar da Dada, i love you so much my baby Allah ya nuna mana ranar auren mu lafiya." Tayi murmushin jin dad'i tace "Amin my soul love you too, bari naje Mami tana kirana sai anjima." Yace "Awwn kamar kar ki tafi, amma zan kiraki anjima, take care." Sukayi sallama ta kashe wayan, yana cire wayan a kunnensa ya hango Najeeb tsaye a bakin k'ofa yana kallonsa. Ya hau susan kai yace "Najeeb me kakeyi a nan? Ka k'araso ciki mana." Najeeb yayi ajiyar zuciya ya k'araso ciki ya zauna gefen Faruk kan gado tare da dafa sa. Yace "Faruk a gaskiya banga dalilin da zaisa ka yaudari yarinya ba alhalin ba itace tayi maka laifi ba." Faruk yayi murmushi yana kallon Najeeb yace "Don na yaudare ta shine me? Wannan shine first step da zan d'auka shine auren d'iyarsu!" Najeeb yace "Faruk da zaka ji shawarata da ka k'yale yarinyar nan akwai hanyoyi da dama da zaka d'auki Fansa ba dole sai ta wannan hanyar ba, she's too innocent wallahi dana ganta ta bani tausayi." Nan take Faruk ya fara huci, bak'in ciki had'e da 6acin rai suka taru suka masa dirar mak'iya! Ya mik'e a lokacin ne kuma idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa ja tsabar 6acin rai, shi kanshi Najeeb ya tsorata da ganin yanayinsa. Faruk ya soma magana cikin 6acin rai. "Najeeb! Kar ka manta alk'awarin da na d'auka a baya, na k'watar mana 'yancinmu, auren Meenah shine abu na farko da zanyi, don gudanar da duk wani bincike na da zanyi. Idan har ban auri d'iyarsu ba ta yaya zan cimma burina na gano musabbabin yadda aka kashe mana iyaye? Dole sai na kusance su, sun yarda dani sun kuma amince dani, ta haka kad'ai zan sa ido sosai akansu. Bayan haka! Sai nasa sun raina kansu, sai sunyi dana sanin abinda suka aikata, ita kanta Meenah lokacin kad'an nake jira dana aure ta zan kuma wulak'anta ta, dole idan nayi haka abin zaiyi wa iyayenta zafi, to wannan kad'an ne daga cikin abubuwan dana tanada!" Najeeb ya mik'e tsaye da sauri zuwa inda Faruk ke tsaye. "Dan girman Allah ka sauke k'udurinka na wulak'anta d'iyarsu, bata ji ba bata gani ba, haba ya laifin iyayenta zai shafe ta?" "Ya shafe ta! Kai harta karensu ko magensu laifin ya shafe su, na tsane su, na tsane su! Na tsane su! Wallahi duk sadda na kalli Meenah ko wani nata sai na ji kamar yanzu nake kallon gawar iyayena kwance cikin jini." Ya runtse idanunsa gam gami da dunk'ule hannu, take jijjiyoyin kansa suka mik'e tar! "Ka barni na cigaba da abinda na sa gaba, abinda kawai nake buk'ata daga gareka shine fatan alkhairi, amma idan ba wannan ba to bana buk'atar shawararka." Ya fad'a cike da 6acin rai "Haba Faruk! Meyayi zafi haka? Kayi hak'uri don Allah ka kwantar da hankalinka, mubi komai a sannu, insha Allah zaka cimma burinka." Take yayi murmushi. Rungume Najeeb yayi yana fad'in. "Yawwa ko kaifa, haka ya kamata ka fad'a." Najeeb ya k'ak'alo murmushi kurum. * Da daddare bayan Dada yaci abinci sai ya aika a kira masa Faruk, bayan ya shigo parlon Dada yana kallon tashar BBC, rage volume yayi yana kallon Faruk sadda yake zama kan carpet, bayan ya gaishe shi kamar kullum Dada ya soma magana. "Faruk dalilin da yasa na kiraka shine, naji labarin daga wurin Hajiya cewar ka samu matar da kake so haka ne?" Yace "Haka ne Dada." Dada yace "To alhamdulillahi, daman abinda nake jira kenan Allah yasa albarka 'yar gidan waye?" Faruk yace "Sunan mahaifinta Alhaji Hamza, 'yan garin Katsina ne amma nan garin yake aiki baban nata." Dada yace "To yayi kyau, da fatan kayi k'wak'waran bincike kafin ka fara soyayya da ita?" Yace "Eh Dada, mahaifinta ma'aikacin banki ne, shine manager na First bank yanzu haka, kuma mutumin kirki ne, to yama ce na fad'a maka na tura magabatana a yi magana." Dada yace "To alhamdulillah, indai wannan ne babu matsala kar ka damu zamu je insha Allah, ni na d'auki nauyin komai kai da k'anwarka, zan shirya nida Alhaji Musa da Alhaji Sufyan (k'aninsa da yayansa) sai muje insha Allah. Jeka kira min Nabeel da Najeeb." Yace "To Dada." Ya mik'e ya fita, ba'a juma ba suka shigo tare gaba d'aya, bayan sun zauna Dada ya fara magana. "Kamar yadda nayi muku alk'awarin gina muku gidaje, to an kammala, ga ma makullen nan, kai Nabeel bazan baka ba sai ka samo wacce zaka aura, amma da Faruk da Najeeb su tunda suna da wad'anda suke so, sheyasa zan damk'a masu takardun gidajen da kuma mukallen. Sai kuma anyi maku order d'in motoci guda uku, zasu iso nan da sati d'aya insha Allah. Sai abu na k'arshe maganar lefenku Hajara (k'anwarsa) na damk'a mata ragamar yin lefe na kowanenku, abinda zakuyi list sai ku rubuta duk abinda kuke buk'ata, Allah yasa alkhairi yasa ayi damu." Suka amsa da "Amin." Sannan kuma suka shiga jero masa godiya marar adadi tare da fatan alkhairi. Sai yanzu Faruk ke tunanin anya zai iya cin amanar Meenah kuwa? Ko don albarkacin Dada wannan kaya da ya masa haka? Sai dai ya k'udiri a ransa ya zama dole ya d'auki Fansa kota wani hali ne! Jikinsa yayi matuk'ar sanyi a yayinda dayake fita daga parlon. AUREN FANSA 25 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Miss Hafsy and Aisha Ali Garkuwa❤️ 🌹25 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Da gudu ta fad'a jikin Mama tana kuka sosai, Mama dake had'a kayan wankinta a cikin kwando ta dakata tana kallonta cike da mamaki, sannan kuma tace "Jidda lafiyarki haka zaki shigo kina kuka? Wani abin ne ya faru?" Ta k'ara fashewa da wani kukan har tana shasheka. Hankalin Mama ya tashi matuk'a har ta fara tunanin ko batada lafiya ne ma. "Wai bazakiyi magana ba, ni sa'ar ki ce ina miki magana kin min shiru?" Cikin kuka tace "Mama ki taimake ni! Mama idan na rasa shi kamar na rasa raina ne, bazan iya rayuwa bashi ba Mama ki taimake ni Mama!" Taci gaba da kukanta. Da mamaki Mama tace "Waye kuma idan kika rasa shi zaki rasa ranki? Ke bakida hankali ne? Akan namiji ki zauna kina wannan kukan, ni kin ma bani haushi. Wai waye ana miki magana kin ma mutane shiru?" "Ya Faruk ne Ma..." Ture ta Mama tayi daga jikinta tana kallonta galala sannan tace "Wa kika ce? Wane Faruk d'in?" Cikin kuka tace "Na nan gidan, naji ance aure zaiyi, ni na yarda ya had'a mu ya auremu tare da wadda yake so..." Buge mata baki Mama tayi hakan yayi sanadiyar katsewar maganar tata, ta dafa wurin tana cigaba da kuka. "Lallai yarinyar nan ashe bakida mutunci? Kawai sai a shiga hak'kin yaro babu dalili? Shi baice yana sonki ba haka kawai sai a takura masa, to wallahi ahir d'inki! Kar na kuma jin magana makamanciyar wannan a nan gidan, tun wuri ki fitar da Faruk daga ranki kinji na gaya miki, ashe bakida wayau bansani ba? Tashi ni ki bani wuri." Da gudu ta fice tana kuka, tsakanin d'a da mahaifi kuma sai Allah, take tausayin Jidda ya kamata don haka sai tabi bayanta. Rarrashinta ta shiga yi da nasiha, har ta samu tayi shiru, nan dai tayi ta kwantar mata da hankali cikin hikima da dabara. *** Ranar Juma'a magabatan Faruk suka gabatar da komai na auren d'annasu. Duk wata dukiya da ake buk'ata ta aure da kuma al'ada sun gabatar tare da sadakinsu. Bayan kammala komai aka saka bikin wata d'aya saboda Baba ya buk'aci hakan, don yace yafi so ta fara karatu a d'akin mijinta. Bayan Sati biyu da hakan kuma suka kawo lefe saitin akwati/jaka takwas da kit. Akwatinan sunyi kyau kalar purple. Yanzu bikin ya rage saura sati biyu kenan. To daga nan kuma aka cigaba da shirye shiryen biki, tun daga kan su dilka, gyaran gashi Baba ne yasa aka d'auko ta daga maiduguri mai suna Salima. Matar ta k'ware a gyaren jiki da gyaran amarya. Kwanan ta d'aya amma Meenah ta fara murjewa, ko wucewa tayi sai k'amshin jikinta ya bugo mutum. Kayan d'aki kuwa Baba daga dubai yasa akayi mata order, gado set biyu masu matuk'ar tsada da kyau, sai set d'in kujeru suma biyu, kayan dining da kitchen ma duka a can akayi order komai da komai. Don Baba a shirye yake don nuna ma Meenah gata. Hartta katin d'aurin aure daga dubai d'in aka bugo su, sheyasa ya fita daban ko kallon shi kayi kasan ya had'u! Tun ana saura sati d'aya bikin Baba ya tafi Katsina ya d'auko Goggo. Nan itama aka fara hidimar biki da ita. A 6angaren ango shima shiri sukeyi sosai, don su mutum hud'u ake ma biki, da Faruk da Najeeb da Yusra, sai Anisah, Nabeel da Jidda suka rage kasancewar basu fiddo wad'anda suke so ba. Don haka gidan ya kacame da hidima ba kad'an ba. Events d'in da Meenah zatayi kamu ne kawai tasa sai yinin biki, sai d'aurin aure sai walima sai kai amarya sai ango zasuyi dinner shikenan. Tun ana saura sati d'aya aka fara jere a unguwar Aso Villa, manyan gidaje ne jere guda uku amma kowa da katangarsa haka ma kowa da gate d'insa, babban gida ne ba laifi don yana da wadatar fili, gidan dai yaji shuka banda carpet grass dake shimfid'e a k'asa, ginin zamani mai d'auke da parlor biyu, d'akuna uku, kitchen da dinning. Gidan yayi sai dai fatan Allah basu zaman lafiya! Ranar laraba ta kama ranar da ake ma Meenah k'unshi, nan fa aka zauna daga can garden aka shiga yaryara mata k'unshi. Sai wata kuma daban tana ma 'yan matan amarya da sauransu. Ranar alhamis ranar da ake kamu k'arfe hud'u za'a fara a gama k'arfe shidda. Amarya tayi shiri cikin ja da silver bridal gown wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau! A yayinda da Zarah suke sanye cikin ashobi pink da black. Bayan an gama shiri aka rufe mata fuska suka tafi wurin kamu. Nan kuma aka shiga gabatar da kamun yadda ya kamata, tun a wurin kuma Nabeel yake ma Zarah wani irin kallon da har sai da ta tsargu, shikam tunda ya ganta yaji ta masa. Anyi taro lafiya, ansha hotuna. K'arfe shidda daidai aka kammala aka watse. Bilki anata fama da jama'a, 'yan uwa, mak'ota, abokan arzik'i, 'yan cin arzik'i, da kuma k'awayenta don haka ko tana cikin 6acin rai ma bazaka gane ba. Hidima tasha kanta, gidanta a cike yake taf ba matsaka tsinke. Hartta dai Hajiya Laila da d'iyarta sunzo tun ana saura kwana biyu bikin. Nabeel dai ya kasa hak'uri ya sanar da Najeeb yana son k'anwar Meenah, aiko yaji dad'in haka. Don haka ya sanar da Faruk, Faruk ya sanar da Meenah ita kuma Meenah ta tuntu6i 'yar uwarta taji ta bakinta. Batayi saurin amincewa ba sai daga baya, take kuwa suka kar6i number juna yanzu har sun fara gaisawa ta waya! Ranar juma'a cikin garin Abuja dubban mutane suka shaida auren FARUK ADAM DA AMINATU HAMZA, NAJEEB DA ANISAH, YUSRA DA SADIQ. Daga nan angwaye suka zarce walima a guest house d'in Dada dake can Asokoro. Washe gari akayi wunin biki, tun safe jikin Meenah ya fara yin sanyi kuma, ko abinci tak'i ci, jinta take kamar wata marar lafiya. Gashi Bilki bata damu ba bare kuma ta tilasta mata taci. Zarah keta lalla6a ta har dai ta samu tasha ruwan tea. Haka aka cigaba da gudanar da wunin biki cike da kwanciyar hankali. K'arfe takwas na dare motocin d'aukar amarya suka iso. Tun a sannan Meenah ta fara kuka, tun tana ganin zata rabu da 'yar uwarta sai kuma hankalinta ya tashi sosai. Take suka rungume juna suna ta kuka mai ban tausayi. Da k'yar wata daga dangin Faruk ta janyota, bayan an kaita parlon Baba take kuma ta fara sabon kuka, shi kansa Baban idanunsa sunyi ja, su Goggo da Bilkin duk suna zaune a wurin, nan aka shiga mata nasiha mai ratsa jini da jijiyoyi, kuka kawai take, suka sassaka mata albarka da fatan zaman lafiya, sannan aka jawo ta wajen mota ana ta rangad'a mata gud'a. A kan hanyarsu ta zuwa hankalin Meenah yayi matuk'ar tashi, tunda zataje inda bata sani ba, bata ta6a rayuwa a ciki ba, zuwa cikin rukunin sabuwar rayuwa mai cike da garari, dad'i ko akasin haka.... AUREN FANSA 26 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹26 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan an kawo amarya masu ganin gida suka gama gani tare da fatan alkhairi, sai kuma suka soma tafiya, nan kuma aka bar 'yan matan amarya wad'anda zasu kwana saboda gobe walima. Haka kuwa akayi washe gari aka gudanar da walima, aka k'are lafiya, bayan an gama aka maido amare gidanjensu, nan kuma su Zarah suka taya ta zama har dare haka sukayi jugum babu mai cewa uffan. K'arfe takwas, tara, goma har da rabi shiru babu ango babu alamarshi. Ganin sha d'aya saura yasa Zarah cewa. Gaskiya nikam na gaji da zaman jiran ango Meenah." D'aya daga cikin cousins d'in su Meenah mai suna Khadija tace "Abinda za'ayi ko idan sunzo ki kar6a mana kud'inmu zan dawo gobe in amsa har ma da sauran kazar da kuka rage ta amarci." Wannan karon Zarah bata tanka ba don takaicin rashin zuwan ango akan lokaci, haka sukayi ta mata bankwana suka bar gidan. Tayi shiru tana tunanin abinda ya hana shi zuwa har wannan lokacin, tayi tagumi. Har kusan sha biyu saura shiru, ta gaji ta yaye lullu6in tayi zaune ta zurfafa cikin tunanin babu ango babu alamarshi. Gyangyad'i ta fara yi tun tana yi sama sama har ta kusa 6ingirewa k'asa. A tunaninta idan ta farka zata ganshi kan gadonta sai dai wayam ta ganta ita kad'ai. Ta mik'e ta sauya kayan bacci ta duba agogo k'arfe 1:36am. Ta koma kan gadon ta kwanta cike da fargaba, sai kuma ta mik'e tana tunanin ko lafiyarsa k'alau don abin ya fara bata tsoro. Wayarta ta d'auko ta kirasa amma abin mamaki wayarsa a kashe! Ta dafe k'irji tare da d'ora kanta bisa pillow tayi lamo. Can bacci 6arawo ya sace ta, a tunaninta zata farka ta ganshi ya dawo amma abin mamaki babu alamarshi. Ta duba agogo 4:50am, a sanyaye ta shiga toilet ta d'auro alwala tayi sallah. Sai da gari ya d'an fara haske ta fito don ta duba ina angonnata kuma taji dalilin da ya hanashi zuwa da daddare. Bata san kan gidan ba haka tayi ta shiga tana fita amma ba alamun mutum a gidan. Ta cika da tsoro haka ta koma d'akinta tana tunanin ko ba'a gidan ya kwana ba? Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin ash material doguwar riga ta d'aura d'ankwalin kayan ta hau gado ta kwanta tare da lumshe idanu tana k'ok'arin tunanin meya faru da angonta haka har ya hana shi zuwa gareta duk da kuwa yana zakwad'in zuwan wannan rana. K'arfe sha d'aya aka soma bubbuga gidan, ta mik'e ta fito har bakin k'ofa tare bud'ewa. "Ina kwana?" Ta fad'a gami da kawar da fuskarta gefe. "Lafiya lau, Bismillah." Bata tanka ba kawai tabi ta gefenta ta wuce tana k'ok'arin had'iye kishinta. Parlor suka zauna sannan tace "Sunana Jidda, ni k'anwar Faruk ce abinci ne aka bada a kawo muku daga gida." Ta fad'a tana matsar mata da kwandon gabanta. Meenah tayi murmushi "Allah sarki, mungode Allah saka da alkhairi." Tayi yak'e tace "Babu komai, ina yayan ko bai tashi ba?" Ta hau inda inda. "Eh... a'a ya tashi ya shiga wanka." Jidda ta sunkuyar da kanta k'asa tace "Allah sarki ni zan wuce ki gaishe shi idan ya fito." Meenah tayi murmushi tace "Zaiji insha Allah a gaida Mama." "Zataji." Ta fice. Bud'e kular ta soma yi, soyayyar doya ce da k'wai da pepper soup sai k'osai da kunu. Kasa cin abincin tayi don rashin zuwan Faruk gareta ya mata zafi duk da kuwa har yanzu batasan dalilin rashin zuwan nasa ba. Bata buk'atar komai a halin yanzu sai son ganin Faruk da kuma son jin dalilin da ya hana shi zuwa. Ganin tunanin bazai mata ba yasa ta jawo kular abincin ta soma ci, kasa ci ma tayi sai kawai ta zuba kunun tasha ta koma kan gado. Wayarta ta d'auko ta k'ara kiransa wannan karon a kunne taji ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba. k'walla suka cika mata ido, lallai al'amarin mai girma ne. Sai da tayi kwana biyu a na ukkun ne taji alamar shigowar mota, da sauri ta lek'a shi d'inne yana sanye da suit kalar toka da wando kalar tokar shima. K'in fitowa tayi don tana tsananin fushi da shi. Tana zaune taji alamun bud'e k'ofa, da alama d'akinsa ya shiga. Sai da ya d'auki akalla minti talatin sannan taji alamun fitowa, da sauri ta kwanta gami da rufe idonta kamar mai bacci. Bud'e k'ofar d'akin yayi yana tsaye yana k'are mata kallo, daurewa yayi ya tako har bakin gadon gami da zama kusa da ita. "My baby..." Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa. Kamo hannuwanta yayi yana murza su a hankali cikin salo na k'warewa, bugun k'irjinta ya k'aru. "Haba my baby shirunki yana iya haifar min da matsala babba idan baki amsa ni ba, kinji my baby please ki tashi kiji abinda zan fad'a miki." Tsananin son da take masa shi ya hana ta yi masa musu, tashi zaune tayi fuskarta kuwa kamar an mata albishir da gidan wuta. "Nasan ban kyauta miki ba, amma kiyi hak'uri babban dalili ne yasa kika ga ban zo ba a ranar da aka kawo ki..." Ta kalle shi idanunta cike da kwalla tace "Wane dalili ne ya hana ka zuwa? Wane dalili ne ya hanaka zuwa gareni duk da kuwa yadda kake zakwad'in zuwan wannan rana! Wane dalili ne yasa ka mance dani har kak'i d'aukar wayata a lokacin da nake nemanka? Wane dalili ne yasa a daren da aka kawo ni ka mance dani ka maida ni dani da bola duk d'aya suke a wurinka? Wane dalili ne ya hanaka kwana a gidanka ranar dana fara takowa a gidanka? Wane dalili ne...?" Toshe mata baki yayi da hannunsa yana girgiza mata kai, take hawayen da take rik'ewa suka yi nasarar saukowa, sannan ta bishi da kallo na ina jiran amsa. "Don Allah ya isa haka my baby, wallahi ba laifina bane, Dada ne bashida lafiya dole tasa muka tafi wurinsa..." Ta girgiza kanta. "Dada bashida lafiya meyasa da jidda tazo rannan da safe ta kasa sanar dani hakan, har tambayarka tayi ko kana ciki? Ta yaya mahaifinta bashi da lafiya ta kasa sani?" Take ya hau inda inda. "Eh ay ko ita kanta bata sani ba saboda bata gidan, amma banyi tsammani zaki zarge ni da yin k'arya ba Meenah." Ya k'arasa yana k'ak'alo hawaye. Hankalinta ya tashi tace "Ko kusa ba haka bane, na yarda da kai my soul, amma ka gane duk abinda ya shafe ka nima ya shafe ni, daka sanar dani ko addu'a dana yi masa, Allah ya bashi lafiya." Yayi murmushi "Yawwa my baby ko kefa? To yi murmushi mana." Ya fad'a cike da shagwa6a, hakan ya bata dariya sosai. Kamo ta yayi yana fad'in. "Zo muje na siyo maki abin dad'i." Tayi murmushi suka fice. *** Da misalin k'arfe 8:35pm yayi sallama, Dada na aiki a laptop nasa ya dakata gami da amsa sallamar sannan yayi murmushi. "Ahh Faruk kaine tafe? Shigo mana." Faruk ya shigo bayan ya zauna yace "Dada an wuni lafiya?" Yace "Lafiya lau ya iyalin naka da fatan tana lafiya?" Yace "Lafiya lau Dada daman wurinka nazo." Ya dube shi kafin ya cire gilashin dake idonsa na karatu yace "To gani lafiya dai?" Faruk ya sunkuyar da kai tukunna yace. "Dada daman so nake na nemi izini wurinka zan k'ara aure." A razane Dada ya dube shi gami da gyara zama yace "Aure fa kace Faruk? Aurenku da ko sati ba'ayi ba sai kace zaka k'ara aure? Kaima kasan hakan bazai yiwu ba. Tukunna ma wacece zaka aura?" Ya sukuyar da kai "Dada daman Jidda ce..." "Ban lamunta ba! Idan ma mafarki kakeyi to ka farka!" Mama ta fad'a tana tsaye a bakin k'ofa daga ganinta kasan tana cikin 6acin rai. MSB💖 AUREN FANSA 27 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Hip!!!hip!!!hipp!!! Hurray!!!!!!! Wishing u long life in Islam and prosperity Faridat Allah k'aro shekaru masu albarka ya kuma k'ara basira da hazak'a Amin💃🏻💃🏻💃🏻😍😍 🌹27🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Gaba d'aya suka dube ta sadda take k'arasowa cikin parlon tare da zama gefen Dada sannan ta d'ora. "A gaskiya Alhaji banga amfanin aurensa ba duka duka yaushe akayi aurennan da zai bijiro mana da zancen wani auren kuma? Haba me kake so duniya tace mana? Ko sati d'aya fa bakuyi ba da aure haba Faruk ka bani mamaki, me tayi maka? Me ta tsare maka? Yarinya salihar baiwar Allah zaka ce zakayi ma kishiya daga yin aure yanzu? To a gaskiya ban lamunta ba Alhaji, ya sake lala." Dada bai ce uffan ba yana dai ta kallon Mama tana zuba har sai data gama sannan ya numfasa yace "Wai da kike ta wad'annan maganganun kece zaki zauna masa dasu ne? Bashi yace yaji ya gani ba? Ba wanda ya masa dole ay, kuma ni bazan iya hanasa yin aure ba, amma abinda nakeso ka sani Faruk shine kasan shi aure ba abin wasa bane, sannan kuma kaji tsoron Allah idan har kayi aurennan tofa dole sai kayi adalci a tsakaninsu, idan kuwa bazakayi adalci ba gaskiya ban yarda ka sake aure ba kuma bada yawu na ba, sannan magana ta k'arshe sai na tuntu6i ita Jiddar naji ta bakinta tukunna..." "Ay Alhaji kar ma ka 6ata lokacin ka saboda Jidda ta dad'e da ciwon son Faruk a cikin ranta, don ma ina kwa6ar ta ay da tuni ta sanar maka tana sonsa, sai dai Alhaji dole fa sai mun tashi tsaye kasan halin Jidda bata jin magana ina gudun kar taje tasa d'iyar mutane a gaba kaga babu dad'i hakan." Dada yace "Haka ne, Faruk a gaskiya sai ka tsawatar ma Jidda sosai saboda duk wani abin tashin hankali ta guje shi, idan kuwa bazata iya kiyaya ba to a fasa auren. Hajiya kira min Jidda tazo ina nemanta." "To Alhaji." Bayan fitar Mama Dada yace "Ina fatan ka sanar da ita Aminar batun k'ara aurenka? Kuma ta yarda ta amince da hakan?" Yayi shiru, Dada ya ce "Alamu sun nuna min cewa baka sanar da ita ba Faruk, to a gaskiya idan kaga ka auri Jidda sai da amincewar Amina, don haka kaje ka nemi shawarar matarka." To kawai ya iya cewa ya mik'e, a daidai bakin k'ofa sukayi kaci6us dasu Jidda zasu shigo, bai tanka mata ba yasa kai ya fice, bayan sun shigo Dada ya soma magana. "Jidda Faruk ne ya zo mana da wani zance wai yana son auren ki..." Bai k'arasa ba ta mik'e cike da murna tace "Dada? Da gaske kakeyi ko wasa? Da gaske Faruk zai aure ni? Mama da gaske kukeyi don Allah?" "Ke meye haka wai!"? Dada ya daka mata tsawa, zama tayi tana ta murna a yayinda Dada ya cigaba "Kinga Jidda ki nutsu ki saurare ni da kunnen basira, kamar yadda na fad'a miki Faruk yazo man da zancen aurenki, amma inaso kisani kiji tsoron Allah Jidda, kar ki cutar da d'iyar mutane kinsan dai Allah na kallonki, sannan duk wani abin da zakiyi da bai kamata ba na samu labari to ki sani k'arshen zamanki gidan Faruk yazo kenan, don haka ki kama kanki. Hajiya kisa ido akanta sosai, tashi ki tafi." Da gudu ta fice tana zuwa d'akinta ta fad'a kan gado cike da murna, har ma ta fara imagining wai gata can

Chapter 10 of 11