Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels AUREN FANSA 01 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _AUREN FANSA_!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM! Wannan shafin tukuci ne gareku members na pure moment...! FATY AXLAND SUHANA JANNART, AUNTY KHADY, HUSNAH, DEEJA WAZIRI, ZEE YABOUR, UMMUHANEEF, MOMYN SULTAN, UMMYN YUSRAH, ZARAH SURBAJO, MOMYN KHADIJA, UMMA YAHYA MUSA (SISIN MAMA), BIEBIE DEE, NANA FA'AD, FAtY MANSUR (XARAH), FATY KHALID NA SHUKA, SHAFA ABDUL, SUMYNBASH, SALMA ALI WADA, ROOKY KAZ, AISHA ALI GARKUWA, UMMI HAMBALI, UMMEE GARKUWA, RUFAIDA YUSUF, HAFSAT MUSA, SADNAF, FHARIEEDAT, RAFEE'AT, SAMRAH, BIBA WADATA, SEEMALUV, NEERATU LUV, AYSHA HANWA, AYSHA GANA, UMMU SAFWAN, DELU CHOGAL, MRS FAWWAZ (YESMEN TAFEESU), RAFI'AT DIKKO, MAMAN IHISAN.❤️💖🌹 🌹01 🌹 Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka, don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka fuskarta ta kanyi ja. A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance tana kukan fitar rai. A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin wata irin sigar rarrashi. "Hajiya Bilki." Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata. A hankali ya soma magana. "Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki wallahi." Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma zuciyarsa ta raunana! Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana cikin 6acin rai. "Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata mujiya haba!" Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana. "Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai kin samu haihuwa zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya baki kyau, arzik'i ya wadata ki da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?" Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya cigaba da magana. "Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa sannan ki rok'e sa gafara da rahama. Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi. Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o, kina jina?" Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na manya yace. "Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa nakeji." Ta6e baki tayi tace "Kayi hak'uri na manta ban girka ba." Yayi murmushi yace "Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?" Tace "Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya kamata ka barni na huta mana." Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi murmushi yace "Haka ne Allah ya baki lafiya." "Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki. D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci ya sace sa. Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm, zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah, bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya, kiranta yayi a hankali. "Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana fusakarsa ba annuri ko kad'an. "Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi sallah?" Tace "Kayi hak'uri na manta ne." Girgiza kansa yayi yace "Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo." Ko kallonsa batayi ba tace "To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama mana." Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar nauyi ya fice daga gidan. Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen da kullum baya son shi. "Ya maganar aure Hamza?" Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa dai na k'asa. AUREN FANSA 02 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee💘 🌹02 🌹 "Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma bakada shi babu damuwa." Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole yace. "Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan zan zo na sanar dake." Murmushi tayi tace "Allah ya nuna mana." Yace "Amin." Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare, gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito parlor. Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani American series, jin alamun shigowa yasa ta kalleshi lokaci guda kuma tace "Har ka dawo?" Yace "Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa. Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse shirun nasu "Hamza, wai ya maganar mu ne?" Yace "Wace magana kenan?" Ta zum6uro baki tace "Ba dai har ka manta ba?" Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce tana son kud'i. Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da shagwa6a tace "Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro kaya." Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi yace "Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa basai ki bata ba ta kawo maki." Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi don haka sai tace "Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in nawa zaka bani?" Yace "Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai na k'ara maki." Da sauri ta tashi zaune "Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an." A fusace ya tashi tsaye yace "Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana, ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki." Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan don ya fusata. Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci. K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi. Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji yunwa sai yaci kawai. A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa musulmai. Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin. Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a hankali ya ture ta yace "Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi." Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa. Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da kwarkwasa. Can kuma tace "Alhaji." Bai kalle ta ba yace "Na'am." Tace "Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..." Da sauri yace "Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?" Murmushi tayi tace "Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka huta sai muyi magana." Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don yaga lokacin sallar magriba ta gabato. *** "Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin makekiyar kujera tana duba magazine da glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace. "Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?" Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana murmushi, sannan kuma yace. "Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya lashe baki gaba d'aya wato overall as always." Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi. Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk sosai a jikinta tace "That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka ta mussaman." Cike da jin dad'i Faruk yace "Allah Mummy?" Tace "Kayi ka gani I promise." Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace. "My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo muci abinci." Faruk yace "Ok Daddy." Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa. Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna Adam tace "Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?" Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara fizgarsa sannan yace "Muje sahibata." Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna... AUREN FANSA 03 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to my darling Maman Ihsan (SAFNA) much love darl💕💘❣️ 🌹03 🌹 *** Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi 6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma cikin d'aki tsabar borin kunya. Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren akHTTP/1.1 200 OK Content-Type: applicatioin/OCTET-STREAM;charset=utf-8 Content-Disposition: attachment;filename="AUREN+FANSA+CMPLT+BY+09063626602.txt" Content-Length: 301602 Server: Jetty(i-jetty 1.4.1129.gionee) AUREN FANSA 01 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _AUREN FANSA_!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM! Wannan shafin tukuci ne gareku members na pure moment...! FATY AXLAND SUHANA JANNART, AUNTY KHADY, HUSNAH, DEEJA WAZIRI, ZEE YABOUR, UMMUHANEEF, MOMYN SULTAN, UMMYN YUSRAH, ZARAH SURBAJO, MOMYN KHADIJA, UMMA YAHYA MUSA (SISIN MAMA), BIEBIE DEE, NANA FA'AD, FAtY MANSUR (XARAH), FATY KHALID NA SHUKA, SHAFA ABDUL, SUMYNBASH, SALMA ALI WADA, ROOKY KAZ, AISHA ALI GARKUWA, UMMI HAMBALI, UMMEE GARKUWA, RUFAIDA YUSUF, HAFSAT MUSA, SADNAF, FHARIEEDAT, RAFEE'AT, SAMRAH, BIBA WADATA, SEEMALUV, NEERATU LUV, AYSHA HANWA, AYSHA GANA, UMMU SAFWAN, DELU CHOGAL, MRS FAWWAZ (YESMEN TAFEESU), RAFI'AT DIKKO, MAMAN IHISAN.❤️💖🌹 🌹01 🌹 Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka, don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka fuskarta ta kanyi ja. A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance tana kukan fitar rai. A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin wata irin sigar rarrashi. "Hajiya Bilki." Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata. A hankali ya soma magana. "Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki wallahi." Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma zuciyarsa ta raunana! Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana cikin 6acin rai. "Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata mujiya haba!" Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana. "Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai kin samu haihuwa zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya baki kyau, arzik'i ya wadata ki da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?" Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya cigaba da magana. "Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa sannan ki rok'e sa gafara da rahama. Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi. Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o, kina jina?" Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na manya yace. "Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa nakeji." Ta6e baki tayi tace "Kayi hak'uri na manta ban girka ba." Yayi murmushi yace "Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?" Tace "Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya kamata ka barni na huta mana." Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi murmushi yace "Haka ne Allah ya baki lafiya." "Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki. D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci ya sace sa. Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm, zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah, bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya, kiranta yayi a hankali. "Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana fusakarsa ba annuri ko kad'an. "Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi sallah?" Tace "Kayi hak'uri na manta ne." Girgiza kansa yayi yace "Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo." Ko kallonsa batayi ba tace "To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama mana." Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar nauyi ya fice daga gidan. Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen da kullum baya son shi. "Ya maganar aure Hamza?" Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa dai na k'asa. AUREN FANSA 02 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee💘 🌹02 🌹 "Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma bakada shi babu damuwa." Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole yace. "Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan zan zo na sanar dake." Murmushi tayi tace "Allah ya nuna mana." Yace "Amin." Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare, gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito parlor. Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani American series, jin alamun shigowa yasa ta kalleshi lokaci guda kuma tace "Har ka dawo?" Yace "Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa. Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse shirun nasu "Hamza, wai ya maganar mu ne?" Yace "Wace magana kenan?" Ta zum6uro baki tace "Ba dai har ka manta ba?" Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce tana son kud'i. Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da shagwa6a tace "Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro kaya." Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi yace "Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa basai ki bata ba ta kawo maki." Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi don haka sai tace "Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in nawa zaka bani?" Yace "Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai na k'ara maki." Da sauri ta tashi zaune "Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an." A fusace ya tashi tsaye yace "Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana, ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki." Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan don ya fusata. Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci. K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi. Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji yunwa sai yaci kawai. A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa musulmai. Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin. Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a hankali ya ture ta yace "Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi." Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa. Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da kwarkwasa. Can kuma tace "Alhaji." Bai kalle ta ba yace "Na'am." Tace "Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine nake so ka bani kud'i

Chapter 1 of 11