Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar anyi ne an gama." Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in "Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe ta!!!" AUREN FANSA 04 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to my Zarah Surbajo and Sadnaf💘❤️💘 🌹04 🌹 Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi kan gadonsa yana mai maida numfashi sama sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki bata yi mata ba, batada kamun kai ga shegen yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an zata sa masa kuka. Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin, wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace "Hamza kana ina yanzu?" Yace "Inagida Goggo, lafiya dai ko?" Tace "Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza, kayi sauri don Allah." A rud'e yace "Gani nan yanzu wace asibiti ce?" Tace "Alheri clinic kayi sauri." "To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin, takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo. Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin kuka tana fad'in "Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan fad'a maka." Jikinsa yayi sanyi yace "Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..." "Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!" Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka sai yace "Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan." Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take "Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min alk'awari na k'arshe." Da sauri ya kalleta "Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana." Girgiza kanta tayi tana hawaye "Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin kawai." Goggo ce ta sa baki tace "Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata alk'awarin a shiga da ita." Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace "Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki lafiya." Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata yin mumushi ba, sannan tace "Nagode ya Hamza nagode!" Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu aka raba su da k'yar." Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru. Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri suka fara murna suna hamdala. Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa "Alhamdulillah! Ta haihu lafiya." Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana murmushi sosai. Nurse d'in ce tace "Ta haifi mace." "Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa. Kafin kuma Goggo tace "Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu shiga?" Nurse d'in ce tace "Sai dai kuyi hak'uri..." "Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace "Bamu gane abinda kike cewa ba." Nurse d'in tace "Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga mahaliccinmu." Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta sukayi ta zauna da sauri. Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro. "Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke kuka rungume da babyn. Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka 6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin doguwar ambulance. Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi. Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa. Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida. Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin sakata a makwancinta. Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa. Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata damuwa ba. A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki, inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar. Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace, Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin thumma Amin. AUREN FANSA 05 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to mairo😜 aka Maryam Gafai I heart you sis❤️ and my sisi Ammin SS 😘😘😘 🌹05 🌹 BAYAN KWANA BIYU Ranar suna yarinya taci sunan mamanta marigayiya Amina, daman bawani taron sunaHTTP/1.1 200 OK Content-Type: applicatioin/OCTET-STREAM;charset=utf-8 Content-Disposition: attachment;filename="AUREN+FANSA+CMPLT+BY+09063626602.txt" Content-Length: 301602 Server: Jetty(i-jetty 1.4.1129.gionee) AUREN FANSA 01 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _AUREN FANSA_!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM! Wannan shafin tukuci ne gareku members na pure moment...! FATY AXLAND SUHANA JANNART, AUNTY KHADY, HUSNAH, DEEJA WAZIRI, ZEE YABOUR, UMMUHANEEF, MOMYN SULTAN, UMMYN YUSRAH, ZARAH SURBAJO, MOMYN KHADIJA, UMMA YAHYA MUSA (SISIN MAMA), BIEBIE DEE, NANA FA'AD, FAtY MANSUR (XARAH), FATY KHALID NA SHUKA, SHAFA ABDUL, SUMYNBASH, SALMA ALI WADA, ROOKY KAZ, AISHA ALI GARKUWA, UMMI HAMBALI, UMMEE GARKUWA, RUFAIDA YUSUF, HAFSAT MUSA, SADNAF, FHARIEEDAT, RAFEE'AT, SAMRAH, BIBA WADATA, SEEMALUV, NEERATU LUV, AYSHA HANWA, AYSHA GANA, UMMU SAFWAN, DELU CHOGAL, MRS FAWWAZ (YESMEN TAFEESU), RAFI'AT DIKKO, MAMAN IHISAN.❤️💖🌹 🌹01 🌹 Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka, don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka fuskarta ta kanyi ja. A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance tana kukan fitar rai. A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin wata irin sigar rarrashi. "Hajiya Bilki." Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata. A hankali ya soma magana. "Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki wallahi." Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma zuciyarsa ta raunana! Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana cikin 6acin rai. "Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata mujiya haba!" Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana. "Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai kin samu haihuwa zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya baki kyau, arzik'i ya wadata ki da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?" Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya cigaba da magana. "Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa sannan ki rok'e sa gafara da rahama. Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi. Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o, kina jina?" Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na manya yace. "Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa nakeji." Ta6e baki tayi tace "Kayi hak'uri na manta ban girka ba." Yayi murmushi yace "Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?" Tace "Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya kamata ka barni na huta mana." Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi murmushi yace "Haka ne Allah ya baki lafiya." "Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki. D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci ya sace sa. Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm, zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah, bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya, kiranta yayi a hankali. "Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana fusakarsa ba annuri ko kad'an. "Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi sallah?" Tace "Kayi hak'uri na manta ne." Girgiza kansa yayi yace "Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo." Ko kallonsa batayi ba tace "To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama mana." Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar nauyi ya fice daga gidan. Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen da kullum baya son shi. "Ya maganar aure Hamza?" Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa dai na k'asa. AUREN FANSA 02 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee💘 🌹02 🌹 "Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma bakada shi babu damuwa." Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole yace. "Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan zan zo na sanar dake." Murmushi tayi tace "Allah ya nuna mana." Yace "Amin." Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare, gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito parlor. Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani American series, jin alamun shigowa yasa ta kalleshi lokaci guda kuma tace "Har ka dawo?" Yace "Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa. Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse shirun nasu "Hamza, wai ya maganar mu ne?" Yace "Wace magana kenan?" Ta zum6uro baki tace "Ba dai har ka manta ba?" Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce tana son kud'i. Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da shagwa6a tace "Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro kaya." Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi yace "Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa basai ki bata ba ta kawo maki." Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi don haka sai tace "Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in nawa zaka bani?" Yace "Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai na k'ara maki." Da sauri ta tashi zaune "Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an." A fusace ya tashi tsaye yace "Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana, ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki." Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan don ya fusata. Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci. K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi. Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji yunwa sai yaci kawai. A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa musulmai. Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin. Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a hankali ya ture ta yace "Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi." Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa. Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da kwarkwasa. Can kuma tace "Alhaji." Bai kalle ta ba yace "Na'am." Tace "Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..." Da sauri yace "Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?" Murmushi tayi tace "Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka huta sai muyi magana." Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don yaga lokacin sallar magriba ta gabato. *** "Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin makekiyar kujera tana duba magazine da glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace. "Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?" Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana murmushi, sannan kuma yace. "Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya lashe baki gaba d'aya wato overall as always." Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi. Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk sosai a jikinta tace "That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka ta mussaman." Cike da jin dad'i Faruk yace "Allah Mummy?" Tace "Kayi ka gani I promise." Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace. "My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo muci abinci." Faruk yace "Ok Daddy." Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa. Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna Adam tace "Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?" Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara fizgarsa sannan yace "Muje sahibata." Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna... AUREN FANSA 03 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to my darling Maman Ihsan (SAFNA) much love darl💕💘❣️ 🌹03 🌹 *** Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi 6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma cikin d'aki tsabar borin kunya. Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka amsa sannan tace. "Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?" Sai da yayi murmushi sannan yace "Lafiya lau Amina ya gida?" "Alhamdulillah, ya Anty Bilki?" "Tana nan lafiya ya zafi kuma?" "Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?" Yace "Alhamdulillah ya jiki kuma?" Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace "Alhamdulillah gashi nan muna ta fama." Dariya yayi yace "To Allah ya raba lafiya." Tace "Amin." Sannan ta kuma cewa "Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan na baka shi ka rik'a..." "Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai ki dinga kawo min shi hutu." Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace "Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu." Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici yace "Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har ma ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu haka ba dad'in ji." Tayi dariya "Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?" Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora "Naji shikenan are you happy now?" "Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!" Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann ya kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata tambaya "Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike buk'ata?" Tace "Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na bata." Yace "Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a siya." Tace "Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i." Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da d'an uwanshi. Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya, bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan ta haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya. Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba. Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa, bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke cikin garin Katsina a G.R.A. Wannan kenan! *** BAYAN 'YAN KWANAKI Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki tace. "Hamza zan fita." Ya kalleta da mamaki yace "Ina zakije?" Ta had'e rai "Gidan Hajiya Laila." Shima ya had'e rai "Ba inda zakije." Ta mik'e zumbur! "Me kace?" Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa masifa "Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai! Kuma ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta taka duk ta zuge ka." Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa "Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu saboda babu ruwanta, kina ji na?" "Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi." Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace "Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in magana makamancin wannan a bakin aurenki!" Ta zaro idanu waje "Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu kayi baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i gaskiya shikenan kaje Allah zai saka min." Yace "Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To mugani idan kin isa!" Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo. "Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara na gaji da zama da mace irinki wadda batasan inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure." A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura taga nama. "Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni kad'ai ce babu k'ari!" Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on da tayi masa sannan yace "Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar anyi ne an gama." Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in "Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe ta!!!" AUREN FANSA 04 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to my Zarah Surbajo and Sadnaf💘❤️💘 🌹04 🌹 Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi kan gadonsa yana mai maida numfashi sama sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki bata yi mata ba, batada

Chapter 3 of 11