Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamun kai ga shegen yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an zata sa masa kuka. Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin, wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace "Hamza kana ina yanzu?" Yace "Inagida Goggo, lafiya dai ko?" Tace "Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza, kayi sauri don Allah." A rud'e yace "Gani nan yanzu wace asibiti ce?" Tace "Alheri clinic kayi sauri." "To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin, takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo. Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin kuka tana fad'in "Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan fad'a maka." Jikinsa yayi sanyi yace "Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..." "Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!" Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka sai yace "Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan." Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take "Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min alk'awari na k'arshe." Da sauri ya kalleta "Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana." Girgiza kanta tayi tana hawaye "Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin kawai." Goggo ce ta sa baki tace "Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata alk'awarin a shiga da ita." Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace "Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki lafiya." Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata yin mumushi ba, sannan tace "Nagode ya Hamza nagode!" Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu aka raba su da k'yar." Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru. Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri suka fara murna suna hamdala. Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa "Alhamdulillah! Ta haihu lafiya." Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana murmushi sosai. Nurse d'in ce tace "Ta haifi mace." "Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa. Kafin kuma Goggo tace "Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu shiga?" Nurse d'in ce tace "Sai dai kuyi hak'uri..." "Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace "Bamu gane abinda kike cewa ba." Nurse d'in tace "Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga mahaliccinmu." Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta sukayi ta zauna da sauri. Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro. "Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke kuka rungume da babyn. Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka 6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin doguwar ambulance. Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi. Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa. Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida. Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin sakata a makwancinta. Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa. Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata damuwa ba. A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki, inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar. Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace, Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin thumma Amin. AUREN FANSA 05 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to mairo😜 aka Maryam Gafai I heart you sis❤️ and my sisi Ammin SS 😘😘😘 🌹05 🌹 BAYAN KWANA BIYU Ranar suna yarinya taci sunan mamanta marigayiya Amina, daman bawani taron sunan da akayi wane taro ma ana zaman makoki? Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji yunwa ko wani abin na damunta. Kammaninta sak na mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin nata ne lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba sa6anin marigayiya da take fara tas kamar yayanta Hamza amma Amina babyn ita ba fara bace tas, sai dai tana da kyau duk da batada hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas! Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20 cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki gidanta akan cewa tana son magana dasu. Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace "Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin haka, don haka yau na damk'a maka Amina a matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka rik'e ta bisa amana." Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace "Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya." Hamza yace "Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya taya mu rik'o." Goggo tace "Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar mata a ciki ake siya mata su pampers da su madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma tunda yanzu zata dawo hannunku da zama sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda kaga ya dace." Jiki a sanyaye Hamza yace "Insha Allah Goggo." Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin mota. Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar Amina kamar 'yar cikinta. Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e yake gwanin kyau. Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci, duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki nayi. Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama don haka sai ya yafe mata suka shirya. Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta da kuma an bata madara zata koma shikenan kuma sai asuba. Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin ba. Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da maganar k'arin aure. Duk sadda Hamza ke gida to Amina na hannunsa yana mata wasa, yana ce mata "Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta har sai tayi bacci. A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah yake ce mata idan yana mata wasa. Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta, ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai dad'a kyau takeyi kullum. Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum yana manne da ita especially weekends ranar da ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba, tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta taso cikin ingatacciyar rayuwa. Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki, Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi. Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda akayi ya kashe su. *** Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama. Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne. Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina nace to shi kuma son jirgi yake? Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta dafa shi. Juyowa yayi yana kallonta kafin yace. "Mummy na." Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan tace "Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a islamiyya?" Murmushi yayi yace "Nayi Mummy." Tace "Anya Faruk?" Yace "Allah yanzu na gama." Tace "Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta 'yar shekara uku) suna jiranmu." "Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi bayan Mummy.... MSB💖 AUREN FANSA 06 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹06 🌹 Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke zaune suna labari harda dariya, zama sukayi itada Faruk da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun ta hanyar jefo ma Daddy tambaya. "Daddy idan na girma me zan zama?" Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata yana kallon Anisah kafin kuma yace "Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama ay." Anisah tayi dariya "Ni banason na zama komai nafiso na shiga aljanna." Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta kafin kuma Mummy tace "Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?" Mummy tace "Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko sun fasa?" Daddy yayi murmushi "Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba cancanta kafin su bada, idan na dace a bani manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a ba za'a bashi." Tayi murmushi "Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a a dukkan lamuranka" Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba, abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace "Amin ya Allah Reemah." "Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in kuwa?" Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin yace "Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su Faruk sun gama exams a islamiyya." "Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?" Mummy tayi murmushi tace "Eh Mamana ko bazaki ba?" Anisah ta zum6ura baki "O'o ni zanje." Faruk yace "Kalle ta to baza'a dake ba." Anisha ta sa kuka "Daddy wai baza'a je dani ba?" Daddy yayi murmushi "Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu iya barinki ba." Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk yasa dariya. Anisah tasa kuka. "Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?" Mummy ta harari Faruk "Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin kukan k'anwarka ne?" Yayi dariya "Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata hak'uri ba?'' Ya buga k'afa. "Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab bazan bada ba." Daddy yace "Just say sorry Faruk, you know she won't stop crying unless you apologize." Mummy tace "Oya Faruk now!" "Ok sorry!" Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin abincinta kafin kuma ta kalli Daddy "Daddy zansha ice cream." Mummy tace "Me nace miki akan zak'i?" Anisah ta turo baki "O'o ni zansha." Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga mata hannu "Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream." Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana tsallen dad'i. Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace "Anisah kenan, badai rigima ba." Daddy yayi dariya "Lokacinta ne, kema kinyi naki ay." Mummy tace "Daddy Faruk fa na wurin." Yayi dariya "To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay" Da sauri ta tashi tana fad'in "Haba Daddy!" Yayi dariya "Kina tantama ne? Bari kiga..." Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya. Daddy ya tashi ya bi bayanta "Guduwa kikayi Reemah!" Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin ransa yace "Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely family!" *** Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki dake zaune saman kujera tana shan rake tana kallon wani movie da take so kukan Meenah ya cika mata kunne. Tsawa ta daka mata "Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen kuka haba!" Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya kwashe ta a nan. Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da zama kan kujera tana rirriga ta. Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki ta kalle shi "Sannu da zuwa Alhaji." Yana murmushi yace "Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?" Tayi murmushi "Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga ta tayi bacci." Yayi murmushi "Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai baccin takeji daman." Tayi yak'e "Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada rigima." Yace "Hakane Allah ya raya mana ita." Tace "Amin." Yace "Bari naje na watsa ruwa na gaji." Tace "Ok sai ka fito." Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a d'akin Meenah d'in kan gado. Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace "Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar da kikeyi. Allah ya baki lada." Ta kalli Alhaji tace "Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine, kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina ba." Yayi murmushin jin dad'i "Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na yaba da k'ok'arinki." Tayi dariya "Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da pampers sun k'are shine nace ya kamata a bad a siyo mata wasu." Yace "Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison madarar ma akan abinci." Tace "Hakane." Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma ya bata. Amsa tayi tace "Shikenan zanje na siyo mata. Yace "Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana." Da sauri tace "Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake gida kullum ka bari zan siyo mata." Yayi murmushi "Toh shikenan." *** Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu. Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan, Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai k'oshin lafiya. Haka aka cigaba da zaman barka inda komai Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana tafiya daidai. Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna aka watse lafiya kowa ya koma gidansa.... AUREN FANSA 08 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Another page for my Ummi Aisha thanks for all the support and care one love dear💖Allah ya k'ara basira Amin🌹 🌹08 🌹 Laila ce ta cigaba da magana. "Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?" Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace "A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya mu chanza shawara dai." Laila tayi kwafa. "To sai akace mu zamu bisu mu aikata k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba, abinda nake nufi a nan shine..." Nan naga ta rad'a mata wata magana daga k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya. Bilki tana dariya tace "Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma ke shu'uma ce wallahi." Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai sannan tace "Kema haka." Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta tana kallon Laila tace "Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta." Laila tace "Yi sauri kuwa nima naji." Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake, saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu. Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah tace "Maama wunwa." Laila ta ta6e baki tace "Uban me tace?" Bilki tace "Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri." Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim! "Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila had'e da jan tsaki. Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta fashe da kuka. Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana tsaki sannan ta dire mata k'asa. "Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan ta fito daga kitchen d'in. Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta kammala sannan aka bata ruwa. A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da papered chicken sai had'ad'en salad. Wuraren uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi gida. Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma Meenah wanka ta bata abincin rana. Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar fira kafin a kira sallar magrib. Kasancewar Meenah batasan dawowar Baban nata ba, tana can d'aki tana wasa. Sai data fito, aiko tana ganin shi ta rugo da d'an gudunta ta zo kusa da shi tana fad'in "Dada!" Cike da jin dad'i Alhaji yace "D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan." Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai tace "Dada kaga Maama ta bije ni d'azu." Ya ware idanu "Me kikayi wa Maama ta bige ki?" Tayi shiru tana kallonsa can tace "Bakomai." Bilki ta taso tana dariya tace "Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga wanka nazo na iske ta tana zubar da madara, shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi dariya "Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko? Idan Maama tace a daina a daina kinji?" Ta gyad'a kai. Sai kuma yace "Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son cin abinci?" Tayi dariya tace "Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi mamaki sam batason ci na rasa dalili." Yace "To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba fad'a zatayi ba." Tace "To k'ila dai." Ya juyo da dubansa ga Meenah "Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?" Nan ma shiru. Yayi murmushi "Zaki sha ice cream?" Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji dad'i yace "Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo gida zan siyo maki harda biscuit ma." Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace "Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi sai na dawo." Tace "A dawo lafiya." Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da Meenah dake tsaye a tsorace gaban Bilki. Tana huci tace "Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan nan yake da yarinyar nan amma naga ba ruwanshi ma da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya a cikinka amma ka nuna son d'iyar wata? To da sake mts." Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana zare idanu. Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit sai ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara. Zarah kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya siya mata tunda yasan bata isa shan wad'annan kayan ba. Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna, ya bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye tas sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki. Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi. Bilki na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah. Can Alhaji yace "Ina Meenah tayi ne?" Tayi tsaki a ranta tace "Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma tunda bazata ci abinci ba." Tashi yayi yana fad'in "Ina zuwa." Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah. Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa da biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta. Murmushi yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan gado, ya gyara mata kwanciya sannan ya kashe fitilar ya fito. Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka. BAYAN KWANA BIYU Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo, tana d'auka Laila tafara magana "Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji Adam sun koma Abuja gaba d'aya." Da sauri Bilki tace "Haba dai? To yanzu ya kenan?" "Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji ne a gidan." Bilki tace "Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara." "To shikenan." Laila tace tare da katse kiran. Nan tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita. *** Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi shekara d'aya amma har yau sun rasa wata mafita. A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta iya saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta fito ga surutu ba abinda bata fad'i. Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin komai har ya fara zarginta... AUREN FANSA 09 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹09 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Haka kuwa akayi washe gari da safe Hamza da Bilki suka fita don saka Meenah a makaranta. Gobarau Academy itace makarantar da suka nufa, da zuwansu da komai basu wuce minti talatin ba aka kammala komai aka saka ta Pre nursery, duba da shekarunta kuma a k'a'idar makarantar idan yaro bai kai shekara 3 ba to baza'a saka shi nursery ba daman. Daman 'yan pre nursery ba'a saka musu uniform. A ranar aka barta makaranta kuma ko kuka batayi ba da su Hamza zasu tafi don ta samu abin wasa sai dad'i takeji. K'arfe 12 suke tashi don haka dole Bilki ke d'auko ta don Hamza na wurin aiki lokacin, ba yadda ta iya haka nan take hak'ura tana d'auko ta d'in. Haka rayuwar ta cigaba da

Chapter 4 of 11