Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gudana cikin hukunci da hikimar ubangiji, Meenah har ta shiga nursery. Meenah Allah ya bata k'walwa komai aka koya mata ta iya sai dai idan ba'a koya mata ba, kuma idan ta dawo gida ta dinga yi kenan ko gajiya batayi. Ba'a saka Zarah makaranta ba sai da Meenah ta shiga nursery 2 a lokacin ita kuma Zarah tana da shekara 3 a duniya yayinda Meenah keda hud'u. Ranar wata juma'a akayi ma su Meenah hutu suna zuwa gida Meenah ta fara neman babanta don nuna mai report card nata, sai dai rashin sa'a yayi tafiya zuwa Lagos a safiyar ranar, tayi ta kuka tana kiran ita Baba. Bilki tana tsaki ta ansa report card nata dana Zarah tana dubawa, abin takaici a wurinta wai Meenah na d'aya tayi ita kuwa Zarah na ashirin tayi cikin su ashirin da shidda. Bilki kamar tayi kuka don takaici. Wato Meenah dai tafi d'iyarta k'ok'ari kenan? "Gaskiya da sake!" Ta kalli Meenah tace mata "Ke! Zo nan!" Meenah tayi tsaye idanunta k'wal hawaye a duniya tana tsoron Bilki, fizgo ta tayi da k'arfi. "Ke dan ubanki sai da kika yi na d'aya wannan karon ma? Kin manta bugun da nayi maki last term kenan? Salon kija babanta ya dawo ya zane Zarah ko? Ke ga mai k'ok'ari ko? Shegiya mai kama da mage! Wuce ki bani wuri!" Da gudu Meenah tayi d'aki tana kuka sosai, jawo Zarah tayi ta rungume tace. "Don Allah d'iyar Baba ki dage kifi waccan yarinyar k'ok'ari kinji?" Zarah ta gyad'a kai. Da rana ta zuba ma Zarah abinci ta shiga wanka, Meenah na zuwa Zarah tace. "Zo muci." Ba musu ta zauna suka fara cin abincin tare. Ba'a jima ba Bilki ta fito wanka tana lek'owa taga Meenah nacin abin da d'iyarta abinda ta tsana! Da tsawa tace "Ke!" A firgice Meenah ta tashi tana kyarma, Bilki ta k'ara daka mata tsawa. "Bana hana ki cin abinci tare da Zarah ba? Shegiya wuce ki tafi d'aki." Tayi d'aki da gudu a tsorace. Zarah ta aje cokalin hannunta tace "Bazan ci ba nima sai da Meenah." Daman Bilki tasan abinda zatace kenan, tsaki taja tace "To sai dai kar kici wallahi amma bazakici tare da Meenah ba, kinji na fad'a miki!" Aikuwa aje cokalin tayi tana fushi sosai ta bar parlon. Tsaki Bilki ta k'ara yi tana k'ara jin haushin Meenah... *** Sauri yakeyi ya dawo gida don nuna ma iyayensa result nasa na shedar kammala jss3 nasa. Driver na yin parking ya fito da gudu yana murna shigarsa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga masa hankali, ya kuma gigita shi a lokaci guda, take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri a yayinda k'walwarsa ta tsaya cak! ta bar aiki lokaci d'aya!!! Iyayensa ne kwance jina jina, a yayinda wasu mutane kusan su bakwai ke tsaye cikin bak'ak'en kaya hartta fuskokinsu an rufe da black mask! Tsaye yayi ya kasa tantance a wace duniyar yake, take kuma ya fashe da kuka yana fad'in. "Su waye ku? Mey...asa ku...ka kashe min iyaye?" Direwa yayi k'asa yana kuka yana jijjiga iyayen nasa a yayinda yake kiran Anisah! Mutumin yayi dariya yace. "Ka bar kuka yaro, sun tafi inda ba'a dawowa kaima kuma yanzu zaka bisu!" Yakece da dariya sannan ya saita bindigar daodai saitin k'irjinsa ya harba. A gigice ya farka duk da Ac d'in da ke aiki amma hakan bai hana sa yin sharkaf da zufa ba. Ta6a jikinsa ya soma yi amma baiga jini ba, ajiyar zuciya ya sauke ya shiga yin addu'a don ba k'aramin tsoro yaji ba. "Wane wane irin mafarki ne haka..... ?" Ya fad'a yana mai k'ara tunawa da mafarkin da yayi. Zumbur! Kuma ya mik'e ya fice da gudu don duba lafiyar iyayensa don gani yake kamar da gaske ne....! AUREN FANSA 10 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹10 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com "Mummy...! Mu.." A firgice suka farka daga bacci, da mamaki suka ce "Waye?" Kasancewar d'akin gauraye yake da duhu fitila a kashe take, Daddy ya kai hannunsa ya kunna bedside lamp yana kallon Faruk dake tsaye, da sauri Faruk ya rungume mahaifiyar tasa yace. "Alhamdulillah! Ashe duk lafiyarku lau, wallahi naji tsoro." Mummy tayi murmushi don tasan ya k'ara yin mafarki. Tace "Faruk nasha fad'a maka mafarki ba gaskiya bane ka daina d'aga hankalinka akan mafarki, nasha fad'a maka bakaji." Faruk yace "Nasani Mummy amma meyasa a duk lokacin da nayi mummunan mafarki sai naji gabana ya fad'i, sannan na kasa samun nutsuwa, gani nake kamar wani abu na shirin faruwa da mu!" Daddy yace "Haba Faruk! Ka zamo mai tawwakali mana, an fad'a maka mafarki ba gaskiya bane haba! Tashi kaje ka kwanta." Sum sum ya tashi ya fice, Daddy ya kalli Reemah yace. "Wai shin kuwa yaron nan na addu'a a duk lokacin da zai kwanta bacci?" Reemah tace "Yana yi, kullum sai na je na tabbatar da sai sunyi addu'a kafin su kwanta su duka." Daddy ya numfasa yace "To Allah ya kyauta amma sai ya k'ara dagewa da addu'a sosai." Reemah tace "Insha Allah." *** BAYAN WATA D'AYA Zaune yake yana karatu wayarsa ta fara k'ara, ganin sunan Daddynsa yasa yayi saurin d'agawa. "Hello kaine Faruk?" Yace "Eh nine lafiya ina mai wayar nan?" "Sai dai kayi hak'uri mai wayar nan ya rasu dashi da matarsa!" "What? Innalillahi wa'inna ilahir raj'un!" "Ya Faruk!" A firgice ya farka ganin Anisha tsaye gabansa tana kakkarwa, yasa yace "Ke lafiya menene?" Ta fashe da kuka. "Mummy! Ya Faruk Daddy da Mummy babu." Yace "Kamar ya? Ina suke?" Tace "Wasu mutane na nan sun zagaye Mummy da Daddy..." Kafin ta k'arasa ya mik'e da gudu ya fita." Zuwansa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga masa hankali lokaci guda kuma ya gigice ya shiga rud'ani! Murza idanunsa ya fara yi don yayi tunanin wannna karon ma mafarki yakeyi, la6ewa ya shiga yi a bakin k'ofa yana sauraren mutanen da ke tsaye. Kusan su hud'u majiya k'arfi. "Hello Hajiya Laila Sunusi! Aikin da kika samu fa an kammala abu biyu ya rage. Na farko bamuga yaransu guda biyu da kika lissafa mana ba! Na biyu takardun gidannan da sauran mahimman takardun da kika ce a baki." "Yes Ma! Ok Ma! Insha Allah na miki alk'awarin cika miki dukkan aikin da kika samu da ke da aminiyarki ya sunan ta ma? Haha yes Bilkisu Ringim! Ok..." Kamo hannun Anisah yayi yana kuka d'akinsa ya fad'a ya kwashi wasu takardu nasa dashi dana Anisah na makarantarsa da abubuwan da yake buk'ata ya jefa jikka suka fito da sauri sukayi hanyar fita. Anisah na kuka shima yana kuka suka fito gate, gaba d'aya masu gadinsu basu nan, security sunfi goma amma yanzu bai ga kowa ba. Adaidaita ya samu suka wuce wata police station, yana zuwa ya fad'a masa dukkan abinda ya gani ya kuma ji sannan yace suzo su ceci iyayensa kafin su mutu. Ba 6ata lokaci suka nufo gidan sai dai da zuwansu abin mamaki ba komai gidan asali ma gidan a rufe yake da kwad'o sai dai gawar iyayensa, nan akayi examining d'insu aka tabbatar da basuda rai, take Faruk ya rasa a wace duniyar yake, kansa yayi dip, hawaye kuwa kamar an bud'e pampo. Sambatu kawai yakeyi yana fad'in. "Daman nasha yin mafarki an kashe mana iyaye! Nace abin kamar zai faru amma ba wanda ya kula ni..." Duk police d'in da yayi yunk'urin tab'asa da niyyar rarrashi turesu yakeyi suna fad'uwa k'asa, gaba d'aya kamar ya zauce. Yama k'i nutsuwa asan ina danginsa suke a sanar masu de abinda ya faru. Gaba d'aya gidan ba mota ko d'aya, motocin mahaifinsa sunfi kala takwas amma yanzu ko d'aya babu. Nan kuma kan Faruk ya fara juyawa kafin ya ankara ya fad'i k'asa tim! AUREN FANSA 11 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹11 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com A hankali ya bud'e idanunsa bakinsa d'auke da salati, sai kuma ya fara kiran "Mummy! Daddy! Wai da gaske ne an kashe su? Ina Anisah? Wallahi duk wanda ya kashe min iyaye sai na rama masu koma waye..." "Alhamdulillah kunga ya farka ma ashe! Sannu ya jikin?" Kallon likitan yakeyi kafin kuma ya fashe da kuka sosai. Da k'yar aka rarrashe shi, sannan likitan ya zauna kusa da gadon da yake kwance tare da dafa sa. "Faruk, hak'uri zakayi iyayenka sun riga sun rasu, kukanka bazai ta6a maido su ba, yanzu addu'arka ita kad'ai suke buk'ata, kayi hak'uri kaganni nan na maka alk'awari k'wato maka 'yancika a gurin azzaluman da suka aikata maka wannan mummunan aikin, kar ka d'aga hankalinka kaji ko?" Ya share hawayensa "Nasani doctor, iyayena basa buk'atar kukana amma kuma ya zama dole nayi kuka, ba wanda zai gane abinda nakeji a zuciyata abin yana min ciwo, zuciyata tana min zafi, iyayena sune komai na, banida kowa a garinnan sai su, don haka dole nayi kuka saboda na rasa komai na rayuwa, na rasa iyayena, sannan na rasa gidanmu da dukiyar mahaifina..." Kuka yaci k'arfinsa. Doctor ya numfasa "Faruk kaganni sunana Dictor Ishaq Aliyu, ni d'an garinnan ne, daga yau na maka alk'awarin taimaka maka har sai ka samu ingantacciyar rayuwa da kai da k'anwarka, inada mata d'aya da yara hud'u, maza na guda biyu sai mata biyu, kar ka damu bazakayi maraici ba Indai kana tare dani don haka ka bar kuka ka share hawayenka." Faruk ya kalleshi da mamaki yace "Da gaske doctor? Zaka taimaka min duk da baka san koni waye ba?" Likitan ya gyad'a kai "Zan taimaka maka kuma zan taya ki fighting battle d'innan har sai kayi nasara, yanzu kaga kwananka hud'a a nan asibitin, kana buk'atar muje gida ka huta." Faruk yace "Nagode doctor! Nagode Allah ya saka da alkhairi! Ya k'ara budi." Likitan yayi murmushin jin dad'i yace "Amin Faruk mu tafi ko?" Yace "Eh, amma ina Anisah?" Likita yayi murmushi. "Gata can office d'ina tana bacci muje mu d'auke ta sai mu wuce." Ba'a d'auki lokaci ba suka iso gidan Doctor Ishaq, gida ne tangameme na gani na fad'a da ke Maitama, lallai shima doctor Ishaq mahashuk'in mai kud'i ne. Shi ya jagorance su har cikin gidan, suna shiga wata mata dattijuwa ta fito da murmushi a saman fuskanta. "Sannu da zuwa Alhaji." Ta fad'a tana k'ok'arin amsar jakarsa dake rataye a kafad'arsa. "Yauwa sannu da gida Malama Rukayya." Tayi murmushi. "Ahh bak'i mukayi kenan, sannunku da zuwa ku shigo mana." Suka shiga suka zazzauna kan kujera. Alhaji ya fara magana, ga yara nan, ki shiga dasu ciki suyi wanka ki basu abinci akwai maganar da zamuyi da ke bayan nan." Tace "To Alhaji." Ta tashi sannan su Faruk suka bi bayanta. Wani d'aki suka nufa daga gani na yaranta ne mazan, tace ma Faruk ya shiga yayi wanka, sannan ta fiddo masa kayan da zai saka. Hannun Anisah taja, ta mata wanka ta saka mata kaya masu kyau. Kan dinning taja su ta zuba masu abinci suka ci sosai sannan suka wuce parlor inda Alhajin ke zaune da alama abinci ya gama ci. Bayan sun zauna Alhajin ya fara magana. "Ina su Yazeed?" Tace "Suna can waje suna buga ball." Yace "Jeki kirawo man su gaba d'ayansu." Da girmamawa ta amsa ta fice. Can sai gata yaran na biye da ita a baya. "Dada welcome." Suka fad'a gaba d'aya. Yace "Thanks, ku zauna." Duk suka zauna, nan kuma suka hau kallon su Faruk. Alhaji ya numfasa ya fara magana. "Hajiya kinga wad'annan yaran guda biyu?" Tace "Eh nagansu." Yace "Yauwa, wannan shine Faruk sai ga k'anwarsa nan Anisah, shine yaron da nake kula dashi a asibiti bayan rasuwar iyayensa." Tace "Allah sarki sune yaran kenan? Allah ya jik'ansu da rahama." Yace "Amin, so nake mu cigaba da rik'esu a matsayin iyayensu, na farko kinga marayu ne gasu yara k'anana, na biyu duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Yara ne kuma marayu, basuda kowa sai Allah, shine na ga dacewa in d'auko su in rik'e don samun lada, ko ya kika ce?" Ta numfasa. "Haka ne Alhaji, wallahi wannan ba wani abu bane, insha Allah zan rik'e su a matsayin uwa a garesu, Allah ya bamu ikon rik'e amana." Yace "Amin, Faruk wad'annan k'annenka ne gasu nan, kaga wannan shine babba mai suna Yazeed, shekarsa sha biyar sai mai bi masa Hauwa'u ana kiranta Jidda shekararta Sha hud'u, sai k'aninta Nabeel shi yakeda da sha biyu sai auta gata nan Yusra ita keda shidda, don haka kuna jina wannan 'yan uwanku ne ban yarda wani ya nuna musu wariya ba a cikinku, kuna jina?" Suka ce "To Dada." Alhaji yayi murmushi "Faruk ga kannenka nan sai kuje kuyi wasa ko?" Faruk yayi murmushi inda gaba d'aya suka mik'e suka fice. Alhaji ya ce "Allah ya bamu ikon rik'e su amana, ya tona asirin azzaulumai." Tace "Amin ya Allah Alhaji, yaran sun bani tausayi wallahi, Allah ya bi musu hakk'insu." Yace "Amin amin, anjima zanje inyi magana da manyan lauyoyin da na sani, asan me za'ayi a kai." Tace "Hakan yayi daidai, yanzu makarantarsu fa?" Yace "Makarantarsu ba matsala bace na d'auki nauyin karatunsu, yanzu ayi k'ok'ari a saka su makarantarsu Yazeed." Tace "Haka yayi daidai, Allah ya k'ara bud'i." Yace "Amin Amin, bari inje in d'an kwanta kafin anjima zan koma asibiti." Tare suka mik'e ya fice tabi bayansa. (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹12 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Washe gari aka saka su makaranta. Yanzu abubuwan sun ma Faruk sauk'i tunda yanzu gidan da suke basuda matsala, daidai gwargwado suna samun kulawa sosai, sai dai har yau hoton gawar iyayensa ya kasa 6ace masa kai, ko rufe ido yayi sai ya gansu ya kuma ga mutanen da suka kashe su, sannan sunayen da aka ambata har yanzu ya kasa mantawa hasali ma ya samu diary nasa ya rubuta sunanayen nasu. Ya samu shak'uwa mai k'arfi tsakaninsa da su Yazeed komai a tare sukeyi su uku abin sha'awa sun had'e kansu. Duk inda kaga d'aya to zakaga d'ayan. Haka ma Anisah da Yusra sun zama k'awaye, ita Jidda ta girmesu don haka sai dai sama sama suke shiri, daga gaisuwa sai kuma cin abinci ke had'a su. Duk da k'arancin shekarun Anisah ta fuskanci Jidda nada wuyar sha'ani sannan miskila ce ta k'arshe, sai dai akwai kuma kirki halayen nata dai gasu nan a baibai, mutum ce mai wuyar fassara, sheyasa ta lura yaran gidan basu shiga harkarta, don haka itama sai tayi baya baya kad'an. Har yau Anisah ta kasa gane iyayensu sun mutu har abada bazasu dawo ba, don kusan kullum sai ta tambaya. Meyasa suka dawo nan da zama, ina Daddy da Mummy? Yaushe zasu dawo? Haka take tasa Faruk gaba da ire iren wad'annan tambayoyin har idan ya rasa amsa sai tasa masa kuka, dole sai dai yace sunyi tafiya mai nisa kuma zasu dad'e basu dawo ba. To tun wata rana da abin ya fara isarsa ya daka mata tsawa yace tayi hak'uri Mummy da Daddy basu dawowa, da farko ta tsorata amma da Faruk ya zauna yayi mata bayani sai kuma ta fahima, ya kuma d'ora da cewa ta dinga yi musu addu'a kullum, aikuwa tun daga ranar bata k'ara tambayarsu ba haka ma da ta motsa sai tayi musu addu'a. *** BAYAN WANI LOKACI... Zaune suke kan dinning suna breakfast gaba d'ayansu, Dada ne ya aje cokalin hannunsa ya soma magana. "Wai ina Faruk ne?" Hajiya Rukayya da suke kira da Mama tace "Inaga yana ciki kamar wanka ya fito." Sanye yake cikin bak'in wando wulik pencil trowser sai ya d'ora ash shirt marar hannu, tun daga k'afafuwansa ya isa ka gane cewa kyakkyawan mutum ne, don kuwa k'afar tasa fara ce tas kalar larabawa har wani gashi gashi ake gani a tsakankanin yatsanshi na k'afa. Haka nayi ta d'aga kaina har na sauke su kan fuskarsa... tabbas duk inda ake neman namiji toh a nemi wannan mutumin, gashin kansa irin mai cikar nan ne mai yawa sannan nannad'e yake kamar na jarirai. 'Ya Faruk Dada na jiranka fa za'a ci abinci." Kai! Wannan Anisah ce ta k'ara girma haka? Lallai idan na tsaya muku bayani bazaku gane ba, kamarta d'aya da Faruk gashinta mai kama dana larabawa an tufke shi daga can tsakiya amma duk da haka sai da ya zubo bayanta, kyakyawa ce itama. Sanye take cikin light pink dress 'yar kanti. Murmushi yayi mai bayyana hak'ora yace. "Ina zuwa." Da sauri ta fice, turare ya feshe a jikinsa sannan ya zura takalmansa ya fice. Yana zuwa ya gaida Mama da Dada ya samu wuri ya zauna kusa da su Nabeel. Nan aka soma cin abinci. Dada ne ya dakata ya soma magana. "Faruk kamar kullum bazan gaji da ce maka kayi hak'uri ba, wallahi har yanzu kan aiki ake ganin an kamo wad'anda suka kashe iyayenku..." Faruk yayi murmushi yace "Haba Dada wallahi babu damuwa, komai lokaci ne, insha Allah Allah zai bayyana mana su." Dada yayi murmushi, sheyasa yake son Faruk yaro ne mai kaifin tunani, da kuma nutsuwa da hangen nesa. Don haka sai yace "Haka ne, amma insha Allah za'a cigaba da aiki Allah yasa a dace." Suka amsa da "Amin." Dada ya cigaba. "Kunga yanzu kuna dab da gama makaranta, to kamar yadda nayi alk'awari mazan zan tura su Saudia don neman ilimi, to zan had'a da kai Faruk kowa ya za6i abinda zaije ya karanta. Abinda yasa kuka ga na za6i wannan k'asar saboda nayi k'wak'waran bincike ana tsaro sosai da yaran mutane, to kuma yaro ko yaso koya k'i dole ya kama kansa. Amma kamar kullum bazan gaji da jawo hankalinku ba, don Allah ku nutsu ku tsare mutuncinku, kar kuga bana kallonku to ku tuna Allah (S.W.A) yana kallonku, wallahi kuji tsoronsa abinda kuka je nema shi zakuyi, kunaji ko? Allah yayi muku albarka sai ku dage ku fito da grade mai kyau." Suka ce "Amin Dada, insha Allah zamu kiyaye." A haka suka cigaba da karyawa. *** "Mami don Allah ki barni zan sa da kaina." Hajiya Bilki tayi tsaki "Ke da Allah wuce can, ki bari na sa miki." Ta zum6uro baki. "Assalamu Alaikum..." Bilki ta d'ago tana k'are mata kallo. "Wa'alaikumusalam." Daga sama har k'asa na k'are mata kallo, Meenah ce ta girma haka? Tayi tsawo ta k'ara kyau, wannan ita ake kira black beauty, ga gashin kanta duk d'ankwalin da ke kanta hakan bai hana shi fitowa ba... "Mami na gama wanke kayan." Bilki ta ta6e baki. "Kin gyara min kitchen?" Tace "Eh na gyara." "Kinyi shara da wanke wanke?" Meenah tace "Eh nayi..." "Kin wanke toilets?" "Eh na wanke naki..." "Na d'akin Zarah fa? Shifa wa zai wanke?" Ta d'an bata rai. "Mami home work kawai zanyi sai na wanke, an bamu home work har biyar gashi ko d'aya ban ta6a ba." Ta doka mata harara, "Sannu 'yar boko, toh bari kiji bazakiyi ba sai kin gama min aikina tsab a gidannan sannan zaki yi wani home work." Tayi narai narai da fararen idanunta wadda suke kamar an d'iga madara a ciki. "Ke! Bansan iskanci ya ina miki magana kin tsaya kina wani kallon mutane zaki wuce ko sai na mauje ki!" A zahirin gaskiya bawani assignment d'in da zatayi, don ta riga tayi shi da asuba, daman gudun aiki yayi mata yawa sheyasa data gama sallah take home work ko karatu, kawai ta gaji ne tun safe take aiki bata huta ba, daga wannan sai wannan ko kalaci batayi ba... "Mami zan taya ta." Bilki ta 6ata rai "Kiyi ki gani yadda zanyi da ke a gidannan, maza kije kuma kar tayi nata home work d'in sai ta gama maki naki!" Sum sum Zarah ta fice zuciyarta cike da tausayin Meenah... AUREN FANSA 13 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹13 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Duk'e take tana faman wanke toilet Zarah ta lek'o, cikin muryar rad'a rad'a tace. "Meenah bari na taya ki." Meenah ta d'ago tana duban Zarah tace "A'a ki rufa man asiri Zarah, yanzu da Mami tazo zata dake ni." Zarah tayi murmushi "Ay dana ji ta taho zan bari..." "Nidai gaskiya ina tsoro ki bari kawai..." Da sauri Bilki ta shigo d'akin, tana zuwa ta jawo Meenah. "Ke maza kije kiyi wanka ga babanku nan dawowa, bar wankin toilet d'in zan k'arasa..." Halin maman tasu na basu mamaki, sun rasa meyasa da babansu ya kusa dawowa sai ta hana Meenah yin ko wane aiki. Sum sum Meenah ta fice daga d'akin. "Mami meyasa kike sa Meenah aiki ni baki sani? Kuma meyasa idan Baba ya kusa dawowa kike kora Meenah tayi wanka ko taci abinci?" Bilki ta daka mata tsawa "Ke! Kar ki k'ara min ko wace irin tamaya a nan kina jina? Kema fita ki bani wuri." Sum sum ta fita tana jinjina hali irin na uwarta. Ba'a jima ba ya shigo gidan a gajiye, Bilki ta tasa yaran gaba suna kallo ya shigo da ledoji a hannunsa, da sauri Zarah da Meenah suka mik'e suka kar6a kayan hannunsa. Bayan ya zauna yana murmushi yace "Kaza ce da ice cream na siyo maku kuje kuci." Da murna suka shige ciki. Bilki tana murmushi tace "Yaran nan na shan gata Alhaji, kana tunanin baiyi yawa ba kuwa?" Alhaji yayi murmushi yace "Bilki kenan, ay ba wani abu nake musu na gatanci ba, bana sangarta su, haka ma bana 6ata su da kud'i ko wani abin duniya, abinci ne nake basu wanda kuma yin hakan ba laifi bane." Tayi murmushi "Bakayi laifi ba kam nima dama wasa nake maka." Sai kuma yayi ajiyar zuciya "Kinsan abinda ke damuna?" Tace "Sai ka fad'a." Yace "Mutuwar Alhaji Adam, su waye marassa imanin da suka bishi har gidanshi suka kashe shi dashi da matarsa?" Bilki ta had'iye miyau da k'yar tace "Nima abinda yake damuna kenan kullum Alhaji, nasan mahassada ne kawai." Ya numfasa "Wai me duniyar nan keso ta zama ne? Mutane akan kud'i ba abinda bazasuyi ba?" "Uhm...uhm Alhaji bari na kawo maka ruwa kasha." Bai kawo komai a ransa ba yace "To." Aikuwa da daddare Meenah bata samu abincin dare ba, wai ay taci kaza ta k'oshi bataga dalilin da yasa za'a bata abinci ba. Da safe Baban na fita aiki ta jibga mata uban wankinta dana Zarah, duk da suna da mai wanki amma tsabar mugun hali irin na Bilki sai da ta jibga mata wankin daya fi k'arfinta. Tana gama bata wankin ta shigo daidai bakin k'ofa taci karo da Zarah tana fad'in. "Mami idan Baba ya dawo sai na fad'a masa abinda kike ma Meenah idan baya nan..." Finciko ta taji anyi, tayi d'aki da ita tana zuwa ta shiga tsula mata bulala, sai data zane ta tas sannan tace "Wannan kad'an nayi miki akan bayan kin fad'a masa, sai jikinki ya gaya musu, zaki fad'a ko kuwa?" Da sauri ta girgiza kanta tana kuka. Haka dai kwanaki sukayi ta tafiya cike da wahala a gurin Meenah, sam batada lokacin kanta sai aikin gida, bata samun lokacin karatu sai can cikin dare, sheyasa gata nan wata 'yar ficit sai tsawo amma ba kumari, Zarah kuwa wata 'yar duma duma ga ta fara sol fatar jikinta irin ta 'yan hutun nan ce da basu san wahala ba, ita kuwa Meenah batada k'iba sai tsawo. *** A haka rayuwar tayi ta mirginawa, har Meenah ta kai SS3 a yayinda Zarah ke SS2, yaran sun girma sun zama 'yan mata, daka gansu tare sai ka k'ara kallonsu don kuwa ko a makaranta tare sukeyin komai, shiga aji kawai ke raba su. Halayen nasu ne kawai ya banbanta, ita Meenah tana da wani calm attitude, tanada nutsuwa komai nata a hankali takeyinsa, ko maganarta wani a hankali takeyi, ba kamar Zarah da take abu kazar kazar ba, ita tsaye take kamar ba mace ba, she's too lousy dai tana da hayaniya.... Sannan uwa uba Meenah ba irin girkin da bata iya ba, da kuma ko wane irin aiki yi take irin su shara wanke wanke, wanki da sauransu, kuma bata gajiya da gyara wuri koda za'a shekara ana 6ata shi, Meenah bata damu da abin duniya ko wayar da take rik'ewa batada komai na social media a ciki, ita dai kawai tayi waya idan ta kama shikenan, amma Zarah akwai son harkar social media, ga yin hoto kamar hauka, to a wannan fannin ne halayensu suka banbanta, ga son jiki bata iya ta6uka komai na aikin gidan saboda haka ta taso ba'a sata tayi, sheyasa ko gyaran d'akin bata iya ba, sai Meenah tazo ta gyara mata... AUREN FANSA 14 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Susu, thank you for everything!❤️ 🌹14 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bakajin komai a d'akin sai k'yalk'yatar dariya, da k'yar suka dakata, Laila ce ta soma magana. "Shegiyar gari, wato kina nan kina facaka cikin dukiya, kina nan kina taka matsayin da kika d'ad'e kina burin takawa, kina nan kina hawa kud'i ki taka kud'i ki yadda kikeso a cikinsu, lallai shawara d'aukar d'aki yau gashi mun da'auka tayi mana amfani!" Suka sake sa dariya, Bilki tace "A da na bijirewa shawararki, kuma da farko na tsorata amma yanzu abin sai wanda ya gani." Suka sake sa dariya gami da tafa hannu. Laila ta kuma cewa tana dariya "Yayi daidai kin birgeni! Yanzu keda talauci sai dai ko a lahira..." Bilki tace "Kada Allah ya had'ani da shi koda a lahirar ne ma. Yanzu tsoro na kada wata rana a gano mu ya zamuyi kenan?" Laila tace "Daman ay ke bugun Abuja ce, daman ke kalarki bata k'auye bace ba..." Bilki tayi dariya "To kin dai gani, rabona da k'auye har na manta, tunda muka dawo Abuja idan kin ganni k'auye sai dole..." "Assalamu Alaikum..." Ta shigo d'auke da tray d'in lemo da glass cups guda biyu sai plate d'in cincin da dambun nama. Ta ajiye tray d'in sannan ta gaishe su, sai da suka watsa mata harara sannan suka ce "Lafiya." Bilki tace "Kin d'ora abincin rana?" Tace "A'a yanzu zan d'ora." Bilki tace "Aikin me kike da tun d'azu baki d'ora ba har kusan k'arfe sha biyu?" Tace "Wanke wanke ya taru da yawa shine na..." "Yi min shiru a nan!" Ta daka mata tsawa. "Duka duka wanke wanken guda nawa ne da har zaki ce yayi yawa? Sai anyi magana ki dinga rissina kai kamar wata yarinyar kirki, zaki wuce ki d'ora ko sai na san me zan miki!" "Uhm... me za'a dafa?" Tayi tsaki "Ki dafa mana fried rice da peppered chicken, sai ki had'a coleslaw, akwai kaji a freezer ki d'auki guda biyu kiyi amfani dashi. Sai kinsan halin babanku yafison tuwo, kiyi masa tuwo miyar busassar ku6ewa." Da k'yar tace "To." Ta fice idanunta cike da hawaye! "Anya bataji mu ba d'azu?" Cewar Laila cike da damuwa. "Ko taji me za'ayi? Ah babu ay." Sukayi dariya Laila tace "Haka ne fa." Tana kitchen tana yanka kaji Zarah ta shigo tana sanye da wando jeans sky blue sai light pink shirt marar hannu. "Meenah zo ki ga..." Da mamaki take kallonta tana d'aga mata fuska don taga idan idanunta ba k'arya suke nuna mata ba. "Meenah kukan me kike? Hala Mami ce? Me tayi miki?" Ta k'ak'alo murmushin dole tace "Babu komai, wani abu ya fad'a min ido ne." Zarah tayi murmushi "Uhm baki iya k'arya ba Meenah, ni nasan wani abu Mami tayi miki." Meenah tace "Bakomai amma don Allah Zarah zan miki tambaya inaso ki fad'i man gaskiyar abinda kika sani." Zarah tace "Ina jinki." Meenah tace "Don Allah a iya zamanki a gidannan kin ta6a ji koda a wurin wani ne cewar tsintso ni akayi?" Zarah ta k'yalk'yale da dariya harda duk'ewa, Meenah ta kalleta galala cike da mamaki tace "Meye haka wai Zarah? Ya ina tambayarki kin tsaya kina min dariya?" Har yanzu dariya takeyi, da k'yar ta tsagaita tana duban Meenah tace "Anya baki buk'atar ganin likita Meenah? Kanki d'aya kuwa?" Meenah ta k'ule tace "Shikenan sai kije kiyi ta dariyar, gani kike kamar wasa nakeyi ko?" Zarah tace "Daman ay wasan kikeyi, ta yaya ma zaki fara irin wannan tunanin?" Meenah tayi murmushi mai ciwo tace "Dole nayi tunanin haka Zarah, na rasa meyasa Mami bata sona..." Da sauri Zarah ta rufe mata baki "Kar kice haka, ay indai zaki kula halinta ne haka, koni tana min." Meenah tace "Eh amma ba kamar yadda take min ba, dole ne na fara tunanin duk yadda akayi ko tsinto ni akayi ba'a san asali na ba, ko kuma ni 'yar rik'o ce." Zarah ta 6ata rai "To yayi miki kyau, ki cigaba da fad'in haka ni kuma daga yau na daina miki magana a gidannan." Meenah ta juyo da sauri "Haba dai?" Zarah tace "Ki

Chapter 5 of 11