Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cigaba ki gani." Da sauri Meenah tace "La na bari, ya za'ayi na bari mu 6ata?" Zarah tayi murmushi "Yawwa sweet sis bara na taya ki aikin don ayi sauri, kuma idan kika hanani yi sai na daina miki magana a gidannan." Ta fad'a cike da shagwa6a, Meenah tasa dariya ta kwaikwaiye ta "To bazakiyi ba wuce ki tafi ki kwanta." Zarah tace "Nak'i" Haka suka k'arasa aikin suna zolayar juna, wasu abubuwan sai da Meenah ta dinga koya mata, kuma ba laifi tana fahimta. *** "Wai bazakuyi sauri ku fito ba Jidda? Kodai a tura driver ya d'auko su ne?" Da sauri Anisah ta fito cikin shigar atamfa d'inkin doguwar riga kalar blue and purple sa ta d'ora purple mayafi. "A'a Mama mu zamu d'auko su, nifa na gama shiri su ya Jidda ne tun d'azu basu gama ba." Mama tayi dariya. "Au kin k'agu kiga yayan naki hala? Wannan irin zakwad'i haka?" Anisah dariya, daidai nan sauran 'yan matan suka fito sun sha ado sunyi kyau inda dukansu suke cikin shiga iri d'aya. Yusra tayi dariya "Kai Mama duk kin k'osa a dauko miki yaranki ne haka?" Mama tayi dariya "Ke ni ba kakarki bace, ku wuce ku tafi haka nan." Da sauri suka tafi suna dariya... Jidda ta dubi agogon dake mak'ale a hannunta, k'arfe sha biyu harda rabi ta wuce. "La Ibrahim kayi sauri sun kusa sauka." Ibrahim yayi murmushi "To ranki ya dad'e." Tunda suka dira a airport hankalinsu ya kwanta ganin har yanzu basu sauka ba, amma daga inda suke suna hango jirgin yana niyyar sauka k'asa. Duk sukayi ajiyar zuciya. A hankali jama'a suka fara fitowa daga jirgin, haka ma duk wanda ya hango d'an uwansa sai ya ruga ya taro sa. Tsaye suke kusa da kujerar zama wato (waiting chair) idonsu k'yam saitin k'ofar jira kawai suke suga ta inda zasu 6ullo. AUREN FANSA 15 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹15 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Ba'a fi minti biyar ba suka kunno kai, ko wanensu yana tura trolley nasa, tunda suka fito Jidda ke kallonsa ya za'ayi ta mance da wannan fuskar? Ya chanza gaba d'aya ya zama wani babba, k'irar jikinsa kansa abin kallo ce irin giant d'innan, abinka ga fari sai ya k'ara murjewa ya zama bature sak! Ta kalleshi yana murmushi. "Sannu da zuwa yaya!" Anisah ta ruga tare da mak'alk'ale shi, a yayinda Yusra ke mak'ale da nata ya'yyen, sai a lokacin Jidda ta dawo duniyar tunani. Da k'yar ta daidai nutsuwarta tace "Sannunku da zuwa!" Ko alama bai gane ta ba. "Yauwa sannu... Jidda ko?" "Wow haka muryarsa take?" Ta fad'a tana k'ara kallonsa cike da mamaki. Tace "Eh nice yaya." "Wow duk kun girma..." Suka taya su jan kayan nasu har bakin mota. Tafiya suke amma idonta na kansa. Abu d'aya take maimaitawa a zuci... "What kind of change is this?" Haka aka loda kattunan jakunansu a boot. Koda suka shiga mota shi ya zauna gaba, daga baya babu abinda Jidda keyi sai aikin kallonsa. "Ya Faruk? Ya Faruk? Ya Faruk?" Wannan abu shi take ta fad'i a ranta. Ta d'an k'ara kallonsa ta baya, gashin kansa kad'ai abin kallo ne, ya k'ara kyau akan wanda yake dashi da, sai shinning yake kamar taurari a sama... "Anya bayada iri da larabawa?" "Wa kenan?" Ta kai dubanta tana kallon Najeeb daya tsareta da kallon tuhuma, tace "Uhm uhm bangane ba." Nabeel yace "Rabu da ita tun d'azu na lura da yadda ta chanza." Tace "Na chanza kamar ya?" Najeeb yasa dariya. "Kamar yadda kika fahimta." Daga nan ba wanda ya tanka har suka iso gida. Mama harda d'an gudunta tana fad'in "Welcome home." Suka shiga parlor Najeeb ya kalli matan yace "Ku kai mana kayanmu d'aki." Sannan ya maida kallonsa da Mama. "Bari mu d'an watsa ruwa muyi sallah." Mama tayi murmushi "Eh hakane lokacin sallar azahar yayi ya kamata ayi sallah sai aci abinci, sannunku da hanya." Nabeel yace "Yauwa Mama, ina Dada?" Tace "Yana Ireland yau satinsa d'aya da tafiya, amma insha Allah ya kusa dawowa." Najeeb yace "Ok... hakane munyi waya yake fad'a min batun tafiyar tasa Allah ya dawo dashi lafiya." Aka amsa da "Amin" Daga haka kowa yayi hanyar d'akinsa. Faruk d'akinsa ya burgeshi yadda yayi tsab sai k'amshi da sanyin ac ke ratsa dukkanin illahirin jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya fad'a toilet. Yana gamawa ya saka k'aramar riga da dogon wando. A dinning aka hallara kowa yayi serving kansa jollof d'in shinkafa, da pepper soup, sai kaza gasassa sai salad. Sun fara cin abincin ne Mama tace. "Alhamdulillah, Allah na gode maka daka nuna man wannan ranar, ranar da 'ya'yana suka kammala karatunsu lafiya, fatana Allah ya albarkaci karatunku, Allah ubangiji ya baku sa'a." Gaba d'aya sukace "Amin amin." Ta cigaba "Yanzu dai ga Likita Najeeb, ga Detective Faruk, ga kuma Banker Nabeel, kai masha Allah! Allah yayi albarka." Suka ce "Amin Mama mun gode Allah ya saka da alkhairi." Tace "Amin, yanzu dai ya kamata kuyi settling kowane ya nemi mata yayi aure, shine kad'ai abinda ya rage." Duk kansu k'asa basu ce komai ba, itama Mama murmushi tayi a haka suka cigaba da cin abinsu. *** Bayan Wata D'aya...! Zaune yake kan kujerar office d'insa yana faman dube dube a computer d'insa, aka shigo da sallama, a hankali ya d'aga ido ya kalli k'ofa yayi murmushi. "Ah Usman! Shigo mana ya zaka tsaya a bakin k'ofa?" Ya k'araso yana gaishe shi "Ina wuni sir?" "Lafiya lau zauna magana zamuyi." Bayan ya zauna, Faruk ya soma magana. "Wani aiki zan saka, don Allah ina so duk abinda nake nema ka yi k'ok'ari wajen ganin ka samo min duk wani abu zan buk'ata." Usman yace "Insha Allah, ay ba yau ka fara sani aiki ba, kuma duk lokacin da kake sani abu ina k'ok'ari waje ganin na gano maka koma me kake nema." Faruk yace "Haka ne, to yau ma ina tafe da wani aikin mai matuk'ar mahimmanci a wurina." Ya fad'a yana fiddo wani abu a cikin drawer d'in table d'insa. "Karanta kaga." Da ladabi ya kar6a ya soma karantawa. Bayan ya gama yace "Yalla6ai amma suna ne kawai nake gani." Faruk yayi wani d'an guntun murmushi yana juya kujerar da yake zaune akai. Sai da ya d'auki tsawon mintina biyu zuwa uku sannan ya soma magana. "Eh sunaye ne na mutum biyu, bincike nake buk'ata akansu." "Toh yalla6ai." "Yawwa, i want every bit of information regarding them. Ina buk'atar komai idan nace komai i mean everything. Wane gari suke? Wace unguwa? Sunada 'ya'ya? Guda nawa ne? Suna da miji? Meye sunansa? Wane aiki yake? Ina da ina suka fi zuwa? Wace makaranta yaransu suke? Don't left out anything, including their photos." Usman ya gyara zamansa yana fuskantarsa. "Angama amma yalla6ai meyasa kake neman information d'innan haka? Sannan ta ina zan samo hotunan su?" Faruk ya mik'e tsaye tare da dawowa gaban Usman gami da zama saman table a kusa da shi yace "Usman bana son shishigi, aiki na saka shi zakayi min, kawai kaje ka kawo min abinda na saka please banda wasa, sannan hotunansu wannan kai zaka nemo." Usman yace "Hakane insha Allah zanyi k'ok'ari." "Yauwa kana iya tafiya." Daga haka ya fice, inda Faruk yayi murmushi yace. "This is my first step towards my goal, waiting for the next step." Yayi murmushi yana kad'a kai. AUREN FANSA 16 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹16 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Tsaye take a gaban wardrobe tana gyara zaman skirt d'inta, duk da kayan dake jikinta sun mata kad'an hakan bai hana ta yin kyau ba, ji tayi an rungume ta ta baya, tasan baya wuce aikin Zarah. "Auch! Haba mana Zarah so kike ki k'arasa ni ne?" Zarah tasa dariya, tace "To sarkin fad'a, yanzu dai maida wuk'ar albishir nazo miki dashi." Meenah ta juyo da murmushi saman fuskarta tace "Ina jinki." Zarah tace "Fari ko ja?" Meenah tace "Fari k'al ma kuwa." "Baba yace nayi WAEC d'ina yanzu idan naci mu tafi university tare!" Zarah tace cike da murna. Meenah farin ciki ta rasa ina zata sa ranta, dama ta dad'e tana addu'ar su tafi university tare da Zarah, sai dai tasan Baba ne ya hana yace bazatayi ba sai ta kai SS3, amma yanzu ko ya akayi ya yarda? Meenah tace "Amma ya akayi ya yarda?" Zarah tace "Wallahi ikon Allah, kuma fa ba tambayar sa nayi ba, shi da kansa ya kirani yace na shirya yin exam tare da ke." Meenah cike da murna tace "Lallai ikon Allah, Allah yasa kici." Zarah ta rungume Meenah tana murna tace "Amin sisi." "Kai meye kun cika ma mutane kunne da hayaniya?" Cewar Bilki daga bakin k'ofar d'akin tana tsaye, fuskarta ba yabo ba fallasa. Sukayi tsit, ta kuma daka musu tsawa "Ba da ku nake ba?" Zarah tace "Da... dama, Baba ne yace za... zan iya tafiya university tare da Meenah..." Take ta washe baki kamar ba ita ba, tace "Allah d'iyar Baba? Yaushe ya yarda?" Tace "D'azu kafin ya tafi wurin aiki." Bilki tace "Alhamdulillah, yayi daidai Allah ya bada sa'a sai ki dage, tun kafin ace bakida k'ok'ari, ko kuma ace wasu sun fiki." Ta k'arasa tana ma Meenah wani irin mugun kallo. Duk sun san abinda take nufi kuma hakan ya sosa ransu. "Ke! Meenah zo ki matsa man k'afa ta." "Mami zan taya ta." Wani kallo ta watso mata na irin kika k'ara magana sai na kakkarya ki sannan ta fice. Meenah ta dafa ta tana fad'in. "Don Allah Zarah daga yau ki daina cewa zaki taya ni idan tasa ni aiki, wallahi fad'a kike ja man duk sadda kika fad'i haka." "Uhm." Kawai Zarah tace, daga haka Meenah ta juya da sauri zuwa sashen Mami. Da sallama ta shiga, zaune take kan wata kujerar hutawa ta baje k'afafuwanta ma'ana ta mik'ar dasu saman kujerar, tana faman danne danne a wayarta k'irar iPhone 7plus, tana zuwa ta durk'usa har k'asa tace "Gani Mami." Sai data samu tsarabar harara sannan tace "Meya tsaida ki tun d'azu nake zaman jiranki?" Bata ce komai ba kanta na k'asa dai. "Sai anyi magana kiyi sum sum da kai kamar mutuniyar arzik'i..." "Kiyi hak'uri Mami, wallahi ban tsaya yin komai ba nan na taho." Tayi tsaki gami da mik'o mata k'afa. "Ni matsa man k'afata, kuma saura kiyi mani mugunta irin na rannan wllh sai na yi maganinki, don yau sai dai a kaiki asibiti don sai nayi miki lis!" A hankali take matsa mata cikin lalla6awa, sai kuma ta sakar mata k'wanya a kai. "Ke bakida hankali ne? Ya zaki dinga mani abu kamar susar k'adangare?" Sai ta hau yi da d'an k'arfi, nan ma ta kai mata wanda yafi na d'azu zafi. "Yau ga muguwa! Zaki 6alla min k'afa ne?" Ta rasa yadda zatayi, mistake kad'an sai taji k'wanya mai shegen zafi a kanta. Da daddare tana kwance ita dai abin duniya yabi ya dame ta, zuwa yanzu ta yarda ta amince ba Mami ta haife ta ba, ta yarda Baba ne babanta amma sam ta kasa yarda Mami ce ta haifeta. To ina mahaiyarta? Ta rasu ne ko tana raye? Ko kishiyar Mami ce? Kullum ire-iren wad'annan tambayoyin sune suke mata yawo a cikin kai, kuma har yanzu ta rasa amsa. Daga k'arshe ta yarda ta amice mahaifiyarta ta rasu kuma kishiyar Mami ce kawai. Wasu zafafan k'walla suka zubo mata, ita kam batasan dad'in uwa ba, bata san ya ake ji ba idan mutum na tare da mahaifiyarsa. Sama sama tayi bacci gudun makara saboda ga aikin gida ga kuma shirin makaranta. Da asuba ta mik'e bayan ta gabatar da sallar asuba tayi wanka, ta yi aikin gidan kamar kullum, ta had'a kalaci, d'aki ta wuce ta sanya uniform d'inta da basu samu guga ba, bayan ta gama shirinta tsab ta fito don ta karya, tana bud'e kular abinci sai ta ganta wayam! Nan ta hau dube dube amma kaf ba komai a ciki. Mami ce ta sauko cikin kayan bacci da d'aurin gaba tana zuwa tabi Meenah da mugun kallo, ta wuce kitchen. A ranar haka nan ta hak'ura da kalacin daman sun makara, sauk'inta ma Baba ya basu kud'in makaranta da batasan ya zatayi ba. *** BAYAN KWANA BIYU Da sallama ya shigo office d'in, yana zaune yana fama da aiki kamar kullum, d'ago da fuskarsa yayi yace "Shigo mana Usman." Sai da ya kammala abinda yakeyi sannan ya maida dubansa ga Usman dake zaune d'auke da wata babbar brown envelope. "Yalla6ai daman akan aikin da kasani ne, to Alhamdulillah na kammala maka komai shine na kawo maka ka gani." Da sauri ya d'ago yana duban Usman yace "Da gaske ka kawo duk abinda nake buk'ata?" Usman yana murmushi sosai yace "K'warai kuwa gasu." Ya sa hannu ya zazzaro wasu hotuna guda biyar ya dire a gabansa, sannan ya fiddo wani dogon paper mai rubuce rubuce a samanta.... AUREN FANSA 17 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the support you are special to me! Love you guys❤️ 🌹17 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon Usman yace. "Nagode, sai kayi min bayaninsu." Usman ya gyara zama yace "Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta komai amma duk da haka zan maka bayani da baki. "Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran bincike akansu kafin nazo nan." Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa. "Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata. Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar. Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana Kaduna da zu Alaikum..." Bilki ta d'ago tana k'are mata kallo. "Wa'alaikumusalam." Daga sama har k'asa na k'are mata kallo, Meenah ce ta girma haka? Tayi tsawo ta k'ara kyau, wannan ita ake kira black beauty, ga gashin kanta duk d'ankwalin da ke kanta hakan bai hana shi fitowa ba... "Mami na gama wanke kayan." Bilki ta ta6e baki. "Kin gyara min kitchen?" Tace "Eh na gyara." "Kinyi shara da wanke wanke?" Meenah tace "Eh nayi..." "Kin wanke toilets?" "Eh na wanke naki..." "Na d'akin Zarah fa? Shifa wa zai wanke?" Ta d'an bata rai. "Mami home work kawai zanyi sai na wanke, an bamu home work har biyar gashi ko d'aya ban ta6a ba." Ta doka mata harara, "Sannu 'yar boko, toh bari kiji bazakiyi ba sai kin gama min aikina tsab a gidannan sannan zaki yi wani home work." Tayi narai narai da fararen idanunta wadda suke kamar an d'iga madara a ciki. "Ke! Bansan iskanci ya ina miki magana kin tsaya kina wani kallon mutane zaki wuce ko sai na mauje ki!" A zahirin gaskiya bawani assignment d'in da zatayi, don ta riga tayi shi da asuba, daman gudun aiki yayi mata yawa sheyasa data gama sallah take home work ko karatu, kawai ta gaji ne tun safe take aiki bata huta ba, daga wannan sai wannan ko kalaci batayi ba... "Mami zan taya ta." Bilki ta 6ata rai "Kiyi ki gani yadda zanyi da ke a gidannan, maza kije kuma kar tayi nata home work d'in sai ta gama maki naki!" Sum sum Zarah ta fice zuciyarta cike da tausayin Meenah... AUREN FANSA 13 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹13 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Duk'e take tana faman wanke toilet Zarah ta lek'o, cikin muryar rad'a rad'a tace. "Meenah bari na taya ki." Meenah ta d'ago tana duban Zarah tace "A'a ki rufa man asiri Zarah, yanzu da Mami tazo zata dake ni." Zarah tayi murmushi "Ay dana ji ta taho zan bari..." "Nidai gaskiya ina tsoro ki bari kawai..." Da sauri Bilki ta shigo d'akin, tana zuwa ta jawo Meenah. "Ke maza kije kiyi wanka ga babanku nan dawowa, bar wankin toilet d'in zan k'arasa..." Halin maman tasu na basu mamaki, sun rasa meyasa da babansu ya kusa dawowa sai ta hana Meenah yin ko wane aiki. Sum sum Meenah ta fice daga d'akin. "Mami meyasa kike sa Meenah aiki ni baki sani? Kuma meyasa idan Baba ya kusa dawowa kike kora Meenah tayi wanka ko taci abinci?" Bilki ta daka mata tsawa "Ke! Kar ki k'ara min ko wace irin tamaya a nan kina jina? Kema fita ki bani wuri." Sum sum ta fita tana jinjina hali irin na uwarta. Ba'a jima ba ya shigo gidan a gajiye, Bilki ta tasa yaran gaba suna kallo ya shigo da ledoji a hannunsa, da sauri Zarah da Meenah suka mik'e suka kar6a kayan hannunsa. Bayan ya zauna yana murmushi yace "Kaza ce da ice cream na siyo maku kuje kuci." Da murna suka shige ciki. Bilki tana murmushi tace "Yaran nan na shan gata Alhaji, kana tunanin baiyi yawa ba kuwa?" Alhaji yayi murmushi yace "Bilki kenan, ay ba wani abu nake musu na gatanci ba, bana sangarta su, haka ma bana 6ata su da kud'i ko wani abin duniya, abinci ne nake basu wanda kuma yin hakan ba laifi bane." Tayi murmushi "Bakayi laifi ba kam nima dama wasa nake maka." Sai kuma yayi ajiyar zuciya "Kinsan abinda ke damuna?" Tace "Sai ka fad'a." Yace "Mutuwar Alhaji Adam, su waye marassa imanin da suka bishi har gidanshi suka kashe shi dashi da matarsa?" Bilki ta had'iye miyau da k'yar tace "Nima abinda yake damuna kenan kullum Alhaji, nasan mahassada ne kawai." Ya numfasa "Wai me duniyar nan keso ta zama ne? Mutane akan kud'i ba abinda bazasuyi ba?" "Uhm...uhm Alhaji bari na kawo maka ruwa kasha." Bai kawo komai a ransa ba yace "To." Aikuwa da daddare Meenah bata samu abincin dare ba, wai ay taci kaza ta k'oshi bataga dalilin da yasa za'a bata abinci ba. Da safe Baban na fita aiki ta jibga mata uban wankinta dana Zarah, duk da suna da mai wanki amma tsabar mugun hali irin na Bilki sai da ta jibga mata wankin daya fi k'arfinta. Tana gama bata wankin ta shigo daidai bakin k'ofa taci karo da Zarah tana fad'in. "Mami idan Baba ya dawo sai na fad'a masa abinda kike ma Meenah idan baya nan..." Finciko ta taji anyi, tayi d'aki da ita tana zuwa ta shiga tsula mata bulala, sai data zane ta tas sannan tace "Wannan kad'an nayi miki akan bayan kin fad'a masa, sai jikinki ya gaya musu, zaki fad'a ko kuwa?" Da sauri ta girgiza kanta tana kuka. Haka dai kwanaki sukayi ta tafiya cike da wahala a gurin Meenah, sam batada lokacin kanta sai aikin gida, bata samun lokacin karatu sai can cikin dare, sheyasa gata nan wata 'yar ficit sai tsawo amma ba kumari, Zarah kuwa wata 'yar duma duma ga ta fara sol fatar jikinta irin ta 'yan hutun nan ce da basu san wahala ba, ita kuwa Meenah batada k'iba sai tsawo. *** A haka rayuwar tayi ta mirginawa, har Meenah ta kai SS3 a yayinda Zarah ke SS2, yaran sun girma sun zama 'yan mata, daka gansu tare sai ka k'ara kallonsu don kuwa ko a makaranta tare sukeyin komai, shiga aji kawai ke raba su. Halayen nasu ne kawai ya banbanta, ita Meenah tana da wani calm attitude, tanada nutsuwa komai nata a hankali takeyinsa, ko maganarta wani a hankali takeyi, ba kamar Zarah da take abu kazar kazar ba, ita tsaye take kamar ba mace ba, she's too lousy dai tana da hayaniya.... Sannan uwa uba Meenah ba irin girkin da bata iya ba, da kuma ko wane irin aiki yi take irin su shara wanke wanke, wanki da sauransu, kuma bata gajiya da gyara wuri koda za'a shekara ana 6ata shi, Meenah bata damu da abin duniya ko wayar da take rik'ewa batada komai na social media a ciki, ita dai kawai tayi waya idan ta kama shikenan, amma Zarah akwai son harkar social media, ga yin hoto kamar hauka, to a wannan fannin ne halayensu suka banbanta, ga son jiki bata iya ta6uka komai na aikin gidan saboda haka ta taso ba'a sata tayi, sheyasa ko gyaran d'akin bata iya ba, sai Meenah tazo ta gyara mata... AUREN FANSA 14 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Susu, thank you for everything!❤️ 🌹14 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bakajin komai a d'akin sai k'yalk'yatar dariya, da k'yar suka dakata, Laila ce ta soma magana. "Shegiyar gari, wato kina nan kina facaka cikin dukiya, kina nan kina taka matsayin da kika d'ad'e kina burin takawa, kina nan kina hawa kud'i ki taka kud'i ki yadda kikeso a cikinsu, lallai shawara d'aukar d'aki yau gashi mun da'auka tayi mana amfani!" Suka sake sa dariya, Bilki tace "A da na bijirewa shawararki, kuma da farko na tsorata amma yanzu abin sai wanda ya gani." Suka sake sa dariya gami da tafa hannu. Laila ta kuma cewa tana dariya "Yayi daidai kin birgeni! Yanzu keda talauci sai dai ko a lahira..." Bilki tace "Kada Allah ya had'ani da shi koda a lahirar ne ma. Yanzu tsoro na kada wata rana a gano mu ya zamuyi kenan?" Laila tace "Daman ay ke bugun Abuja ce, daman ke kalarki bata k'auye bace ba..." Bilki tayi dariya "To kin dai gani, rabona da k'auye har na manta, tunda muka dawo Abuja idan kin ganni k'auye sai dole..." "Assalamu Alaikum..." Ta shigo d'auke da tray d'in lemo da glass cups guda biyu sai plate d'in cincin da dambun nama. Ta ajiye tray d'in sannan ta gaishe su, sai da suka watsa mata harara sannan suka ce "Lafiya." Bilki tace "Kin d'ora abincin rana?" Tace "A'a yanzu zan d'ora." Bilki tace "Aikin me kike da tun d'azu baki d'ora ba har kusan k'arfe sha biyu?" Tace "Wanke wanke ya taru da yawa shine na..." "Yi min shiru a nan!" Ta daka mata tsawa. "Duka duka wanke wanken guda nawa ne da har zaki ce yayi yawa? Sai anyi magana ki dinga rissina kai kamar wata yarinyar kirki, zaki wuce ki d'ora ko sai na san me zan miki!" "Uhm... me za'a dafa?" Tayi tsaki "Ki dafa mana fried rice da peppered chicken, sai ki had'a coleslaw, akwai kaji a freezer ki d'auki guda biyu kiyi amfani dashi. Sai kinsan halin babanku yafison tuwo, kiyi masa tuwo miyar busassar ku6ewa." Da k'yar tace "To." Ta fice idanunta cike da hawaye! "Anya bataji mu ba d'azu?" Cewar Laila cike da damuwa. "Ko taji me za'ayi? Ah babu ay." Sukayi dariya Laila tace "Haka ne fa." Tana kitchen tana yanka kaji Zarah ta shigo tana sanye da wando jeans sky blue sai light pink shirt marar hannu. "Meenah zo ki ga..." Da mamaki take kallonta tana d'aga mata fuska don taga idan idanunta ba k'arya suke nuna mata ba. "Meenah kukan me kike? Hala Mami ce? Me tayi miki?" Ta k'ak'alo murmushin dole tace "Babu komai, wani abu ya fad'a min ido ne." Zarah tayi murmushi "Uhm baki iya k'arya ba Meenah, ni nasan wani abu Mami tayi miki." Meenah tace "Bakomai amma don Allah Zarah zan miki tambaya inaso ki fad'i man gaskiyar abinda kika sani." Zarah tace "Ina jinki." Meenah tace "Don Allah a iya zamanki a gidannan kin ta6a ji koda a wurin wani ne cewar tsintso ni akayi?" Zarah ta k'yalk'yale da dariya harda duk'ewa, Meenah ta kalleta galala cike da mamaki tace "Meye haka wai Zarah? Ya ina tambayarki kin tsaya kina min dariya?" Har yanzu dariya takeyi, da k'yar ta tsagaita tana duban Meenah tace "Anya baki buk'atar ganin likita Meenah? Kanki d'aya kuwa?" Meenah ta k'ule tace "Shikenan sai kije kiyi ta dariyar, gani kike kamar wasa nakeyi ko?" Zarah tace "Daman ay wasan kikeyi, ta yaya ma zaki fara irin wannan tunanin?" Meenah tayi murmushi mai ciwo tace "Dole nayi tunanin haka Zarah, na rasa meyasa Mami bata sona..." Da sauri Zarah ta rufe mata baki "Kar kice haka, ay indai zaki kula halinta ne haka, koni tana min." Meenah tace "Eh amma ba kamar yadda take min ba, dole ne na fara tunanin duk yadda akayi ko tsinto ni akayi ba'a san asali na ba, ko kuma ni 'yar rik'o ce." Zarah ta 6ata rai "To yayi miki kyau, ki cigaba da fad'in haka ni kuma daga yau na daina miki magana a gidannan." Meenah ta juyo da sauri "Haba dai?" Zarah tace "Ki cigaba ki gani." Da sauri Meenah tace "La na bari, ya za'ayi na bari mu 6ata?" Zarah tayi murmushi "Yawwa sweet sis bara na taya ki aikin don ayi sauri, kuma idan kika hanani yi sai na daina miki magana a gidannan." Ta fad'a cike da shagwa6a, Meenah tasa dariya ta kwaikwaiye ta "To bazakiyi ba wuce ki tafi ki kwanta." Zarah tace "Nak'i" Haka suka k'arasa aikin suna zolayar juna, wasu abubuwan sai da Meenah ta dinga koya mata, kuma ba laifi tana fahimta. *** "Wai bazakuyi sauri ku fito ba Jidda? Kodai a tura driver ya d'auko su ne?" Da sauri Anisah ta fito cikin shigar atamfa d'inkin doguwar riga kalar blue and purple sa ta d'ora purple mayafi. "A'a Mama mu zamu d'auko su, nifa na gama shiri su ya Jidda ne tun d'azu basu gama ba." Mama tayi dariya. "Au kin k'agu kiga yayan naki hala? Wannan irin zakwad'i haka?" Anisah dariya, daidai nan sauran 'yan matan suka fito sun sha ado sunyi kyau inda dukansu suke cikin shiga iri d'aya. Yusra tayi dariya "Kai Mama duk kin k'osa a dauko miki yaranki ne haka?" Mama tayi dariya "Ke ni ba kakarki bace, ku wuce ku tafi haka nan." Da sauri suka tafi suna dariya... Jidda ta dubi agogon dake mak'ale a hannunta, k'arfe sha biyu harda rabi ta wuce. "La Ibrahim kayi sauri sun kusa sauka." Ibrahim yayi murmushi "To ranki ya dad'e." Tunda suka dira a airport hankalinsu ya kwanta ganin har yanzu basu sauka ba, amma daga inda suke suna hango jirgin yana niyyar sauka k'asa. Duk sukayi ajiyar zuciya. A hankali jama'a suka fara fitowa daga jirgin, haka ma duk wanda ya hango d'an uwansa sai ya ruga ya taro sa. Tsaye suke kusa da kujerar zama wato (waiting chair) idonsu k'yam saitin k'ofar jira kawai suke suga ta inda zasu 6ullo. AUREN FANSA 15 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹15 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Ba'a fi minti biyar ba suka kunno kai, ko wanensu yana tura trolley nasa, tunda suka fito Jidda ke kallonsa ya za'ayi ta mance da wannan fuskar? Ya chanza gaba d'aya ya zama wani babba, k'irar jikinsa kansa abin kallo ce irin giant d'innan, abinka ga fari sai ya k'ara murjewa ya zama bature sak! Ta kalleshi yana murmushi. "Sannu da zuwa yaya!" Anisah ta ruga tare da mak'alk'ale shi, a yayinda Yusra ke mak'ale da nata ya'yyen, sai a lokacin Jidda ta dawo duniyar tunani. Da k'yar ta daidai nutsuwarta tace "Sannunku da zuwa!" Ko alama bai gane ta ba. "Yauwa sannu... Jidda ko?" "Wow haka muryarsa take?" Ta fad'a tana k'ara kallonsa cike da mamaki. Tace "Eh nice yaya." "Wow duk kun girma..." Suka taya su jan kayan nasu har bakin mota. Tafiya suke amma idonta na kansa. Abu d'aya take maimaitawa a zuci... "What kind of change is this?" Haka aka loda kattunan jakunansu a boot. Koda suka shiga mota shi ya zauna gaba, daga baya babu abinda Jidda keyi sai aikin kallonsa. "Ya Faruk? Ya Faruk? Ya Faruk?" Wannan abu shi take ta fad'i a ranta. Ta d'an k'ara kallonsa ta baya, gashin kansa kad'ai abin kallo ne, ya k'ara kyau akan wanda yake dashi da, sai shinning yake kamar taurari a sama... "Anya bayada iri da larabawa?" "Wa kenan?" Ta kai dubanta tana kallon Najeeb daya tsareta da kallon tuhuma, tace "Uhm uhm bangane ba." Nabeel yace "Rabu da ita tun d'azu na lura da yadda ta chanza." Tace "Na chanza kamar ya?" Najeeb yasa dariya. "Kamar yadda kika fahimta." Daga nan ba wanda ya tanka har suka iso gida. Mama harda d'an gudunta tana fad'in "Welcome home." Suka shiga parlor Najeeb ya kalli matan yace "Ku kai mana kayanmu d'aki." Sannan ya maida kallonsa da Mama. "Bari mu d'an watsa ruwa muyi sallah." Mama tayi murmushi "Eh hakane lokacin sallar azahar yayi ya kamata ayi sallah sai aci abinci, sannunku da hanya." Nabeel yace "Yauwa Mama, ina Dada?" Tace "Yana Ireland yau

Chapter 6 of 11