Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har sunyi aure da Faruk... *** Da sallama ya shigo parlon tana zaune kan kujera tana kallo, tana ganinshi ta mik'e tana murmushi sosai ta k'arasa wurinsa tace "Sannu da dawowa my soul." Ta fad'a tana amsar ledojin da ke hannunsa. Ya kalle ta tana sanye da army green Indian sari d'inkin riga da wando, kayan sun matuk'ar amsarta, fuskarta babu wata kwalliya don Meenah ba ma'abociyar yin kwalliya bace bata ma iya ba, hakan yasa kullum fuskanta take fresh gwanin kyau, d'ankwalin kayan kuwa yana d'aure akanta d'aurin ya zauna daram a kanta. Haka kawai kuma sai ta basa tausayi, ganin mummunna labarin da zai fad'a mata, yana tunanin yadda ma zata d'auki maganar. "My soul inata magana kayi shiru." Ya susa kai yana k'ak'alo murmushi yace "Ohh sorry baby, banji ba me kika ce?" Tace "Nace muje na saka maka ruwan wanka kayi sai kaci abinci." Yace "Ok ok bismillah muje." Tana gaba yana biye da ita, duk wani motsi nasa akan idonsa haka kazalika k'amshin turarenta duk ya cika masa hanci hakan ya haifar masa da kasala, jikinsa ya mutu. Suna shiga d'akinsa yau a karo na farko data ta6a shiga, simple d'aki ne mai d'auke da black gado duka furnitures d'in dake d'akin black ne, hartta wasu 'yan kujerun hutawa guda biyu da table tsakiyarsu suma black ne, carpet black, sai paintin d'akin ne kawai yake fari k'al hakan ya haskaka d'akin. K'amshi gami da sanyin ac kuwa sun had'u sun mata sallama. Kan gado ya zauna a yayinda da ta shige toilet nasa ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Tana fitowa tace "My soul ga ruwan can na had'a maka, idan ka fito ina parlor." To kawai ya iya cewa shi duk jikinshi a mace yake ya rasa dalili. Bayan ya fito ya kimtsa cikin kayan baccinsa kalar dark blue, ya fesa turare mai sanyin dad'i ya fito. Tana zaune a parlor tana jiranshi, yana zuwa ta mik'e tana murmushi tace "Har ka fito my soul? Ga abinci nan na girka maka." Yayi yak'e yace "Thanks my baby." Tare suka zauna ta shiga zuba masa tuwon shinkafa miyar ku6ewa d'anya da k'ashin rago a ciki sai man shanu, bayan ta zuba masa da tsiyaya masa lemon kwakwar da tayi masa a glass cup, sai taja kujera tana fuskantarsa, a natse ya fara cin abincin sai dai gaba d'aya hankalinsa ba'a kwance yake ba. Ya kalle ta yaga hankalinta a kwance tana kallonsa, ya k'ak'alo murmushi yace "Baby bangane ba ke bazakici abincin bane?" Tayi murmushi tace "Zanci amma ina so sai kaci ka k'oshi tukunna." Ya kalleta cike da mamaki yace "Sam ban yarda ba, idan bakici ba nima bazan ci ba." Da sauri tace "Haba dai? To zanci." A tare suka ci abincin bayan sun kammala ta gyara wurin. Tana kitchen tana d'auraye plates ya kirata. Ta fito tana zuwa yace. "Baby zauna ina son magana da ke." Tace "to." Ta zauna. Ya had'iye wani miyau mai d'aci tukunna ya fara magana. "Meenah kinsan dai ina sonki ko?" Da mamaki tace "Sosai ma my soul, nasan kana sona amma lafiya?" Yace "Kuma kinsan dai ina k'aunar ki ko?" Tayi murmushi "Nasani." Yace "Yawwa, kinsan kaddara mai kyau da marar kyau ko?" Tayi dariya mai cike da mamaki tace "Nasani mana." Yace "Kinsan kuma dai kowa da tasa kaddarar Meenah, maganar da zan fad'a maki tana da nauyi, amma ina so badan ni ba don Allah da kuma soyayyar da kike min ki fahimce ni." Jiki a sanyaye tace "Don Allah my soul ka fad'a min ko meye, sai kwana kwana kakeyi." Yayi shiru cikin nazari, can yace "Hakane zan fad'a maki amma ina so kiyi min alk'awari guda d'aya." Tace "Na me?" Yace "Bazaki d'aga hankalinki ba sannan bazakiga laifi na ba." Gabanta yayi mummunan fad'uwa, tace "Don Allah ka fad'a min my soul ka barni a duhu don Allah." Tashi yayi tsaye yana mai juya baya don ya kasa ma had'a idanu da ita. Da k'yar ya iya tattaro kalamunsa wuri d'aya, yace "Auren zan k'ara Meenah..." A gigice take kallonsa, kanta yayi wani dum! Nuna sa takeyi da hannu tana fad'in "Anya naji da kyau, sake maimaita mini." Yace "Kiyi hak'uri haka d'in dai nace, aure zan k'ara." "Innalillahi wa inna ilahir raj'iun." Take kuma gumi ya dinga sassarfo mata ta ko ina, kafin kuma taji wani irin kuka ya taho mata cikin tashin hankalin ta fasa ihu sai dai yaji abu ya fad'i k'asa tim! AUREN FANSA 28 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Wannan page d'in nakune members na MARZAH HAUSA NOVELS, nagode da k'aunar da kuke nuna min, Allah ya bar zumunci amin❤️ 🌹28 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Da sauri ya juya abin mamaki wai Meenah ce kwance kamar ba rai, a gigice yayi kanta ya shiga jijjiga ta, abin mamaki ko alamar motsi babu a tattare da ita. Tunda yake a rayuwarsa bayan mutuwar iyayensa bai ta6a tsintar kansa cikin matsanancin tashin hankalin irin wannan ba, ya rud'e ya shiga tashin hankali mai wuyar fassara. Da gudu kuma yayi dinning ya d'auko robar ruwan sanyi ya shiga bud'ewa har wani kyarma yakeyi. Yayyafa mata ya dinga yi amma ba alamar zata farka, hakan yasa ya juye mata shi gaba d'aya a fuska, aikuwa take ta saki ajiyar zuciya sannan ta bud'e idanunta wanda suka kad'a sukayi ja kamar garwashi, tarr take kallonsa kamar sabuwar halitta, shi d'in ma ita yake kallo babu ko k'yaftawa, a hankali ya sure ta in banda sannu babu abinda ke fita a bakinsa. D'akinsa ya wuce ya shimfid'ar da ita kan gado sannan ya nemi wuri ya zauna gefen ta har yanzu ita yake kallo. "Sannu Meenah... ya kike ji yanzu?" Kauda fuskarta tayi daga kallon da take masa zuwa d'ayan 6angaren sannan kuma hawaye suka shiga kwarara daga idanunta masu zafin gaske. "Meenah..." Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa. Hannunta ya kamo duka biyun yana murzawa, runtse idanunta tayi a take kuma wasu hawayen sukayi nasarar saukowa, tana cikin mawuyacin hali mai wuyar fassara, ita kad'ai tasan me takeji a halin yanzu. "Tabbas nasan dole kiji ba dad'i, nasan kin fara tunanin bana sonki ko? Sheyasa nace zan k'ara aure ko Meenah? Ina so ki fahimce ni Meenah har yanzu ina sonki kuma ina k'aunarki babu abinda ya chanza, auren da kika ga zanyi yana d'aya daga cikin kaddara ta, ina so a matsayinki na musulma ki d'auki kaddara Meenah, kawo wata mace cikin gidannan bazai chanza son da nake maki ba, nidai fatana ki yarda kuma ki amince don bazan iya k'ara aureba ba tare da kin amince ba." Fuskarta ya shafa ya cigaba "Wallahi ko yanzu kika ce kar nayi aurennan na fasa kenan ko da kuwa yanzu za'a d'aura shi, kuma ko wacece zata shigo cikin gidannan zan zamo mijin da zai kare miki martaba da kuma mutunci, har abada bazan wulak'anta ki ba, nidai fatana inji ta bakinki a halin yanzu Meenah..." Wani gumi ya ziyarce ta, wato dai da gaske kishiya zai mata kenan? Ita kam batada sa'a a rayuwa, ta taso tun tana k'arama tana d'and'ana bak'in ciki a koda yaushe ba kwanciyar hankali, tana tunanin auren da zatayi hutu ne a gareta ashe tayi kuskure. Sai dai kuma dole zatayi hak'uri tunda haka Allah ya kaddara mata ita kam. Ta yunk'ura ta tashi zaune tana mai share hawaye duk da kuwa wani na bin wani amma dole ta share, kanta kuwa kamar ana sara mata guduma haka takeji. Cikin wata irin muryar data dishe tace "Haba my soul, meyasa sai ka nemi izini a wurina sannan ka k'ara aure? Ka manta Allah ya halasta maka daga mace d'aya zuwa hud'u? Bana cikin irin matan da idanunsu ke rufewa da kishi har su fad'a halaka, Allah ya halasta maka aure ni wacece da zan hana? Ay ban isa ba ma." Tayi murmushi mai ciwo ta cigaba. "Ba k'arin aurenka ya fi d'aga min hankali ba, kasan me ya tada man hankali?" Yace "A'ah." Tayi murmushi "Wai ace aurenmu da ko sati ba'ayi ba amma ace zakayi aure, sannan kuma ina tsoron ka daina sona ne sheyasa ko kuma ka gaji dani." Yace "Haba my baby, kima daina irin wannan tunanin har yanzu ina sonki, kuma insha Allah zan cigaba har in mutu." Tayi murmushi "Na yarda da kai my soul, kuma ina alfahari da kai a matsayin mijina, a koda yaushe ina gode ma Allah da ya bani mai sona mai kuma k'aunata, idan aurennan alkhairi ne Allah ya tabbatar, idan ba alkhairi bane ba Allah ya za6a maka mafi alkhairi." Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya lumshe idanunsa kafin ya bud'e, ya kalle ta cike da sha'awa! Tunda yake a rayuwarsa bai ta6a cin karo da mace makamanciyar wannan ba. Matsowa yayi dab da ita yace "A gaskiya kafin a samu mace irinki a wannan zamanin sai an tona Meenah. Nima ina so ki sani ina sonki ina k'aunarki sannan ina alfahari da ke a matsayin matata." Duk da tana cikin wani hali hakan bai hanata yin murmushi ba, ta yunk'ura zata tashi jiri ya kwashe ta, da sauri Faruk ya taro ta sai kuma ta fad'a jikinsa haka ya rungume ta kamar wata jaririya. Wani shock ya kama ko wanensu, sannan kuma suka dubi juna cikin ido. Sun kai minti kusan d'aya a haka kafin Meenah ta fara kauda tata fuskar tana k'ok'arin tashi daga jikinshi. Duk ya dabarbarce, kwanciya tayi sakamakon wani bacci da taji yana neman kwasar ta. Duka duka batafi second goma ba bacci yayi awon gaba da ita. Jikin Faruk yayi matuk'ar sanyi, sannan kuma take ya fara tsintar kansa cikin wani irin yanayin da bai ta6a tsintar kansa a ciki ba. Wani abu yaji yana bin dukkanin illahirin jikinsa tun daga kansa har zuwa tafin k'afarsa, take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr! "Hasbunallahu wani'imal wakil." Shine abinda yake fad'i, sannan ya mik'e jiki a sanyaye ya fad'a toilet, a gaban sink ya tsaya tare da bud'e pampo ya shiga wanke fuskarsa, bayan ya gama sai ya tsaya yana kallon kansa kuma ta mirror, ba abinda idanunsa ke gani kamar fuskar Meenah, wani gurin tana murmushi wani gurin kuma dariya, tsintar kansa yayi yana mai murmushin shima. Da sauri kuma ya girgiza kansa ya fice daga toilet d'in yana ta faman maimaita "No." Kwanciya yayi gefenta tare da rufe idanu yana jin wani bak'on al'amarin da bai ta6a ji ba a tsawon rayuwarsa ba.... Sassanyar iskar asuba mai k'unshe da ni'ima tare da tarin albarka shi ya daki fuskar Meenah kasaancewar tagogin d'akin a bud'e suke. Hakan yasa taja dogon numfashi tare da motsawa, tayi tsawon minti biyu a haka kafin a hankali ta fara k'ok'arin tashi zaune. A natse ta juya tana maida kallonta kan Faruk da baisan inda duniyar take ba. Tuni abinda ya faru jiya ya fara dawo mata, nan ta yunk'ura cikin k'arfin hali ta mik'e duk da batajin k'arfin jikinta, kasancewar tana fashin sallah sai ta taka a hankali zuwa jikin window. Hadari ta gani sosai, iskar damina had'e da yayyafi ya daki fuskarta, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba, tayi ta shak'ar iskan gami da ware hannayenta don ya ratsa ta sosai, take taji ta samu k'arfin jikinta fiye da dah. Ruwan saman ne ya sauko mai k'arfi, ta mik'a hannayenta duka ta tari ruwan. K'arar ruwan saman ne ya farkar da Faruk, idanunsa k'yam a kanta, sai yau ya ta6a ganinta ba d'ankwali, gashin kanta ya zubo har bayanta hakan ya faru ne saboda cirewar ribbon d'inta jiya da daddare. Kanta a nannad'e yake kamar na jarirai gashj bak'i wuik! Yayi zumbur ya mik'e tare da duba time ganin lokacin sallar asuba yasa ya mik'e da sauri ya nufi toilet. Har ya gama sallarsa a d'aki Meenah batasan yanayi ba. Tana can tsaye tana kallon ruwa na sauka k'asa, abin burgeta yake tun tana k'arama, ita dai rayuwarta tana son ruwan sama yanzu haka ji take kamar ta shiga ciki tayi wanka. A hakan ya cigaba da kallonta wanda baison yana yi ba. "Ina kwana." Ta fad'a gami da zama gefen gado. Yayi murmushi "An tashi lafiya? Ya k'arfin jiki?" Tace "Alhamdulillah." Har yanzu kallonta yake ganin ba wani yanayi na damuwa a tattare da ita dangane da maganar jiya ba. "Lokacin dana suma jiya kasan me ya kamata kayi min amma ka kasa sai rud'ewa, ashe dai kana sona haka?" Take gabansa ya fad'i, ya rasa dalili da ta ambaci yana sonta sai ya tsinci kansa da fad'uwar gaba? Yana jiyo dariyarta har cikin kansa. "Yanzu dai ina so ka fad'a min kai da ka ganni cikin wani irin yanayi ka rasa abinyi saboda kana tunanin ko mutuwa nayi? Ashe kana tsoron rasa ni?" Ta k'arasa maganar tana dariya. Yayi dum, sannan ya mik'e ya zauna gefenta tare da rik'o hannunta yace. "Ay dole na tsorata tunda ina ganin zan rasa masoyiyata ta hak'ik'a." A zahirin gaskiya baisan ya furta wad'annan kalaman ba... Don haka sai yayi saurin tashi tsaye yana fad'in "Bari nayi wanka yau zan fita office da wuri." Da mamaki ta kalleshi "Yanzu fa k'arfe shidda." Yace "Eh wurin bakwai nakeson barin gidannan." Tace "Ok bari na had'a maka breakfast kafin ka fito." Da sauri ya tsaida ta "A'a kar ki wahalar da kanki tunda bakyajin dad'i." Tayi dariya "Haba ba wani wahala bari yanzu zan gama." Bata jira amsar sa ba ta fice da sauri. Ya dad'e tsaye a wurin kafin yayi saurin shigewa toilet. MSB💖 AUREN FANSA 29 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Anty Zee and AishatFareeda❤️ nagode da k'auna😍 🌹29 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan ya gama shirinsa yayi breakfast sai ya fara k'ok'arin fita, ba yadda Meenah batayi dashi ba akan ya hak'ura a gama ruwannan yak'iya yace aikin da zaiyi yana da mahimmanci sosai. Haka nan ya d'auki umbrella ya fice cikin ruwannan. Bayan ya fita kuma ta hau aikin gida kamar kullum, ta kimtsa ko ina ta turara gidan da tuararen wuta ta bi da freshener ta fesa ko ina. Tayi kalacinta bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin wani simple lace kalar sararin samaniya (sky blue) da pink. Tana shirin d'aura d'ankwali wayarta ta fara ringing, ganin Zarah yasa tayi murmushi ta kara a kunne. "Assalamu Alaikum..." Zarah tayi murmushi "Wa'alaikumusalam, ya kike?" Meenah tace "Uhm bansani ba bayan kin manta dani ma." Zarah ta d'anyi dariya tace "Haba sis, ni na isa ne? Gani nayi bai kamata na takura miki ba nasan kina can kina cin amarci yadda ya kamata, ba kya buk'atar takura..." "To aku sarkin magana ya isa haka, ya garin ya su Mami?" Tace "Suna nan lafiya, daman kiranki nayi naji idan kina gida zan biyo, daga school nake ance admission ya fito shine naje na dubo mana..." Cike da murna Meenah tace "Haba don Allah? Munci?" Zarah tayi dariya tace "Oho sai nazo dai, amma ina fatan ango baya gida don wallahi idan yana nan zan wuce gida kawai." "Haba mana Zarah wallahi baya nan kizo ina kewarki da yawa." Zarah tayi murmushi "Nima haka sai nazo." Da haka sukayi sallama. Minti sha biyar tsakani Zarah ta iso, rungume juna sukayi suna murna, Meenah ba k'aramin dad'in ganin Zarah tayi ba. Can ta shiga kawo mata kayan motsa baki su lemo da cake, su dambun nama da sauransu. Meenah tayi murmushi tace "La Zarah kinga yadda kika jik'e kuwa? Meyasa kika fito cikin ruwa? Ki shiga d'akina ki cire wad'annan kayan ki saka nawa." Tace "Tab kayanki sun mani kad'an ay." Meenah tace "Inji waye? Akwai wanda sukayi min yawa ay." Zarah tace "To." Tunda Zarah tazo take bin Meenah da kallo, har dai Meenar ta tsargu a lokacin da take tsiyaya mata lemo a cikin glass cup, bayan ta gama ta koma ta zauna tana kallon Zarah tace "Wai lafiya kike min wannan irin kallon haka?" Zarah ta zuba mata idanu, kafin kuma ta saki ajiyar zuciya tace "Meenah gani nayi kin rame sosai, akwai abinda ke damunki ne?" Meenah tayi murmushin da bai kai zuci ba tace "Babu komai me kika gani?" Zarah tace "Haba Meenah, tsawon shekarun da muka d'auka tare da ke nasanki, nasan idan kina cikin matsala ko akasin haka, kuma a matsayina na k'anwarki bai kamata ki 6oye min abinda ke ranki ba Meenah." Meenah taja ajiyar zuciya tace "Hakane, bawai na 6oye miki abinda ke raina bane, kawai abinda zan fad'a ne nasan zai rud'a ki had'e da mamaki marar misaltuwa." Da mamaki Zarah tace "Niko zanso inji menene wannan da zai rud'a ni haka zai kuma bani mamaki." Meenah tace "Uhm bari kedai, to ki nutsu kar ki rud'e dan Allah Zarah, to ba komai bane ba illa wai Faruk zai k'ara aure..." Lemon da ta kai bakinta shi yayi sanadiyyar k'warewar da tayi hakan yasa ta dinga tari, da k'yar Meenah ta dinga bata ruwa har tarin ya tsaya tana ta faman yi mata sannu. Sai da ta nutsu Zarah tace "Wai wane Faruk d'in tukunna Meenah?" Meenah ta d'anyi dariya tace "Akwai wani Faruk da kika sani bayan mijina ne? Shi dai nake nufi Faruk da na aura a matsayin mijina to shine zai k'ara aure." Salati Zarah ta shiga yi cikin tashin hankali sannan tace "Faruk dai your soul Meenah? Wai aura fa kika ce? To kuma shine kika zauna kamar baki damu ba?" Meenah tayi murmushi "To ya kikeso inyi? Kashe kaina zanyi ne? Abinda Allah ya kaddara waya isa ya hana? Nidai na rungumi kaddara kuma ina fatan wadda zai aura mutuniyar kirki ce, sannan ina fatan bada tashin hankali zata shigo min ba, amma nidai idan mijina na sona banida matsala." Zarah nata kallonta tana magana cike da mamaki, sai data gama Zarah tace "Lallai an gaishe ki Meenah, kinyi k'ok'ari sosai, ba kowace mace bace zatayi abinda kikayi ba, ni gaskiya inda nice bazan yarda ba, sai anyi tashin hankali ba kad'an ba, tab kishiya fa lallai!" Meenah tayi dariya. "To Allah ya kyauta dai, kedai kiyi ta addu'a Allah ya baki miji na gari shine kawai. Wai shin ina Nabeel kuna ta shan soyayya ko? Kuma yana zuwa zance ko kuwa?" Zarah tayi dariya "Han! Kin cika ni da tambaya wane zan fara amsawa?" Suka d'ara su duka, Meenah tace "Duka zaki amsa mana." Zarah tayi murmushi mai bayyan hak'ora tace "To Nabeel yana nan lafiya lau, yana ta zuwa wurina and kuma Baba yace ya turo iyayensa." Cike da murna Meenah tace "Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi Zarah." Tace "Amin... yauwa Meenah ina za'a samu mai aiki?" Meenah tace "Mai aiki kuma? Me za'ayi da ita?" Zarah tace "Mami mana, ta matsa ita 'yar aiki takeso, wai gwara ta samo don idan nayi aure nima babu kowa gidan." Meenah tace "To kin ta6a ganin na samo masu aiki ne? Amma zan tambayi Faruk ko yasan inda ak An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11