Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aka fara gagarumin shagalin biki Musamman ma cikin gidan sarautar inda anan ne akafi shagalin bikin Inda jawwas da suraif suka fito suka caba ado na musamman, suka jero tareda amarensu suna tafiyar kasaita bayan kuwa fadawa ne suketa faman busa kakaki, da take musu baya Koda jama'ar gari suka hango tahowarsu sai duk suka fara mika musu gaisuwa tareda kirari Ba tareda bata lokaci ba aka fara gudanar da shagalin biki inda su sarki suraif suka fara rabe raben makudan kudade da tufafi na alfarma ga talakawansu Inda a gefe guda kuma kuyangi ne suketa yawon raba abinci da abinsha ga mutanen dake A tsakiyar fadar kuwa Wasu tsala tsalan 'yan mata ne cikin shigarar banza suketa tikar rawa, makada nayi musu busa da kida Nanfa guri ya rincabe da jama'a kowa na farinciki, wasu kuwa tuni sun bugu sun fara layi saboda buguwar da sukayi da barasa Su kuwa an gwaye da kansu ne suka dinga raba kyaututtuka ga talakawa nadaga kyautar dirhami da kayan sawa da abinci ga talakawa Kai saboda farinciki a wannan rana sai ka kasa gane wanene angon A wannan rana dai anyi gagarumin shagalin bikin da ba'a taba yin kamarsa ba Acikin birnin gaba Inda aka daura auren attajiri jawwas da wata santaleliyar budurwa mai suna huraisa Haka Shima sarki suraif aka daura aurensa da masruf 'ya a gurin daya Daga cikin hakimansa Bayan an gama daurin aurene kowa ya watse saura angwaye kadai Sannan ne sarki suraif ya shammaci matayen nasu ya dauko wata farar hoda daga aljihunsa ya hura musu ita afuska Take hodar ta shiga cikin hancinsu ta ratsa ta cikin kwakwalwarsu Wanda alokaci guda yanayin fuskokinsu suka caccanja cikin murmushi suraif yace ya kai aminina Yanzu lokaci yayi da zaka dauki matata kaje ka tara da ita na iya Wannan dare sannan nima na dauki taka Kamar yadda boka hulbaz ya shaida mana, dajin wannan batu sai jawwas ya rikice ya kama inda inda ya rasa inda zaisa kansa Yayinda sarki suraif ya lura da halindaya shiga sai kawai ya bushe da dariya daga can ya murtuke fuska yace Haba abokina kai har yanzu baka gama sanin tuggun rayuwa ba , Shin kana tunanin zanyi abinda zai tona mana asirine? Har abada asirin mu bazai taba tonuwa ba, domin a halin yanzu matayenmu duk basa cikin hayyacin su, ba zasu dawo ba har sai zuwa gobe Kaga kenan Babu ta yadda zasu san da abinda muka aikata musu bare su zame mana matsala. Don haka domin kawar da zargi yanzu kuyangi tareda dakaru zasu dauki amaren su kaisu gidajensu Inyaso bayan tafiyar su kai sai ka sanya tufafina ajikinka nima kuma na sanya naka Kai ka wuce dakin amaryata nima kuma na wuce dakin taka Inyaso idan dare ya raba kafin gari yayi haske sai kowa ya koma gidansa yanzu haka na sa, Yana gama fadin haka saiya tafa tafin hannayen sa Faruwar hakan keda wuya sai ga wasu kuyangi guda dari sun shigo Tareda dakaru dari suna shigowa sai suka raba kansu biyu dakaru hamsin, kuyangi hamsin suka Ware daban daban Kaso daya suka tsaya a bayan masruf dayan kuwa suka koma baya huraisa suka tsaya Ba tareda bata lokaci ba wasu dakarun suka shigo da kekunan doki guda biyu suka ajiye Wasu kuyangin suka kama hannun amaren suka sanyasu acikin kekunan dawakan suka fice dasu daga cikin fadar , makada suna ta buga manyan ganguna, har suka kai kowacce daga cikinsu dakinta Fitarsu keda wuya sai su jawwas suka shiga cikin wasu dakuna sukayi musanyen tufafin dake jikinsu sannan kowanne daga cikinsu yayi badda kama Bayan tafiyar dakarun da sa'a guda sai suma suka fice daga cikin fadar kama hanyar tafiya ga matayen nasu Kamar yadda suka tsara, kowa yajewa matar abokinsa A wannan dare suka kwana adakunansu sannan a karshen dare kafin gari ya soma yin haske suka fice daga cikin dakunan Kowa ya koma gidansa ba tareda wani ya ankara dasu ba suka koma dakunan Matayensu na ainihi, har zuwa wannan lokaci Matan nasu basu dawo hayyacin su ba Tun daga wannan rana sukaci gaba da rayuwa da matan nasu cikin kwanciyar hankali kuma a kullum babu abinda suke face tunani da nazari akan yadda zasu kare rayuwar 'ya'yansu daga sharrin boka hulbaz Bayan auren nasu ne da wata guda alamomin samun juna biyu suka fara bayyana ga matayen nasu Nanfa suka kamu da tsananin farinciki mara misaltuwa, don haka da kansa sarki suraif ya tako ya kawowa jawwas ziyarar bazata Yana zuwa kuwa ya iskeshi an zube masa tarin abinci tarin abinci da abubuwan sha yana ci tare da matar sa cikin nishadi Koda ya hango sarki suraif sai fuskarsa ta fadada da murmushi ya taso da sauri ya tareshi Yace lale marhaban da zuwan babban abokina , na sani abindake tafe dakai shine irin yanayin da nima nake ciki yanzu, Zoka zauna mu taya juna barka ba tareda bata lokaci ba ya sami guri ya zauna Suka cigaba da cin abincin tare suna cin abincin suna hira cikin nishadi Suna cikin cin abincin ne jawwas ya dubi huraisa yayi mata nuni da ta basu guri zasu tattauna Ba tareda bata lokaci ba ta tashi ta fice daga turakar Kawai ya dubi sarki suraif yace Ya kai suraif kayi sani cewa daga yanzu zama agaremu ya kare dolene mu mike tsaye mu zage damtse da kyakykyawan tanadi tun kafin zuwan wadannan jarirai Mu don haka ni yanzu na shirya shiga duniya domin haduwa da Wasu manyan bokayen da suke nahiyoyi daban daban, kodajin wannan batu sai suraif ya tuna da maganganun da boka hulbaz ya fada Kodayin wannan tunani sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi cikin sauri yace Gaskiya mun tafka kuskure kuma munyi ganganci da sakaci akan wannan lamari Maganarka gaskiyace ya zama dole mu tashi ayanzu mu tafi cika wannan aiki. Ba tareda bata lokaci ba suka tashi duk su biyun sukayi sallama da matayensu , suraif kuwa ya bada ajiyar karagarsa a gurin matarsa Sannan suka fice daga cikin garin, Tundaga ranar da suka fita suka fara ziyartar manyan bokaye daban daban suna neman sirrikan tsafi daga nahiyoyin dake makobtaka har saida Suka shafe wata takwas suna zagaye kasashen duniya da duk inda suka sami labarin wani babban bokan Yayinda akan hanyar su kuwa suka dinga haduwa da manyan dabbobin daji, 'yan fashi da sauransu Amma da karfin tsiya suraif da hadiminsa suke tarwatsasu Su budawa kansu hanya A sannan ne jawwas yayi nadamar kasancewarsa ba mayaki ba domin dashi kadai ne babu makawa ba zai iya tseratar da rayuwarsa ba Acikin wata na tara ne suka dawo daga tafiyar tasu cikin sululalun dare alokacin garin yayi tsit babu sautin da kakeji face na karnuka sai kuma dakarun da suke gadi Basu sauka ako'ina ba sai tsakiyar birnin, sautin kada fuka fukan aljanin saida ta haddasa wata 'yar karamar guguwa Wacce karfintane ya fargar da dakaru zuwansu Cikin sauri dakaru sukazo cikin girmamawa suka tarbesu suka rakasu har gidajensu ba tareda sauran jama'a sun ankara ba Yayinda jawwas ya isa gida acikin wannan dare kwatsam saiya iske matarsa tana nakuda Koda ganin haka sai hankalinsa ya tashi cikin sauri ya tura dakaru suka kirawo masa wata babbar ungozoma Domin tarbar haihuwar Da zuwan ungozoman cikin sauri ta sanya aka kawo mata kayan aiki sannan taja dakin ta rufe Kafin cikar sa'o'i biyu tuni ta haifi santala santalan jarirai guda biyu Koda akazo aka sanar dashi wannan haihuwar take ya kamu da tsananin farinciki ba shiri yaja ungozoman cikin baitul malinsa Yace daga yanzu zuwa wayewar gari na baki duk dukiyar da kika diba acikin dakin nan Domin yau burina ya gama ciki Yana gama fadin haka saiya koma inda huraisa take wacce tuni angyarata cikin koshin lafiya Su kuwa jariran tuni anyi musu wanka Sannan an yanke musu cibiya, har an sanya musu tufafi na alfarma Take ya debi jariran guda biyu yana kwallar farinciki wacce bata taba zuba daga idanunsa ba. Itakuwa ungozoma ba shiri ta fita acikin murna ta samo hayar rakuma ta dawo ta dinga jidar darhami har zuwa wayewar gari bata debi Koda kaso daya bisa goma ba Kashe gari kuwa da sassafe haka ya fito da tarin dukiya ya dinga yana rabawa sadaka ga mabukata Tun suna zuwa karba har saida Suka gaji suka daina zuwa , bayan fitowar ranane ya dauki jariran ya hau keken doki Ya tafi gidan sarauta domin yayiwa sarki albishir Koda isarsa saiya iske shima sarki suraif masruf ta haifi 'ya mace Ba tareda bata lokaci ba suka hadu su biyun suna taya juna murna 'Yan majalisu da dakaru sai zuwa suke suna kawo gaisuwa da taya murna, suna cikin wannan yanayi ne kwatsam sai suka ga gaba daya fadar tayi duhu kai kace dare ne ya raba Nanfa guri yayi tsit kai kace babu wata halitta mai numfashi a gurin Da ganin wannan bakon yanayi take kowa ya shiga taitayinsa dakaru suka fara zare makamai Jim kadan sai duhun gaba daya ya yaye komai ya koma yadda yake a baya Adaidai lokacinne wani bakon boka ya bayyana wanda akalla shekarunsa sun haura casa'in da doriya Saboda tsananin tsufan da yayi har doron bayansa ya fara durkufawa, gashin kansa kuwa gaba daya fari ne babu digon baki ajikinsa Hannunsa na hagu yana ruke da wata sandar tsafi wacce yake dogarawa da ita Kai da ganinsa kasan irin boyayyun bokayen nan ne wadanda suka jima sunayiwa kansu tanadi Koda dakaru sukayi arba da wannan bakon bokan sai gaba dayansu sukayi kukan kura suka afka masa da nufin suyi gunduwa da sassan jikinsa Ba tareda bokan yayi wani yunkuri ba koda ya rage baifi saura taku daya ba a tsakaninsu Sai kawai wata iskar tsafi mai karfi tazo ta zukesu ta watsa su wajen fadar sannan kofofin gaba daya suka rufe kansu Da ganin abindaya faru ga wadannan dakaru sai zuciyar sarki suraif ta fara tafarfasa take yayi kukan kura Tare da zare takobin sa ya afka kan sa da nufin yayi masa zuwa daya Yana zuwa daidai inda yake sai Yakai masa mummunan sara a dokin wuya da nufin ya tsarge wuyan Daga jikinsa Koda takobin ta sauka ajikinsa take ta ratsa shi ta wuce kai kace haske ya sara ba tareda ya sami ko kwarzane ba a jikinsa Cikin zafin nama ya dunkule Hannunsa taredav kara kai masa wani dukan a gefen muka mukinsa Koda Hannunsa ya sauka ajikinsa sai yaji kamar an kwarara masa tafasasshen karfe akan hannun nasa Don haka Baisan sanda yaja da baya ba, ya koma amfani da sihirin tsafin sa Amma sai shima sihirin yaki yayi tasiri akan wannan bakon bokan Bisa mamaki sai yaji bokan ya tuntsure da dariya cikin wani irin sauti mai amsa amo Sannan ya fara bayani kamar haka Haba Yakai wannan jarumin sarki ni banzo gareku da zummar yaki bane kawai nazo ne Da nufin taimakonku akan kudurin daya fitar daku daga birnin Nasan da cewa kun fita kun zagaye duniya inda kuka ziyarci bokaye dari da sittin da biyu Da nufin baiwa jariran ku kariya da kuma sa'a abisa abokin hamayyarsu wanda kuma shine silar zuwansu duniya wato boka hulbaz Har su rigashi mallakar KARAGAR AJALI da kuma SAIFUL LAIHAM Ku sani cewa hakika a halin yanzu yayi mummunan tanadi akan wadannan jarirai wanda idan har ba'a dauki kyakykyawan mataki ba To da zuwansu duniya da kuma wahalar da kuma kukasha akansu duk zasu zama na banza Dajin wannan batu sai jikin suraif yayi sanyi ya mayar da takobin sa cikin kube Yayiwa bokan nuni da wata kujera daya zauna akanta Maimakon bokan yaje inda kujerar take sai suka kujerar ta babbako daga mazauninta ta dawo inda yake tsaye ya zauna akanta Zamansa keda wuya sai suma suma sami guri suka zauna , jawwas yayi gyaran murya daga bisani yace dashi Yakai wannan boka Shin wanene kai kuma menene ke tafe dakai? Dajin wannan tambaya sai yayi murmushi yace da farko dai sunana Hushairul hasnal kuma ni mahaifine ga boka hulbaz, Yaku wadannan manyan mutane ku sani cewa Inbanda na fito daga inda nake zaune nazo nan inda kuke Yanzu haka shekarata hamsin da biyar acikin kogon tsafina ba tareda na fito waje ko kuma mutane su san ina rayeba Tsawon wadannan shekaru babu abinda nakeyi face bincike akan wata karaga wacce akewa lakabi da KARAGAR AJALI tare da lokacin bayyanar ta, Kai harma da wanda zai iya mallakarta kuma yayi amfani da karfin sihirinta Amma har kawo yanzu babu wanda yasan inda take kai a wannan lokacin ma kaf duniya Babu wanda yasan labarin ta face ni kadai Sai aranar dana sanar da dana wato boka hulbaz a wannan lokaci bai wuce shekara bakwai ba Sai bayan na sanar dashi labarinsu ne nadama tazo min domin Nasan dolene yayi kokarin mallakarsu kota wanne hali Idan kuwa har ya mallakesu to babu makawa sai yayi amfani dasu wajen bautar da duk wasu halittu na duniya Saboda zallan rashin imaninsa Tun daga ranar dayasan labarin wadannan abubuwa shima saiya dukufa kan tanadin hanyoyin da zaibi domin mallakarsu Ana zaune wata rana sai na wayi gari hulbaz ya gudu yabar gida Tun daga wannan lokaci ban sake haduwa dashi ba, saidai bincike ya nuna min cewa yanzu haka ya mallaki sihirin tsafi mai karfin gaske Kuma har yaje inda ake tsammanin za'a haifi jaririyar da zata zama silar bayyanar karagar AJALI , Kuyi sani cewa yanzu haka duniya bata Farga da wadannan abubuwa ba Domin babu wanda yasan da batun su face ni sai hulbaz da kuma ku dinnan Bayan haka inaso ku sani yanzu haka hulbaz yayi gagarumin shiri akan jariranku Saidai shirin ba zai fara tasiri ba sai nan da Wasu 'yan shekaru masu zuwa, Kuma ba komai ne zai fara tashinsa ba face mace, babu irin binciken da banyiba Domin in gano wacece ita ba amma na kasa A wannan lokaci gaba dayansu kawunansu zasu rarrabu ya zamana kullum suna farautar juna kamar rana da wata Dare da rana Kowanne kuma daga cikinsu zai dinga fada da dan uwansa ne akan yakinin cewa shine mai gaskiya Kai hatta ku ba zaku iya banbance waye mai gaskiyaba acikinsu daga karshe dai idan har da rabo dole daya Daga cikin sune zai iya mallakar KARAGAR AJALI Kuma a sannan ne daya Daga cikin su zai rasa rayuwarsa, To a wannan lokacin zasu gane kuskuren da suke aikatawa har ma suyi nadama Babu kalar binciken da banyiba Domin gano wanda zai yi nasara , da kuma wanda zai mutu acikin su amma Abu ya gagara Don haka ya zama tilas mu tsaresu daga hulda da mata har zuwa sanda zasu gama mallakar hankalin kansu Idan kuwa har anaso su taso da gagarumin tsaro da karfin sihiri Dolene daga wannan rana a sanyasu acikin kwalaben sihiri na tsawon shekaru shida da wata tara A sannan ne zasu fito da gagarumin sihirin tsafi na ban al'ajabi kuma zasu fito da kwarin jiki kamar 'yan shekara sha hudu Daga ranar da suka fito kuma sai a mikasu inda zasu koyi dabarun yaki na musamman Kodajin wannan batu sai sukayi shiru suka fara kallon juna ba tareda sanin hukuncin daya kamata su yanke ba. SHIN SUNA AMINCEWA DA SHAWARAR BOKA HUSHAIRUL HASNAL? TAYAYA MACE ZATA IYA SHIGA TSAKANINSU KUMA WACECE ITA? SANNAN DAGA INA TAKE? WANENE ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR KARAGAR AJALI ACIKIN SU? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBRKARAGAR AJALI 4*********** PART ********C LBR ***********HABIBULLAH KBR Daga can sai sarki suraif yace Yakai wannan boka to kai menene ribarka idan har ka taimaka mana? Dajin wannan tambaya sai ya ajiye gwauron numfashi sannan yace ni acikin wannan abu babu abinda zai amfaneni Saidai ina da burin ganin mamallakin wannan karaga da saiful laiham da idanuna kafin ajali ya riske ni Idan kuwa har kukayi sakaci ina tabbatar muku da cewa duk wahalar da kukasha ta zama ta banza, don haka ina sauraron hukuncin da zaku yanke Koda yazo daidai nan azancensa sai ya dakata da maganar da yakeyi ya zuba musu idanu Ba tareda bata lokaci ba jawwas ya janyo suraif gefe yace Yakai abokina ka sani a halin yanzu bamu da zabin daya wuce amincewa da wannan boka domin a bokayen da muka ziyarta babu wanda yayi mana irin cikakken bayanin da shi yayi mana , don haka nidai na amince dashi dari bisa dari, Dajin wannan batu sai shima ya gyada kansa yace ainima babu abinda zanyi a yanzu sai yadda kayi don haka na amince Suna gama wannan tattaunawar sai suka dawo inda boka Hushairul hasnal yake sukace sun amince Koda jin amincewarsu sai ya ya kama hannayensu tareda karanta wasu dalasiman tsafi Faruwar hakan keda wuya take sai dukkaninsu suka bace bat daga cikin fadar Basu bayyana ako'ina ba sai cikin kogon tsafin boka Hushairul hasnal wanda ke can kusa da birnin Hindu Da bayyanarsu sai su jawwas suka yi arba da wasu manyan kwalabe guda hudu acikin fadar wacce wani shudin ruwa yake sauka akansu duk bayan dakika goma da zarar ruwan ya sauka akansu sai kwalaben suyi wani irin kara mai kama da an zuba ruwa acikin tafasasshen mai Kodaya lura da irin kallon da suke yiwa kwalaben sai ya dafa kafadunsu yace ku kwantar da hankalinku Wannan ruwa ba mai cutarwa bane agaresu, Bane komai bane face mai amfani agaresu Yana gama fadin haka saiya nuna kwalaben da Hannunsa take duk kwalaben guda uku suka bude kansu, Sannan jariran suka fice daga hannunsu da kansu suka shiga cikin kwalaben Faruwar hakan keda wuya sai akwatunan suka sake rufe kansu ruf tamkar basu taba wanzuwa ba Boka Hushairul hasnal ya sake duban sarki suraif yace Yakai wannan sarki ina bakin cikin sanar dakai cewa daga yanzu ba zaka sake samun haihuwa ba har abada , Kai kuwa jauwas nan da wata uku matarka zata sake samun wani juna biyun wanda zata haifi da namiji Wanda daga shi ba zata sake haihuwa ba Don haka a daidai wannan lokaci kafin ta fara da samun cikin zan tura daya Daga cikin hadimai na Ya sato min dan tayin dake cikinta a sanyashi. Acikin waccan kwalbar da tayi ragowa Ta yadda za'a kyankyashe shi tareda 'yan uwansa kuma su fito duniya tare Don haka a halin yanzu zamu rabu daku ku koma gidajenku ina mai umartarku daku rarrashi matayenku Domin Nasan irin ciwon da zasu ji na rashin 'ya'yansu, amma karku sanar dasu inda suke domin hankalinsu ba zai kwanta ba Ku kuwa na baku dama a duk lokacin da kuke son ganin su zaku iya zuwa nan da zarar kun kira sunana Amma kafin ku tafi ku fara radawa 'ya 'yanku suna wanda zasu tashi dashi yayin girmansu Dajin wannan batu sai fuskokinsu suka kama murmushi Sukaji damuwarsu da fargabarsu sun ragu acikin zukatansu Don haka caraf sai suraif yace ni na sanyawa 'yata suna HUSNAILA nan take shima jauwas ya sanya wa nasa suna SAFRAN da MUFRAN Sannan yayi shiru Yana tunanin sunan da zai sanyawa na karshen … Kafin ya bude baki ya fadi sunansa take suka ga wata walkiya ta haska cikin kogon wacce saboda karfin ta saida suka rufe idanuwansu Koda budewarsu sai suka ga Ajikin kwalbar Da babu komai acikinta anyi rubutu kamar haka FARHAN !! Ragowar kwalaben kuwa an rubuta sunaye kamar yadda suka fada Da ganin wannan rubutu sai boka Hushairul hasnal ya dubeshi cikin al'ajabi yace To ka gani da idonka Tunda kai ka kasa zabar masa suna to abin bauta ya zabar masa Anan zamu rabu daku sai mun sake haduwa agaba Yana gama fadin haka take su sarki suraif suka bace daga cikin kogon nasa basu bayyana ako'ina ba sai cikin fada Har zuwa lokacin da suka dawo dakaru basu iya bude kofar fadar ba bare su shigo ciki Tun daga wannan rana akaci gaba da renonsu Husnaila acikin kwalaben sihiri Ana kara tsamasu da sirrikan tsafi har zuwa wata uku sannan kamar yadda Hushairul hasnal ya fada Saidaya aika da hadiminsa yaje ya ciro dan tayin dake cikin huraisa Aka ajiyeshi acikin wannan ragowar kwalba, tare da renonsa tareda sauran 'yan uwansa Sannan akai akai mahaifansu suna zuwa ziyartarsu Kwanci tashi saida suka shekara shida da watanni tara Acikin wadannan kwalabe Aranar da suka cika wata tarane tun da duku dukun safiya su sarki suraif suka bayyana acikin kogon tsafin nasa Saidai a wannan rana Basu ga boka Hushairul hasnal ba amma kuma ga kwalaben nan a jiye kamar yadda suke Saidai acikin kwalaben cike suke da wani hayaki wanda ya hana idanuwansu kallon abinda yake ciki Nanfa zuciyarsu ta buga da karfi suka fara tunanin anya kuwa boka Hushairul hasnal ba amanarsu yaci ba ? Cikin tsoro da fargaba jawwas yaje kusa da kwalaben ya mika hannunsa da nufin tabawa Kwatsam sai yaji boka Hushairul hasnal ya daka musu tsawa Wacce saboda karfin ta saida yaji zuciyarsa ta buga da karfi bai san sanda yaja da baya ba da sauri Kawai sai suka hangi boka Hushairul hasnal hasnal ya taho inda suke fuskarsa cike da damuwa kamar wanda akayiwa albishir da ranar mutuwarsa Yana dogarawa da sandar tsafinsa, koda ya iso inda suke sai yace lale marhaban da zuwan Kuyi hakuri Nasan kunyi jirana kuma harkun kosa da jirana Ba komai ne yasa kukaga bana nan ba face halwar tsafin dana shiga akansu farhan Wannan kuma hayaki da kuka gani bana komai bane face sirrikan tsafina wanda na zuba ajikinsu gaba daya A halin yanzu babu wani sihiri da yayi saura ajikina duk na mai dashi jikinsu Ba don komai ba sai don ina da tabbacin anan gaba zasu baiwa tsafi kariya daga azzalumai masu burin tarwatsa duniya dashi A halin yanzu akwai wani hadimin aljanina da zai dauke su ya wuce dasu makarantar da zasu Kuyi yaki Ina mai tabbatar muku da cewa Koda basu mallaki karagar AJALI ba sunansu zai bazu a duniya yadda baza'a manta dasu ba Saidai alokacin da zasu sami wannan nasarar bai zama lallai ina raye ba Abu daya Kawai nake shakka, wannan abu kuwa ba Komai bane face tuggun da dana hulbaz yake shiryawa a yanzu Domin ni kaina ina shakkarsa duk da cewa ni na haifeshi amma ance mai laya ya kiyayi mai zamani Da gama fadin haka ya takarkare cikin daga murya ya karanto wasu dalasiman tsafi Faruwar hakan keda wuya sai kwalaben suka fara tsatstsagewa tare da kumbura wani sauti Yana fita daga jikinsu Daga can sai sukayi bindiga suka tarwatse gaba daya, sai ga su farhan sun fito daga cikinsu tsirara ko tufafi babu ajikinsu Sannan Hushairul hasnal ya mika musu tufafi suka sanya ajikinsu Abin wani abin mamakin ma shine safran da mufran kai harma da Husnaila duk yanayin jikinsu daya Ma'ana girda girdane masu girman kirar jiki, saidai kuma farhan siffarsa ta fita daban da tasu Bai karasa su a girma da kaurin jiki ba amma kuma gabaki dayansu babu sa'ansa a fagen kyau Sannan yana da kirar jarumai kamar su Suna fitowa sai suka raba idanu suka rasa gurin wanda ya kamata suje Tsakanin boka Hushairul hasnal da iyayensu Da ganin haka sai Hushairul hasnal yace dasu me kuke jira ne ai sai kuje gurin iyayenku Dajin haka sai suka ruga da gudu gun iyayen nasu kuma kowa sai yaje gurin mahaifinsa na zahiri ba tareda kuskure ba Nanfa su jawwas suka rungumesu tareda hawayen farin ciki sakamakon ganin 'ya'yansu lafiyayyu Kafin ajali ya riske su bayan sun dan tattauna sai suraif yace da Hushairul hasnal Yakai wannan boka muna godiya da duk taimakon da kayi mana Amma ka sani na dade da yiwa kaina alkawarin nine mutum na farko da zan fara baiwa su safran horon yaki Zanso ka bani damar zama dasu domin na cika alkawarin dana daukarwa kaina ko kuma na kasance taredasu a inda zasu karbi horon yaki Dajin wannan batu sai Hushairul hasnal yayi guntun murmushi daga bisani yace ai Wannan ba matsala bace daga wannan aiki ni zan fita daga sabgar su Domin na gama aikina Don haka kaima zaka iya kasancewa taredasu har ma ka basu horon yakin da kake dashi yayinda kuka isa can, Idan kun shirya yanzu hadimin aljanina zaizo ya daukeku gaba daya zuwa can Da gama fadin haka saiya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa a kan kasa Faruwar hakan keda wuya sai kasa ta fara girgiza wani bakin hadari ya tokare sararin samaniya kafin cikar dakika goma take suka ga wani shirgegen aljani ya ratso saman rufin kogon ya shigo ciki A ka'ida girman kogon yayiwa Koda fuka fukin aljanin guda daya kankantar da ba zai iya sakewa acikinsa ba Amma Koda saukar sa aciki sai suka ga kogon ya kara girma da fadi ninkin ba ninkin din nada har saida aljanin ya zamo dan mitsitsi acikinsa Koda bayyanarsa sai yayi sujjada ga Hushairul hasnal sannan dube shi cikin kakkausar murya yace ya shugabana kai kuwa yau wacce irin bukatace dakai wacce har tasa ka nemeni alhalin rabonka da nema na yau shekara hamsin da biyar kenan lokacin da mukaje yaki duniyar fatalwa? Yanzu kuwa har girma ya kamaka kuma karfinka ya ragu fiye dana baya na tabbata ba zaka iya jarumtakar da kayi ba a lokacin Dajin wannan batu sai ya tuntsure da dariya dariya sannan ya dubi aljanin yace Yakai AMSADUS RAS ka sani cewa ko kura ta fadi tafi karfin wasan yara , kuma komai lalacewar tsohon zaki yafi saurayin kare Ka sani cewa duk da na

Chapter 9 of 21