Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta taho da likitar masarautar Cikin kankanin lokaci ta tafi cika umarnin da aka bata Kafin su iso tuni Gimbiya suhaila ta debo wasu magunguna ta fara aikinta akan sarki kafin likitar ta iso Ragowar dakarun na tsaye sun zuba idanu cikin matukar damuwa kan halinda sarki yake ciki Bayan isowar likitar masarautar sai da aka shafe sa'o'i biyar ana aiki akan sarki gulbas sannan ya dawo cikin hayyacinsa Farfadowarsa keda wuya saiya dubi gimbiya suhaila Aikuwa take yaji zuciyarsa ta buga da karfi wanda shi kansa ya kasa gane dalilin hakan Kawai sai ya kurawa kwayar idanunta ido tsawon dakiku ba tareda ya koda kifta idanunsa ba Yana so yayi wani bincike akanta Koda ta lura da abinda yake yi sai kawai tayi murmushi kamar bata san me yake shirin yi ba tace Yakai abbana kai kuwa kallon me kakeyi mini shin baka taba ganina bane? Ko kuwa ka manta da 'yarka guda daya a duniya ne? Dajin wadannan tambayoyi sai sai shima ya mayar mata da martanin yake Sannan ya dubi dakaru da likitarsa yace inaso ku bani guri domin na tattauna da 'yata ta cikina Cikin girmamawa dakarun suka rissinar da kawunansu suka kama hanya suka fice daga cikin turakar suka barsu su biyu rak Sarki gulbas yace yake 'yata bawai na manta dake bane Tabbas akwai al'amarin dayake shirin faruwa acikin wannan masarautar Atsakanin ni da kuma ke amma ya zame mini tilas na gano ko menene wannan abu kafin yazo ya zame mana matsala Koda jin haka saita tuntsure da dariya tace haba ya abbana shin aduniyar nan Akwai wani mugun al'amari wanda zai iya faruwa har muji tsoron zuwansa Kadafa ka manta shi kansa tsautsayi yana tsoron tunkarar wannan masarautar Kai bama kaiba ni kaina daka haifa na gaji sadaukantaka a nono don haka babu abinda za taba firgitani a rayuwa bare kuma kai da kake matsayin fasa taro afilin daga Koda tazo nan a zancenta sai kawai yayi wani guntun murmushi mai nuna rashin yarda yace Ke yarinya ce kuma mace tunaninki b zai taba zuwa daya da nawa ba Don haka bazan taba gasgata zancenki ba sai nayi bincike mai zurfi sannan zan duba Abubuwan da suka faru acikin wannan masarautar bayan tafiyata Kuma duk wanda na sami hannunsa acikin yunkurin cin amanata to tabbas sai na dauki mummunan hukunci akansa Komai kusancinsa agurina domin ba zan taba yarda da maci amana ba Dajin haka saita yi wani murmushi mai nuna yarda da kanta tace Ni kuwa zanso naga an kama wannan maciyin amanar da kuma hukuncin da doka zata dauka akansa Tana gama fadin haka saita juya ta kama hanyar fita daga cikin turakar Har ta dora kafarta abakin kofar sai kawai taji sarki gulbas ya kira sunanta Cikin sauri ta juyo da baya alokacin dataji zuciyarta ta buga da karfi Kawai sai yace mata ki ci gaba da lura da wannan birni ni kuma a yau zan fara kokarin gano maciya amanar da suke masarautar nan Tace babu damuwa sannan ta fice daga cikin turakar Fitarta keda wuya sai kofar turakar ta maida kanta ta rufe Kai tsaye ta wuce cikin dakinta ta kullo kofa ta rufe rufe ruf Kawai saita tuntsure da dariya tace ai tuni na gama toshe hanyoyin da zakabi ka iya gano tanadin da kakeyi akanka Don haka gaba daya yanzu idanu zan zuba muku har sai kun gama shan wahalar ku sannan zan mallaki abin da kuke ta rigima akai Tana gama fadin haka sai ta murtuke fuska sakamakon ganin wani farin tsuntsu zaune akan tagar dakinta ya kura mata ido Da alama duk abinda take fada yana saurarenta tana ganin wannan tsuntsu sai taji ajikinta bata amince dashi ba Koda suka hada idanu da wannan tsuntsu sai take ya bude fuka fukansa ya tashi sama da nufin ya tsere mata Cikin sauri ta karanta dalasiman tsafi kawai sai wata ragar tsafi ta bayyana ta bi Wannan tsuntsu da gudu ta cafkeshi ya kasa ci gaba da tafiya Take ta tashi sama tabi wannan tsuntsun donta kamashi ta gano meye dalilin zuwansa Tana zuwa daidai inda yake sai takai hannunta don ta kamashi Kwatsam ba zato ba tsammani sai taga wata guguwa da karfi ta taso daga nesa da ita Kafin ta ankara tuni ta dagata ta buga ta da bango Sannan ta shuri tsuntsun suka bace gaba daya Cikin matukar fusata itama ta rikide ta koma guguwa sannan ta tashi ta bishi Sai dai kash ! Tuni sun bace mata da gani Bisa dole ta dawo kasa Lokaciin da hankalinta yayi matukar dugunzuma ta rasa mai ke mata dadi kawai saita ta karkare ta kwarara uban ihu taji kamar ta fashe da kuka saboda rashin sanin daga ina wannan tsuntsun tsafi yake Domin tabbas asirinta yana daf da tonuwa idan har batayi da gaske ba tana da yakinin 'yan leken asiri ne suka turo shi To amma abin tambayar shine Daga ina yake kuma wanene ya turo shi? Nanfa hankalinta ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe Ba shiri ta juya cikin dakinta don tayi zuzzurfan tunani akansa da kuma hanyar da zata bullo masa Tana shiga cikin turakar tata sai ta sami guri ta zauna gefen wata kujera ta fara tunane tunane daban daban Acan cikin turakar da sarki gulbas yake kwance kuwa gimbiya suhaila na fita daga cikinsa bata jima ba Sai ya fara karanto wasu kalaman tsafi marasa wahalar furtawa Faruwar hakan keda wuya kasa ta fara rawa tana tsagewa wani sauti ya dinga tashi daga cikin kasa Jim kadan saiga wani matashin aljani ya ratso Daga cikin karkashin kasa ya taso samanta Shi dai wannan aljani siffofinsa gaba daya irin na sarki gulbas ne babu wani banbanci atsakaninsu kamar an tsaga kara Babu alamar da zata nuna maka bashi bane komai kallon kurullanka Yana bayyana sai ya zube kasa yayi sujjada ga sarki gulbas yace Gani ya shugabana me kake bukata yamzu na biya maka ita? Dajin wannan tambaya sai sarki gulbas ya dube shi yace Inaso yanzu ka tashi ka shiga ko'ina a gidan sarautar nan Amatsayin ni kayi mini leken asiri kan duk abubuwanda suke faruwa cikinsa kazo ka sanar dani Don hakika ina da yakinin akwai tuggun da ake shiryawa anan gidan Dajin haka sai aljanin ya rissina yace an gama ya shugabana Yana gama fadin haka ya tashi ya fice daga cikin turakar yana tafiya ta kasaita duk da cewa kuwa ga ciwuka nan ajikinsa rututu kamar yadda suke ajikin sarki gulbas Koda fitarsa daga turakar sai ya fara kutsa kansa ko ina na masarautar cikin wani wani azababben sauri Duk inda ya ratsa sai kaga ana kai masa gaisuwa kuma ana binsa da kallo cike da mamakin yadda yake tafiya da kuzarinsa duk da munanan raunikan da suke jikinsa Hatta cikin dakunan da suke rufe sai daya dinga ratsawa yana ganin duk abubuwan da suke faruwa Yana cikin tafiyar ne yazo giftawa ta kofar turakar gimbiya suhaila adaidai lokacinda yake wannan zagaye ne Yazo giftawa ta kofar tagar gimbiya suhaila kwatsam sai yaga giftawar wannan farin tsuntsu yana kallon tsuntsun yaji zuciyarsa bata gamsu dashi ba Sannan ya hango sanda yanar tsafi ta fito daga cikin turakar ta kama wannan tsuntsu Har zuwa sanda ta fito tazo da nufin ta kama shi Koda ganin haka sai yayi fitar burgu daga inda yake boye Cikin siffar guguwa ya shureta ya bugata da bango ya dauki wannan tsuntsun da nufin Kai tsaye ya wuce turakar sarki gulbas dashi Saidai kash!!!! Hakika rashin sani yafi dare duhu inda yasan abinda zai faru dashi sanadiyar daukar wannan tsuntsun tsafi da baiyi kuskuren daukarsa ba Domin kuwa yana daukarsa ne shima yaji gaba daya ya kasa sarrafa kansa kamar an daure shi da murtukekiyar sarkar tsafi Kawai sai ji yayi shima wata iskar wacce tafi karfinsa ta zukeshi gaba daya har tsuntsun sun bace daga harabar gidan sarautar Babu irin kokarin da baiyiba domin ya kwace kansa amma ya kasa samun damar hakan bisa dole ya hakura ya zuba idanunsa don ganin abinda zai faru dashi Tafiyar dakiku dari da sittin kacal sukayi kawai sai iskar ta jefar dashi cikin wani kogon dutse Wanda ya kasance mai matukar duhu ta yadda ko tafin hannunsa baya iya gani aciki Yana dira aciki wata yaji kamar an zare masa lakar jikinsa ko tafin hannunsa ya kasa dagawa Jim kadan sai ga haske ya mamaye kogon wanda saboda karfinsa saidaya runtse idanunsa don kar hasken ya cutar dasu Jim kadan saiga boka farraz ya bayyana yana mai kyakyata mahaukaciyar dariya Fuskarsa cike da fara'a kai kace anyi masa kyautar duniya gaba daya Koda ya gama shigowa cikin kogon dutsen sai ya ci gaba da dariyar tasa daga bisani kuma ya murtuke fuska ya dubeshi yace Yakai wannan aljanin hakika hukuncin kisa ne ya dace dakai sakamakon daukar 'yar leken asirina da kayi Saidai kuma kayi sa'a alkalamina ya riga ya juye akanka ba zan cutar da kai ba Domin hakan da kayi ba karamin taimakona kayi ba Inaso ka sani daga ni har hadimai na babu mai ikon shiga masarautar sarki gulbas ya fito a raye duk da karfin sihirin da nake dashi Kai bama ni ba hatta su jarumi rukyan da boka gulbas Domin kowa a gidansa sarki ne, don haka ba karamin sihiri na acikin wannan gida ba Wannan ne yasa duk wanda yayi kuskuren shiga cikin gidan sarautarsa daga cikin mu Take jikinsa zai zagwanye kamar narkakken mai Don haka nima na sami wannan tsuntuwar na sihirceta na turata cikin masarautar tana yi min leken asiri tana dawowa ta sanar dani Ba tareda na wahala ba ina daga nan nasan duk motsin da sarki gulbas da gimbiya suhaila suke Saidai kuma abu daya daya daure min kai shine Akwanakin baya gimbiya suhaila ta kebanta da wata kuyangarta mai suna ruwaisa acikin turakarta Wanda tunda ta karanta wasu dalasiman tsafi take allon tsafi na ya daina aiki ban iya ganin abindaya faru a sannan ba Kuma nasan dole abinda suka tattauna akansa abune mai matukar mahimmanci kuma dole sai na gano mai suka tattauna akai Yanzu kai zan sakeka ka koma gurin mai gidanka duk da cewa ina da ikon kasheka amatsayinka na yaron abokin gaba ta Amma zan kyaleka ka tafi saboda ka taimake ni ammafa ka sani koda ka koma wajensa baka isa ka sanar dashi wannan abubuwan da suka faru anan ba Dajin wannan batu sai hankalin aljanin ya dugunzuma ya dubi boka farraz yace Kai kuwa menene dalilin dayasa ka dauki gaba ka dora akan sarki gulbas da gimbiya suhaila? Dajin wannan tambaya sai yayi dariya Yace Ba wai dasu kadai nake gaba ba Ina gaba ne da duk wani mai burin mallakar KARAGAR AJALI Domin tun ina karami mahaifina yake bani labarin ta Kuma nima na dauki kudurin mallakarta saidai kuma tawaya ta guda daya ce Itace rashin karfin damtse da iya yaki, babu yadda banyi ba akan in zama mayaki amma na kasa Bisa dole na hakura hakane yasa su sarki gulbas suka wuceni Amma badon hakaba da tuni na dade da hawa kan KARAGAR AJALI Duk da haka kuma banfidda raiba domin dukkansu babu wanda ban ginawa mugayen tarkuna ba wadanda ina da yakinin dole sai daya daga cikinsu ya fada Domin ni kalar baiwar da ubangiji yayi mini kenan ina da baiwar tsara tuggun da zaiyi aiki a shekaru dubu nan gaba Wannan ne iya amsar da zan iya baka a halin yanzu Yana gama fadin haka take ya bace daga gurin shida tsuntuwarsa ta tsafi Suka bar shi shi kadai a sannan ne yaji jikinsa ya saki har zai iya sarrafashi Take ya kada fukafukansa ya tashi sama cikin tsala gudu domin yaje ya sanar da sarki gulbas abinda ke shirin faruwa Saboda karfin gudun da yakeyi bai jima yana tafiya ba ya isa bayan katangar gidan sarautar Yana isa take ya rikide ya kara komawa siffar sarki gulbas sanye da alkyabba Da kwagirin sarautarsa a hannunsa ya karasa bakin kofar shiga masarautar Da isarsa bakin kofar sai shugabar dakarun ta rugo aguje ta rissina tace Barkanka da dawowa ya shugaban mu kawai saita koma cikin dakaru suka fara aikin bude kofar masarautar wacce ta kasance katuwar gaske Kamar kofar shiga wani babban birnin Ita kanta kubar kofar katuwar gaskece domin sai dakaru goma sun hadu suke iya dagata Koda ya wuce sai suka mai da kofar suka rufeta bam Wata daga cikin dakarun ta dubi shugabarsu tace anya kuwa daya daga cikin mu yaga lokacin da sarki gulbas ya fita daga cikin gidan nan? Dajin wannan tambayar sai ta girgiza kai tace tabbas bata nan ya fitaba Amma babu yadda zamuyi domin mutum ne da gidansa sai yadda ya tsara Tana gama fadin haka saitayi shiru da bakinta bata kara cewa komai ba Lokacinda aljanin nan ya shiga cikin gidan sarautar cikin siffar sarki gulbas Sai ya dinga tafiya cikin sauri don ya isa cikin turakar sa ya sanar da sarki abinda yake shirin faruwa Duk inda ya zo giftawa take sai kowa yabar abinda yake yi ya kame yana girmama shi Har ya isa bakin turakar ya bude kofar ya shige ciki, aikuwa kafarsa na shiga ciki sai yaji kansa ya sara da karfi Take anan ya manta da duk abubuwanda da boka farraz ya fada masa da isarsa gaban sarki gulbas sai ya fadi yana zazzare idanu ya kasa bayanin Komai Ya tsaya kame kame , da ganin haka sai sarki gulbas ya kura masa idanu yana nazarin halin da yake ciki Daga can kuma sai yace yakai hadimina tabbas na lura da cewa bai kamata ka kasance acikin hadimai na ba Domin ba zaka iya biya min bukatu na ba, Kuma ina mai tabbatar maka cewa nan da dan wani lokaci zan gano abinda kwakwalwarka ta kasa dauka. Kai kasheka zanyi yanzu Dajin haka sai aljanin ya rikice ya fara rokon sarki gulbas yayi masa afuwa amma ko saurarensa baiyi ba kawai sai ya nunashi da yatsansa aikuwa take wata wuta ta fito daga jikinsa ta kama aljanin ta babbakeshi Kurmus tokarsa ma ta tashi tabi iska kamar babu abinda ya faru Ita kuwa gimbiya suhaila lokacin da wannan iskar ta shureta ta buga ta da bango Ta dauke wannan tsuntsun tsafi tana mikewa saitaga tuni iskar da tsuntsun sun bace mata da gani kawai sai tayi tsaki Ta ciki yatsanta tace Du yadda akayi nima bani kadai ce nake dakon su mahaifina ba akwai wani daban Amma duk halinda ake ciki lokaci zai bayyanashi Tana wannan zancen zucin saita koma dakinta ta janyo labule da tagogi ta rufe Sannan ta zauna akan kujerar da take dakin a gaban kujerar kuwa taburin cin abinci ne An zuba abinci da abin sha iri daban daban na alfarma Ba shiri ta kama cin abincin tana gamawa saita tashi ta shiga bandaki da yi wanka sannan ta shafe jikinta da turarruka kala daban daban Tana gamawa saita shige cikin wani daki dake turakar tata Inda anan ne take ajiye duk wasu kayan sirrinta, tana shiga dakin ta turo kofa ta rufe Sannan ta cire tufafin da suke jikinta gaba daya, Ta dauko wasu daban wadanda suka kasance kayan yaki ne domin gaba dayansu an kerasune da zallan bakin karfe Irin kirar kwararrun makeran birnin sin ta sanya ajikinta Wohoho abinka da mace me kyau musamman ma idan ta hadu da kyawu dan uwanta Aikuwa koda ta sanya wadannan kayan yaki sai gashi sun fito da tsantsar kyawun da allah ya bata da kuma siffarta ta jarumtaka Ita dai gimbiya suhaila ta kasance doguwar macece amma ba can ba Tana da zara zaran yatsu sannan kaurin jikinta daidai misali ne Idanunta kuwa dara dara ne masu haske kamar madara Gashinta baki ne sidik sai sheki da walwali yake ya zuba har zuwa mazaunanta kirjinta a cike yake, hakama kugunta, cikinta kuwa ashafe kamar bata cin abinci Hakika duk. Inda ake kwatancen mace mai cikar kyawu gimbiya suhaila ta kai Tana gama sanya wadannan tufafin sai ta dauki takobin ta Ta rataya a gadon bayanta sannan ta dauki kwari da bakanta ta rataya su Sannan ta fito daga cikin dakin ta maida kofa ta rufe Ta fita daga cikin turakar tata gaba daya ta janyo kofa ta rufeta Sannan ta nufi inda bargar dawakai take Tun daga nesa idan dakaru suka ganta take suke buda mata hanya ba tareda sun tsaya yi mata tambayoyi ba Saboda ita kadaice mai kalar wannan kayan yakin kuma tana sanya su ne idan za'a fita yaki ko kuma zataje farauta farautar sirri **********KARAGA­R AJALI 3 PART ****************** B LBR ********************­ HABIBULLAH KBR Acan gidan sarauta kuwa lokacin da sarki gulbas ya bayyana acikin turakarsa Babu kowa acikin turakar sai shi kadai adaidai lokacin ne wata kuyanga wacce take aikin share share acikin turakar ta bude kofa ta shigo domin yin aikinta Shigarta cikin turakar keda wuya ta wuce can ciki da kayan aikinta Kawai sai tayi arba da sarki gulbas, cikin razana ta kwarara ihun neman taimako don a zatonta wani aljanin ke ya bayyanar mata cikin siffarsa Cikin kankanin lokaci dakaru suka rugo da gudu cikin turakar don ganin abinda yake faruwa Koda sukayi arba da sarki gulbas sai dukkaninsu tsaya cak Bisa rashin tabbacin sanin shine ko kuma bashi bane Saida sarki gulbas ya daka musu tsawa sannan suka tabbatar da shine Cikin sauri shugaban dakarun ta ruga da gudu cikin turakar gimbiya suhaila ta sanar da ita cewa ga sarki ya dawo Take kuwa tabar abinda takeyi ta tafi cikin turakar tasa Tana ganin halinda yake ciki saita umarci wata badakariya dataje ta taho da likitar masarautar Cikin kankanin lokaci ta tafi cika umarnin da aka bata Kafin su iso tuni Gimbiya suhaila ta debo wasu magunguna ta fara aikinta akan sarki kafin likitar ta iso Ragowar dakarun na tsaye sun zuba idanu cikin matukar damuwa kan halinda sarki yake ciki Bayan isowar likitar masarautar sai da aka shafe sa'o'i biyar ana aiki akan sarki gulbas sannan ya dawo cikin hayyacinsa Farfadowarsa keda wuya saiya dubi gimbiya suhaila Aikuwa take yaji zuciyarsa ta buga da karfi wanda shi kansa ya kasa gane dalilin hakan Kawai sai ya kurawa kwayar idanunta ido tsawon dakiku ba tareda ya koda kifta idanunsa ba Yana so yayi wani bincike akanta Koda ta lura da abinda yake yi sai kawai tayi murmushi kamar bata san me yake shirin yi ba tace Yakai abbana kai kuwa kallon me kakeyi mini shin baka taba ganina bane? Ko kuwa ka manta da 'yarka guda daya a duniya ne? Dajin wadannan tambayoyi sai sai shima ya mayar mata da martanin yake Sannan ya dubi dakaru da likitarsa yace inaso ku bani guri domin na tattauna da 'yata ta cikina Cikin girmamawa dakarun suka rissinar da kawunansu suka kama hanya suka fice daga cikin turakar suka barsu su biyu rak Sarki gulbas yace yake 'yata bawai na manta dake bane Tabbas akwai al'amarin dayake shirin faruwa acikin wannan masarautar Atsakanin ni da kuma ke amma ya zame mini tilas na gano ko menene wannan abu kafin yazo ya zame mana matsala Koda jin haka saita tuntsure da dariya tace haba ya abbana shin aduniyar nan Akwai wani mugun al'amari wanda zai iya faruwa har muji tsoron zuwansa Kadafa ka manta shi kansa tsautsayi yana tsoron tunkarar wannan masarautar Kai bama kaiba ni kaina daka haifa na gaji sadaukantaka a nono don haka babu abinda za taba firgitani a rayuwa bare kuma kai da kake matsayin fasa taro afilin daga Koda tazo nan a zancenta sai kawai yayi wani guntun murmushi mai nuna rashin yarda yace Ke yarinya ce kuma mace tunaninki b zai taba zuwa daya da nawa ba Don haka bazan taba gasgata zancenki ba sai nayi bincike mai zurfi sannan zan duba Abubuwan da suka faru acikin wannan masarautar bayan tafiyata Kuma duk wanda na sami hannunsa acikin yunkurin cin amanata to tabbas sai na dauki mummunan hukunci akansa Komai kusancinsa agurina domin ba zan taba yarda da maci amana ba Dajin haka saita yi wani murmushi mai nuna yarda da kanta tace Ni kuwa zanso naga an kama wannan maciyin amanar da kuma hukuncin da doka zata dauka akansa Tana gama fadin haka saita juya ta kama hanyar fita daga cikin turakar Har ta dora kafarta abakin kofar sai kawai taji sarki gulbas ya kira sunanta Cikin sauri ta juyo da baya alokacin dataji zuciyarta ta buga da karfi Kawai sai yace mata ki ci gaba da lura da wannan birni ni kuma a yau zan fara kokarin gano maciya amanar da suke masarautar nan Tace babu damuwa sannan ta fice daga cikin turakar Fitarta keda wuya sai kofar turakar ta maida kanta ta rufe Kai tsaye ta wuce cikin dakinta ta kullo kofa ta rufe rufe ruf Kawai saita tuntsure da dariya tace ai tuni na gama toshe hanyoyin da zakabi ka iya gano tanadin da kakeyi akanka Don haka gaba daya yanzu idanu zan zuba muku har sai kun gama shan wahalar ku sannan zan mallaki abin da kuke ta rigima akai Tana gama fadin haka sai ta murtuke fuska sakamakon ganin wani farin tsuntsu zaune akan tagar dakinta ya kura mata ido Da alama duk abinda take fada yana saurarenta tana ganin wannan tsuntsu sai taji ajikinta bata amince dashi ba Koda suka hada idanu da wannan tsuntsu sai take ya bude fuka fukansa ya tashi sama da nufin ya tsere mata Cikin sauri ta karanta dalasiman tsafi kawai sai wata ragar tsafi ta bayyana ta bi Wannan tsuntsu da gudu ta cafkeshi ya kasa ci gaba da tafiya Take ta tashi sama tabi wannan tsuntsun donta kamashi ta gano meye dalilin zuwansa Tana zuwa daidai inda yake sai takai hannunta don ta kamashi Kwatsam ba zato ba tsammani sai taga wata guguwa da karfi ta taso daga nesa da ita Kafin ta ankara tuni ta dagata ta buga ta da bango Sannan ta shuri tsuntsun suka bace gaba daya Cikin matukar fusata itama ta rikide ta koma guguwa sannan ta tashi ta bishi Sai dai kash ! Tuni sun bace mata da gani Bisa dole ta dawo kasa Lokaciin da hankalinta yayi matukar dugunzuma ta rasa mai ke mata dadi kawai saita ta karkare ta kwarara uban ihu taji kamar ta fashe da kuka saboda rashin sanin daga ina wannan tsuntsun tsafi yake Domin tabbas asirinta yana daf da tonuwa idan har batayi da gaske ba tana da yakinin 'yan leken asiri ne suka turo shi To amma abin tambayar shine Daga ina yake kuma wanene ya turo shi? Nanfa hankalinta ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe Ba shiri ta juya cikin dakinta don tayi zuzzurfan tunani akansa da kuma hanyar da zata bullo masa Tana shiga cikin turakar tata sai ta sami guri ta zauna gefen wata kujera ta fara tunane tunane daban daban Acan cikin turakar da sarki gulbas yake kwance kuwa gimbiya suhaila na fita daga cikinsa bata jima ba Sai ya fara karanto wasu kalaman tsafi marasa wahalar furtawa Faruwar hakan keda wuya kasa ta fara rawa tana tsagewa wani sauti ya dinga tashi daga cikin kasa Jim kadan saiga wani matashin aljani ya ratso Daga cikin karkashin kasa ya taso samanta Shi dai wannan aljani siffofinsa gaba daya irin na sarki gulbas ne babu wani banbanci atsakaninsu kamar an tsaga kara Babu alamar da zata nuna maka bashi bane komai kallon kurullanka Yana bayyana sai ya zube kasa yayi sujjada ga sarki gulbas yace Gani ya shugabana me kake bukata yamzu na biya maka ita? Dajin wannan tambaya sai sarki gulbas ya dube shi yace Inaso yanzu ka tashi ka shiga ko'ina a gidan sarautar nan Amatsayin ni kayi mini leken asiri kan duk abubuwanda suke faruwa cikinsa kazo ka sanar dani Don hakika ina da yakinin akwai tuggun da ake shiryawa anan gidan Dajin haka sai aljanin ya rissina yace an gama ya shugabana Yana gama fadin haka ya tashi ya fice daga cikin turakar yana tafiya ta kasaita duk da cewa kuwa ga ciwuka nan ajikinsa rututu kamar yadda suke ajikin sarki gulbas Koda fitarsa daga turakar sai ya fara kutsa kansa ko ina na masarautar cikin wani wani azababben sauri Duk inda ya ratsa sai kaga ana kai masa gaisuwa kuma ana binsa da kallo cike da mamakin yadda yake tafiya da kuzarinsa duk da munanan raunikan da suke jikinsa Hatta cikin dakunan da suke rufe sai daya dinga ratsawa yana ganin duk abubuwan da suke faruwa Yana cikin tafiyar ne yazo giftawa ta kofar turakar gimbiya suhaila adaidai lokacinda yake wannan zagaye ne Yazo giftawa ta kofar tagar gimbiya suhaila kwatsam sai yaga giftawar wannan farin tsuntsu yana kallon tsuntsun yaji zuciyarsa bata gamsu dashi ba Sannan ya hango sanda yanar tsafi ta fito daga cikin turakar ta kama wannan tsuntsu Har zuwa sanda ta fito tazo da nufin ta kama shi Koda ganin haka sai yayi fitar burgu daga inda yake boye Cikin siffar guguwa ya shureta ya bugata da bango ya dauki wannan tsuntsun da nufin Kai tsaye ya wuce turakar sarki gulbas dashi Saidai kash!!!! Hakika rashin sani yafi dare duhu inda yasan abinda zai faru dashi sanadiyar daukar wannan tsuntsun tsafi da baiyi kuskuren daukarsa ba Domin kuwa yana daukarsa ne shima yaji gaba daya ya kasa sarrafa kansa kamar an daure shi da murtukekiyar sarkar tsafi Kawai sai ji yayi shima wata iskar wacce tafi karfinsa ta zukeshi gaba daya har tsuntsun sun bace daga harabar gidan sarautar Babu irin kokarin da baiyiba domin ya kwace kansa amma ya kasa samun damar hakan bisa dole ya hakura ya zuba idanunsa don ganin abinda zai faru dashi Tafiyar dakiku dari da sittin kacal sukayi kawai sai iskar ta jefar dashi cikin wani kogon dutse Wanda ya kasance mai matukar duhu ta yadda ko tafin hannunsa baya iya gani aciki Yana dira aciki wata yaji kamar an zare masa lakar jikinsa ko tafin hannunsa ya kasa dagawa Jim kadan sai ga haske ya mamaye kogon wanda saboda karfinsa saidaya runtse idanunsa don

Chapter 6 of 21