Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
inda za'a iya rukeshi da hannu Amma saboda karfin sihiri na boka surkais sai gashi yana sarrafashi kamar yadda yakeso Ya zurashi acikin idanunsa aikuwa sannan ya dubi rubutun dake jikin fatar Aikuwa take rubutun ya fadada akan idanunsa ya zamana yana kallonsu sosai da idanunsa Take ya fara karanta rubutun dake jikin fatar afili cikin wani irin yare mai wahalar fahimta Aikuwa yana gama karanta wadannan dalasiman tsafin take kogon tsafin nasa ya fara girgiza komai dake cikinsa ya soma tuntsurewa yana faduwa kasa duwatsu suka dinga fadowa kasa daga jikin dirkar gini Duk wasu kayan tsafi nasa suka dinga bacewa da kansu daga cikin kogon Wata irin iska mai karfi ta dinga kadawa acikin kogon wacce tasa hankalin boka surkais ya dugunzuma Daga can kuma sai wannan iskar ta dunkule aguri guda ta rikide ta koma siffar wani dan gajeren aljani Wanda gaba daya tsawonsa bai wuce girman karamin dan maraki ba Amma da ka ganshi zakasan cewa ya shafe shekaru dubunnai adoron kasa Kuma ya sha gwagwarmaya sosai a rayuwarsa 1 Agefen kugun aljanin kuwa wata zabgegiyar kuba ce wacce ta ninka shi kansa aljanin a girma sau ashirin Amma abin mamaki ita wannan kubar bata rinjayar aljanin bare yayi yunkurin faduwa kasa Shidai wannan aljanin yana da jajayen idanuwa wadanda suka kasance manya manya kuma fafare ne tas babu ko digon baki acikinsu Fuskarsa kuwa cike take da farin gashi mai yawan gaske Yatsun hannunsa kuwa zara zara ne masu dogayen farata masu kaifi da tsini ajikinsu Da bayyanar wannan aljani saiya dubi boka surkais ya bushe da dariya Yace lale marhaban da boka surkais bin sardas Ni sunan aljani gudmasul kar kuma nine aka wakilta kan baka horon yaki na musamman Yakai zurkais ka sani cewa yanzu haka nine nake da alhakin baka horon yaki wanda mai girma sadauki farhan ya wakiltani akansa Domin dalasiman daka karanto nawa ne ni kadai don haka daga kai har abokan adawarka zaku karbi horon yakine kala daban daban Ba tareda ba wani yayi kama da na wani ba Kuma zaku gamane alokaci guda saidai ina tausaya maka Idan na tuna cewa bai zama dole kaida 'yan uwan adawarka ku sami nasarar mallakar karagar ajali ba domin tafi karfinku Saboda irin mahaukatan matakan tsaron da suke kan hanyar zuwa nemo saiful laiham Kuma daga yanzu har zuwa sanda zaka gama karbar horon ina mai sanar dakai cewa sihirin tsafinka ba zai sake tasiri ba saidai kayi amfani da tsagwaron karfin damtsenka ,naci juriya ,bajinta da kuma sa'arkane kadai zasu cece ka a wadannan ranaku Yana gama fadin saiya nuna boka surkais da tafin hannunsa Take duk su biyun suka bace daga cikin kogon basu bayyana ako 'ina ba face wata duniyar wacce take a saman iska Kuma a gaban wani tamfatsetsen gida wanda aka ginashi da zallan duwatsun wuta Girman wannan gida ya wuce kwatancen mai kwatance Awajen gidan kuwa wutace take ci kamar ana azawa wutar makera makamashi wanda karfin wutar kadai ya isa ya narkar da halitta tun kafin ta isa gaban wutar Da bayyanarsu a wannan guri sai aljani gudmasul kar yace wannan shine mataki na farko na fara karbar wannan horon yaki na ka Ka sani cewa da farko dolene ka nemi hanyar da zaka ratsa ta cikin wannan wuta ka shiga cikin wannan masarauta Acikinta ne zaka karbi ragowar horon yakin naka guda tara ammafa ka sani ba lallaine ka fito a raye ba Don haka dolene kayi amfani da kaifin basirarka acikinsa don tsira da rayuwarka Ba zaka iya shiga cikin wannan masarautarba kuwa har sai ka nemi inda kofarta take anan ne zakayi amfani da wannan kubar domin budeta Yana gama fadin haka saiya mikowa boka surkais wannan kubar da take daure a kugunsa Koda ya karbi kubar sai yajita babu wani nauyi kamar ya dauki sillen kara kafin ya budi baki yayiwa aljani gudmasul kar ya daga masa hannu alamar bayason yawan tambaya yace anan zan rabu dakai sai ka dawo a raye sannan zaka sake ganina Inayi maka fatan samun nasara Yana gama fadin haka saiya bace daga gurin yabar shi kadai Bacewar aljanin keda wuya sai boka surkais ya juya ya kurawa , wannan wutar da take ci idanu yana nazarin hanyar da zaibi ya shiga cikinta har ya isa inda kofar wannan gida take ya bude ta Shi kansa yasan cewa tunkarar wannan katanga a gurinsa daidai take da tunkarar mutuwa Saboda yadda wutar take zabalbala da kanta tana laso gefe da gefe Tundaga inda yake yana jiyo turirin wukar kamar agabanta yake Yana cikin wannan yanayi ne kawai ya hango wutar tana fizga da kanta tana kokarin Kwacewa daga inda take tayo kansa kuma alokacin ne yaga an zubo wani bakin makamashi daga sama zuwa kan wutar Aikuwa take wutar ta kwace da kanta kamar yadda ruwa yake samawa kansa hanya Ta nufo inda boka surkais yake da gudun gaske tana wani karaji kamar ana kona kirare Wohoho duk inda kaji ance ga ki gudu to sa gudu ne bai zoba Don duk taurin rai Irin na boka surkais da yaga yadda wannan wutar ta nufo kansa da gadan gadan Baisan sanda ya takarkare ya ruga da wani mahaukacin gudu domin ceton ransa ba Sai gashi suna gudu kamar mai kaya ya biyo barawo Duk inda wannan wutar ta gifta saboda zafinta sai dai kaji kasar gurin tana soyewa Kamar ana zuba ruwa acikin tafasashshen mai kai Saboda tsananin zafin wutar kasar ma har narkewa takeyi kamar ruwa Nanfa hankalin sa ya dugunzuma ainun ya fara tunanin hanyar daya kamata yabi domin ceton ransa don ya tabbata idan har aka cigaba da tafiya a haka Dolene ya gaji kuma saboda ba zai iya dauwama yana wannan gudun ba zai gaji ta riskeshi kuma da zarar hakan ta faru shikenan an shafe tarihin rayuwarsa Tun baiyi nisa ba acikin neman hawa kan karagar ajali ba Koda yin wannan tunani sai yaji wani sabon kuzari yazo masa Ya ji tabbas sai ya kubuta daga sharrin wannan sihirtacciyar wutar WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA BOKA SURKAIS A RANA TA FARKO DAYA FARA KARBAR HORON YAKIN SADAUKI SAIMAN TUN KAFIN YA FITA NEMAN TAKOBIN SAIFUL LAIHAM DOMIN YA HAU KAN KARAGAR AJALI +++++ ****** ++++++ Acan wata nahiyar kuwa wani Kyakkyawan Matashin saurayine wanda shekarunsa ba zasu gaza ashirin da bakwai ba dan asalin birnin rum yake tsala azababben gudu Bisa gadon bayan wani matashin aljani Kallo daya zakayiwa wannan saurayi ka tabbatar da cewa Dolene ya kasance jarumin gaske kuma sadauki tun daga kallon yanayin siffar kyakkyawan jikinsa Da yadda damatsan jikinsa suka mummurde kamar zasu yaga hannun rigarsa Kamar yadda damatsan hannunsa suka cuccure haka shima kirjinsa da cikinsa suke Kai kace nama ne aka cura aka manna masa shi a jikinsa Gashin kansa kuwa duk da ya daureshi agadon bayansa Hakan ba hana shi yawo ba acikin iska kai duk inda siffar kyau take da kwarjini akwaita ajikinsa Agadon bayansa kuwa ya goya wata sharbebiyar takobi mai kaifin gayawa jini na wuce Domin komai ya sara da ita take yake rabewa biyu ko kuma tsinka shi Wacce idan ba jarumin mutum ba babu wanda zai iya amfani da ita Ba kowa bane wannan matashi ba face jarumi rukyan bin haiwan daya daga cikin mutanen da suke burin mallakar KARAGAR AJALI Kuma babu inda yake saurin zuwa a wannan lokaci face kebantaccen gidansa Wanda yake aikin sihirinsa aciki Domin a wannan rana ne zai kammala hada sihirin tsafin daya dade yanayi na fara karbar horon sadauki farhan Shi kadai yake tsala mahaukacin gudu acikin sararin samaniya Yana ratsawa ta saman manyan duwatsu da tsaunika masu tsayi cikin gudun fitar hankali Duk inda sukazo giftawa saidai kaga kafin kiftwar ido suke wuce gurin Hakika wannan aljanin nasa yana da matukar gudu Saboda girman manya manyan fuka fukansa Duk da wannan gudu da sukeyi shi gani yake yi kamar basa yi saboda kaguwar da yayi Tafiyar sa'a uku cur suka shafe daga birnin Rum sannan Suka isa bakin wani dogon tsauni wanda yake a tsakiyar wata babbar teku Shidai wannan tsaunin yana da matukar girma da tsawo Koda isowarsu bakin tsaunin sai aljani haskar ya saki fukafukansa ya dira bisa tsuburin yace ya shugabana mun iso tsuburin JURRAS Dajin haka Sai fuskar jarumi rukyan ta fadada da murmushi Take ya daka tsalle ya dira daga kan aljani haskar Sannan ya dubeshi yace Godiya gareka ya kai haskar daga yanzu ka sami 'yan cinka har zuwa wanda zan fito daga wannan gidan sirrin nawa Yana gama fadin haka saiya juya masa baya sannan ya tafa hannayensa Faruwar hakan keda wuya sai dutsen ya dinga tsatstsagewa yana darewa ahankali Take wani katon gida ya faso dutsen ya fito waje girman Wannan gida kadai yakai girman wata masarautar Kuma an kawata ginin gidan sosai kai da ganinsa kasan ba ginin mutane bane Aljanune suka ginashi kuma suke gadinsa da lura dashi Koda bayyanar wannan boyayyen gida sai take kofa ta bayyana ajikinsa Kai tsaye ya shige cikin kofar sannan dutsen ya sake tsagewa gidan ya sake nutsewa aciki Hakika wannan gida an kawata shi ainun domin kuwa za'a iya kiransa da aljannar duniya Domin komai na kawa akwaishi acikinsa ga wasu kyawawan kuyangi sunci kwalliya na jinsin mutane da aljanu suna yawo acikinsa Suna ta aikace aikacensu kamar suna cikin gari Koda sukayi arba da jarumi rukyan sai dukkansu suka sunkuya suna kwasar gaisuwa agareshi Ko amsa gaisuwar bai tsaya yiba Yayi amfani da sihirinsa ya shige cikin dakinsa shi dai wannan daki babu komai acikinsa face tarkacen tsafi kala daban daban Atsakiyar dakin kuwa wata kasaitacciyar kujerace ta da zallan zinare Kai tsaye ya wuce ya zauna akan kujera sannan ya bude tafin hannunsa Ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi cikin daga murya Aikuwa faruwar hakan wuya sai wani farin haske ya ratso cikin turakar ya shige cikin idanunsa Take yaga wani irin rubutun tsafi ya bayyana acikin idanun nasa Wanda aka rubuta da yaren tsafi Cikin farinciki ya karanta dalasiman yin hakan keda wuya sai Dakin nasa ya dumame da wani irin duhu wanda ko dan yatsansa baya iya gani Wata iriyar tsawa mai firgitarwa da walkiya suka dinga tashi. Acikin dakin wacce jinta zai iya sa mace mai ciki ta haife dan dake cikinta ba tareda lokacin haihuwar yayi ba Jim kadan sai ga wani aljani mai matukar girma da kwarjini Ya ratso ta cikin rufin dakin kamar yadda haske yake ratsa iska haka ya ratso ta saman turakar ya shigo ciki Koda bayyanar wannan aljani sai komai ya koma ya koma daidai kamar yadda yake a baya aljanin ya dubeshi yace lale marhaban da jarumi rukyan bin haiwan Ni sunana murwanulhas yanzu haka nine wanda zaka karbi horo Daga hannuna Don haka ina mai sanar dakai karbar wannan horo daidai yake da siyan mutuwa da hannunka kuma da kudinka Don haka ina mai sanar dakai cewa yayin wannan horo sihirin tsafinka ba zai taba cetonka ba kuma ba zaiyi tasiri ba Zallan karfin damtsenka, nacinka , zafin namanka da kuma sa'arka ne kadai zasu cece ka Dajin wannan batu sai fuskar jarumi rukyan ta fadada da murmushi Yace yakai murwanulhas ina mai tabbatar maka da cewa indai da ruhi ajikina babu abinda zai hanani mallakar karagar ajali Don haka duk wata jarrabawa na shirya mata koda kuwa zan rasa komai na wannan duniyar Marwanulhas ya bushe da dariya yace haka akeson jarumin gaske ya kasance Amma ku 'yan adam akwaiku da tarin burika kuma karshe burikankune suke kaiku ga hallaka Don haka tunda kaima zuciyarka ta kekashe sai ka shiga sawun abokan adawarka Koda gama fadin haka saiya dafa kafadarsa yin hakan keda wuya Sai wani jan haske ya ratso cikin ginin fadar ya shigo ciki ya shuresu gaba daya suka bace daga cikin turakar Duk su biyun basu bayyana ako inaba sai cikin wata nahiyar daban Wacce kallo daya zakayi mata kasan cewa ta banbanta da nahiyoyin da ake zaman lafiya acikinsu Cikin wani tamfatsetsen gida mai matukar girma da kwarjini Tun a bakin kofar gidan jarumi rukyan ya fara arba da kwarangunan bil'adama fululu masu yawan gaske Wadanda saboda tsabar dadewa har ruburbushewa suke da kansu Da alama sun shafe daruruwan shekaru acikin wannan gida Kasan wannan gida kuwa daben da akayi masa ya kasance mai matukar santsi ta yadda mutum bai isa yace zaiyi gudu sosai akansa ba face ya fadi saboda santsin gurin A saman rufin gidan kuwa wasu mazurarai ne sirara kamar na'urar bada ruwa Kai da ganin wannan guri kasan dole akwai mugun abinda aka tanada Jim kadan duk su biyun suka tsaya suna kallon wannan daki ba tareda dayansu yace uffan ba Daga can sai aljani Marwanulhas ya katse shirun dake tsakaninsu da fadin cewa Yakai wannan matashin saurayi da idonka kaga irin abubuwan da suke wannan guri Wadannan kwaranguna da ka gani bana kowa bane face na zaratan jarumai, matsafa da kuma sarakunan masu yawa Wadanda suma a zamaninsu babu zaratan jarumai kamarsu Kuma suma duk irin burinka ne dasu amma karshe tun a mataki na farko suka dinga rasa rayukansu acikin wannan daki saboda kuskure kadan da suka aikata Don haka kaima sai ka kula da kanka don gudun karka shiga sawunsu Acikin wannan gida zaka iske dakuna har guda tara bayan wannan kuma ko wanne daki ana so ka wuce shi ne a rana guda ka shiga daki na gabansa Akwai tarkuna kala daban daban acikinsu wadanda sai kayi da gaske da kuma tsananin sa'arkane zasu tseratar da rayuwarka Wadannan mazurarai kuma daka gani ba komai bane acikinsu ba face narkakkiyar dalma wacce akullum dada tafasa takeyi Ana sone duk wuya duk runtsi karka bari wannan dalmar ta taba jikinka Dominbda zarar ta taba jikin naka a take zata zagwanyar da naman jikinka acikin dakika guda shi kenan an gama da tarihin rayuwarka Kamar yadda na baya sukayi alokacin da suke tashen sadaukantaka Don haka a nan gurin zanyi bankwana dakai idan da rabon zamu sake saduwa dakai Zaka iske ni a wajen wannan kuma ka cike sharadi na farko na mallakar KARAGAR AJALI Koda gama fadin haka sai take aljani Marwanulhas ya bace daga cikin gidan yabar shi shi kadai acikin wannan gida wanda kana iya yi masa lakabi da sansanin mutuwa ME ZAI FARU GA JARUMI RUKYAN ACIKIN WANNAN GIDA DAYA SHIGA ? TSAKANIN SHI DA BOKA SURKAIS WANENE ZAI FARA TARAR DA KALUBALE KUMA WANENE ZAIYI NASARA? SHIN SARKI YANA SAMUN DAMAR KARBAR HORON SADAUKI FARHAN? SHIN YANA YARDA YA TAFI DA 'YARSA NEMAN TAKOBIN SAIFUL LAIHAM DON HAWA KARAGAR AJALI? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENTS AND SHAREKARAGAR AJALI *****1 PART C ****************LBR **********HABIBULLAH KBR Whatsapp no 09133502477 Lokacin da aljani marwanul ya bace yabar jarumi rukyan tsaye acikin wannan daki Saiya soma tafiya a hankali yana nazarin cikin dakin da kalle kalle sama da kasa don yaga ta inda za'a fara kawo masa farmaki Yana cikin tafiyar ne kawai yaji ya taka wani guri mai matukar santsi Take kasar gurin ta dare gida biyu Kamar an raba ta almakashi wani dan siririn rami ya bayyana wanda mutum na fadawa cikinsa atake wannan narkakkiyar dalmar zata zubo da kanta cikin ramin sannan ya rufe kansa Har kafarsa ta zame zai fada cikin ramin sai take yayi alkafira ya daka tsalle sama domin kaucewa daga bakin wannan ramin Aikuwa kafarsa na jaucewa daga kan ramin take wata bakar tafasashshiyar dalma ta kwaranyo acikin ramin Tana zuba aciki take wata iriyar kara kamar an zuba ruwa acikin tafasashshen mai ta tashi gami da turiri Lokacin salyar yayi alkafira a sama domin kaucewa daga saitin wannan ramin Koda ya dira. Awani gurin daban shima sai take santsin wajen yaja kafarsa zuwa inda wani ramin yake Kafin ya ankara shima gurin ya dare kuma atake mazurarin dalmar ya sake budewa wata dalmar ta sake kwaranyowa cikin Bakin zafin nama kafin ta zuba akansa tuni ya mirgina daga inda yake ya koma wani gurin daban Aikuwa cikin rashin sa'a sai kansa ya bugu da jikin da jikin dirkar gini Take gurin ya dare jini ya soma zuba daga goshin nasa Cikin sauri ya mike tsaye ya gyara damarar rigarsa sannan ya shafa magani agoshinsa Yana gamawa kawai ya sami guri ya tsaya cak yana kallon ko'ina acikin dakin Yana kara nazari akansa Sai a sannan ne ya kula gaba wannan daki daga inda yake zuwa gaba Duk gurin taka loba ne babu inda zai sake takawa da kafarsa Ba tareda ya rufta ciki ba sabod shi kansa daben dake gurin shi kadai yake lobawa kasa Lokacinda jarumi rukyan ya kare nazarin dakin da yake ciki sai take ya zaro wasu Kananun wukake guda biyu daga kugunsa Kawai sai ya caka wukaken a saman katangar dakin Nanfa ya dinga amfani da wukaken yana caka su ajikin katangun kuma yana karawa gaba Sai gashi a wannan lokaci Yana tafiya ajikin katangar kamar kadangare Ba tareda kafafunsa sun taka kasa ba Kuma alokacin da yake wannan bin bango duk sai mazuraran dalmar suka bude suka dinga feshi da kansu Wani lokacin ma sai yaji kamar fatar jikinsa ta narke gaba daya Saboda yadda turirin dalmar yake tashi akwai lokutan ma da zaka Kamar dalmar zata laso inda yake Amma bisa sa'a sai kaga ya kauce mata ba tareda ta taba koda rigarsa ba Sai da yayi Tafiyar rabin yini sannan ya isa karshen dakin Kuma adaidainan ne komai na dakin ya kare ya zamana babu duk wadannan mazuraran Koda isowarsa daidai wannan guri sai ya sauko kasa ya zare wukakensa Yamai dasu cikin kube sannan yaci gaba da tafiya Koda isarsa gaban katangar karshen dakin Sai take katangar ta dare da kanta wata kofa ta bayyana Kai tsaye ya kutsa kansa Cikin dakin domin ganin abinda yake ciki Shigarsa keda wuya sai kofar dakin ta maida kanta ta kulle bam ta yadda babu damar komawa da baya Shi dai wannan dakin babbane sosai yana da matukar girma da fadi Gashi da matukar duhu ta yadda mutum baya iya ganin Koda ganin tafin hannunsa kuma tun farkon shigowarsa ya dinga jin wani irin sautin gurnani mai ban tsoro yana tasowa karfin sautin gurnanin kuwa Ya dinga amsa kuwwa ta ko ina acikin dakin wacce sautinta kan iya zautar da mutum ya rasa tunaninsa gaba daya Koda jin wannan sauti sai jarumi rukyan ya zaro takobinsa daga cikin kube ya ruketa da hannayensa biyu Sannan ya maida hankalinsa akowacce kusurwa ta dakin Yana jiran ta inda za'a fara kawo masa farmaki don ya tabbata dolene a kwai wata muguwar halittar aciki Yana kuma ci gaba da tafiyar ba tareda Wani abu ya faru ba Bai tarar da wani abun cutarwa ba sai daya isa tsakiyar dakin adaidai wannan yaga wasu jajayen abubuwa kamar fititu Acan sama sun tsaya akan iska koda ganin wadannan fitilu sai ya kamu da matukar farin ciki a zuciyarsa yace Aikuwa babu abindaya kamace ni dayi ayanzu face naje na dauko wadancan fitilu kome yin hakan zai jawo min Domin bai kamata na dinga tafiya acikin wannan duhun ba Kash! Wannan shine babban kuskuren daya aikata a wannan lokaci Domin wadannan abubuwa ba fitilu bane idanuwan wani maridin dodo ne Yanzu haka shekararsa dubu biyu da doriya acikin wannan kogo yanata sharara barci abincinsa Karfin jan da idon nasa yake dashi ne yasa ko yana barci sai ya ratsa fatar idon ya fito waje Koda gama yin wannan shawarar sai yaja da baya sannan ya rugo da gudu da gudun gaske Sai daya rage saura abinda bai wuce taku hudu ba tsakaninsa da inda jan hasken yake Sai ya daka wani mahaukacin tsalle daga inda yake kamar an harba shi daga cikin baka Yana isa daidai inda jajayen fitilun suke ba zato ba tsammani sai yaji an gabza masa wani mahaukacin naushi da karfin gaske Saboda karfin naushin sai da yayi sama kamar an doka kwallo ya gwaru da jikin rufin dakin sannan ya dawo ya maku da kasa Saboda tsananin buguwar da yayi sai da yaji kamar gaba ki daya kashushuwan jikinsa sun kakkarye A sannan ne wannan dodon ya bude idanunsa wadanda suka kasance masu hasken gaske take hasken ya dallare masa idanu Cikin karfin hali rukyan ya mike tsaye tareda gyara tsayuwarsa yana mai fuskantar dodon Dodon ya tsaya ya karemasa kallo sama yaga irin siffar jikinsa da kankantar da yake da ita Sannan yace yakai wannan karamar halitta shin acikin halittun duniya acikin wanne jinsin halittu kake Kuma menene ya kawoka cikin wannan gida ko kaima kana Daga cikin tsagerun da suke da burin. Mallakar tsohuwar karagar mai girma sadauki farhan wato karagar ajali? Dajin wannan tambayar sai rukyan ya kamu da mamaki ganin cewa dodon bai san halittar dan adam ba Don haka sai yayi murmushi Yace ina daga cikin jinsin halittar dan adam Wadanda tun farkon kafuwar duniya suka kasance masu galaba akan sauran halittu Game da tambayarka ta biyu kuwa nazo wannan guri ne domin sanin hanyar da zan mallaki karagar ajali Koda yazo daidai nan. Azancensa sai dodon ya bushe da dariya wacce sautinta yasa dakin amsa kuwwa har sai daya sa hannu ya toshe kunnuwansa don ji yayi Kamar zazu fashe saboda karfin sautin dariyar tasa Yayita kyakyata wannan dariyar kamar bazai daina ba Daga can kuma sai ya murtuke lokaci guda yace aikuwa Kayi kuskure domin baka isa ka fita daga nan gidan. Araye ba bare kuma har kaje ka dauko saiful laiham don mallakar karagar ajali Yanzu take zan kamaka na tsotse jinin jikinka sannan na daune kokon kanka Don na gusar da tsohuwar yunwar da nake ji tsawon shekaru Yana gama fadin haka sai ya daga shirgegen hannunsa ya kawowa jarumi rukyan wawan duka dashi da nufin ya karya kashushuwan jikinsa Kafin hannun ya sauka akansa cikin bakin zafin nama tuni yayi zame akasa ya kaucewa harin dodon Koda hannun ya sauka a kasa take ya fasa kasa ya nutse aciki Nanfa ya kara juyowa da zafin sa ya kara kawo masa wani dukan da dunkulallen hannunsa Cikin sa'a kuwa ya sameshi Ya bugashi sama sai gashi yana reto a saman iska take dodon ya bude wangamemen bakinsa yana jira ya fado acikinsa Kodaya lura da abin da yake shirin faruwa yaga idan ya fada ciki zaiyi wuya ya tsira da ratuwarsa sai take ya wulkila jikinsa a saman ya kauce daga saitin bakin Sannan ya jera masa wasu mahaukatan naushi akan bakinsa Ya dira acan gefe daya bisa kafafunsa yana mai fuskantar dodon Daga can sai ya taho da gudun gaske yana zuwa daidai inda dodon yake Ya daka tsalle yakai masa wani mahaukacin sara da takobinsa Kafin saran ya sauka ajikinsa tuni dodon ya sa hannunsa daya ya kare saran Tuni gurin saran ya dare jini yayi tsartuwa daga gun Dodon yayi wani mahaukacin gurnani wanda kan iya saka mutum ya zauce gaba daya Idan akwai mace mai ciki ma agun zata iya haife abinda ke cikinta ba tare da ta sani ba Take yasa kafarsa guda daya ya kawo masa daku da ita Da nufin yayi raga raga da namansa, cikin bakin zafin nama rukyan yayi alkafira a saman ya kauce Koda sawun Dodon ya sauka a kasa take gasar gurin ta dare kafar tasa ta nutse aciki Yana zaro kafar sai yayo kansa gadan gadan cikin mugun nufi yana ta faman gurnani Ai ku shima rukyan sai yayi kansa da gudu yana mai kwallara kara Ai kuwa suna haduwa a tsakiya sai suka kachame da azababben yaki mai ban tsoro Ya zamana suna kaiwa junansu mugayen hare hare Wohoho hakika rukyan ya cika jarumin gaske mai matukar taurin rai Domin inba don haka babu ta yadda za'ayi ya iya tarar wannan shirgegoyar halittar mai girman gaske Don idan ka duba girmansa sai kaga kamar baifi a ajiye kyanwa agaban kare ba Amma duk da haka sai gashi yana iya fafata yaki da wannan shirgegiyar halitta Nanfa suka hargitsa dakin saboda kwarmatsuwar da suke yi Sai gashi rukyan ya zamewa dodon alakakai ya kasa samun galaba akansa Ba komai ne ya janyo haka ba face tsananin zafin naman da yake dashi Kuma amma har suka sake shafe wasu lokutan masu yawa ba'a samu wanda ya sake samun nasara akan abokin gwaminsa Domin dodon yana kare hare haren da rukyan yake kawo masa ne da wani bakin almudi Wanda da zarar almudin ya hadu da takobin hannunsa saidai kaji kara ta tashi tareda tartsatsin wuta idan kuwa Ya kawo masa duka da wannan almudi ya kauce duk dirkar ginin daya samu take yake rugurguzata WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA JARUMI RUKYAN BAYAN YA KUBUTA DAGA DAKI NA FARKO YANZU KUMA YA SHIGA CIKIN DAKI NA BIYU +++++++++ +++++++++ Al'amarin gimbiya suhaila kuwa lokacin data rabu da wannan bakon dattijon Mai ilimin sanin abinda zai faru gaba Yayinda ta kama hanyarta ta komawa gida sai zuciyarta ta shiga rudani sakamakon bayanin da wannan dattijon yayi mata Domin tasan abu ne da bazai taba yiwuwa ba ta hada kanta da abokin adawar mahaifinta Don hakan kamar cin amana ne gashi mahaifin nata Kuma yin hakan kan iya jawo rushewar alakar dake tsakaninta dashi Tana cikin yin wannan tunanine taji dokinta yaja tunga ya tsaya da tafiya Kawai saita lura da cewa ta iso gidan sarautar mahaifin ta ne Don haka saita sauka daga kan dokin take wata badakariya tazo taja dokin ta tafi dashi zuwa bargar dawakai Ita kuwa gimbiya suhaila sai ta wuce izuwa cikin gidan sarautar zuwa nata bangaren Duk inda ta gifta saidai kaga dakaru da masu hidima acikin gidan suna durkusawa sunayi mata jinjina A wannan lokaci damuwa kala biyu ce a zuciyarta ta farko itace abindaya faru tsakaninta da mahaifinta Ta biyu kuwa bayanin wannan tsoho agareta Kawai saita tsinci kwakwalwarta cikin tunani daban daban Dangane da hukuncin daya kamata ta yanke kawai saita dauko wata kwalba ta zinare wacce take cike dam da wata giya mai dadin gaske Amma bata bugarwa sosai ta zuba acikin kofi ta fara

Chapter 2 of 21