Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hadiye mutun goma alokaci guda suji kamar basu hadiyi komai ba Yayinda wadannan halittu suka kyallara idanunsu sukayi arba dasu Farhan take suka falfalo da gudu kansu da nufin su dasa musu wawa Nantake shima Farhan yayi kukan kura ya afka musu ita kuwa nauwaratul hasnal har zuwa wannan lokacin bata bude idanunta ba kuma bata daina karanta dalasiman tsafin da take karantawa ba Koda Farhan ya hadu da wadannan halittu take suka kacame da azababben yaki mai matukar muni da razanarwa mai ban tsoro Saboda tsananin mugun yawan da suke dashi sai gashi sun lullubeshi kamar an ajiye kwayar gero atsakiyar gidan tururuwa tako ina sai faman kawo masa hsri suke yana karewa tareda mayarda martani Yana cikin wannan haline ya tuna da nauwaratul hasnal wacce a wannan lokaci take cikin nazari ahallarar tsafi bata ma San abinda yake faruwa ba Kuma a wannan lokaci har wasu daga cikin dodannin sun nufi inda take gadan gadan Take Farhan yayi kukan kura wanda saidaya razana halittun suka danja da baya Cikin tsananin zafin nama ya dinga tarwatsasu da kaifin takobinsa domin zuwa inda nauwaratul hasnal take Koda ya rage saura kiris tsakanin nauwaratul hasnal da wadannan halittu take Sai ta rikide wasu nauwaratul hasnal din guda biyu masu matukar kama da ita suka fito daga tsagin jikinta na dama Dana hagu Saidai su wadannan guda biyun suna dauke da makaman yaki a hannayensu Komai Kellen kurillar mutum bai isa ya iya banbance tsananin ta gaskiyar ba da wadannan guda biyun Da bayyanarsu Sai suka sanya nauwaratul hasnal a tsakiya suka fara kare farmakin da ake shirin kai mata Nanfa guri ya Kara hargitsewa da karafkiyar karafa da rurin halittun duk inda ta durfafa saidai kaga wadannan masu kama da itan sun juya wajen sunata ragargazar halittun tareda bata kariya Acan gefe daya kuwa Farhan ne a tsakiyar su kamar iblishi yana kai musu sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta Hakanan duk inda yasa gaba saidaya kaga yana zubar da halittun kasa kamar Ana sassabe a gona Aduk sanda yakai musu sara saidai kaga kaifin takobinsa ta tafi da kawunan diya da guda goma Kuma yana fadan ne cikin kuzari babu alamun gajiya a tare dashi Har aka shafe sa'o'i sama da bakwai batareda an tsayar da wannan fada ba A sannan ne hankalin halittun ya tashi sakamakon ganin yadda yake musu muguwar barna Ba Tareda sun sami damar yi masa Koda kwarzane ba shi kuma bai Dakata da shayar dasu gidauniyar mutuwa ba Don haka Sai lokaci guda suka guys daga bangarensa suka koma inda nauwaratul hasnal take sukayi mata kawanya da nufin dasa mata wawa tareda mataimakanta Tunda shi sun tabbatar da babu yadda zasuyi dashi WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA SADAUKI FARHAN BAYAN GUGUWAR TSAFI TA RABA SHI DA 'YAN UWANSA ++++++ ++++++ +++++ Al'amarin gimbiya Husnaila lokacin da wannan guguwar ta shureta bata sauketa a ko'ina ba Sai a birnin farisa da yammaci tsakaliya alokacin kowa yana gudanar da harkokinsa kamar yadda aka saba Yayinda mutane sukayi arba da ita sai suka fara gudu azatonsu yar harin sumame ce sakamakon ganin ta bakuwar fuska agunsu Cikin kankanin lokaci guri ya rikice da guje guje Kodata lura Koda ta lura halinda suka Shiga sai tayi sauri ta janyo rawani ta rufe fuskarta dashi Sannan ta dauko madubin tsafinta ta shafeshi domin ta nemi inda zata samu makwanci Acikin madubin ne ta gano Manyan gidajen kwanan garin masu tsadar gaske Batareda bata lokaci ba ta mayarda madubin tsafin nata ta nufi hanyar da zata kaita babban gidan kawunan garin wanda yake kusa da masarautar birnin Bata jima tana tafiyaba ta isa gidan wanda ya kasance babban gida kuma kerarre wanda babu kamar sa a kaf fadin birnin inka dauke gidan sarauta Ko ina acikin birnin kewaye yake da dakaru masu yawan gaske dauke Manyan makaman yaki Yayinda suka hango tahowar gimbiya huraisa cikin wannan Shiga da tayi sai suka gyara rukon makaman su suka tsaya jiran isowarta azatonsu 'yar fashi ce Ba tareda fargabar komaiba kuwa taci gaba da tunkararsu Koda ya rage baifi saura taku goma ba Sai taja tunga ta tsaya Sannan daya daga cikin masu tsaron ya karaso gaban kofar. Ya dubeta yace Yake wannan bakuwa wacece ke kuma meke tafe dake ? Dajin wannan tambaya sai ta basu amsa cikin irin yarensu tace Nice gimbiya Husnaila 'ya agurin sarki lasmar na birnin sin kuma nazo ne domin na kama dakin da zan kwana idan gari ya waye naci gaba da tafiya Kodajin wannan batu sai badakaren yayi murmushin mugunta sannan yace Idan har kinson Shiga wannan gida dolene ki bude fuskarki sannan ki biya ninki biyu na abinda mutanen wannan gari suke biya Batareda gardamar komai ba kuwa ta kwance nadin dake kan fuskarta sannan ta dauki curin kamar kudi ta jefa masa Cikin sauri badakaren ya dauki jakar kudin hannunsa na kakkarwa ya fara lissafawa sakamakon ganin da yayi adadin yawan kudin yakai kudin da suke samu a akwana hudu na duk bakin da suke kama hayar gidan Cikin rawar jiki yasa yasa yaransa suka bude mata kofa ta wuce ciki Tana Shiga ta iske gidan ta iske 'ya'yan sarakai tare dana masu fada aji acikin birnin sai sharholiyarsu suke Cikin gidan kuwa an kawata shi ainun da kayan alatu nau'i daban daban irin na sarakai Acan gefe guda kuwa 'yan mata ne kyawawa sai tikar rawa sukeyi agaban wasu katti don sanya musu nishadi Mafi yawan mutanen dake wannan guri attajiraine, sarakai da kuma kasurguman 'yan fashi wadanda suka Shahara anahiyar Yayinda suka hango tahowarta take suka fara yafuto junansu suna nuna gimbiya Husnaila Ita kuwa sai ta kau Dakanta kamar bata gansu ba Kuma ta koma gefe tayi zamanta Zamanta keda wuya sai wata ma'aikaciya tazo ta ajiye mata nau'ikan abinci da abinsa iri daban daban domin gusar da yunwar dake addabarta Har Husnaila takai hannu da nufin fara cin abincin don tana matukar jin yunwa Sai ta tuna da wanda take matukar kauna wato sadauki Farhan Lokaci guda hannunta ya fara kakkarwa ta kasa cin abincin sakamakon tunawa da abin daya faru tsakaninta dashi Ta kuma tuna cewa a halin yanzu dolene 'yan uwansa suci gaba da yunkurin hallaka dashi Don haka ya zama dole itama tayi kokarin bashi kariya Koda kuwa aboyene Amma Koda ta tuna cewa ayanzu shi zuciyarsa bata tareda ita ta karkata ne akan lasmira Sai taji bakin ciki ya turnuke ta kuma taji ya zama wajibi tayi iya kokarinta don ganin bai hadu da lasmira ba Nanfa taji ta kasa samun nutsuwa dole saita duba halinda yake ciki Don haka sai ta karanta wadansu dalasiman tsafi ta tofa akan teburin abincin dake gabanta Take teburin yayi haske sai dai kuma maimakon fuskar farhan ta bayyana ajiki sai taga nauwaratul hasnal acikin madubin shi kuma ta kasa ganinsa Nantake taji zuciyarta ta buga da karfi Nanfa ta Kara zage damtse Domin janye ta daga madubin tsafin nata amma sai Abu ya gagara Saboda bakin ciki bata san lokacin bata rafka uban ihu ba wanda ya janyo hankalin mutanen dake gurin ya dawo kanta Kawai saita sunkuyarda kanta akan teburin ta fashe da kuka tareda rera dadadan baitocin yabo ga masoyin nata Tana cikin wannan haline saiga yarima ramsin ya shigo cikin gidan abincin tareda dakaru fiye da dari abayansa masu bashi kariya Agabaki daya birnin farisa babu azzalumi wanda yake takurawa mata kamarsa Saboda tsananin tsoron da suke masa saida ta kai 'yan mata sun daina fitowa daga gidajensu domin da zarar yayi ido biyu da mace tofa ta karfi da yaji zai sa dakaru sa kamo masa ita don yayi lalata da ita Idan kuwa tayi taurin kai tofa zaiyi mata fyade ne abainar jama'a ko kunya baya ji Idan kuwa mace ta sami juna biyu dashi tofa zai turo dakaru ne a sirrance su kasheta Yayindaya lura gaba daya mata sun koma buya agidajensu sai ya koma binsu har cikin gidan agaban iyayensu ya aikata mugun nufinsa akansu Lokacin da yarima ramsin ya shigo wannan gidan abinci sai guri yayi tsit kai kace mutuwa ce ta gifta Kowa ya mike tsaye domin girmamawa shi kuwa sai ya kurawa kowa ido yanayi musu wani kallon banza A wannan lokaci ne yayi arba da gimbiya huraisa wacce har a wannan lokaci bata dago da kanta ba Wannan ne ya tabbatar masa da cewa lallai ita bakuwa ce a wannan nahiya Don haka dolene ya koya mata hankali kuma yaci mata mutunci kamar yadda ya saba yadda ko agaba zataji tsoron haduwa dashi Ba tareda bata lokaci ba kuwa ya wuce inda take sunkuye fuskarsa cike da murmushin mugunta Yana zuwa daidai kanta sai ya kai hannunsa da nufin ya taba ta Ba zato ba tsammani sai yaji tayi caraf ta kama kansa ta buga da teburin dake gabanta Take kan basa yayi kwatsa kwatsa kamar an buga kwai akan dutse ya fadi kasa matacce Koda dakarun sukaga abinda ya faru ga shugabansu take suka zazzare makamansu suka afka mata da nufin su hallaka ta Kash!!!!! Hakika rashin sani yafi dare duhu inda ace sun san abinda zai faru da basuyi gangancin tunkararta ba Domin Koda suka tunkareta sai itama ta Shiga cikinsu ta dinga budasu da karfin tsiya Nanfa guri ya rincabe jini ya dinga fallatsi yana kwaranya akan kasa Sautin karafkiyar karafa ta cika dodon kunne cikin abinda bai wuce dakiku goma ba ta Bazar da dakarun Adaidai wannan lokaci ne sarki farsad ya iso gurin tareda dubban dakarunsa Domin tuni labari ya riske shi kan babban laifin data tafka masa Da zuwansa Sai ya umarci dakarun dasu afka mata Aikuwa take sukayi kukan kura suka afka mata gaba daya Koda ya rage baifi saura taku uku ba a tsakaninsu sai sukaji an daka musu tsawa daga gefe guda sannan wata iska mai karfi ta shuresu ta watsar dasu Ba kowane ya aikata wannan Aiki ba face boka shuraim wanda ya kasance dan uwa na jini ga sarki farsad A ka'idar sarautar garin shine wanda za'a baiws sarautar birnin amma saboda baya ra'ayi sai yaki karba ya gwammace abarshi ya cikagaba da aikin bokancinsa Cikin kakkausar murya sarki farsad ya dubeshi yace yakai dan uwana akan wanne dalili zaka hanani daukar fansa akan abinda wannan yarinya ta aikata min? Dajin wannan tambaya sai yayi murmushin karfin hali sannan ya matsa kusa dashi Cikin karamar murya yace Kayi hakuri yakai dan uwana ka sani cewa yaki a wannan lokaci bashida amfani Domin koda zaka tara gaba daya dakarun sannan ka nemo aron wasu daga kasashen makobtaka ba zamu iya samun galaba akan wannan yarinya ba Badon komai ba sai don irin sadaukantakar da take da ita Bama dakarun mu kadai ba hatta n din nan babu yadda zan iya da ita domin an renetane acikin kwalbar tsafi mai karfin Gaske Amma kamar yadda ka sani Komai na duniya Yana da nasa lagon To itama tana da nata lagon shine abokinta Farhan wanda take matukar sonsa fiye da kowa a rayuwarta Mu kuwa dashine zamu kafa mata tarkon da zata fada mu binne ta Da goma fadin haka take suka umarci dakarun dasu koma da baya Ba tareda bata lokaci ba suka fice daga gidan suka barta ita kadai acikinsa sai ragowar dakarun da suka rage A sannan ne ta iya samun damar cin abincin dake gabanta amma ko kadan batajin dadinsa jinsa take kamar madaci abakinta Badon komai ba sai don abinda ta gani acikin madubin tsafinta Tana cikin wannan haline Kawai saita ga gidan ya fara girgiza kai kace kasa ce zata tsage ya nutse a karkashinta Nanfa hadiman suka rikice suka fara gujeguje don ceton rayuwarsu Daga can saiga wani shirgegen bakin aljani ya ratso rufin dakin ya shigo ciki mai matukar muni Saboda matukar girman da aljanin yake dashi saida gidan ya ruguje gaba daya Nanfa aka fara kallon Kallo tsakaninta da aljanin daga can sai ya zube kasa cikin girmamawa yace Barkanki da hutawa gimbiya Husnaila ya agurin sarki suraif Dajin wannan batu saita dubeshi tace kai kuma wanene kuma meke tafe da kai ? Koda jin wadannan tambayoyi sai ya dago da kansa yace ni sunana marna'ul safran kuma na fito daga jinsin bakaken aljanu na bangon duniya tsagin gabas Badon komai nazo nan sai domin mu hada kai duk mu biyun mu biya bukatun dake gaban mu Bukatarki ta farko itace ki riski dan uwanki ki rabashi da macen dake tare dashi Sannan ki rigashi mallakar sarauniyar kyau wato lasmira To a halin yanzu ni kadai ne zan iya biya miki wannan bukata Domin babu wani aljani da yake da karfin guduna duk duniya. Saboda ina iya zagaye duniya cikin abinda bai wuce yini guda ba kachal Ni kuwa Abu daya Kawai nake nema a wajenki Wannan Abu kuwa ba komai bane face digon jinin nauwaratul hasnal wacce ke tareda dan uwanki Domin gama hada wani sihiri da mahaifina yake aikatawa don farfado da kabilar mu daga doguwar suman shekaru ashirin da mahaifinta ya jefasu aciki Idan kuwa har bamu iya karya wannan shiri to. Nan da wasu shekaru kabilarmu zata shafe daga doron kasa Dani da mahaifina bamu da ikon tunkararta Domin da zarar mun yi hakan zamu kone kurmus Amma ke ina da tabbacin zaki iya wannan Aiki Idan har kin amince zamu yimin wannan Aiki tofa nima a shirye nake n zama bawanki har zuwa sanda zaki mallaki lasmira Kodajin wannan batu sai tayi shiru tana nazari acikin zuciyarta Anan jefa taga bata da wani zabi face tabi bayansa idan kuwa karya yake mata da zarar ta gane take zata yake shi ta hallaka shi Da gama wannan tunani take tace masa ta amince Nantake kuwa ya rankwafar da bayansa ta haye ta zauna Zamanta keda wuya sai shima ya bude manya Manyan fuka fukansa guda dari hudu da doriya ya tashi sama da ita cikin azababben gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya Tunda huraisa take bata tabajin labarin aljani mai karfin karfin gudu kwatan kwacin marna'ul safran ba Saboda yadda yake kada fuka fukansa da karfin gaske, ta yadda acikin dakiku kadan yake shafe tafiyar watanni WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA GIMBIYA HUSNAILA BAYAN TA HADU DA ALJANI MARNA'UL SAFRAN ++++++++ +++++++++ +++++++ Acan kuwa Al'amarin sadauki Farhan lokacin da wadannan dodanni suka juya inda nauwaratul hasnal take da nufin yi mata taron dangi domin sanin ba zasu sami nasara akan farhan ba Koda ya lura da nufin su sai ya dinga kure musu gudu yana rafkesu da takobinsa Kan ajima ya tuni yayi musu gagarumar barna wacce tafi ta farko A wannan lokaci tuni kogon ya gama malalewa da jinin dodannin tareda gawarwaki Saida gaba daya fuskarsa da jikinsa suka yi caba caba da jini Yana cikin wannan haline kwatsam sai yaji an harbo masa kibiyoyi guda biyu daga nesa Take kibiyoyin suka fasa kirjinsa suka fito ta gadon bayansa Jini yayi feshi daga kirjin nasa Kafin yayi wani yunkuri sai ya sake jin an jefo masa mashi wanda saidaya faso ta kwuibin cikinsa Bai san lokacin daya kwallara ihu ba Saboda tsananin zafi da zugin dayaji Yayin da yayi baya gaba taga taga kamar zai fadi amma koda yaje daf da kasa Sai cake takobinsa ya tokare da ita bai yadda ya fadi kasa ba A sannan ne ya hango sadauki safran daga can nesa ruke da baka a hannunsa yana mai kyalkyala dariyar mugunta Koda ganin haka take sai ya daina jin duk wani zugi da radadi Nantake ya gyara tsayuwarsa tareda zare wuka daga kugunsa ya jefa masa Kafin yayi wani yunkuri tuni wukar ta datse hannun da yake ruke da bakar jini yayi tsartuwa Daga dungulmin hannun nasa Sannan yasa takobinsa ya karye kibiyoyin dake jikinsa da kuma mashin Sannan ya yagi rigarsa ya daure raunikan dake jikinsa don tsayar da jini Ya ci gaba da yakin a haka ba tareda ya nuna alamun gajiya atare dashi ba Kai sai ka dauka ma kara masa kuzari ake Domin a wannan lokaci yana yaki ne da dukkan karfin sa tareda zafin nama, juriya da bajinta Ya hana dodannin kuntatawa nauwaratul hasnal itama acan gefe daya dakarunta sunata kokarin bata kariya Kodata lura da halinda yake ciki sai hankalin ta ya tashi sakamakon sanin cewa tabbas idan aka ci gaba da yakin a haka komai juriyarsa dole ya sare sakamakon jinin dake zuba ajikinsa dayin wannan tunanin saita kara zage damtse wajen sarrafa dakarun nata da alkaluman tsafi A sannan ne jiri ya fara dibarsa ya dinga layi sakamakon dafin kibiyoyin da ke jikinsa Idanunsa suka lumshewa amma duk da haka bai yadda ya yarda takobinsa ba A daidai wannan lokaci ne safran bayyana da dungulmin hannunsa wanda har yanzu ke digar da jini Hannun damansa kuwa ruke da takobi tsirara, fuskarsa amurtuke babu annuri Daga days gefen kuwa mufran shima da takobi tsirara sai murmushin mugunta Yake Yayinda farhan ya kyallara ido yayi arba dasu sai ya gyara rukon takobinsa Domin ya tabbatar da cewa wannan karon dolene ayi dauki ba dadin da yafi na farko Acikinsu wajibi ne daya ya rasa rayuwarsa ko shi ko kuma su Kafin ya gama tunanin da yake tuni duk su biyun sun falfalo da gudu kansa suna masu karaji da kururuwa Take shima ya afka musu sunasuna haduwa suka kai masa mahaukacin sara a dokin wuyansa Cikin zafin nama ya kaucewa saran nasu suka sari iska Koda takubban nasu suka hadu sai wani tartsatsin wuta ya tashi tareda karar haduwar karfe karfe Nanfa suka kacame da azababben yaki mai matukar muni Hakika sadauki Farhan ya cika namijin gaske mai matukar juriyar wahala duk da cewa akwai dafi mai karfi ajikinsa ga kuma jiri na dibarsa kamar zai fadi Sai gashi a hakan ya zame musu alakakai sun kasa samun nasarar lakutar jikinsa al'amarin daya matukar daure musu kai kenan Kaico koda aka fara wannan bakin artabun sai wadannan dodannin suka dakata da yakar nauwaratul hasnal suka kewaye suka zama 'yan Kallo Don haka cikin tsawa ta umarci dakarun dake bata kariya dasu kai masa dauki Take suka falfala da azababben gudu inda su farhan ke fadan Tun daga nesa farhan ya dinga yi musu nuni dasu dakata karsu karaso amma sukaki Koda zuwansu sai suka kaiwa safran suka akan ruwan cikinsa Cikin zafin nama yasa takobinsa ya kare hare haren nasu Cikin fushi yasa kafa ya gabzawa daga daga cikinsu duka akan ruwan cikinta Saboda karfin dukan saida tayi sama sannan ta gwaru da jikin dirkar gini Dayar kuwa sai yasa hannunsa ya shekaru tareda dagata sama kafafunta sai wutsil wutsil da reto suke a sama Don kare kanta amma abu ya gagara Ita kuwa nauwaratul hasnal ta gaskiyar sai ta fara shure shure daga inda take har tana kakarin mutuwa saboda azabar da take ji sakamakon shakar da akayiwa mai bata kariya WANENE YAKE RASA RAYUWARSA TSAKANIN FARHAN DA KUMA. 'YAN UWANSA? SHIN NAUWARATUL HASNAL TANA TSIRA DAGA WANNAN SHAKAR DA AKAYI MATA? SHIN GIMBIYA HUSNAILA TANA BIYAWA ALJANI MARNA'UL SAFRAN BUKATARSA ? WANE IRIN MATAKI SARKI FARSAD YAKE DAUKA AKAN GIMBIYA HUSNAILA ? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR WHATSAPP NO 09133502477 LIKE, COMMENT AND SHAREKARAGAR AJALI +++++++6 PART B ++++LBR HABIBULLAH KBR Koda ganin abinda yake faruwa ga sarauniya nauwaratul hasnal sai nan take farhan ya daka tsalle ya gabza safran mahaukacin duka a gadon bayansa Saboda karfin dukan baisan lokacin daya saki wuyanta ba tayi gaba taga taga yana neman faduwa amma sai ya cake bai yarda yaje kasa ba Cikin rashin sa'a koda farhan ya je kasa sai kafarsa ta zame sakamakon jirin dake dadinsa kansa ya gwaru da kasa ya fadi kasa sumamme Koda ganin wannan gagarumar nasara da suka samu take sai su mufran suka daga makamansu alokaci guda suka kai masa mahaukatan hare hare da nufin suyi gunduwa gunduwa dashi Ba zato ba tsammani Kawai saiga gimbiya Husnaila ta bayyana kamar walkiya bisa gadon bayan aljani marna'ul safran amma bai yarda yaje kusa da nauwaratul hasnal ba Take ta daka tsalle daga inda take tana mai yin karaji gami da kururuwa ta dira a tsakiyar su Ta kare dukka hare haren da suka kawo masa Koda takubban su suka hadu da tata sai tartsatsin wuta ya tashi kamar Ana aza wuta a makera tareda Sautin haduwar karfe da karfe Sannan ta gaba musu duka a kan fuskokinsu wanda saboda karfin dukan saida sukaga taurarin wuya a idanunsu Suka dan jajja da baya taga taga taku uku saboda mamakin ganin ta Itakuwa nauwaratul hasnal bata san lokacin da zancen zuci ya kamata tace Lallai wannan shi ake kira da turnuku fadan iblisai wanda wani daga waje bai isa ya shiga ciki ba" Tana cikin wannan zancen zuci ne Kawai taga su safran sun kara tasowa gimbiya Husnaila zasu saka ta atsakiya suyi mata taron dangi Kuma ta tabbatar da cewa indai sukayi haka tabbas zasu sami nasara akanta Koda ganin haka take ta rikide ta koma soffar rikakken batoyi Ta tashi sama ta feshe su mufran da wuta mai karfin Gaske sannan ta shuri su farhan da gimbiya Husnaila a gadon bayanta Kawai sai wata farar kofa ta haske ta bayyana suka shige cikinta Take itama kofar ta bace bat kamar bata taba wanzuwa ba Koda ganin wannan abu daya mufran da safran suka kwallara ihu saboda tsananin takaici Suka bi daidai inda kofar hasken ta bayyana da Kallo Suna kokarin dawo da ita da sihirin tsafinsu amma sai yakiyin tasiri don dole suka hakura ++++++++ ++++++++ +++++++ Yayinda gimbiya lardisa tazo daidai nan a karatunta sai ta dakata Sakamakon ganin da tayi Wani mahaukacin gumi yana tsatatsafowa daga jikin jarumi rukyan Kamar wanda aka tsomashi acikin ruwa jikinsa yanata kakkarwa kai kace zai fado daga kan gadon da yake kwance Cikin tsananin tashin hankali ta ajiye littafin dake hannunta ta tashi Da nufin nemo mai kula da lafiyarsa Kwatsam sai taji yasa hannunsa ya riko hannunta tareda yaye mayafin dake rufe dashi Koda juyowarta sai taga taga ciwukan dake jikinsa suna warkewa gaba dayansu Kafin cikar wasu dakiku masu yawa tuni sun gama wakewa kamar basu taba wanzuwa ba Al'amarin daya matukar daure mata kai kenan ta saki baki tana kallonsa Koda ya lura da kallon da take masa sai ya tuntsure da dariya sannan yace nasan kinyi mamakin ganin samun kafiyata alokaci guda Ba komai ne ya janyo hakan ba face karfin sihirin da muka samu a yayin da muke karbar wannan horon A halin yanxu inajin karfin da ban tabajin kamarsa ba kamar zan iya daukar duniya gaba dayanta Don haka a yau zan fita neman SAIFUL LAIHAN kafin su boka surkais su riga mu Yana gama fadin haka sai ya sauka daga kan gadon da yake kwance Ya shiga cikin wani daki daban ya kullo kofa Jim kadan sai gashi ya fito cikin gagarumar shigar yaki mai matukar ban tsoro Hannayensa kuwa cike da gurayen tsafi a damatsansa Yana fitowa sai ya dubeta tareda cewa yake ma'abociyar hikayoyi Nayi rantsuwa da kabarin kakana nan gaba kadan sai nayi jarumtakar da baki taba rubuta irinta ba acikin wannan kundi naki Don haka nan gaba kadan zanso ki karasa bani labarin hikayar yadda gabar wadannan 'yan uwa take karewa da wanda yake nasara Sai kuma wanda yake mutuwa daga cikinsu, Kai hardama lokacin da boyayyen sirrin dake tsakaninsu yake tonuwa Nangaba kadan idan mun sami lokaci zaki ci gaba da bani wannan daddadar hikayar mai cike da rudani acikinta da abubuwan al'ajabi Yanzu kema sai ki tashi ki shirya mu fita neman abinda ke gaban mu Ba tare da bata lokaci ba itama ta mike ta shiga cikin masaukinta jim kadan sai gata ta fito sanya da nata kayan yakin Wadanda akayiwa ado da zaren zinare ba karamin kyau kayan sukayi mata ba kasancewar anyi su ne da zaren zinare Sannan ta daukar karamar akwatin da take sanya kundun hikayoyi aciki ta mai dashi ciki ta rufe Sannan ta daureshi agadon bayanta daga nan ta fito daga cikin dakin ta iske rukyan a tsaye Yana jiranta Kodaya ga irin shigar da tayi sai ya tuntsure da dariya yace Ai wannan shigar da kikayi kadai ta isa ta nunawa duniya cewa ke kadai zaki iya yakar duk abinda ke cikinsa kuma kiyi nasara akansa Dajin wannan batu saita girgiza kanta tareda maida masa da martanin murmushi tareda cewa Ka iya bakinka domin akoda yaushe hakkin daka raina shine yake tsone maka ido Daga wannan furuci babu wanda ya kara magana daga cikinsu Sannan rukyan ya runtse idanunsa tareda karanta wadansu dalasiman tsafi azuciyarsa Fara karatun keda wuya sai gidan da suke ciki ya fara girgiza kamar zai dilmiye a karkashin kasa Komai na gidan kuwa sai ya bar kan doron

Chapter 13 of 21