Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kar hasken ya cutar dasu Jim kadan saiga boka farraz ya bayyana yana mai kyakyata mahaukaciyar dariya Fuskarsa cike da fara'a kai kace anyi masa kyautar duniya gaba daya Koda ya gama shigowa cikin kogon dutsen sai ya ci gaba da dariyar tasa daga bisani kuma ya murtuke fuska ya dubeshi yace Yakai wannan aljanin hakika hukuncin kisa ne ya dace dakai sakamakon daukar 'yar leken asirina da kayi Saidai kuma kayi sa'a alkalamina ya riga ya juye akanka ba zan cutar da kai ba Domin hakan da kayi ba karamin taimakona kayi ba Inaso ka sani daga ni har hadimai na babu mai ikon shiga masarautar sarki gulbas ya fito a raye duk da karfin sihirin da nake dashi Kai bama ni ba hatta su jarumi rukyan da boka gulbas Domin kowa a gidansa sarki ne, don haka ba karamin sihiri na acikin wannan gida ba Wannan ne yasa duk wanda yayi kuskuren shiga cikin gidan sarautarsa daga cikin mu Take jikinsa zai zagwanye kamar narkakken mai Don haka nima na sami wannan tsuntuwar na sihirceta na turata cikin masarautar tana yi min leken asiri tana dawowa ta sanar dani Ba tareda na wahala ba ina daga nan nasan duk motsin da sarki gulbas da gimbiya suhaila suke Saidai kuma abu daya daya daure min kai shine Akwanakin baya gimbiya suhaila ta kebanta da wata kuyangarta mai suna ruwaisa acikin turakarta Wanda tunda ta karanta wasu dalasiman tsafi take allon tsafi na ya daina aiki ban iya ganin abindaya faru a sannan ba Kuma nasan dole abinda suka tattauna akansa abune mai matukar mahimmanci kuma dole sai na gano mai suka tattauna akai Yanzu kai zan sakeka ka koma gurin mai gidanka duk da cewa ina da ikon kasheka amatsayinka na yaron abokin gaba ta Amma zan kyaleka ka tafi saboda ka taimake ni ammafa ka sani koda ka koma wajensa baka isa ka sanar dashi wannan abubuwan da suka faru anan ba Dajin wannan batu sai hankalin aljanin ya dugunzuma ya dubi boka farraz yace Kai kuwa menene dalilin dayasa ka dauki gaba ka dora akan sarki gulbas da gimbiya suhaila? Dajin wannan tambaya sai yayi dariya Yace Ba wai dasu kadai nake gaba ba Ina gaba ne da duk wani mai burin mallakar KARAGAR AJALI Domin tun ina karami mahaifina yake bani labarin ta Kuma nima na dauki kudurin mallakarta saidai kuma tawaya ta guda daya ce Itace rashin karfin damtse da iya yaki, babu yadda banyi ba akan in zama mayaki amma na kasa Bisa dole na hakura hakane yasa su sarki gulbas suka wuceni Amma badon hakaba da tuni na dade da hawa kan KARAGAR AJALI Duk da haka kuma banfidda raiba domin dukkansu babu wanda ban ginawa mugayen tarkuna ba wadanda ina da yakinin dole sai daya daga cikinsu ya fada Domin ni kalar baiwar da ubangiji yayi mini kenan ina da baiwar tsara tuggun da zaiyi aiki a shekaru dubu nan gaba Wannan ne iya amsar da zan iya baka a halin yanzu Yana gama fadin haka take ya bace daga gurin shida tsuntuwarsa ta tsafi Suka bar shi shi kadai a sannan ne yaji jikinsa ya saki har zai iya sarrafashi Take ya kada fukafukansa ya tashi sama cikin tsala gudu domin yaje ya sanar da sarki gulbas abinda ke shirin faruwa Saboda karfin gudun da yakeyi bai jima yana tafiya ba ya isa bayan katangar gidan sarautar Yana isa take ya rikide ya kara komawa siffar sarki gulbas sanye da alkyabba Da kwagirin sarautarsa a hannunsa ya karasa bakin kofar shiga masarautar Da isarsa bakin kofar sai shugabar dakarun ta rugo aguje ta rissina tace Barkanka da dawowa ya shugaban mu kawai saita koma cikin dakaru suka fara aikin bude kofar masarautar wacce ta kasance katuwar gaske Kamar kofar shiga wani babban birnin Ita kanta kubar kofar katuwar gaskece domin sai dakaru goma sun hadu suke iya dagata Koda ya wuce sai suka mai da kofar suka rufeta bam Wata daga cikin dakarun ta dubi shugabarsu tace anya kuwa daya daga cikin mu yaga lokacin da sarki gulbas ya fita daga cikin gidan nan? Dajin wannan tambayar sai ta girgiza kai tace tabbas bata nan ya fitaba Amma babu yadda zamuyi domin mutum ne da gidansa sai yadda ya tsara Tana gama fadin haka saitayi shiru da bakinta bata kara cewa komai ba Lokacinda aljanin nan ya shiga cikin gidan sarautar cikin siffar sarki gulbas Sai ya dinga tafiya cikin sauri don ya isa cikin turakar sa ya sanar da sarki abinda yake shirin faruwa Duk inda ya zo giftawa take sai kowa yabar abinda yake yi ya kame yana girmama shi Har ya isa bakin turakar ya bude kofar ya shige ciki, aikuwa kafarsa na shiga ciki sai yaji kansa ya sara da karfi Take anan ya manta da duk abubuwanda da boka farraz ya fada masa da isarsa gaban sarki gulbas sai ya fadi yana zazzare idanu ya kasa bayanin Komai Ya tsaya kame kame , da ganin haka sai sarki gulbas ya kura masa idanu yana nazarin halin da yake ciki Daga can kuma sai yace yakai hadimina tabbas na lura da cewa bai kamata ka kasance acikin hadimai na ba Domin ba zaka iya biya min bukatu na ba, Kuma ina mai tabbatar maka cewa nan da dan wani lokaci zan gano abinda kwakwalwarka ta kasa dauka. Kai kasheka zanyi yanzu Dajin haka sai aljanin ya rikice ya fara rokon sarki gulbas yayi masa afuwa amma ko saurarensa baiyi ba kawai sai ya nunashi da yatsansa aikuwa take wata wuta ta fito daga jikinsa ta kama aljanin ta babbakeshi Kurmus tokarsa ma ta tashi tabi iska kamar babu abinda ya faru Ita kuwa gimbiya suhaila lokacin da wannan iskar ta shureta ta buga ta da bango Ta dauke wannan tsuntsun tsafi tana mikewa saitaga tuni iskar da tsuntsun sun bace mata da gani kawai sai tayi tsaki Ta ciki yatsanta tace Du yadda akayi nima bani kadai ce nake dakon su mahaifina ba akwai wani daban Amma duk halinda ake ciki lokaci zai bayyanashi Tana wannan zancen zucin saita koma dakinta ta janyo labule da tagogi ta rufe Sannan ta zauna akan kujerar da take dakin a gaban kujerar kuwa taburin cin abinci ne An zuba abinci da abin sha iri daban daban na alfarma Ba shiri ta kama cin abincin tana gamawa saita tashi ta shiga bandaki da yi wanka sannan ta shafe jikinta da turarruka kala daban daban Tana gamawa saita shige cikin wani daki dake turakar tata Inda anan ne take ajiye duk wasu kayan sirrinta, tana shiga dakin ta turo kofa ta rufe Sannan ta cire tufafin da suke jikinta gaba daya, Ta dauko wasu daban wadanda suka kasance kayan yaki ne domin gaba dayansu an kerasune da zallan bakin karfe Irin kirar kwararrun makeran birnin sin ta sanya ajikinta Wohoho abinka da mace me kyau musamman ma idan ta hadu da kyawu dan uwanta Aikuwa koda ta sanya wadannan kayan yaki sai gashi sun fito da tsantsar kyawun da allah ya bata da kuma siffarta ta jarumtaka Ita dai gimbiya suhaila ta kasance doguwar macece amma ba can ba Tana da zara zaran yatsu sannan kaurin jikinta daidai misali ne Idanunta kuwa dara dara ne masu haske kamar madara Gashinta baki ne sidik sai sheki da walwali yake ya zuba har zuwa mazaunanta kirjinta a cike yake, hakama kugunta, cikinta kuwa ashafe kamar bata cin abinci Hakika duk. Inda ake kwatancen mace mai cikar kyawu gimbiya suhaila ta kai Tana gama sanya wadannan tufafin sai ta dauki takobin ta Ta rataya a gadon bayanta sannan ta dauki kwari da bakanta ta rataya su Sannan ta fito daga cikin dakin ta maida kofa ta rufe Ta fita daga cikin turakar tata gaba daya ta janyo kofa ta rufeta Sannan ta nufi inda bargar dawakai take Tun daga nesa idan dakaru suka ganta take suke buda mata hanya ba tareda sun tsaya yi mata tambayoyi ba Saboda ita kadaice mai kalar wannan kayan yakin kuma tana sanya su ne idan za'a fita yaki ko kuma zataje farauta farautar sirri**************KAR­AGAR AJALI 3 ******************PA­RT C ************LBR ********************­*HABIBULLAH KBR Lokacinda gimbiya suhaila ta nufi bargar dawakanta Cikin shigar yaki sai dakaru suka dinga bude mata kofofi tana wucewa kai tsaye Su kansu sunyi mamakin irin wannan fita da zatayi domin kuwa batayin irinta sai dai idan za'a fita yaki ko kuma wata gagarumar gasar jarumtar Amma sai aka rasa wacce zata iya tunkararta ta tambayeta dalilin wannan shigar tata acikinsu Tana isa bakin kofar bargar sai mai tsaron kofar ta janyo kofar ta bude ta Da wata murtukekitar kuba mai siffar dawisu, ai kuwa take sakatun jikin kofar suka bubbude Kai tsaye gimbiya suhaila ta shige cikin bargar inda aka killace dawakai kala daban daban wadanda aka hora su sosai suka saba da gwagwarmaya Tana shiga ta zabo wani farin ingarman doki wanda ajikinsa akwai ratsin baki baki Kofaton kafarsa kuwa gashi ya lullube shi, ba tareda bata lokaci ba ta daurawa dokin sirdi sannan ta zabureshi ta fice daga cikin bargar ta kama hanya ta fita daga gidan sarautar gaba daya duk wanda yaga gimbiya suhaila tareda wannan ingarman doki yayinda suke wannan gudu dolene ta burgeshi Ganin yadda dokin ya kara mata kwajini duk inda dokin ya taka da kafafunsa saidai kaga kura ta tashi ta turnuke sama Saboda karfin takun nasa da kuma yadda yakeji da samartaka Tana fita bayan gari saita juya linzamin dokinta zuwa wata hanyar daban Hanyar da zata kaita can gidan gonarta inda anan ne take shakatawa Tun tana karama sarki gulbas yasa aka gina mata wannan gida domin nishadinta ita kadai Daga baya ne ta dawo gidan sarauta da zama amma duk da haka tana lekawa lokaci zuwa lokaci Shi dai wannan gidan shakawa girmansa yakai na wani karamin kauyen Kuma an kawata shi ainun da kayan kawa Takanas gimbiya suhaila ta dinga turawa kasashen duniya ana samo mata karfafan bayi masu matukar jarumta da juriyar wahala ana killace su acikin wannan gida Ba tareda mahaifinta ya sani ba a kullum babu abinda sukeyi face baiwa kansu horon yaki ta fannoni daban daban Kuma ba don komai tayi hakan ba face don ta dinga jarraba jarumtakarta akan tasu Saidai kuma tun lokacin bata taba zuwa bangaren da suke ba don haka basu santa ba itama kuma bata sansu ba Saboda tazarar dake tsakaninsu Akullum basu da burin da tafi su ganta ido da ido don suga irin jarumtakar da take takama da ita har ta dauki nauyin kula da rayuwarsu Domin kuwa tayi musu alkawarin idan koda daya daga cikinsu ne Ya sami nasara akanta to daga wannan rana dukkansu sun kubuta daga rayuwar bauta sun zama 'yantattu sun kubuta daga rayuwar bauta har abada Wannan daliline yasa akoda yaushe suke kara zage damtse Kullum dare da rana babu abinda suke face kara baiwa kansu horon yaki Domin su sami damar kubuta daga wannan mummunar rayuwa da suka tasu suka gansu aciki Lokacinda gimbiya suhaila ta isa kofar gidan sai taja linzamin dokinta ta tsaya cak dokin yayi tirjiya gami da haniniya ya daga kafafunsa sama Cikin sauri wata badakariya ta leko ta cikin wata 'yar karamar taga Koda tayi arba da lta sai ta saki murmushi sannan ita da abokan aikinta suka fara kokarin bude tangamemiyar kofar gidan Dukkansu sukace barkanki da zuwa wannan gida ya mai martaba Shugabarsu tace lale marhaban da zuwanki gidan renonki tabbas da ganin wannan ziyara da kika kawo mana zata kawo sauyi da farinciki awannan gida Dajin wannan batu sai ta maida mata da martanin murmushi Sannan ta wuce kai tsaye suka maida kofa suka rufe Maimakon ta wuce bangarenta sai ta juya linzamin dokinta ta zuwa bangaren da bayin suke A wannan lokaci yamma tayi rana tana shirin faduwa Don haka dukkanin bayin gidan sun fara kokarin komawa cikin dakunansu kamar yadda suka saba Adaidai wannan lokaci ne kwatsam sai sukayi arba da gimbiya suhaila Duk da cewa basu taba ganinta ba labarinta kawai suke ji amma saida suka ganeta Saboda banbancin sutirar dake jikinta data sauran hadiman da suke gidan Nanfa dukkansu suka kakkame kamar gumaka suka tsaya kallonta guri yayi tsit in banda sawun Kofaton dokinta babu abinda ake ji, Kai tsaye ta shiga tsakiyar harabar gidan ta sauka daga kan dokinta Ta kadashi da tafin hannunta take dokin yayi haniniya ya zabura da gudu yabar harabar Y koma gefe guda ya tsaya shima kamar dan kallo Alokacin gaba daya hadiman gidan suka rugo da gudu suka kewaye harabar gidan suna sauraron abinda zata fada Tsawon dakiku masu yawa tana tsaye tana kallonsu ba tareda tace uffan ba Daga can sai tayi gyaran murya tace Yaku hadiman wannan gida a yau nazo wannan gida ne domin cika burin da nake dashi Na Sanin matsayin dana taka a fannin jarumta Kamar yadda nayi alkawari abaya Zan fafata yaki ni kadai da gaba daya bayin da suke cikin gidan nan Kuma inaso su sa a ransu cewa idan har suka zage damatsansu wajen yaki dani to kamar sun kujerar da rayuwarsu ne gaba daya daga kangin bautar da suke ciki Ta juya inda bayin suke tace inaso ku yakeni tamkar nice na kashe makusantanku na kawo ku wannan guri Kada ku duba matsayin da nake dashi, domin kuwa koda kashe ni kukayi nayi muku alkawarin babu abinda zai sami daya daga cikin ku Kuma alkawarin da nayi muku tun farko shima yana nan babu abinda zai hana cikashi Tana gama fadin haka saita saki doguwar alkyabbar dake jikin ta ya zamana daga ita sai kayan yakin dake jikin ta Ya zamana daga ita sai kayan yaki zalla ajikinta, sannan dakarun suka debo wasu makaman yaki masu yawan gaske da hatsari kala daban daban suka zube agaban bayin domin kowa ya dauki kalar makamin da yafi kwarewa wajen iya fada dashi Take suka dinga rububin daukar makaman suna murmushi Mai kama dana farin ciki ko kuma mugunta, Ita kuwa shugabar dakarun hankalintane yayi matukar dugunzuma ganin yawan dakarun Cikin sanyi ta matsa gabanta tace Ya shugabata ina mai baki shawara kada Kiyi yaki dasu a lokaci daya zaifi miki kyau kuyi daya bayan daya Domin sarkin yawa yafi sarkin karfi, kada ki manta wadannan ba kananun jarumai bane na musamman ne su Dajin haka saitayi murmushi tace aini abinda nakeson yi kenan don haka keda hadimanki sai ku zama 'yan kallo Abangaren bayin kuwa kallon raini Kawai sukeyi mata Domin suna ganin kamar duka daya zasuyi mata su kakkarya kashushuwan jikinta saboda banbancin kirar jikinsu da tata Har suna wani dan murmushi mai kama da na mugunta ko kuma raini Suna gama diban makaman nasu duk sai sukayo kanta suka saka ta a tsakiya suna kewayata Ita kuwa sai ta tsaya cak a inda take ba tareda ta koda zare takobinta daga cikin kufe ba Lokaci guda dukkansu suka rugo aguje kanta hannayensu ruke da makamai tsirara suna kukan kura Suna zuwa daidai inda take duk sai suka kai mata sara da makaman da suke hannayensu Aikuwa cikin bakin zafin nama kafin makaman nasu su sauka ajikinta tuni ta dunkule jikinta ta daki kasa da hannayenta Take ta tashi sama ta kaucewa takubban nasu suka hadu a tsakiya tareda tashin tartsatsin wuta Gaba dayansu sai suka daga kawunansu sama sannan sukayi tsalle suka bita domin a hadu a saman Suna haduwa a saman sai tayi Wata katantanwa. Atsakiyarsu ta kwarfi kafafunsu gaba daya suka zubo kasa Kamar ana ruwan ganyayen bishiya, amma koda suka zubo duk sai duk sai suka kara mikewa tareda daura damararsu Suka sake afkawa kanta suna kai mata hare hare ta ko'ina gabas yamma kudu da arewa kamar masu kokarin daukar ranta Suna masu karaji wanda ya gauraye gidan gaba daya wohoho!!! Kaji mace mai kamar maza wacce take kan ganiyar gasawa maza gumba a hannu Hakika idan kaga yadda wadannan bayi suke kai mata hari sai ka dauka kasheta suke sonyi Domin su kansu dakarun dake kewaye da harabar hankalinsu a matukar razane yake Saboda rashin sanin abinda zaije ya komo a wannan bakin artabu da akeyi Sun san cewa idan har wani mugun ciwo ya sameta ko kuma ta rasa rayuwarta to babu makawa sarki gulbas ba zai kyalesu ba Don haka kawai atsaye suke sun zazzare makamansu suna kallon fafatawar da ake Duk irin wannan fada da akeyi hankalin gimbiya suhaila a kwance yake Domin tana iya kare duk irin hare haren da suke kawo mata har ma da maida martani tamkar hannaye da dari ne da ita Duk inda kuwa ta durfafa saidai kaga tana budawa kanta hanya ta karfin tsiya Duk yawan nasu sai ya zama na banza don an rasa wanda zai iya koda lakutar jikinta Sai gashi ta zama kamar shaidaniya acikinsu, saboda duk sanda tayi kukan kura ta durfafa a tsakiyarsu saidai kaga maza suna zubewa kasa magashiyan kamar busassun karare Amma sai kaga sun karkade jikinsu sun sake mikewa sun afko mata da mugun nufi Don ganin sun samowa kansu yanci Nanfa guri ya kara yamutsewa kura ta tokare sararin samaniya Acikin wadannan bayin ne wani garjeje daga cikinsu wanda yafi kowanne daga cikinsu girma da kwarjini kuma ya kasance bakar fata ne Saboda bakinsa har Wani maiko fatar jikinsa takeyi Kai kace an mulke jikinsa da mai Zuciyarsa ta kufula ganin duk lokacinda suka dauka suna karbar horo yana neman zama na banza Ba shiri ya lallabo ta bayanta ta bayan ta ya daga takobinsa ya kai mata ma haukacin sara a gadon bayanta Saidai kash tuni ta jiyo hucin kaifin takobin ba shiri ta sunkuya takobin ta wuce Sannan ta shuri kafafunsa ta daga shi sama ta jijjigashi tayi jifa dashi Kai kace ta shuri karamin yaro sannan ta dira akansa ta dora kaifin takobinta akan wuyansa , ba tareda ta yanka wuyan nasa ba. Bisa dole ya saki takobinsa ta fadi kasa Har ta juya Ta dauke kafarta daga kansa ta juya zata tafi Sai ya shammace ta yayi katantanwa ya kwashi kafafuwanta Nan da nan tayi baya taga taga kamar zata fadi amma sai ta juya jikinta ta dira akan hannayenta ba tareda ta fadi kasa ba Alokacin har dakaru sun zaburo da gudu amma sai ta dakatar dasu Kawai Itama saita daka tsalle ta fara jerawa bakin bawan kutufo da kafafunta a saman tun yana tsaye saidaya fadi kasa magashiyan yana furzar da jini daga bakinsa Sannan ta mika masa hannu ta tasheshi tsaye fuskarta cike da murmushi tace Tabbas daga yau kun kwatowa kanku 'yanci daga yanzu babu wani wanda zai kara bauta akarkashin masarautar nan, Kuma yanzu take zaku chanja tufafin jikinku ku koma nahiyar da aka sayoku acan wanda kuma yake ganin zai zauna atare damu to ga guri nan Dajin haka sai farin ciki ya turnuke bayin suka fara shewar farinciki suna masu yi mata addu'ar samun nasara Tana gama fadin haka saita umarci dakaru dasu debo tufafi da abin guzuri su rabawa bayin Take kuwa dakarun suka tafi domin cika umarnin ta. Awannan rana gimbiya suhaila ta shirya musu gagarumin bikin 'Yanta su acikin gidan gonar tata Bayan an gama ne ta sallame su gaba daya WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ACIKIN BIRNIN IKARUL UZBAR BAYAN GIMBIYA SUHAILA TA TSIRA DAGA BINCIKEN DA SARKI GULBAS YAKE KAN YI ******* ******* ******** Acan bangaren jarumi rukyan kuwa washe gari da sassafe ya aika aka kirawo masa gimbiya lardisa cikin turakar sa Domin ya fada mata hukuncin daya yanke game da tafiyar da suke shirin yi na naman takobin saiful laiham da kuma karagar ajali Cikin kankanin lokaci ta karaso turakar tasa fuskarta cike da fara'a Awannan lokaci babu kowa acikin turakar sai shi kadai Da isowarta sai ta sami guri ta tsaya a kusa da gadon da yake kwance tana mai cewa Barkanka da safiya namijin duniya kuma gwarzon karni Naji dadin wannan kiran naka domin zuciya ta acike take da zumudin jin hukuncin daka yanke game da wannan tafiya da zakayi, Shin ka amince da muyi tafiyar nan tare? Dajin wannan tambaya saiya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta a tsanake cikin nutsuwa fuskarsa babu alamar wasa ta yadda ita kanta saida taji ta tsargu dashi Yace Yake suhaila da farko kafin kiji hukuncin dana yanke inaso nayi miki wasu tambayoyi kuma inaso ki amsa min su bisa gaskiya ki sani idan kikayi mini karya na gano ki zan yanke duk sanayyar da take tsakanina dake Da farko Inaso ki sanar dani hakikar abinda yasa kike son tafiya neman saiful laiham tare dani Da kuma dalilin dayasa ke baki fita neman ta da kanki ba Sannan Inason Sanin dalilin dayasa kike rubutun kundun tarihi? Dajin wannan tambayar sai lardisa tace Da farko dai inaso ka sani da tambayarka ta farko data karshe duk amsa iri daya ce dasu Ba komaine yasa na zabi Tafiya neman saiful laiham tare dakaiba face sanin cewa Kaine mutumin da nake yakinin zaka iya mallakar karagar ajali Saboda atarihin duniya matasa sune masu iya tsallake duk wani mataki na sadaukantaka da kuma daukaka Ni kuwa ban isa ba ma na iya ketare koda matakin horon yakin da kukayi bare kuma na shiga neman saiful laiham Domin bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane Ni kuma burina shine naga mun mallaki wadannan abubuwa tare koda kuwa ni bazan amfana dasu ba, domin na rubuta sunana akarshen littafin kundun tarihi don duniya ta dinga tunawa dani Game da tambayarka ta karshe kuwa Ba komaine yasa nake rubuta wannan littafi ba face don tunawa da mazajen jiya wadanda sukayi jarumtar da bai kamata duniya ta manta dasu ba. Dajin haka sai yayi murmushi Yace lallai kina da aiki agabanki, yanzu na amince da tafiya dake amma zan gargadeki kada kiyi tunanin zakiyi amfani da kyawun da kike dashi na 'ya mace kice zaki ci amanata Koda gama fadin haka saita bushe da dariya al'amarin daya natukar bashi mamaki kenan yace ke kuwa mene dalilin wannan dariya taki? Dajin wannan tamabaya saita gyada kai tace ai dole nayi dariyadomin tuni kyawu ya dena burgeni, Tun daga sanda na tsinci hikayar sadauki farhan na birnin sin da sarauniyar kyawu ta duniya wato lasmira 'ya agurin almajiri sulban na kauyen Manarul munnas Ka sani tundaga farkon kafuwar duniya kamar yadda akadinga yin zamani kala daban daban na gwarazan sadaukai wadanda suka sha gwagwarmayar rayuwa wasun suma soyyayya ta zama sanadiyar ajalinsu kamar su SADAUKI HANTARU DA GIMBIYA LARZIYA, SHADDADU DA 'YAR UWARSA ZIYA'ULHAK, HULKAS SAI KUMA SADAUKI HASSANUL BASARI DA GIMBIYA BAHJAHAT wasun su sunyi gwagwarmaya ne saboda soyayya har suka rasa rayukansu ta dalilinta To haka akayi zamanin Sadauki FARHAN da Sarauniyar kyawu ta duniya wato lasmira , Tun da nake karance karance ban taba karanta labari mai sosa zuciya ba kamarsa domin saida na kwana ina hawaye alokacin da nake karantashi Domin acikin sa ne na fuskanci cewa kyawu yana iya sanya mutum cikin matsalar da ba zai iya kwatar kansa ba ta yadda mutun zai gwammacewa mutuwa da rayuwarsa Kuma kyau yana iya rikita duniya, ya janyo kashe kashen rayukan da basu ji ba kuma basu gani ba Hakika ba'a taba samun mace wacce kyawunta ya rikita duniya tundaga jinsin aljanu dana mutane ba face kyawun lasmira Kai atakaicema saida kyawun ya zama annoba agareta Kyau shi kadai yana iya zama silar rabuwar masoyi da masoyinsa , ka sani wannan hikayar ta kunshi tsantsar tsagwaron soyayya, cin amana, zalunci, jarumta da kuma tsafe tsafe Ta yadda idan kaji shi da kai dasu sarki gulbas duk sai kun raina kanku ni kaina wannan hikayarce ta sanya min sha'awar rubuta kundun tarihi Tun lokacin dana tsinceta arubuce ajikin wata jemammiyar fata acan birnin misra lokacin da ina karama acikin wani tsohon kogon dutse wanda ya shafe shekaru dabu da doriya babu halittar da take shiga cikinsa sakamakon tsananin tsoronsa da mutane sukeyi domin azatonsu wasu mugayen halittun ne acikinsa Yanzu kaf duniya babu inda zaka iya samin wannan hikayar sai cikin kundun tarihi ,na rubutashi ne ababin farko kuma kai ma baka da ikon karantawa face da izini na Cikin mamaki rukyan yace ke kuwa dama kina da wannan hikayar? Ina mai rokonki daki gaggauta sanar dani ita don inji yadda rayuwar sadauki farhan da lardisa ta kasance da irin jarumtar da sadauki farhan yayi a zamaninsa har zuwa sanda ya mallaki karagar ajali. Kodajin haka sai tayi masa guntun murmushi mai kama da murmushin mugunta kokuma gadara sannan tace Sabodame zan sanar dakai wannan labari alhalin bansan hukuncin daka yanke akaina ba. Caraf sai ya tari bakinta da cewa ai tuni na amince da tafiya tare dake matukar zaki sanar dani hikayar sadauki farhan da sarauniyar kyau wato lasmira.KARAGAR AJALI 4 +++++++++PART A *************LBR HABIBULLAH KBR Dajin wannan bukata ta rukyan sai lardisa ta tuntsure da dariya sannan tace Aikuwa yanzu zan fara baka labarin soyayyar Sadauki farhan da lasmira Duk da cewa labarine mai matukar tsawo zanyi kokari na takaice maka shi Idan kuwa damar hakan bata samu ba zan karasa makashi koda alokacin tafiya neman karagar AJALI ne Tana gama fadin has saita mike tsaye kyam ta kama hanyar komawa cikin turakarta shi kuwa rukyan kawai saiya bita da kallo ba tareda yace uffan ba Tana isa cikin masaukin nata sai ta dauko wata 'yar karamar akwati wacce aka kerata da zinare sannan ta koma cikin turakar da jarumi rukyan ke kwance Da zuwanta sai ta sami guri ta zauna a kujerar dake kallon gadon da yake kwance suna fuskantar juna, daga can kuma saitaja dogon numfashi sannan ta dora tafukan hannayenta biyu akan akwatin Take wani haske ya fito daga cikin akwatin ya ratsa cikin tafin hannayen nata Faruwar hakan keda wuya sai akwatin ta bude da kanta wani katon littafi ya bayyana acikinsa Wanda akayi masa bango da karfen zinare da ratsin zubardaju Ajikin bangon littafin anyi rubutu kamar haka

Chapter 7 of 21