Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasa suka kama yawo akan iska amma wani abin mamaki babu ko burbushen kasa da take zubowa Lokaci guda kuma sai ga rufin gidan ya bude kansa kamar an bude littafi hasken rana ya dallare ko ina acikin gidan Sai ga wani shirgegen aljani mai matukar girma da kirar sadaukai ya ratso ta saman rufin ya shigo cikin gidan Kai da ganin wannan aljani kasan dolene ya kasance jarumin gaske wanda yasha gwagwarmaya arayuwarsa Tunda gimbiya lardisa take bata taba ganin aljani mai girma da kwarjininsa ba a rayuwarta Sai dai tasha jin labarin ire irensu acikin labaranta Koda bayyanar wannan aljani take ya rissina ga rukyan Cikin girmamawa yace Gani ya shigabana mai kake bukata na biya maka nan take komai wahalarsa koda kuwa zan rasa rayuwa ta? Koda aljani rafkana yazo daidai nan a zancensa sai sadauki rukyan yayi masa wani murmushi mai kama dana mugunta daga bisani yace Yakai rafkana ayaune nakeso kayi mini aiki na karshe don haka Inaso ka dauke ni Tareda abokiyar tafiyata ka kaimu can tsuburin makabur ka shigar damu cikin duniyar da take kasan wannan duniyar tamu Wacce akewa lakabi duniyar hallaka domin dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAN wacce ake ajiyeta a tsakiyar ita wannan duniyar Bisa kan narkakken dutsen wuta…… . Kafin ya gama rufe bakinsa tuni aljani rafkana ya fashe da kuka har yana birgima akasa tareda cewa Ya shugabana kayi mini rai hakika wannan Aiki haka yafi karfina bazan iya ba Domin na dade inajin labarin wannan duniya a bakin mahaifiyata tun ina karami ta fada min cewa Inda ace za'a debo watar Wannan narkakken dutse cikin mudu daya ta isa ta narkar da wannan duniyar gaba daya Iyayena da kakannina duk sun mutu ne akan tafarkin duniyar hallaka don dauko ita wannan takobi Acikin kofofin duniyar hallaka guda dubu babu kofar da basu jarraba shiga ta cikinta ba Amma ko daya daga cikinsu bai. Dawo a raye ba Ina mai tabbatar maka da cewa mutuwa tafi tunkarar wannan duniyar sauki Don haka ina rokon daka gaggauta kashe ni yanzu akan na tunkari wannan duniyar Koda yazo daidai nan azancensa sai rukyan ya bushe da dariya daga nan kuma yace Haba namijin duniya kada ka manta da gwagwarmayar da kasha abaya Ka tuna da fafatawar da mukayi a cikin duniyar fatalwa wacce saida muka shafe sati guda muna yaki da mugayen fatalwu babu hutu Kuma babu ci babu sha kamar ba zamu tsira ba Amma saboda dagiya da kuma kwarin gwuiwar da muka sa a zuciyar mu sai da muka sami nasara akansu Ina tabbatar maka da cewa muddin muka kwarin gwuiwa azuciyar mu tabbas a wannan karon ma zamu sami nasarar tarwatsa duniyar hallaka mun dauko saiful laihan daga cikinta Kuma mun karya alkadarinta munyi abinda iyaye da kakanni suka kasa yi Hakadai yaci gaba da karfafa masa gwuiwa har saida yaji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa Yaji wani kwarin gwuiwa ya shige shi don haka take ya rankwafar da gadon akasa suka haye suka zauna a sannan ne wani aljani ya kawo musu kayan guzuri suka karba Zamansu keda wiya sai rafkana ya bude fuka fukansa ya tashi sama Yana fita daga harabar gidan sai gidan ya koma kamar yadda yake abaya Nanfa aljanin ya dinga tsala a zababben gudu a sararin samaniya kai kace duniyar gaba daya zai bari saboda tsananin karfin gudunsa Saida suka shafe lokaci mai tsawo suna tafiya ba tareda dayansu yake uffan ba Kowa yana tunanin wani abin daban Don haka sai rukyan ya katse shirun dake tsakaninsu yace Yake ma'abociyar hikayoyin mazan jiya tun dazu zuciyata a kage take dason jin cigaban hikayar da kike bani don haka zanso ki karasa bani ita Don naji yadda zata kasance tsakanin wadannan tagwayen 'yan uwa masu abin al'ajabi Dajin haka sai ta gyada kanta tareda yi. Masa tattausan murmushi sannan ta zaro littafin taci gaba dakaratun afili kamar haka ++++++++ ++++++++ +++++++ Lokacin da wannan batoyi ta shuri su sadauki farhan daga wannan kogon dutse Sai gashi tana tsala mahaukacin gudu dasu kamar walkiya tana ratsawa ta karkashin kasa da kuma tekuna kamar yadda haske yake ratsawa ta cikin gilashi ba tareda wani abu ya tare shi ba Basu sauka ako'ina ba sai Cikin wata masarauta mai dumbin tarihi Wacce ta shafe dubunnan shekaru da shudewa Suna sauka bisa turba sai wannan batoyin ta rikide ta koma nauwaratul hasnal Nantake ta share dattin dake kasa itakuma huraisa ta kwance rawanin dake kanta aka shimfidar dashi a kasa Cikin tashin hankali nauwaratul hasnal ta durfafeshi da nufin saka masu magani don rage masa zugin da yake ji Kawai sai ganin Husnaila tayi ta zare takobi ta kawo mata mahaukacin sara a dokin wuya da kaifin takobin ta Maimakon takobin ta yanka jikinta sai gashi ta ratsa ta ta wuce tamkar ta sari iska Cikin murmushi nauwaratul hasnal ta dubeta tace ba fada dani ne abindaya kamata ki fara yi ba A binda yafi a halin yanxu shine ceton rayuwarsa daga halin da yake ciki Idan har bamuyi da gaske ba zai iya rasa rayuwarsa akowanne lokaci Dajin wannan batu sai jikin huraisa yayi sanyi ta mayarda takobi ta cikin kufe Duk su biyun suka dukufa akansa suna kokarin tsayar da jinin dake zuba ajikinsa Don har a sannan bai farfado daga doguwar suman da yayi ba Cikin sauri huraisa ta dauko wani garin magani takai hannunta da nufin zuba masa akan raunin Kafin Hannun ta yakai jikinsa tuni nauwaratul hasnal ta rike hannunta tareda cewa Wannan ba shine makarin dafin dake jikinsa ba Da zarar kin kuskura kin zuba masa wannan garin magani take jikinsa zai fara zagwanyewa har ya rasa rayuwarsa Idan har muna son samun makarin wannan gubar dolene mu koma inda aka fafata wannan kazamin yaki Mun kwato kuttun kibiyoyin sadauki safran domin acikine kadai makarin wannan dafi yake Kafin sannan dolene daya daga cikin mu ya arawa farhan rayuwarsa ma'ana ruhinsa Domin ya sami karfin da zai iya wannan Aiki acikin Abinda ba zai wuce sa'o'i uku da rabi ba Daga ke har shi babu wanda zai iya zama da wannan dafi ajikinsa na tsawon wadannan sa'o'i face ya zama gawa Ni kuwa zan iya zama dashi har na tsawon sa'o'i biyar A halin yanxu abin da ya rage masa a rayuwa ba zai haura rabin sa'a ba Don haka ni yanzu zan bashi aron rayuwata in yaso ke ku tafi tare dashi ku samo kokarin Amma fa ki sani rayuta ta dogara da taku idan kukayi nasarar dawowa kafin sa'o'i biyar na tsira Idan kuwa kuka haura zan mutune da farincikin mika rayuwata ga masoyina Dajin wannan furuci dai huraisa taji Kamar an watsa mata tafasasshen ruwa amma sai ta danne kishin nata Ba tareda bata lokaci ba nauwaratul hasnal ta fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana tofawa akan raunin dake jikinsa Nantake saiga wani bakin Abu mai kama tsutsa ya fito daga cikin kirjinsa ya shiga nata kirjin Faruwar hakan keda wuya take ta sulale ta fadi kasa tana shure shure dafara ta fara fita daga bakinta Kafin 'yan dakiku tuni ta zama sumammiya Adaidai wannan lokaci ne farhan ya farfado daga mawuyacin halin da yake ciki Kodaya kyallara ido yaga huraisa agabansa agefensa kuma yaga sarauniya nauwaratul hasnal ce akwance Saiya mike zumbur kamar babu abindaya same shi ya dubeta cikin rashin yarda yace wanene ya kawo ni wannan guri kuma me ya faru ga abokiyar tafiyata? Dajin wannan tambaya ba tareda bata lokaci ba ta zayyane masa duk abindaya faru Kodajin wannan bayani take yaji tausayinta ya kamashi a karon farko Yaji dolene yayi mata halacci don haka nan take ya mike tsaye tareda gyara damararsa Take yayi girgiza ya fuka fukai suka fito daga kafadunsa ya budesu ya tashi sama Ganin haka yasa itama Husnaila ta falfala da azababben gudu n gaske Tana fita daga masarautar ta iske aljani marna'ul safran a tsaye a bakin kofa sai kada fuka fukansa yake Ba tareda bata lokaciba itama ta dane bayansa ya luluka da ita cikin gajimare Yabi bayan sadauki farhan iya karfin gudun sa domin su isa wannan kogo kafin su mufran su fice daga cikin sa Sai a sannan ne ta gane cewa tabbas Akwai banbancin karfin sihiri tsakanin ta da farhan Kasancewar a wannan karon suna gudun tareda amfani da karfin sihirinsu domin takaice tafiyar dake gabansu Domin da kyar da sidin goshi marna'ul safran Yake iya bin sawun farhan Abinda basu sani ba shine shi kansa farhan a wannan lokaci mamakin da yakeyi kenan domin baisan inda ya sami wannan gagarumin karfin sihiri ba Ba komai ne ya janyo haka ba face aron ruhin da nauwaratul hasnal ta bashi Cikin kankanin lokaci suka bayyana acikin wannan kogo da suka fafata yaki aciki Adaidai lokacin da su safran ke shirin fita daga cikinsa Kawai sai gani sukayi farhan ya faso ta saman rufin kogon Kamar saukar aradu ya bayyana acikinsa Sumul mul kamar babu abindaya sameshi Al'amarin daya matukar razana su kenan har suka dan ja da baya arazane saboda mamaki domin suna san cewa matukar aka sanyawa mutun wannan dafi dake jikin kibiyar mufran bai isa ya iya wuce sa'a guda a raye ba Adaidai. Nan ne farhan tayi musu wani murmushi mai kama dana mugunta yace Kunyi mamakin ganina a raye ko ? Duk da mugun tanadin da kuka jima kunayi akaina wanda baiyi tasiri ba to a yanzu sai ku shirya tarba ta Koda gama fadin haka sai ya afka musu yana mai karaji da kururwa ba tareda bata lokaciba Suma suka afka masa koda ya rage baifi saura taku uku ba a tsakaninsu sai gimbiya huraisa ts faso ta karkashin kasa bisa kafafunta Suna haduwa gaba dayansu sau suka kara kachamewa da wani sabon bakin artabun mai tsananin firgitarwa da kuma ban sha'awa ga 'yan Kallo Domin fada suke mai matukar ban al'ajabi sakamakon ganin yadda karfinsu tareda iya yakinsu sukazo daya Husnaila da safran suka ware guri daya Yayinda shi kuma farhan suka ja tunga da mufran Fara wannan fada keda wuya sai kogon ya kara birkicewa fiye da farko sawayensu suka dinga dudufniya wanda ya nemi ya haddasa girgizar kasa a cikin kogon Babu abinda zai kara baka tsoro face ganin yadda suke kaiwa junansu mugayen hare hare domin ganin bayan juna Duk sanda wani daga cikin su. Yakaiwa abokin gwaminsa hari da zarar ya kauce duk abinda ya samu take yake tarwatsewa Koda kuwa dirkar gini ce take take karyewa ta fadi kasa Idan junansu suka samu sai kaga sun shanye kamar babu abindaya same su duk da cewa sunaji ajikinsu Saida suka shafe kusan sa'a guda suna wannan fafatawa ba tareda dayansu ya sami akan daya ba Sakamakon yadda karfinsu da iya yakinsu suka zama daya A wannan lokaci sunyi rushe rushe da yawa acikin kogon harya soma kokarin rugujewa Sannan ne fa hankalin farhan ya dugunzuma sakamakon tunawa da yayi da halin da nauwaratul hasnal take ciki Mai kama da rayuwa da mutuwa Idan har basuyi da gaske ba tabbas tabbas zata iya rasa rayuwarta Koda gama wannan tunani sai. Ya kara zage damtse A can bangaren Husnaila da safran ma haka al'amarin yaci gaba da kasance wa Domin kuwa kaiwa junansu kyawawan hare hare suke wanda da zarar takubban su sun hadu da juna sai dai kaga tartsatsin wuta gami da turiri suna tashi sama Saidai kuma. Ita tanayin fadan badon ta ceci nauwaratul hasnal bane Tana fadan ne domin taga ta riga farhan kwatar kuttun safran domin ta sace shi ta gudu gaba daya Haka dai suka dinga kaiwa junansu sara babu kakkautawa har takai kogon ya fars marmsowa yana neman danne su Ana Cikin Wannan fafatawa ne huraisa ta shammaci safran ta dankara masa duka a agadon baya wanda saboda karfin dukan saidaya dukushe kasa Ai. Kuwa nan take cikin zafin nama tasa hannu ta tsinke kuttun daga kafadarsa Ta ruga da gudu ta dare bayan aljani marna'ul safran ya bude fuka fukansa ya tashi da nufin guduwa Koda safran yaga abindake shirin faruwa take ya nuna aljanin da yatsunsa Nantake wata murtukekiyar sarkar tsafi tayi fitar burgu daga hannunsa ta harde fukai fukan marna'ul safran dai gashi yana reto akan iska Kawai sai safran ya daka tsalle daga inda yake ya dira agadon bayan sa suka ci gaba da fafatawa a haka Karfin dudufniyar kafafunsu ce ta rikits aljani marna'ul safran ya fara layi da tangal tangal a sama yana neman fadowa kasa Tsananin tangal tangal din da yakeyi ne yasa kuttun dake kafadar huraisa ya subuce ya fado kasa Tun kafin ya iso kasa saiga wani shudin ruwa ya kwaranyo daga cikinsa zai zube akasa Koda ganin haka take sai farhan ya taho da mahaukacin gudu Kafin ruwan ya sauka. A kasa tuni ya tara bakinsa ruwan ya zuba acikinsa Sannan ya daka tsalle shima ya haye gadon bayan marna'ul safran Ya tsinke sarkar data daureshi da takobinsa tareda jefo safran kasa Kafin su mufran su kara wani yunkuri tuni wasu sarkokin tsafi sunyi fitar burgu daga karkashin kasa sun daure su tamau Nantake wannan kofar hasken ta sake bayyana suka shige ciki sannan ta kara bacewa kamar farko Basu bayyana ako'ina ba sai Cikin sai masarautar da gangar jikin nauwaratul hasnal ke kwance Suna bayyana sai marna'ul safran ya fice daga cikin ta Gimbiya Husnaila ce ta fara rugawa da gudu inda nauwaratul hasnal take kwance ta tallafo kanta ta dora akan cinyarta A wannan lokaci baifi saura dakiku uku suka rage sa'a biyu su cika ba Koda Farhan ya iso inda take sai ya sunkuya ya kafa bakinsa akan nata ya dura mata wannan ruwan magani Wannan ce damar da Husnaila ta samu ta zaro wata karamar allura da mazubi ta zuki jinin nauwaratul hasnal Kafin farhan ya dago da kansa tuni ta sulale ta bace daga masarautar SHIN NAUWARATUL HASNAL TANA FARFADOWA DAGA WANNAN HALI MAI KAMA DA RAYUWA DA MUTUWA ? SHIN HUSNAILA TANA KAIWA ALJANI MARNA'UL SAFRAN WANNAN JINI KUMA YANA. AMINCEWA DA ZAMA HADIMINTA ? SHIN WANNE KALUBALE JARUMI RUKYAN ZAI FUSKANTA AKARON FARKO NA NEMAN SAIFUL LAIHAM? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR WHATSAPP 09133502477 LIKE, COMMENT AND SHARE PLSKARAGAR AJALI +++++++++++6 PART C ++++++++++++LBR HABIBULLAH KBR Lokacin da gimbiya huraisa ta sulale ta gudu bayan ta debi jinin nauwaratul hasnal Farhan bai dago da kansa ba sai bayan fitar ta Bayan ya dago dinne ya lura babu Huraisa a gurin don haka nan take yaji zuciyarsa ta buga da karfi ya tabbatar da cewa tabbas Akwai mugun abindaya kawo Huraisa Nauwaratul hasnal bata motsa daga dogon suman da tayi ba Sai bayan wasu dakiku kadan a sannan ne idanunta suka fara budewa ahankali Daga baya tayi kwakwkwaran tari guda uku gami da aboyene zuciya Koda tayi arba da farhan daidai da saitin fuskarta sai taji Kamar ta rungumeshi a kirjinta Amma tsananin kunya da jinkai suka hanata aikata hakan , kawai sai tayi murmushi tace Ina mai Godiya bisa ga ceton rayuwata da kayi sannan ta mike daga kwancen Haka shima sai ya bita da kallo bisa jin cewa da tayi ya ceci rayuwarta alhalin itace ta ceci tasa rayuwar Har ya budi baki zaiyi magana sai ta fara numfashinsa da cees ina kuma huraisa ta tafi? Dajin wannan tambaya sai yayi shiru ya rasa amsar wannan tambaya da tayi masa Daga can kuma sai yace yanzu muka rabu da ita domin ta koma can nahiyar data baro A sannan ne farhan ya karanta wasu dalasiman tsafi sannan ya tofa akan raunikan dake jikinsa Ai kuwa nan take raunikan suka hade kansu kamar an shekara dajinsu Bayan nan suka fara shirye shiryen cigaba da tafiya WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A BANGAREN SU JARUMI FARHAN DA SARAUNIYA NAUWARATUL HASNAL BAYAN GIMBIYA HURAISA TA SSKI NASARAR DIBAN JININTA WANDA ZATA BAIWA ALJANI MARNA'UL SAFRAN +++++++ ++++++++ Acan kuwa bangaren gimbiya huraisa kuwa lokacin data debi Wannan jini ta sulale ta gudu Tana fita daga gidan sarautar saita iske aljani marna'ul safran yana ta zaman jiranta Cikin sauri huraisa ta nuna masa wannan battar jinin tace wannan shine jinin da kake bukata don haka sai muyi don haka sai muyi sauri mu bar wannan yanki gaba daya Tana gama fadin haka sai ta haye gadon bayansa shi kuma ya bude fuka fukansa ya Nufi hanyar da zata mai dashi can birninsu cikin azababben gudu domin cika burin mahaifinsa na son dawo da kabilar su. Ta bakaken aljanu doron kasa Saida suka shafe yini guda suna tafiya a sararin samaniya sannan suka fara hango nahiyar bakaken aljanu Suna shiga cikin garin kuwa sai ta cika da tsananin mamaki Badon komai ba sai don ganin yadda birnin ya kawatu ainun fiye da yadda mutane suke kawata nasu Kai harma ya ninka na mutane fiye da sau dari Ko ina acikin birnin gashi ban cike da jinsin aljanu manya da yara mazansu da mata atsaitsaye birjik Kamar Kayi musu magana su amsa Saidai duk jikinsu babu inda yake motsi ko kuma numfashi A sannan ma har kura da Gama lullube jikinsu Gaba daya Wacce idan zaka kankarewa daya daga cikinsu kurar jikinsa Sai ka shafe fiye da wata guda A gefe guda kuma dakarunsu ne cikin shirin yaki ruke da garkuwa cikin shirin yaki Kai da gani kasan cewa alokacin da wannan annoba ta same su suna fafata kazamin yaki ne da wani abokin gabar nasu Lokacin da huraisa ta gama karewa sai ta kara cika da mamakin yadda wannan ibtila'i ya same su duk da irin kirar karfin da suke da Ita Bata san Lokacinda ta tunkari inda wadannan dakaru suke ba ta kai hannu da nufin taba jikin daya daga cikinsu Kwatsam sai taji an daka mata tsawa Wacce a karon farko a rayuwarta ta buga da karfi Bata san lokacin data janye hannunta ba Ta juyo da sauri don ganin daga inda tsawar ta tawo Kawai sai tayi arba da wani dattijon aljani sanye da hular karfe hannunsa kuwa yana ruke da kwagirin tsafi Kallo daya zakayiwa wannan aljani kasan cewa ya jima a duniya Domin a Kallo zai shafe sama da shekaru dubu uku da doriya Cikin murmushin aljanin ya dube ta yace lale marhaban da gimbiya huraisa 'yar sarki suraif mai mulkin birnin sin Yake wannan Gimbiya badon komai na hanaki taba wannan badakare sai domin cetonki Saboda da kin kuskura kin taba jikinsa take kema zaki Shiga cikin halinda suka ciki saboda karfin sihirin da yake jikinsa Kodajin wannan batu sai tace nagode da ceton rayuwata da kayi amma menene ya sanya jama'arka cikin wannan mugun yanayi? Dajin wannan tambaya sai dattijon aljanin yayi shiru Kamar ba zaice komai. Ba daga can kuma sai yace Ba zan iya baki. Amsar wannan tambayar ba domin abune wanda ya shafi rayuwata saidai in sanar dake wanda ya aikata hakan Ba kowa bane face sarki hasnal mahaifin sarauniya nauwaratul hasnal wacce a halin yanxu take tareda dan uwanki Yamzu dai sai ku biyo ni zuwa dakin bokanci na Yana gama fadin haka sai. Ya wuce gaba suka bishi a baya Tafiyar 'yan dakiku sukayi sannan suka isa tsakiyar wani katon daki wanda babu komai acikinsa face kayan aikin bokanci, da tarkace iri daban daban A tsakiyar dakin kuwa an ajiye wata babbar kwatarniyar tsafi wacce aka gauraya nau'in jinin halittu sama da dubu dari uku da doriya acikinta Sai faman zabalbala suke kamar zasu fasa tukunyar su fito waje Koda isarsu gaban wannan kwatarniyar sai yaja tunga ya tsaya Sannan ya miko mata hannunsa tareda umartar ta data miko masa wannan battar da jinin Yake ciki Nan take kuwa ta kwanto battar daga jikin mugunta ta mika masa Take ya bude battar ya dagata sama da nufin juye wannan jinin acikin kwatarniyar Kwatsam sai yaga babu komai acikin don haka cikin tashin hankali ya dubi huraisa yace Ina kika saka jinin ai babu komai acikin battar nan Kodajin wannan batu sai tayi wuf ta karbi battar daga hannunsa Cikin sauri tasa idonta ta leka cikin ta Koda idanun ta suka sauka acikin battar sai. Taga babu komai acikinta face tarin yashi Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan don haka ba shiri ya kwanto madubin tsafinta ta shafeshi don taga Abin daya faru ga jinin Shafar madubin keda wuya sai ga hotonta lokacin da take nuna wa aljani marna'ul safran wannan jinin Ashe ta manta bata rufe murfin battar daidai ba Don haka lokacin da marna'ul safran yake tashi da Ita sama sai wannan battar ta tuntsure jinsin jinin ya tsiyaye akasa Saidai kafin jinin ya sauka akasa saiga boka durgas ya bayyana dauke da tasa battar ya tare jinin da ita sannan ya bace Koda gama Ganin abindaya faru sai gaba dayansu suka kwarara uban ihu wanda saboda karfin sa sai da kasa ta fara girgiza daga bisani kuma suka turbune fuska Mahaifin marna'ul safran ya dubi huraisa yace Yake wannan jaruma ki sani cewa a halin yanzu zama bai kamaku ba Dolene ku tashi ku kara samo wannan kafin lokaci ya kure domin yana daf da kurewa A halin yanzu sun canja salo a gaba dayan duniya , ma'ana sarauniyar kyau wato lasmira tana daf da bayyana Idan kuwa har ta bayyana ba zamu taba mallakar jinin nauwaratul hasnal ba Kai koda ma mun samu babu amfanin da zaiyi mana Yake huraisa ki sani a halin yanzu ba lasmira ce abokiyar gabar ki. Ba Nauwaratul hasnal itace babbar matsalar ki domin idan har tana tare da farhan wata rana sai tace amanarsa ko kuma tayi sanadiyar rushewar duk farincikinsa Ko kuma ta janyo ya rasa rayuwarsa gaba daya Nauwaratul hasnal shu'umar mace ce wacce tasan yaudara gami da cin amana, Sannan kuma tana da karfin basira sosai fiye da yadda kike tsammani Abu daya kachal ta rasa a rayuwarta, wannan abu kuwa ba komai bane face karfin damtse Inda ace ta gado mahaifinta sarki hasnal da sai shuhura a duniya fiye da yadda yayi a zamaninsa Domin da a zamaninsa ne lasmira ta bayyana ina mai tabbatar miki cewa babu abinda zai hanashi mallakar KARAGAR AJALI Yanzu sai ku gaggauta tashi ku tafi neman wannan kafin nan da cikar kwana uku kacal Idan a wannan karon kike iso nan da wannan jinin muka karasa wannan sihiri da nake hadawa kabilar mu suka dawo Nayi alkawarin da kaina zan taimake ki muga bayanta Yana gama fadin haka saiya juya musu baya Nan take aljani marna'ul safran ya shuri huraisa ya dorata a gadon bayansa sannan ya bude fuka fukansa suka tashi sama gaba daya WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN GIMBIYA HURAISA DA SARKIN BAKAKEN ALJANU ******** ******** ******* Al'amarin sadauki Farhan da sarauniya nauwaratul hasnal kuwa Lokacinda suka baro wannan tsohuwar masarautar da nufin ci gaba da tafiya Kwatsam lokaci guda sai suka ga bakin hadari ya tare da guguwa mai karfi alokaci guda sun turnuke duniyar Aka dinga wata. Mahaukaciyar tsawa mai karfin Gaske tamkar zata farka kirajensu ta fito da zuciyoyinsu Gami da walkiya Wacce ta dinga tarwatsa duwarwatsu da tsaunika Saboda karfin iskar dake kadawa saida ta kwance rawanin da suka rufe fusokokinsu Kasa kuwa ta dinga girgiza tana tsagewa , bishiyoyi da duwarwatsu suna fadawa ciki Su din ma sai mafaka suka samu suka samarwa kansu mafaka Suna cikin wannan haline Kawai wani katon tsauni yayi bindiga gami da tsawa Wata mahaukaciyar bakar wuta mai matukar zafi ta kwaranya daga cikinsa Ta nufo inda suke da gudun gaske duk. Inda wutar ta gifta take yake komawa kurmus Abinda Yake garin kuwa sai ya daskare ya koma dutse Koda sukayi arba da wannan wutar take farhan ya kama hannun Nauwaratul hasnal suka falfala da azababben gudu domin ceton ransu Suna gudun ne Iya karfin su tamkar kafafunsu zasu tabo keyarsu Amma Wani Abin tsoro shine duk gudun da suke da zarar sun juyo bayansu Sai suga tsakaninsu da wutar bai wuce taku uku Zuwa hudu ba Nanfa suka kara zage damtse tareda amfani da karfin sihirinsu domin su dakatar da wutar amma sihirin yaki yayi. Tasiri Al'amarin daya matukar kara razanasu kenansuna Cikin wannan haline kafar nauwaratul hasnal ta zame ta fada cikin wani rami da kasa ta rufta Cikin zafin nama kafin ta karasa ciki tuni farhan yasa hannu ya cafo sannan ya fito daga ramin Duk Cikin Abinda bai wuce rabin dakika ba ya goyata agadon bayansa yaci gaba da gudun a haka dauke da ita ba tareda ya tsaya ba A haka yaci gaba da gudu dauke da ita tun safe har rana ta fadi adaidai wannan lokaci ne Wutar ta dauke dif komai ya koma. Yadda yake abaya Haske farin wata mai karfi ya dallare duniya kai kace tsakar rana

Chapter 14 of 21