Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kai wa hannunta dake rike da sarkar wani mahaukacin sara da nufin tsargeshi gaba daya Inbadon tayi saurin kaucewa ba da tuni ya sami nasara akanta , amma duk da haka sai daya yanke ta a gefen Hannunta na dama Kash !!!! Wannan shine babban kuskuren da boka surkais ya aikata domin Inbadon yayi saurin nuna zalamarsa ba da hankali kwance zata bashi Wannan sarkar domin zuciyarsa tafi aminta dashi Koda gama ganin abindaya ga gimbiya sai sarki gulbas ya kwarara uban ihu wanda ya janyo hankalin dakaru da hadiman Gidan gaba daya suka taho da gudun gaske , don su farwa boka surkais Amma sai sarki gulbas ya dakatar dasu sannan ya daka tsalle ya farwa Boka surkais tare da kai masa fusataccen sara a dokin wuya Cikin matukar zafin nama ya sanya takobinsa ya tare saran ai kuwa takubban nasu na haduwa take wani tartsatsin wuta ya tashi Nanfa suka ruguntsume da azababben yaki mai matukar ban tsoro da daukar hankali wanda ya tayar da hankalin gaba daya dakarun dake gefe suna kallo Cikin kankanin lokaci suka hargitsa turakar gaba daya sautin karafkiyar karafa ta cika dodon kunne Kafin a dau wani dogon lokaci suna wannan fafatawa tuni sun yiwa turakar raga raga Tareda kakkarya dirkokin ginin Cikinta wadanda ke ruke da rufin turakar har rufin ya soma barazanar ruftowa Al'amarin daya tayar da hankalin dakarun dake gurin kenan suka fara ja da baya domin sun san Wannan karon ba nasu bane Ita kuwa gimbiya suhaila sai ta tsaya cak a gefe daya tana kallon abinda ke gudana Ba tareda ta kara ko taku daya ba , Al'amarin daya baiwa sarki gulbas mamaki kenan Ganin yadda take da dakakkiyar zuciya alhalin bata kasance mayakiya ba Abinda bai sani ba shine duk tsawon shekarun da suka dauka da ita bai Gama Sanin wacece itaba Acan kuwa bangaren manyan giwayen biyu kuwa fada kara tsamari da tsanani Yake kamar sannan aka soma shi saboda babu alamun gajiya atare dasu Kowanne daga cikinsu bashida burin dayafi yaga ya sami nasara akan abokin gwaminsa Domin kare martabarsa da kuma kimarsa musamman ma sarki gulbas wanda ake fadan acikin gidansa Kafin a dauki lokaci mai tsawo sun rikita Gidan gaba daya kai kace wasu manyan rundunonin ne ke kwafsa yaki Kasa kuwa ta fara tsagewa saboda dudufniyar kafafunsu Suna cikin wannan azababben yaki ne kwatsam ba zato ba tsammani saiga Wata matashiyar budurwa akan Wata kibiyar tsafi ta ratso ta cikin ginin turakar ta shigo cikinta Cikin wani a zababben gudu, Kafin suyi wani yunkuri tuni ta cizge sarkar daga wuyan suhaila Sannan ta tashi sama ta bace musu da gani Duk wannan abu ya faru ne cikin abinda bai wuce rabin dakika ba Da ganin haka dukkansu basu san lokacin da suka wangame bakinsu ba suka daga kawunansu sama Suka dakata da yakin da suke yi take suka daka tsalle alokaci guda tareda naushin rufin turakar Nan take sai gashi sun fasa rufin sun tsaya akan iska Wannan ce damar da boka surkais ya samu yayi amfani da sihirin tsafinsa ya sulale ya gudu Shi kuwa sarki gulbas sai ya tsaya yana ta dube dube ko zaiga inda wannan bakuwar jaruma ta gudu da kuma tarihinta cikin madubin tsafinsa amma sai kasa gano komai game da ita Abinda bai sani ba shine tuni Wannan bakuwar jaruma ta shiga cikin kurkukun karkashin kasa domin dauko aljani hursad bin zaffar Koda ya gama dubansa ya rasa inda tayi sai ya rusa mahaukacin ihu Saboda tsananin takaicin daya turnukeshi sakamakon wannan ne karon farko a rayuwarsa da irin haka ta taba faruwa dashi ko kuma masarautarsa da aka shigo har gida a ka cisu da yaki. SHIN WACECE WANNAN BAKUWAR JARUMA KUMA DAGA INA TAKE? SHIN WANNAN BAKUWAR JARUMA TANA SAMUN DAMAR FITA DAGA WANNAN GARI SHIN GIMBIYA HUSNAILA TANA SAMUN DAMAR DIBAN JININ SARAUNIYA NAUWARATUL HASNAL A KARO NA BIYU? YAYA ZATA KASANCE IDAN HAR DA GASKE ALKALUMAN TSAFI SUN CANJAWA KANSU KADDARA LASMIRA TA BAYYANA , WANENE ZAI MALLAKETA ? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENT AND SHAREKARAGAR AJALI 7 ++++++++PART B +++++++++LBR HABIBULLAH KBR Ba kowa bace ba Wannan bakuwar jarumar data saci wannan sarkar ba face Face jaruma bhajat 'ya agurin sarauniya Marsufa mai mulkin birnin kufa awannan lokaci Ita dai sarauniya marsufa ta kasance gagarumar sarauniya mai karfin mulki gami. Dana tsafi Atarihin rayuwarta sau daya ta taba aure inda tayi aure da wani hamshakin attajiri mai suna hukairu Saidai aranar da aka daura musu aure dashi a daren ta kashe shi sai wayar gari akayi aka tarar da gawarsa Kuma ba Kowa ya hallaka shi ba Face ita da kanta domin tayi. Alkawarin babu namijin da zata zauna tayi bauta agareshi Kawai dai tayi auren ne domin ta samu juna biyun da zata sami magajin karagarta Bincike ya tabbatar mata da cewa a ranar data fara saduwa da namiji a wannan rana ne zata sami juna biyu Haka dai sarauniya marsufa tayi ta renon cikinta har ta haifeshi Inda ta haifi kyakkyawar jaririya mai kyan gaske a wannan rana Sarauniya marsufa tayi. Matukar farin ciki inda ta dinga rabon kudade da dukiya masu yawa ga mutanen birninta inda ta radawa jaririyar suna bhajat Sai da aka shafe mako guda ana shagalin biki A ranar da jaririyar ta cika mako guda ne ta dauki gimbiya bhajat da rana tsaka ta shiga da ita dakin tsatsube tsatsubenta Shigar ta dakin keda wuya saita ajiyeta akan Wani karamin Akwati na haske Sannan itama taja gefe ta zauna akan Wani buzun tsafi tareda tankwashe kafarta ta fara karanta wadansu dalasiman tsafi Aikuwa faruwar hakan keda wuya take iska mai karfi ta fara kadawa acikin kogon da karfin gaske har saidata kwance dogon gashin sarauniya marsufa ya fara yawo a kan iska Jim kadan sai ga wani dogon farin aljani ya bayyana acikin kogon hannunsa na ruke da sandarsa ta tsafi gashin jikinsa gaba daya fari ne babu ko digon baki ajikinsa Koda gama bayyanar wannan aljani sai ta sunkuya ta zube agaban sa Cikin ladabi kafin ta budi baki tayi magana tuni ya tari numfashinta Take aljanin ya dubeta yace lale marhaban da sarauniya marsufa Hakika ina mai tayaki murnar samun kyakkyawar jaririya taki Wacce zatayi abubuwan al'ajabi a rayuwarta Yake wannan sarauniya inaso ki sani nan gaba da wasu 'yan shekaru wannan jaririya zatayi suhura da kuma jarumtakar dake kanki bakiyi kamarsu ba Zata gwabza da manyan sarakuna da bokayen da suke wannan duniya taku Labarin jarumtakarta da abubuwan al'ajabinta zasu ratsa gaba daya duniya Saidai ki sani wannan kuduri naki bazai taba cika ba dole sai kin hakura da wannan jaririya gaba daya kisa a ranki cewa baki taba haihuwa ba kuma ba zaki kara ba Dajin wannan batu sai hankalin ta ya dugunzuma tace ya Abin dogaro na me kake nufi da wannan zance naka Shin kana so na rabu da itane ko kuwa in hallaka ta ? Idan kuwa har kashe ta kake so nayi tayaya zata tashi ta zama Abinda kake fada? Kodajin wannan batu sai aljanin ya bushe da dariya daga baya kuma ya turbune fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa Daga bisani kuma yaci gaba da cewa ba ina nufin ki kashe ta bane Sai dai zan dauke ta ne gaba daya daga hannunki na wuce da ita duniyar tsafi domin a raineta acan Ba zata dawo hannunki ba sai ta zama cikakkiyar budurwa kuma ta mallaki sirrikan tsafi masu karfi Sannan ta karbi gagarumin horon yakin da zata iya ceton rayuwarta a duk irin mugun yanayin da zata fada a rayuwa Ta haka ne kadai bayyanarta zai rikita duniya kuma ta zama bayyananniya agurin manyan sarakuna Kodajin wannan bayani sai jikin sarauniya marsufa yayi sanyi ta rumgume jaririyarta akirjinta na tsawon lokaci mai tsawo tana kukan rabuwa da ita Daga bisani ta mikawa wannan aljanin ba tareda bata lokaci ba ya karbi gimbiya bhajaht Sannan wata guguwa mai karfi ta shuresu gaba daya suka bace daga wannan daki Tun daga wannan rana aka soma tsuma gimbiya bahjhat acikin na'uikan tsafi masu karfi Har ta fara girma ta cika shekaru da daya a sannan ne siffofin jarumtaka suka fara bayyana agareta Tareda abubuwan al'ajabi wadanda suka shafe tunani Kai sai da kai cewa acikin jinsin aljanun da take rayuwa babu jarumin da ake tsoro kamarta Duk da cewa siffarta ta bil'adama ce amma ta kasance gagarumar basadaukiya Mai matukar karfin damtse juriya da bajinta gami da sa'a a dukkan abubuwan data saka a gaban ta Kai sai da takai ga cewa ko yaki za'a fita a tsakanin kabilar aljanun data taso acikinsu da wata kabilar itace take jagorantarsa Ita kadai take tarwatsa su kuma ta sami nasara Wannan daliline yasa labarin jarumtakarta ya karade duniyar aljanu A wannan lokaci ne ta sami labarin karagar ajali abokin aljani shubbas wanda shine ke rike da ita Tun daga wannan ranar data Sami labarin wannan karaga ta nutsa acikin binciken tsafin ta sai data samo dalasiman tsafin karbar wannan horon na sadauki farhan Don haka daga wannan rana ta fara karbar nata horon Kamar yadda su rukyan sukayi Wannan shine dalilin dayasa agaba daya rayuwar su sarki gulbas basu taba sanin labarin ta sai a wannan lokaci da tayi musu bayyanar ba zato ta sace wannan sarkar tsafi Koda sarki gulbas ya karaci duban jaruma bhajaht yaga baiganta ba Sai ya gyada kai cikin takaici ya dubi gimbiya suhaila yace lallai nayi sakaci a rayuwata dana bari har abokan gaba suka shigo har cikin gida suka cini da yaki Amma ba zan karayin irin wannan sakacin ba a gaba don haka dolene Yanzu mu tafi duniyar hallaka Kafin su rigamu isa can Yanzu haka nasan Boka surkais ya nemar wa kansa hanya mafi sauki da zai isa duniyar hallaka akan lokaci A halin yanzu Wannan bakuwar jaruma zamu kurewa gudu Kafin ta isa karshen kurkukun karkashin kasa har ta kwanto aljani fauzan daga cikinsa Yana gama fadin haka sai ya ruga da gudu zuwa Hanyar da zata sadashi da turakar gimbiya suhaila ita kuwa tana biye dashi abaya Suna isa Cikin turakar sai suhaila ta cika da mamaki sakamakon ganin yadda gaba daya kasan turakar ta bude kanta kai kace wani babban littafin aka bude wata 'yar karamar kofa ta bayyana acikinsa Ba tareda bata lokaciba duk su biyun suka kutsa kansu Cikin wannan kofa Suna shiga cikin kofar sai suka tsinci kansu acikin wata sabuwar duniyar kai kace ba acikin karkashin kasa suke ba Al'amarin daya matukar basu mamaki kenan musamman ma ita suhaila Wacce a wannan karon ne ta san da wannan guri Haka dai suka ci gaba da tafiya acikin karkashin kasa suna kara tafiya Cikin a zababben gudu domin riskar jaruma bhajaht Kafin Saidai kash!!!! Duk irin wannan sauri da sukeyi sai koda ya rage baifi saura dakiku kadan su isa karshen kogon ba Kwatsam sai suka jiyo wani sauti mai karfi Tareda girgizar kogon gaba daya Duwarwatsu suka dinga zubowa kasa nanfa kogon ya fara girgiza yana zubowa kasa Koda ganin wannan al'amari take jikin sarki gulbas yayi sanyi a karon farko kamar kwalla xata zubo daga idanunsa Yace karon farko kenan a rayuwata da aka shigo har cikin gidana aka cini da yaki Ya zama dole mu fita daga wannan kurkukun Kafin ya gama rushewa muna cikinsa Domin a halin yanzu Wannan bakuwar jaruma ta riga ta kwance aljani fauzan Yana gama fadin haka take duk su biyun suka turnuke suka zama hayaki shima hayakin sai ya ratsa ta saman kurkukun ya fice alokacin ne gaba daya kurkukun tq gama rushewa Ita kuwa turakar gimbiya suhaila sai ta koma ta hade gaba daya kamar Wani Abu bai taba faruwa acikinta ba Nantake sarki gulbas ya kwarara uban ihu saboda tsananin bakin ciki daga bisani wata kwallar takaici ta zubo daga cikin idanunsa Koda ganin irin halinda ya shiga sai suhaila tayi sauri ta goge kwallar da take fuskarsa tace Haba ya abba na Irin wannan kwallar bata dace da namijin duniya, kuma jan gwarzo sha gwagwarmaya kamarka ba , kada ka manta da irin gwagwarmayar da kasha. Abaya da Manyan mazaje kuma ka kaisu kasa, a yanzu fa kaine sarkin da duk duniya ake shakkar tunkararsa Idan har zaka bari kwalla ta dinga zuba daga idanunka Kamar ka karya alkadarinka ne da hannunka Dajin wannan batu sai gulbas ya dubeta cikin wani yanayi Mai nuna tsantsar damuwa daga bisani kuma yace Yake 'yata ki sani bawai karayar zuciya ko kuma tsorone suka sakani wannan kwallaba Face tunawa cewa tun farkon kafa Wannan birni tun zamanin iyaye da kakanni ba'a taba samun mahalukin daya taba shigowa cikin wannan birnin ya fita a raye ba Amma a wannan karon gashi har mutum biyu sun shigo cikin masarautata sun cini da yaki ba tare dana iya kama ko daya daga cikinsu ba Ki sani da wannan abu ya faru dani gwanda na gwammacewa mutuwa ta atsakiyar abokan gaba suna yankan nama na danye suna ci yafi min dadi da wannan abu daya faru a yau, Abu daya ne zai rage min zugin Wannan bakinciki a halin yanzu Dolene na riski wannan bakuwar jaruma Kafin ta isa duniyar hallaka nayi mata kisan wulakanci na nuna mata banbancin karfin damtse gami dana sihirin dake tsakanin mu Yana gama fadin haka saiya tuntsure da mahaukaciyar doriya kamar babu abindaya taba bata masa rai Daga bisani sai ya cire wani zube daga dan yatsansa na hagu ya ajiye shi kasa Tareda karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa akansa Faruwar hakan keda wuya nan take saiga wata shirgegiyar halitta mai matukar girma ta ratso ta cikin karkashin kasa Wacce tunda gimbiya suhaila take bata taba ganin halitta mai girmanta ba Itadai wannan halittar ta kasance mai matukar girma sannan tana da Manyan fuka fukai gura goma masu kama dana jemage a kowannen bangare na jikinta, hakama fuskarta Irin ta jemage ce, sai dai Ita akwai wani dogon kaho a tsakiyar kanta mai kama dana mugun dawa sannan tana da hannaye guda biyu ajikinta Sannan tana da kafafu Irin na mikiya Koda bayyanar wannan halitta saita rissina agaban sarki gulbas Cikin girmamawa tace na amsa kira ya shugabana me kake bukata? Ba tareda tsayawa bashi amsa ba sarki gulbas da gimbiya suhaila suka daka tsalle suka haye bayansa Sannan ya shafi madubin tsafinta mantake hoton jaruma bahjhat ya bayyana ajikinsa ya nunawa halittar sannan yace Inaso Yanzu ka daukemu gaba daya Ka kurewa Wannan jarumar gudu ka sadani da ita Kafin ta isa duniyar hallaka Sannan ka shigar damu cikin wannan duniyar domin dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAM…… Kafin sarki gulbas ya gama rufe bakinsa tuni halittar ta bude Manyan fuka fukanta ta luluka Cikin gajimare Nan Take kura ta tashi sakamakon kadawar fuka fukansa Sai gashi yana tsala azababben gudu asararin samaniya Cikin jin karfi kai kace zai bar duniyar gaba daya Nanfa ya dinga shafe doguwar tafiya acikin Lokaci kankani haka shima sarki gulbas ya dinga amfani da karfin sihirinsa Domin kara masa karfin gudu da rage musu nisan tafiya Kai sabo da tsabar kaguwar da yayi sai ya dinga Gani kamar a guri daya suke tafiya Har sai daya dakawa halittar tsawa tare da umartarsa daya kara Karfin gudunsa Cikin girmamawa tsuntsun tsafin yace ya shugabana Wannan shine iyakar Karfin gudu na Ba zan iya yin wanda yafi wannan ba Dajin wannan furuci sai sarki gulbas yayi shiru cike da takaici ba tareda ya kara magana ba, haka dai suka dinga tsala azababben gudu a sararin samaniya ba tareda sun hadu da wani abin cutarwar ba Saidai kash ! Duk wannan saurin da yakeyi baisan cewa yana nisanta kansa ne da karagar ajali ba Domin indai yana bukatar isa duniyar hallaka akan Lokaci dolene ya hakura da riskar jaruma bhajaht Badon komai ba sai domin Koda ace ya riske ta bai isa ya iya shiga duniyar hallaka ta cikin kofar data shiga ba Saboda kamar yadda Kowa ya karbi horon sa daban to haka Itama duniyar hallaka Tana da kofofi fiye da dubu Kowa kofar da zai shigeta daban Kuma Abinda Wannan ya hadu dashi bai zama lallai wani ya hadu dashi ba acikin wannan duniyar ita kuwa gimbiya suhaila sai tayi shiru Tana tunani da nazari a zuciyarta Daga bisani kuma tace ya abbana shin ka manta cewa dakai da abokan gabar ka Ba guri daya kuka karbi horon yaki ba? Dajin wannan tambaya saiya dubeta cikin alamun tambaya yace kwarai kuwa me kike zato Kodajin haka sai tayi gwauron numfashi tace indai kuwa haka ne to. Mun tabka babban kuskure domin kuwa ina tabbatar maka cewa Yanzu a kokarin riskar Wannan bakuwar jaruma baya muka mayar da kan mu Ina mai tabbatar maka cewa kamar yadda baku karbi horon yaki guri daya ba To ba zamu taba shiga cikin duniyar hallaka ta kofa guda daya ba Da jin wannan bayani sai jikin sarki gulbas yayi sanyi Ya fada dogon tunani domin ya san Tabbas maganarta gaskiyace Ba tareda bata lokaciba ya fara bincike acikin madubin tsafin sa Bisa mamaki sai madubin tsafin nasa yaki yayi aiki mai makon hoton wani abu ya bayyyana sai madubin yayi duhu sosai don dole ya mayar da madubin Cikin aljihunsa Bayan wasu 'Yan dakiku kuma sai yaji kirjinsa ya dau zafi da radadi Nanfa wani gumi ya fara tsatsatsafowa daga kirjinsa Idanunsa suka kada sukayi jawur Bai san sanda ya sunkuyar da kansa kasa ba yana ta faman shure shure Tareda gurnani A hankali kuma sai komai ya dauke ya daina jin zugi da radadin da yake ji Daga bisani kuma yace da gimbiya suhaila kinyi Gaskiya Yake 'yata Hakika kina da kaifin tunani Tabbas ba Wannan ce Hanyar daya kamata mubi ba domin shiga duniyar hallaka Yana gama fadin haka sai yiwa tsuntsun tsafinsa umarni daya canja hanya tareda yi. Masa nuni da Wata hanyar ta daban Ai kuwa ba tareda bata lokaciba Wannan tsuntsun ya canja akalar tafiyarsa Suna cikin tafiyar ne ya sake Shafar madubin tsafinsa nantake sai ga hoton Boka surkais ya bayyana ajikinsa shima ya fito cikin shigar yaki akan hanyarsa ta tafiya duniyar hallaka Zaune akan wani bakin aljani sai tsala azababben gudu suke kamar sa tashi sama Saboda karfin gudun aljanin saida sarki gulbas ya raina Karfin gudun tsuntsun da yake kai Har mamaki ya kamashi yace acikin zuciyarsa Dama boka surkais yana da wannan shu'umin aljanin amma yazo har gidana domin Neman aljani hursad ibn zafran? Bazai taba yiwuwa ace aljani hursad bin zafran yazo nema ba Dole Akwai abindaya kawo shi na daban kuma ya zama wajibi na gano abindaya kawoshi kasa ta WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN SARKI GULBAS BAYAN YA FITO DA NIYYAR RISKAR JARUMA BHAJAHT ++++ ++++++ ++++++ Al'amarin jaruma bhajaht kuwa bayan ta shammaci su Sarki gulbas ta sace aljani farsad bin zafran daga wannan kurkuku Sai sukayi ta tsala gudu a sararin samaniya, bayan sunyi nisa da barin yankin birnin ikarul izbar sai ta tuna yadda su sarki gulbas keta faman yaki da junansu wanda ya janyo har sukayi sakaci ta shammacesu ta fizge wannan sarka daga wuyan suhaila Saita kyalkyale da dariyar farinciki kamar ba zata daina ba daga bisani kuma sai jikinta yayi sanyi kamar mara lafiya Badon komai ba sai don tunawa da tayi da wata magana da aljani malsara ya fada mata Kafin su rabu dashi Mutum daya ne kacal zai mallaki karagar ajali acikinsu sannan mutum biyu wadanda zasu iya tsira da rayuwarsu, ragowar kuwa duk mutuwa zasuyi acikin duniyar hallaka, Babu yadda batayi ba akan ya fada mata wadanda zasu tsira da rayuwarsu amma sai yaki Daga bisani ya shaida mata cewa yake bhajaht shawara daya zan baki kawai ki zage damtsenki Wajen Ganin ko ta wanne hali kiga kin tsira da rayuwarki akan wannan tafarki Domin ina mai tabbatar miki cewa su kansu jarumi rukyan da sarki gulbas da zasu fita su. Bibbiyu akwai lokacin da zaizo su tarwatse kowa tasa ta fishshe shi Saboda haka babu wanda yake da tabbacin zai dawo a raye ko kuma ya mallaki KARAGAR AJALI Haka dai tayi ta sake sake acikin zuciyarta tafiyar sa'o'i biyu kachal sukayi Sannan suka iso wani katon daji Mai matukar girma da kwarjini gami da tarin manyan bishiyoyi Suna isowa wannan daji take jaruma bhajaht ta fara duba tasiwirar dajin A sannan ne aljani farsad ya fara sakin fuka fukansa domin sauka akan turba Ba zato ba tsammani take suka ga sararin samaniya ta tsage wata tangamemiyar kofa ta bayyana a jikinta tareda iska mai karfi Kafin suyi wani yunkuri tuni iskar ta damkesu da karfin tsiya ta zukesu cikinta Sannan kofar ta maida kanta ta rufe Nantake suka tsinci kansu a cikin wata sabuwar duniyar wacce akewa lakabi da duniyar hallaka Saidai komai na wannan duniyar ya fita daban dana duniyar da muke ciki Kuma sun kasance na musamman da kuma daukar hankali, ba don komai ba sai don ganin yadda abubuwa marasa yiwuwa da suke faruwa a zahiri acikinta Misali kamar duwatsu wadanda zakaga suna yawo a saman iska kamar Tsuntsaye Wasu kuwa zaka gansu jikinsu gaba daya na haskene ta yadda kana iya ganin komai na cikinsu Bishiyoyi kuwa har magana sukeyi da junansu Cikin wani yare na daban wanda su kadaine ke fahimtar yaren nasu, bayan haka har tafiya sukeyi daga guri zuwa guri Dabbobin gurin kuwa gasu nan manya da kanana suna rayuwarsu Ba tareda wani yana cutar da daya ba Wani gurin kuwa sai kaga dutsen wuta yana ta zabalbala a tsakiyar kankara ba Tareda kankarar ta narke ba A takaice dai komai na wannan duniyar yana zaman lafiya ne da dan uwansa Koda wadannan halittu suka kyallara idanunsu sukayi arba dasu jaruma bhajaht da aljani farsad bin zafran Suka tsaya na dan tsawon lokaci suna kallonsu kamar mutuwa ta gifta , daga bisani kuma suka kau da kansu sukayi kamar basu gansu ba Suka ci gaba da harkokinsu abin su, Wannan al'amari ba karamin daurewa aljani farsad bin zafran mamaki yayi ba Har ya kasa yin shiru da bakinsa ya dubi jaruma bhajaht yace Yake tunda nake a tarihin rayuwata ban taba ganin guri mai abin al'ajabi da kuma zaman lafiya ba kamar wannan daji da muke ciki a yanzu Ki duba fa kiga yadda komai Yake zaman lafiya da dan uwansa har ta kai ga zaki ma Yana iya zama guri daya da barewa Dajin wannan batu kawai sai tayi guntun murmushi tace Haba farsad me kake ci na baka na zuba? Na fuskanci iya tsawon rayuwarka Labarin dadin karagar ajali kakeji Amma baka san wahalar dake cikin yunkurin mallakar ta ba To ka sani komai ka gani a wannan tuniyar to kayi taka tsan tsan dashi Kada Ganin kawaici na halittun Wannan duniyar ya rude ka domin ina tabbatar maka cewa ruwa baya tsami banza Akwai wani mugun nufi a tare dasu Hatsarin dake Cikin wannan duniyar ya ninka wanda ke duniyar mu fiye da sau dari Don haka daga yanzu sai ka kasance Cikin shiri da kuma taka tsantsan Domin a kowanne Lokaci komai zai iya faruwa, Daga wannan furuci bata kara cewa uffan ba suka ci gaba da tafiya abinsu sai da suka shafe sa'o'i suna tafiya ba tareda sun hadu da wani abin cutarwar ba har sun fara sakin jikinsu Kwatsam sai yanayin dajin ya fara sauyawa a Lokaci guda yayi duhu kai kace tsakar daren farkon Wata ne Lokaci guda kuma kasa ta dare biyu sai ga wata shirgegiyar halitta mai matukar girma da kwarjini ta fito daga cikinta Girman wannan halittar kadai ya isa ya razana mai kallo Tana da wasu dogayen hannaye masu matukar karfi wadanda akoda yaushe karawa kansu tsawo suke yi Idan kuwa tana tafiya akan kasa gani zakayi kasar tana girgiza tamkar zata rufta ciki Koda bayyanar wannan halittar take ta daga hannunta sama. Ta kamo fuka fukan aljani farsad da karfin tsiya yana ji yana gani dokasu da kasa SHIN SU JARUMA BHAJAHT NA KUBUTA DAGA HANNUN WANNAN MUGUWAR HALITTAR? YA LABARIN BOKA SURKAIS WANENE MAI MATUKAR SA'AR DA ZAI MALLAKI KARAGAR AJALI? SANNAN SU WAYE ZASU RASA RAMSU A WANNAN TAFARKI? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DOMIN JIN CIGABAN WANNAN LABARI NAKU HABIBULLAH KBRKARAGAR AJALI ++++++++++7 PART

Chapter 16 of 21