Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya tashi ta fara tunanin inane ya shiga ya barta a wannan guri Daga karshe taga ya kamata ta tashi ta shiga cikin gari dubashi. Wata kila ya tafi nemo musu abinci ne kamar yadda ya saba Ba tareda bata lokaci ba ta tashi ta nufi cikin kasuwa domin neman mahaifinta duk da cewa bata san hakikar gurin da yake zaune ba Haka dai ta dinga tafiya akan kafafunta tana duba duk guraren da taga tarin almajirai da kuma gurin sadaka ko zataga Ruzyal Amma abu ya gagara kamar wasa har rana ta take gumi ya soma tsatstsafo mata saboda matukar zafin rana Tana tafiyane ta zo giftawa ta gaban sarkin yaki uhaisu sai ta hango yara guda biyu a tare dashi wadanda shekarunsu da nata zasu iya zuwa daya Daure cikin sarka a hannun daya daga cikin dakarunsa take tausayinsu ya kamata Bata san sanda ta dinga tafiya tana waigen wadannan yara ba har tayi nisa tana cikin wannan waiwayene bata sani ba kwatsam sai tayi tuntube da wani katon dutse dake gabanta Nantake ta fadi kasa kasa kanta ya gwaru da wannan dutsen jini yayi tsartuwa Faruwar hakan keda take sararin samaniya ta hautsine wani bakin hadari ya mamaye gaba daya duniya ta yadda koda dan yatsa mutum ba zai iya gani ba Wata irin tsawa mai karfi gami da walkiya suka dinga tashi sama yawo a sararin samani kai kace Zata kece garwashin wuta ya zubo daga cikinta Wanda tsawarce ta dinga tarwatsa manyan duwarwatsu da tsaunika suka dinga gangarowa suna turmushe mutane tareda aman ruwan wuta acikin dajijjika wanda ya dinga kone su tare da birane Tsibirurrukan dake cikin tekuna kuwa suma suka dinga tarwatsewa wanda hakan ya igiyoyin tekuna suka dinga tsinkewa Ruwa ya dinga ambaliya yana malalowa cikin garuruwa tareda shafe su Sannan wata irin iska mai karfi itama ta dinga kadawa tana jijjige manyan gine gine da bishiyu daga doron kasa tana bazar dasu akan Nanfa gabaki daya duk wata halitta mai numfashi hankalinta ya tashi suka fara guje guje da iface iface domin ceton rayukansu Amma babu dama saboda a garin wannan gudun da sukeyi ne suka dinga fadawa cikin tarkunan da suka zamo ajalinsu Haka kasa itama ta fara girgiza tana neman dulmiyewa Kafin adauki lokaci mai tsawo dubunnan daruruwan rayuka suka alwanta Sai da aka dauki lokaci mai tsawo ana cikin wannan mawuyacin hali a gaba daya duniya ya zamana babu abinda kake ji face sautin ihun neman taimako alokacin da kowa ke kokarin ceton ransa Sannan a hankali kuma komai ya tsaya cak kamar yadda yake a baya Duwarwatsu suka daina fashewa , suma tekuna suka daina ambaliya haka kasa itama ta daina girgizar da takeyi hasken rana ya mamaye duniya Adaidai wannan lokacine hijabin sihirin dake jikin lasmira gaba daya ya lalace Har a wannan lokaci suna kokarin ceton rayukansu idan ka kalli kasa kuwa a sannan babu abinda zaka gani face gawarwakin mutanen da gine gine suka turmushe Amma koda suka daga kai sukayi arba da lasmira take suka tsaya tamkar wadanda aka zarewa lakar jikinsu Hakika allah ya azurta lasmira da matukar kyawu wanda tsayawa kwatanta siffofin kamanninta ma bata lokaci ne da kauyanci Nanfa mutane suka manta da tashin hankalin da suke ciki wasu ma akwai manyan raunika ajikinsu Suka fara dafifin zuwa ganin lasmira a wannan lokaci ita kuwa ji take wani jiri yana dibarta tareda matsanancin ciwon kai a karon farko a rayuwarta Shi kuwa Sarkin yaki uhaisu kodaya daga kai yayi arba da lasmira take ya daka tsalle daga inda yake tsaye da karfin tsiya ya nufi inda lasmira take domin cika umarnin uban gidansa Saidai kafin hannunsa ya karasa jikinta tuni yarinyar fursunan daya kamo wato Hilaliya ta rikide ta koma siffar Sadauki safran Namijin kuwa wato Nargis sai ya rikide ya koma Siffar Sarauniya Nauwaratul hasnal Cikin zafin nama nauwaratul hasnal ta nuna Uhaisu da tafin hannunta Tuni wata iska mai karfi ta fito daga jikin hannun nata ta shureshi tayi sama dashi tana wujijjigashi akan iska Shikuwa safran take ya zaro adda daga jikin kugunsa ya da gudun gaske ya daka tsalle sai gashi ya tashi sama kamar wanda aka harba daga cikin baka ya tari uhaisu nantake ya sassara shi asaman gangar jikinsa ta zubo kasa Adaidai wannan lokacine Gimbiya husnaila ta iso wannan guri sai. Kuma sadauki mufran Dukkaninsu cikin wani azababben gudu mai kama dana harbin kibiya Suka nufo inda lasmira take kamar zasu dasa mata wawa Abangaren Sarauniya nauwaratul hasnal kuwa take itama dakarun kariyarta suka bayyana abayanta Take duk. Su biyar din suka afkawa lasmira Ba zato ba tsammani saiga wata katuwar mikiya ta bayyana cikin azababben gudu wanda ya haura nasu ta shiga tsakiyarsu ta shuri lasmira tayi sama da ita koda mikiyar ta tashi sama take ta rikide zuwa siffar boka Hulbaz yana mai kyalkyala dariyar farinciki SHIN LASMIRA TANA KUBUTA DAGA HANNUN BOKA HULBAZ MENENE ALAKAR SARAUNIYA NAUWARATUL HASNAL DA SADAUKI SAFRAN?KUMA MENE YA HADASU A GURI DAYA? INA LABARIN SADAUKI FARHAN? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYIN SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 21 of 21