biyu
Mummy tayi murmushi tace ai gwamma da aka maka kafar taje can nima na huta da zaman kishi da ita
Daddy yace kai mummyn Hakeem badai kishiba
To nikuma ba inda za aje min da mata inasonta
Meenat dai yau duk surutunta bakin ya mutu
Hakeem yace amina Dan Allah karkisake biye ma su laila kizo kibamu kunya
Kinga dai gidan mutunci ne ko
Meenat tadaga kai sama tace to daddy
Hakeem yawa mummy da daddy saidafe yawuce part dinshi
Daddy da mummy suka cigaba dawa meenat nasiha harshima daddyn yaje byakwanta
Hakeem nashiga part dinsu yaga husnah kwance tayi bacci cikin wasu fitunannun sleeping dress
Ya karasa kusa da ita yakwantar da kashi a kirjinta husnah dai bacci yayi nisa
Yaga dai bazata tashiba Dan tunda tasamu cikin intafara bacci kaman ta mutu
Yashiga yayi wanka kafin yafito yayi shirin kwanciyar sa
Ya kwanta tare da manno husnah ajikinshi Dan harsunsaba baya iya bacci saiyajita jikinshi haka itama idan tabude ido taga yana kusada ita tofa tana jikinshi
Yana nashafa mata kanta yaso yatasheta sai kuma yafasa
Dan yaga taji dadin baccin ta
******
anty kubra zaune itada umma suna lissafin kudin dazai kawo na sayayyar kayan lefe itafa anty kubra komai takeyi daurewa kawai saboda kwata kwata bata jin dadi sosai
Taki nunawa ne saboda karaga kaman saboda maganar auren yasata damuwa
Suna gama wa ta tashi tadauki hijabinta tace umma barin shiga nan makwafta yarinyar salma ba lafiya manal
Umma tace ayya koshiyasa bana ganinta kwana biyu anty kubra tace wallahi
Umma tace kigaishemin Da ita
Anty kubra tana fita gidan doctor salma tashiga taci sa akuwa tana gida
Doctor salma tace kai yau kubra kece komafarki nakeyi anty kubra tayi murmushi tace nice wallahi doctor
Tace mushiga daga falo
Nan suka shiga bayan sungaisa
Takewa doctor salma bayanin yadda takeji kusan sati uku da suka wuce
Doctor salma tayi mata tambayoyi ta amsa
Tace kitashi kishiga kiyi fitsari zanmiki P T test
Anty kubra batayi musuba
Tayi doctor tayi gwaje gwajensu
taga yasa mata positive aikuwa da murna tasanar da anty kubra
anty kubra tsaban farin ciki saiga hawaye sharshar yana bin kuma tunta
Doctor salma tace haba kubra ai murna yalamata kiyi ba kukaba
Kubra tace hakane Allah nagode maka
amma Dan Allah karkifa dawa megidanki Kinsan idan megidanki yasani zaifadawa shamsu kuma banason mijina yasan da wannan cikin
Doctor salma ta gwalo ido tace kekuwa kubra meyayi zafi haka abinda kukadade kuna nema Allah yabaki kice kar a fadawa mijinki
Kubra tace ina da dalili mai karfi ne yasa nafadi haka kuma zanfada miki yanzu
Nan anty kubra tabata labarin komai
Tace kinga idan wallahi nasan zaice yafasa auran
Kuma idan yafasa auran bazan yafewa kaina ba zanga kaman nice sila
Kuma gashi gidan mutunci zai yi auran idan yace yafasa ai zasu daukeshi karamin mutum
Doctor salma baki tasake kawai tana sauraron karfin hali irin na kubra
Gaskiya ko ita kubra ta matukar burgeta
Tana hali mai kyau Wanda kowani miji zaiyi alfahari da ita
Murmushi salma tayi tareda jinjina mata tace Allah dai yabiyaki kubra wannan jahadi da kikeda niyyar yi
Kuma insha Allah keda kanki zakifadawa mijinki alokacin daya dace
Nan sukayi sallama kubra ta koma gida
*******
Biki ya rage saura sati kowani bangare sunata shiri kamar masu aurar da budurwa ko saurayi komai da ake bukata ya shamsu kubra yakeba itakuma tazage tsakaninta da Allah tanayin komai
Ba Wanda ya lura da cewan tana da shigan ciki ajikinta saboda komai da jikinta takeyi abunta
Kayan lefe kuwa masu kyau da tsada guda dozin wato shabiyu itama kubra yasake mata komai kuma yabata makudan kudi taki karba yanuna rashin jindadinshi
Saita karba tamishi godiya
Kamar kullum sunzo kwanciya tace honey yanzu Dan Allah abinda kakeyi ka kyauta
Ya shamsu dake aiki a lap top dinshi yajuyo yace meya faru honey
Anty kubra ta ce yau kusan saura sati fa auranka amma Baku taba magana ba aizaka sa iyayenta suji badadi suzargi basonta kakeba kaman dole akama
Ya shamsu ai basonta nakeba kubra inada mace kamanke mezan nema agun wata mace
Kubra ta taso ta ringumeshi tabaya tace nasani mijina amma inason kaduba iyayenta Dan Allah
Ya shamsu yasaukar da ajiyar zuciya yace yanzu yakikeson ayi
Kubra tace gobe kaje Kaduna kufahimci juna Dan Allah kabata abinda take bukata na hidimar biki
Ya shamsu yace naji Allah yakaimu shikenan hankalinki ya kwanta
Kubra tadaga kai tace yauwa honey
Yanzu kabar wannan aikin Dan Allah kazo mukwanta bacci nakeji gashi gobe zakayi tafiya ta kashe computer taja hanunta mijinta zuwa kadu gado
******
Washagari kubra takira Husnah tasanar da ita zuwan ya shamsu
Tace tasanar da meenat
Husnah tace toshike nan kifada mishi yataho minda furar umman nan Dan Allah
anty kubra tace to mama food
Husnah tace anty hardake ko kinacemin mama food ko
Anty kubra tayi murmushi tace aidole wannan babyn dai yasaki ci wallahi
Suna gama waya husnah ta kalli meenat tace yaufa mijinki yanahanya saiki tashi kifara shiri
Meenat tace banason wasafa niwacece da zakice zaizo domina tadafa kirji
Husnah ta ce ke amatarshi mana
Meenat tayi murmushi tace hmm ninasan fa bawani sona ya shansu yakeba
amma zanmishi biyayya insha Allah zaiyi alfahari dani
Yauwa antyna meya yashamsu yafi so acikin abinci amma fa saikin tayani kisan har yanzu hanun baifada ba
Tayi murmushi
Husnah dai tausayin meenat yakamata ashema itama tasan ya shamsu bayasonta
Tare sukaje kitchen sukayi aikin abinci
Large shabiyu da rabi sukagama
Kowacce tashiga wanka
Meenat tasha gayu sosai da taimakon husnah
Yashamsu karfe daya darabi
Next page
Your comment is needed fans
Ina alfahari da Ku over wallahi
ππππππππππππππ
[06/05, 11:22 AM] UMMU AFAN πΉ: ππππππππ
πππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
STORY & WRITTEN
BY
THE SPECIAL AUTHOR /WRITER
UMMU AFAN πππππππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉF.C.T.W.A.πΉ
πΉHOME OF QUALITY AND TRUSTED WRITERS OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU SISTER BALARABA
Ina alfahari da comment dinki over kina kokari sosai wajen suburbudo comment Allah yabar zumunciππΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
πAKWAI LOKACI π
π PAGE 158 to 150π
Afalon su mummy aka sauki ya shamsu shi sosai suka gaisa da
Da mummy Husnah dake da mummy tace yaya ina furana
Ya shamsu yayi murmushi yace mummy kina fama da shawagwabar husnah umma dai huta sai mummy kuma
Mummy tayi murmushi tace tayi abinta lokacinta ne ai tana debe min kewar yarinya mace
Yashamsu yace aitagirma dayawa mummy tace mummy tace wadin ai husnah yarinya ce idan batayi shagwabar ta yanzu sai yaushe zatayi
Husnah tayi murmushi tace to yaya kaji daiko
Saika bani furana kawai
Ya shamsu yace ai na manta da furar ki
Husnah tayi murmushi tace caf ai kuwa da bazan bari kaga matarka ba nima sai ka koma kakawo min kafin kaganta
Mummy tayi murmushi yanayin shakuwar ya shamsu da husnah yabata sha'awa
Sosai duk da yagirme mata hakan bai hanashi Jan kanwarshi ajikiba
Key din motar yabata yace tadauko a mota
Da murna ta karba tayi hanyar waje
Mummy tace yi a hankali 'yata kefa saikace bame cikiba bakya nauyin cikin ma kai yarinta me dadi
Mummy tace to nibazan Barka kaci abinci
Barin turo ma ita aminar
Ya shamsu wayarsa yadauka yayi Dial number din kubra tana ganin kiranshi tadauka tayi sallama tace honey ka isa lafiya ya kanwata
Ya shamsu yace zakifara ko nifa nakiraki ne naji nice voice dinki
Kubra tayi murmushi tace nagode mijina dafatan kasamesu lafiya yace kowa lafiya
Husnah tashigo falon ganin yana waya yasa ta haura sama gurin mummy can falon daddy
Clashing sukayi da meenat zata sauko husnah tace kai matan yaya kinyi kyau wallahi kar ki safa saikuma tayi shiru tana murmushi meenat tace karnasa me kinganki
Kina nan sai tsokana ko am kinsan meye husnah wallahi kunya nakeji sosai
Husnah tadafa kafadarta tace kisawa kanki kwarin gwiwa kefa mace ce haba yakikeson badani ne kaman ba meenat din Dana sani ba
Kinsan Allah saikinyi da gaske kafin kisamu kan yayana wannan kunyar duk bazai fishshekiba wallahi
Saboda bahaka antyna take mikishiba
Beside ma fa namiji baya son yawan kunya
Saboda kunyar yana cutar dasu dayawa
Meenat tace nagode da shawararki yar uwa kuma small mama na
Zanyi aiki dashi
Ta kalli ledar hanun husnah tace karfa kishanye kekadai please nasan cinki
Nasan wannan furrar tunda kika damu dashi zaiyi dadi over wallahi
Husnah tace jeki fa kinshanya min yaya na a falo
Meenat tayi murmushi ta karasa sauka
Cike da ladabi da kunya ta durkusa kasan carpet tana jiran yagama wayar sa
Shikam ya shamsu soyayya sosai suke zubawa a waya da anty kubra
Yadau kusan minti talatin kafin kubra tace Dan Allah idan kana kusa da kanwata ka kashe wayar nan
Ba dadi wallahi cin fuskane
Ya shamsu ya kalli gefen da meenat take tunda ta ajiye kanta kasa bata dago ba saita bashi tausayi
Yacewa kubra gata nan yamika wa meenat wayar batayi tsamma niba taga wayar dago kai tayi suka hada ido yace karba
Ta karba suka gaisa da anty kubra meenat ta tambayi umma kubra tace umma lafiya qalau
Kafin sukayi sallama kubra ta kashe wayar Dan karma yakarba wayar yasake wata maganar
Meenat ta kalli screen din wayar ya shamsu hoton taga hoton anty kubra dashi sunsa kaya iridaya suna murmushi hoton yamata kyau sosai
Ya shamsu ganin bata mika mishi wayar ba yasa ya kalleta da kyau yaga metake kallo yaga dai tazubawa
Wayar ido
Meenat tamika mika mishi wayar
Tace ya shamsu ina wuni yace lafiya ya mutan gidan
Tace kowa lafiya yace madallah
Daga nan kowa yayi shiru
Tsawon minti goma daga baya yace amina bakya maganane ko kuma nine bakyason ma magana
Meenat tace bahakabane to bakaci komai na gashi ankawo ma komai
Ya shamsu ya kalli kayan gurin yace ai bakiso naciba tunda baki bani komaiba haka ake barin bako
Meenat tagirgiza kai tamatsa kusada abincin ta saving dinshi komai
Tace bissimillah ya shamsu yace to anty meenat
Tayi murmushi batace komaiba kasa yasauka yafara cin abinci
Meenat haka kawai tatsinci kanta da sahanu tadauki wayar ya shamsu
Ya shamsu ganin tadauki phone dinshi murmushi yayi kawai yacigaba da cin abincinsa
Meenat kallon hotuna take sosai daga hotunan shi saina kubra saina husnah da su umma
Ta dauki wayarta tayi connecting ta xender tayi ta tura pic masu kyau na shi Dana anty kubra
Ya shamsu yace mekike turawa tace hotuna
Yace nawa kenan tace na anty kubra
Yace banyarda ba inga wayar idan dagaske kike
Meenat tayi murmushi yabashi wayar duka yaduba yaga abinda ta tura
Yadauki number dinta yabata wayar
Yaciro kudi bai Masan tawansuba ya ajiye yace ga wannan kiyi hidima dasu
Meenat tace wallahi kabarsu niba abinda zanyi
Sai walima kuma mummy ce zatayi komai
Yace yace nariga nayi niyya
Tayi godiya kawai daga nan ya kalli agogo yaga time yace zan wuce kinsan sainabi office din daddynki Dan baimasan na zoba
Meenat dai tana ta wasa da hanunta
Duk wayoyin ya kwashe yazuba a aljihunshi meenat kuma takasa magana
Yace kikara su mummy muyi sallama
Meenat ta wuce yabita da kallo harta sama amma batasan yana kallon ba
Sunyi sallama da mummy tace Dan Allah kagaishemin da umma kace mata munga tsaraba mungode tabashi aika yakaiwa umma
Husnah tace to yaya sai munkawo ma amaryar ka
Yace shikenan yar kanwata kikula da kanki
Tace insha Allah yaya sakon gaisuwa na zuwa ga antyn data fikowacce anty aduniya
Ya shamsu yayi murmushi yace zataji insha Allah meenat tadauki kayan da mummy tabayar akaiwa su umma
Tarakashi hargurin mota tabude tasaka kafin ta jingina da jigin motar tana son tambayar wayarta tana kunya
Ya shamsu kuwa baimasan tanayiba tashiga motar shiyace to amaryar shamsu sakin kinzo ko yana gama fadar haka yaja motarshi yayi gaba
Murmushi meenat tayi tace nasan bakasona ya shamsu amma ina fatan kasoni a ranka koda bazai kai yadda kakeson anty kubra ba daman bankai kaina nanba
Saiga hawaye yana zubo mata
Saiji tayi ana share mata hawayen
Tabude ido taga husnah ce
Meenat bata San lokacin data fada jikin Husnah tana kuka ba
Kukan datarasa namenene shi
Da daddare YOUNG PROF da husnah falonsu Hakeem yace sweet albishirin ki Husnah dake kwance jikinshi tace goro Prince
Yace saikinfada min goron albishir dazaki bani idan nafada miki husnah ta tura baki tace kaifa Prince nasan irin goron ka fa tayi maganar tana shagwaba
Yayi murmushi yace to aike kekadaice me iyabani wannan goron
Husnah tasake kwantar da kanta a shimfudaddan kirjin mijinta tana shakar kamshinsa
Tunda tasamu ciki itakuma takeson kamshin Hakeem sosai kullum suna manne da juna idan yadawo daga office
Tace inajinka yace angama miki gidan marayun nan da asibitin saboda haka bayan biki
Saimuje mukwaso su umma suzo sugani susa albarka aciki
Baiyi aune auene ba yaji hawaye a kirjinshi
Yadago kanta yace lafiya sweet meye kuma na kuka husnah tace bansan mezan maka nabiyaka Prince kamin komai a rayuwata kacika min burina danake dashi tun ina yarinya Allah ya
Kafin takarasa godiyar dai Hakeem ya hade bakinsu guri daya saidaya kusan minti biyar kafin yace karkisake min godiya
Wallahi aini bawan Allah kuma ni bawankine kiyi yadda kikeso dani bayan su mummy banida samada ke
Itama dai husnah ganin bazai barta tamishi asalin godiyaba
Yasa tafara nuna mishi farincikinta tahanyar abinda yafiso
*****
Hajiya rukayya da hajiya Laila suna kasa metsarki tun bayan faruwar alamarin nan suke saudiya
Suna ta ibada da Neman yafiya agurin Allah
Daddyn Hakeem suna waya sosai dasu danshi yake musu komai shida Hakeem
Daddyn Hakeem kuwa shiyake sanar da su zancen auran meenat da wan husnah
Sosai suma sukaji dadi sukasa albarka
To shine yanzu suke shirin dawowa saboda auran meenat
***
Ya shamsu Yakoma gida lafiya anty kubra ta tarbeshi da murnarta takai mishi ruwan wanka
Yayi wanka yaje part din su umma sukaci abinci da shi ya shamsu indai badasu umma yaci abinciba anaci anahira kamar dai yadda suka saba ada
Sunyi shirin kwanciya sai akakira wayar yashamsu
Yace kubra tamiko mishi
Anty kubra tayi murmushi ganin wayoyi biyu a aljihunshi
Takwaso duka tace honey wannan wayarfa batareda yakalleta ba yace nawane
Tace amma dai wayartayi kyau tana danna screen din wayar wani hoton meenat ne ya bayyana ajiki tayi kyau kuwa
Cike da mamaki anty kubra tasake kallon wayar tace lalle ma namiji kaman bashinake ta matsamai yaje gurintaba
Ganin ta tsaya kallon wayar yace kikawo min mana Honey
Kafin kubra tayi magana har ankira wayar ya shamsu akarona biyu
Kubra Tamika mai yaga lovely sister husnah kenan
Bayan tamishi yagajiyar hanya tace yaba anty kubra itama suka gaisa tace abawa kanwarta
Suka gaisa da meenat
Kafin husnah takarba anty kubra taba ya shamsu wayar husnah tace yaya shine baka ba meenat wayarta ba itakuma takasa maka magana ko
aikuwa ya shamsu yatashi daga kwancen dayake yace subhanallah ai nazaci tadauka nema
amma gobe zan bayar akai mata
Husnah tace OK kasan zama bawaya ba dadi
Sukayi sallama Ya shamsu yakai kallonshi kanwayar dake hanun kubra yace wallahi basan nataho mata da wayaba
Honey
Kubra tayi murmushi tace badamuwa ai hakan ma yanuna min kai karbi meenat sosai Allah yabaka ikon aldalci atsakaninmu
Ya shamsu kunyar anty kubra ce ma shitakamashi Dan yasan bashida bakin kare kansa
anty kubra talura da hakan yasa tashiga mantardashi wanann kunyar
****
Rana bata karya yaune daurin auren SHAMSUDDEN DA AMINA
next page π
Your comment is needed fans
Love you all
πππππππππππ
[06/05, 11:24 AM] UMMU AFAN πΉ: ππππππππ
πππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
STORY & WRITTEN
BY
THE SPECIAL AUTHOR /WRITER
UMMU AFAN πππππππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉF.C.T.W.A.πΉ
πΉHOME OF QUALITY AND TRUSTED WRITERS OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU SISTER MAMA AL'AMIN
Ina alfahari da comment dinki over kina kokari sosai wajen suburbudo comment Allah yabar zumunciππΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
πAKWAI LOKACI π
π PAGE 161 to 162π
YONG PROF yayi rawan gani sosai Dan abinda yawa meenat shiyawa anty kubra colour ne kawai ya ban banta su
Anyi biki an watse kowa Yakama gabanshi Husnah tayi tayi Hakeem yabar takai amarya yace Sam baiyadda tabi rubibiba kar ature mishi hancin baby
Sosai taji haushi amma haka ta hakura ba yadda zatayi
Su anty Aisha matar Ahmad da su hajiya rukayya suka kai amarya gidan mijinta dake kano
Tarba sosai aka musu yan kawo amarya sunji dadin tarbar sosai komai cikin girma akayi shi
Yarage saura amarya itakadai adakin ta bakowa
Can anty kubra tashigo tace sannu dazuwa kanwata Dan Allah meenat wannan kunyar kirageta mijinkifa ba maison kunyabane
Kizage kinuna wa mijinki so yadda shima zaisan yes yayi amarya karkiji kunyata munzama daya tunda yanzu mundawo karkashin adalin miji kamar mijinmu Dan haka kirage indan nine wallahi
Dazuciya daya nake tare dake kanwata fatana Allah yahada kanmu muhadu mufaranta ran mijinmu banda jin zugan kawaye da zuciya zasu kaimu subaro mu ne kawai
Kinji ko meenat tadaga kai tace insha Allah anty na
Nagode da kaunarki gereni
Anty kubra tace ba komai yanzu kitashi kikara gyarawa kafin angon naki yashigo
Meenat taki tashi anty kubra data lura bazata tashi ba
Tayi murmushi ta tashi tamata sallama tafita
Kubra nakomawa dakinta tafashe da wani kuka mai ciwo yauce rana tafarko dazata kwanta batareda mijinta basa raba shinfida saidai idan tafiya yayi
Yau gashi zama sufara raba kwnane dawata
Tace ya Allah kasan niyyata na alkairi Allah kabamu zaman lafiya da mijinmu kasa yazama shine mujinmu a aljanna
Ta kashe wutar dakinta ta kwanta
Ya shamsu yana shigowa direct bedroom din kubra ya wuce yanshiga yasameta tana bacci Wanda azahirin gaskiya ba bacci takeba batason ganinsane kawai
Ya shamsu zama yayi dai dai kanta yana shafa gashinta
Yace Allah yamiki albarka matata
Allah yasa kece uwargidata nagidan aljanna
Kinsadaukar da komai saboda ni
Nima ba abinda bazan iya yiba saboda ke
Allah yabarmu tare mutukaraba
Ya manna mata kiss agoshi
Yafita zuwa bedroom dinshi yayi wanka yasa kayan bacci aiko yanagama shirin kwanciya ya kwanta abinshi tare da kara karfin AC din abinshi sai muce yashamsu asuba tagari ango
Meenat dama tasan ba lalle yazoba Dan talura saitayi da gaske kafin tadan samu hankalinsa
Ta tashi itama tayi shirin bacci takwanta
Umma kuwa suna hira dawata aminyarta
Maisuna hajiya zulai
Hajiya zulai tace nikuwa hajiya anya kinlura da yarinyar nan kuwa khadijah dakyau kuwa
Umma tace a a lafiya kikace haka
Hajiya zulai tace ai daga yarinyar nan tana da juna biyu
Bakiga yadda ta dashe tayi kyau ba cikin idonta zaki duba dakyau zakiga zahiri
Umma tace nikaina naso nazargi haka
Saikuma nace yaran yanzu da suke Neman cikin ido a rufe
Da cikin ne zadasu sanar dani
Hajiya zulai tayi murmushi tace aiko dai daga shamsu har khadijar bazasu iya ba yarane masu kunya
Umma tayi murmushi tace allah nagode maka daka nufemu daganin wannan Abu Allah ka tabbatar da zarginmu akan kubra
Hajiya zulai tace saikiyi kuma wani zargi aiko kaffara bazanyiba yarinyar nan cikine da ita Allah dai yaraba lafiya
Nan sukayi ta tattaunawa tasakaninsu
****
Washagari da asuba meenat tashi tashiga kitchen tafara aiki anty kubra kuwa tanayin sallah gajiyar biki yasa bacci yakwasheta a sallayar
Meenat tagama komai tashirya a dining din falon su umma nan taga anacin abinci
Kafin tawuce zuwa dakinta donyin wanka
Anty kubra kuwa farkawata tayi dasauri ta kalli agogo taga taga takwas saura salati tayi
Cikin sauri tafita zuwa kitchen ko hijabin ma bata tsaya cirewa ba
Tana zuwa falo taga kan dining anjera komai takarasa da mamakinta ta bubbude
Tace tomehakan yake nufi kenan
Duk yadda akayi honey ba adaki sa takwana ba
Ta wuce bedroom din ya shamsu tana shiga taga yana kwance abinshi
Jinbudewar kofar yasa ya shamsu ya farka sukayi ido hudu da juna ya ware hanunshi wai ta taho
Kubra ta nuke kafada ya shamsu tashi yayi dasauri yace wayatama min baby na
Kubra tace yanzu kayi adalici kenan kabar yarinya ta kwana itakadai tana Bakuwa
Ya shamsu yayi murmushi yace hoo kubra rigima
Yatashi yazo yakamota yace kinsan namanta ma sai yanzu da kika tuna min
Kubra ta kalleshi da mamaki tace yanzu akawo maka amaryar kace wai kama man daita
Sakeni Dan Allah honey gaskiya baka kyauta ba su haka sukewa husnah ba duba wannan hallaci nasu karikemusu yarinya dakyau
Ya shamsu yarungume kubra yace am sorry NY wife nayi tunanin zato zo nan ne
Tace amma kace min kaman ta yasosa keya yace a banmantaba
Yayi murmushi yanayin yadda yake maganar yabata dariya sosai atare suka fasheda da dariya
Tace Dan Allah yau ka gaiyaceta dakin nan dakanka Dan taji itama kadamu daita
Ya shamsu yayi murmushi yace yadda kikeso haka za ayi madam tayi murmushi tace kaje kashirya muje muyi break tagama komai yace wa
Kubra tace kanawata mana
Ya shamsu yayi murmushi yace to zauna kijirani nafito
Kozaki tayani
Kubra tayi murmushi tace ai kodaya bazanyiba honey
Nima wanka zanje nayi kakira kanwata tatayaka
Tana fadar haka yafada bathroom abinshi
Kubra kuma takebe baki tayi waje abinta
Wanka sosai meenat tadauka tayi kyau sosai abinta
Kubra ma tadau gayu abinta tayi kyau sosai ba kadan ba
Meenat ganin kubra yasa taraina kanta
Dan ganin kubra tamata zarra
Kubra da murmushi tace sannu da aiki kanwata amma fa kinyi laifi
Meenat tadago dasauri ta kalleta kubra ta ce hakkina nane nabaki abinci yau my kanwa meyasa kika shiga kitchen batareda da la'akari dake amarya bace
Meenat murmushi kawai tayi tace bakomai anty aikomai namiki banfadi ba
Kafin kubra tayi magana umma tafito suka gaisheta ta amsa sosai tace inashi shamsun kubra tace
Yana zuwa yanzu nakirashi umma tace kuci abinci mana kinyi shiru
Kubra tayi murmushi tace to umma aike muke jira
Umma tayi murmushi tace o ni kam zanga ranar dazaku girma keda shamsu wai kuce saida umma kwaci abinci
Takarasa maganar tana murmushi
Kubra tace umma ai munriga munsaba ne
Ya shamsu yashigo da sallamarsa umma yagaisar kafin yace umma Abba yafitane tace yafita yanzu yanagama karyawa
Ya shamsu yace amma yayi sammako dayawa
Umma tace ai suna dataron dattawan unguwane yau
Shamsu yace OK hakane natuna yaja kujera yazauna
Ya kalli kubra yayi murmushi yace kekuma bagaisuwa
Kubra tace bayan Wanda nama dazu
Kafin yayi magana meenat tace yashamsu ina kwana
Ya amsa batareda ya kalleta ba abin yaba umma kunya danta Lura ko kallon ta baiba
Ya shamsu kam azuciyarshi hamdala yayi daya bashi mata kaman nashi Dan harga Allah sunmishi kyau dukansu
****
Da daddare bayan sungama dinner meenat ta tafara tashi tayi musu saida safe umma tace amina har kingudu kenan
Meenat tayi murmushi tace umma ai ina bacci da wurine shiyasa
Umma tace shikenan jeki kwanta abinki Allah yamaku albarka yabaku masu yimuku abinda kuke mana
Ya shamsu yabita da kallo ta wutsiyar ido
Umma na kallonshi murmushi kawai tayi anty kubra ma tayi musu saida safe
Sai wayajen goma ya shamsu yayi yatafi bedroom dinshi bayan yagama shirin baccin shi daga shi sai gajeran wando
Yadauko aikinshi yafarayi a laptop
Can dai yaji wani kasala yasaukar mashi
Shifa baisaba rabuwada matarshi ba itakuma wannan