nabaki izini ba
Laila mutuwar tsaye tayi yace kifita nace
Sum sum Laila tafita
Hakeem yadawo kan husnah cak yadauketa sukayi kan bed yana rarrashinta
Husnah dake kwance kan faffadan kirjin yana shafa mata gashin kanta
Tace nifa banji haushi ba aikoba komai uwace bazan taba sa insa da ita tunda ta haifi kamata
Hakeem yayi murmushi yace Allah yamiki albarka my baby
Daga nan fa prof yafara canja salo
Tun husnah Dan basarwa hardai idanta yafara raina fata
Husnah tuntana magiyar yayi hakuri hartafara kuka amma prof dinmu yaji 'yarshila
Dan baimasan tanayi ba wai kunu awani gida
Husnah taji jiki agurin prof saikace wani Sabon shiga haka yama husnah
Yakasa control din kansa
Bashi yasami kansa ba sai wajen asuba amma fa Husnah taji jiki sosai
Saida komai yayi normal Prof fa yaga barnar data aikata
aikuwa shima ya rude dasauri yasureta zuwa bathroom yatara ruwan zafi sosai a sink din wankan yana sata aciki ta kwalla kara saboda azaba
Hakeem yaji tausayinta sosai Dan shima ba a hayyacinsa yakeba sosai take kuka saboda azaban zafi
Sai da ta Dan Dade da aruwan sannan yabude ramin sink din ruwan ya wuce
Yasake Tara wani maizafin saida ya tabbabar ta gasu sannan yatara mata wani ruwan danyin wankan tsarki
Sannan yafita zuwa dakin zanin gadon yacire ya shinfida Sabon zanin gado tas yagyara bed din kaman wata mace ce ta gyara
Shikansa baisan ya iya gyaran gado haka ba komai cikin nishadi yakeyinsa tare da sakawa Husnah albarka
Shidai zai iya cewa baitaba samun kanshi cikin farinciki da annushuwa irin nayau ba
Jiyake kaman acire mishi wasu qayoyi ajikinsa
Gawani irin son Husnah dayasake mamaye cikin jikinsa
Yana kan fito mata da jijabi yaji alamun fitowarta daga bathroom aikuwa dasauri yakarasa wajen ta yadago ta
Itakuma tana ta wurga kafa alamun yasauketa ina aisaida yadireta akan bed
Kafin ya manna mata kiss yace I LOVE U ASMA'U
Kafin yashige wanka bayan fito daga wanka ne yasaka wa Husnah jallabiyarsa yasaka mata hijabi duk ya saboda ita ya ajiyesu
Sunyi sallah amma fa Hakeem ya kwararo musu adduoin zaman lafiya da Neman kariya daga sharrin masu sharri
Juya wan dazaiyi yaga husnah tabaje kan sallaya tana bacci
Murmushi yayi yadauketa yakaita kan bed yacire mata jallabiyar
Ya manna ta ajikinsa akan tayi baccinta aikuwa sai prof fa yafara lalubeta
Cikin bacci Husnah taji yana lalubeta aikuwa bashiri ta fashe da kuka tace Dan Allah kayi hakuri wallahi dazafi
Hakeem yace oh baby nima bansan haka nake ba wallahi sai akanki
Bansan nidin jarumibane sai jiya kasancewata dake saboda haka ina kisaba da matsalata
Wallahi jinake kaman bantaba kusanta wata 'yamace ba Husnah sai akanki
Ina son kijerwa bukatuna
Nasan yarinyace ke amma nasan zaki iya kin mallaki duk wani abin da zasu biya min bukatuna husnah
Na ji dadin kasancewa dake Allah yamiki albarka
Yabamu 'yaya masu albarka
Sosai Husnah taji dadin yabon da mijinta yake mata tareda fadin asirin cikinshi
Akanta
Nan dai yacigaba da shafan bayanta zai zarce Husnah tace Dan Allah yaya kayi hakuri
Yakai bakinsa dai dai kunnenta yace zanbarki yanzu amma bashi zakibiyani da daddare
Husnah dai cewa ya hakuran ta sauke ajiyar zuciya
Sai da yaji sauke ajiyar zuciyarta akan kirjinsu
Shikam Hakeem jiyake ina ma yau weekend ne da konan da nan ba zai fita ko inaba
amma hakan bazaiyi yuba saboda tare ma zasu fita da daddynsa
Shida da rabi dai dai Hakeem yafarka yashirya cikin wasu suit Brown colour nacikinsa fari neck tied din kuma brown kai duk Wanda yaga Prof yasan yasamu nutsuwa saboda wani kwantaccen murmushi a fuskarsa
Ya kalli husnah datake baccinta cikin kwanciyar hankali gashinta duk ya rufe mata ido wasu duk sun barbazu akan pillow
Yakalleta yana tattare mata gashinta yace ILOVE YOU BABY
Harzai fita kuma sai yatuna ba kaya ajikinta sai ya dauki key din part dinta
Ya wuce yanazuwa baiga kowa a falon ba aranshi yace basu tashiba kenan
Yasa key yabude yashiga komai tas kaman ba a zama a falon ga wani kamshi dayake tashi kwani kusurwa na d'akin
Yabi ko ina da kallo cike da shawar tsaftar dakin
Direct yashige bedroom din wurin wardrobe dinta ya wuce
Yazabo mata wata doguwar Riga Mara nauyi da da mayafinsa yadauko mata
Ya rufo dakin yayi samansa har yanzu baccinta takeyi yaye bargon yayi
Rantse ido yayi saboda bayyanar kayan aikin dayagani bai Ankara ba yakai hanu zai tabata sai wayarshi tadau kara aikuwa daddy ne har yashirya yafito sutafi
Bayadda zaiyi haka yakai harshensa gurin kunnenta aikuwa husnah ta ware ido sukayi ido hudu da prof akuwa tamayar da idonta ta rufe
Murmushi prof yayi cikin wani Sabon sonta matarshi yace au kunyata ma kikeji ko wato kunyar bancireta duka ba kenan
aikuwa yasai ma tasake cusa kanta cikin pillow
Yakai bakinsa yamata magana
Kafin yamata kiss yabar dakin dan daddy najiranshi
Tana ganin fitansa ta tashi da kyar saboda duk jikinta tsami yakemata na gajiya
da kyar tasamu tayi wanka tazo sabin inner wears tanagani nan saka kafin tasaka rigar ta koma ta kwanta saboda wani zazzabi dake San kamata
PROF yana saukowa kasa yaga hajiya rukayya da hajiya suwaiba Laila da kuma suby suna ta karyawa ansamu banza komai burjik gashinan sun baje suna ta kai
Murmushi Hakeem yayi har kasa yadan durkusa yagaida su hajiya rukayya
Suka amsa da sauri kaman wasu marasa gaskiya
Suby tagaishe shi yadda yake ta amsa musu gaisuwarne duk suke mamaki sosai yake cikin farinciki
Ya kalli Laila yace maman meenat bakwa bukatar komai zan wuce gurin aiki
Daga Laila har suby saida suka kusan kwarewa da tea
Laila kuwa ganin tasamu guri harda wani Dan shagwabarta
Tace wace no Laila kadai tambayi wacce ka mareni saboda ita
Hajiya rukayya tace Ashe baki da kunya Laila mijin naki kike fadawa haka
Maza bashi hakuri kafin ranki yabaci sha sha kawai
Laila kuwa ganin irin pretending din uwarta yasa tagano jirgin ta
Tayi saurin cewa kayi hakuri
Hakeem yayi murmushi Dan gabadayansu yagano su
Ya kalli hajiya rukayya yace ai bata min komai ba
Hajiya rukayyar tace bishi kibashi hakuri Hakeem yace hajiya ga wanan kwayi tsaraba
Nan fa sukayi ta godiya suna samishi albarka murmushi kawai Hakeem yayi
Ya wuce
Laila ta taso biyoshi tace bakan bani kuma
Yajuyo yace ban baki meba
Tace katambayeni koina da bukata
Yace OK kina dashi kenan
Tace a yace mecece bukatar naki tace kudi nakeso
Yace kaman nawa tace 5 hundred thousand
Hakeem yayi murmushi yaciro cheque yayi rubuta yabata
aikuwa da farinci Laila ta koma dakin
Hakeem kai kawai yagirgaza ya wuce part dinsu mummy
Yanashiga yasamu mummy da daddy suna break
Bayan yagaishesu shima zaifara cin abinci
Mummy tace mezakayi yace break fast zanyi
Tace baka isaba sainaji lafiyar 'yata
Hakeem yayi murmushi ya Sosa keya yace bata lafiya
Daddy ashsha yajikin nata
Hakeem yace dasauki dama zazzabine kawai yamasauka bacci matakeyi
Mummy tayi salati tareda maka wa prof harara tace ashe baka da hankali zazzabinne kawai
Barinje nadubo 'yata
Ta wuce su tayi part dinsu surukanta
Tana shiga falon tagansu sunata ciyeciye ana shewa
Tace to su yaya rukayya ne agidan namu
Suka washe baki sukace sunzo duba suby ne bataji dadi ba
Mummy hafsat takebe baki tace to Allah yasauwaka
Tawuce zuwa kofar Husnah taji ta a kulle da key
Hajiya rukayya tayi sauri tace aibata sauko daga samanba nima yanzu nakeson nayi magana nace wannan irin bacci ai yayi yawa
Mummy hafsat tace au anan ma kuka kwana kenan da harkukasan lokacin data haura saman
Duk sukayi shiru kaman ruwa yacinyesu
Mummy hafsat tace Allah yasawaka zata hau saman
Saitaji hajiya rukayya nacewa waike hafsat mekika dauki kankine karfa kimanta yaron nan nima danane kamar yadda yake danki
Saboda haka Dan Nazo gidan Dana bazaki zageniba
Mummy hafsat tayi murmushi tace kudai abin kunya baya karemuku wallahi
Haba mutane saikace wasu hallittu nadaban
Hajiya rukayya ta taso cikin zafin rai tadaga hanu zata mari mummy hafsat
Hajiya suwaiba tace ke rukayya karkikuskura kimareta
Tasauke hanunta tace kinci darajar hajiya dayau natsinka miki Dan innuna gaba nake mijinki ma balleke
Mummy hafsat tayi murmushi tace dakinsake hanunki jikina dakingane kuskurenki
Bazan kiraki da shasha ba
Saboda darajin mijina dasainace shasha kawai
Tayi wucewarta saman tabar hajiya rukayya da cizon
Laila tace wallahi abin matar nan fa yafara isata ya agabanmu zata zagi uwarmu
Hajiya suwaiba tayi gyaran murya tace duk kubarta aiduk Takamarsu dai 'Dan ne aiko
Zamuyi gaggawar kawardashi kaman yadda mukawa kakarsa amina
Daga kunga sunshigo hanunmu saimu maidasu bayinmu
Hakadai suka ta kulle kellensu
Mummy hafsat tana shiga falon direct bedroom tawuce India take tunanin zata same husnah
Tanashiga taganta kwance tana bacci mummy takarasa kusa da kanta ta taba goshinta taji zafi rau
Mummy tace subhanalla ashejikin yayi zafi haka mazata shi mutafi asibiti
Husnah cikin bacci taji kaman
Muryan mummy
Tana bude ido kuwa ta tashi da sauri tace sannu mummy wallahi rana tayi hakaba
Mummy tace kedakike fama kanki zakifara magiya kuma 'yata tashi maza muwuce hospital yanzu Dan gaskiya yayi zafi sosai
Husnah bata son jayya da mummy shiyasa ta sauko duk da taso tayi tafiyarta normal amma hakan ya gagara
Abinda mummy zargi yatabbata kenan
Dama taso tazargi ba abinda yashiga tsakaninsu
Saboda yadda take muamalarta
Cikin farinciki mummy takamata tace sannu kinji 'yar albarka
Allah ya albarkaci rayuwarku yabaku zuri' masu albarka
Itadai husnah ko kallon mummy takasayi saboda gani take mummy tasan me yafaru da ita kenen
Ita rikemata hanu sukayi kasa da ita aikuwa mutan falon suka zubo masu ido cike da tuhuma
Mummy kuwa dagangan take Dada Jan husnah ajikinta
Tana mata sannu
Suna fita Laila tace nashiga uku kardai yarinnyar nan cikine da ita
Suby tace kema dai anty dawani magana
Yarinyar da kullum a dakinta take kwana yaune fa kawai suka hada gurin kwana
Laila tace nashiga uku na mutu na Lalace
Shikenan aikinmu ya ware
Wallahi duk atunanina bazai kwana da yarinyar nan ba saboda alkwarin da malam yayamana
Nan Laila tafadi kasa sumammiya
Duk sukayi kanta
Next page
Your comment is needed fans
ππππππππ
[05/05, 8:59 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU sister Sameera (masha Allah) Allah yabar zumunci ina alfahari dake wallahi keep it upπ
πAKWAI LOKACI π
πPAGE 121 to 130π
HUSNAH ta kalli Hakeem daya Zuma mata ido yana kallonta
Tace kayi mamakin ya akayi nasan Kaine ya muallim dina ko
Tayi murmushi kawai ta tashi taje inda ya boye akwatinshi tafito da fuskar (masks) kenan tafito da zoben data bashi
Sannan uwa uba Nokia din shi meroba
Husnah tayi murmushi tace kaga nagansu
Kuma yana son kafada min komai saboda nasan komai
Dan nakaranta a diary din ka
Ina sonka mijina wallahi inasonka kuma nasan kaima kasan haka saboda haka niba yaya Hakeem na aura ba
Ya muallim na aura ta juya baya
Tana murmushi
Hakeem yayi murmushi dan tariga tagama dashi yana daga zaune yakasa cewa komai
Ya tashi yakamota yazaunar daita kan cinyarshi
Yace nagode da kaunarki agareni Allah yamiki albarka
Cikin shagwaba husnah tace ameen
Yace kinsan wani ta girgiza kai yace nabaki rayuwata Husnah kiyi yadda kikeso dani
Nikam kingama mallakar zuciyata
Zaiyi magana Husnah ta tashi daga kan cinyarshi da sauri tawani maka mishi kallon so
Tace OK saiyanzu ma kabani rayuwarta ka
Dacan ma kenan ba dagaske kake ba ko
Hakeem yace ani tunranda nafara ganinki a school dinku kikagama dani
Husnah tayi murmushi dimple dinta suka lotsa sosai
amma dai ka rage wadan nan kyautar dan Allah wallahi sunyi yawa
Yace OK sunmiki kadan ne barin kara miki
Husnah tayi saurin kama kunnenta tace a a wallahi sunma yi yawa ne
Tace amma kai zaka rike a gurinka ko
Yace a a sai dai zanbaki shawara
Husnah tabashi hankalinta
Yace kibawa yaya shamsu ya rinka juya miki su anasa kasuwancin
Cike da mamaki. Husnah tace ya shamsu yafara business ne
Hakeem yace a a idan yagama makaranta nake nufi
Tace to nagode yayana
Hakeem yashafi kanta yace banason godiya kamata yayi idan namiki
Abu nizan gode miki dan kincancanta
Hakeem dai bai bar Husnah haka ba sai dayasake hutawa sukayi wanka
Husnah takalli Hakeem dake saka turare tana kallonshi kuwa shima yana juyowa aikuwa suka hada
Tayi saurin saukar danata
Murmushi Hakeem yayi ya ma daf da ita yana kokarin cire towel din dake jikinta
Wai zai shafa mata
Tace a a nida kaina zansha fa Hakeem ya lakace mata hanci yace waya fada miki zanbari idan ina tare dake kiyima kanki wani Abu
Zanbarki kiyi aiki ne kawai idan nizakima dan kisamu lada
Daga yau nizan miki wanka nizan shafa miki mai nizansa miki kaya
Abinkwai da zaki kimin kwalliyar fuskarki duk da kefa da kwalliyar ki aka haifeki
Husnah tayi murmushi tayi fari da ido tace OK aikinka yafara yanzu
Hakeem yace yes madam tace to kayan dazansa zaka debo min a bedroom dina
Hakeem yayi murmushi yace angama madam ya wuce yafita
Yana fita Husnah tayi murmushi ta tashi dasauri kafin yadawo tagama shafa manta dama wayo tamishi
aikuwa Hakeem da yadawo yaga tashafa mai tana mishi dariya yace OK wato wayo kikamin ko aikuwa
Sai nabaki punishment tunda kin kar ya min doka
Kafin Husnah tayi magana
Hakeem ya hada bakinsu waje daya
Takasa kwace kanta karshema dai cak yayi da kan bed tana bashi hakuri
Ina baijita ba yayi nisa sosai
Sai daya dawo hayyacinsa kafin yarungumota yace duk randa kika sake shiga min aiki ko to punishment dinki kenan
Husnah dai ta gurzu baki ya mutu
Tana kwance kan kirjinshi
Yace barin hada mana ruwan wanka
Husnah ta rufe ido kaman tayi bacci ya leka fuskarta yaga a rufe
Sai yayi murmushi shima yadada mannota da jikinshi kafin bacci yayi a won gaba dasu
Sai karfe goma Hakeem ya bude ido
Yaduba agogo yaga har goma
aikuwa ya tashi da sauri dan makara office
Ya je yahada musu ruwan wanka cak yazo yadauki husnah sai cikin ruwa
Ita Husnah abin nashi har mamaki yakebata kokadan baya jin kunyarta
Tare sukayi wankansu yadaukota zuwa kan bed
Saida yafara shiryata cikin wata doguwar rigar shadda Wanda yazabo mata acikin kayanta
Ya feffesa mata turarruka masu kamshi kafin yace maza yi na fuskar da daurin dan kwalin
Husnah ta turo baki tace kai kamin kwalliyar tunda kace karnayi komai
Nima ban iyaba
Hakeem yayi murmushi dan yarin tar da tanuna mishi ya burgeshi sosai
Yace OK gani kikeyi bazan iya ba bari kiga ni zanbaki surprise
Nan fa Hakeem yazage sosai waishi yana mata kwalliyar fuska
Itadai husnah tana ganin ikon Allah
Har yagama yamata dauri shima dai daurin gashi ga yanayinshi
Ya hanata kallon madubi wai sai yagama
Yana gamawa yajata zuwa gurin mirror
aikuwa husnah tana hada ido da fuskarta ta kwalla kara ta kankameshi
Tace nisai ka biyani fuskata
Dariya sosai Hakeem yake
Damshima kanshi yasan yabata mata fuska
Sosai take mishi rigima wai sai yabiyata fuskarta
Saida yagama dariyarshi sannan yadauketa zuwa bathroom ya wanke mata fuska
Kafin suka dawo
Hakeem yace insake miki mekyau ne
Husnah tace wallahi na yafe zanyi abuna
Yace OK tashi maza kiyi nabaki 5 minutes kigama
Kizo kizauna kawai inashiryawa ina kallon kyakkyawar surarki
Murmushi husnah tayi kafin tayi kawalliyarta Hakeem masha Allah kawai yake nanatawa tunyanayi azuciya yadawo afili yadawo
Husnah ta taso tazo gabanshi tahure mishi ido
Murmushi yayi husnah tace yada kallo
Hakeem yakamota yazaunar da ita bakin bed
Yace kinyi kyau mamatata I LOVE
Husnah tayi murmushi cikin salon shagwabar ta tace kardai kasa love yakare fa
Dan nasan kafada yafi a kirga
Hancinta yaja yace ai saidai yakare dan ba ranar da bazakijishi ba abakina
Ya tashi zaifara shafa mai yaga hanun Husnah tarike
Yakalleta tace niban amince inanan kama kanka komai ba wannan ai kina ne banakaba
Sai dai ranar da kake gurin anty na
Shine zan barmata kai amma fa ba wai dan naso ba sai dan yazama dole
Nan kuma tacigaba da samishi kaya
Tabbas tabashi mamaki baizata tana da wannan wayewar ba amma yanzu. Ya tabbatar wa kansa yasan yayi aure
Atare suka fito zuwa kasa bayan husnah tasaka key ta kullo saman Yakama hanunta suka gangaro
Laila ce kwance suna waya da meenat
Dan ta nunawa Husnah cewan itama fa tana da martaba agidan
Tace wa meenat ga ma daddyn naki yasauko
Ta taso jiki narawa tana iyayi itaga mai uban 'yarta
Hakeem ya kalleta yace Bata San layi na bane
Kice takira ni ta layi na
Zaiyi waje husnah taja hanunshi tace haba my one
Dan Allah kakarba bazata jidadi bafa
Kafin Hakeem yayi magana Laila to bakar munafuka
ai basaikince yakarba koya karba koka karya karba sundai fi kusa 'yarsace bai isa yacanja taba kefa duk lokacin dayaga dama zakiyi waje
Zatayi magana Hakeem yarungumota suka fita
Takaici yadami Laila tayi kaman ta hadiyi zuciya ta mutu
Suby tace kai wallahi akwai matsala babba agidan caf
Ashe Laila Bata kashe wayartaba
Meenat ta ce mummyna yanaji hayaniya
Lafiya kuwa kafin Laila tayi magana har suby takarbi wayar takwashe komai tafada mata
Meenat tace nazo koni ko 'yar iskar yarinyar nan
Ta kashe wayar saboda takaici
Husnah da Hakeem tare suka shiga falon mummy
Ganin mummy na falon husnah sai kacaniyar kwace hanunta takeyi
amma Hakeem yaki sake ta
Dahaka suka shiga Husnah tayi saurin zubewa tagaida mummy
Mummy tace zonanki kizauna Husnah kidaina zama akasa keda falon mummynki
Husnah murmushi kawai amma ita bazata iya mummy nasama kujera itama tazauna ba
Mummy tace kukarasa kuyi break fast
Husnah tace mummy ina daddy
Mummy tace yafita sunyi wasu bakine
Hakeem yace OK bakin sun isokenan
Mummy tace ina tunanin haka
Hakeem da Husnah suka yi dining area mummy tasan idan tazauna husnah bazata ci wani abin kirkiba
Yasa ta tashi ta haura sama
Hakeem kuwa kaman jira yake mummy ta fita yajanyo husnah yadaurata kan cinyarsa yana feeding dinta da kanshi
Sai da yatabbatar takoshi yabarta
Kafin shima zaifara cin nashi yadaga spoon zai kai baki sai husnah tarike cokalin
Tace aimunyi alkawarin karwani yashiga ma wani aikinshi
So kadina shiga min nawa
Ta dauki spoon tafara feeding dinshi shima
Hakeem cikin wani shauki yake jinshi mewuyar fassara saboda yadda yaga babynshi tafara sakin jiki dashi sosai tana nuna mishi soyayyar da be taba tunanin zata iya nuna mishi duba ga yanayin kunyarta
Suna gamawa tadauki brief case dinshi tarataya tace oya
Kaje kawa mummy sallama yace inje ina tace office mana
Yace ai ba inda zani jeki dauko mayafinki kawai muje yawo
Cike da murna husnah tace wallahi kaman kasan inason ganin waje
Yayi murmushi yace maza jeki dauko kafin nakirga ashirin
Bai rufe baki ba tayi waje da gudu kaman Bata jin zafin jikinta
Murmushi kawai yayi mummy ce tasauko daga sama tace Ku gama break din yace mungama mummy
Zamu dan zagaya ne taga gari mummy tace yakamata taga gari itama tasan Kaduna
Next page
Your comment is
Needed fans β€β€
Love u all
ππππππ
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU UMMU HISHAM ina alfahari dake wajen nice comments wallahi Allah yabar zumunci keep it upπ
πAKWAI LOKACI π
πPAGE 131 to 135π
HAKEEM DA HUSNAH
Hakeem na driven amma hanun daya yana makale da hanun husnah
Wayar Hakeem yadaukara yana gani yaga Ahmad ne
Ahmad yace kai young Prof wai mekake tun tuni baka fito ba
Hakeem yayi murmushi yace ganinan a hanya zuwa amma fa aiki zanzo ba zanbada
Wasu muhimmam takardu ne wa manager yacigaba da kula da komai saina nan da kwana biyar zan koma office
Ahmad yace kai soyayya manya
Wannan irin rawan kai Man
Karka rikita musu yarinya fa
Hakeem yace zamu karaso gidan naku ma kasanar da madam Aisha
Ahmad yace a haba kace muna da Mayan baki kenan
To barin koma gidan najiraku
Hakeem yace OK saimun karaso
Ya kashe wayar ya kalli Husnah dake ta chat a wayarta
Yace kedawaye tace nida anty kubra ne wallahi
Saida suka jajja wurarn shakatawa na kaduna kafin suka wuce gidan Ahmad
Suna zuwa Aisha ta karbi husnah hanu biyu taja hanunta tace kinga zo muwuce can ciki
Su suzauna abinsu anan
Ahmad yace indai akayi gulmam mu Allah nagani dake da kanwarkin nan
Husnah tayi murmushi Bata ce komai ba
Aisha tace Ashe kunsan Baku da gaskiya kenan shiyasa kuke tunanin za ayi gulamarku
Suka wuce abinsu suna dariya
Ahmad yakalli Hakeem yace kai mutumina gaskiya balalle nan da wata daya mugane kaba gaskiya duk kawani canja gawani kyau da fresh
Hakeem yace kai dai duk aikin babyna ne
Kasan Allah Dana San haka aure yake da ban tsaya batawa kaina lokaci wajen gwada taba
Kaga wakila da yanzu tana shirin Haifa min baby
Ahmad yace yanzu baka tunanin kuma 'yata tadawo taga ubanta yana cin soyayya da kawarta yazakayi kenan
Hakeem yayi murmushi yace koda meenat da Husnah kawayene ba ruwana da alakarsu
Ballantana ma Husnah tanuna min ba kawarta bace suna dai gaisawa kadan
Kasan meenat gaba daya uwarta ta Bata ta
Kaga kuwa ballebane suhada hanya da Husnah
Ahmad yace to da saukima tunda ba kawarta bane
Allah ya rufa asiri
Hakeem yace ko kawarta ce baruwana
I love my wife more than her expectation
Ahmad yace wallahi mutumina meenat ta ruda ka dayawa fa gaskiya ta ciri tuta acikin mata
Hakeem yace bakadan ba
Aisha ta kai musu abinci dining
Kafin tadauki nasu da Husnah ta wuce da shi ciki
Hakeem yace madam kikula min da ita fa dan bata son cin abinci sanayi dagaske take cin abinci
Aisha tayi murmushi tace karka damu zataci sosai indai nice
Yayi dariya yace yauwa maman twins
Tace kai Allah ya amshi bakin ka tawuce
Ahmad yace kasan yadda Aisha takeson twins kuwa
Nan dai sukayi hirarsu sai wajen karfe biyar suka koma gida
Husnah tace oyoyo mummyna nayi missing dinki wallahi
Mummy tayi murmushi tace nima wallahi ina zaune Dan wunin da kikayi bakya nan duk sainaji ba dadi
Hakeem yayi murmushi yace wato ma mummy batani ma kikebako
Mummy takalleshi tace au dama ka shigo ne ai banganka ba ma
Husnah dariya tayi tafaki idon mummy ta mishi gwalo
Hakeem yace mummy kinga kinja tana min gwalo ko
Wato nine baki gani ba ko
Mummy tace danaganka ai Dana kulaka Husnah da mummy sukayi dariya
Husnah ta tashi tace mummy ga tsarabarki nan keda daddy taga rakene aka gyarasu sunyi kyau da sha'wa
Mummy ta ce kai kaman Kinsan ina matukar son rake allah yamaki albarka Husnah tace amin mummy na
Hakeem yace tunda ni baki ganniba basai nabaki naki tsarabar kenan
Mummy tayi murmushi tace a naji tunda 'yata tabani ai wadatar Husnah tayi dariya
Hakeem yayi murmushi yace wakike wa dariya husnah tace nida kujera nefa badakai ba
********
Bayan sati biyu shakuwa soyayya da kuma wayewa duk sun bayyana ajikin husnah ga uba kyau da Hutu
Bata kara kiba ba amsa fa tayi wani fresh da bulbul da ita gwanin sha'wa ga uwa uba soyayyar