tace tabbas basobane sai yanzu nasan soyayya anty na amma tazo min a inda bai kamaceni ba
Husnah tayi murmushi tace indai tayi wari maji ai
Meenat tayi murmushi tace seson gulma
Husnah tayi murmushi tace bakida kunya ko wace meson gulmar meenat tayi saurin kama kunne tace am sorry my mum
Husnah tace an miki afuwa
Tayi kamar bazatayi da dariya ba sai kuma suka kwasheda dariya gaba dayansu
Hakeem ne yashigo falon da sallama ganin suna dariya yace dariyan me kukeyi
Kuncika wa mummy kunne
Meenat ta tashi da sauri ta karbi brief case dinshi tace sannu da dawowa daddy yace yauwa 'yar daddy
Dariyar mekuke keda antyn taki
Meenat tace wallahi daddy abincin data ci yau muke kirgawa ga kuma dashishi mummy tamata yanzu tana kan ci
Hakeem ya kalli husnah datake cin abincinta bata kulashi ba saboda yayi laifi yau kafin yafita tace yabarta taje taga ummanta ya hanata
Murmushi Hakeem yayi yasan fushi takeyi
Meenat ta wuce zuwa can part din daddynta takai mishi jakar
Hakeem yamaka mata kallon so
Matsawa yayi gabanta yadauke plate din abincin
Cikin shagwaba ta tace kabani abincina
Yace anki abaki meyasa baki min sannu dazuwa ba
Tace yau she kashigo aini bangan kaba ma
Yanayin yadda take maganar yamatukar bawa Hakeem dariya yazauna kusa da ita yace mama food
Inga cikin naki wai a ina kike ajiye abincin ne Husnah tajuya kai abinta batason hirar
Hakeem ya janyota jikinshi yace baki huceba
Tayi shiru
Yace shikenan ina dai kano ne kishirya gobe kaiki
Bata San lokacin data dada rungumeshiba Dan tama manta inda take
Tace yauwa my Prince kokaifa wallahi har naji dadi sosai
Cikin shagwaba tayi fari da idonta tace amma naga yau kadawo da wuri lafiya kuwa
Yayi murmushi yace nazo mugaisa da babyna nane
Husnah tasan irin gaisawar dayake nufi
Dan haka kawai watarana idan taraya mishi zaibar office yadawo gida ya fitineta
Murmushi husnah tayi tace naki wayon wannan gaisawar taka
Hakeem yakalleta Wanda idonsa tuni yacanja kala
Yace nima kuwa nafasa zuwan naki kanon tunda hakane yayi murmushi
Mummy tasauko daga sama tace a a Ashe Kaine Hakeem yace a mummy wannan acicin ne
Mummy tayi murmushi tace wayafada maka son kanta ne yasa take cin abincin dayawa ai dankane yake sata cin
Hakeem yayi murmushi
Mummy tace katashi kaje dining mana akwai abinci
Hakeem dashi kadai yasan meyadawo dashi gida
Yace wa mummy zanyi bacci tukun nadan huta kafin abincin
Mummy tace afito lafiya to
Hakeem yatashi yanasatar kallon Husnah
Yaga dai bata daniyar tashi tabiyoshi
Yace kizo kibanin number din inason nakirasune
Husnah taji mamakin wannan karya daya mako
Mummy tace tashi kije kibashi number idan kindawo saiki karasa ci kisha magani
Husnah tace to atare suka fito
Mummy tayi murmushi tace kai wai kahaifi 'da acikinka yace zai maka wayo
Allah yadada zaunar Ku lafiya yabaku zuri'a tagarai
aini idan duk shekara Husnah zata Haifa maka 'da Son murna zanyi naga gidan koina da jikokina
Mummy nata zancen zucinta meenat tazo tazauna tace
Uwargida sarautar mata
Mummy hafsat tace to sarkin surutu kinfito meenat tace nafito wai yaushe wannan tsohon zai dawone
Mummy hafsat tace kinga wallahi kifita a idona dacewa mijina tsoho
Meenat tayi murmushi tace tsufa kuma aikungama tsufa nan sukayuta dariya
Hakeem kam yanashan yana hutawa kamar yadda yacewa mummy
Bayan sunfito daga wanka ne suna zaune akan resting chair dake bedroom din Hakeem husnah kwance kan kirjinshi yana shafa gashinta itakuma tana wasada gashin kirjinshi
Yace sai kitashi muje kimusu shopping ko
Husnah tace a a wallahi kabarshi karyazama barnar kudi tunda ba adade da kaimusu tsaraba ba
Hakeem yayi murmushi yace ba abinda zanwa su umma yazama barnar kudi
Dan Wallahi banajin ban bancin umma da mummy agareni Dan haka kidauka nima umma mahaifiyatace yadda kika dauki mummy na amatsayin uwa nima haka umma take agurina
Husnah tace banida bakin dazan gode maka akan yadda kake kula da mu gabadayanmu
Allah yakara arziki my Prince
Hakeem yace nifa banason wannan godiyar da kike min
Dan komai nawa nakine kina da damar dazakiyi yadda kikeso da komai nawa nariga nasa hanu
Nan dai suka shirya sukatafi shopping
Sai dare suka dawo
Washagari meenat tace itama zata Hakeem yace tashirya suje suyi kwana biyun
Husnah taji dadi kuwa dazuwan meenat
*****
Sun isa kano wurin la'asar
Ya shamsu da anty kubra suka taresu suna murnar ganin su
Meenat tadurkusa har kasa tagaida ya shamsu
Yace a a mutanen Kaduna yasu mummyn meenat tace lafiya kalau suke
Husnah tace kai anty kubra wannan irin kyau wallahi komawa baby kikeyi
Anty kubra tayi murmushi tace keba kiga yadda kika koma ba ko
Anty kubra ta ruko hanun meenat tace meenat sannun dazuwa kinji husnah ta tareni dashirme hanun meenat rike da hanun anty kubra suka Shiga
Umma tayi murna sosai da zuwansu
Abinci kala kala a ka saukesu dashi
Meenat dai takasa sakewa kwatata
Washagari husnah nazaune a falo itada umma meenat da anty kubra kuma suna kitchen suna abinci
Sungama suka jera komai kafin nan kuma kowacce tawuce wanka
Meenat dakin dasuka sauka tawuce
Itada husnah ne dakin anan suka sauka
Bayan salar isha abba da yashamsu sunshigo husnah sai shagwaba takeyi yadda ranta yakeso kowa naji daita
anzauna za afara cin abinci
Sai umma tace Husnah tashi kikira amina tazo taci abinci itama cikin mutane
Narasa takasa sakin jikinta ai komai yawuce tunda anzama daya
Husnah ta tashi zataje kiran meenat
Kubra tace zauna abinki zankirata
anty kubra ta na Sakai cikin dakin tadawo dabaya tatsaya turus
Kunnenta takunnenta sosai
Meenat dabatasan anshigo ba tace ya Allah narokeka kacire min son Wanda nasan bazan taba samunshi ba ya Allah nasan ya shamsu yafi karfina
Ba abinda zaiyi dani yana da mata kamar wacce yake da ita
Nasan yafi karfina ya Allah kai kajarrabeni da kaunarsa Allah ka yaye min
Allah natuba Allah kacire minshi acikin arayuwata ya Allah
Tana kuka mecin rai
Anty kubra kasa jurewa tayi cikin tsananin tashin hankali tajuya zata koma dabaya
Sai kuma tayi tunanin to idan antambayeta mezatace
Sai kawai ta daure tashiga dakin aikuwa meenat naganinta tace sannu anty
Kubra tace yauwa kanwata kifito muci abinci kinji
Meenat tayi murmushi tace to anty
Da daddare anty kubra kasa bacci tayi tana ta tunanin abinda kunnenta yaci mata
Can tayi tunin haba kubra kiduba fa gidan nan basu da wadatar yara umma zataso taga 'ya'yan shamsu amma bawanda yataba maganar rashin haihuwarta kowa nuna mata kauna yakeyi
Kuma tabbas sunje asibiti an tabbatar itace da matsala
Dan meyasa zata zama meson kanta dayawa Yakama itama tarama hallacin da mijinta da iyayenshi suke mata arayuwa
Kuma ai meenat ta shiryu ta tabbatar zasuyi zama na girmama juna
Sai dai kuma ta yaya zata hada wannan Abu bayan tasan balalle bane su amince mata
Juyawa tayi takalli yaya shamsu dayake baccinsa
Take tausayinsa yakamata tasan yana balain son yara
Kuma gashi ita bata halin bashi wannan farincikin
Tana da yakinin ya shamsu bazai taba juya mata baya ba koda ya auri meenat ta Haifa mishi yara
Tayi murmushin dole tace meenat Allah zaibaki abinda kikeso fatana Allah yasa muzauna lafiya
Kubra ta Dan taba ya shamsu kadan yatashi yace a a honey mekike yi baki kwanta ba
Tace katashi muyi magana Dan Allah
Dayake ya shamsu yana matukar bawa kubra muhimmanc acikin rayuwarsa
Yatashi yace Allah yasa lafiya kubra tayi murmushi tace
Alkairi nema
Next page
Your comment is needed Fan's
Love you all
ππππππππππ
[06/05, 11:18 AM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU MAMAN MUFIDA
Ina alfahari dake wallahi kina kasheni da wannan nice comments din naki Allah yabar kaunaππππππ
πAKWAI LOKACI π
πPAGE 153 to 155π
YA SHAMSU yace inajinki honey
Kubra tace wallahi inasha awar naga yara agidan
Koda kuwa bani zan haifesu ba inason ganinsu
Ya shamsu yace bangane mekike fada ba kubra
Kubra tace nazauna nayi tunani
Halaccin da kukayi min a rayuwa Dan me nima bazanso abinda zai faranta ran ka Dana su umma ba
Wallahi koba afadamin ba nasan yadda kakeson yara
Koba kaiba ma su umma fa girma ya kamasu zasuso suga yaranka kafin sukoma ga mahallincinsu
Saboda son dasukeyi min da nuna kulawa agareni yasa bantaba jin umma tayi magana akan rashin haihuwataba
Kuma nasan dole abin zai dameta
Kaga idan har nacika masoyiyarka ta gaskiya dole ne nayi kokarin ganin farin ciki arayuwarka idan har INA da damar hakan
Ya shamsu yace duk meyakawo wannan maganar kubra mekike nufi kenan
Kubra tace ina nufin kayi aure Dan Allah muna bukatar muga yara acikin gidan nan
Dan Allah karki yadda da bukatuna
Kayi tunani mai kyau akan magana bakai zaka duba ba su umma zaka duba
Ya shamsu Wanda mamakin kubra yakeyi tubaran
Yace anya kina cikin hankalinki kuwa kubra
Meyasameki
Bantaba ganin macen datake jawa kanta kishiya ba saike
Kokuma kindaina sonane yasa kike fatan nakawo wata cikin rayuwarmu
Please banason sake jin wannan maganar a bakinki Dan Allah bana samum sabani dake amma akan wannan zan baki mamaki
Kubra tasauka kasa tazuba gwiwarta akasa tana kuka tana rokanshi akan yacika mata burinta
Yaga abin nata ma dagasake ne yafita daga dakin yakoma dayar dakin yasaka key
Kubra kuwa ganin yabar mata dakin
Yasa tama rasa tunanin dazatayi
ahaka bacci yadauketa rana nafarko dasuka fara raba shimfida kenan da mijinta
Washagari da safe bayan sungama karyawa meenat tace zata ta kwanta Dan tana komawa baccin safe falon yarage daga husnah sai umma sai anty kubra
Umma ta lura da kubra yau kaman bata lafiya takasa yinshiru tace khadijah lafiya kuwa
Kubra tayi murmushi tace umma ina da magana amma keda Abba nakeson magana daku
Umma da husnah suka kalli juna Dan basu taba ganin kubra cikin wannan halin ba
Umma tace to kutashi mutafi can falon abban naku sai kiyi maganar acan
Tare umma da kubra suka wuce sukabar husnah da damuwar rashin sanin maganar da kubra zatayi
Can husnah tace kodai fada sukayi da yaya shamsu
Tace haba ya shamsu me anty kubra zata maka da har zai kasata adamuwa irinhaka
Haka ta tashi ta wuce part dinsu anty kubra tanazuwa tasamu ya shamsu a falo yana kwance fuskarshi nakallon sama husnah tashiga
Husnah tayi sallama ya shamsu ya amsa tare dayin yaken dole
Husnah tace ya shamsu wai meke faruwa kaida anty kubra ne
Yatashi da sauri yace tafada miki wani abunne
Husnah tace a a amma yau bata cikin walwala kuma tace tanada magana da Abba
Ya shamsu yace ita kubaran yanzu tana ina husnah tace suna falon Abba
Dasauri ya shamsu yafita yayi hanyar falon Abba yanazuwa yace kubra wai meyasa bakya jin maganane Dan Allah
Abba yace karaso mana ubana yafi nakowa sham sudden
Ya shamsu yashiga yasamu guri yazauna
Abba yayi gyaran murya yace matarka tasamemu da wata magana wacce da bamu amince da itaba sabida ganin rashin dacewar hakan amma kuma tafimu hujja da da dalilu masu yawa
Ya shamsu yadaga kai yace Abba yanzu inbanda shirme irin na kubra ta ina zanfara Neman matar aure
Abba yace ai har matar ma tariga tasama maka ita
Dasauri yadago kai yakalli kubra wacce tamaida kanta kasa
Yace bangane tasamamin matar aureba
Abba yace wannan yarinya amina
Ya shamsu yace amina kuma wacece wannan kuma
Husnah dake bakin kofa tace meenat kenan
Duk suka kalleta anty kubra tace a itanake nufi
Na tabbatar a yanzu duniya ta mata karatun tanutsu zata zauna lafiya
Kuma meenat bakowa takeso sai yayanki
Tana son ya shamsu kobadan itaba ai zamu duba babanta da kakaninta tashiryu duk abinda tayi da ina da tabbacin yarinta ce amma yanzu hankali yazo mata Dan Allah ke ma husnah kifahimce ni
Husnah tace yanzu anty kubra dakanki kikeson janyo meenat ajiki bayan munsan ta musan halinta
Anty kubra tace sanin da kika ma kuma kema na San kinyarda meenat ta canja
Abba yace duk kuzauna mufahimci juna
Nan Abba yayita musu nasiha
Sannan kuma yanuna musu faidar yin abinda kubra tace
Umma tace gaskiya khadija samun mace irinki awannan zamani maison farinciki Wanda take taredashi koda ita zata rasa nata farincikin
Kai kuma shamsu idan wannan aure dazaka yi zaisa kubra tayi farinciki to kaje kanemi auran amina
Abba yace wannan banyarda kabata wa kubra ba shamsu a rayuwar ka mace ce tagari
Wacce samun irinta a rayuwa sai antona
Kubra tace nagode dakuka fahimceni
Abba yace Allah yamiki albarka yabaku masuyi muku abinda kukamana
Anty kubra ta tashi tafita
Abba yakai kallonshiga shamsu dayayi suman zaune
Abba yace abinda yakamata yarinyar tayi a yanzu tabbas lokaci yayi dayakamata karamawa kura aniyarta ba abinda zamuce ga wannan yaro Abdul Hakeem da iyayensa saidai Allah yasaka musu da gidan aljanna
Kaduba yadda suke kula da 'yar uwarka ba abinda tanema tarasa
Baka tunanin hanyar dayakamata kaima kamishi wani Abu dazaiyi jidadi a rayuwarshi
To Allah ne yabaka damar dazaka sakamasa shima shine ka auri yarinyar nan amina kariketa kamar yadda yake rike maka naka 'yar uwar
Nan dai su Abba sukayi ta fahimtar dashi faidar yin hakan
Da daddare kubra da yashamsu sunyi shirin kwanciya
Sunkwanta kubra kallon kayan da akaturo mata nasiyarwa ne wata kawarta ce take kawowa daga Dubai
Ya shamsu yakarba yana kallo shima yace kai amma sunyi kyau wanne kikazaba
Kubra tayi dariya tace daga ganin Abu a waya kuma saina hau zaba kawaidai ita tafara nunamin ne inga irin kayan data saro kuma nagani kaga nace mata ma sunyi kyau sosai
Yace hakane to ninace kizaba muku masu kyau keda asmau
Kubra tace a a fa wallahi bada niyar kasayamin nabude kaganiba kawaidai nabudene Dan nasan ta turo sai dai nazabawa
Husnah dai tunda kayi niyya saya
Ya shamsu yace kizaba muku banason musu
Kubra tace to ai kabari muji kudinko
Ya shamsu yace bakyajin magana ko
Kubra tayi murmushi tace shikenan angama rankayadade
Saikuma tace muka saya mana kanwata fa meenat kagafa tunyanzu yakamata ka kafara kwatanta adallcin fa
Ya shamsu yace yasalam kubra rigima wai ba anwuce wannan shafin bane
Kubra tayi murmushi tace yanzu aka bude shafin kuwa kasan fa jibi zasu koma gida yakamata kagabatar da kanka agurin meenat
Ya shamsu yace Ashe kuwa saidai afasa kenifa barin fada miki wallahi bayadda na iya ne yasa na amince muku keda su Abba
amma wallahi duk abinda yafaru dake zanyi kuka
Kubra tayi murmushi tace ba abinda zaifaruma sai alkairi
Yanzu dai mu uku zan zaba mana ko
Ya shamsu yakwanta yace yadda kikace
Murmushi kawai anty kubra tayi tace shikenan
Tace nazaba mana nida husnah katashi kazabawa meenat nata
Duk kubarshi amfasa indai nizan zaba mata
anty kubra ta kunshe dariya acikin bakinta Dan yadda yayi maganar yabata dariya
Husnah da meenat suna kwance sunyi shirin bacci
Husnah tacewa meenat duk da kinfada min Wanda kikeso yanzu idan Allah yacika miki burinki kika aureshi Wanda kikeso yazakiyi wani irin tanadi kika mishi wurin faranta mishi
Meenat ta tashi tazauna tayi murmushi tace hmm wannan sirri nane tsakanina da mahaliccina
Dan Allah yaga niya ta akan shi idan Allah yacikamin burina Wanda banma taba mafarkin cikansaba
amma wallahi Allah yasani inason shi sona hakika so mai tsabta
Husnah tayi murmushi tace Allah yacika miki burinki
Zaki auri Wanda kikeso meenat
Cikin tsananin mamaki meenat tace taya akayi kikasan Wanda nakeso bayan nasan banfada mikiba
Husnah tace labarin zuciya a tambayi fuska kawata kuma nima antyna a yanzu
amarya agurin anty kubra mace daya tamkar yadubu
Mata agurin masoyinki ya shamsu
Meenat da mamaki take kallon husnah tace ya akayi kika fahimci asirin zuciyata
Husnah tayi murmushi tace karkidamu Allah dai yanuna mana lokacin
Ni husnah nafi kowa gata da samun matan yaya guda biyu masu sona Allah yabaku zaman lafiya
Bana son tambaya bacci zanyi idan kika dameni zanfada wa dad dinki
Kin hanani bacci ta kwanta abinta tana cike da farincike
Meenat tarasa abinyi murna zatayi kokuma akasin haka
To kodai shima ya shamsun yanasonta ne kai a a akwai dai wani Abu
Kuma mai bata amsar taki fito da daita daga duhu
Tashi tayi tashiga bathroom alwala tayi tana Neman zabin Allah
Washagari da safe meenat takasa fita falo tayi takasa hada ido kowa inba husnah ba
Umma ana cin abincin rana
Anty kubra ta kalli husnah tace wallahi baki kyauta ba yanzu gashi kinsa tunsafe takasa fitowa cikin mutane
Husnah tayi murmushi tace
ai dole takasa fitowa tunda bata da gaskiya takarasa maganar tana dariya
Umma tace tashi wa husnah kitashi kije kikiramin ita
Husnah tace to ta tashi ya shamsu yayi kaman yayi magana sai yabasar kawai
Next page
Yau kunga typing din kadan watspp ne yakebani matsala
Please marasa comments ina ganinku fa kara nake muku
Masu comment ina alfahari daku Allah yasaka da alkairi
Love you all
ππππππππππ
[06/05, 11:21 AM] UMMU AFAN πΉ: ππππππππ
πππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
STORY & WRITTEN
BY
THE SPECIAL AUTHOR /WRITER
UMMU AFAN πππππππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉF.C.T.W.A.πΉ
πΉHOME OF QUALITY AND TRUSTED WRITERS OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU SISTER SHAFA'ATU (UMMU KHALEEL)
Ina alfahari da comment dinki over kina kokari sosai wajen suburbudo comment Allah yabar zumunciππΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
πAKWAI LOKACI π
π PAGE 156 to 157π
HUSNAH tashiga dakinsu da sallama tasamu meenat kwance dawa a hanunta
Tana chart husnah tace anty meenat umma nakiranki
Meenat tadafa kirji tace nashiga ukuna
Wallahi ina matukar jin kunyar 'yan gidan nan
Husnah ta ballawa meenat harara tace saikizaba
Ko zuwa kiran umma ko jinkunyar
Meenat tayi saurin saka hijabin dogo har kasa
Tace muje amma Dan Allah ya shamsu yana falon wallahi banason hada ido dashi kunyarshi nakeyi wallahi
Sosai dariya yakama husnah tace yaukuma kece da kunya meenat
Meenat tazunburo baki tace bake kika fada ba kuma alhalin niban fada miki da bakina ba
Husnah tayi murmushi tace to ai labarin zuciya atambayi fuska
Husnah taja hanunta suka fito alokacin ya shamsu yadauki cup din tea dinshi
Yayi gefen kujera yazauna yana shan abinshi
Meenat suka fito da taga baya falon tayi hamdala azuciyarta
Ta durkusa harkasa tazauna gaban umma tace umma ina kwana
Umma tayi murmushi tace haba amina kinbuya adaki kinki fitowa kisha iska
Meenat tayi murmushi tace ba komai umma tace umma azumi nakeyi
Kafin umma tayi magana anty kubra tafito daga part dinta tace yauwa kokefa meenat amma kinki fitowa kisha iska
Meenat kanta akasa tace anty ina kwana anty kubra tace lafiya qalau antashi lpy
Umma tace wani irin azumi yau lahadi
Husnah tace au umma har kinyarda ma azumin takeyi
Wayace tayi ringing kan dining din dasuke husnah tace ya shamsu ankiran wayarka
azabure meenat ta kalli bayan ta kan kujera aikuwa caraf suka hada ido
Tayi saurin saukar da fuskarta kasa tana
Shima ya shamsu baisan lokacin da yakalleta ba yakau da kansa
Husnah ta kallesu tayi murmushi kawai
Umma talura da yadda meenat tarikice tace tashi mana kici abinci
Meenat tace to umma amma kasa yafi min dadin cin abinci
Anty kubra tadauki wayar ya shamsun takai mai
Yakarba yace tazauna anan
Tayi murmushi tace ina karyawa nefa honey
Ya tashi yadauki wayarsa da yace biyoni
Anty kubra tabi bayansa sukatafi part dinsu meenat ganin sunbar falon yasa tadan sake kadan
Prof da Ahmad ne sukawa kano diran bazata
Ya shamsu sosai yakarbesu a falonshi prof yakira wayar husnah yace baby kufito mutafi ko
Husnah tace badai kunzo kanoba
Murmushi prof yayi yace naki wasane ke atunaninki zan iya barinki har kwana hudu ukun ma dakyar nayi
Yashamsu yashigo falon yaga Hakeem nawaya
Ahmad yace kaga wannan romeo din barnar kati baya mishi wahala
Wai kuna gida dayama amma kana kashe murya a waya
Ya shamsu yayi murmushi kawai yana jin dadin yadda Abdul Hakeem yake ba wa kanwarsa kulawa ko agaban wayekuwa
Kodan wannan zai auri meenat zai riketa tsakaninshi da Allah
Meenat da husnah suka fito cikin rakiyar anty kubra da umma
Sosai umma tahadawa meenat tsarabar su humra ne da dai sauransu anty kubra ma tabasu nata
Sosai sukayi kewa meenat dai Allah Allah take sutafi Dan ta takura sosai wallahi
********
Bayan sati biyu da komawarsu Abban su husnah da wani abokinshi sukatafi Kaduna
Dama daddyn Hakeem yasan dazuwansu
Shida daddyn Ahmad suka karbesu
Bayan anci ansha Abba yakawo musu bukatarsu
Daddyn Hakeem yanisa yakalli daddyn Ahmad yace lalle wannan yarinya amina Allah yanasonta
Mutum kamili mai nutsuwa kaman shamsu yanemi auranta bayan duk Abu abuwan datayi abaya
Abba yace duk wannan yawuce alhaji muyi maganar yanzu kawai
Daddy yace duk da bani ubanta jikatace to amma da ubanta da itadin duk mallakinane wallahi naba wa shamsu ita halak malak
Nan sukayi hamdala da godiya
Abba yace idan bazaka damuba tunda ba auran farko bane daga ita harshi shamsun zanso a yanka mana sadaki mubiya
Daddy yace hakane amma naji wannan alamari sosai
Daddyn Ahmad yace tunda hakane ga sadakin nan nabiya wa Dana shamsu
Abba yace a a haba alhaji karmuyi haka daku mana wallahi da komai mukazo
Daddyn Hakeem yace haba ba komai karka daga hankalinka dan yabiyawa danshi sadaki kuma ma ai shamsu Dan mune kana nufin da wani guri yaje Neman auren aimune masu biyamasa sadaki bawai Dan bashidashi ba sai Dan can cantarsa
Hakadai sukata raha abinsu har suka tsaida lokacin aure nan da wata biyu masu zuwa
Abban ya shamsu ya fito da kudi yace tunda anbada nasadaki to ga kudin Nagani inaso
Dakyar daddyn Ahmad yakarba
Da daddare daddy da Hakeem sun gama cin abinci
Daddy yace akwai maganar danakeson nayi daku kaida mummynka
Mummy hafsat tayi murmushi tace to tasamu kenan tunda naji meeting
Daddy yayi murmushi yace sosai kuwa
Nan daddy ya sanar dasu komai
Hakeem yace daddy kar ayi haka wallahi matar shamsu yarinyar kirkice
Aje amina taje tabata musu zaman dasukeyi mai cike da kwanciyar hankali
Daddy yace duk namusu bayanin wannan sai suka nuna min matar ma bata da matsala itama tabada goyan baya kuma tayi alkawarin zama da meenat tsakani da Allah
Hakeem yace aidama itabata da matsala su laila ne damuwata kunsan halinsu
Suje suyita abin kunya mummy tace Gaskiya kam
Kuma gaskiya yarinyar nan kubra bata can canci kishiya ba
Muna zumuncinmi gwanin sha'awa da mutane azo ana raba mana abin kunya
Daddy yace to duk naji baya ninku
Nan yadauki waya yafada wa abbansu husnah komai abban su husnah yace bani Abdul Hakeem din
Abdul Hakeem ya yakarba da ladabi kaman yana gaban abban sun dade suna magana kafin sukayi sallama
Abdul Hakeem yace Allah yasa dai karsu dinga jamana abin kunya a inda ake ganin mutuncinmu
Dadddy yafito da sadakin da kudin Nagani inason yakuma fada musu ranar da suka tsayar
Mummy tace har cikin raina naji dadin wannan Abu sai dai ita aminar akira ajamata kunne sosai tazauna lpy dasu
Hakeem yakira wayar meenat tazo tazauna akasan carpet
Ke yaushe kuka fara soyayya da shamsu
Mummy hafsat ce ta wurgo mata wannan tambayar duk ta gigice tayi shiru kawai
Daddy yayi murmushi yace yanzu dai mamana kinason asake minkafa kenan ko akaro na