maganin ma nasan idan naganta shikenan
Yace show tace show yace OK take care of your self tace I will
Ya fita meenat ta faikace idon husnah ta balla mata harara
Husnah tadago ido ta kalli meenat
Meenat tayi murmushi tace sannu anty na barin kawo miki magani
Meenat tayi saurin barin gurin
Husnah tayi murmushi tace hmmmm
Meenat tadawo tace gashi husnah takarba tace nagode sosai
Meenat tace ba godiya ai yiwa Kaine
Husnah takarba taduba ruwan da kyau taga bai mata ba
Ta ajiye meenat ta ce ya kuma zaki ajiye bayan na kawo miki Dan kisha kisamu lafiya
Husnah tace ai naji ma kan yayi sauki sosai
Meenat tace bangane ba kina nufin bazaki kishaba kenan
aikuwa su madam laila da suby suka taso
Suby tace kedan ubanki karki ba kisha
Husnah tace ubana fa kikace Dan bakisan darajar naki ubanba
Kafin husnah takarasa magana meenat takai mata mari
Tashakota tace kokisha ko wallahi kici. Ubanki
Kafin meenat takai karshen magarta husnah ta wanka mata wani gigitaccen mari
aikuwa Laila da suby suka rufu akanta duka ta kota ina
Kaman sun samu jaka
Tun husnah na Neman taimako har takasa
Laila tadago husnah data Riga ta galabaita ta kaimata naushi aciki
Wani gigitaccen kara Husnah tayi
Tazube kasa sumammiya yayi dai dai da shigowar
Prof da mummy
Next page
Your comments is needed fan's
Love all
ππππππππππ
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU Umulkhairi Mahmoud ina alfahari dake over my sis comment dinki yana kara min kwarin gwiwa keep it up πππππππππππππππππ
πAKWAI LOKACI π
πPAGE 145to 146π
HAKEEM cikin tsananin gigicewa yakaraso falon kasa yayi yana jijjiga husnah amma ina ta sume kuma gajini ya balle
Mummy takaraso tana salati
Ta yarda jakar hanunta ta sumkuya itama gun husnah
Prof cikin tsananin tashin hankali yadaga idonshi da yayi ja jawur da alamu hankalinshi ma yabar jikinshi
Tunda ga kan Laila da meenat da suby Wanda jikinsu ibanda rawa ba abinda yakeyi
Meenat dai fitsari tasaki atsaye Dan tasan yau takade
Hajiya rukayya da hajiya suwaiba suka taso cikin tsananin tashin hankali
Kai meyasa zakuyi haka duk da ita tafara ai baikamata kubiye mata ba
Hajiya rukayya tace duk da yarinyar ce bata dakunya
Cikin tsananin bacin rai Hakeem yadaka wasu hajiya rukayya tsawa
Yace ya isa haka mummy hafsat inbanda kuka ba abinda takeyi tace daukota mutafi asibiti
Muceci rayuwarta karta mutu suci nasara abinda suka aikata
Cak Hakeem yadaga husnah zuwa mota mummy tabi bayansa dasauri suka shiga mota
Megadi yabude musu gate Hakeem yatsaya yacewa baba megadi karyabar kowa yafita daga gidan har sai yadawo
Impact kasa kwado ka kulle gate din
Yana gama bada sallahun
Yaja motar dasauri sai hospital
Suna zuwa akazo da gado za atura ta Hakeem bai saurari gadon nasuba ya sungumeta sai imargency yanashiga likitoci suka bi bayansa danshi sananne ne asanshi sosai
Dakanshi ya ajiyeta a gadon wani daga cikin doctors din ya matso kusa da Hakeem yace
Ya shiga lallaba Hakeem akan yayi hakuri akan yayi hakuri yajirasu anan kar yashiga
Hakeem yace badamuwa amma Dan Allah kuyi iya kokarinku akanta itace farincikin mu daga har iyayena
Likita yace insha Allah zamuyi iya iyawar mu akanta
Hakeem yafito yaga mummy a waiting room cikin tashin hankali tana waya da daddy
Dan dama daddy yatsaya gurin babban aminansa suna ganawa
Mummy tasanar mishi da halin da tasamu gidan yace subahanallah kuna wani hospital din ne tasanar dashi
Hakeem ya kalli mummy yaga duk yadda hankalinta yatashi
Nan ranshi yadada bacci
Baibari mummy tagan shi ba yawuce gidan
Su Hakeem nafita Laila tace shikenan shiga uku aurena yakare
Hajiya rukayya tace rufe minbaki akan wata kina jininshi zai sakeki
Suby tace munshiga uku yau Allah kadai yasan yadda zamu kasance
Cikin kuka meenat tace mummy wallahi da baki daketa a ciki ba
Yanzu idan ta mutu fa kinyi kisan kai fa kenan
Allah kasa kar husnah ta mutu Allah kayafe mana
Allah muntuba
Kafin ta rufe baki Laila ta bige bakinta shegiya idan dukan ne ma aike kikafara
Meenat tace amma aini marinta nayi bazantaba dukanta aciki ba
Yanzu kunsan wani irin hukunci daddy zai yanke mana
Kafin ta rufe baki Sunga anbako kofar cikin tsananin bacin Hakeem yacire belt din jikinshi tundaga kan Laila meenat suby
Yafara tafarsu ihu suke sosai suna bada hakuri amma ina baisaurara musuba
Hajiya rukayya tace Ashe baka da hankali agabanmu kake dukan matar ka da 'yarka da 'yar uwarka akan mace
Hakeem bai saurareta ba
Tunsuna da bakin ihu har suka kasa bude murya hajiya rukayya da hajiya suwaiba sun ga tashin hankali a idonsu ake Neman kashe musu yara
Hajiya rukayya tayi kiran duniyar nan wa daddyn Hakeem amma yaki daga warta
~~
Mummy data ga shiru Hakeem baidawo kawai jikinta yabata yatafi gidan ne tasan irin zuciyarshi idan yabaci ba kyau
Ta kalli daddy da dddyn Ahmad tace yakamata abi Son zai iya yin abinda baidace ba
Daddyn Hakeem yace barshi yadau duk matakin dazai dauka akansu
Yau bazan hanashiba cikin damuwa mummyn Hakeem tace wannan ba dai dai bane daddyn Hakeem zai iya daukar matakin daza azo ana danasani
Daddyn Hakeem yace barshi yadauka koni idan naje abinda zanmusu zaki sha mamaki
Mummy tayi shiru tunda taga daddy yadage tasan ankaishi makura
Daddyn Ahmad yace a a baza ai hakaba alhaji abubakar idan rai yabaci bai kamata hankali ya gushe ba
Daddyn Ahmad yakira Ahmad a waya yace yayi maza yaje gidan Hakeem akwai matsala
Yana gama fadin haka yakashe wayarshi Ahmad cikin sauri yaduki key din motarshi yayi gidan Hakeem
Duka iya duka sunshashi agurin Hakeem yamusu rugu rugu da jikinsu
Ahmad yashigo cikin tashin hankalin abinda yagani
Yayi saurin kama belts din Hakeem yace haba prof wannan aiba girmanka bane dukan mata
Hakeem yace Ahmad kabani belts din nan naci ubansu dakyau kisa suke Neman yimin agida kisan ba akan kowaba sai akan baby
Ahmed yayi salati yace tana ina ita yanzu
Hakeem yace hospital da mummy
Hakeem yadauki wayarshi yakira doctor yace yajikin matarshi
Likita yace munsamu nasaran farfaduwarta amma am sorry to say tasamu miscarriage (wato bari kenan )
Hakeem yace what's wayar hanunshi tafadi kasa tafashe kuwa akasa rugu rugu
Baisan lokacin dayazauna ba Ahmad yace yaya dai mesukace maka
Hakeem yace I lost my unborn baby
Husnah tayi bari asakamakon dokan dasuka mata
Hakeem yadago kanshi yakalli Ahmad yace Ahmad yanzu daba mushigo shikenan haka zasu kashe min husnah itama da narasata kaman yadda narasa cikin dake jikinta ko ? Ahmad yadda yake maganar kadai ya isa yasaka ji tausayinsa
Ahmad cike da tausayin abokinsa yasa hanunshi kan kafadar Hakeem yace kayi hakuri abokina mugodewa Allah dayasa husnah tarayu
Insha Allah
Allah zaiba kuwani masu Albarka
Hakeem yadaga kai yakalli su meenat datake kuka kamar ranta zaifita ga jikinta yayi rudu rudu da dukar mahaifinta suby kuwa ta gudu gurin uwarta tana kuka acan
Laila kuwa tayi shiru ne tana kukan zuci
Kaman daga sama Laila taji Hakeem yace nasakike saki uku kamar yadda aka wa 'yarki
Wani gigitaccen ihu Laila ta fasa
Hajiya rukayya da hajiya suwaiba sukasa salati
Sukace yanzu sakamakon dazaka mana kenan Abdul saboda mace aiko ba aure a tsakaninku kai me rike
Laila ne
Hakeem ya watsa musu wani mugun kallo yace karna dawo nasameku a gidan nan
Yadaga waya yakira DPO na police yace yace yanason yaturo mishi yaransa zasu taho da masu laifi yanzu nan
Dayake DPO amininsane sosai batareda tambaya ba yace OK nan gidanka zasu kenan Hakeem yace a atakaice
Meenat ta rarrafo takama kafan daddynta tace daddy na tuba Dan Allah kayafemin
Wallahi daddy Sharron shaidan ne bazan sakeba daddy kayafemin
Cikin tsawa Hakeem yace sakemin kafa kafin na nakara miki mugun duka yanzun nan
Ahmad yace kayi hakuri karka hadasu da hukuma ai abinsai yai yawa
Hakeem yayi murmushin takaici yace duk abinda zanmusu bazaikai na asarar da suka sa nayiba
Hajiya rukayya sukasa baki suna ta bada hakuri akan karyakira police
Laila kuwa kuka take sosai tana bawa Hakeem hakuri
Yace nayi danasanin sanainki a rayuwata Laila
amma yaudai Allah ya kawamin karshen zamana danadake daga ke har iyayenki mata Allah ya isa tsakanina daku
Laila suna kuka suna rokonshi da yayi hakuri amma ina kokallonsu baiba
Haka sunaji suna gani aka tusa keyarsu zuwa police station
Hajiya rukayya tace Ashe baka da mutunci abdulhakeem harda mu zaka hada ka kulle baka dubi girmanku a matsayinmu na iyayenkaba
Ahmad zaiyi magana Hakeem yadaga mishi hanu
Yace a kwashesu a tafidasu
Suna ji suna gani aka kwashesu zuwa police station
Hajiya suwaiba kawai akabari itama din Ahmad yace a barta
Hajiya suwaiba ta tashi tafita driver din ta yabude mata kofar mota
Tace kawuce dani katsina daman yasaba zuwa dasu gurin bokansu shiyasa tana ce mishi katsina yagane Inda zasu
*****
Husnah sai datayi kwana biyu a hospital kafin ta war ware amma fa ita keda ciwon amma zafin Hakeem ne mejinshi
Dan a can yake kwana mummy ma tare suka zama acan sai dare yayi daddy zaizo sukoma gida
Mummy ta kalli Hakeem tace son yakamata afada wasu ummanta cewan tayi bari ko
Kaga yanzu kosunzo zasuganta da kyau bakaman shekaranjiya ba
Hakeem yace hakane nan yakira wayar ya shamsu yasanar dashi
Ya shamsu ya jajanta sosai kafin yace yanzu baya gida amma zaikoma kida yasanar da umma
Nan sukayi sallama
Mummy ta kalli Husnah dake bacci hankalinta kwance tace Allah yasaka miki abinda suka miki
Duk da ba kekadai abinyataba ba amma aikece kwance gadon asibiti
Mummy tace wai ni inasukayi ne kanon suka gudu ko suna gidan hajiya suwaiba
Hakeem yace suna police station mummy ta dafa kirji tace subhanalla police station kuma Son
ai baikamata ba sai duniya ta zageka
Kafin Hakeem yayi magana sai daddy dake shigowa yace kamin dai dai son Allah yamaka albarka
Inasane da hukuncin daka dauka akansu kuma yayi dai dai
Yanzu haka suma suna nan hospital din
Mummy hafsat tace waye balafiya daddy yace abin badadi
Hajiya suwaiba tayi hatsari a hanyar katsina tun shekaran jiya da abin yafaru
Driver din ta atake ya mutu ikuma aka rasa 'yan uwanta akayi da ita general hospital katsina to anan aketa bincike a gidajen TV dake ina zaune a office nagani shine mukaje muka dauko ta
Babu kafafuwanta ba hanu daya ga wani wari dake fita daga jikinta
Sai yanzu take fada min inda zata wai gidan boka zata takai Abdul Hakeem a tufe bakinsa kar yasake maganar yasaki Laila
Mummy tasaki salati tace idan ba a mutuba za asha kallo aduniya
Yanzu har yanzu matar nan bata rabuda dazancen boka da malamn tsubbu ba
Hakeem yasaukar da ajiyar zuciya yace Allah mungode maka daka nuna musu tun aduniya
Daddy yace wanann kadai ya ishesu ishara idan masu shiryuwane
Daddy yace ganin tanan rai hanun Allah yasa naje nayi Berlin su suzo sugana tanemi gafararsu
Kuma kutashi kuje kuyafe mata
Cikin sanyin jiki Hakeem yakalli husnah dake bacci
Mummy tace muje mudawo kafin ta tashi Allah yarufa asiri
Ahmad yashigo da shida a Aisha da kulan abinci
Mummy tace a a Aisha wato bakya jin magana ko kina fama dakanki nace kihuta da kawo abincin nan kinki ko
Aisha tayi murmushi tace bakomai mummy ai bana jin komai
Mummy tayi murmishi tace to Allah yaraba lafiya 'yar albarka
Nan Ahmad suka gaisa da su daddy
A tare suka je can dakin da aka kwantar da hajiya suwaiba
Suna shiga suka ga ba abinda takeyi sai tonawa kanta asiri tare da cisge cisgen gashi da hanun daya rage mata
Duk Wanda ke dakin kuka yakeyi na wannan abin mamaki da al'jabi
Hakeem yabisu da kallo daya bayan daya yaga tabbas sun ji jiki
Lokacin dayaga meenat zaune gefe tana kuka gashi tayi baki tayi duhu Dan duk da meenat da uwarta take kama amma fa hasken babanta ta kwaso meenat farace sosai ba sarki amma kwana biyun dasukayi a daure yasata koma kaman bata da gata take tausayin 'yarsa yakamashi yayi tur dasu hajiya rukayya dasuka bata mishi tarbiyar gudan jininshi
Zai yafe was meenat amma sai ya tabbatar tagyara halinta tazamo mutum
Bai ankaraba yaji wata kara
Dubawan dazaiyi yaga duk sun rufu akan hajiya suwaiba Wanda rai yayi halinsa
Da razanan nan ihu tacika
aikuwa suka hau koke koke
To jama a yaufa ga karshen hajiya suwaiba nan kungani
Allah yarabamu dason zuciya irin na hajiya suwaiba
Next page
Your comments is needed fans
Love you All ππππ
ππππππππ
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU AGAIN UMMU FARHAN ina alfahari dake wajen nice comments wallahi Allah yabar zumunci keep it up dole nasake Baki kyautar page Dan kin can canta sosai ππππππππππππππππ
πAKWAI LOKACI π
πPAGE to 147 to150π
HUSNAH zaune acikin lambunsu
Kafarta cikin ruwan sweemingfull dinsu
Hakeem yana cikin ruwa yana wanka
Husnah tana watso mishi ruwa
Tana dariya yace niko barin zo kiga wallahi sai kin shigo ruwanan
aikuwa tana jin zai kamota cikin ruwa ta tashi
Tagudu shikuwa tana ganin yafito daga ruwa yabita harzuwa part dinsu
Tagama gudunta yakamata yace wanakama tace natuba Prince
Yace bazanyi hakuriba saikinzo munkoma munyi wankar tare tazaro ido cikin tsoro tace kasan fa inatsoron ruwa
Yace nasani sosanke tsoron yafita a ranki karfin yakai karshen maganarsa wayarsa ta daukara
Yaduba yaga Ahmad ne yayi sallama Ahmad yace albishirin ka
Prof yace goro Ahmad yace kayi 'dafa
Cikin farin ciki Hakeem kai haba yaushe kenan Ahmad yace gamunan mundawo gida ma
Hakeem yace naji dadi wallahi Allah yaramana shida imani
Gamunan zuwa yanzu insha Allah
Nan sukayi sallama ya kashe wayarshi
Husnah ciki murna tace anty Aisha ta haihu ko Hakeem yace a maza kishirya muje muga baby ko
Husnah tace to tare sukayi wanka yashiryata itama tashiryashi
Husnah cikin duguwar Riga maron colour da adon bakin flowers ajiki
Tayi rolling baki mayafi tayi kyau sosai yarintar ta dada fitowa yayi sosai
Hakeem yashirya cikin kananan kaya yasaka bakin wando da T shirt maron colour sun balain karbarsa sosai
Husnah tace gaskiya kayi kyau sosai bana son 'yan mata su kalle min kaifa kasan 'yam matan nan bakunyace ta ishesu ba
Hakeem yayi murmushi yace kedakinga kanki aini Bakomai bane
Shiyasa inzamu fita tare nake kokarin ganin nayi kyau sosai Dan kar mutane su dauka driver dinki
Husnah tayi murmushi dimple ta yalotsa sosai Hakeem yasa hanun yace yauwa kingani ko
Banyarda idan munje kiyi murmushi ba saboda karkowa ya kallemin wannan two beautiful point dina
Yanuna dimple dinta
Husnah tayi murmushi tace ai sai idan magana ne bazanyi tunda duk yadda bakina yamutsa sai shima ya lotsa
Hakeem yace zan nanesu kuwa idan yazama daga nisai ke saina daye
Husnah tayi murmushi tace wallahi sweet idan nabiye naka baza mutafi ba fa
Yace gaskiya kigoge jambakin nan
Saboda yamiki kyau sosai
Husnah cikin shagwaba tace haba sweet kaga fa jambakin kalan kayanane maroon kuma dankai nasaka
Yace mai wayo kawai mutafi amma kirage murmushi
Atare suka shiga part din mummy hanun su a hade da juna
Wacce suka gani zaune kan carpet din mummy
Da alamu mummy fada take mata ga akwatin kayanta nan da alama dai yanzu tazo
Meenat kenan tana ganin shigowar daddyn ta
Ta tashi taje ta tsuguna gabanshi tana kuka tace daddy Dan Allah kayafemin bazan sakeba
Natuba da zuciya daya daddy Hakeem tsaki yayi
Ya karasa gurin mummy Husnah har cikin ranta bata ji dadin abinda yafaru ba
Ga mamakinta meenat ta rike rigarta tace Dan Allah asmau kiyi hakuri kiyafemin wallahi nayi nadamar abinda yafaru bazan sake kwatan tawaba da izinin Allah
Husnah tayi saurin sa hanu takamo hanun meenat dake kuka kaman ranta zaifita tace Dan Allah meenat karkisake tsuguna min wallahi na Dade da yafe miki tun tuni daman ina rokon Allah yakawo lokacin dazaki fahimci gaskiya
Kuma gashi Allah yanufa nayafe miki duniya da lahira my besty na
Nima kiyafe min idan nabata miki rai
Meenat tayi murmushin jin dadin yafiyar data samu daga aminiyarta
Tace wallahi baki min komai ba anty na nasan kuma bazakitaba min badai dai ba saboda nasan kyakkyawar zuciyarki fari tas
Husnah tayi murmushi tace nagode da kwarai da yabonki agareni
Husnah taja hanunta sukayi falon mummy tace gaskiya husnah kina da kyakkyawar zuciya Allah yamiki albarka yasa kamiki dagidan aljanna
Hakeem yace ameen
Hakeem yafada wa mummy haihuwar Aisha mummy tace kai amma naji Allah mungode maka
Me aka samu yasanar da ita
Tayi musu addua
Tace zuwa gobe nasa driver yakaini Hakeem yace kitaso muje kawai mummy
Mummy tace a a kudaiyi tafiyarku nisai Allah yakaimu gobe
Nan sukayi sallamawa mummy husnah ta kalli meenat ta mata rada akunne meenat to Allah yadawo daku lafiya
Ta kalli daddynta tace daddy saika dawo
Bai amsa ba yayi waje abinshi sukatafi
Mummy tadawo da kallonta kan meenat tace nifa bazan iya zama dakeba karkizo nima kikwace min nawa mijin king a Dan santalelen gaye
aikuwa meenat tafashe da dariya tace lalle ma tsohuwar nan wayafada miki daman mijin nakine kekadai
Meguri yazo sai maitaburma yanade ta tashi tadauki jakar kayanta tayi dashi wani daki Wanda ba abinda babu aciki nan tagyara a matsayin dakinta
****
Ranar sunar Aisha yaro yaci sunan baban Ahmad sai suka samishi sameer
Komai na suna Prof ne yayi ba abinda yabari Ahmad yayi
Su anty kubra ma tazo inda take rike da yaron kubra bata taba jin tanason haihuwaba irin na yau tayi matuka Sha'awar haihuwa
Husnah takatse mata shirun anty muma Allah yasa shekara mezuwa kihaifomana baby kaman wannan mekyau
Kubra tayi murmushi tace Allah yakarbi bakinki 'yar kanwata
Aisha dake jinsu tace dake ma ai husnah
Husnah tayi murmushi tace ai idan naga Dan ya shamsu kaman naga nawane
Kuma ma aini bana ma son na haihu nan kusa harsai mungama karatun mu dazamufara kwanan nan
Kubra ta kalli husnah tace idan Allah yabaki saikice bakyaso tunda baki da wayo mijinki nason haihuwa kice saikingama school ko
To karma kifada yaji Dan zakusamu sabani Dan kiji nafada miki
Husnah ta turo bakin shagwaba tace wallahi kubra nifa haihuwarce tsoronta nakeji
Aisha tace karkiji tsoron haihuwa Dan da alama saikin dire wa Prof shabiyu
Husnah tazaro ido ta shafa cikinta tace wa ni cab wallahi bazan iyaba
Yanayin yadda tayi maganar cike da wauta taba anty kubra da anty Aisha mejego dariya
Meenat tashigo dakin cikin sallama tace anty nazo kiga zainab ismail
Wacce take zama abayan desk dinmu
.husnah tafasheda ihu tace Dan Allah meenat itama cikin murna tace wallahi amma fa banmata maganaba kuma da alamu itama sunan tazo
aikuwa da gudu suka kwasa zuwa waje
Anty kubra tayi murmushi tace rayuwa kenan wazaiyi tunanin zasu dawo kamar da
Anty Aisha tace gaskiya fa husnah mutumce Allah dai yadada karesu daga sharrin shaidan
******
Bayan shekara biyu husnah da prof soyayya sosai suke zubawa kasar London yau kusan shekarar su daya da rabi kenan acan
Wani kwangila yakai Hakeem can sosai yake kula da husnah
Bata taba Neman wani Abu tarasaba
Kaman yadda shima bata gajiya da bukatunsa Dan zata iya cewa Prince din mabukaci sosai Dan baya daga mata kafa
Tana kokarin jurewa hakan ganin ta faranta mishi rai
Ayayinda shikuma prof baisan yanada wannan feelings din daya waba sai akan husnah Wanda yake jinbazai iya rayuwa batareda itaba
Kamar kullum husnah cikin wasu kana nan kaya Dan prof dinta baya gajiya da kallonta cikin su
Shiyasa duk inda yaga masu kyau Wanda suka burgeshi zai sai mata
Tayi wankanta cikin wani Dan karamin skirt baikai tsayin gwaiyarta ba ma sai wani hadadden half vest wanda shima yatsa dai dai breast dinta
Cikinta zuwa cibi duk awaje suke
Gawani kamshi mai dai dake fitowa daga jikinta Wanda dama yariga Yakama jikinta sosai kullum cikin kamshi take
Ga gyaran gashinta Dada yawa yake
Tana zaune tanacin gurgurunta Wanda take so sosai
Bataji shigowar shiba saidai jin hanunshi cikin kirjinta tayi aikuwa ta tashi a firigice zatayi ihu suka hada ido
aiku wa husnah tashagwabe fuska tace wallahi bazan yarda ba saina rama aikuwa haka suka ringa zagaye falonsu
Wai ita saita kamashi shikuwa Hakeem yaki tsayawa takamashi
Dakanta tagaji tafada kan kujera tana kukan shagwaba Wanda prof yana balain son shagwabarta yana kara sonta karuwa cikin zuciryasa
akanta ya kwanta yahade bakinsu guri daya sai yayi kissing dinta son ranshi kafin yasaketa yace matsorociya
Yakai kansa kan cikinta tace yadai yace inagaisawa da baby nane husnah tayi murmushi tace wani babyn dabaicika 1 months ba har kafara gaisawadashi
Prof yace ai kece bakisaniba run randa mukaje hospital aka min albishir da cikin dake jikinki
Kullum kina bacci sai munyi hirada baby
Kinsan wani Abu kuwa mummy fa bakaramin shirin zuwan jikanta takeba hakama daddy
Husnah tayi murmushi tace nidai banason cikina yakai na Anty Aisha wallahi har tausayi takebani
Hakeem yace ainaki sai yafinata saboda ke komai kikagani zakici acici kawai please baby kihaifo min yan biyar mana husnah tace ninafison na haifo guda Dari dai
Hakeem yafashe da dariya yace kefa in anbarki wai bakar magana kika fada minko tayi dariya tace sosai kuwa
******
Satin su husnah biyu da dawowa gida
Suna zaune itada meenat afalon mummy Dan yanzu komai tare sukeyi
Mummy tafito daga kitchen dinta tamiko wa husnah kwano ga dashishin naki
Husnah tayi murmushi tace yauwa mummyna Allah yakara miki lafiya
Mummy tayi murmushi tace amin 'yata kema Allah yasaukeki lafiya
Husnah tayi shiru
Meenat tayi murmushi tace wallahi Granny ta ce amin aranta
Husnah ta galla wa meenat harara
Tana murmushi
Mummy tace a din ta amsa din
Mummy ta haura sama tace kigama ci kisha maganinki
Meenat tafashe da dariya tace anzo gun wallahi shan magani
Husnah tace wallahi maganin ba dadi
Dariya kike minko zan rama ai zakiyi auran kema
Nan danan fuskar meenat yacanja tace Dan Allah anty na kidai na min maganar aure
Dan nasan Wanda nakeso bazan taba samunshi ba
Husnah cikin tashin hankali tace nayi nayi kifada min Wanda kikeso kinki
Natambayeki ko uncle bash din kikeso kince Allah yasauwake
Ke kincireshi a ranki baya ranki a yanzu
Towa kikeso kifada min Dan Allah
Meenat tadaga kai ta kalli husnah fuskarta cike da hawaye
Next page
Your comment is needed fans
Love you all
πππππππππ
[05/05, 10:19 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY HUSBAND MR SULAIMAN ALLAH YABAR KAUNA TSAKANIN MU YA YARAMANA LOVELY KID'S DINMUβ€β€β€β€β€β€β€ππππππ much love to you
πAKWAI LOKACI π
πPAGE 151 to 152π
MEENAT tayi murmushi tace bazan iyafada mikiba
Dan nasan kona fada miki bashida amfani bazan taba samunshiba
Takarasa maganar tana kuka
Husnah tace haba meenat yanzu akwai abinda zai dameki kice bazaki fada minba saboda me
Meenat tace zanfada idan har naci nasarar cireshi daga cikin ratuwata
Husnah tayi murmushi tace kenan sonda kika nunawa uncle bash basone bane
Meenat