wani Dan akwati ta gani yamata kyau sosai
Garin ta gyara mashi zama sai yafafo kayan ciki cuka zubo
Ba abinda tafara gani sai fuska(masks)/kuma da ya mu'alim yake kama sak abin har yaso yabata tsoro zata gudu idonta yakai kan nokia yarsa wacce tasha dauri da roba
Cikin tsananin mamaki husnah tace badai ya Hakeem shine ya mua'allim dina bansaniba
To meye hujarsa na boye kansa
Tasake bincika kayan taga zoben data bashi Wanda sukayi canji yabata tabashi
Nan tasake tabbatarwa kanta ya Hakeem shine ya mu'allim
Taga wani diary kamar yadda taga anrubuta a bayan littafin
Nan ta hau karanta abinda ke rubuce
Nan ta tababbatar Abdul Hakeem shine ya mu'allim dinta
Kukan dadi suka gangaro mata
Sosai tayi kuka ammafa na murna ne
Tace meyasa zaka cutar da kanka har haka meyasa baka fada minba kabari har na dauki alhakinka ya mua'llim
amma bakomai insha Allahu zakasan kayi auren soyayya
Ya Allah ka karemin mijina Daga sharrin wadan nan mutanen tabas a labarin dake rubuce cikin diary dinshi mummy hafsat da daddynsa sunbata tausayi
Dole ya mua'llim yayi taka tsan tsan gurin sake Neman matar
Baka da laifi kuma na tabbatar kosu umma da ya shamsu bazasu zargekaba idan sukaji Kaine ya mua'llim kuma suka ji dalilinka
Wani irin son mijinta yadawo sabo fil azuciyarta tareda tausayinsa Dana iyayensa tashare hawayenta tashiga yin abinda yakawota cikin farinciki da dokin dawowar mijinta
Acikin mitoci kadan daki yakoma kaman bashiba kafin tashiga bathroom dinsa ta wanke mishi kayansa tsaf da kananun kayansa na ciki
Taje farandar saman shi ta shanyasu tsaf tasaka abin kamawa ta kamasu karsu fadi kasa
Tagyara bathroom dim ma tasaka kayan kamshi koina ya San anayi
Kafin kuma ta koma falon tagyara tsaf yadawo kaman bashi ba sai sanyayyar kamshin dake tashi akowani lungu da sako na falon
Sai da ta tabbatar ba inda bata gyara ba kafin tafito key din dake jikin kofar tacire ta cire ta kullo saman abinta
Ta wuce da keyn har yanzu su Laila suna inda tabarsu
Zata shige dakinta hajiya rukayya tace ke zonan yanzu agidanku haka kikewa manyanki
Husnah tadago ido takallesu
Batayi magana ba tayi shiru Dan taga ba abokan yinta bane
Suby tace ke 'yar marasa kunya ba magana akemikiba
Husnah ta kalle suby sama da kasa tace kekuma fa 'yar masu kunya ya akayi
Laila tace kutuman uba lalle yarinyar nan ma kinsamu guri
Uban me yakaiki saman dakin mijina
Husnah ta tashi tsaye ta kalli Laila sama da kasa tayi dariya
Tace ai gwamma da kika nuna min kece matar gidan Dan gaskiya na kasa tan tancewa acikin Ku hudun nan
amma yanzu kinga nasani
Maganar miji kuma point of correction mujimmu zakice please kina saka munjaye idan zaki furta kallma kamar haka
Kafin ta kalli suby ta banka mata harara tace kekuma 'yar cin arziki banda lokacinki
Tabuga tsaki tashige part dinta ta banko kofar
Cikin tsananin tashin hankali Laila tace me yΓ rinyar nan take nufi da wai bata San matargidan acikin muhuduba
Hajiya rukayya cikin takai ci
Tace abinda kunnenku yabiya muku shitake nufi harda mukenan namuke nan ai mu hudu
Suby ta yashi tana haki tayi kofar husnah tashiga bugawa da karfi
Tace kifito Dan ubanki kiga yadda ake rashin kunya karamar 'yar iska yar talakawa kawai shasha
Ita kuwa husnah ko jima batayi ba saboda tana bathroom tashiga wanka
Hajiya suwaiba da tsufa yakamata sosai tace kai kai kedawo nan bakuda hankali ko
Duk abinda kuka mata za ace mu ne muka saku
Kuma kunga zasugane ba tuban Allah mukayiba
Abinda nakeso daku kibari sai randa bama nan bamuzo ba sai Ku hadu kumata shegen duka dakanta zata gudu
Kunga idan mukazo sai murufeku da fada sosai akan abinda kukayi Baku kyauta ba
Hajiya rukayya tayi murmushi tace kai hajiyata Ashe haryanzu da sauranki a tunani kuma wallahi wannan shawarar tayi dari basa Dari
Suby tace ai gaskiya idan nakama yarinyar nan saina fasa mata baki wallahi wai nice 'yar cin arziki
Nan dai sukata gulmacensu
Husnah kuwa wanna tafesa cikin wani tsadaddan material Wanda ummanta ta kawo mata Daga Sudan
Ya hadu iya haduwa gashi dinkin ya kwanta ajikinta Daga tundaga samanta a matse yake
Sai Daga kasan gwaiwarta aka sake irin dai dinkin amare idan zasu dinner
Ta gyara gashinta cikin mayuka masu kamshi da dadawa
Tasaka ribbon tadauki sarka ta metsada tasaka
Rabin kirjinta awaje suke amma cikin net Wanda akayi ado dashi har wuyanta Wanda akecewa high neck
Sai da tagama komai tay sallar magriba Dan taji anata kira
Ta dauki tiren abinsu tayi waje saida ajiye akasa tasaka ta kullo sashinta kafin tayi saman mijnta
Dining din saman tajera komai cikin wayewa da Jan hankalin mecin abincin
Kafin ta dauko remote din TV kunna ta dauko tasaka tashar sunna TV
Kafin ta fito bayan ta kullo kofar da key guri tasamu itama zauna a falon ganin ta zauna yasa duk suka dawo da kallonsu kanta
Itakuwa husnah bata San Allah yayi ruwan tsiransu ba
Tadauki wayarta tana watspp tashiga group din mutuniyarta wacce tazama mata kamar roll model dinta wato ummu afan
Wani littafi ake turowa maisuna 'YAN BIYU NE kuma husnah tana bin novel din daki daki
Tana balain son NANA DA SAMHA jarumar cikin novel dinne
Gaskiya itadai zata iyacewa novel biyune sukamata a rayuwarta Daga 'YAN BIYU NE
Sai kuma 'YAR MAKARANTA wacce ficacciyar marubuciyar nan ta rubutashi wato UMMY KHALEEL
Gaskiya mutanen biyu tana matukar alfahari da littafinsu
Tana ta karatunta na novel dinta inda Nana tama Hussain karyan rashin sallah
Sai kawai taga ankarbi wayar an rada da kasa
Husnah tabi wayar da kallo kafin ta kalli wacce ta karba wayar
Laila ce tsaye tana karkada jiki tace nafasa kozaki yi magana nane
Husnah tayi murmushi tace kodaya abinda baninasayaba
Wanda yasai wannan shizaisaje sayan wani kinga kuwa ai basai nayi magana bako
Laila tayi tsaki saiya saya mugani ai wallahi bai isa yasai miki waya a gidan nan ba saidai kizauna haka ba wayar
Husnah tace to Allah yakawo sauki
Kafin Laila tace wani abu prof yayi sallama yashigo
Idonshi direct kan babynsa suka sauka itakuwa Husnah ta shi tayi cikin tafiyanta mai kara rikitashi
Ta isa gurin prof ta fada kirjinshi
Cikin tsananin mamki Prof ya ajiye jakar hanunshi shima ya rungumeta da kyau yana ajiyar zuciya
Husnah tadago kai tace sannu da dawowa
Kasa amsawa yayi saboda mamakin Husnah
Itakuwa husnah ganin haka yasa ta sunkuya tadauki brief case Dan daya yar takama hanunshi shikuwa prof binta kawai yake harzasu haura sama husnah tace sweet baka gaidasu hajiya ba
Har ga Allah prof bema san da mutane a falonba
Laila datayi suman tsaye baki kawai tasake da ido tana kallon ikon Allah
Hakeem yayi murmushi yakalli su hajiya suwaiba da hajiya rukayya ya ce sannunku hajiya hankalina yayi gaba bangankuba Sam
Hajiya rukayya tace inazaka ganmu
ai hankalin ka baya taredakai
Nan ya gaishe su kaman karsu amsa amma dai gudun tuhuma yasa suka amsa mishi
Suby tsabar haushi ko gaishe shi batayiba bare uwar gayya datakasa magana
Kota Kansu baiyiba yajuya zai haura sama saiyaga wayar Husnah a tarwatse akasa
Yace garin yaya kuma wayarta yafashe
Caraf hajiya rukayya tayi tace ai da gangan tafasashi munata mata magana tace ai tagaji dashi tana ce Kasai mata wata zaka saya
Shine fa Laila ta mata magana akan abinda tayi fa almubazzaranci ne shine fa tahau zagin Laila
Laila zatayi magana nace tabarta yarinya ce ai
Tana gama was Hakeem wannan bayani
Yayi murmushi yace oh baby rigima aidata fada ma da nataho matadashi
amma bakomai barin ci abinci nayi wanka saimuje nasaya mata wani
Ya kalli Laila yace kekuma data zaga kiyi hakuri kamar yadda hajiya tabaki hakuri Dan yarinyace
Ya kalli suby yace ke tashi kigyara wajen data fasawayar
Yayi haura sama abinshi Dan tunda yatsaya gaisuwa husnah tashige da brief case dinsa
Yana shiga falomshi nasama yaji wani sassanyar kamshi mai ratsa zuciya
Tabbas yasan aikin husnah ce wannan Dan tunda aka zuba kujerun falon nan yana jinma ba ataba share waba duk da ba azama sosai amma ai yana bukatar gyara
Yana shiga bedroom nan ma mamaki yakasheshi ganin yadda komai tas
Ya kalli koina fes
Husnah tafito Daga bathroom din shi tanufo shi tashiga cire mishi takallmimsa da cire mishi bottle din suit dinshi
Har neck tied ita tacire mishi
Shidai Abdul mamakinta yakeyi kuma yakasa magana saida yarage saura farin naciki da wandon suit din
Ta kwashe Sauaran ta ajiyesu Indayakamata
Kafin tace kashiga wanka kafito kacin abinci
Tana fadar haka tayi hanyar kofa
Hakeem yayi wuf yakamota
Suna fuskantar juna ya kureta da ido takam takasa kallonshi
Yakai bakinshi kun nan ta yace thanks my wife
Husnah dai kanta a kasa yazaunar da ita bakin gado yace bana son kitashi kijirani harsai na fito OK
Husnah tadaga kai
Ya sumbaceta kafin yashige bathroom
Husnah tana dubawa kan side bed taga phone dinshi
Tadauka tahaye gadon tana kallon hotuna duk yawancin hotunan natane abin ya matukar bata mamaki yaushe yasamu wadan nan hutunan Dan itadai bata san lokacin daakayisuba
Ganin hotunan meenat taredashi ranar graduation dinsu
Abin yamatukar bata mamaki
Kardai AMINA ABDUL HAKEEM itace 'yar shi
Caf ai idan haka ta kasance zanji dadi duk wani masoyina dole yaji min dadin wannan Abu
Tana ta murmushi itakadai har prof yafito Daga wanka yaga tana kallon wayar tana dariya koba fada mishiba hotuna take kallo
Karasowa da ruwan jikinshi ya hauro gadon ya kwanto da ita akan kirjinshi
Yace meyabaki dariya baby
Tace bakomai
Ta budo hoton amina tace wannan fa kasantane
Yayi murmushi yace kice kinga kawarki ko
Maganar taba husnah mamaki daman yasan amina kawarta ce
Husnah tace muna dai gaisawa amma bakawata bace
Sai ta wayance tace kasanta ne
Yace 'yarkice she is my daughter
Tana aure a kano sunyi tafiya da mijinta
Zakiganta wataran ,ita kadai Allah yabani
Kidage nan da nine months kibani baby kaman ke
Husnah ta boye fuska
Ta yi saurincewa muje kaci abinci
Hakeem yashirya cikin farar jallabiya
Kafin yaja hanunta sukayi dining
Sosai yaci abinci amma fa saida yatabbatar takoshi kafin yafara nashi
Tundaga kan dining din wasa yafara canja salo
Cak yadauketa zuwa bedroom Daga nan kuma sukayi bathroom Dan yin alwala
Hummm
Next page
Your comment is needed fans
Love you allπππ€²ππβ€
[05/05, 8:59 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU sis Fatima Umar ina alfahari dake wajen comments mai Allah yabar zumunciππ (π
πAKWAI LOKACIπ
πPAGE to116 to 120π
DUK wani taimako da uwa yakamata ta wa 'yarta mummy tama Husnah
Ta hada mata hadaddan tea maikauri da farfesun kayan ciki
Yasha kayan sirrin na mata
Ta lura husnah kunyarta take sosai
Sai ta wayance
Tace ai zazzabi ba dadi husnah bama saimunje asibitiba
Zazzabin nan nayanzu ai sai a hankali
Sannu kinji
Ganin kaman mummy bata gane ba yasata saki jikinta taci abincinta
Tasake komawa bacci a gadon mummy
Ranar dai Husnah taga tattali da gata
Kuma alhamdullila gaskiya taji dadin jikin sosai
Mummy taki tabarta tafito ma ko falo
Laila kuwa tana farfadowa tafara kuka jikin hajiya rukayya
Tana shiga uku hajiya shikenan sun rabani da Abdul
Hajiiya rukayya tace audama sabodashi kike kuka asararrariya
Ni ma dauka saboda dukiyarsa kike kukar wani so ana zaune kalau
Nan sukayita mata fanfo
Hakeem zaune a office sai Ahmad yace amma gaskiya natayaka murna wallahi
Dasamun kan madam yanzu zaka bani labarin yadda zama da mata biyu yake konima zansamu nakara
Hakeem yayi murmushi yace baka da hankali kai kuma wani aure zakayi sha'awar yi
Ahmad yace wallahi ba abun da Aisha ta rageni dashi kawai dai sunna nakeson cikawa
Hakeem yace tonidai baruwana
Nan Hakeem yadauki wayarshi yakira mummy yace mata yajikin Husnah tace
Bansaniba marakunya
Hakeem yayi murmushi yace haba daliba toshikenan ina babyn
Mummy tayi murmushi tace tana bayana
Hakeem sosai yayi dariya Dan yasan mummyn shi da caka magana
Mummy takashe wayarta
Ahmad yace waye balafiya
Hakeem yayi dariya yace Husnah
Yana murmushi ya lumshe ido kawai
Ahmad yace wallahi young Prof kabimusu 'ya a hankali fa she is very young fa
Hakeem yabude idonshi tar yace innan bita a hankali ai bazata saba da mijinta ba kullum tsorona zataji
amma intariga ta saba she is always welcome me
Ahmad yace lalle ma mutumin nan
Allah yataimaki 'yar mutane daba ita kadaibace
aida ka karar musu da yarinya
Hakeem yayi murmushi yace bazaka fahimta bane
Nifa Allah Allah nake ma daddy sugama ganawar nan da shugaban kasa yazo mutafi gida
Ahmad yace taresuke da daddyna ko
Hakeem a suna tare Ahmad yace OK nima barinjirashi kawai muwuce tare
Ahmad yace wallahi kabar yarinya nan nayau dai karka koma Hakeem yayi murmushi yace caf
ai hakan ma ba zai yiwuba
Tashi muje karani nasiya mata waya
Nata ya fashe
MEENAT kwance kan bed dinta suna waya da antynta suby tana ta bata labarin abinda kefaruwa da uwarta
Meenat ta fashe da kuka tace meyasa daddy zai ma mummy haka duk da dadewar dasukayi tare saboda yayi are shine zai wulakanta ta
Suby tace kedai bari kawai ai daddynki ya canja hali sosai
Kuma duk ba laifinsabane akan wannan 'yar figigiyar yarinyar da yakawo ne
Kokefa zaki girmi yarinyar nan
Meenat tace nashiga uku wallahi nazo gidan nan saidai daddy yazaba ko mu ko shegiyar yarinyar
Suby tace gaskiya dai kam tunda ke 'yarsa sace ai watakila yaji maganarki tunda ai duk haukarshi bazai zabi mata yabar 'yaba
Meenat tace munkusa da wowa muna sauka a kano zanyi Kaduna inzo karuwar da ake wa mummyna wulakanci saboda ita
Bayan sunkashe wayar ne
Meenat tacigaba da kukanta
Ita abin ma yamata yawa ga wulakancin da bashir yakemata
Dan idan baidaketa sau biyu to zaikai uku kullum
Baya cin abincinta baya hira da ita
Inya zauna bashida magana saina Asmau Asmau
Tana cikin tunaninta bash yashigo
Yana ganinta yadauko ruwa mai tsananin sanyi a fridge ya kwarama ta tashi ra wan jiki
Tace Dan Allah uncle menamaka ka tsanani haka auren soyayya mukayifa bana kiyayya ba
Bash yamata wani matsaya cin kallo yace wallahi bansan ya akayi har nawa masoyita wulakanci saboda jaka irinki ba wallahi
Ke wai dan uwarki ma ya akayi har naji banason ganin kowa saike ne har na aureki na bar asmau
Meenat ta yi tsilli tsilli da ido
Yace ba magana nake mikiba bazaki ban amsaba yashakota idon meenat yafito tace wallahi ba abinda namaka
Bash yasaketa yace wallahi duk ranar da na tabbatar da abinda nake zargi tattare dake zanbaki mamaki
Mutum daya nakejin kunya shine babanki
Mutumin kirkine
Da Dan uwarkice da kakanki da na Dade da kada ki gida wallahi
amma yanzu zanmiki uziri har na tabbatar da zargina akanki tukun
Maganar auren da babban ki yayi audole yayi aure indai mata irin uwarkice saikace akuya namaga kokarinsa da ya iya hada jini da dabbar matar
Cikin tsawa meenat tace ya isheka haka bashir kamin komai amma karkasa uwata aciki
Kafin ta rufe baki bashir yakai mata duka abakin fas
Aikuwa ta kwalla kara saboda azaba
Yace kuma kifara hada duk wani tsummo karanki
Sati maizuwa zamu koma gida
Yasa kai yafita abinshi
Sosai amina take kuka ba mai rarrashinta
Dadin data jima sati maizuwa zasu bar kasar
Zataje takakkarya wacce tayi kasadar zama kishiyar uwarta
***
Hakeem da daddy sukayi sallama suka shigo
Mummy da Husnah suna hira a falon
Husnah tagaida daddy ya amsa cike da kulawa
Tareda mata yajikin Hakeem kuwa kureta yayi da kallo Dan sake canja mishi tayi wuni daya kawai
Husnah kuwa tana gaida Hakeem tayi sama dakin mummy abinta
Tana shiga bedroom din mummy tafada kan bed abinta
Hakeem kuwa suna gama cin abinci yaki tafiya har daddy ya haura sama
Yazama daga shi asai mummy hafsat mumme tace wai bazaka je ka kwanta bane
Hakeem yasosa keya yace mummy tafito mutafi mana
Mummy ta harareshi tace da tare kuka shigo
Tariga tayi bacci katafi kawai abinka
Hakeem zaiyi magana mummy tace kaga nikam saida safe indan kafita kaja min kofa
Hakeem badan yasoba yaja kafarsa yayi part do shi
Yana shiga ya tarrar da suby da Laila sunkasa sun tsare
Dama abinka da wanda yake wuya
Yanashiga yafara musu masifa
Yace waiku bakuda falo ne kullum kuna falona saboda tsaban fituna ko
Laila tace au dama akwai inda aka mana iyaka dashi ne agidan
Ya kalleta ya balla mata harara
Ya haura sama
Suby ta kalli Antin tata tace yaufa abin ya motsa miskilancin
Laila ta tabe baki
Hakeem bayan yagama shirin kwanciya
Ba abinda yake tunanin husnah
Da irin farin cikin dayasamu tattare da ita
Wayar da yasiyo mata yadauka yacire yasama a acaji Dan yacika wayace metsadar gaske
****
Washagari da daddare karfe takwas na dare bayan sungama ma dinner
Mummy ta haura sama gurin husnah tace
Tace kinkunta ne husnah tace a mummy
Mummy tace Allah yatashe mu lafiya kafin husnah ta amsa wayar mummy yayi kara taduba taga Hakeem
Nan dai mummy tayi murmushi bayan sungama wayar ta kalli husnah tace kije mijinki na kiranki wai yasayo miki waya
Husnah gabanta yafadi ras tace mummy yabari gobe zankarba
Mummy tace kedai jekikarbo kidawo kiyi kwanciyarki
Husnah tace to mummy tafita zuwa falon mummy baya falo ta wuce sashinsu Dan tasan yanacan
Tana shiga taga su Laila da suby suna kallon Hausa film
Tace sannunku
Duk suka kalleta suka buga mata tsaki
Husnah bata bitakansu ba ta huce zuwa saman gurin kiran mijinta
Suby tace anty yau bakwanankibane naga wannan 'yar talakawar ta haura
Laila tace kwarai kuwa barinje naga ikon Allah
Husnah tana shiga bedroom din taganshi kwance daga shi gajerar wondo
Yana danna waya ganin shigowarta ya kura wa mata ido itadai bata son suhada ido
Tanemi gefe ta zauna tace gani yaya
Yatashi ya ajiye wayar agefe
Yakamota yace wai guduna name kikeyi ne baby
Husnah tayi shiru yace bazaki magana ba ko
Kafin husnah dake kwance kan kirjin Hakeem tayi magana Laila tashigo dakin ko sallama babu
Hakeem yace o my GOD wai yaushe zakiyi hankali ne
Laila bance karkisake shigo min daki a wannan lokacin ba
Laila tace taya za ayi nayi tunanin yin sallama bayan kana kokarin cin amanata
Hakeem kalleta yace kamanya cin amanarki dawata kika kamani koda matata
Tace duk da matarka ce ai yakamata kasan yau kwanana ne
Yace OK dama abin kenan
Saikije kifara kirgawa daganan zuwa 5 day's saikufara raba kwana Dan ita yanzu take amarya Kinga kuwa sai ta min 7 day's kafin kufara raba kwanan
So fita kiban waje ganin da gaske yakeyi
Ta juya hade da banka wa wa husnah harara
Ta banko kofar tayi waje
Hakeem yabita da kallon takaici
Ya dawo kan husnah yace nadawo kanki kekuma meyasa jiya kika gudu dakin mummy
Husnah tace nima fa gigin baccine bani najeba
Hakeem yayi murmushi yace ko
Tadaga kai sama ya dauko wayarta da yasayi mata yabata cikin nuna jin dadi da wannan kyautar da yayi mata tace Allah yakara budi
Bata gama godiyar ba ya hade bakinsu guri daya yashiga sarrafata
Duk yabi yagigitata da salon soyayyarsa kafin yatashi yaje yasamusu key a can kofar falon
Yauma fa basauki husnah takwashi kashinta a hanu saidai da sauki zafin bakan nafarko ba
Sosai tasha tattali itakuma sai shagwaba take zabawa son ranta
Da asuba bayan yadawo daga sallar asuba sunyi karatun alkur'ni maigirma
Yajata kan bed yace baby kinbani komai arayuwata ba abinda zance saidai Allah yabar minke mutukaraba
Yadauko wasu files da takardu acikin yace karba wanna tace nameye wannan
Yace tukwicin first night dinki ne
Tabude taga takardun company ne da takardun gidaje guda biyu
Saikuma mukullin motoci guda biyu
Sai kuma kufi a account har Naira million goma
Husnah ta tashi daga kwanciyar datake
Ta ajiye mishi takardun tace haba yayana ta durkusa agabanshi tasa hannayenta kan laps dinshi tace karkamin haka hakkin ka nefa danme kenanma kabiyani karkasa Allah yayi fishi dani fa
Kuma ma wallahi abubuwan nan sunyi yawa sungirmi tunanina
aikosu mummy ma saisuma fada Dan naga kaman kayi almubazzaranci da dukiyarka
Hakeem baki kawai yasake yana kallonta tabbas Allah yabashi matar da iyayensa suke mishi fata
Ya kamota yadawo da ita yace baby kinsan wani Abu da izinin daddy da mummy na miki wanna kyautar shima daddy yabaki filayensa guda biyu dake abuja
Mummy kuma tasaya miki zinare duk kuma sunabani nabaki aibaki gama kallon kayan ba tukunnan
Husnah takai dubanta kan sauran dayake nuna mata
Cike da tsnanin son mijinta ta ta kwanta ajikinshi
Tace Allah nagode maka daka hadani da mummy da daddy amatsayin iyayen mijina sunasona tamkar susuka haifeni
Sanna kuma Allah yabani masoyina alokacin danake tunanin na rasashi
Allah na gode maka da kabani ya mu'allim dina a matsayin miji
Dasauri Hakeem yadago da fuskarta suka kalli juna tace kayi mamaki ko
Next page
Your comment is needed fans
Love all
ππππππ
[05/05, 8:59 PM] UMMU AFAN πΉ: πππππππππππππππ
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
πππππππ
πΉFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATIONπΉ
πΉπΉ (F.C.T.W.A)πΉπΉ
πΉHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATIONπΉ
πI DEDICATE THIS PAGE TO YOU HUSNAH ina matukar alfahari dake Allah yabar zumunci
Kicigaba da comments dinki mezafin nan πΊπΉπ
πAKWAI LOKACIπ
πPAGE 111 to 115π
Suna idar da sallah bayan yayi adduoin da yakamata miji yayi akan matarsa
Cak yadauketa sai kan bed bayan yacire mata hijabin
Ganitayi ya bude wani Dan karamin akwati shima maishegen kyau yadauko wasu sleeping dress masu kyau da tsada kamshi ne kawai yake tashi ajikinsu
Ya matso dai dai kun nanta yamata rada komai yafada mata oho
Gani nayi kawai husnah ta ce a a zansa da kaina
Murmushi Hakeem yayi yace oya tashi kisa
Tace nidai gaskiya kadaina kallona tukun ya rufe idonshi da tafin hanunshi
Can kuma sai yace minti biyu sweet yanzu zandawo
Yasauka can kasa har yanzu suna falon basu tashiba aranshi yace wai wadan nan mutanen suna da hankali kuwa
Zai wuce yace sannunku hajiya
Suka amsa dacewan Yauwa sannu dai anfito kenan
Yace a amma yanzu zandawo Abu zan dauka a mota ya wuce yafita
Sai yashigo da wasu manyan ledoji guda biyu
Yana falon yace wa Laila ganata
Ya haura sama abinshi
Laila tsaki tayi tace kakusa Shiga hanu
Suby tace to wannan ledar da ya haura dashi kuma fa
Laila tace ta wannan yar talakawar ne mana
Suby tace wallahi kibishi kice ina nasu hajiya tunda ai yagansu a falon
aikuwa Laila ta tashi tayi saman
Dai lokacin da Hakeem yake ba Husnah nama ta banko kofar tashigo
aikuwa Husnah ta tsorata sosai bata San lokacin da kankame Hakeem ba
Shikuwa Hakeem kallon kofa yayi yaga Laila ce yace kewace irin dakikiyace Laila
Zaki shigo wa mutane daki ba sallama
Laila tace nida dakin mijina sainayi sallama zanshigo
Saboda kana tare da 'yar matsiyatar
Me zubin karuwar yan tasha
Cikin zafin nama Hakeem ya tashi yazabga mata mari yace. Kinmanta wanene Abdul Hakeem ko
To wallahi zanfada nafarko na karshe duk randa kikasake kiran matata da wannan sunayenda kika ambata ranki inyayi dubu zai baci kuma a ranar ne zakisan waye Abdul Hakeem shasha kawai
Get out my room right now
Karkisake shigomin daki batare da kinyi nocking