Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
fara jin kunya gwara ya d’au matarsa su k’ara gaba”. Tana fitowa dai-dai Aisha na hawa matakala Hajiya ta ce”ah! Aisha har kun dawo”, cikin jin kunya ta sun kuryar da kanta ta amsa da “eh mun dawo”. Hajiya ta ce”to yayi kyau kije d’aki Hasna zata kawo”. Miki abinci, Aisha ta ce”Hajiya a k’oshe nake naci abinci a can” Hajiya ta ce” to shikenan”. Aisha ta wuce d’akinta sai da tasha maganin Haiydar ya bata kafin ta kwanta sai ido ta lumshe tana mai tuna abunda ya faru tsakanin su da nan wani tunani ya fad’o mata yanzu fa in da rabo hala ciki ya shigeki, murmushi tayi kafin ta shafa cikinta haka har bacci ya d’auketa. Yau Aisha ta kammala jarabarwata wanda aka shirya musu liyafa nagani na fad’a Sarkin Fulani da shi da Lamid’o sun halarci bikin walimar abun dai sai wanda ya gani walima akayi na gani na fad’a, bayan walima da kwana biyu Hajiya ta shirya ‘Yarta da kanta ta mayar ta gidan Haiydar tare da mata nasihu masu sayaya jiki. Da dadare Haiydar da wuri ya dawo Falmi ya samu a falo tayi d’aurin rashin mutunci sai kad’a k’afa takeyi. Ganin ko kallonta bai yi ba zai shiga d’akin sa tazo tasha gabansa ta ce”to muna fuki wai mai kake nufi ne kasani lokaci yayi da zaka saki Indo, ko ka manta kai da bakin ka kace baka sonta sai yanzu kuna neman ku kareta wai tasamu ubanta mtss zaku raina min Hankali ai ‘Yar shehe ‘Yar she……”. Wani kyawawan mari Haiydar ya bata nan tafara shirin kama sa da kokuwa shi kuma bai son yawan dukar mace kawai ya jata zuwa d’akinta ya kulleta ta baya, d’akin sa yaje yayi wanka kafin yasaka kayan bacci d’akin Aisha ya shiga ya ganta cikin wasu mayun kayan bacci wanda dashi da babu duk d’aya. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [10:50PM, 7/21/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-229~230.* Da daddare haka suka sha hiransu cike da k’aunan juna sai kusan goma Sarkin Fulani ya musu sallama shima Lamid’o d’akinsa ya tafi da ya kwanta yau jinsa yake cikin farin ciki, Hajiya ta kalli su Aisha ta ce”kuma ku tashi ku tafi d’aki ku kwanta dare ya soma yi”. Duka suka mik’e tare da mata sallama, Haiydar ko ya marai-raice fuska Hajiya duk ta d’ago nufinsa ta ce”kai kuma mai ka tsaya yi da bazaka tafi masaukinka ba ne?”. Jiki ba kwari Haiydar ya mik’e ya nufi d’akin sa shima tukun Hajiya ta tafi nata. Aisha tana shiga d’aki wanka ta fad’a Hasna kuwa kitchen taje had’a ruwan zafi take so tasha kafin ta kwanta, Haiydar ganin Hajiya ta tafi d’akin ta ya dawo cikin sand’a ya tura d’akin su Aisha nan ya ga ba kowa sai da ya rufe k’ofar tukun ya k’arasa ciki k’aran ruwa yaji a bayi gefen gadon kusa da bayi ya zauna don kar ma tana fitowa ta gansa, Hasna da take shirin fitowa ganin Haiydar ya shiga d’akin su tayi murmushi sai ta nufi dining kawai don ta sha ruwan zafinta a can. Aisha da ‘yar wakanta fito d’aure da tawul iya cinya sam bata lura da mutum ba dake ta na goge kanta zagawa yayi ta bayanta ya rungumeta tare da zare d’an k’aramin tawul d’in, cikin razana tayi tana shirin sakin ihu ya toshe mata baki da hannusa a kunne ta ya rad’a mata” nine mijiki Haiydar kuma d’an uwanki”, dumm! Taji gabanta ya fad’i juyo da ita yayi duk kunya ya ishe ta, hannu tasa tana kare k’irjinta, ya saki murmushi ya ce”mai yasa kike rufe min abunda yake halal a gareni kuma nake marari ganinsu tare da begen…”. Magana kunya ta bata sai ta rufe ido hannuta ya kama ya kawar daga k’irjinta tare da janta zuwa gado cikin muryan kuka ta ce”Ya Haiydar miye haka? Dan Allah ka bari mai kazo yi a nan?”. Murmushi yayi ya ce”yau nazo karb’an hakkina da ya dad’e shekara da shekaru ana min rowa kai ta gir-giza masa tare da k’ok’arin turjewa sai da ya kaita kan gado ya kwantar da ita, salon k’auna iri-da-kala yasoma nuna mata wanda ya fi k’arfin in tsaya zayya ne mu ku acin nan. Hasna ko ganin haka da man akwai d’aki wanda da komai a ciki d’akin hajiya ta koma ta dauko kayan bacci, tazo tayi wanka ta kwanta a nan. Haiydar ko sai da yayi wasa da Aisha son ransa ya kuma tabbatar da ya gamsu kafin ya mik’e cike da nishad’i ya fito cikin sand’a ya koma d’akinsa wanka yayi ya kwanta yau yana mai jinsa cikin farin ciki kasa bacci yayi can iya tuna mai ya faru sai ya saki lallausar murmushi tare da buga hannusa a katifa alamar jin dad’i. Aisha ma wanka ta sakeyi kafin tazo ta kwanta tana mai tunano abunda ya faru haka har bacci ya d’auketa. Da safe bayan sun karya sun dawo falo an gaggaisa yau Aisha sai wani sunne kai takeyi Haiydar ko idonsa akan ta yake suna had’a ido zai kashe mata ido d’aya, Sarkin Fulani ne yayi gyan murya sai da yayi addu’a kafin ya fara da cewa”hukuncin dana yanke shine da zaran Aisha ta kammala jarabawan ta zamu tafi Yola a kaita taga dangin Mahaifiyar ta sanna gonar Lamid’o inaso zamu mayar dashi kamfanin yin su Madara da yogurts san nan gefe d’aya kuma a mayar dashi gidan gona gefe d’aya kuwa zamu k’awata shi ya dawo gun tutawa zamu zuba k’ananun namun daji don su kawata gun da d’akunan hutawa da gun abinci mai kyau, hakan zai kawo kud’i kuma wasu manya zasuna zuwa gun kasancewar yayi wajen gari kuma ba hayaniya a gun”. Ya d’ago ya kallesu ya ce”kunaga hakan yayi ko da wani tsarin da yafi hakan?”. Hajiya da Lamid’o suka amsa da yayi nan ya ce”to na nasa an muku komai sabida komawarku Bauchi don gobe Aisha tana da jarabawa”. Daga nan kuma suka ci gaba da hiransu. Da yamma kuwa sarkin Fulani har dashi da Lamid’o aka musu rakiya zusa filin jirgi suka dawo Bauchi. Washe gari Aisha ta nufi makaranta nan taba masu Sadeey da Sanah labari ba k’aramin murna suka mata ba da samun Mahaifinta. Haiydar ko yana komawa gida ya samu Falmi amma sai me fiskanta yaga kamar alamun nadama da murna ta tarbesa don ita damuwarta taji ina yaje sai da ya huta cikin kissa take tambayarsa ko da yabata labari nan fa ta dira tsalle ta mik’e ta ce”ina wannan k’arya ne kawai baki kuka had’a don ku rufa mata asiri” nan fa rikici ya kaure a tsakanin su daga k’arshe falon ya barmata ya koma d’akinsa. Bayan kwana biyu duk damuwar sa ya ga Aisha gashi yanzu saura mata jarabawa d’aya ta gama, zuwa makarantar yayi yasamu suna jarabawa ya tsaya ya jirata sai da suka fito yasa aka kirata tana zuwa ya ce”ki shiga mota”, sam fiskan sa ba alamar dariya hakan yasa ta shiga da sauri ya ja motar ya bar harabar makarantar gudu yakeyi sosai hanyar UNGUWAN SARAKUNA ya nufa, cikin razana Aisha ta ce”lafiya yanaga ba hanyan gida ka nufa ba?”. Wani kallon da ya aika mata dashi yasa tayi shiru har suka isa wani k’ofar madai-daicin gida mai kyau horn yayi mai gadi ya bud’e masa yana shiga ya ajiye motarsa ya zago ta gun Aisha fiska a d’aure ya ce”matsawan in kika min gardama to kinsan sauran”. Yau kam ya dawo mata Haiydar d’insa na da tuni wani tsoro ya shige ta hannun ta ya kama tare da mannata da jikinsa suka nufi cikin gidan suna shiga ya kulle k’ofar tare da zare makullin yasa a aljihun sa, wani d’aki ya nufa da ita, suna shiga ta ja ta tsaya a k’ofar d’akin cikin dauriya ta ce”wai lafiya yau kuwa mai yasa ka kawo ni nan gidan?”. Wani mayen kallo ya bita da shi tare da matsowa kusa da ita ya ce”yau hakkina nake buk’ata a gunki nagaji da jamin rai da kikeyi”. Janyota yayi ta fad’a jikinsa tare da rufe k’ofar d’akin tafara k’ok’arin kwace kanta wani tsawa ya daka mata ai ba shiri tayi shiru sai hawaye ke sauka, wayarsa ya ciro ya tura ma Hajiya message kamar haka. *_Assalamu’alaikum_* _Hajiya barka da rana kar a tura d’auko Aisha naje d’auko ta muna tare yanzu haka da ita, zamuje unguwa karkuga shiru sai mun dawo_. Yana tura ma Hajiya yana ganin ta bud’e sak’on ya kashe wayarsa ya sa a gen gado, hannunsa yasa ya janye karamin hijab d’in Aisha tare da sanya hannusa a gashin kanta ya fara shafawa Aisha ko sai hawaye takeyi, hannusa ya zura ta cikin riganta ya balle bra d’in ya fara….. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *_RASH LUV_ * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:09PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-233~234.* Zuwa yayi ya rungumeta ya ce”baby na kinyi kyau sosai”, murmushi tayi ya lakaci hancinta ya ce”kullum kyau kike k’arayi ina rok’on Allah banu baby mai kama da ke”. Da irin wannan kalaman ya lallab’a Aisha suka lula duniyar masoya. Washe gari Haiydar ya fita zuwa aiki Falmi ta tattari kawayen ta ‘Yan bariki suka zo da niyar dukan Aisha kowacce da bulalarta a hannu ana haka sai ga Haiydar ya dawo ganin su yasa ya kira jami’an tsaro aka tattaresu ko wacce taji a jikinta suna kulle a gurin jami’an tsaro, cikin Falmi ya faro ciwo kafin me sai ga jini wanda hakan yasa aka kira Haiydar da gaggawa aka kaita asibiti suna zuwa ana dubata cikin inkon Allah suka zai da jinin suka shaida ma Haiydar cewa magani Hana Haihuwa ta sha wanda yayi wa haifarta illa, nan ran Haiydar ya k’ara b’aci sosai, sai da aka taimaka mata jini ya tsaya, tana farfad’owa ya ce”Fatima naga abu abunki yayi yawa don haka in kin samu sauki ki wuce gidan ku”. Ya juya ya fita hawaye ke zuba afiskansa tabbas Haiydar na son Falmi amma ita tana bin zugar kawayen banza shi yasa da kishin hauka dake damunta. Bayan kwana biyu Haiydar, da Sarkin Fulani dasu Lamid’o da Hajiya suka tafi Yola tabbas Aisha taga ga tanta da dangin ta ko ina sai murnan ta akeyi. Batun gona ko Sarkin Fulani ba k’aramin kud’i ya kashe a gun ba an k’awata gun sosai gwanin burgewa wanda aka sanya masa suna *AISHA VILLA GARDEN* sai da akayi bikin bud’e gurin Lamid’o ya damk’a amanar gurin wa Maharbin nan daga nan kuma aka d’ibi ma’aikata a kauye da birnin Yola, kafin suka dawo lokacin Aisha ta k’ara kyau tayi haske ga wani kwad’ayin da takeyi kulum sai tasha ice cream rigimar yau daban na gobe daban. Yau ma kamar kulum Haiydar ya dawo Aisha ta tasashi gaba da shagwab’a dole sai sunje shan ice cream ba yanda ya iya dole ya fita su tafi, bayan sun saya ice cream dai-dai zasu shiga mota Aisha ta hango wasu mutane take ta rud’e tafara kuka ta mak’ale Haiydar yayi ta tambayan ta duk ta rud’e sai da Haiydar ya sanya bakinsa cikin nata ya bata wani sassayan kisses kafin ta dawo hayyacinta rungeta yayi ya ce”mai ya faru wa ya tab’a ki mai ya tsorata ki”. Cikin kuka ta ce”sune sune”. Haiydar ya ce”waye su d’in?”. Aisha ta ce”sune suka d’aukeni lokacin dana b’ata”. Haiydar ya ce”what!!” Gwada min su nan ta nuna masa su suna shiga gun shan ice cream d’in Haiydar yasa ta a mota ya ce”ki zauna anan karki fito”, rikesa tayi ta fara kuka dan Allah ka kyalesu kar su cutar da kai”. Murmushi yayi ya ce”karki damu kimin addu’a Allah zai kareni”. Kai ta gir-giza masa wayansa ya d’aga ya kira ‘Yan sanda da suke kusa ya na zuwa ya bada umurni aka rufe gun aiko saiga police nan suka shiga aka kamasu duka, nan yasa aka tafi dasu ya ce”bari ya mayar da matar sa gida”. Gidan Hajiya ya kaita ya koma gun aiki. Azaba akayi ta gana wa mutane nan da kyar suka fad’i wacce ta sa su ran Haiydar ya k’ara b’aci da kansa yaje har gidansu Falmi yasa aka kamota sai da ta daku a gunsa sosai kafin ya ce”ki sani na sakeki saki d’aya tunda har haukan ki ya kai kiyi tunanin kisa”. Falmi taji wahala har tayi nadama abunda ta aika, ga wahala ga auren ta ya mutu,.*************** Bayan wata takwas Aisha na hango da zungureren ciki tana tafiya tana ciza baki ta dafe cikin ta Haiydar ne ya fito daga d’aki da sauri ya riketa ganin kamar nak’uda ne da gudu yayi d’aki ya d’auko akwatin kayan haihuwar ta ya fitar ya dawo ya sun kuceta sai asibiti cikin ikon Allah bata dad’e tana nak’uda ba ta haifo baby boy d’inta, nan fa Haiydar yayi ta kiran ‘Yan uwa yana fad’a musu kasancewan lafiyarta lau ta haihu hutawa tayi aka sallame su kafin kace me gida ya cika da ‘Yan uwa da abokan arziki. Bayan kwana bakwai ranan suna yaro yaci sunan *_ABDUL SHAKUR_* Yaro kyakyawa gwanin burgewa bikin suna yayi kyau ida muka samu kyatuttuk’an zannuwa ne mai hoton yaro da Al- qur’ani mai girma abun sai wanda ya gani haka aka watse. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:42PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-235~236.* 4yrs latter Wani kyakyawan Yaro na hango rik’e da teddy a hannusa yana gudu yana dariya ko dana kalli wanda yake bi wani kyakyawa ne fari sol tamkar shi yayi kansa ko dana kalleshi da kyau sai naga kaman Haiydar wata kyakkyawar mace ce ta fito ta ce”Abban Abdul in kun fara wasa kai ma sai kadawo kamar wani k’aramin yaro ya tsaya jin maganar ta Abdul~shakur ne yazo ya kama Abban sa ya dariya ya ce”na kama na kama”. Haiydar yayi dariya ya d’agashi ya cilla shi sama duka suna dariya, Assalamu’alaikum jin sallama duka suka juya sai da suka kalli mai sallaman sosai suka gane Falmi ce da sauri tazo ta durk’usa tana basu hak’uri Haiydar ya kau da fuska ya tashi zai tafi Aisha ce tazo ta rungume Falmi ta ce”Aunty na ni bakimin komai ba na yafe miki Aunty na”, Falmi ta share hawaye ta ce”nagode ina rokinki dan Allah ki rok’ar min Haiydar da ya mayarni d’akina wallahi nayi nadama”. Ta karashe maganan tana kuka Aisha ta rungume ta tace”Aunty kar ki damu Haiydar zai mai daki kuma Haiydar na sonki kawai zugan kawaye ne daman”. Falmi tayi godiya ta tafi, Aisha da daddare tasamu Haiydar da maganan dawo da Falmi ya nuna bazai dawo da ita ba, ganin tayi yaki hakan yasa tayi fushi ta juya masa baya kusan kwanan su uku basa magana kafin Haiydar yaga bazai iya jure rashinta ba da kansa yazo ya bata hak’uri ta ce”in ka ga na hak’ura ka mayar da Aunty na”. Haiydar da kyar ya yarda sai da suka sanar da su Hajiya tayi murna don ita ma Falmi har gida taje ta bata hakuri. Aisha ita da Hasna sukayi ta jagale Haiydar shi ya basu kud’i suka had’a kayan akwati aka biya sadaki ranar jumma’a aka d’aura aure, dadadare amarya ta tare a gidan ta Haiydar bayan ya shigo sai da ya tarasu ya musu nasiha tare da kashedi banda fad’a bare hayaniya suka amsa, Aisha ita taje ta taya Haiydar shiryawa ta basa jallabiya mai kyau sabo ta fesheshi da turare ta kama Hannusa kafin ta rakosa Har d’akin Falmi bayan sun shiga da sallama Aisha tana ta addu’a a zuciyar ta don wani irin kishi takeji amma tana ta addu’a ta kori shaid’an cikin sanyi murya ta ce”Aunty ga Ango ki na kawo miki ina muku fatan alkairi sai da safe”. Tana fita da gudu tayi d’aki tanahawaye niko Rash na ce”hmm kishi kumallon mata”, Falmi ita ta matso kusa dashi ta fara shafa sa daga haka na fito, washe gari Aisha ta shirya musu karin kumalo mai lafiya. Bayan kwana biyu zaman lafiya a gidan Haiydar ba’a magana dukkansu suna girmama junasu, yau k’awar Falmi ne Gwantsi ta kawo mata ziyara ganin irin zaman da sukeyi nan ta fara hure mata kunne tun kafin tayi nisa Falmi ta ce”kee tsaya da fa da yanzu ba d’aya band in ada kin zugani na d’auka yanzu na nutsu nasan mai nakeyi, dakam nasan *NA TAFKA BABBAN KUSKURE* amma yanzu ina cikin hankali na kinaso in fito muna yawon kan titi tare tare”. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* * (MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:50PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-237~238.* Falmi ta ci gaba da ce wa”a yanzu kam na gane hanya kuma na rungumi kawaye na na kirki sune Mesha luv da Zahra BB sune masu sona da gaskiya, kamar yanda naga ‘Yar uwata Aisha bata da kawayen da suka fi mata Sanah da Sadeey don haka tashi ki fita bana son ganinki”. Gwantsi ta tsaya tana mata kallon mamaki ganin bazata fita ba Falmi ta d’auko waya ta ce”ko ki fita ko na kira Haiydar”, jin haka yasa Gwantsi fita ba shiri tana zuwa k’ofa taga Haiydar wanda duk abunda sukeyi yaji, Falmi da sauri taje ta rungumesa ta masa sannu da dawo hannusa ta kama ta kaishi d’aki tare da rugemasa kayan jikinsa sai da yayi wanka ta kawo masa abinci a baki take basa, Haiydar ya kalleta ya ce”Alhamdulilah! Tabbas yau ina farin ciki kuma na yarda matata Fatima ta nutsu kuma ina gode ma Allah da ya kawo Aisha cikin rayuwan mu don yanda nake samun kulawa da k’auna daga Falmi ba tare da na biya kud’i ba”. Ya karashe maganar cikin zolaya dukan wasa ta kai masa tare da rungumesa ta na sha fa kansa, suna haka aka kwan- kwasa k’ofat suka bada izini a shigo Aisha ce tashi go rik’e da hannu Abdul~shakur yaro mai kyau da gudu yazo ya haye Baban sa yana masa oyoyo Aisha da Falmi sai dariya suke masa nan ya biye masa sukayita wasa. *ALHAMDULILAH!* Dukkan yabo ya tabbata ga ubangiji sammai da kassai , nan na kawo k’arshen wannan labari na *BABABN KUSKUREN DANA TAFKA* kuskuren dana yi aciki ya Allah ka yafe min ka bani ikon gyarawa Ameen. *KIRA GARE KU MAKARANTA* Ina fatan kun gane sak’on da na isar a ciki kusani ba wai ina nufin d’aukar ‘Yar aiki da matsala ba a’a sai dai kamar yanda Falmi ta sake ma ‘Yar aiki komai na Mijinta hakan ba dai-dai bane, sannan kuma da masu halayyan hana mijinsu hakkinsu sukuma nuna cewa sai aun basu kud’i kafin su biya musu buk’atarsu na Auratayya wannan ba dai- dai bane haramun ne ke/ni dukkan kowace ta san kanta inda mai yi sai ku gyara Allah ya bamu ikon bin dai-dai Ameen. *SADAUKARWA* Na d’auki wannan *LITTAFIN* mai suna *BABAN KUSKUREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng*na sadaukar wa *AISHA MUHAMMAD (MAMAN ADUL~SHAKUR)* Allah ya bar k’auna. adsense 2 hereBABBAN KUSKUREN DANA TAFKA Na Rasheeda A Kardam Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9