Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
d’au k’una yana mata rad’ad’i. Gashi Hajiya Firdausi tace”ta hak’ura boka yace, suna da nasara tunda yar aiki ce. “Kuma Haiydar ya tsaneta Falmi yake matuk’ar qauna, a zuciyansa. “Kuma bazai tab’a sin Indo ba. A gidan Hajiya kuwa yau akaje akayi jere ma Indo, d’an kayan rufin asiri suka mata bak’arya, side d’inta ita d’aya da d’aki biyu, sai kitchen da store. Komai yaji dai-dai, gidam kam ya tsaru ba laifi, don a tsakar gidan ga swimming pool, ga garden, da wajan wasani abun gwanin nurgewa. Yautake Alhamis duk inda ka leka a gidan su Haiydar, anata kamu ne, kawayen amarya sunsha kyau, suna sanye cikin wani material baki da ash colour, sunyi kyau sosai, sai da aka debi mutane tukun aka kawo wata k’atuwar Jeep ciki za’a d’au amarya. Niko Rash zuba ido nake inga fitowar wannan amarya mai ji da kyau. Mutane naga suna ta d’aukar hoto, da sauri na mik’e, ina zuwa kuwa na hango amarya cikin kayanta, less ne dark ash da silver colour, ohohoho masu k’aratu, gaskiya in baku ga Indo a wannan rana ba, to kalo ya wuceku, don da kyar na iya gane cewa Indo ne, yar wanke- wanke da shara, don yau inda Falmi zata ganta, inaga sai zuciyarta ya buga. Cikin takun nutsuwa su Hasna da Pinky suka rike hannuta, yayin da Cutie ke gabansu, har suka isa mota. Larema hotel sukaje, gurin ya tsaru sai wanda ya gani, a cikin kwanciyan hankali aka gudanar da komai, Sadiq wasu abikan ango suka kirasa suna yabamasa irin tsabin da su Hajiya suka masa, gaskiya tayi bana wasa bace. Shiko haushi suka basa ma, ana haka har aka kammala kamu, suka dawo gida cike da murna, kasancewan gidansu Haiydar na da girma side guda aka bama yan biki, basa ta cikin gidan side d’insu daban. Hajiya ce ta kira Haiydar, bayan yazo ta masa nasiha sosai, gameda rike mata biyu, Hajiya tace”Haiydar na sanka da zafin zuciya ka k’ara hak’uri da halin Fatima. “Don rashin kunya da kishi suna damunta, amma dan Allah kayi hak’uri. Sai da sukayi hira sosai yace”zai tafi a kwai wanda suke jiransa, ya mik’e ya fito. Hasna ko sun dawo sallah sukayi nan suka soma hiran yanda biki ya kasance, Hasna ta mik’e barinje na karbo mana sakon da Aunty Rahma ta bari. Shiru- shiru Hasna bata dawo ba, hakan ya sa Falmi ta mik’e don taje gun Hajiya taji ko tananan, kanta ko d’an kwali babu, gashi yasha gyara, gashinan yazubo har gadon bayanta, cikin karai-raiya take tafiya mai d’aukan hankali. Tazo dai-dai corridor d’akin Hajiya aka d’auke wuta, laluben hanya ta fara tana kiran sunan Hasna, sam bata lura da mutum yana tahowa ba, sai ji tayi ta rungumi mutum, cikin tsoro da ta gudu, Haiydar dake ya ganeta, sai ya tsinci kansa da kara rungumeta, harda sakin ahiyan zuciya. Duk jikin Indo ya d’au bari, ga k’amshin turarensa ta cikata, da sauri da sauri k’irjin Haiydar ke bugawa, hannusa d’aya, ya sanya cikin gashinta yana wasa dashi, cikin zuciyarsa ko cewa yake”duk da gashin Falmi amma Indo ta fita sosai. Sunkuyo da kansa yayi dai-dai hab’arta, ya tallabo, yana mai kalon fiskanta duk da duhun da ke gun, d’an k’aramin bakinta nan ne ya burgesa, bakinsa ya kai kusa danata kenan, Nepa ne suka kawo wuta dai-dai lokacin take wajan ya gauraye da haske, ni Rash ina d’aga kaina wa zan gani…….. Sai kunji ni gobe in dama tasamu, in kuma bansamu yin typing ba, sai bayan Sallah in Allah ya kaimu. Taku a kulum mai qaunarku Rasheedah Abdullahi Kardam DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-126~130. Haskene ya mamaye ko ina nacikin corridor d’in, da sauri ya kali fuskan Indo hawaye ke sauka, yana d’aga kai yaga Husna tsaye zata fito daga d’akin Hajiya. Take ya ji haushin kanshi, cikin zuciyarsa ko cewa yake”wai me ke shirin faruwa dani ne?. Hannusa da ke rike da Indo yayi saurin tunkud’ata, sai data kai har kasa ya tsata mata yawu, Hasna kuwa wani mugun harara ya wurga mata, wanda yasata komawa d’aki bashiri jikinta harna b’ari, don ta san halin Haiydar in ransa ya b’aci bayida sauki. Sai da taji ya banko qofa alamun ya fita, kafin ta fito da sauri tayi gun Indo, ta kamata ta d’agota tace”Aunty na dan Allah kiyi hak’uri da halin Ya Haiydar. “Watarana sai labari kinji. “Kuma ga dukkan alamu ya Haiydar na sonki amma shi kansa bai san haka ba. Indo kam in banda hawaye ba abunda takeyi, haka har suka koma cikin d’akin, Indo kaya ta cire tasaka na bacci ta kwanta, amma sam ba bacin take ba, sai tunanin irin wulakancin da Haiydar ya mata. Wata zuciya tace”Indo ina ke ina Haiydar. “Inake ina iya kishi da Falmi ko kin manta suwaye Falmi?. “Ke fa ba kowa bace face yar aikin gidansu. “Marar asali bakida gatan ki sai Allah. “Bakisan kowa ba. Wani zuciya kuma yace”a kul d’inki Indo, guduwa ba naki bane. “Kina d’iya mace kinsan inda zakije ne?. “Ta iya yuwa kije gunda za’a b’ata miki rayuwanki. “Kawai dai ki hak’ura har Haiydar ya gaji ya sakeki. Ajiyar zuciya ta sauke tare da k’ara lumshe idonta, tare da tuna abunda ya faru dazu. Washe gari da safe, aka tashi da aiki sosai, don ranane ran d’aurin aure. Abba saida ya yanka saniya, Hajiya ko baki har kuni, don murna. K’arfe d’aya da rabi bayan Sallah jumma’a dubban mutane suka sai da d’aurin auren Aisha Muhammad da agonta Aliyu Khaleed Baba(AK Baba) da Amaryansa Aisha Muhammad(Indo). Akan sadaki naira dubu sitin 60k. Bayan d’aurin aure ne, jama’a suka wuce Sogiji Hotel don gudanar da Waliha, duk wanda yaje gun yaci ya sha, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya, tare da k’azantan d’aki. Haiydar tun daga nesa na hango shi, cikin fararen shadda da gare, ya matuk’ar yin kyau tamkar bashi ba, fiskan nan tashi ba yabo ba fallasa, duk yanda naso in gane wani abu, amma dul yanda naso na kasa tan-tace, yau farin ciki yakeyi ko bakin ciki. Haka suka kammala kowa ya kama gabansa. Ango ko ya nufi sabon gidansa, inda Falmi da kyar ta koma, don cewarta ita sai dai ya barta ita kad’ai, da kyar ya lallab’a ta takoma, sai da ya zuba mata kud’i masu yawa kafin ta yarda ta koma. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV 6/3/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-131~135. Haiydar sai bayan la’asar ya nufi gida, tun a falon Falmi yaji muryan yan’uwanta, sai ya fasa shiga d’akinsa ya nufa ya cire manyan kayan, ya shiga bayi ya watsa ruwa, yana fitowa ya tsane jikinsa ya saka kaya maras nauyi don ba inda zai je. Kwanciya yayi ya d’auko wayarsa Falmi ya kira, wayar sai ringing takeyi amma taki dagawa, don wani masifan haushinsa takeji kamar tayi hauka. Nasiba tace”Falmi ki d’auka kiji mai ze ce miki, ai yanzu ne lokacin da zaki zuba mulkinki son ranki a gidan nan. Kowa da kalan nata munanan shawaran, Falmi ta d’aga wayar tace”hello ina jinka. Cikin isa take maganar, Haiydar yace”My Luv bazakizo ki ga lafiyata ba?. “Gani sai tunaninki nakeyi nakasa samun sukuni. “Mtssss to mai zan maka bacin ga amaryanka ba sai kaje gunta ba. “Ai tana da abunda kake buk’ata sai ta baka. Kawshe wayar tayi suka tafa tare da shewa, Nasiba tace”shawaran da zan baki duk yanda zakisan yanda zakiyi kar ki bari yaje gun dinner nan. Falmi tace”Nasy taya zan hana shi zuwa gun dinner?. “Mtsss haba Falmi sai kace ke ba mace ba. “Kisan duk wani hanyan danzakibi ki hana sa zuwa. Nuwairay tace”kin san mai zakiyi Falmi. Cike da k’osawa tace a’a. Nuwairat tace” yanzu in ya sake kiranki ki d’auka ki gwada masa kin sauko, amma kice kina tare da baki, ya d’an jiraki. “Sai ki bari dab da magriba kiyi kwaliya ki tafi d’akinsa, kar ki bari ko sallah isha’i ya fita waje. “Ki nuna masa salonki ki kuma nuna masa kina da buk’atarsa yanzu, ko da kunyi ki nuna bai ishe kiba, kin ga ai dole bai son bacin ranki dole ya hak’ura. Shewa sukayi da tafawa Nasy tace”shegiyar kin kawo idea fa. Ana haka ko sai ga kiran Haiydar haka Falmi ta d’auka ta rinka fad’amasa kalamai masu dad’i, tace”Honey ina tare da baki barin sallamesu zanzo mu gaisa. Ko da ankira magriba karka fita kayi a gida, ko in kaje ka dawo ka jiran zamuyi magana. Haiydar cike da murna ya amsa mata da”ba komai ni yau ji nake kamar nafi kowa farin cikin, tunda kin bar fushi dani. Haka sukayita hira daga k’arshe sukayi sallama. A gidan Hajiya ko bayan d’aurin aure, da yamma walima suka shirya na gani na fad’a, komai cas-cas, akayi walima aka tashi, da daddare kuma zasuyi dinner. Tun bayan sallah magriba suka soma shirin dinner, amarya na hango cikin fafaren net yayi matuk’ar yi mata kyau. Abun gwanin burgewa, ana kiran Sallah isha’i sukayi sallah suna jiran zuwan angwaye. Falmi bayan sallah magriba wanka tayi na musamman ta sanya wani riga iya gwiwa, daga gefen cinyan a tsage yake, bata sanya bra ba, duk wani sassan jikinta kana gani. Kayan sun haska jikinta dake fara ne, dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga wanka d’aure yake da towel, ganin falmi da sauri ya k’araso gunta, janta jikinsa yayi, yace”Honey nayi misin d’inki kwana biyu. Hannuta tasa tafara wasa da sajensa da ya kwanta luf-luf gwanin burgewa, cakul-kuli tasoma masa, dariya yayi yace”wato yau tsokana kikeji ko?. Hannu ta kai tasoma ware towel d’in da ke jikintsa, wasa yasoma yi da gashin kanta, ganin tsayuwa ba zai d’aukesuba ya d’auketa cak sai kan gado, yasoma mata wasani sai da abu yayi nisa Falmi tasoma jan jikinta, komai ta tuna ta tashi zata mik’e, ya kamo hannuta cikin dashashiyar murya yace”Honey miye haka? “Kinsan ina tsananin buk’atarki a wannan lokacin. Wani banzan kalo ta wurga masa da niyar mikewa ta fita, cikin azama ya diro tare da kaimata wani kyakyawan cafka. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-136~140. Cikin hanzari ya kaimata cafka, yayi sa’an riketa, Falmi tayi ta kwace takasa, kuka tasoma masa duk ya rikice, sakowa yayi ya mata nil down ya riko hannuta yace”haba Falmi na mai na miki kike hukuntani ta wannan hanyan?. “Shin kaki tsoron kamun Allah Falmi?. “Kisani ko dai-dai da seconds daya kika tutarni a wannan harka Allah zai saka min. “Kulum cikin azarbtar dani kikeyi Falmi. “Ko so kike in fara bin matan banza. Wani kalon ko oho ta aika masa cikin muryan kuka tace”Aliyu in ka ga dama ka kama d’aki a bayan gari ba ruwana. “Kasani da *KISHIYAR GIDA GWARA TA WAJE* na tsani in gani da wata matsayin matarka. cikin kuka tace” ni daka auro min Indo gwara ka ringa bin mata a wa…. Bata k’arasa ba taji saukar lafiyayen mari a fuskanta, cikin huci yace”Falmi asai baki da hankali?. “Asai bakisan mai kikeyi ba?. “Tabbas na yarda bakisan ciwon kanki ba. “Kinga ina lallab’aki ko don kibani hakkina. “To wallahi ta karfi zan ringa karb’a yanzu, banza kawai. Falmi ba k’aramin tsorata tayi da yanayin Haiydar ba, qofar d’akin yaje ya zate key d’in ta sanya a saman Waldrop d’insa, ya suma bin Falmi tana hawaye suka soma kokawa da kyar Haiydar ya samu ya wurgata kan gado, Falmi ta fara ihu, kamar k’araman yarinya, cikin b’acin rai yace”keee baki da hankali ko? “Yau ko a gaban wakike sai na karb’i hakkina, Haiydar da iya karfin sa ya zage yake abunda yakeso. Niko Rash ina ganin haka na tattaro yan matan kafata na fito. Su Indo sun gama shiryawa shiru ba labarin ango, har an kai wasu a mare cikin *LAREMA HOTEL* anan za’ayi dinner, ya rage daga cutie sai Hasna da pinky suma yanzu saurayin Pinky Nura yazo d’aukarta, sai Hasna da Cutie Sadiq zai tafi dasu. Ana haka saiga Haugal ta iso ita da Ghalinta,(masu karatu ina fatan baku manta da Haughal ba ko?. Nacikin litafin *BAZATA*). Ghali yaje gunsu Sadiq yace”wai ina Man d’in ya shiga ne?. “Tun zamu taho nake ta kiran wayansa bai d’aga ba. Sadiq yace”wallahi muma hakane amma bari zamuje gidansa muduba shi, daga nan sai mu wuce. Jiddah da sallama ta shiga gidan, da su Hasna ta gamu da su, cikin girmamawa Hasna tace”lah! Aunty Jiddah kin isone? “Jiddah tace”eh yanzu muka zo. “Hasna tace”ina Uncle Ghalin”yana waje yanzu zanje muwuce kenan. Jiddah tazo kusa da Indo tace”amaryan mu kinsha kyau bari mu fara gaba sai kun iso. Indo murmushi ta iya mata don tana gabda yin hawaye, sabida tasan daman Haiydar ya tsaneta wahala zatasha ba kad’anba. Haughal ta fita zuwa gun Ghali don su wuce gun dinner. Sadiq yace”Ghali bari muje gidansa kawai mu duba sai muga ko lafiya ne. Ghali yace”ok hakan za’ayi. Sadiq ya kira Hasna yace”ku fito da amaryan kawai mu wuce. Da kyar Indo ta fito don hawaye take amma sai kalura ka gane hakan, suka sakata a motar da za’a kaita Cutie a da Hasna motar Sadiq Hasna ce a gaba sai cutie a baya. Pinky kuma Ya Nuranta. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [6/3/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-141~145. Suka d’au hanyan gidan sa, Indo ko in banda hawayen takaici babu abunda takeyi, tana rokon Allah ya kawo mata d’auki a rayuwanta. Haiydar ko bai kyale Falmi sai da ya tabbatar ya gamsu sosai, ya mike ya shiga wanka. Bayan ya fito yayi Sallah isha’i kenan ya d’auko wayarsa, mai zai gani 60miss call na Hajiya 20 na Sadiq 46, sai na Ghali da wasu abokansa, sam ya manta da zasuje dinner sai a lokacin ya tuna, cikin hanzari yasa d’anyar boyal d’insa mai ji da shek’i, ya kawo agogon hannu ya d’aura ya sanya takalminsa, ya d’auko hularsa itama fara yazo gaban miro ya na d’aurawa, Falmi dake kwace jiki ba k’arfi ta mike cikin zuciyarta ko cewa take”nayi ma kaina gashi ban hanasa zuwa dinner ba, gashi ya gurjeni son ransa amma dole na b’ata kwaliyan nan kuma bazaije ba. Tana d’ingisawa tazo ta tare qofan fita Haiydar ya gama shiryawa yazo zai wuce tace”baka isa ba yau kaje dinner auren wata marar asali. “Yar titi kuma tsintaciyar mage bazai yuwu ba. Haiydar yace”kiyi hak’uri ana jira na kuma kinga mutane sunzo doni ne. “Ni badan Yar aiki zanije ba. “Sabida mutanen da suka taru domin ni zanje in fita kunya. “Falmi kinsan ina matuk’ar qaunanki. Falmi tace”k’arya ne *MAYAUDARI* maha inci kawai. “Da kana sona bazaka yarda ka auri Indo Yar aiki na ba. “Haydar yau ko ni ko kai don ba inda zakaje maci *AMANA* kawai. “Ka kasa rike *AMANA TA* da iyayena suka baka. Ganin zata b’ata mishi lokakaci ya d’auko key zai bud’e qofa tazo ta rike hannu qofar. Ganin bata da nutsuwa a tare da ita, kuma ya mata magana duk taki fahimta. Wata zuciya tace”bata k’yak’yawan mari zata fi fahimtan wannan yaren. Sai da ya gyara hannusa ya bata lafiyayen mari, take Falmi takoma gefe don sai dataga wasu Stars suna mata shining. Haiydar ya bud’e qofa har yafito harabar gidan yana shirin sanya k’afarsa waje kenan, Sai ga su Sadiq nan suka fara tambayamsa lafiya?. Sadiq ya fara masa surutu Haiydar yace”mutafi lokaci ya kure. Yazo sai shiga mota kenan, Falmi ta fito da gudu ta rik’e murfin motan tana cewa”yau ba inda zakuje indai inanan. “Alo tsiya alo danja ba mai fita da kai. Cikin takaici ya tureta ya rufe motar. Falmi batayi k’asa a gwiwa ba ta je ta tatare gaban motar tabaje tana cewa”yau sai dai in ta kaina zakubi ku fita ehe. “Sai ku kasheni in huta. Haiydar bai ma lura da Indo da take gefe tana hawaye ba. Takaici duk ya ishesa da kunya, gashi a gaban abokansa. Sadiq ya mata Horn amma taki matsawa sai ihun da take kurma musu kamar masu satan mutane. Cikin zafin rai Haiydar ya bud’e qofar mota. Ga d’an wannan ina samu lokaci zakujini da daddare in nasamu lokaci, in bansamu ba kuwa sai bayan *SALLAH* In Allah ya kaimu da rai da lafiya. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-146~150. Sam Haiydar bai ma lura da Indo, da take gefe tana sharan k’wala ba. Sadiq ya mata horn amma Falmi taki matsawa, sai ihu take musu kamar wacce tayi hauka. Cikin zafin rai da qunar zuciya Haiydar ya bud’e murfin motan ya nufota, kasancewan gidan da hasken k’oyayen wuta, yasa ta ga Haiydar ya nufota. Sai data ga ya kusa da ita da sauri ta mik’e taje jikin motar ta bud’e side din da Indo take, ta soma shiga duk ta buge indo ta ture ta, tana shirin haye kanta ta zauna ne Haiydar ya finciko ta, cak ya d’agata tana turjewa sai da ya kaita dakinta, yasaka key ya fito. Duk ta ya mutsa masa kayan jikinsa. Takaici goma da ishirin ya had’u masa, zuciyar sa sai rad’ad’i take masa tamkar zata fito waje. Ji yake ina ma da zai iya kuka, tabbas da yaji sassaucin zafin da zuciyar sa ke masa. Da k’yar ya janyo k’afarsa ya shiga mota, sai a lokacin ya lura da Indo da ta had’a kai da gwiwa tana rusan kuka. Nan yaji wani sabon bak’in ciki ya tur nukesa. Shi kenan shikan yazu ya rasa farin cikinsa, ga auren yar aiki, ga Falmi ta rikice masa. Bai san lokacin da yasaki wani tsaki mai k’arfi ba. Haka aka ja motar duk da sun makara, suka nufi gun dinner, mutane har sun soma tafiya, MC ya fara magana da ayi a hakuri, a zauna ga ango sun iso. Sai da abokai suka shiga, ya rage daga Ghali sai Jiddah da Sadiq da Hasna, Su zasu shigo da Amarya da Ango. Amarya da Ango a gaba, sai abokai a bayansu, bayanda Ghali baiyi ba akan Haiydar ya rike hannuta fir yaki. Harda d’an matsawa gefe, ya bar tazara a tsakaninsu. Jidda ta jawo Ghali tace maasa” kasan me kai ka dawo gefen Ango, ni zan dawo gefen Amarya, in munzo dai-dai qofar shiga ka d’an ta kurasa. In hanyar yaji ya takura, dole zai matsa ya mannu da Amaryan. Hasna kuma saita san yanda zatayi, ta manna hannusu guri guda, nasan ba haufi zai rike hannuta. Aiko haka akayi Jiddah ta cike gu, wanda yasaka Indo matsawa kusa da Ango, shi ma haka Ghali ya masa, dai-dai lokacin DJ ya sake musu kidan Loakcin kine yayi Amarya yar *AMANA*. Kasancewar Haiydar na son wak’ar, bai san lokacin da ya saki lallausar murmushi, wani farin ciki ya ratsa zuciyarsa, yasoma bin wak’ar a hankali. Hasna ko hannu Indo ta kama ta d’aura kanna Haiydar. Take yaji wani sanyin dadi ya ratsa zuciyarsa, sai ya samu kansa da k’ara rik’e hannun. Ya d’an janyota jikinsa, sabida laushin fatarta da kanshim da ke tashi a jikinta, ya mantar da shi da wa ma yake tare. Indo ko sai niman zillewa take, don tun da take in banda ranar da suka dawo daga gidansu Haiydar yayi hug d’inta sai ranar walima, namiji bai taba mata irin wanann rikon ba, sai yau. Shiko sai janyota yakeyi cikin jikinsa. Masu k’aratu karkuga yanda suka burge, suna sanya k’a farsu cikin Hall d’in, masu d’aukar photo suka fara, Jiddah tace”ma Hasna bari kuga next target d’in mu. Hasna yi sauri ki d’an zo kusa da Aisha, kin ga ta kalminta na da tsayi, ki d’an samata k’afa kamar zata fad’in, zai taro ta tunda kinga rabin jikinta ansa yake, ba zai bari ta fad’i ba. Ina son ayi shooting d’insu a haka don ya isa gun Falmi, ni kuma zan d’aukesu da IPhone d’ina. Sai ki tutura masa a wayansa. Hasna ta d’aga ma Jiddah hannu, ta sara mata alamar target d’in yayi. Hasna ta yi saurin sanya ma Aisha Indo k’afa sai gata zata fad’i, da sauri Haiydar ya tarota, ya rik’ota duk gaba d’aya ajikinsa take, ita kuma ta rufe ido ta sadak’ar fad’uwa zatayi, shiko kallonta yakeyi, da d’an k’aramin bakinta nan, mai d’aukar hankali. Sam ya manta ida suke, sai ji yayi ya samu kansa da yi mata kiss a lab’en bakinta. Haiydar sai da ya wani lumshe ido, azuciyar shi ko cewa yake”tabbas mata suna suka tara. Don kiss d’in da yayi ma Indo, wani laushi yaji a leb’en bakinta, ga k’amshi gamida zaki. Jama’an da suke hall d’in, abun ba k’aramin burgesu yayi ba, take suka saka sowa da ihu. Masu camera kuwa suna kan aikinsu, haka Jiddah ma ta d’aukomai harda yin editing. Abun sai wanda ya gani, Don ko ni Rash sun burgeni, amma ina tunani photo nan in ya isa gun Falmi da k’aramar yaki. Haiydar cak ya d’aga Indo, bai ajiyeta ko ina ba, sai kan kujeran da aka musu mazauni, ya sak’aka hannusa cikin nata. Hasna da Jiddah ko sai murna suke, don ba wanda zai gane cewa Haiydar ba son Indo yake ba, niko Rash na tab’a k’awata Lovely Aisha Mazoji nace”Lovely kin ga kirsan mata ko, da kirsa da dabara Jiddah tasa Haiydar ya manta k’iyaya, ya shagala da soyayya. Aisha Mazoji tace”taya ni gani kam, kuma in an tab’ashi, ya iya kurin baya son bak’ar mace, sai gulmar tsiya. “Kiga yanzu a gaban mu harda mata kiss fa. Nace”hmm kedai bari kawai zamuga yanda wannan drama zai k’are. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/4/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-151~155. Haka aka gudanar da dinner kowa cike da farin ciki, Haiydar kam tun da ya rike hannu Indo ya kasa saki. Sai da aka gama taro suna sauk’owa Sadiq ya kasa hakuri yazo kusa dashi, yace”ASP Aliyu Khaleed Baba. Sai da Haiydar yayi murmushi yace”Haka sunan yake A.K Baba. Sadiq ya cigaba da cewa “gaskiya yau naga lurv, wato wannan kiss d’in ma duk acikin kiyayyar ne ko?. “Da tsanar bak’ar mace. Sadiq yana wani shu’umin dariya Hasna da ke gefe itama dariyan tafara, sai alokacin Haiydar ya dawo hayyacinsa, ko kalon gunda Indo take baiyiba, ya tureta wanda k’ad’an ya rage ta fad’i, Hasna ta taro ta. Ghali yace”kaga Man d’in nan kora kunya da hauka zaka mana. Ko sauraronsu baiyi ba ya nufi mota. Indo ko daman atakure take don tayi hawayen har ta gaji, ba wanda ta bari ya gane kuka take, ta b’oye har aka gama taro. Hasna ta rikota, tazo zata sata motar da suka zo, Haiydar ya daka mata tsawa”kee ina wasa dake ne?. “Ni sa’anki ne?. Sadiq ya iso gunsu yace”mai kake nufi ne?. “Da wani mota kakeso tashiga?. Cikin harzuk’a Haiydar yace”in dai zata shiga motar nan sai dai in koma a qafa. Gannin yanda ya yake masifa, yasa Sadiq ko magana bai k’aramasa ba, Yace”Hasna kushiga mota in mai daku gida. Hasna ta rik’o hannu Indo suka shiga mota sai gida. Haiydar ko kansa ya jawo ya dawo gida. Ransu Ghali ya baci sun bar masa motan suka tafi. Ko da ya dawo gida dakinsa ya nufa ya kwanta, baibi ta kan Falmi ba, bare yaja ma kansa magana. Washe gari a harabar gidansu aka shirya crossing sword, police ne suka sha kakinsu da mopol, sai wasu friends d’insa yan *WAI BURGET* su kuma sun sanya kaya Green white green. Abun dai sai wanda ya gani. Police sun cire yan Colour paty da yan Sub gard n gard Commander. Haka yan WAI ma. Ba abunda ke tashi a filim sai kid’an Band, har wata yar waka suke musu, da busa mai dad’in sauraro. Amarya na hango cikin shigar cut less mai kalar blue da baki, sai handbag da takalmi blue da baki. Ta sha gwagwaro tayi kyau sosai da sosai. B’ab garen Falmi ko dak’yar su Meesha lurv da Xhara BB, su tursasata tasaka less light pink, gata fara bai mata wani kyauba. Fir taki tsayawa tayi make-up, duk kishi ya dameta. Ta dauro d’an kwali suka fito, gun Haiydar suka nufa, sai wani harara take aika masa, in ta ga Hasna ko ji take kamar ta shak’eta. Ana ahaka akace Amarya da Ango da Uwargida su fito za’ayi Inspection kafin a fara gabatarda bikin. Haiydar ne yazo dai- dai inda Falmi take yariko hannuta. Sai k’ok’arin fisgewa take, yace”kinga mutane a nan gwamma ki tsaya. Tsaki tayi masa ta kauda kanta gefe. Ana haka sai ga Jiddah da Hasna sun riko hannu Indo, ae take kalo ya koma kanta, don hatta mazan da ke gun sun yaba da tsarin kwaliyarta. Cikin nutsuwa take takawa, Haiydar tun da ya d’aga ido ya kalleta, ya kasa d’auke kai yarasa mai yasa duk lokacin da ya kalleta, sai yaji wani abu gameda ita. Sam ya shagala da kallonta, sai da Falmi ta mutsunesa ya dawo hayyacinsa. Hasna ta saka Indo a gefen damansa, yayin da Falmi ke hagunsa. Wasu police ne biyu da wuk’a a hannusu sai shek’i take suka mik’e, tare da sarawa da buga k’afarsu a k’asa. Ba tare da b’ata lokaciba masu band suka saki kid’an taken k’asarmu *NIGERIA*. Duk wanda suke gurin saida suka mik’e tsaye, tare da kame domin girmama qasarmu. Cikin busa mai dadi, akayi kidan National anthem, yayi da mutane ke bin sautin kidan har aka gama. Mutanen dake gun suka saka tafi raf-raf. Aka zauna nan masu band suka cigabada bugawa, ni da lovely na munsaki baki sai kalo muke, nan wayan nan police biyun nan suka soma paret, suka iso har gabansu Haiydar suka sara masa, tukunan su juya tare da buga kafa, sukayi masauni a gabansu. Anan masu kaya kalan green white green suma suka fito, bayansu Haiydar suka tsaya . Karan kidan ya fara tashi da k’arfi. Take suka soma zaga filin da paret, in gun manyan Haiydar suka je, sai ya sara musu in k’ananan sane, su sara masa. Masu camera sai d’aukarsu sukeyi. Sai da suka zaga ko ina, kafin suka zo suka zaun. Gard d’in police suka fara wucewa, suna parret suna zuwa gun Haiydar da iyalansa, sai su sara masa. Sai da police suka gama nasu kafin yan *WAI BURGET* suka faso karkuso kuga ihu da sowa, don yanda suke gudanar da parret d’indu, da tsarin komai abun burgewa ne. Fatyma S.Y itace parret commoder, yayi da Farida Jigides take yan colour patty. Gaskiya abun ya k’awatu sai wanda suka gani. Sai da aka gama parret tukun masu mik’a musu gifts suka taso. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV * [2:32PM, 9/14/2016] Rash

Chapter 4 of 9