Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
da Falmi keyi bata bashi hakkinsa wataran sai ya mata kuka kafin tasa ya ajiye mata kud’i tukun ta kulashi, a hakama sai ya sha masifa kafin ya samu. Tabbas Allah baya bacci kuma shine maji rokon bawansa don shi ya ce mu rokesa zai amsa mana sai dai ya jinkirta don ya ga imanin bawansa. Haka abun ya faru a gun Hajiya don yau Haiydar yana office yaji kaman an tsikaresa take ya tuna abunda ya faru da irin rashin zuwa gun iyayensa har kuka sai da yayi, cikin hanzari ya mik’e ya nufi gida wanka yayi yasaka kaya mai kyau ya fesa turare yayi kyau amma ya rame yayi duhu amma kyansa nanan hancinsa ne yakara fitowa. Ya fito falo sai zuba k’amshi yakeyi dai-dai lokacin Falmi ta fito ganin wanka da yayi ranta ya b’aci da sauri ta nufosa sam yau ta manta bata shafa turare bare ta kuskure bakinta da magani ta ce”kai Haiydar ina zakaje harda yin wanka haka? Ko kamanta kana k’ark’ashin izini nane?”. Bai tanka mata ba don zuciyarshi na azal-zala ganin zai fita tazo tasha gaban sa daman yana cike da ita yanda da safe tayi ta masa tsawa kamar shi d’anta ne, kwalan rigan sa ta sha cikin hanzari ya bata kyawawan mari ya fara ball(kwallo) da ita saida ya jibgeta son ransa ya fita, motarsa ya shiga sai gidan Hajiya masu gadi na ganinsa sai da sukayi mamaki da sauri ya ajiye motarsa ya nufi cikin gidan da sallamansa ya shiga, Aishat ya fara hangota tana jikin Hajiya Hasnat ma ta hango shi kasa d’auke idonsa yayi akan Aishat Hajiya na ganin sa tayi hamdalah amma ta d’aure fuska dole ta gwada masa kurensa duk da ba da sonsa bane. Hajita ta ce”Hasna Aisha maza tashi ku shiga d’aki da sauri suka mik’e Aishat duk da taji dad’in ganinsa amma zuciyarta na suya da abunda ya mata da sauri tayi d’akinsu da gudu ta fad’a kan gado ta fara kuka mik’ewa tayi ta d’au hoton Abban ta da Ummanta da na iyayen Abban ta tare da awarwaron zinari mai tsada da kyalli nan tasa a gaba tana kalon su tana kuka. Hajiya ta ce”lafiya dai ko? Amma b’atan kai kayi yau ko?” Ya russuna ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska san nan ta ce”yauwa da man kai nake jira tunda yau Allah ya kawo ka inaso ka ba ma ‘Yata takardan sakinta don bazata koma gidan ka ba wannan shine hukunci dana yanke kuma umurni nake baka ba wai shawara ba”. Haiydar ya durk’usa akan k’afarsa ya soma kuka yana bata hakuri. Hajiya ganin ita tsaya kallonsa zai sa ta kayara ta mik’e ta bashi guri d’akinta tashiga taga Hasna ita kad’ai ta ce” Hasna ina Aishat d’in?” Hasna ta ce” tana d’akin mu ina ga”. Hajiya ta mik’e ta nufi d’akin su sam Aishat tayi nisa cikin tunanin iyayenta bata san da shigowar Hajiya ba. Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k’arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d’in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k’irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d’aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad’in La….mi…..d bata k’arasa ba ta yanki jiki ta fad’i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d’akin ta saki razananne k’ara tayi kanta. Ni Rash danake gefe na ce” to mai ke shirin faruwa kar dai ace……… Bari dai zamuji koma miye. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [6:58PM, 7/18/2016] Kardawiya : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-221~222.* Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k’arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d’in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k’irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d’aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad’in La….mi…..d bata k’arasa ba ta yanki jiki ta fad’i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d’akin ta saki razananne k’ara tayi kanta. Hasna ta fara jijiga Hajiya amma ina ta sume Aishat ma da sauri ta sauko tazo ta k’ank’ame Hajiya tana kuka, Haiydar da ke falo jin k’aran Hasnat yasa ya hauro sama da gudu ya nazuwa yaga Hajiya a k’asa duk ya rud’e sai da ya jijigata da sauri ya mik’e yayi cikin bayin d’akin ya d’ibo ruwa yana zuwa ya watsa mata, ya k’ara watsa mata take ta saki sassanyan ajiyar zuciya gefen idonta hawaye ne ke zuba. Ta ja jikinta ta jin gina da jikin gado Haiydar da su Aishat sai sannu suke mata Haiydar ne ya bata ruwa mai sanyi tasha ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce”Aishat ina son ki fad’amin gaskiya dan Allah ina kika samu wannan awarwaron da hoton d’an uwana k’anina Lamid’o wanda shekara da shekaru ya rasu?”. Haiydar da Hasna sun zuba ma Hajiya da Aishat ido suna masu mamaki da rud’u a cikin al’amarin Aishat jiki a sanyaye ta ce”Hajiya wannan hoton Mama na ne da Baba na sai d’ayan kuma Mama na ta ce Baba na ya ce mata Kakan ni na ne suke d’ayan”. Cikin hanzari Hajiya ta mik’a hannu zuwa inda hoton ya ke ta d’auko tabbas ko makawa babu Lamid’o ne d’aya hoton kuma ita ce a ciki tana budurwa sai Lamid’o yana k’arami ya dai girma ba sosai ba sai Iyayensu dukkansu sanye suke da alkyabba wanda taji ado da k’ayatarwa cikin rashin fahimta ta ce”Aishat ban fahimce ki ba kina so ki ce min Lamid’o shine Mahaifin kuma kenan bai mutuba?”. A fili ta ce”Aliyu to kodai in mutum ya mutu yana dawowa ne?”. Aliyu ya kalli Hajiya tabbas bata hankalinta don a rud’e take. Aliyu cikin sassanyar murya ya ce”ai duk wanda ya mutu baya dawowa sai dai in daman bai mutum ba”. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce”Aishat ina so ki bani labarin ki iya yanda Mahaifiyarki ta sanar dake”. Ba tare da b’ata lokaci ba Aishat ta basu labari ta harzuwan Mamanta garin Bauchi, idon Hajiya cike da kwalla ta ce”tabbas ke ‘Yar Lamid’o ne ga saida nan wannan awarwaron da kuma cewa Mahaifiyarki ta je Gombe ta nimi ‘Yan uwansa da hoton nan ya isa sai da bare wasu sassan jikinki duk irin na Mahaifinki ne shiyasa ko da yaushe nake jinki a jikina tamkar ‘Yar dana Haifa, a sai da ‘Yata nake tare nan Hajiya ta fashe da kuka wanda itama Aishat kukan farin ciki takeyi Hajiya ce ta mata alamar tazo kusa da ita tana zuwa suka rungumi juna suna kuka zuwa wani lokaci suka tsagaita Hajiya ta kali Aishat ta ce”ke ba ‘Yar shege bane da ake fad’a miki haka ke ‘Yar gatace kuma ‘Yar dangi kafin muje gimbe ya kamata ki san ko ke wacece kuma waye shi Muhammad Lamid’o”. Haiydar ko yafi kowa farin ciki da bayyanan iyayen Aishat asai ‘Yar uwansa ce kanwan sa tabbas sai yanzu yake jin kunyan zagin shegen da yamata tabbas yasan dole yanzu Hajiya ta k’ara hura masa wuta a kan Aishat don yasan yanda Hajiya take tsananin son d’an uwata Lamid’o bare ace yarsa dole ya k’ara kwantar da kai. Hajiya ta ce”Kamar yanda ki ka gani a hoton nan Mahaifin mu Sarkin Fulani ya kasance shahararen mai kud’i a cikin garin Gombe tun asalin Kakan mu shine sarkin Gombe kinga kenan wannan Sarautan tana k’ofar gidan mu ne lokacin da Kakan mu ya rasu sai ya zamana Mahaifin mu Sarkin Fulani bazaiyu a bashi Sarauta ba, sai aka d’auka aka bama Wazirinsa kinga daganan Sarauta ta bar gidan mu kenan ko da Mahaifin mu ya girma ba halin k’arban Sarauta sai aka bashi Sarkin Fulanin Gombe wanda alokacin matan sa biyu ne sai nice ‘Yarsa ta farko kuma bai kara haihuwa daga kaina ba sai bayan shekara biyar aka Haifi Muhammad wanda ake kira da Lamid’o kasancewan shine d’a namiji d’aya ma Sarkin Fulani ya d’auki son duniya ya d’aura masa wanda hakan ya ke kona ran Kishiyar Hajiyan mu tun yana k’arami take kai masa hari da niyar kasheshi Allah bai bata sa’a ba har yasoma tashi, ana haka akayi aurena da Baban su Aliyu muna zama a cikin garin Gombe lokacin a gun yake aiki kafin mu dawo Bauchi da zama kasancewar shi d’an k’aramar hukuman Katagun ne da ke Bauchi, bazan manta da ranar da Abban mu ya dawo daga saudi ba rannan nazo gida masa murna da dangi duk mun had’u a gida”. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [10:16PM, 7/18/2016] Kardawiya : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-223~224.* Abban mu ya dawo daga Saudi na zo gida masa sannu da dawowa da wasu dangi bayan ya huta ya ciro tsara ba ya bai ma ‘Yan uwa da abokan arziki ya raba musu su Hajiyar mu ko wanna awarwaron ya sayo musu wanda kud’insa bana wasa bane anan yaraba musu ana bama Hajiyar mu nata Lamid’o yasa kuka shidai sai dai abasa wannan awarwaron ne na zinari ya masa kyau ba irin rarrashin da ba’a masa ba yaki nan Hajiya ta d’auka ta bashi kyauta. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Sarkin Fulani na gwada mana gata kasancewar mukad’ai ya haifa ‘Ya’ya biyu bayan wasu shekaru Lamid’o ya girma a kwai ranar da bazan manta ba ranar da muka masa ganin k’arshe ranarda kishiyar Hajiyar mu ta aiki driver (mai tuk’a mota) garinsu Lamid’o naji zasu tafi ya ce shi sai ya je Alkaleri kasancewar ita ‘Yar garin ne nan Lamid’o ya d’au yar jakarsa yasa kaya kala 2 kasancewarsa mai tsafta ne kuma sai washe gari zasu dawo, kuma duk inda ya ke baya rabuwa da hoton iyayen mu wanda mukayi tare don shima ya shaku da baban mu sosai, suka tafi da driver(mai tuk’a mota) can kusan yamma sai ga wasu mutane da kukan su wai Lamid’o sunyi hatsari harshi kamma ya kone k’urmus sai tokan sa akà gani to kinji labarin rabuwan mu da Lamid’o wanda sanadin rasuwarsa yasa hawan jini ya kama Hajiyar mu itama bata dad’e ba Allah ya mata rasuwa. Aishat wacce take hawaye ta sauke ajiyar zuciya Hajiya ko ta ce”Hasnat je d’aki ki d’auko waya na kira Abba na in sanar masa don na san zaifi kowa farin cikin ganin ‘Yar Lamid’on sa” Hasna ta d’auko waya Hajiya ta kira Sarkin Fulani ta koro masa bayani cike da murna wanda sai da yayi kwalla harda sujudu shukur yayi nan take yasa aka bama Aishat suka gai sa. Hajiya ta karb’i wayar Sarkin Fulani ya ce” Gobe ku biyo jirgi da wuri kuzo naga jikata don bana jin dad’i ne ni da yau nazo”. Hajiya ta saida masa suna zuwa, take Hajiya ta sanar ma Babansu Haiydar shima yayi murna ya ce”in Allah ya yarda cikin satin nan shima zai dawo”. Haiydar shi ya je ya musu komai harda shi a tafiyan, ranan Aishat kasa bacci tayi dan farin ciki da murna harda yi nafiloli ta gode ma Allah tare da addu’a Allah ya jikan mamanta. Washe gari da safe suka shirya sai gombe, tun daga Airport suka ga jerin dogaraye suna jiransu ga wata rantsaysiyar lemozine k’atuwa da akaje d’aukarsu a cikin ta. Aishat kam in banda kalo ta dawo kamar ‘Yar k’auye sai kale-kale takeyi har suka zo wani k’aton katafaren gida wanda in aka bar Aishat sai ta ce wannan shine white house da ake fad’a na Abuja. Suna sauka nan dogaraye suka fara gaishesu har suka shiga falo, Sarkin Fulani dake Falon idonsa nakan Aishat tabbas wanan jinin sa ne take idonsa ya kawo kwalla duk da yana daurewa hannu yamata alamar tazo ya rike hannuta tare da dafa kanta yana hawaye ji yake kamar Lamid’o ya rike sai da suka zauna kowa ka gani fuskan sa d’auke da fara’a da farin ciki in ka d’auke Hajiya k’arama da ko dariya batayi nan Sarkin Fulani ya sake niman jin k’arin bayani Hajiya ta basa labari Aishat ma ta d’aura da iya sanin ta nan ya rungumi jikarsa yana kuka itama tanayi. Ana haka sukaji an turo k’ofa tare da sallama dukkansu suka d’ago kai tare da kallon k’ofar ko ni ma Rash dana kalli k’ofar wani farin bafulatani dogo mai karan hacci kyakyawane wanda za’a kwatanta a gurin kyau amma ya d’an girma amma kuma girman ta had’u da wahala fuskan sa ta cika da k’asun ba da alamar dai yana cikin wahala cikin sauri Hajiya ta mik’e a razane Sarkin Fulani da k’afarsa ke ciwo bai san lokacin da ya mik’e ba murtsuk’e idonsa yasoma yi don yaga ko mafarki ne yakeyi amma ina ba mafarki bane wannan zahiri ne tabbas wanna ko ba makawa babu tam-tama……… *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-225~226.* Ba kowa bane ya turo k’ofar illa Muhammad Lamid’o d’a d’aya tilo Namiji kuma magaji ga Sarkin Fulani Gombe cikin razana da firgici Hajiya k’arama ta mik’e don ba k’aramin kid’ima tayi da ganin sa ba nan take taji wani fitsari na shirin zubo mata sai zazzare ido takeyi jikinta sai b’ari ya farayi Sarkin Fulani da kansa ya taka ya je ya rik’o hannu Lamid’o yana hawaye bai san lokacin da ya rungume sa ba farin ciki ba’a cewa komai baran Aishat da ganin fuskan sa ba tam-tama ta gane Mahaifinta ne don yawan kalon sa da takeyi a hoto, Sarkin Fulani ya kamo hannu sa ya zaunar da shi Hajiya ma kukan murna takeyi ikon Allah kenan, sai da suka zauna Sarkin Fulani ya ce”Lamid’o kaine?”. Lamid’o ya ce”eh nine Abba”. Sarkin Fulani ya furta ikon Allah kenan ya wuci wasa”. Ya kalli Hajiyan su Haiydar ya ce”kije d’akina ki had’a masa ruwan wanka tukun ya ci abinci don naga da gajiya a tattare da shi ga alamar yunwa”. Haka ko akayi nan take ta kaisa d’akin Babansu ta dawo kitchen da ita da su Aishat suka had’a masa girki mai k’ayatarwa, yana fitowa a wanka ya tarar da sabbin kayan da aka ajiye masa ya sanya ya gyara jikinsa, falo ya fito ya tarar da su, sai a lokacin idonsa ya kai kan Aishat da ta k’ura masa ido shima kallonta ya farayi cikin zuciyar sa ya ce” wannan tamkar Safinatun sa, ayya ko dai ita ce yar cikin Safinatu da taho da shi?”. Hannusa yaji an rike ko da ya duba Sarkin Fulani ne ya kama hannusa duka suka nufi dining, Hajiya da kanta ta sanya ma kowa abinci ta zauna Sarkin Fulani yana mak’ale da Lamid’on sa sai Hajiya da ke kusa dashi sai Aishat a kusa da Hajiya yayin da Haiydar ke kusada Lamid’o sai Hasna a kusa dashi. Haiydar yana kallon Aishat yana aika mata da wasu sak’on ninsa, gun shiru kowa yana fama da abinci fiskan kowanne su yana d’auke da murmushi don suna cikin farin ciki bana wasa ba. Haiydar ne ya mik’ar da k’afan sa ta k’asan dining table d’in yanda zai na tab’a k’afar Aishat babban yatsan k’afarsa ya sanya a tafin k’afar Aishat ya fara mata tafiyan tsutsa a take taji wani yarrr! saurin d’ago fiskan ta tayi karaf su ka had’a ido wani lalalusar murmushi ya sakar mata ya kashe mata ido d’aya. Sai da ta d’an saci kalon su Hajiya taga kowa na ta kai da abincin sa ta murgud’a masa baki, Haiydar yayi murmushi ya sake sosa mata k’afa harda wuce wansa zuwa sawun k’afar ta da sauri ta kau da k’afar asai Hajiya tana lura dasu ta share ne kuma taji dad’in hakan suna kammala cin abinci suka koma babban falo suka zazzauna. Sarkin Fulani ya kalli Hajiya ya ce”wai ina Hajiya k’arama ne banganta ba har a gurin cin abinci kuma yanzu ma bata fito ba ko lafiya?”. Hajiya ta ce”ina ga lafiya zata fito”. Sarkin Fulani ya kalli Lamid’o ya ce” zaka iya gane wannan fuska kuma da wa ta ke maka kama?”. Lamid’o ya kalli Aisha sosai ya ce”tun shogowata fuskanta ke min kama da fiskan Matata Safinatu”. Sarkin Fulani ya murmusa ya ce”tabbas wannan d’iyarka ce da Safinatu”. nan suka kwashe labarin komai suka fad’a masa sosai Lamid’o yayi kuka ya tausaya wa Matarsa da ‘Yar sa tare da mik’o hannu ma Aishat tazo yana kuka ya rungumi d’iyarsa take Aisha taji sanyi dad’i na ratsa ta wai yau ita ce take tare da Mahaifin ta daman ita ba ‘Yar shege bane da ake kiranta, zanso Falmi taga gatana taga Mahaifina asai mu ‘Yan uwa ne da Haiydar nan tasaki sassanyan Ajiyar zuciya, Sarkin Fulani ya ce”zan so kabamu labarin bayan barin ka Gombe yanda al’amura suka kasance”. Lami’o ya nisa tare da gyara zama ya ce”bayan da muka shiga mota munyi nisa sai da muk’a k’usa shiga Alkaleri Idi driver ya tsaya”, ya ce” Lamid’o bazanso na kashe ka da hannuna ba don an bani kwangilan kasheka ne Hajiya k’arama amma sabida kirkin Hajiya babba bazan ci *AMANAN* ta ba ta rik’e mu da gaskiya” Lamid’o ya ci gaba da cebwa”kafin nayi wani magana kawai ya shafamin wani abu a hanci na tun daga lokacin ban san inda kaina yake ba sai a cikin wasu kauyukan Yola na samu kai na tare da wani mutumi wanda aka had’a ni dashi dan ya baro bauchi dani gudun kar Hajiya k’arama ta ganni, mutumin nan sai da ya tabbatar da na dawo cikin hayyacina shima ya zame ya barni, a tasha kauyen ribad’o na zauna nan yunwa ya fara damuna daga nan na fara aikin k’arfi ina kula da kaina kuma na samu wani Bafulatani mukayi dashi zanna tayasa kiyo yana biya na haka muka fara randa ba kiwo inje niman kud’ina da haka har na tara kud’ad’e na sai na sayi saniya ta mace nan muka fara kiwo cikin ikon Allah ya sanya ma saniyar nan albarka tayi ta haihuwa kuma inayi niman kud’ina na sai na sai wasu da haka Allah ya azurtani da garken shanu na kuma yi suna a cikin kauyukan da ke yanki don ba mai shanuna a haka har Allah yayi na auri Matana Safinatu muna zaman lafiyan mu wasu daga cikun yan kauyen suka fara adawa da dukiyata hakan yasa suke min barazanan kisa, a haka wasu daga cikin ranar laraba da bazan manta ba suka fara bina suna neman kashe ni cikin hanzari na taho gida na umurci matata da tazo mu gudu. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-227~228.* Na tattara dukkan shanuna da ‘yar sanda na muka d’au hanya sai da mukanshiga cikin daji kawai mutanen nan suka b’ullo mana ba k’aramin razana mukayi ba amma duk da haka nayi iya k’ok’arina akan su amma Allah baiyi ina da nasara ba haka suka kwad’a min sanda a kafad’a ganin bazan iya kare kaina ba shine na wurgo ma Safinatu jakata da kud’i a ciki da awarwaron da Hajiya ta ban sannan da hoton mu da ku da nawa ni da ita wanda mukayi a auren mu”. Ya nisa tare da gyara zama ya d’an kurb’i ruwan Faron da ke gefensa ya ce”kunji yanda muka rabu da Safinatu”. Duk fiskan su d’auke da hawayen tausayi Sarkin Fulani ya share kwala ya ce”muna jinka yanda ku ka k’are da mutanen”. Lamid’o ya ci gaba da ce wa”bayan tafiyar Safinatu tana kuka tana waige na haka mutanen nan suka kwada min sanda na suma a gun, sukuma suka kad’a shanuna suka tafi, ana haka sai ga wani Maharbi ya zo ganin halin da nake ciki ya d’aukeni yaje ya ta min magani, da ikon Allah ciwukan dana ji duk sun warke amma me sai na samu tab’in hankali haka Maharbin nan yayi ta jinyana tsawan shekara goma sha bakwai kafin da ikon Allah ya samomin magani shekara guda da rabi yayi yana min jinya da maganin cikin ikon Allah na samu lafiya, daga nan ya tambayeni labari na na basa labarina tun daga kawo ni da akayi Yola har zuwa lokacin. Maharbin nan shi ya tara ‘Yan uwansa da mai gari aka karb’a min shanuna ko da suka dawo hannuna sai na saida guda uku a cikin garin yola na dawo kauyen fofure na sai babban fili a jeji wanda filin ba k’arami bane (kunsan filin kauye ba zada sosai). Nan na sake biyan kud’i aka kewaye min da wayoyi nazuba shanuna aciki sannan nasaka su kaji da raguna da akuyoyi da talotalo da agwagi ruwa, bayan dana gama aikin sai na damk’a wa Maharbin nan gonan a hannusa zai na kula dasu don ana saran koyayen zabbi da sayan madaran shanu a gun na masa sallama na sanar da shi zanzo Mahaifata na ga iyayena da Matata da na turota tare da cikin da ke jikinta nan na kamo hanya zuwa Gombe, to kunji labarina”. Wannan karon harda Haiydar a ‘Yan yin kwalla labarin gwanin ban tausayi. Sarkin Fulani cikin fushi ya ce”yanzu abinda Hajiya k’arama zata min kena batare da b’ata lokaci ba ya kira police ya ce su zo gidan sa yanzu- yanzu”. Hajiya k’arama da ta lab’e tana jin duk abunda ya faru cikin sauri ta koma d’akin ta tafara shirya kayanta a k’aramin jaka sai ta nufi d’akin Sarkin Fulani ta d’ibi kud’i da dollars cikin jaka, nan ta fara dariyan mugunta tasan wa’yan na kud’in sun isheta rayuwa a ko ina take ga kuma wanda ta tarasu a account d’inta K’ofar baya tabi tayanda sarki bazai ga fitarta ba cikin hanzari take tafiya dan kar a ganta. A falo kuwa police sunzo d’akinta aka nufa kai tsaye amma me sai wayam suka gani ba kowa nan suka bazama aiko suna zuwa k’ofar baya suka ga ta k’ofar a bud’e cikin hanzari suka bazama bakin titi suka hango ta tana shirin shiga napep ganin haka wasu suka tsari mashin aka bita wasu a mota [10:29PM, basuyi nisa ba aka kamata aka sa mata ankwaf aka nufi C.I.D da ita ana kamata aka sanar ma Sarkin Fulani nan ya ce”Lamid’o muje C I D tare suka fita a jikin mota ko da suka je nan ma aka basa duk abunda aka kama a hannuta, ransa ya k’ara b’aci sai da yabata kyawawan mari masu lafiya ya kuma ce” wallahi kin cucen na yarda da ke sakayyar da ki ka min ke nan ki sani ba amfanin zamana da ke na datse igiyar aurena uku da ke kanki”. Nan ya ba da umurnin abata wahala sosai tukun a turata kutu. Haiydar ko Hajiya na mik’ewa ya nufo gun Aishat Hasna na ganin haka ta ja ‘yan matan k’afar ta ta bar falon, Aisha cikin hanzari itama ta mik’e har ta fita a falon taku k’alilan yayi ya fisgota sai a k’irjinshi ta fad’o nan wani kamshi mai tattare da sanyi ya daki hancinta Haiydar cikin kwayan idonta ya fara kallo ganin haka ta lumshe ido dul jikinta b’ari yakeyi, hancinsa ya d’aura akan nata ya fara gogawa tare da sanya bakinsa cikin nata nan yaji wani laushi a labb’an ta, tun da yake da Aishat sai yau yasamu wannan damar Aisha ko k’ok’arin ta gudu take amma me hannuta ya manna da garu tare da d’aura hannusa akan nata yasona kiss d’inta kamar wani mayunwaci, duk yanda taso ta kauce ba hali gashi jikin ta na b’ari sosai hawaye ke zuba harshensa yasaka yana lasar hawayen sai da ya lashe tass, Aisha gashi ba halin tayi magana ya had’a bakinsa danata dai da ya jagwa-gwata son ransa ya saketa da gudu tayi hanyan cikin d’akinsu sai hakki takeyi cikin sa’a ba Hasna a d’akin kan gado ta fad’a tana maida numfashi sama-sama tare da lumshe ido cikin zuciyarta ko cewa take” a sai haka kiss d’innan ke da… *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [3:18PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-231~232.* Tuni ya fara rikita ta da salon soyayyan sa wanda ganin yafi k’arfin idona yasa na tattara ‘yan matan k’afana nayi gaba, ina daga k’ofar d’aki ina jiyo kukan Aisha wanda ba halin na kai mata taimako haka na zauna jigum, sai kusan k’arfe uku Haiydar ya saurara mata, Aisha in banda hawaye ba abunda takeyi ni ko Rash ina gefe na ce”yau Ashanty anji maza bakin tsiwa ya mutu…..lol..”. Haiydar ruwan zafi ya had’amata sai da yayi wanka kafin yazo ya taimaka mata sam tak’i yarda su had’a ido da kanshi ya mata wanka tukun ya barta tayi wankan tsarki, sai da tafito ya mik’a mata wasu kaya kafin ta sanya harda hijab a ciki tayi sallah kafin ya kawo musu abinci suka ci. Haiydar ya kalli Aisha ita duk kunyansa takeji sabida in ta tuna irin sambatun da yayi jiya sam bata son su had’a ido, hab’arta ya kama ya d’ago fiskanta ido ta lumshe cikin sanyin murya Haiydar ya ce”Aisha Allah yayi miki albarka na rasa kalman da zan gode miki ila wannan yukurci”. wani d’an k’aramin a kwati yaciro mai kyalli ya bud’e tare da zaro wani zobe white gold mai kyalli da haske wanda ni kaina Rash sai dana kare fuskata da tafin hannuna sabida hasken yana kashe min ido, ko da na duba da kyau jikin zoben naga ansa A&A forever, yana sanya mata yayi kiss d’in zoben don bak’aramin kyau yayi mata ba hannu ya rike yana murzasu tare da janyota jikinsa yana mata wasu kalamu masu dad’i acikin kunnenta wanda duk sonjin gulmata ban jiyo mai ya ce ba. Hajiya ko ganin sak’on sai da hankalinta ya tashi tabbas tasan Haiydar yayi hak’uri sosai, dole ta bashi matarsa don taga ya nitsu sosai kuma ya damu da Aisha, ganin matarsa ce bata kawo komai ba amma zuciyarta na d’ar-d’ar. Basu bar gidan ba sai bayan magriba suka d’au hanya sai da yabiya da ita super market ya mata sayya masu yawa suna isa harabar gidan sai da yaga tashiga falo ya juya ya tafi sabida yasan bai da gaskiya shiyasa bai shiga ba. Aisha tana shiga sai da ta d’an lek’a bata ga kowa ba hakan yasa ta fara tafiya a hankali, Hajiya da tafito daga kitchen ta hangota ganin tafiyar da takeyi tuni ta d’ago abunda ya faru a zuciyar ta ta ce”lalle Haiydar ya gwada min shi d’an yau ne ai ban isa ba tun kafin ya sanya na

Chapter 8 of 9