Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k’asan k’afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan- garowa ta k’asan k’afarta. Niko Rash mai zanyi in banda dariya nace”haba Indo karki bada ni mana duk kurarinki nan ace kina wannan tsoro haka?”. *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-200~203.* Aishat da take ciki d’aki jin an kwan- kwasa k’ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k’asan k’afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan- garowa ta k’asan k’afarta. Sai rarraba ido takeyi jin an kara buga k’ofar ae sai ga fitsari na zuba take idanunta suka soma ciko da kwalla addu’a ta fara karantowa duk wanda yaxo bakinta kawai yi takeyi. Falmi ko duk wani tugu da zata had’a ta had’a, bata soma shirin dawowa gida ba sai k’arfe tara da mintuna. Haiydar jin shiru yayi yawa ba a bud’e ba da har zai tafi sai ya fasa, sunan Aishat ya kira sai da yayi baki uku. Aishat daga bayi taji muryan Haiydar da kamar bazata fito ba, amma sai ta daure tana d’an sand’a ta fito falo muryan shi taji, sai da ta tattara nutsuwarta ta amsa ta ce”gani ina zuwa”. Bayi ta koma ta d’auraye jikinta ta fito zani ta d’aura kafin ta bud’e k’ofar. Haiydar ya ce”beauty ina kika shiga?”. Sai da ta d’anyi jim kafin ta ce”na d’an shiga wanka ne shiyasa”. Haiydar yayi murmushinsa mai k’ayatarwa ya ce”beauty shine bazaki kirani inzo na miki ba, bai kamata kina wahala da kanki alhalin gani a cikin gidan miye amfanina? Kin san bana so ki wahala da yawa”. Haiydar ya karashe maganan tare da d’aga ma Aishat gira tare da kashe mata ido d’aya. Aishat ta kauda kanta gefe ta ce”bana bukatar hakan kuma da wake min wanka? Ko kaine kake min? Don haka bana bukatar hakan”. Zai sake magana ta ce”wai lafiya kuwa? Ni fa zan rufe k’ofa don ina da abunyi”. Haiydar ya san halinta da sauri ya mik’a mata ledar bata bari yayi magana ba ta ce”thanks you”. (Nagode maka). K’ofar ta mayar ta rufe tare da sakin sassayan ajiyar zuciya ledar ta ajiye taje tayi wanka kafin tazo ta bud’e ledar sai da taci abinci dake ciki tayi hamdalah ta tattara kayan zata fitar waje nan fa ta tuna da abunda ya faru kamar zata koma ta ce”ai Haiydar yana gida ba zai bari ta bugen ba”. A hankali ta bud’e k’ofar d’akin da sand’a ta ke tafiya, sai da tazo dai-dai falo ta d’an leka taga ba koma sai da ta leka hanyar d’akin Falmi taga ba kowa kafin ta fito sad’af- sad’af take tafiya har ta kai komai kitchen (madafi) tukun ta dawo nan ma sai da ta leka har tazo tsakiyar falo taji ance kee ba karanin razana tayi ba take kayan cikinta suka soma bada sauti shooky. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/14/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.KARDAM. *®NWA.* *Pg-204~206.* Kee taji ance bak’aramin razana tayi ba sai da kayan cikinta suka fara shooky. Duk ta gama d’auka Falmi ce harta had’a hannayenta biyu alamar zata bada hak’uri, a hankali ta juyo sai ganin Haiydar ne ke waya da alamar ransa na b’ace gashi kuma ya ganta ta rasa ya zatayi sai kawai ta wayance taci gaba da sand’ar sai ta d’an jiyo kamar mai wasa abinko sai ya mata kyau. Haiydar kasa d’auke idonsa yayi daga gareta harta shiga side d’inta. Aishat tana shiga ta sauk’e ajiyar zuciya bayi taje tayi brush tazo ta kashe wuta tayi addu’a ta kwanta. Haiydr kasa tashi yayi a falon yana jiran yaga dawowar Falmi ransa ya gama b’aci sosai. Falmi ne tashigo da sallamarta ganin Haiydar ta b’ata rai itama tare da k’arasowa cikin falon, Haiydar cikin b’acin rai ya ce” kee daga ina kike?”. Falmi bata tanka masa ba sai wani harare-harare takeyo, Haiydar ya ce”Falmi kinason ki b’atamin gidana don Aishat duk abunda taga kinayi shi zata koya wanda ni kuma bana so ko kad’an ta koyi munanan d’abi’unki”. Wani harara Falmi ta b’alla masa tare da jan tsaki tayi d’akinta, da sauri ya bita ama kash! Ta sanya ma d’akin key (mabud’i). Ransa ya gama b’aci bai san lokacin da ya fara safa-da-marwa a falo tare da dunkule hannusa ya bugi iska, da kyar yasamu ya koma d’aki ya kwanta zuciyarsa na masa suya. Da safe da wuri Haiydàr ya fita Aishat ma ta shirya school bus yazo d’aukarta, ko da taje school da suka zauna da su Sanah ta basu labari abunda ya faru dariya sukayi sosai kafin suka bata shawarwari. Sai da aka tashi ta bi gidan Hajiya sai da tayi la’asar kafin ta d’au motar ta nufi gida daman a gidan ta bar motar. Tafe take tana tuk’i cikin nutsuwa tun daga unguwansu Haiydar taga kanar wata mota kirar jeep bak’a da glass bak’ak’e tana binta, sam bata kawo komai ba tayi ta tafiyanta sai da tazo hanyar shiga unguwansu bayan Airport taga wannan motar tazo da gudu tasha gabanta, gashi gurin bakowa shiru gurin wasu bak’ak’en mutane ne suka fito daga bak’ar jeep d’in nan tare da zuwa dai- dai jikin motarta suka bud’e, cike da tsoro ta ce”lafiya mai na muku? Dan Allah kuyi hak’uri in motar kukeso in fita na baku amma kar kuyi min komai”. Wani daga cikinsu ya wanka mata lafiyayen mari ya ce”zaki rufa min baki ko-ko sai kinji maza?”. Take jikinta ya soma b’ari idonta sai ruwan hawaye ke zuba, d’aya daga cikin mutanen ya ce”yah! Oga zamu gama da ita a nanne?”. Wani murmushi Ogan yayi ya ce” no zamu tafi da ita don naga ta min zata yi test(d’an-d’ano)dole sai na huta da ita kafin mu gama da ita. Aishat najin haka ta fara zatayi ihu d’ayan ya zaga ta bayanta ya mata kyakkyawan riko wani yazo manna mata salatab a baki, k’okarin janta suka somayi amma tana turjewa abunka da fatar mace mai samu hutu, garin janta taji ciwo a hannu sai ga jini yana zuba har saida ya d’idd’iga a gun. Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b’ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan ‘Yan iska ya ce”tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b’ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da’aka samu sai nida Yarana mun biya buk’ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k’irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin. Ni Rash bansan lokaci da nasaki k’ara ina binsu ina kiran Haiydar amma ina sunyi nisa ba taimakon da zan iya bata a lokacin sai addu’a. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* * (MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/16/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-207~209.* Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b’ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan ‘Yan iska ya ce”tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b’ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da’aka samu sai nida Yarana mun biya buk’ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k’irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin. Gudu suke sharara wa Aishat ko sai hawaye takeyi tanaso ta basu hak’uri amma ina ba hali bakinta yana rufe gam da salatab Ogansu ko tasata yayi a gaba yana kalonta don ya rinyar ta matuk’ar masa kyau ji yake koma dai ya fasa aiwatar da abunda aka sasune kawai ya b’oyeta ya mayar da ita Matar sa kuma inda zai na hutawansa. Fatan bakinsa ya lashe tare da yin wani murmushin mugunta. Falmi ko tana cikin wasu kawayenta wanda kalo d’aya zaka musu ka gane tattatun ‘Yan bariki ne masu ji da bariki, wata kawar Falmi ta kaleta ta ce”Falmi gaskiya baki da kyau yanzu abunda ki ka sa ayi kenan niko kishiyarki kyau ta ke min”. Wani mugun harara Falmi ta sakar mata ta ce”yanzu zamu b’ata da ke don duk wanda zai bi bayan Indi ko ya sota to tabbas makiyina ne ina adawa da shi”. Gwantsi da ke gefe jin kalaman Falmi ta shek’e da dariya ta ce”har uwar Haiydar d’in kenan kina adawa da ita”. Falmi ta ja tsaki”mtsss ita a su wa yanzu next harina ita ce daga nan ina fita gidan mu zaje gun Mummy na ne, dole mu koma gun Malamin nan inaga asirin nan ya karye ne”. Gwantsi ta ce”ni ko in da ni ne ke Falmi bazan tayar da hankalina ba tunda gaki kintara kud’i kin dawo babbar mace, gaki da naira kuma ai Haiydar yana sonki da yawa tunda ke kikace da hannusa ke baki kud’in nan”. Falmi ta ce”ke fa zabaki gane bane Haiydar nawa ne ni kadai da kinga abunda Indo ta min jiya sai kin bani goyan baya dari- bisa-dari”. Wata Mama Zeey da ta ke gefe ta ce” ina bayanki karki ragar musu ko d’aya ai kishiya ba abin so bace kishiya! Kishiya!! Kishiya!!! ina bayanki a gama da ita kawai ki huta”. Haka suka ci gaba da hiransu kowace da gur-guwan shawaran da take bata a gun. Haiydar yana office duk ya ji hankalinsa ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye zuciyarshi ba abunda take tunaso masa sai Aishat, haka kurun ya tsinci kansa da son ganin Aishat a wannan lokacin cikin hanzari ya tattara komai daman time d’in tashi ya kusa. Da sauri ya fito ya nufi motarsa ya shiga cikin sauri ya ke tuk’in sai da ya kusa shiga unguwamsu gabansa ya soma fad’uwa sai gumi ke ketomasa, k’ara gudun motarsa yayi ga gumi sai k’ara keto masa yakeyi duk da sanyin A.C da ke motar amma bai hana sa yin gumi ba. Tun daga nesa ya ke hango wani mota sak irin na Aishat amma sai wata zuciya ta ce masa” mai zai kawo Aishat nan kawai dai kalar motar ce d’aya, ko da ya iso gun k’ofofin motar a bud’e ya ke, ganin school bag d’in Aishat bai san lokacin da yatak wawan burki ba ya fito daga motarsa. Da gudu yayi gum motar baiga kowa ba sai ya lek’a ciki ba ta nan ga hijab d’in mak’arabtarta a gun da hularta, sai takalminta kafa d’aya ko da ya kali kasa nan yaga jinin da ya d’id’iga a hankali ya soma bin jinin har ya kaisa gun da ‘Yan iskannan suka aje motarsu, nan ma yaga alamar kafa inda kayi kokawa da kuma alamar ta k’arfi aka d’auketa, ga tayar motarsu da yayi ribas da kuma yanda ya tashi. Haiydar baisan lokacin da yasaki k’ara ba ya na kiran”Aishat! Aishat!! Aishat! Kina inane? Mai ya same ki? Wa ya tab’a min ke?”. Fad’uwa yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k’araji yana ihu ga hijab d’in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Masu karatu sai kun gansa abun gwanin ban tausayi ni kaina Rash bansan lokacin da hawaye yasoma gan-garo min ba. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-210~213.* Fad’uwa Haiydar yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k’araji yana ihu ga hijab d’in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Ya dad’e a haka ya kasa tab’uka komai sai kuka tamkar mace kamar ba jarumin d’an sanda ba mai hazak’a da kwazo wayarsa ne tayi k’ara yana kuka ya ciro daga aljihunsa ya ga sunan Hajiya kafin ya d’auka harta tsinke. B’an garen Hajiya ko ta ce”yau lafiya banga Aliyu ya d’au wayata ba?”. Kamar ta ajiye wayan sai wani zuciya ya ce”kawai ki sake kira kiji lafiyarsa dana d’iyarki”. Cikin hanzari ta danna kira. Haiydar jin waya na ringing ga jikinsa sai b’ari yakeyi (daman wannan yanayinsa ne in ransa ya b’aci jikinsa b’ari zainayi). Da kyar ya iya danna gun amsa kira yasa a kunnensa kuka yakeyi yana kiran Aishat! Ciki razana Hajiya ta ce”Aliyu lafiya mai yasamu Aishat?”. Bai iya amsa mata tambaya ba sai ce mata” Hanyan gida b’ata Aishat”. Sam kwakwalwarsa ta kasa tuno masa ma ya zai had’a kalman a dai-dai ya fad’a Hajiya cikin kid’ima tun da taji yananyi Haiydar tasan abun ba k’arami bane, ta d’auko hijab d’inta ko Abban su Haiydar dake hanyan dawowa yau bata sanar masa ba ta fito a gi-gice, bata tsaya kiran driver ba(mai tuk’a mota) kasancewar daman ta iya mota da sauri ta figi mota tun daga nesa take horn ma mai gadi, shi kansa mai gadi sai da ya rud’e da horn d’in da takeyi ai ya na wangale gate(gareji) da mugun gudu ta fita. Gudu take shararawa cikin min tunan da baifi hud’u ba ta soma hango Haiydar ga kuma motar Aishat! Gudu ta k’ara tana isowa ta gansa a durk’ushe a kan gwiwansa zuwa tayi da sauri ta rugumesa tana jijiga sa ta ce”Aliyu lafiya? Ina Aishat d’in?”. Jinsa a jikin Hajiya ya saki sassayan ajiyar zuciya sai a lokacin nutsuwa ta zomasa, cikin kuka ya sanar da Hajiya abinda ya tarar Hajiya ta ce”innalilahi wa inna ilaihi raji’u ai ba zama zakayi kana kuka ba, kaman ba jarumin police ba?” Abunda ya da ce zamuyi yanzu tashi kabi sawun motar sannan ka kira duk wata ma’aikatar police da ke kusa a sane dasu don a baza matakan tsaro. Haiydar ya shiga motarsa zuciyansa na suya gun aikinsu ya kira yasanar musu ya ce”susanar da sauran ma’aikatar hukumar ‘Yan Sanda a bazama wasu su biyo sa, hayar da mota tayi yafara bi har ya fitar dashi bakim ti-ti, daga nan kuma hanya ta kasu kashi uku ya tsaya yana tunani sai ga wasu motocin police(‘Yan sanda) sun iso mota uku nan suka kasu kashi uku d’aya yabi Haiydar biyu suka bi sauran hanyoyin. Abu wasa-wasa suna neman Aishat ba labarinta gashi har anyi sallah isha’i. Aishat tare da ‘Yan iska tafiya sukeyi sai shiga cikin daji sukeyi yayinda jinin jikinta sai zuba yakeyi kasancewar ta mai yawan cin abinci mai kyau tanada wadattace jini amma sanadin zuban da yayi da yawa ya haddasa mata jin jiri, idanunta suna wani iri, hakan baisa Ogan ‘Yan iskan nan yayi niyan saurara mata ba sai aika mata da mayen kalo yakeyi. Su Haiydar ko sunyi nima harsun gaji amma shi baijin gajiya a tare da shi zuciyarsa suya yake masa yama rasa wani irin kalan hukunci zai yanke ma wanda ya d’au Aishat d’insa tabbas ba zai iya saurara masa ba baran yanda yanzu yake jin tsananin k’aunar Aishat na yawo a jinin jikinsa da jijiyoyinsa tafiya suke ga dare yayi ko da ya kali agogon da ke hannusa 11:49 wani kwana ya gani wanda ya lula cikin deji kuma hanyar k’aramace mota bazata sake acikin hanyan ba wasu suna cewa kar abi hanyan halane ko sunbi ta gun gashi yayi daji ko da Haiydar batunsu ransa da ya b’aci ya finciki motar ya shiga cikin dajin, sauran suna ganin ya shiga suka bisa a baya sai yayi tafiya sosai sai yaga wani abu a gefe kamar mutum ne ko tudu, da sauri ya tsaya ya fito da wani touch light d’insu mai haske yana haskawa ya hango Aishat kwance bata motsi da gudu yayi gunta yana haskawa yaga jini na fitowa daga k’asan skirt d’in makarantarta wani razazane k’ara ya saki ya soma jijigata ganin bata motsaba, dai-dai lokacin sauran police d’in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce”ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku”. Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMA ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [8:05PM, 7/16/2016 BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-214~216.* Dai-dai lokacin sauran police d’in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce”ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku”. Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. Gudu yakeyi sam ba nutsuwa a jikinsa wani wawan duka ya kaima sitiyari motar tare da furzar da wani isaka mai zafi zuciyarsa na masa rad’ad’i wai ace abunda yagama tanadi wani ya rigasa wasu zafafan hawayene suka zubo masa wata b’an gare na zuciyarsa ya ce”haba Haiydar duk da abin da ciwo kardai kace zaka guje ma Aishat don son da ka ke mata na gaskiya ne bawai jikinta kake so ba. A fili ya furta” Aishat a kowani hali ki ke ina k’aunarki ke ce SIRRI NA bazan gujeki ba”. Wasu hawaye ne suka sake zubo masa, wayarsa ce tayi k’ara sunan Hajiya ya gano ya d’aga cikin muryan kuka ya ce”Hajiya an sameta amma sun mata fyad’e gata ko motsi batayi”. Hannu a ka Hajiya ta d’aura ta saki salati ta ce”yanzu kuna ina ne Aliyu?”. Ya ce”gani a hanya da ita zan wuce T.H”. Hajiya ta ce”okay gamu zuwa da Abban ka yanzu shima ya dawo”. Kashe wayar yayi ya k’ara gudu wanda kiris ya rage motar ta kwace a hannusa Allah ne ya kare. Bai dad’e ba ya isa Asibiti take a ka shiga da ita Emergency Haiydar ya gagara tsaye ya gagara zaune sai safa-da-marwa ya keyi a k’ofar idonsa na zubar da hawaye, Hajiya ne da Abba suka iso kalonsu kawai yayi ya fashe da kuka mai cin rai, Hajiya ma hawaye tafara don abun ya mata ciwo bana wasa ba. Falmi ko gidansu ta nufa ita da Mum d’inta suka tafi gun boka ita duk a zatonta an gama da Indo dan haka ta ce”boka kaban maginda sai abunda na fad’a ma Haiydar zai yi ba kuma zai ki bin umarni na ba”. Bokan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya ce”anyi angama yarinya kinzo inda za’a share miki kukan ki hahahah”. Kwarya ya d’aga sama saiga wasu magun-guna sun zuba a ciki nan ya mik’a mata ya ce”ga wannan turaren ki tabbatar kulum kinshafa a jikinki, sannan wannan maganin ki kuskure bakinki da shi kulum”. Falmi cikin zud’i ta ce”anyi an gama boka”. Bokan ya kara wata dariya kafin ya ce”maganin mu da doka kisani duk randa kika tsallake d’aya aciki asiri zai karye kuma zai miki wulakanci mummuna”. Ta ce”zan kiyaye boka”. Kud’i ta zuba masa suka tafi. A can asibiti kuwa Dr ya bata taimakon gaggawa saida numfashinta ya dai-daita kafin suka duba kasanta asai ba fyad’e a ka mata ba kukkurjewa tayi acinya wanda ya janyo mata zuban jini. To ni Rash abun ya d’auremin kai bare masu karatu, amma bari mu wai- wayi baya, in baku manta ba na ce muku”ciwon da Aishat taji ya haddasa mata zuban jini sosai wanda haryasa idonta yin wani iri”. Bayan da ‘Yan iskan nan suka cigaba da tafiya da ita jininta ya zuba ga razana da tayi hakan ya sanya ta yanki jiki ta fad’i tayi dogon suma idanunta sun kafe, ‘Yan iskan nan da suka ga haka sun d’auka mutuwa tayi, shiyasa Ogansu ya ce”kawai su yarda ita anan tunda ta mutu ba amfanin su fita da gawa karma a kamasu”. Tundaga bakin hanyar da zai shigarda mutum dajin da aka sameta suke janta a kasa wanda yasa skirt d’inta kwayewa jikinta ya jijiciwo kunji dalilin zuban jinin bari mu koma labari. Ko da Dr ya gama dubata ya gito cikin hanzari Haiydar da Hajiya sukayi gunya a tare suka jefo masa tambaya “Dr ya jikinta?” Dr ya ce”da sauki Alhamdulilah kuma ba fyad’e aka mata ba kurjewa tayi, ga jini ya zuba da yawa don haka muna buk’atar jini cikin sauri Haiydar ya ce” Dr muje a d’ibi nawa a samata”. Cikin ikon Allah jininsu yayi dai-dai aka samata Dr ya ce”ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b’aci”. Haiydar ya amsa da “to”. Ya kalisu Hajiya ya ce”barinje gida na d’auko mata wasu kayan”. Hajiya ta kalli agogo wayanta karfe biyu da rabi ta ce”to kaje Allah ya kareka”. Ya amsa da “Ameen”. Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d’in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k’ofar falo. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/17/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-217~218.* Dr ya ce”ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b’aci”. Haiydar ya amsa da “to”. Ya kalisu Hajiya ya ce”barinje gida na d’auko mata wasu kayan”. Hajiya ta kalli agogo wayan ta karfe biyu da rabi ta ce”to kaje Allah ya kareka”. Ya amsa da “Ameen”. Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d’in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k’ofar falo. Cikin rashin sa’a kafin ta riskeshi har ya shiga d’akin Aishat ya d’ibi mata kaya kala biyu marasa nauyi ya fito kenan sukayi two eyes(ido biyu) da Falmi hannuta a kan k’ugunta cikin isa da gadara ta ce”kai daga ina kake a cikin wannan dare?”. Haiydar duk sai ya ji komai ya kwance masa ya tsinci kansa da ba zai iya yi mata musu ko gardama bare yaki bin umurnin ta, sai da ya yayi jim kafin ya ce”daga Asibiti nake”. Cikin hanzari ta ce”waye a Asibiti?” Haiydar ya kalleta ya ce”Aishat ce”. Dammmm! k’irjin falmi ya bada sauti bata san lokacin da ta sanya hannu a k’irjinta ta dafe ba ta ce”mai ka ce?”. Haiydar yasake mai-maita abunda ya fad’a nan take zuciyar Falmi yafara azal-zala ta ciji bakinta hannuta ta had’a ta buga tare da fara safa-da-marwa tana zagaya guri idonta ya kad’a yayi jajazur ta d’ago ta ce”yanzu a wani hali take?”. Haiydar ya ce” jikin da sauki sosai”. Ran Falmi in yayi dubu ya b’aci ta kalli Haiydar ta ce”maza kaje ka ajiye kayan nan ka wuce d’akinka”. Da sauri ya amsa mata da “to”. Amma wani bangare na zuciyarshi bataji dad’in haka ba yana so yaje amma ba halin yi mata musu. Haka Falmi ta tasashi gaba sai da yaje d’akinsa ya kwanta ta nufi d’akinta. Acan Asibiti kuwa shiru-shiru hajiya suka ga bai dawo ba hankalinsu ya tashi sosai, da sassafe hasnat tazo musu da kayan tea da ruwan zafi har wajan bakwai Haiydar bai zoba, hakan yasa Abban da kansa ya ce”Hasna muje gidan Aliyu muga ko lafiya”. Hasnat da sauri ta amsa suka nufi gidan a motan Abba suna zuwa mai gadi ya wan gale musu gate (gareji) suka shiga, Mai gadi yana ganin Abba ne ya gaidasu cikin mutunci da girmamawa, Hasnat ta bud’e falo taga bakowa ganin haka tayi magana ma Abba ya shigo kasancewar tsakanin Main falonsu da side d’in kowaccen su da taraza Abba na zama Hasna ta nufi k’ofar d’akin Haiydar ta kwan-kwasa kamar a kunne Falmi sai gata ta fito tana karairaya ganin Hasna ta ja tsaki ta ce”ke lafiya zaki zo kina tashin mutane da safen nan?”. Hasna ta kalleta a wulakance ta ce” gun d’an uwana nazo ni da Mahaifinsa ke son ganinsa”. Falmi tayi dariya kice min ke da tsoho kuka zo”. Ran Hasna ya baci ta juya ta koma falo Falmi ta biyo bayanta ta ce”aa Tsoho ne haka a gidan mu”. Abba yana jin ana bada labarin rashin kunyan Falmi bai tab’a gani ba sai yau ransa ya b’aci sai karairaya take tana fad’an banzan magana Haana cikin fushi ta kaiwa bakin duka wanda saida jini ya zuba, Abba kasa cewa komai yayi ila fitowa daga gidan Hasna ta kalleta ta ce” ki iya da bakin ki don bazaki tab’amin iyaye na kyaleki ba banza shasha”. Fuuuu Hasna ta bi bayan Abba sai a lokacin suka ga motan Haiydar kenan yana gida. Ran Abba ya gama b’aci amma ya daure ya boye ya ce”Hasna muje gida ki d’auko ma Aishat wasu kaya acikin kayanki”. Haka ko akayi suka dawo Asibiti da kayan Hasnat. Satin Aishat d’aya a Asibiti aka sallameta jiki yayi sauki, wanda duk kwanakin nan Haiydar bai tab’a tako k’afarsa ba abun yayi ma umma ciwo amma taki nunawa a b’an garen Aishat ma haka. Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b’an gare na zuciyarsa baya kin dad’in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya. *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDIL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/17/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-219~220.* Hajiya tasa ka Hasna taje ta d’iba ma Aishat duk wasu abunda zata buk’ata ta koma gidan su da zama kulum tana cikin sanyaya mata zuciya akan halin Haiydar. Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b’an gare na zuciyarsa baya jin dad’in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya sai dai abun na damunsa a cikin zuciyarsa kulum yana cikin tagumi da damuwa.******************** 8months latter. Cikin wa’yan nan watannin abubuwa da dama sun faru harda fara jaraban Aishat sunyi WAEC yanzu suna NECO har sun kusa gamawa, yanzu driver Hajiya ta samar mata shi ya ke kai ta ko ina, Hajiya kuma ta dage da addu’a akan halin da Haiydar ke ciki tanayi kullum bata daina ba. Rayuwan Falmi da Haiydar ko abin tausayi don tana gasa masa aya a hannu bana wasa ba duk ya rame yayi baki kamar ba ASP A.K BABA ba. Kuma duk da tsareshi

Chapter 7 of 9