Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
bakwai Hajiya Firdausi tace”yanzu sai ki maye gurbi Uwarki da aikin da kike ko kuma kisan inda dare ya miki. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/27/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-41~45. Aisha Indo ba yanda ta iya, haka taci gaba da aiki a gidan, Hajiya da kanta ta rage mata Salary zuwa 7k, hakan yasa bazata iya d’aukan nauyin, karatunta ba ta hak’ura. Aliyi Khaleed Baba, tun randa yaga Falmi ya rasa nutsuwarsa, kasancewan ya ganta irin matar da yakeso, gata fara sol, don shi tsarinsa bai son bak’ar mace. Masu karatu zamuso sanin, WAYE ALIYU KHALEED BABA(AK BABA). Alhaji Khaleed Baba asalin d’an Bauchi ne shi, cikin k’aramar hukuman Sakuwa, dake garin Misau. Yata so cikin garun Bauchi yana aiki a kar-kashin Treasuring a yawon aikisa yaje garin Gombe suka had’u da Hajiya Khairat wanda take da zama a garin Gombe. A haka akayi auresu da Alhaji Khaleed ya d’aukota suka dawo cikin garin Bauchi, Suna da zama a State Low cost, bayan aurensu Allah ya azurta su da d’a Aliyu, sai da Aliyi ya girma sosai kusan shekara 12 kafin aka Haifi k’anwarsa Hasna. Wanda yanzu itace auta. Wanan kenan bari mu dawo labari. Haiydar yakasa hak’uri takanas yazo gidan su Falmi, tun daga ranar suka sasanta kansu. Soyayya mai k’arfi tashiga tsakaninsu. Kusan kulum suna tare da juna, wata rana yazo gun Falmi tun daga nesa yaga, Aisha zata shiga gidan sam bata lura dashiba, horn ya mata sosai don tayi nisa cikin tunani. Sai da ya taka burki ya fito ya fara zazaga mata masifa. Ko da Falmi tadawo ta ga sai huci yakeyi, tace”My Haiydar mai ya faru haka?. Nan ya fad’a mata laifin da yarinya tamasa. “Mtsss miye na d’aga hankalunka, akan wannan yar shegen, da ba’a san ubanta ba. “Uwarta tazo tayar mana ita. Nan taba ma Haiydar kabarin komai harda k’arya aciki. Madadin Haiydar ya tausaya mata sai yaji haushinta. Kwanaki sun tafi, magabatan Haiydar sun zo ansaka ranar Aure wata d’aya, sai shiri sukeyi, Falmi tasha gyara sosai, Falmi kasancewar yar casu ne, event tashirya bana wasa ba, tun daga rantalata suka fara event, har Friday idan nace zan tsaya baku labari, events d’in bikin nan da yanda komai ya kasance, charged d’in wayata zai d’auke, ban gama shiba. Ranar Friday aka d’aura aure. Duk wani abun al’ada anyishi, ranar yini da daddare abokai suka raka ango, sai da sukayi yan barkwanci, kafin suka musu sallama suka tafi. Haiydar ya rakasu ya dawo, Falmi tana ganin ya dawo, tazo cikin shagwab’a tafad’a jikinsa, azuciyar Haiydar kuwa cewa yake”wanna wata irin Amarya ce ba kunya, amma sai ya share wata zuciya tace”Son da take maka ne yasaka haka. Falmi bata bari sukayi Sallah farinci da godiya ma Allah ba, ta fara aikin sha- shafa Haiydar tare da masa wasu salo, Haiydar kasa jurewa yayi ya d’auketa sai kan bed. Salon da ya mata, ya rikitata ranar Falmi taji jiki, kasancewa ta kawo budurcinta, Haiydar irin Mazan nane wanda zamu iya cewa shi Hariji ne, a ranan sai da ya gurjeta sau uku. Da safe sai da yayi wanka yayi Sallah kafin, yazo ya mata wanka ya gama shiryata kena, wayarsa tayi k’ara ya d’aga, ganin daga office ne, ya kara a kunnesa tare da fad’in “Hello” daga d’aya b’an gare akace”Sir kazo Commissioner ne yazo yana son ganika yanzu, akan wani case d’in da’aka kawo. Ba yanda ya iya dole ya fita, Falmi ko tunda taga 8:00 bai dawi ba, ga bedsheet d’in da suka kwanta ya b’aci, ko yaye wa batayi ba. Waya ta d’auko ta kira, Mum bayan sun gaisa tace”Mum ki turo min da Indo zata min aiki. Mum tace”ke kina da glhankali kuwa?. “Kice na turo miki Indo gidanki. Falmi tace”Mum Haiydar bayanan ankirashi a gentle a gun aiki, gashi bana iya tashi ne fa, kuma ban karya ba. Mum tana jin haka ta gane sunyi abun garin, sai da tayi murmushi tace” gata zuwa yanzu. Mum ta bama Indo kud’in mashine ta hau tazo. Sai da ta mata girki ta jera mata, Falmi tace”kee jeki d’akina ki yayi bed sheet d’in ki wanke. (Mata kira gareku, ku kasance masu kiyaye duk wani abun da ya shafi Sirrin Auratayyan ku, bakomai ake fad’a ba ko anuna, wanna Sirri ne tsakaninku). Indo tunda ta gani, sai taji ba dad’i, amma ba yanda ta iya dole sai ta wanke. Ta d’ebo ruwa kenan ta fara wanki, sai ga Haiydar yashigo, tunda ya hango ta, yaji ransa ya b’aci. Ko da ya ajiye mota ya fito, dole sai yabi gefenta ya shiga gidan kasancewar qofar main falo yana rufe, yana isowa kusa da ita, karaf idonsa ya sauka kan bedsheet cikin kuna rai da zafin zuciya gami da wani kara yayi kamta da gudu. Ni ko Rash ina ganin haka na tattaro yan komatsena, nasa ka gudu dan kar Haiydar ya had’a dani. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD ( MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-46~50. Da sauri yayi kanta, ganin haka, tasoma ja da baya, jikinta sai bari yakeyi. Haiydar yana zuwa kutu ball yayi da boket d’in. Yana huci tamkar wani namijin zaki, yana jin yuwa yafito farauta. Indo ko ta mak’ure a jikin gini, sai b’ari take, don tunda take a rayuwanta, bata tab’a ganin fushi irin na Haiydar ba. Don in ta kali fuskansa, sai taga kamar na zakine yazo gabanta yana huci. Kanta ya nufo yana cewa”waya kawo ki gida na?. “Meye had’in ki da wanke bedsheet d’in da na kwanta da matata. Indo ko gani tsanani fushi ya had’u da tsoro, bata san lokacin da ta sulale, kasa sumamiya ba. Haiydar ganin idonta sun kafe, hakan ya tabbatar masa da suma tayi, wuceta yayi ya nufi cikin gida, da fushinsa. Falmi ko tana zaune a kan gado, takecin indimiee, wani gululun bak’in ciki ya k’ara tokaraansa, wannan wani irin iskanci ne?. A kan gado take cin abinci. “Mtsss yayi tsaki”. Cikin muryan shagwab’a tace”My Haiydar ka dawo?. “Bayan tafiyanka yunwa ta dame ni da… “Keee wa ya kawo min wannan bak’ar mai ido kamar na mage, gida na kuma don iskaci da rainin hankali, zanin dana kwanta da ke take wankewa. “Mtss shikenan nikam nagama yawo, yarinyanan zata rainani. “Ta gama sanin sirina. “Shikenan nikam kin gama dani mtsssss. Falmi tace”to ya kakeso nayi, ni kasan ko a gida ita, take min wanki. Hatta under wears d’ina ita take wankewa. “Mtsss sai kiyi tayi ae. Falo ya fito tare da bata guri, ganin zaman gun bazai masa ba, ya nufi d’akinsa cike da kunan zuciya. Falmiko tana gama cin abinci a gun ta bar kwanon, ta sake kwanciyarta. Indo ko ta dad’e a sume a gun, sai da ruwan da ya zuba ya iso jikinta, hakan yata daman farkawa. Hasken ranane ya haska mata ido, da sauri ta mik’e, cike da tsoro, tace”yanzu ta koma gidane ko ta shiga gidan?. Wata zuciya tace”in kika tafi baki gama aiki ba, wani tashin hankaline. A hankali tashiga gidan d’akin da Falmi take ta nufa, poss d’inta ta d’auka, tafito falo da shirin ko ta kwana. Haiydar ne ya fito, nan rake ta soma b’ari. Cikin fushi da muryan hargowa yace”ke mai kikeyi a cikin gidan nan da baki tafi ba?. Kasa bashi amsa tayi masifa ya cigaba dayi, wanda hakan ya tashi Falmi ta fito. Haiydar janyo Indo yayi yace”ki fita min a gida kar na k’ara ganin k’afarki a gidan nan sai na karya ki. Falmi tace”miye haka wacce zata min aiki zaka kora?. “Kasan dai ni ban iya aiki ba ko?. “Ita zata na mana girki da sairan aiki. Haiydar ya kulu iya kuluwa, yace”kee miye aikin ki da baza kina aiki ba?. “Ni fa ka ganni ko agida ruwan Lipton sai an dafa min. Cike da ta kaici yace”baki isa ba to ni bana son girkin yar aiki. Ya wuceta fuuuu yayai d’akinsa qofar ya bako ya kwanta yana mai takaicin abunda ya faru, “daman haka halin Falmi yake?. Falmi tana zuwa d’aki Mum d’inta takira, sai da ta sanar mata da komai. Mum tace”yayi kad’an daga zuwanki zai fara fida halinsa to bai isaba wallahi. “Yar’aiki kuma kamar ta zauna daram, dole Indo ta dawo cikin satin da zamu shiga, tunda baki saba aiki da kanki ba. “Ki bar min komai a hannuna dole yayi biyayya. Falmi cike da jin dad’i ta mata sallama, ta kashe wayar. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-51~55. Indo tana fita, kuka take maras sauti, tana rokon Allah ya fitarta ya bayyana mata da danginta. Haka har ta iso gida, tana zuwa bata huta ba ta kama wasu ayyukam, da zatayi ma Hajiya, gashi sun k’aru sabida yan biki. Falmi kuwa bata sake leko falo ba sai dare, da yunwa ya dameta, wasu matsatsun kaya tasaka. Haiydar na falo yana kalon tashar BBC WORLD ta shigo sai karairaya rakeyi, kalo d’aya ya mata ya kasa d’auke kansa, kasancewan bai da hak’uri. Take ma manta fushin da yakeyi da ita, ganin taki zuwa kusa dashi, tashi yayi a hankali yaje ya rikota, cikin rad’a yace”haba baby na fushin ne har yanzu?. Sai da ta d’anyi farrr kafin tace”ni yunwa nakeji fa. Hannu ta ya kamo sukaje dinning, asai yamusu take away. Nan yaringa bata a baki tana ci sai da ta k’oshi, ya sun kuceta sai d’akinsa, nan labarin ya canza. Hajiya Fiddausi, sai datayi shige da fice, tasamo kan Haiydar, ya yarda Indo ta dawo gidan da zama tana musu aiki. Hajiya tace”ma Falmi ta bari sucika wara sai Indo tazo, a kwai abunda takeyi ne. Falmi badan taso ba ta amsa ma Mum d’inta. Kwanaki sun tafi yau 3weeks da bikin Falmi, tasoma caza ma Haiydar kai, Haiydar duk lokacin da yazo da buk’atarsa Falmi tayi burus dashi, ko kuma in tabashi had’in kai sau d’aya, to ba zai k’ara ba. Haiydar har ya d’an rame. Mum takira Falmi tace”to ba zama zakiyi ki zuba masa ido ba. “Zaki fara tatsansa ne mu had’a jari. Falmi tace”Mum to taya zan tatse sa da yawa bacin akwai komai a gida?. “Mtss kee sai kace ba mace ba, bakisan tanda zakiyi ki samu kud’iba. “Kina tambayansa mana. “Ko kuma in yazo kwaciyan aure dake, kice sai yazuba kud’i ke bazaki iya ba. Falmi tace”to Mumcyna hakan zanyi ma kawai. Mum tace”yauwa yar albarka. (Kira gareku mata masu irin wannan galin, idan mazajenku sun zo muku da buk’ata, kuce sai sun baku kud’i, wannan BABBAN KUSKURE NE, aikata hakan haramci ne dan Allah akiyaye). Da yamma Falmi tayi wanka tayi kyau sosai, kasancewan bata girki Haiydar ke sayo musu tayi zaman jiransa. Haiydar ko da sallamansa ya shigo gida, tunda ya kyalo Falmi, ya had’iye wani yawu. Take yaji jikinsa ya mutu, dining ya wuce ya ajiye abinci da ya sayo musu, Falmi ko bata iya cemasa sannu da dawowa ba. Sai shine yace”ya gida fatan kin na lafiya?. Sai da ta d’au lokaci, kafin tace”lafiya lau nake. ‘Dakinsa yaje ya watsa ruwa ya saka 3quater da singlet ya fito, a dining ya ganta. Shima can yaje ya zauna, ya kaleta yace”ki d’auko plate da spoon kiyi serving d’in mu. Sai da ta ya tsina fuska taje ta d’auko ta dawo, har ta zauna yace”ruwa fa ko sai mun gama ci za’a d’auko?. “Mtssss ta yi tsaki ni na gaji da yawan tashi. Sai da suka gama ci, Falmi ta zo jikinsa ta zauna, don yau tanason ta fara wankansa, tunda tagane shi mai yawan bukatane, wasani tafara masa, wanda yasaka hankalinsa tashi, gashi kwana biyu Falmi ta hanasa kanta. Shima biye mata yayi suka dulmuya, sai da taji zai wuce ta mike zubur, cikin dashashiyar murya yace”Falmi karki ki amincewa dani. “pls ki taimaken una cikin yanayin bukata. Kafad’a ta ya tsina tace”ni bazan iya ba. Cikin yanayi tausayi tafara”pls My Falmi ki taimaken dan Allah ina buk’atarki sosai. “Duk abunda kike buk’ata zan miki matsawan zaki bani had’in kai. Sai da tayi wani murmushin mugunta tace”kayi alkawari ina fad’i abunda nakeso zaka bani? Da sauri ya amsa mata”da eh! Zan baki koma miy ne. Falmi tace”kud’i nakeso masu yawa. “Haiydar jikinsa na b’ari ya tashi ya duba Aljihun wandinsa ba wani kud’i masu yawa, sai 10k ne kawai don d’azu a gun aiki, yayi sadaka da kud’ade’en da ke jikinsa, ma masu bara, duka dubu goma ta d’ebo yace”ga abinda suka rage min nan. Falmi tace”nawane wannan don naga da alama basa da yawa?. Haiydar yace”10k ne kawai bana da kud’i a jikina suna banki. “Mtss mai dubu goma zasu min, asai baka shirya jin dad’i ba. Haiydar kamar zaiyi kuka yace”haba Falmi ki taimaka ma halin dana ke. Zugunawa yayi akan gwiwansa, don bayason abunda zai b’ata mata rai. “Mtsss to mai kake so na maka ne?. Da rauri yace”ki taimaka min. Ummmm”zan iya barinka kayi kiss a 10k amma fa da sharad’in bazaka wuce haka ba?. “Eh na yarda in har zaki bari namiki d’an kiss d’in. Okay!. Da sauri Haiydar ya taso yazo zai rungumeta, Falmi ta ja da baya, tana masa kalon raini wayo. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-56~60. Haiydar ya rairaice mata, yana had’a ta da Allah, bata yarda dashi ba sai da ta yamata Alkawarin 100k tukun ta yarda tabashi kanta. Tun daga wannan rana Falmi tadawo galfa Haiydar son ranta, tana sati na hud’u, Indo ta dawo gidan da zama, duk wani aiki Indo keyi hatta gyaran d’akin Haiydar, abincinsa da wankin kayansa duk itatakeyi. Bayan kwana biyu, Hasna ta shirya tace”hajiya zanje gidan Yaya indaidasu”. Hajiya tace”ki gaidasu sai kin dawo. Mota ta d’akua sai New GRA, tana zuwa horn tayi ma gadi ya bud’e mata. Sai da ta ajiye motarta, a ma’ajiyin mota, tafito cikin nutsuwa tashiga cikin gidan. “Assalamu’alaikum” Falmi da ke zaune taji sallama, amma tsaban iskanci taki amsawa, Hasna tasake mai- maitawa, Indo da tafito daga kitchen ta amsa, Hasna tashigo cikin falon. Falmi tana ganin Hasna ta ganeta don tun kafin biki sunjemata, amma dan iskanci tawani yatsina fuska, cikin zuciyarta ko cewa take”mtss wannan dangin miji daga gani zanyi fama daku?. “Wata d’aya da sati biyu da biki, amma ace har sun fara sintiri wa mutu. Hasna da murna ta k’araso gun Falmi, tace”Aunty na sannu da gi…. Wani kalon da Falmi ta aika mata dashi, yasata kasa k’arasa maganta. Falmi bata tanka mata ba, sai da ta mik’e tsaban iskanci tace”daga ina haka?. “Wacece ke naji har kina cemin Aunty. Husna ta danne zuciyarta tace”lah! Baki ganeni bane ai k’anwar Haiydar ne Husna. “Oh! Haka fa yana da kwanwa ko?. “Sanuki da zuwa, Indo! Indo!”. Da sauri Indo tazo ta rusuna, tace”gani Aunty”. Falmi tace”ga wannan yarinya, ki bata ruwa tasha, in kin gama girki, sai ki samata”. Falmi ta juya ta kali Hasna tace”kya iya zama anan kafin Yayanki ya dawi. Ta wuce d’aki tana wani karairaya, Hasna baki tasaki tana kalon ikon Allah. Indo tace”Hasna sunaki ko, sannu da zuwa ya gida?. Hasna cikin raha ta amsa, nan suka fara hira tana taya Indo aiki har suka gama. Hasna taji dad’i zamansu da Indo, haka kurum takejin ta kamar yar’uwata, duk da Indo zata ba ma hassna kamar shekara d’aya haka. Da yamma Haiydar ya dawo, ganin Hasna ya saki fara’a, a falo ya zauna suna hira, tukun ya mik’e yaje yayi wanka, yafito zaici abinci, yaga Hasna da Indo suna hira, wani mugun kalo ya sakar ma, Indo sum-sum tamik’e tayi d’akinta. Duk abunda yakeyi Hasna tana lura dashi, abinci yasa Hasna tayi serving d’insa yaci. Sai can Falmi tafito cike da isa tace”kadawo shine bazaka zo ka fad’an ka dawo ba. Haiydar yace”tayi hak’uri. Hasna da yamma tayi musu sallama ta tafi. Ko da takoma gida, tabama Hajiya labarin Indo da kirkinta. Ta kuma yaba da hankalinta, Hajiya hartaji tana son ganin Indon nan. Bayan kwanaki Haiydar yace”Falmi ki shirya zamuje gaida Hajiya na. Da farko Falmi taki ganin Haiydar ya dawo Aliyu na da dole ta shirya sukaje, ranan kam Hajiya taga rashin kunya ayinin da sukayi, nan Hasna ta bata labarin abunda ya faru, nan Hajiya tagane anyi ma Aliyi asiri don ba haka yake ba, sam bayason raini. Hajiya tace “Don haka dole na mik’e da addu’a. Haka su Falmi suka dawo gida. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.KARDAM. Pg-61~65. Falmi kulum da kalan tsiyar da take tsula ma Haiydar, Haiydar sam baida hak’uri, wani sa’in da dambe yake kusantanta. Kuma dole sai ya biya Haiydar ya rame sosai, har d’an bak’i yayi. Hajiya ko ta dage da Addu’a, har masallatai ta aika ana tayata da addu’a, Allah maji rokon bawansa. Haiydar ne zaune a office d’insa, ga tarin takardu, amma ya kasa tab’uka komai, a hankali yake tariyo komai na rayuwansa, duk lokacin da yatuno Falmi, sai ya rintse ido don wani matsanacin sha’awan dayakeji, ajiyar zuciya yayi. Surar Falmi ne ke yawo a Indonsa, a hankali ya mik’e ya d’au key d’in motarsa. Gida ya nufa don ji yake in bai samu biyan buk’ata ba, komai ma zau iya faruwa. A gida ko Falmi tayi wanka, bata aikin komai sai chatt, ga iya taunan chewing gum kamar tsohuwar karuwa. Ita kad’ai tana murmushi, ga k’aran shigiwan massage na Whatsapp kamar me, duk ta cika mana kunne. Indo ko tanata aiki, don karta makara in Haiydar, ya dawo bata gama ba tasan sauran. Haiydar ko gudu yake sosai, don yanda yake jinsa ba k’alau ba. Yana zuwa gida horn ya dinga yi, kamar zai tashi sama, mai gadi ya bud’e masa gate ya shigo, da gudu yaje yayi parking, ya fito cikin sauri ya nufi cikin gidan, yana shiga falo ya hangota, da sauri ya nufi inda take. Yana zuwa ya janyota jikinsa, ya fara shin-shinata, cikin tsawa tace”Malam lafiyarka kuwa?. “Wani irin iskanci ne haka?. “Mutum na zamansa zaka zo kawani damesa. “Ko kamanta da dokanda na kafa maka ne?. Sake matsowa yayi kusa da ita, ta matsa ya biyota, nan suka fara kokawa, ganin yafi k’arfinta tasoma dukansa, d’aukarta yayi kamar yarinya, yanufi bedroom d’insa da ita, yana ajiye ta ta mike tace”Makam anawa zan baka kaina?. Cike da mamaki yace”kamar yaya?. “Bayan kud’in sadakin dana akwai wani kud’in da zan sake biya ne?. “Oh kamanta ko?. Hanyar fita tayi, kafa ya samata ta fad’i ya mayar da qofar ya rufe. Hmmm ranan Falmi taji jiki dan sai da kusan magriba Haiydar ya kyaleta, yace”kuma kisa ma ranki kulum da dadre sau uku ko hud’u, da safe biyu kafin na fita, in nadawo uku in ba ida zanje. “Kinga ina kyaleki ko to daga yau ba sasauci, in kuma kinki to nasan matakin da zan d’auka. “Don bazan saka miki ido nayita kalonki ba. Ya shiga wanka ya fita masallaci abunsa. Ranan Falmi tayi kuka sosai, don taji jiki, kuma ta gane maganin da suka masa yanzu baya aiki Haiydar tun daga wannan ranan ya mayar da Falmi kamar engine sa. Tunda tagane suka shiga wasan b’uya, gashi ya hanata zuwa gidansu. Falmi ko tayi planning, na 5yrs, bazata haihu ba. Haiydar abun duniya ya ishesa, yanzu kusan shekara 3yrs da aurensu, ba abunda ya canza, a halin Falmi, ga shi ba tatab’a koda b’atan wata ba, kuma shi ya kasance mai son yara. Ganin ba zai juri iskancin Falmi ba ya yanke hukuncin k’ara aure. Amma sai ya fuba mai hankali da nutsuwa tukun, ana haka aka kawo wani case, wani mutumi sunyi fad’a da barayi har sunjimasa ciwo, ga jini na zuna asibiti suki k’arbansa, key motarsa ya d’auka yanufi asibiti, duk wani abunda za’ayi yayi aka k’arb’i mutumin. Nan ya had’u da wata nurse sunanta Amrah tana da hankali, hakan yasa ya k’arbi number ta. Tundaga ranna soyya tashiga tsakaninsu mai k’arfi. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-66~70. Haiydar ya samu Hajiya ya mata bayani, yace”ta fad’a ma Dad, Hasna kam tafi kowa murna. Falmi tun dataga take-taken Haiydar tasaka, aka fara bibiyarsa nan tasamu labarin, yana neman Aure nan hankalinta ya tashi, baran da taji ma’aikaciyar asibiti, take ta kira Mum, tana kuka ta sanar mata. Hajiya Fiddausi tace”karyane dole yau naje gun Malam kiyi shiru. “Ki bar komai a hannuna. Hajiya Fiddaisi tana tashi sai gun malamin dake mata duba, ko da ya buga k’asa yayi wasu surkulensa. Yayi shiru can ya d’ago yace”Hajiya sai dai hak’uri fa, dole mijin yarki zai k’ara aure, sai dai shawaran da zan baku shine. “Zamuyi aiki a kai ku sai ku zab’a masa mata. “Don Mahaifiyar yaron ta dage masa da addu’a. “Aikin mu bazaiyi wani tasiri akansa ba. Hajiya jiki ba kwari ta dawo gida nan ta sanar da Falmi kimai. Hankalin Falmi ya tashi ta rasa mai ke mata dad’i, don hatta indo bata barta ba bare Haiydar, kulum cikin fad’a suke. Haiydar ya tsayar da ranan jumma’a magabatansa zasuje, gidansu Amrah. Falmi ta fito zatayi d’akinsa taji yana waya da Amrah ya na sai damata ran Friday, magabatansa zasuzo, Falmi tayi kukan kura tace”kwace wayar nan ta kamashi da fad’a, farko Haiydar ya kyaleta, ya dawo falo tafiyosa. Nan tasha kwalansa, suna kokuwa saiga Hasna ta iso, ganin halin da ake ciki, yasa takiya Hajiya ta fad’a mata. Hajiya ta sanar da Abbansu Haiydar, ta sa driver ya kawota. Zuwan Hajiya tasa Haiydar ya bar dukan Falmi, Hajiya ta musu nasiha sosai, bud’an bakin Falmi tace”Hajiya nifa aure ne bana so ya k’ara. “Yin hak’uri da k’ara aure shine zaman lafiya a gidan nan. Nan tafara rashin kunya son ranta, Haiydar ya taso zai daketa Hajiya ta hanasa. Hajiya tace”kee Fatima aure kam ba fashi sai anyi dole. Falmi tace”to ya auri wata ba wannan ma’aikaciyar ba. “Ai da ya aureta gwara ya aura min Indo a matsayin kishiya. Hasna da ke gefe tace”Hajiya ae gwara Indo sau dubu tana da hankali. Hajiya tace”kee wayasa ka bakinki a ciki. Hasna tace”yi hak’uri Hajiya. Hajiya tace”ke da bakinki kikace haka ko?. “To zan gwada miki na isa da d’ana. “Kuma ina Indon mutum ce?. “Kuma macece?. “To zai aureta in Allah ya yarda. Cikin sauri Haiydar yace”Hajiya ina bana son Indo gwanda ke kini momin wata daban na tsani Indi. Hajiya tace”hukuncin dana yanke kenan. “Fatima ta raina Indo ne tace haka ko?. “Watarana d’an hakin da ka raina shi zai tsole maka ido. “Aliyu! Haiydar da sauri ya d’ago don tunda suke da Hajiya bata tab’a kiran suma ba. Hajiya tace”in nina haifeka to ina si kamin biyya. “Indo ita na zab’amaka kuma wataran zakayi alfahari da ita, amatsayin mata. Hajiya tace”Fatima ina Indon take?. Falmi cikin muryan kuka duk ra rud’e tace”bata nan na aiketa gidan mu. “Ok! In ta dawo Hasna zata zauna sutaho tare. Hajiya ta mik’e tace”ni na tafi kaiku ma kazo dadaddare ina son ganinka. Hajiya tana fita Haiydar ya mik’e sai jiri yakeji ya nufi d’aki, wannan wani irin al’amarine?. “Naike shirin faruwa dani. Hasna abun ya mata dad’i hawan kan kujera ta mik’e, tana jiran dawowan Indo du tafi. Falmi ko ta d’aura hannu aka tana cewa”shikenan naja ma kaina tabbas NA TAFKA BABBAN KUSKURE. “Mai ya kaini furta haka ya akayi na ambaci sunan Indo?. “Wannan shine BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA. “YAR AIKINA ZATA DAWO KISHIYATA. “KUMA YAR CIKIN SHEGE. Nima Rash daga gefe nace Falmi gaskiya kinyi KUSKURE BABBA. Bari dai muga ya wannan gurmin zai k’are don nikam banso abarni a baya. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-71~75. Indo bata dawo ba sai daf magriba tashigo, da sallamata, Hasna dake falo tana kalo tace”oyoyo Aunty Indo sanu da dawowa, tun d’azu nake jiranki. Cikin sassayan murmushi Indo tace”sannu Hasna ya kk?. Yasu Hajiya?. Hasna tace”lafiya lau”. Indo tace”kin dad’e da zuwa ne Hasna. Hasna tace”eh! Hajiyar ma tazo, bata dad’e da tafiya ba. “Tace muje tare dake yanzu nan. Indo ta zaro ido tace”lafiya dai ko Hasna?. Hasna tayi murmushi tace”lafiya lau mudaije zakiji. Indo tace”bara na fad’a ma Aunty aika. Hasna tace”kyaleta ki zo muje kinga Hajiya ke kiranki. Indo tarasa mai zatace ma Hasna, can tace”karfa ta zage ko ta maren ina tsoro. Hasna tace”Itama tasan da Hajiya tana kiranki itama. “Karki damu yanzu zo mu tafi. Ba musu Indi ta bita suka fito, motan Hasna suka shiga ta su zuwa State Low cost. Cikin nutsuwa suke tafiyar har suka iso katon katafaren gidansu, horn tayi mai gadi ya bud’e mata, ta danna hancin motarta cikin gidan. Gurin ajiye motoci taje ta ajiye motar suka fito tare, sannu a hankali sushiga cikin gidan, Indo tun zuwarsu taji gabanta na fad’uwa, addu’a tasomayi. Da sallama suka shiga falon ba kowa, Hasna ta nuna mata kujera tace”zauna Aunty na” Hasna taje fridge ta d’auko mata lemu da cup ta kawo mata, saida ta siyaya sannan tace”Aunty na barinje na kira Hajiyan. Indo murmushi tayi wanda ya k’ara fitar mata da kyauta. Hasna ta hausa sama zuwa d’akin Hajiya, ta tura da sallama tashiga. Hajiya tace”Hasna kun zo tare da ita ne?. “Eh! Hajiya gata a falo tana zaune. “To kije gunta ina zuwa yanzu. Hassana ta sauk’o a hankali zuwa falo, kalo ta kunna musu, sai ta mik’e ta koma d’akinta ta d’ebo ma Indo, hotunansu na school ta kawo mata. Kusa da ita ta zauna Indo ta fara ganin photo, Hasna tana fad’a mata sunan kwayenta. Tun Indo na d’ari-d’ari, har ta saki jiki da Hasna, suka fara hira sosai, a tsakaninsu nan Indo kece ma Hasna itama tayi karatu, amma a Jss3 ta tsaya bata ci gababa. Hasna tace”maiya hana ki ci gana Aunty n?. Nan take idon Indo yaciko da kwalla, ta fara sharewa tace”Mamana ke biyan min kud’in makaranta, ta rasu kuma ba mai d’aukan nauyina. “Hakan yasa na hak’ura da karatu. “Amma ina son nayi karatu wallahi. Hasna tace”Allah sarki Allah ya jikanta da rahma. Indo ta amsa da amin. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-76~80. Hasna hira sosai sukeyi da Indo, abun gwanin burgewa in ka gansu ka d’auka sun dad’e da sabawa da juna. Haiydar da kyar yashifa d’aki wani irin jiri yakeji, cikin zuciyanshi ko cewa yake” amma Fatima ta cuceni gaskiya. “Mai ta kawo bakinta na cewa na Auri Indo. “Ina zan kai b’akar mace?. “Sam ni tsarina bana son b’aka. “Kuma

Chapter 2 of 9