Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA Na Rasheeda A Kardam Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Bismillahi rahmanu raheem, dukkan godiya, da yabo, tsarki da mulki sun tabbata ga Ubangijin sammai da kassai. Na fara rubuta wannan littafin cikin iko Allah, ya Allah ka bani ikon isar da sak’o mai amfani aciki, san nan ka sanya, mutane zasu, nishad’an tu dashi, ta hanya mai kyau ameen. Pg-1~5 Wani kyakyawan Matashi, mai jini ajika, sanye yake cikin, kakin sa na Police, kalan blue da bak’in wando. Kayan sunyi matuk’ar amsan jikinsa, tamkar dashi aka tsara kayan, ko da na kali wannan guy d’in. Dogon ne fari sol, yana da faffad’an k’irji, sannan ga shi da dogon hanci tamkar pencil, yana da k’aramin baki, ga kuma wasu sexy eyes, d’insa da suka rikitani, shekarunsa bazai wuce 37 ba. A hankali yake tafiya, falo ya nufo, dai-dai nan, naji muryan mata tana kiran Indo! Indo! Indo!. Wacce a ke kira da indo ta fito da sauri, sam bata lura da Yallab’oi ba, tana yankowa sai jin, garam sunyi karo, take jikinta ya d’au rawa ta fara dan Allah kayi… Bata k’arasa ba yasakar mata, wani lafiyayan mari a fiska. Da gudu tayi ciki don tana matuk’ar tsoron Haiydar. Shi ko gogan kar-kad’e inda ta tab’a ya fara, cikin zuciyarshi kuwa, cewa yake”mtss na tsane ki bana son ganinki, don ba yanda na iya ne. Indo tana shiga, sai da ta share hawayenta,ta k’arasa cikin d’akin, taje ta rusuna agaban wata mata, wanda da’alama itace matar gidan, cikin sanyi muryanta mai dad’in sairaro tace”gani Hajiya”. Wacce aka kira da Hajiya sai wani yatsina take, tace”ga hulan Haiydar nan ki kaimasa, ya fita ni bazan iya tashi ba, cikin tsoro Indo ta bud’i baki tace”Aunty wal…. “Kee yi min shiru umurni na baki, tashi ki kai masa, kina yar aiki, har zanyi magana kema kiyi. Jikin Indo ba k’wari ta k’arba ta fito falo, dai-dai koma ciki ya d’auko hulan, wani kalo ya watsa mata, take yan hanjin cikinta suka soma rawa, sam bata son had’uwar su, da Haiydar, don ya matuk’ar tsanata, sam baya son ganinta, Indo kuwa ta mak’ure ajikin garu kamar munafuka, duk tayi kalan tausayi. cikin fushi yayi kanta. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-6~10. Cikin fushi Haiydar yayi kanta, hularsa ya fin cike tare da tofa mata yawu, ya wuce abunsa, cikin zuciyarsa na masa suya, “mtss ace wai matar ka ta sunna, batasan kula da hakkin miji ba. “Bata damu da duk wani abun da nake bukata ba, wai sai yar aiki. “Yar aikin ma wanda bata min ba, sam na tsani ganinta mtss. Yayi tsaki, dai-dai lokacin ya shiga motar sa, mai gadi da sauri ya bud’e masa yafita. Tafe yake cikin nutsuwa har ya isa area Commander, yana shigowa aka fara sara masa, da han zari ya nufi office d’insa dake sama. Yana shiga na biyo sa, nima da sauri don na fara aikina, d’an madai- daicin office ne, d’auke yake da tebur sai kujeran zama, gefe ga k’araman fridge, da nesa na hango yar k’aramar TV bango da ke mak’ale, office d’in yayi dai- dai misali. File d’in da ke kan tebur ya duba, nan ya fara yan rubuce- rubuce, nan ya d’aga waya yace”hello Sargent Nasir, kazo ina nemanka a office d’ina yanzu. Wayar ya ajiye ya cigaba da rubutu, ba’a d’au lokaciba wani d’an matashi, ya turo qofar office d’in, yana shigowa ya kame kamar katako tare da buga k’afansa a kasa, hannusa ya sanya shi a gefen damansa tare da waresu. Cikin girmamawa yace” Morning sir”. Naji an kira da sir, bai s’ago kansa ba, yana rubutunsa yace” Morning how is your work?. Sergent Nasir yace”fine too. Haiday ya ci gaba da cewa” na duba file d’in case din mutanen nan, kun kaisu CID ne?. “Eh Sir tun jiya ma aka kaisu. “Ok daman abun da nake son ji kena. “Zaka ita tafiya. Sergent Nasir ya sake sara masa tukunan ya juya ya tafi. Haiydar ko aikin da ke gabansa yayi, bai fito ba sai lokacin Sallah, k’arfe uku da rabi na yamma, ya kamala duk aikin da zaiyi ya fito ya shiga motarsa ya nufo gida. Tun a hanya da yayi tunanin abunda zaije ya tarar tsaki ya farayi, duk sai yaji baya son komawa gidan. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-11~15. Indo ko tun lokacin da Haiydar ya tofa mata miyau, da gudu tashiga d’akinta, kan gado ta fad’a tasoma rusa kuka kamar ranta zai fita, a fili take cewa”wannan wani irin rayuwa ne?. “Mai na tsare masa ya tsaneni?. “Ina da iyayena suna nan nasan duk rashinsu ba ran zauna cikin wanna k’uncin ba. “Wayyo Ummi na! Allah ya jikanki, tabbas nayi rashi. “Ina zansan inda dangina suke na nemesu, nasan su bazasu tsaneni ba. A hankali ta tashi ta d’auko wasu fotuna, da wani awarwaro masu kyau, sai d’aukar ido sukeyi, rungumesu tayi tana kuka mai tsuma zuciya, a haka har baci ya d’auketa. Kamar ama mafarki takejin ana kiran sunanta, firgigit tanfarka, aiko taji an sake kiranta, da sauri ta mike ta b’oye war-waronta da hotunanta, ta fito cikin hanzari. Cikin isa Falmi tace”kee mai kikeyi da baki min aiki na ba?. “Kin san Darling d’ina ya kusa dawowa. “Ke harkina da wani saken da zakiyi bacci a gidan nan?. “Ko kin manta matsayinki na baiwa ne?. “Mtss na baki nan da 30 minutes ki gyara gidan nan, kuna in kin gama kije ki gyara ma only d’akinsa. “Zakiga kayan daya ciresu ki wanke su tass, kuma karkisasu a engine kinsan bai cika son wankin…. Sallamansu Xahra da Meesha luv ne yahanata k’arasa magana. “Oyoyo sis kune haka?. Cikin sakin fuska sukace”eh mune da mayya. Falmi tace”ni fushi nake daku ma rabon ku da gidan nan yau kunsan wata 2 fa. Meesha tace”kawas tuba muke amana hak’uri. “Sadeey tace” kyaleta kamar ita ta a zuwa mana a kai- akai. Falmi tace”kudai ku k’araso tukun sannuku da zuwa. Juyaa tayi ta kali Indo tace”keee mai kikeyi anan har yanzu baki mik’e kinyi aikin gaban ki ba?. “Ko sai na b’ata miki rai ne?. Sum-sum Indo ta wuce cikin gida. Xahrah BB tace”Falmi wacece wannan?. Cikin ko in kula Falmi tace”house girl d’ina ne. Meesha tace”kee baki da hankali zaki d’auko wannan zankad’ed’iyar budurwa, wanda duk na miji mai lafiya sai ya yaba da ita. Sadeey tace”tayani gani fa, amma kinyi gan-ganci. Falmi tace”kai banza haka zan barta, yanda nake da kishi ae ba zan so wani ya rab’i Haiydar d’ina ba. “Muna tare daku bari ku ga yanda zasu k’are in yadawo. “Kuma bana barinta tayi kwaliya. “Kai gasalima ya tsaneta tsana mai muni. Xahrah tace”kee baki san wani lokacin tsana yana dawo soyayya ba. Falmi tace”kee zan bar Haiydar hakane, san a haka ma baya son ganinta. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL-SHAKUR) RASH LUV [2:30PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [26/5/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-16~20. Shewa sukayi, hiransu ta yaushe gamo sukeyi. Indo ko kitchen tashiga, ta d’aura girki, tukun tayi side d’in Falmi, sai da ta gyara ko ina, sannan ta je bedroom d’in Haiydar ta gyara, ta d’ebo kayansa da sukayi datti, ta wankesu, tana duba abinci. K’arfe uku da ta gama komai, ta jera a dining. Falmi tace”ki kawo mana abincin mu falo”. Sai da da d’an rusuna tukun tace”to Aunty”. Taje ta zubu musu a cooler da plate takawo, Falmi cikin isa tace”kee wazai kawo miki ruwan ko ni zanje ba d’auko?. Indo ta rusuna tace”ayi hak’uri zanje na sauke abune akan wuta. “Mtss wuce ki d’auko kafin kiyi abunda zakiyi. Indo ta jera musu komai agun gar zata tashi Falmi tace”ni zanyi serving d’in ko sai na fad’a miki?. Indo ta tsuguna ta jera musu komai, tasaka ta mik’a musu, tukun ta mike ta nufi kitchen, don k’arasa sauran aikin da takeyi. Sadeey tace”Falmi baki da k’yau, gaskiya kina juya yarinyan nan. “Irin tsawan da kike mata ni har ta ban tausayi wallahi. Meesha tace”niko yarinya k’yau ta min gata black beauty. Falmi ta b’ata rai tace”mtss dad’ina da ke rashin ganewa, mai maza zasuyi da bak’ar mace. “Bakijin yanzu cewa suke su Fara ko da mayya ce, suna sonta. Xahrah tace”Falmi ae bazaki gane ba, sirrin k’yau yana tattare da bak’ar mace, don fara inda za’a kwashe farin ba komai zaki gani ba zai tsaban muni. “Amma magaanan gaskiya Indo ta had’u ba k’arya. “Sai dai rashin gyara da wayewa ne ya mata cikas. “Ki kali tsarin jikinta mana, irin shape d’in da maza keso ne. Take Falmi ta b’ata rai jin an kushe farare, don bak’aramin ji take da haskenta ba, gani take tafi kowace mace kyau. A haka har suka cinye abinci su, Indo ta fito ta tattara kwanuka ta kai kitchen, tana ajiyewa ta k’oma d’aki, ko zama batayi ba taji k’aran shigowar motar Haiydar. Sai da gabanta ya fad’i, addu’a tafara yi, sabida duk lokacin da suka had’u, bata kwashewa ta dad’i. Haiydar cikin takun isa ya shigo ckin gidan da Sallamansa, su Sadeey suka amsa, ganinsu yasa ya d’an saki fuska don yasan k’awayen Falmi ne sosai. Gaisawa suka kafin ya wuce d’akinsa, yana shiga wani sassayan, k’amshi ya bugi hancinsa. Ajiyar zuciyzuciya ya sauke, kayansa ya cire ya nufi toilet, yayi wanka ya fito, k’ananan kaya yasaka, sabida ga bak’i, da na shan iska zai saka. A hankali ya tako zuwa falo, Falmi tun da taga ya fito tasan in ba’a yi serving d’insa ba, zata sha surutu, cikin muryan isa ta fara kiran, Indo! Indo! Indo dake d’aki jiki sai b’ari yake ta fito da sauri, ta rusuna a gaban Falmi. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016] RashKardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-21~25. Notice Masu karatu, na cire Sadiya a k’awar Falmi, zan maidata k’awar Indo, sabida wani dalili, ku kasance da YAR’GIDAN JARAWA. Falmi tace”ke kwai bakinsan aikinki bane?. “Bakiga Haiydar ya dawo bane?. “Kije ki zuba masa abinci. Indo ta mik’e jikinta ba k’wari, sai bari yake, ta nufi dinning area, Haiydar ko tun da ya hango ta, yayi yar karamar tsaki, cikin zuciyarsa ko cea yake”wato falmin bata ji, nace mata bana son aikina tana saka wannan wariyan taki ji. “Dun taga ina qaunarta da yawa bana son abunda zai bata min rai. Indo tana zuwa dining ta fara serving d’insa, sai da ta zuba maza jelop d’in shinkafa yaji Salad, sai k’amshi yake tash, gaskiya Indo ba ya bace gurin girki, don ta taso cikin horon aiki, shiyasa bata samun matsala game da iya girki, gyaran guri. Wani lokacin in tayi decoration ta gyara ka d’auka, ba ita bace tayi, wasu daban akayi hayansu sukayi. Sai da ta zuba masa shinkafan ta tura masa gabansa, hannuta sai rawa yakeyi, a haka ta d’auko kofin glass ta zuba masa zob’o drink da tayi, ta d’auko zata ajiyea gabansa, hannuta sai b’ari yakeyi, bisa tsautsayi ya sub’uce ya fad’i aiko sai jikin, Haiydar, take rigansa tarine. Nan ganjin cikin Indo suka soma shooky, hawaye ta fara yi. Haiydar cikin b’acin rai yaga yanda ta b’ata masa jiki, ransa ya b’aci ya rasa mai zai mata, mikewa yayi har yazo zai tafi, sai ya fasa, d’auko juke d’in zobon yayi, ya shek’a mata a fuska. Ae ko sai cikin idonta take tafara mutsu-mutsu, tana niman hanyan saukowa, ganin abunda ya mata bai sheshi ba, sai da ya bari tana lalub’en hanya, ya saka k’afarsa ta fad’i timm! A k’asa, aiko ba shiri ta saki k’ara shiko ya mik’e abincin da bai ciba ya kima d’akinsa. Duk abunda ya faru a idon su Falmi, cikin jin dad’i tace”kun gani ko ita kanta yariyan tsoronsa take, bare shi uban gayya da baya son ganinta. Xahrah tace”to ki dai bi a hankali, don in wahala yayi wahala karta gudu. Falmi tace”ina zata je wa take dashi a Bauchi. “Ina ga ma la Uwarta cikinta tayi tazo ta haife ta. “Don tun zuwanta sai tana cemana ubanta Indo na raye, kulum maganan d’ayq kenan. Meesha tace”Xahra ya kamata mu wuce fa yamma tayi. Falmi tace”kai Messha wato ke kike zugawa ku tafi ko?. Duka sukace yau ai mun dad’e, mu zamu wuce sai gani na biyu. Falmi tarako su har gate kafin ta koma ciki. Haiydar ya fito zai wuce Falmi tace”darling bazaka ci abincin bane?. Ko kalonta baiyi ba yace”nagode fita zanyi. Ya na fita motarsa ya shiga bai zarce ko ina ba, sai k’aton katafaren gida, na alfarma, tun daga kan gate d’in, gidan abun kalo ne, horn yayi mai gadi ya bud’e masa, ya danna hancin motarsa, cikin gidan, gurin da’aka tanada don ajiye motoci, nan ya nufa, sai da ya ajiye motar ya fito. Gidan yana da girma sosai ko da na kali harabar gidan, zagaye yake da fulawas ja da yelo, sun matuk’ar k’awata gurin, a hankali yake takawa har yashiga cikin gidan, falo ya fara tararwa, ko da na kali falon, gaskiya ya tsaru komai na ciki Silver colour ne da baki, abun gwanin burgewa. Daga nesa na hango wata yarinya wacce bazata gaza 17yrs ba, tana danna waya, farace sol kamar Haiydar, kuma suna d’an kama amma shi yafita kyau sosai, da sallama ya k’arasa shiga ciki, Hasna ta mik’e tace” Yaya Haiydar sannu da zuwa. Cikin fara’a ya amsa mata, zama yayi a d’aya daga cikin kujerun dasuke falon. Yace”Hasna kawo min abinci naci”. Cikin tausaya ma Yayanta, mik’e wa tayi ta nufi kitchen, abinci ta kawo masa, sai da tayi serving d’insa, tukun koma gefe ta zauna. DEDICATED TO AISHA MUH’D ( MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]RashKardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-26~30. Cikin zuciyarta ko tana tausaya ma yayanta, wanan wani irin aurene ace mutum sam bai isa da matarsa ba, ko yasata abu batayi, ga rashin kunya, ga kin jama’a, Hmm Allah ya kyauta. Sai da ya gama cin abinci, Hasna ta kale Yayanta tace” Yaya Ya Indo?. “Ina son yarinyan tana da hankali, ga kirki wallahi, Hajiya ma tana yawan tambayanta. Wani harara ya sakar mata, wanda yasata jan bakinta tayi shiru, a zuciyarta ko cewa take”wai me Indo tayi ma Yaya ya tsaneta, ko sunata bai son a kira, kuma ni tafin Falminsa sau dubu wallahi. “Mtss ina ma da itace matar yayan. Maganan Haiydar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, da ta luka. “Hasna ina Hajiya fa? “Tana d’akinta. Mik’ewa yayi ya haura sama. Haiydar na fita Falmi ko kafad’a ta d’aga, alar ko in kula ta d’aki ta koma, WhatsApp ta hau taci gaba da chatting da friends d’inta. TUSHEN LABARI Alhaji Hashim Marad’i, Haifafen d’an Niger ne, ya kasance mutum ne mai neman na kansa, Allah yana bud’a masa, a haka har ya auri matansa Firdausi, bayan aurensu da kwanki ya tattara, yan dukiyarsa ya baro gari, ya dawo Bauchi da zama, shago ya bud’e, cikin ikon Allah, kasuwansa ta bun k’asa, Allah ya sanya ma dukiyar Albarka, nan da nan ya shahara ta ko ina a garin Bauchi. Ana haka Matarsa ta samu cikin karkuso kuga kulawa da tattali, har cikinta ya kai wata tara, ana haka nakuda ya tashi, baiyi wata-wata ba sukaje Asibiti, nan aka karb’e su, sai d’akin haihuwa. Bata dad’e sodai ba ta sankato, yarta fara sol, Nurse suka gyarata, suka dawo gida, ranan suna Yarinya taci sunan Fatima, Alhaji Hashim ya d’au son duniya ya d’aura ma fatima, baya son abunda zai tab’ata, Firdausi ma duk d’ayane, kula ta musamman suke bata, har yarinya tayi wayo ta girma sosai. Fatima tana da shrkara biyar, tayi wayo ko ina tana zuwa har sun sata a makaranta. Wani safiya ranar asabar, anyi ruwa sosai wata mata tana d’auke da k’aramin ciki, tazo qofar gidan Alhaji Hashim ta zauna, sai b’ari takeyi, ana haka Alhaji ya fito, ko da ya ganta, sai yaji ta bashi tausayi sosai. Mai gadi ya kira yace”kaje ka shigo da ita, gida ya koma ya samu Hajiya Firdausi, yace”ga wata mata tana buk’atar tai mako, ki bata duk abunda ya dace. Tukun ya fita. Firdausi tasaka a ka shigo da matar sai yatdina take, ganin kayan jikinta yasa tace”ke biyo ni boys quater ta kaita, nan ta ce bara na kawo miki abinci. Cikin gida takoma ta d’ebo abinci ta kawo mata, nan matan taci sosai, tayi godiya ma Allah. Ko da Firdausi ta dawo, tace” ina zaki kuma daga ina kike?. “Matar tace”ni bakuwace banda kowa na fito garin Yola ne. Firdausi tana wani isa tana yatsina tace”ok kya iya zama anan kafin mai gidan ya dawo. Bata jira amsanta ba ta fita a d’akin, Alhaji Hashim bai dawo ba, sai yamma sai da yaci abinci, tukun yana hutawa, Firdausi tace”matar nan fa tana na. “Oh! Na manta mai ta sanar dake gameda ita, don naga kamar ba’a cikin nutsuwarta take ba. Firdausi ta mayar masa yanda matar ta fad’a mata. Yace”kira min ita. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-31~35. Firdausi ta kirata, suka taho tare, can gefe ta zauna, sai da ta gaidasu. Alhaji Hashim yace”baiwar Allah ya sunanki?. Matar nan tabashi amsa da”sunana Safinatu”. Alhaji Hashim yace”matana tamin bayani yanda kika fad’a mata. ” ko zan iya sanin mai ya kawoki Bauchi?. ” nan take matar ta fara kuka, tace”Ni sunana Safinatu, ni haifafiyar garin Yola ce. “Ina gaban k’anin mahaifina, na taso cikin kulawa, har na girma, duk ran laraba, ake cin kasuwar garin mu, kuma duk ranan laraba, na ke kai tallen nono, cikin garin mu na Girei, a haka har Allah, ya had’ani da Muhammadu, shikuma yana kawo shanu, duk ran kasuwa, yana da zama’a Rugan Ribad’o. Ko da muka dai-daita kamu, nan iyayena suka mana aure. mijin dana aura ya kasance yanada garken shanu sosai, hakan yasaka wasu ke jin haushinsa. Har suna masa gorin zuwa yayi, duk da shima bafulatanine, kwanaki suka tafi, kulum garken shanunsa sai hab’aka yakeyi, hakan yasa mak’iya suka fara kawo masa hari. Tundaga likacin ya fara sanar dani, duk da banjin dad’i, ina fama da laulayin ciki. Bayan wasu watani, lokacin cikina ya fito, dadadare muna kwance, wasu yan rugan mu suka zo donsu kashe, Muhammadu su kwashi dukiyarsa, ganin hakan ya d’ebi, kud’i yaban da wasu hotuna, tare da awarwaro, yace na rike wannan. Ya kad’a shanunsa muka d’au hanya muna tafiya, su Sale suka biyo mu, sunyi artabu da Muhammadu, da kyar Allah ya basu ikon kwad’a masa sanda’a kafad’a, ganin bazai iya kare kansaba, yace”Safinatu ki gudu ki tafi garin Gombe ki nimi yan’uwana, suna Gombe. Kafin yayi wani magana sun kwad’a masa sanda take jini yasoma zuba, a gun ya fad’i ko motsi bayayi. Ganin ina kuka Sale yace”ku kamata don zata iya tona mana asiri, jin haka nasa gudu. Haka har Allah ya taimakeni na fito bakin titi, saiga mai mota na shiga ya kaini, cikin gari nasamu motar Gombe ta tashi, sai na Bauchi, nan wasu sukace, idan ina sauri na shiga na Bauchi, haka nashiga motar Bauchi, ko da na iso yan kud’i na sun k’are, hakan yasa nayita yawon bara, gashi bansan ta inda zan fara niman dangin Muhammadu ba. Alhaji Hashim ya nisa, Yace”naji labarinki, kuma a yanzu niman mutum batare da wani Address ba, ba k’aramin tashin hankali bane. Awarwaro ba zai zama abun shaidan da har za’a gano suba. Firdausi tace”Alhaji mai zai hana tana mana aiki sai ana biyanta, tunda Lami tayi aure wancan Satin. Alhaji yace”haka za’ayi. Ya kali Safinatu yace”Safinatu sunanki ko?. Tace”masa eh! hakane. Yaci gaba da cewa”zaki iya yin mana aikatau, ana biyanki duk wata?. “Kuma zamu baki d’akin da zaki zauna har sai lokacin da kika buk’aci tafiya?. Cikin girmamawa tace”eh zan iya. Alhaji yace”Alhamdulilah! Firdausi zata gwada miki komai. “Sanna salary ki a wata dubu shabiyar. “Tace”nagode Allah ya ban ikon kiyaye komai. Haka tamik’e ta koma d’akin, tundaga wannan rana tadawo itace wankin kayan Fatima da wanke-wanke, ga shara, abunci sai da Firdausi ta koya mata. Duk wani abu ita takeyi. Ana haka har ta haihu, cikin ikon Allah a gida bataje Asibiti ba. Ranan suna yarunya taci Sunan Aisha, amma tana kiranta da Indo, haka rayuwansu ta kasance. DEDICATED TO AISHA MUHAMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RAS LUV 5/27/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-36~40. Aishatu Indo ta girma sosai,, gata da wayo, Indo tana d’ibi dani amma wasu abubuwanta na haifinta ne, hatta muryanta irin nasane, kwayar idonta, yatsun k’afarta duk nasane, bak’in fata na ta d’auko. Gata da gashi kamar me, ganin Indo tayi wayo ga Fatima tana zuwa makaranta, ko d’an abu ya had’asu, karara Fatima ke mata gori, Aisha tayita kuka. Hakan yasa na duba wani private school d’in da ke nesa da gidan mu nasata, 30k ne kud’in makarantan, amma duk term zan bada 10k hakan yasa na sakata a Sky criest, kulum da sassafe zan shiryata, na d’aukota a kafad’ana da kafa zan kaita. Ina dawo gida nayi aikina da wuri inje na d’aukota. Da kud’in aikina nake biya mata, dubu shabiyar, duk wata ake bani kud’in aiki. Kuma ba abinda nake da kud’in kasancewan su suke ciyar damu. Sai in Sallah yazo nayi mana kayan Sallah. Ahaka har Aisha tashiga Junior school, ina biyan mata, na sata a Islamiya, sam Aisha bata isa tayi k’awance da kowa ba Fatima wanda a tana Senior Secondary school, ta sata a gaba, yanzu Aisha itama tana tayani aiki, sosai mukeyi tare. Fatima tana SSS3, a Doll pine Maria, ta canza sunanta daga Fatima ta dawo Falmi, hatta Baban da Falmi yake kiranta, tana harka da kwaye wayayu, masu nutsuwan kenan Meesha da Xahra BB. Sune masu hankali. A haka ta kamala secondary school d’inta. Ko da result yafito sam baiyi kyau ba. Hakan yasa ta fara diploma, tana karanta estet management. Tana final semester, ranan ta fito a motarta, dai-dai Bauchi club, motarta ta tsaya. Ga dare ya farayi, tun daga nesa ta hango wani mota Range Rover baka, bakowa bane aciki face Aliyu Haiydar. Da kamar zai wuce ganin macece tana buk’atar taimako hakan yasa ya, ko da yazo da sallamansa ya mata, ta amsa. Yace”lafiya mai ya samu motarkin?. “Wlh ina tafiya naji k’aranta ya canza, kafin nayi wata-wata ta tsaya. Bud’e motar yayi, yayi nasa iyawar taki tashi, hakan yasa yace”in bazaki damuba in taimaka miki. Tace”ba matsala. Wayarsa ya kira mai masa gyara yazo ya d’au motarta, tare ma da bata address d’insa, abunda yasa bata damu ba, taga Haiydar cikin kayan Police, shiyasa tasan ba zai cutarta ba. Motar suka shiga ya kaita har qofar gidansu, zata fita tace”nagode da taimako gashi zamu rabu bamu san juna ba. Murmushi yay8 yace”Sunana Aliyu Khaleeb Baba, ama ana kirana da Haiydar wasu kuma sukan ce min AK Baba. Cikin yanga tace”wooow nice name!”. “Ni kuma sunana Fatima Hashim Marad’i, amma ana kirana da Falmi. Cikin fara’a yace”suna mai dadi. “Ku ya Niger ne?. Tace”masa eh zamane ya kawo mu Bauchi. Nan sukayi exchange d’in phone number, tamasa godiya tashiga gida. Kwanki sun tafi, yanzu Aisha tana Jss3 suna third term, ranan jumma’a ranar da Aisha bazata manta ba a rayuwanta, shine randa ta wayi gari mahaifiyarta ta rasu, ranan tayi kuka, ta dawo bata kowa bata da gata sai Allah. Bayan kwana

Chapter 1 of 9