Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
a b’akar ma yar aiki, wanda bata wayeba. “Mtssss halama ko secondary school batayi ba?. “Gashi hajiya fiskanta ba alamar wasa aciki. “Dole nasan matakin da zan d’auka. “Don Indo da k’afarta zataje tace ma Hajiya bata son auren. Wani lallausan murmushi ya saki. Falmi ko tana shiga d’aki ta kira wayar Mum d’inta yakinshiga, ganin wannan kukan bazai fiddata ba, tafito d’akin Haiydar ta nufa tana kuka wi-wi da hawaye. Qofar ta tura tashiga tana zuwa ta fad’a jikin Haiydar, kuka mai tsuma zuciya ta saki. Haiydar jin Falmi ajikinsa duk ya rikece, bare yana hannu, take yasa hannusa ya fara share mata hawaye. A hankali yace”Falmi duk ke kika jawo mana. Cikin muryan kukan tace”pls kaje kace ma Hajiya ta hak’ura ni bada nufin ayi auren na fad’a ba. Na fad’a ne irin nagana rainamata, ko kamarta gwara kanemo a waje. Ajiyar zuciya ya sauke yace”karki damu zanbi duk hanyan da ya dace. Haiydar ya lalub’o bakin Falmi ya had’a danasa, a hankali yake mata masu salo mai rikitarwa, duk wani gab’ar cikinta yana bi yana aika musu da sak’o mai sanyi. Cikin nuysuwa ya soma cire mata kayan jikinta Falmi ta rike hannusa, cikin da shashiyar murya yace”kinga irin abun ko mai yasa kike hanani kanki. “Why! Why! Why! Falmi”. Ganin da gaske wai ita fushi take hakan yasa shikuma bazai iya hak’ura ba, ta k’arfi yasoma cire mata kaya. Hajiyansu Haiydar wanka zata shiga, cikim gaggawa ta yi wanka tasaka kayanta, da fara’a ta soma sauk’owa k’asa, tana mai farinciki yau zata yi surka ta gari mai nutsuwa. Don yanda takeyi Husna na yabonta, gakan yasa da Falmi tayi gatse, itakuma ta mayar da gaske, don rasan watarana Falmi zatayi danasani. A hankali take tafiya ta kusa sauk’owa daga step, ta soma jin muryan da ko a mafarki bazata manta shi ba. Ko a wani yanayi take bazata manta da muryanan ba. Duk da shekara ishirin da d’oriya. Cikin hanzari tasoma sauk’owa step d’in don gani take, tankar mai muryan zai gudu. Nima Rash ganin haka yasa nace barana biyo Hajiya. To madu karatu wani murya ne Hajiya ta tsinkayo a falo?. Shin Hajiya tana gane mai muryan nan kuwa?. Donjin wannan amsar ku biyo YAR KARDAMAWA. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-81~85. Cikin hanzari ta soma sauk’owa daga step d’in, don ko makawa babu, wannan muryan Lamid’o ne. Jikinta har b’ari yakeyi, da sauri ta isa falon, sam su Indo basu san, hajiya ta isoba. Sabida karatun da ke tashi a falon, gashi hankalinsu gaba d’aya, yana kan hotuna. Hajiya ta dad’e tana kalon Indo, cikin zuciyarta ko cewa take, “tabbas wannan jinin Lamid’o ne. “In kuma ba haka ba to kaman yayi kama. “To tayama za’ayi ace jinin Lamid’o ne, bayan Lamid’o da’akace ya mutu, har anga tokan gawansa. Jikinta duk ya mutu, da kyar ta iya jan kafarta, zuwa cikin falon tare da yin sallama. Indo a hankali ta d’ago kanta karaf suka had’a ido, take k’irjin Indo ya bada rass! Rass!, kasa d’auke fuskanta daga kan hajiya tayi. Cikin zuciyarta ko cewa take”wannan kamar matan, dana ke gani a photo da Umma tace na Baba nane. “Sai dai wannan ta tsufa wancan kum yarinya ne. “Hmm to nida bayida yan uwa ma. “Kai inaga kama ne, kawai sukayi da matar. Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali, ta sunkuyar da kanta, cikin girmamawa tace”sannu Mama anyini lafiya?. Hajiya da takasa b’oye mamakinta a fili, sai da Hasna tace”Hajiya ana gaidaki ne fa. Firgit ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula, cikin fara’a tace”lafiya Aishatu”. “Ya aikin dai? Indo kanta a k’asa tace”Alhamdulilah!. Can sukayi shiru, don Hajiya tana jin wani abu gameda Indo, ta dawo mata da abunda ya wuce, shekara ishirin da d’oriya. Cikin dauriya hajiya tace”Hasna taci abincin kuwa?. Cike da girmamawa Hasna tace”eh hajiya. Hajiya ta kali Indo tace”Aishatu nina aika ki zo keda Husna. Kan Indo a k’asa tana wasa da yan yatsun hannuta, masu kyau gasu dogaye gwanin burgewa. Hajiya taci gaba da cewa”Aisha ina son ki d’auken a matsayin Mahaifiyarki, kuma wacce zata baki umarni ki bi. “Aishatu! Ta kira Indo, cikin girmamawa Indo ta d’ago, karaf suka gad’a ido, take taji wani qaunar Hajiya ya shiga jikinta, kuma ta hango tsananin soyayyan uwa da d’a acikin kwayar idon Hajiya. Indo ta amsa da”Na’am Mama!. Hajiya tace”Aisha ina rok’on wani alfarma a gunki, kuma ina so kimin alkawari. Zaki amince da duk abunda na fad’a miki. Indo cikin sanyin murya tace”Mama ae ke uwace. “Duk umurnin da kika ban zan kasance mai biyayya a gareki, matsawan bai sab’ama addini ba. Hajiya tace”Alhamdulilah! Nagode Allah ya maki Abarka Aisha. Indo ta amsa da”Ameen ya Allah. Hajiya tacigaba da cewa”Aisha inason na had’a ki aure da d’ana Haiydar. Cikin rud’ewa ta d’ago fiskanta, don ta gaskata mai kunneta ke jiyomata. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/30/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-86~90. Cikin rud’ewa ta d’ago fuskanta, tabbas Hajiya da gaske take maganan, hmm cikin zuciuarta kam cewa take”anya Hajiya tasan mugun tsanar da Haiydar yamin?. “Taya ma zanyi na auri mijin Aunty Falmi. “Ina bazan iya ba Hajiya ki canza. Tana wannan tunanine ta ji muryan Hajiya tana cewa”karki damu nasan tunaniki Fatima ce ko?. “To ita da kanta ta zabi hakan. “Kuma shi Haiydar d’in ma ya amince. Indo sam gani take kamar ma farki abunke faruwa. Hajiya tace” ina fatan bazakiyi min jayayaba. Indo haka kurum ta tsinci kanta da d’aga ma Hajiya kai ta amince. Hajiya albarka tayi ta sa mata, tukun ta mik’e tace”barin hau sama zan yi wani abu. Hasna ne ta amsa da”to Hajiya. Hajiya na tafiya Indo ta fashe da kuka sosai, Hasna ta dawo kusa da ita tace”Aunty Aisha kiyi hak’uri nasan Hajiya bazata tab’a cutarki ba. “Kuma wataran zakiyi alfahari da aurenku. Indo cikin kuka tace”Hasna kin san yanda Yayanki ya tsaneni kuwa?. “Sam baya k’aunar ganina ina numfashi. “Bazan iya kishi da Auntyn Falmi ba Hasna. Hasna tace”hak’uri zakiyi komai zai yi dai-dai. “Kuma batun Ya Haiydar ke zaki ja ra’ayinsa da naki salon. “Amma sai kin dage kin kuma daure. “Tashi muje d’akina in miki make-up, don tare zaku koma in yazo. “Zan kuma baki wasu kaya kina kwaliya sosai. “Ki bar zama ba gayu pls. Hannu ta takama suka haura sama, Hasna ta wanke ma Indo kanta ta gyara ta sosai kamar ba ita ba. Wasu sababin kayanta, da bata saba ta bama Indo, tare da had’a mata kayan kwaliya mai yawa. Falmi ko ita da Haiydar kokuwa suka sha, da k’yar ya rabata da kayan jikinta, sarrafata yasomayi son ransa. Falmi ihu take masa tana cewa”tunda ka amince ma Hajiya sai kaje gun Indo ta baka kanta, banda ni Falmi, tana kuka tana dukansa. Shiko gogan bai masan tanayi ba, sha’aninsa kawai yakeyi. Falmi ta wahala kam, don taki tsayawa, sai da ya d’ibi 2 hours masu kyau, kafin ya koma gefe yana maida numfashi, a hankali ya matso kusa da ita, ya rungumota yace”Falmi ina matuk’ar sinki, amma ke kike jawomana duk abunda suke faruwa. “Mai yasa kike guje ma shimfid’ata?. “Ina kiraki bak’ya amsa min why Falmi?. “Kuma kinsan ni na kasance mai yawan bukata Fatima. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKIR) RASH LUV [5/30/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-91~95. “Mtsss Falmi ta saki wani tsaki tare da mik’ewa tashiga wanka, sai da tayi wanka tana fitowa, kalo d’aya Haiydar ya mata, ya mik’e ya nufi bayi wanka yayi ya fito, yazo gunta yanyota jikinsa yayi, cikin salonsa na rikitarwa yake shafa bayanta, yace”haba my Falmi kinsan ba wata macen da zata tab’a sayen zuciyata. “Ni nakine ke kad’ai kuma ina qaunarki. Kalon banza ta masa cike da masifa tace’ kai Haiydar kasani nayi danasanim aurenka ni Fatima. “Gashi yanzu ka jamin kayan raini. “Wacce nake gani a k’ark’ashina, wai ita zata dawo kishiyata. “In sam ba zai yiwu ba ina. Haiyadr cikin muryan lalashi yace”kinsan bazan tab’a had’aki da wata ba. “Aure ai kamar an fasa tunda baki so. Hararansa tayi tare da d’iban kayanta ta fita. Haiydar ko mai ya sha, tare da saka kayansa, ya d’auki key d’in motarsa, don zuwa amsa kiran Hajiya da bata hak’uri ta janye k’udirinta na batun auren Indo. A gidan su Hajiya kuwa, Hasna ta wanke ma Indo kai, ta gyaramata tare da busar mata shi da dryer, alwala sukayi suka gabayar da Sallah magriba, suka jira sai da akayi Isha’i nan ma sukayi, Hasna tace”Aunty na zo ki zauna gaban madubi kiga wani abu. Ba musu Indo tazo ta zauna, Hasna ta gyara mata fuska, ta gyara giranta, ta fara mata kwaliya, ni dai Rash ina gefe ina kalon ikon Allah, don naga shafe- shafen da goga wancan yayi yawa. Indo tace”kai Hasna nikam abun ae zai min yawa. Hasna ta k’yalk’yale da dariya, tace”Aunty na ki tsaya ke dai kiyi kalo kawai. Murmushi Indo tayi. Hasna tayi kealiya ma Indo, tare da d’auko mata, wani atamfanta riga da skirt, mai kalan ja da bak’i. Indo ta karb’a ta shiga bayi ta saka, tana fitowa Hasna sai murmudhi take, Hasna tace”zauna ki gani. Indo tace” oh ni kam Hasna har yanzu duk a make-up d’inne haka?. “Ina zani da kwaliya bacin yanzu bacci zanje nayi. Hasna tace”Aunty bazaki gane bane. Hasna ta d’aura mata d’an kwali, ta mik’o mata flat shoe, shima kalan ja da bak’i, sai gyale shima ja da bak’in, yana da stone farare, sai haskawa sukeyi, ne sa kad’an Hasna takoma, tana kalon indo, cikin muryan farin ciki tace”wooow My Aunty na you look so beautiful. Muryan Hasna danaji yasa ni Rash na d’ago da sauri, bansan lokacin da wayata ta sub’uce ta fad’i ba. Ba abinda na furta sai kalman”tsarki ya tabbata ga Ubangiji daya k’agi wannan k’yak’yawan suran. “Hmm masu karatu kuyi Imagine d’in Indo a cikin wannan shigan, ya kuke gani zata haska?. Hasna ta fara yabon Indo, tare da d’auko wayarta tashiga d’aukarta photo. Haiydar yana shigowa gidan su Hajiya, d’akinta ya nufa, da sallama ya shiga, ta amsa masa, bayan ya gaidata, Hajiya ta fara masa nasiha mai ratsa jiki, sanan tace”kar kuma naji kasake cewa kalman da za’a fasa aurenka da Indo. “Wataran in Allah ya yarda zakayi alfahari da hakan. Ta dad’e tana masa kalamai masu tsuma jiki, wanda dole yafasa abunda yaso fad’a mata. Hajiya tace”katashi muje ku tafi, in Abba ka ya dawo duk yanda muka tsayar dashi zakaji. “In zata dawo gidan nane kafin ayi aure to ko kuma ta zauna acan, duk sai in ya dawo zamu tattauna. Jiki bak’wari Haiydar ya mik’e suka fito falo, Hajiya ta kira wayan Hasna tace”ku sauk’o k’asa ke da Aisha. Bata jira amsansu ba ta kashe wayar, Hasna ta kama hannu Indo suka fito, suna saukowa kenan Haiydar ya d’aga kansa, dake yana kalon saitin step d’in. Daram! K’irjinsa ya buga, kasa d’auke fuskansa daga kalon Indo yayi, tun dayake da ita yaune rana ta farko da ya fara ganinta da kwaliya, kuma ta saka gyale, gashi shara-shara. Sai da suka iso falon, suka zauna Hasna ta gaida shi, haka Indoma. Hajiya nasiha ta musu sosai tukun tace”ku tashi muje ku tafi kar dare yayi, duka suka mik’e Hajiya ta kama hannu Indo, da kanta tasakata a gaban motar, ta lek’o tace” Aunty na sai kin jini. Wani mugun kalo Haiydar ya sakarmata, bashiri ta jabakinta ta bar gun, ta damotan dukayi yabar haraban gidan, sai da sukayi tafiya mai d’an nisa, kafin suka iso qofar gidansa, horn yayi mai gadi ya bud’e masa suka shiga. Indo ta bud’e qofar mota tafita, hartayi nisa Haiydar cikin tsawa yace” kee tsayawa tayi bata juyo ba, cikin zafin nama ya nufota yana huci kamar zaki, da k’arfi ya k’ara cewa”Kee bakiranki nakeyi ba. Cikin razana Indo ta juyo sam batasan Haiydar ya tahoba, aeko jiyowanda zatayi, sai a k’irjinshi tasamu mzauni, Falmi ko jin muryan Haiydar yasa tafito, hmm dai-dai lokacin kuma Indo ta fad’a jikin Gaiydar bisa tsautsayi, Falmi wani razananen k’ara tasaki, tare da yi kukan kura tayi kansu. Ni ko Rash jin irin gurnanin da Falmi tayi yasa na arci na kare. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-96~100. Indo na fad’awa jikin Haiydar, wani sanyi da ni’ima yaji ga wani lafiyayen k’amshin dake tashi daga jijinta. Bai san lokacinda ya mayar da hannusa, yazamana ya mata rumfa, sosai ya matseta a jikinsa, take ya sake wani sassayan ajiyan zuciya. Indo ko jikinta ya fara b’ari, hawayene ya soma zubo mata, don tunda take a rayuwanta, namiji baligi bai tab’a ko da rike tafin hannuta ba. Haiydar ko sai wani shashafa bayanta yakeyi da d’aya hannusa, d’ayan kuma ya sauko dashi kan wuyanta, take yaji wani laushin da bai tab’a ji ba, duk farin da Falmi ke dashi da laushin jikinta, bai kai na Aisha Indo ba. Indo tana kiciniyar kwacewa sai dad’a kamata yakeyi, don Haiydar ya manta wani duniya yake ne d’aya, ko ni Rash dana leka fuskansa, ya wani lumshe ido, tankar mai bacci. Falmi ganin haka tayi wani kukan kura tayi kansu, Indo ta ta tsin kayo muryan Falmi, tak’ara kaimi gun tureshi. Amma shiko sai k’ara rungumeta yakeyi, Falmi da ta saki wani ihu ta k’araso gurin, wani naushi ta kai ma Indo, amma kash!! Cikin rashin sa’a Indo tasamu ta kwace, sai ta samu Haiydar a k’afa, Indo na kwacewa tayi cikin gida da gudu, d’akinta tashiga tasaka key a qofar. Falmi ko shan kwalan, Haiydar tayi tana ihu tana cewa” munafuki ae daman kana Sonta kake b’oyewa, maci a mana kawai, MAYAUDARI, butulu mai sakayan Quna da kiyayya, waya sani hala kulum d’akinta kake zuwa kuna iskancin ku. Kafin ta k’ara yin wani magana, Haiydar ya sauke mata wasu lafiyayun mari, tass! Tass! Tsss! Kakeji, cikin zafin rai yace”asai bakida hankali?. “Ni Haiydar kike ma cewa d’an iska?. “Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, tunda nake bantab’a lalata yar wani ba. “Har zaki ambaceni da wannan mumuna kalma. Take idonsa ya canza kala tsanani bak’inciki nake hangowa a kwayar idonsa. Cikin kausashiyar murya yace”duk wani abunda ke faruwa ke kika haddasa. Falmi cikin mafifa tasake yo kansa da niyar kamasa da fad’a, yace” kik kuskura kika tab’anini hmm sai na lahira ya fiki jin dad’i. “Mtsss ya wuce yayi cikin gida zuciyarsa na masa rad’ad’i. Wannan wani irin masifa ne, d’akinsa ya tura ya shiga, kayan jikinsa yasoma cirewa yaji kashin jikin Indo ke tashi, har zai ajiye sai yabsamu kansa, da sanya rigan a hanncinsa, yana shakan daddad’an kamshinta, harda lumshe idanu, take abunda yafaru d’azu yasoma dawo masa. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/30/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-101~105. Manna rigan yayi a sai tin hancisa yana shak’an k’amshi, sai ya tsinci kansa cikin nishad’i. Hasna da Hajiya suka koma cikin gida cike da farin ciki, Hasna tace”Hajiya gaskiya naji dad’i wannan al’amarin. Hajiya tace”hmm ae ni nafi kowa farin ciki wallahi. “Sabida Aisha tana da nutsuwa a kalon dana mata. “Kuma haka kurum kalonta danayi sai ta tuno min da Lamid’o na. “Muryansu na tsananin kama, kai hatta murmushinsu iri d’aya ne. “Ko d’azu dana ganta shi kawai nake tunawa. Hasna tace” Allah ya shigan sa. “Hajiya dan Allah in Abba ya dawo in za’asa bikin nan kar asa da nisa. “Inason ayi a kare don gudun makircin matansan nan. Hajiya tace”makircinsu ya kare musu su kad’ai. “Yanzu na gane komai addu’a kam yanzu na fara masa da ikon allah. Haka har suka iso falo hiransu ta yai duk akan Indo da Haiydar ne. Falmi kuka taci agun da k’yar ta iya jan k’afarta zuwa d’akinta, wayarta ta d’auko ta kira Mum d’inta cikin kuka take fad’a wa Mum. Mum tace”jakar uba tun ba’aje ko ina ba?. “Ina fatan kin mata duka kin nakasata?. Falmi tace”tagun cikin d’aki ae. “To ki tabbatar kin bata najaki sosai. “Yanda ko gobe ance ta kali Haiydar bazata kaleshi ba. “Kiyi shiru gobe zanje gun Malam ya duba mana abunda zai biyo baya. Haka sukayi sallama, Falmi ranan ko wanka ba tayi ba ta kwanta bacci. Jikinta duk ba k’wari tafito falo, tun daga nesa takejin nishi, da sairi ta k’araso, turus tayi don abunda ta gani ya matuk’ar razanata, Indo ne sanye cikin wani mini skirts, ya matuk’ar kamata sosai, k’afanta d’aya na kan kujera, d’aya kuma Haiydar ya d’aura akan cinyansa, rabin jikinta yana nata, hannusa yana kan k’irjinta, sai sarrafa na fulaninta yakeyi, a hankali ya kai bakinsa kan nata, tsotsansu yakeyi kamar ya samu lollipop, yana wani nishi. Indo ko sai wani smiling takeyi, tana k’ara rungumosa, Haiydar cikinsanti yake cemata”Ina matuk’ar qaunaki, ke dabance acikin mata. “Tundanake kiss bantab’a jin dad’i irin yanda nake ji dak…….. Cikin k’araji ko salati babu Falmi ta…….lol…. Masu k’aratu sai gobe, maji yanda za’a kaya. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-106~110. Cikin k’araji ko salati babu ta farka, daga mumunan mafarkin datayi cikin baccinta, duk sassan jikinta rawa yakeyi, kasa hak’ura tayi, tana ga kamar abun da ta gani a mafarki, shi zasu aikata a zahiri. Da sauri ta duro daga kan gado tayi hanyar qofar falo, tsit kakeji ba kowa sai k’aran fanka. Wani ajiyan zuciya ta saki, tare da zuwa window d’akin Indo ta leka, Indo na kwance tana baccinta hankali kwance. ‘Dakinta ta koma ta kwanta itama. Haiydar ko da ya rungume rigan can kuma yayi tsaki”mtsss wai me hakan ke nufi?. “Ni bana son raini kar yarinyan nan tazo ta rainani. “Amma fa gaskiya yau tayimin kyau. “Kamar ba itaba wallahi. “Mtss to ina ruwana ma da kyanta?. A haka yayi wanka ya kwanta bacci. Hajiya Fiddausi taje gun boka, a duban da yamata, ha hango zallan koyayar da Haiydar ke ma Indo, don haka yace mata karta damu, su hak’ura ayi auren, don in basu bari anyi da Indo ba, to fa ba makawa sai yayi aure. Hajiya tana dawowa ta sanar da Falmi duk abunda ake ciki, amma tace”karta ragarmata, ta yanka mata kazan wahalan da bazata iya figewa ba. Indo ko wasan b’uya suka shiga yi da mutanen gidan, dan tabbasa tasan abunda ya faru, Falmi bazata kyaleta ba. A gidan Hajiya kuwa Abba ya dawo ta sanar masa da komai. Yace”zaiyi bincike akan yarinyan, bayan kwana biyu da yayi bincike, duk wani labari ya samu gameda zaman gidan su Falmi, ta hankalin Aisha ila dai rashin mahaifinta da basu saniba. Hakan bai damesa ba yana dawowa gida ya mayar ma Hajiya, yace”inaga bikin nan da wata guda kawai, inyaso komai da uba ke ma yarsa, ni na d’au nauyi zanmata. Hajiya cike da murna ta masa godiya, Haiyadar suka kira sukace”yazo yasamu Abban sa, zasuyi magana da shi. Haiydar da yazo Abba yace”mun tsayar da biki nan da wata d’aya dan haka kaje ka fara shiri. “Sannan zansa a gyara maka gidana da ke bayan Airport nan zaku zauna tunda part biyu ne a gidan, kuma tsarin gidan yayi kyau. Haiydar godiya yayi ya tashi ya fita. Hajiya ta mik’e tabi bayansa, a falo ta samesa, ta zauna ya kara gaidata ta amsa, tace”kaji yanda al’amarin ya kasance ko?. “Dan Allah inaso ka d’au komai da sanyi wataran zakayi alfahari da auren nan. “Sannan ina son ka kawo kud’i zamuje mu had’a kayan lefe dana fad’an kishiya. Haiydar cikin girmamawa yace”to zan ciro kud’i zan kawo muku. Hajiya ta sanya masa albarka ya mata sallama.ya tafi. Bayan kwana biyu, Hajiya ta aika Hasna ta je ta d’auko Indo, da duk abunda take da buk’ata, don in ta bar gidan Falmi, ta tafi kenan sai in sun had’u a gidansu. Hasna jiki na b’ari tayi wanka ta d’au hanya, tafiya mai d’an nisa tayi kafin ta isa gidan, horn tayi mai gadi ya bud’e mata, tashiga da murnanta tayi sallama. Turus ta tsaya sakamakon ganin Falmi da tab’arya a hannuta, tana tsaye a qofar d’akin Indo tana son ta shiga ta kwad’a mata. Hasna tace”Aunty Falmi lafiya kuwa?. Cikin fushi ta huyo tace”to bak’ar munafuka algun-guma. “Har wani tambayan lafiya kikeyi? “Bacin duk wani muna furcin da ake had’awa dake ne, da tdohuwar uwar ta…. Bata k’arasa ba taji saukan, lafiyayyen mari a fuskanta. Cikin zafin rai ta d’ago da niyar kwad’a ma Hasna tab’arya don a zatanta Hasna ce ta mareta, amma me cikin mamaki take kalon wanda…… DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [5/31/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A. Pg-111~115. Cikin mamaki take kalon Haiydar yau ita zai mara a gaban Hasna ga Indo, shikenan ai raini kam yagama jan mata yau, cikin muryan kuka tace”Haiydar ni ka mara?. “Kamaren? “Lallae yau zakasan ka maren?. Haiydar yace”na lura bakida kunya wato?. “Duk iskancinki ya tashi a kaina harda uwata ko?. “Don akan auren da ba so nake ba?. “Mtss ki sani ni uwata ta isa dani dole ta ban umarni nabi. “Kuma duk randa kika k’ara zaginta sai kinga abunda zan miki wallahi. Kalon Hasna yayi yace”kekuma mai kika zo yi ne?. Hasna tace”Hajiyace tace nazo in tafi da Indo. Kafin Haiydar yayi magana Falmi tace”ai daman na fad’a bakinku d’aya gashi nan. “Yauko ba wanda ya isa ya fita da Indo a gidan nan. “Tunda ni na kawota a k’ark’ashina take. “Kuma dalilina kuka santa, dan haka ba wanda ya isa ya fita da ita. Haiydar yace”kinyi k’arya mahaifiya ta ke son ganinta dole taje ta. “Don na san darajanta. “Hasna zo ki mata magana ku fita ina nan gurin. Falmi ta gyara d’amaran skit d’inta, tace”inga mai fitan da ita yau?. “Shege ka fasa, yau ko ni ko Indo. “Wai dad’in abun ma shegiyace, a titi akayi cikinta yar kwararao ne. Ran Haiydar sai tafasa yakeyi, don yatsani kalman cikin shrge ko yar shege. Hasna tasaka Indo ta b’ud’e qofar d’akin, sai kuka takeyi sosai. Hasna tace”Aunty ki tattara duk wani abunda kike buk’ata, don in kin tafi bazaki dawoba. Indo bata iya tanka mata ba sai kukan da takeyi, Hasna ce ta taimaka mata suka had’a kayanta, a yar madai- daiciyar trolley d’inta suka jawo zuwa falo. Indo ko sai kuka takeyi, kalo d’aya Haiydar ya mata yaji ta bashi tausayi, yaune rana ta farko da Haiydar ya fara tausaya mata, Falmi tana ganin sun fito tayi kansu, cikin zafin nama Haiydar ya samata k’afa ta fad’i, kanta yayi ya mata kyakyawan runguma, yanda bazata iya kwaceba. Hasna su ganin haka suka fita. Haiydar sunsha rigima da Falmi sosai, don daga k’arshe kuleta yayi a d’aki ya fita abunsa. Hajiya kaya na dai-dai misali suka had’ama Indo na lefe, a kwati hud’u da kit, sai kuma Falmi sun mata biyu da kit itama. Hajiya damtse ta zage gurin gyara Indo, Haiydar ko abun duniya ya ishesa, don sam bai son wannan aure. Shiyasa ma ko ya fad’a ma wani yayi shiru, Hajiya ko ganin haka tasaka a ka kira mata abokinsa, Sadiq ta sanar masa, tace”ya kuma shirya duk wani abumda ake buk’ata, zata bada kud’in. Yau ya kai kayan fad’an kishiya suka nufi gidan Falmi, da Sallamansu suka shiga. Hajiya Firdausi da ke kitsa ma Falmi makirci, ta amsa musu, cike da mamaki suke kalonsu, Aunty Rahma ce tace”daman kayan fad’an kishiya muka kawo muku. Falmi ta zabura ta mike tace”kayan fad’an me?. Aunty Rahma tace”kayan fadar kishiya ko bakiji bane?. Hajiya ta mik’e tace”ke kale mu daga sama har k’asa waye matsiyaci. “Mai zamuyi da wannan d’an tsiyakon kayanku?. Falmi ta mik’e tare da d’eban kayan ta fara watsa ma su Aunty Rahma. Masu karatu kumin afuwa na rashin jina yau, ina busy ne amma in Allah ya yarda, zan tak’aita labarin nan mugama kafin azumi. Sabida wasu na min message, da qorafin a gama kafin azumi, zanyi iya yina inga na k’arasa, In Allah ya so hakan. Khaleesat Haiydar Novel facebook, ina mik’a godiyata mai tarin yawa, comments d’inku, shi yake k’ara bani k’arfin gwiwa. Whatsapp members kuma ban manta kuba nagode dayawa, Allah ya bar zumunci Ameen. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-116~120. Falmi ba kalan rashin mutuncin da basuyi masu Aunty Rahma ba, amma suka kyalesu suka fita a gidan, batare da sun d’au kayan fad’ar kishiyan ba. Indo ko tun tana d’ari-d’ari da Hajiya har tazo ta sake da ita, sam Hajiya bata d’auketa matsayin surkaba, sai dai matsayin d’iyarta. Hasna ko sai rawan kai aketayi, duk wani d’inkunan da Indo zata saka, ita ta kaita gun telan ta, ya ciremata mayun d’inkuna, masu kyau sosai. Hasna ta gayyato k’wayenta Pinky lady da Cutie, sabida Indo bata da k’awa ko d’aya. Hasna ta samu Sadiq shiya basu kud’in events d’in da zasuyi. Walima suka shirya sai kamu, da fulani day. Sadiq kuma dinner da kuma bikin paret d’in police. Tun daga ran laraba aka fara Fulani Day sun tsara gurin yanda ya kamata, su Hasna da Cutie tare da Amarya sun sanya kayan Fulani, sunsha kyau ba kad’an ba, bare daman fulanin asali ka., ae ba’a cewa komai sai wanda ya gani. Duk wanda ke gurin ya girgije, an raba k’warya masu kyau da ado, sai ludaya da bulogari, da nono kindirmo mai kyau yaji fura, hmm masu karatu ko ni Rash danaje gurin sai dana shaida hakan, ga rawan fulani da yan sandunan su kaika d’auka wani k’aramin rugan Fulani ne. Haka taro ya watse kowa cike yake da murna, bayan sun dawo gida Hasna ke kalon photo da ta d’aukesu a waya, tana yaba kyan da sukayi. Yan’uwan Hajiya na Gombe sunzo duk wanda yaga Indo to sai ya tuna da Lamid’o, dan tabbas baza su mantashi ba sunyi rashi a family d’insu, don duk irin dukiyar da Sarkin Fulani ya tara ace baya da magajinsa namiji, sai Hajiyar su Haiydar kad’ai ta rage masa, wannan abun yasa baya yawan magana da mutane, sabida rashin Lamid’o don duk cikkin ‘ya’yansa yafi sonsa fiye da kowa. Falmi ta kaici ya isheta, da k’yar ta kira su Meesha ta sanar musu halin da take ciki, Meesha ta jin- jina al’amarin nan tace”zanzo sai ran yini don yanzu bana gari na tafi Kaduna. Haka sukayi sallama, Falmi duk ta rame sosai, abunci ma bata iya cinsa mai kyau sosai, baran in ta tuna cewa Yar’aikinta ne zata zama kishiyanta, nan take zuciyanta ya d’au suya da k’una. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM [6/2/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-121~125. Nan take Falmi zataji zuciyarta ya

Chapter 3 of 9